na shigo", shi ya sa na gaisa da kowa harda
tsarabar lemo da ayabar da na yiwa Innata, kuma
na je na sanar da ita halin da muke ciki da karima,
ban nuna mata ance ciwon ya yi tsanani ba, a'a
abin da na nuna mata ina son taje saboda Mairo ta
samu ta dawo itama gida gurin 'yan uwanta
innata tace "to duk da kince Bilkisu tana wahalar
komai amma bazan je hannu haka ba don haka
dole tafiya sai jibi, don zan tsaya gobe in siyar da
ragunana guda biyu in yazo ko kudin abincine an
samu.
Da sassafe aka dau raguna zuwa kasuwar
mubi, tausayin inna kawai na ke, wanda saboda
ba bu wanda zai maka wannan sai uwarka, duk
wanda yace sai raba tsakanin da da mahaifi ya
hada kansa da wahala ga irin rashin kulawar da
karima tayiwa Inna, tunda inna ta dawo mubi a
'ya 'yanta kowa yazo ya ganta ban da karima,
amma yanzu ance da inna karima ba bu lafiya har
tana yunkurin siyar da kadararta don so, ni ina
-57-
zaton inna tafi son karima fiye da kowa a 'ya
'yanta, gaskiya ne da ake cewa yawancin mutane
sun fi son wanda baya kulasu.
Sai wajen karfe biyar na yamma aka dawo
daga kasuwa, duk da girman ragunan nan ba su yi
tsadi ba sosai, don duka kudin dubu goma sha
biyu ne, wanda idan lokacin layyane sai dubu ishirin-ishirinm, haka inna ta kulle kudin nan,
washegari da safe kárfe shida mun bar gida,
munyi sa'ar mota karfe bakwai dai dai muka iso
Abuja, sai da muka tsaya a Yanyan tun da kan
hanya ne sanna muka wuce hospital, Mairo tana
zaune tasa karima a gaba tana ta faman jan carbi,
ita kuma an sa mata ruwa tana ta faman barci. Na
lura hankalin inna ya tsahi- matuka yadda taga
karima ta dawo, ni da mairo mun rufeta da dadin
baki ta fara samun sauki don yanzu tayi kiba, a na
haka wayar Bilkisu ta shigo, bayan mun gaisa na
ke gaya ma ta mun zo da inna tace "to za ta zo da
dare ita da Abdul dinta, ya dawo tun ran da na tafi
mubi. Bayan mun yi sallama ne Mairo ta ke gaya
min jiya maman Bilkisu da babanta sun duba
karima sunje sun sami likita sun ce duk abinda ya
taso ya yi musu waya, Mairo ta nu na da hannunta
tace "ga kayan da suka kawo can", na je na janyo
leda kifin gwangawani da lucuzed da kayan tae.
Wadan nan mutane mai za muce musu sai dai
Allah ya sa albarka, Allah ya kara arziki.
Tun da aka yi sallar magariba inna ta yiwa
-58-
Mairo godiya tace "tafi gida, Amina ta raka ki"
Mairo ta ce "ba bu komai inan jima matar kaninta
za ta zo don jiya ma sun zo sun ce za su dawo yau,
in sun dawo ma tafi tare. Kuma godiya da kike ai
da na kowa ne, fatan mu dai Allah ya bata lafiya
kawai." Yau naga Abdul din Bilkisu wanda aka
cikani da labarinsa yana can America yana karatu,
sai yanzu ya gama. Bilkisu kowa ya ganta ya san
tana cikin murnar ganin Abdul, daga ganinsa
mutum ne mai tausayi don ya tausayawa karima
sosai har yana cewa Bilkisu kamata ya yi a fita da
ita waje don su suke da kayan aikin irin wannan
ciwon. Sun je sun sami likita, anan yake gaya
musu daman yace tuntuni idan bamu da kudin fita
waje to za'a yi mata aiki don yