An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[20/10, 7:51 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: *KYAKKYAWAR FAHIMTA*
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 1:
Da misalin qarfe biyu da rabi 2:30Pm na ranar litinin sha biyu ga watan August 2018 hadari ne sosai ya had'o a cikin garin na Abuja Iska se kad'awa take ko ta Ina, garin ya yi duhu qirin kamar gabatowar magariba, kowa ka gani gudu yake yi domin neman mafaka,Wasu daga cikin masu motoci sun gudu sun shige ababen hawan su dan gudun dukan ruwan saman da in ya fara ba a San lokacin tsayawar shi ba, Banda gudun ababen hawa da qarar su tare da hayaniyar mutane da ke d'aga muryar su domin Wanda suke magana da su su Ji su ba abinda ke tashi a wajen.
Gefe d'aya kuma adaidai wannan lokacin ba abinda ya fi mahimmanci a wajen 'yan jaridun mu na qasa da ya wuce son sanin shin ya shari'ar da aka gabatar a babbar kotun tarayya da ke cikin garin Abuja ta kasance a yau?
Major Muhammad Labbo ne a gaban 'yan jaridun da suka tsare gaba suka tsare gefe da gefen shi kamar an fad'a masu matsawa da yawan tambayoyin su ne zai sanya shi basu amsar komai da sike da buqatar sani a wajen shi, a bayan shi kuwa sojoji biyu ne tsaye sai muzurai suke yi suna jiran ko ta kwana su bawa major d'in nasu kariya, gefe d'aya Kuma Barrister Haladu Kangiwa ne shima tsaye cikin cincirindon manema labarai, wata tambaya da aka yi wa Major Muhammad Labbo ne ta Sanya kusan dika manema labarai suka tattare suka koma wajen shi domin Jin kalar amsar da zai basu, cikin kamalar shi da nutsuwar shi ya ke bada amsa kamar haka.
"Kamar yanda mutanen qasar Nigeria suka sani wannan qara da aka gabatar gaban kotu tun 02/03/2018 har yanzu ana ta faman gumurzu ba a kawo karshen ta ba, muna fatan a wannan watan komai yazo qarshe, dangane da amsar tambayar ku Kuma a gaskiya bani da hurumin amsa wannan tambaya duba da cewa magana ta na gaban kotu, bincike da ake ta yi shi ne zai warware komai, ku ci gaba da hakuri sannu ba ta hana zuwa, muna roqon mutanen Nigeria musamman mutanen mu na arewa da mu dage da addu'a har Allah ya fitar da mai gaskiya a wannan shari'a mara gaskiya a yanke masa hukunci daidai da abinda ya shuka."
"Idan na fahimta yanzu kenan dai ranka ya dad'e Major Labbo ka na nufin har yanzu ba a gano wad'anda ke shigo da makamai cikin kasar nan tamu ba har ta'addanci da kashe kashen bayin Allah ya yawaita?"
Kafin ya bud'i baki ya bada amsa, d'aya daga cikin sojan da ke bashi kariya ya bud'a hanya dandazon mutanen da ke wajen duk sun dare Major Labbo ya ratsa ta cikin su ya wuce, Kai tsaye jikin motar shi da aka bud'e masa ya nufa ya shige cikin izza da mazantaka.
Kamar ruwan nan jira yake Major Labbo ya shiga mota nan take ya sauka kamar da bakin k'warya, 'yan jaridun nan kuwa basu da zab'in da ya wuce na su nemi mafaka kada ruwa ya dake su da kayan aikin su, ba tare da sanin 'yan jaridun ba aka fitar da shi ta boyayyiyar qofa aka tura shi mota hannun shi daure cikin sarqar da ake daure masu laifi, a guje motar ta bar harabar wajen, Wanda ya ja hankalin 'yan jaridar da ke ta baza Ido Dan ganin ta Ina za su fito, duk wani yunqurin su na ganin sun Samu zantawa da qasungurmin mai laifin amma inaa hakan ya ci tura, dole suka hakura suka samu mafaka Wasu Kuma suka shiga ababen hawan su suka bar wajen.
Zaune yake cikin kujerar shi ya lumshe Ido ya na tunanin wannan shari'a da ta qi ci ta qi cinyewa, ji yake kamar ya ajiye aikin shi ya huta, abubuwan se qara tsauri suke yi, ya rasa ta Ina complications d'in da ke cikin shari'ar suke zuwa, menene abun wahala? Hukumar rundunar soja ta qasa ta yi nasarar Kama d'aya daga cikin manyan y'an bindiga da ke garkuwa da mutane a jihohin Kebbi,Nigeria, zamfara, da katsina zuwa Wasu sassa na arewacin qasar nan tamu Kama daga Kano Kaduna har zuwa Abuja da shi da yaran sa, amma har yanzu an k'i yanke musu hukunci ana ta d'aga karar tare da Jan lokaci, da alama daga wannan zuwan ba zai sake halartar kotun ba tunda dama son ji da ganin yanda za a yanke musu hukunci ne ke Kai shi ba wani abu ba, hukumar su sun yi iya nasu qoqarin sun gama a matsayin su na Wanda ke kishin kasar su ta gado , yanzu ya rage wa kotu ta zartar da hukunci bisa adalci ko Kuma a bar maganar ta salwanta kamar yanda ake yi a sauran criminal cases da aka Saba yi,tunanin shi ya sake fad'a wa bangaren Wasu daga cikin manyan sojojin qasar nan da ke ta qoqarin danne Wasu bayanai, menene alaqar su da wannan case d'in? Me yasa suka yi ruwa suka yi tsaki a lamarin?
A harabar katafaren gidan nasu motar su ta tsaya, nan da nan ya fita ya sakar wa da drivern shi da ya bud'e masa mota murmushi sanan ya d'aga wa sauran sojojin da suka rako shi gida hannu ya shige gidan shi.
Gate d'in gidan wani soja wanda da alama shi ne me gadin gidan ya bud'e musu suka fita, suna fita ya sauke hannun shi daga qamewar da ya yi, ya kalli hanyar shiga cikin gidan Major Labbo da ke cikin garin Abujan, murmushi ya yi sakamakon jiyo ihun murnar yaran nashi guda biyu 'yan mata har ma da matar shi wadda yake tsananin so da girmamawa.
**************
Zaune yake cikin d'akin da aka rufe shi ya na nazarin rayuwar shi ta baya,fuskar mahaifiyar shi da qanwar shi ce kawai ta bijiro masa a idanun shi a wannan lokacin,wannan ruwan da ke sauka ya fama masa wani miki da ke cikin zuciyar shi Wanda yake ganin da shi zai koma lahira,ya sani Sarai abinda yake aikatawa zalunci ne haramun ne amma shi Kuma abinda aka aikata musu fa? me za a Kira shi kenan?....
'Ajogi bewa do ha banduma asali a yofta anasta sudu sai to feffebe nan gima ko? (Kin riqe akuyar nan a jikin ki kin ki saki ki shigo d'aki se zazzabi ya Kama ki ko?)'
In ji cewar Innah Bad'ejo da ke tsaye jikin ledar bukkar tasu da ke zaune a tsakiyar rugar Chuto da ke garin Katsina,cikin hasala ta sake magana ta ce,
'Shin Addah petel ba da ke nake magana ba? Ki bar akuyar nan ki shigo yau na ji ikon Allah, Muido ka yi Mata magana ko za ta ji ka tunda ni dai ta gama raina ni'
Cikin murmushin shi mai matuqar kyau da kwarjini ya miqe ya d'auki torch light d'in shi ya kafa a goshin shi sannan ya d'auki sandar shi ya rataye addar shi a kafad'ar shi ya samu leda fara babba irin ta buhun sugar d'in nan ya fita cikin ruwan saman da ke ta zuba kamar da bakin kwarya, garken da tumakin su suke ya nufa, ya na taku da sassarfa dan ya yi saurin isa Kar ruwan ya jiqe shi dika.
Shessheqar kukan ta ne ya daki kunnuwan shi, cikin rashin son Jin kukan qanwar tashi ya Isa gaban ta ya durqusa,sannan ya kamo hannun ta guda d'aya ya ce,
'Addaji taso mu shiga cikin d'aki ruwa ya na ta dukan ki, Kar ki yi zazzab'i ni zan zauna na Kular maki da akuyar taki kin ji? Ba zan bari ruwa ya zuba a kan ta ba na maki alqawari'
D'aga kan ta ta yi ta na kallon shi, duk da cewa bata iya hango fuskar shi sakamakon haske ta da touch light d'in da ya yi, amma ta tabbatar Yayan nata ba zai tab'a yi mata qarya ba, duk abinda suke so ita da qannen ta ya na musu musamman ita, dan haka kauda kan ta tayi gefe tare da lumshe idanun ta farare da suka koma jajaye saboda tsabar kukan da ta Sha,baqin idon ta mai kalar brown ya qara haske kamar Wanda aka wanke, se sheqi yake a cikin hasken fitilar, gashin ta da ya Sha qananan kitso duk ya jiqe ya zuba a kafad'un ta gefe da gefe, Wasu Kuma sun zuba a bayan ta se d'igar ruwa suke.
A hankali ta miqe d'an zanin nata da ya jiqe se mannewa yake yi a jikin ta, hannun ta ta Sanya ta na Kare qirjin ta da ruwan saman ya Sanya rigar ta d'ame Mata qirjin nata, a hankali ta miqe a saman guiwowin ta riqe da akuyar tata da take wa laqabi da bewajo am, a hankali ta hannunta Masa akuyar ta ja ta tsaya ta na so ta ga yanda zai bawa akuyar tata kariya a gaban idanun ta.
Da sauri kuwa Muido ya cire ledar nan ya yafawa akuyar sannan ya shiga qasan ledar Shima ya zauna, suna had'a Ido da Addah Petel se ta tuntsire da dariyar farin ciki har da tsallen murna,cikin washe baki Muido ya Mata nuni da hannu ya ce,
'To maza a tafi a cire kayan nan a kwanta ko? Se da safe'
Da gudu kuwa ta bar wajen ta na tsallen murna, bata kwanta ba kuwa se da ta cire jiqaqqun kayan ta ta sauya wasu.
Da safe kuwa haka ta tashi jikin ta ya yi mugun zafi saboda zazzab'in da ta tashi da shi, Muido na can bacci yake da gaske a garken tumaki hannun shi riqe da ledar da ya rufa wa akuya, akuya ta qara gaba ta na cin ciyayin da suka yi kore Shar da su.
Maganin zazzab'i Innah ta ba wa Addah Petel ta Sha sannan ta bata Madara Mai zafi ta Sha ta qoshi sannan ta koma baccin ta.
Shi kuwa Muido se da Baban su ya dawo daga masallacin su dake a rugar sannan ya kula da Muido da ledar hannun shi, kad'a Kai ya yi kawai ya nufe shi ya tashe shi sannan ya ce ya je ya yi alwala ya yi sallah dan kuwa da dikkan alamu bai samu yin sallah ba.
Da sauri kuwa ya miqe ya tafi ya d'auki buta ya wanke bakin shi sannan ya yi alwala ya yi sallah.
Ya na tsaka da shimfid'a abun sallah ne ya ji hirar mahaifan nasa se kawai ya yi murmushi ya tada sallar shi.
'Malam ai soyayyar da Muido ke gwada wa qannen na shi se in ga kamar abun ya yi yawa,ka duba fa ka ga jiya yanda ya kwantar da Jauro na gidan mai gari saboda kawai ya ce ya na son Addah petel, to idan ba a so ta an aure ta ba ya zai yi da ita? Gaskiya ya kamata ya sassauta da yawan fushin nan nashi akan duk Wanda ya rab'i qannen shi,'
'maganar ki gaskiya ne,ni Kai na Ina tsoron yawan fushin nan nashi amma abinda ya fi shine mu had'u mu yi ta yi Masa addu'a Allah ya sanyaya Masa wannan yawan fushin nashi, bari na je wajen mai gari na ji an ce ana neman mu saboda hatsaniyar da ta faru akan burtalin garin Kwano,mutanen yankin sun kawo qara an shiga gonakin su an lalata masu abincin su, na Sha fad'a wa abokan nan nawa idan za mu yi kiwo mu d'iba mu shiga daji cannn ba Wai muna shiga gonakin mutane ba, na Kuma kawo shawara akan idan manoma suka gama kwashe albarkar noman su, mu Kuma su bamu dama da chanun mu mu shiga su ci abinda ya rage, gefe d'aya suna zuba wa filin taki,kin ga wata shekara in an zo se amfanin gonar ya yi kyau,amma kamar kowa na Jin haushin d'an uwan shi ne, kowa kamar jira yake wani ya yi ba daidai ba a fara fad'a'
'Allah ya kyauta, amma Kar ka gaji da nuna masu gaskiya, sannan mu yi ta addu'a Allah ya zaunar da mu lafiya da abokan zaman mu, amma yawan fad'a da ake yi tsakanin makiyaya da manoma abun ya yi yawa Ina tsoron Kar ya Kai ga mummunan tashin hankali a nan gaba'
'Allah ya kyauta ya kawo Mana zaman lafiya a qasar nan Baki d'aya'
A bakin kofar fita daga gidan nasu da suka kewaye da Kara ya had'u da Muido Wanda ke ba wa qannen sa kud'in makarantar Allo da za su tafi, murmushi ya musu tare da shafa kan d'an autan su ya yi gaba dan amsa Kiran da ake masa.
A fadar mai gari kuwa ana can ana fafatawa tsakanin makiyaya da manoma, banda kumfar baki da muzurai ba abinda ke gudana a wajen, mai garin Wanda yake Hausa Fulani ne ya yi iyakar qoqarin sa dan ganin an fahimci juna a sasanta a zauna lafiya amma abun ya na neman ya fi qarfin sa, Wasu daga cikin manoman da suka kawo qorafi fadar ma ba musulmai bane irin arnan nan ne hausawa, shugaban su ne ya miqe cikin tsananin fushi bakin sa na kumfa ya ce,
'Tinda mun kawo Kara ba sau d'aya ba ba Kuma sau biyu ba akan a bi Mana haqqin mu an ki zamu da'u mataki da kammu,zamu kafa qungiyoyin sa kai duk shanuwar da mu ka gani ta shiga gonakin mu zamu kashe ta nan take in yaso duk bala'in da za a yi se dai a yi, ku tashi mu tafi'
Haka suka miqe suka tafi ba tare da mai garin ya basu izini ba, Mahaifin su Maido ne ya miqe ya yi sallama hankalin 'yan uwan sa Fulani duk ya dawo kan shi, Wasu har a wannan lokacin banda masifa ba abinda suke yi, saboda a ganin su manoma sun raina masu hankali ne kawai dan an gan su a daji ba su da ilimin zamani.
'Salamu alaikum Bandirabe,Ina rokon ku da ku bani minti d'aya zan bamu shawara game da abinda yake faruwa, a gaskiyar magana mutanen nan su na da gaskiya,be kamata su gama Chan wuya su yi noma mu Kuma mu bar bisashen(abun kiyo)mu su je su cinye masu amfanin gonar su ba,tinda kun ga dai yanzu damuna ne zamu iya Kora shanayen mu kudu inda ba wani noma suke yi ba sosai akwai abinci sosai, su Kuma nan sanda suka deb'e amfanin gonar su se mu dawo,chanu su ci abinda ya rage sannan su ba wa gonakin su taki saboda noman gaba, kunga idan akai haka za a samu zaman lafiya kowa Kuma zai amfana'
'Kai malam ka rufe wa mutane baki da alama Kai d'an aiken hausawa ne, mutane suna zagin mu suna maganar za su kashe chanun mu Kuma mu taimaka masu da taki?'
'Yi hakuri Modibbo am,ai kafin na ce mu basu takin na yi Wasu maganganu, irin wannan rashin fahimtar ne yake faruwa a tsakanin mu da 'yan uwan mu manoma, bamu fahimce su baaa, ba su fahimce mu ba, amma ba Ina nufin mu basu takin kyauta bane, su bamu gona chanu su cinye sauran hakukuwan gona ka ga mun amfana su Kuma chanu su yi Kashi su basu taki'
Haka aka dinga cece kuce a fada ba a samu matsaya guda d'aya ba, abin farin cikin guda d'aya shine kusan rabi da kwatan mutanen garin sun bi bayan maganar mahaifin Muido, Dan haka sun yi Shirin Sanya ranar sake yin wani taron tsakanin su da manoman Dan a samu maslaha tun kafin su fara tab'a shanun 'yan uwan su azo ana rigima..............
*Assalamualaikum makaranta littafan HAERMEEBRAERH Kuna Ina za a fara sabon zubi babu ku? To ga sanarwa zuwa ga masoya na masu qaunar rubuce-rubuce na da son ci gaba na, wannan labarin kamar da damar labaran da na Saba kawo maku ne domin kuwa shima labari ne na gaskiya,Wanda ya samu 'yan gyare gyare saboda saya wasu abubuwan,labari ne mai tsada ba wai tsadar kud'i ba, tsada ta fuskar abinda ya qunsa, Ina mai maku albishir da ba za ku yi danasani ba kamar yanda a baya ma ba kuyin danasanin karanta labaran da nake kawo maku....za ku biya #500 ne kacal domin samun labarin tun daga farko har zuwa qarshen shi Nan da wani d'an lokaci sai na ji ku*
*Dan neman qarin bayani ku tuntub'e ni ta wannan No 09031416423.*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: *KYAKKYAWAR FAHIMTA*
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 2:
Kamar abun Wasa washegari da safe kowa na hada hadar shi wani maqocin su Muido ya shigo rugar tasu a guje ya na kuka ya na burgima da ihun a je a taimaki shanun shi, Banda fulatanci ba abinda yake sakewa,tsabar tashin hankalin da yake ciki ko d'igon hawaye babu a idanun shi, da kyar Mahaifin Muido ya samu nasarar Sanya shi ya natsu ya yi masu bayanin abinda ya faru, cikin fitar da numfarfashi bafulatanin nan ya ce,
"Sabi'u am chanu na sun halaka, an kashe min Chanu na da tumaki na shikenan maganar sulhu tsakanin mu da manoma ta kare, jiya jiya ka ke bamu chawara mu je a daidaita da manoma Kuma na yi na'am da hakan amma suka kashe min Chanu"
"Assha ! Ashha ! Amma wannan lamari be yi dad'i ba, yanzu dai ba lokacin ganin laifi bane, mu je mu ga barnar da aka yi maka se mu je wajen mai gari"
"Aradun Allah se na da'u fansa, aradun Allah ba zan hakura ba Sabi'u"
"Ka yi hakuri, amma tabbas ba su kyauta ba, da ka sani Kai ma da baka je gonar su ba tunda mun tsayar da magana za mu je a sake zama a yi sulhu, daure ka tashi mu je fada"
Su na Isa suka tarar da Wasu mutane uku Suma sun Kai koken an kashe masu ababen kiwon su, nan da nan kuwa Mai gari ya bada rashin gaskiya zuwa ga Fulani ,tunda da ba su saki shanun su sun shiga gonaki ba da ba a kashe masu su ba, duk bayanin da Wasu mutum biyu ke yi na cewar su fa tafiya kawai suke manoman suka far masu suka dinga saran dabbobin su ba tare da sun ji ba ko kuma sun gani ba, haka Mai gari ya toshe kunnen sa ya ba su rashin gaskiya, wannan abun da ya yi kuwa ba qaramin Sosa ran Fulani ya yi ba, har suka fara zargin ko dan asalin Mai garin ya had'a dangi da hausawa ne ya Sanya shi tsaida rashin adalci a gare su.
Haka fada ta tashi ana ta hayaniya,duk jikin Malam Sabi'u ya yi sanyi har ya Isa gida,Muido na dawowa da qannen shi daga islamiyya Mahaifin sa ya labarta masa komai, akan abinda ke faruwa, sannan ya umarce su da su dinga kiyaye Kai ababen kiwon su wajen da bai dace ba.
Abinci suka ci suka Sha ruwa Muido ya zauna sassaqa wa Adda Petel da Sa'ade 'yar tsanar icce, gefe d'aya kunnen shi na jiye Masa duk wata hirar da iyayen nashi suke yi,ba zato ba tsammani ya ji maganar mahaifin shi na fad'in,
'Bad'ejo ni fa ina tunanin anya ba za mu sauya wajen zama ba? Tsaro da kwanciyar hankali sun yi qaranci a wajen nan, gamu da Yara qanana Ina Jin tsoron wannan rikicin da aka fara Kar abun ya yi tsanani kamar yanda akai waccan shekarar'
'Malam kamar ka shiga zuciya ta, Ina matuqar Jin tsoron yanda na ji kana bada labarin hasalar da mutanen mu suka yi akan wannan lamarin,gashi Suma bangaren makiyayan ba dama'
'Allah dai ya yayyafa wa wannan lamarin ruwan sanyi, gobe zan ga yanda za a yi in shaa Allahu'
'Allah ya Kai mu'
Malam Sabi'u ne ya juya ya kalli Muido da ke miqa wa Addah Petel 'yar tsanar da ya sassaqa Mata ya na tsokanar ta da babbar banza, Yara su yi Wasa da 'yar tsanar itama ta yi,cikin kulawa Malam ya kira sunan Muido ya ce,
'Ka na ji na ko?'
'Eh Baffah Ina Jin ka'
'Nashe gobe Kar a fita da chanun nan ko Ina Kai ma Kuma ka samu waje ka zauna da qannen ka a gida Kar ka je ko'ina mu jira mu ga me zai je ya zo'
'To Baffah Allah ya kaimu'
Da haka suka ci gaba da hirar su kafin daga baya kowa ya kama abinda zai yi.
Washegari da asuba Malam Sabi'u ya dawo daga masallaci ya ga rugar ta yi shiruuu ba mutane a waje sosai, jikin sa ne ya yi sanyi, sannan ya qara tabbatar wa da kan shi barin wajen nan shine ya fi alkhairi a wajen shi da iyalan shi, dan haka da ya Isa gida za su fara Shirin tashi daga rugar.
Tunda ya koma gida suka fara Shirin barin ruggar shi da Innah Bad'ejo da Addah Petel, shiru ba labarin Muido ba alamun sa,tun hankalin su bai tashi ba har suka fara damuwa, suna tsaka da loda kayan su Saman jakunan su suka ji hayaniya, da gudu Malam Sabi'u ya leqa garken shanu inda suke killace masu cikin wajen ya ga bai ga ko d'aya a cikin su ba, salati ya buga Dan kuwa ya fahimci yanzu inda Muido ya tafi, da gudu ya bar wajen ya Isa bukkar su, saidai ya na zuwa idanun sa suka yi Masa mummunan gani, Dan kuwa matar shi ce da 'yar sa da ya fi so kaf cikin yaran sa kwance a qasa, Wasu Karti na saduwa da su a fili ba ko rufi ta qarfin tsiya, nan take ganin shi ya fara d'auke wa, Jiri ya hau diban shi zai fad'i,ihun Addah petel ne ya qarasa Kai shi qasa, zuciyar shi ta buga ko shurawa bai sake yi ba.
Manoman nan Wanda suke arna ne tuni suka gama yi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12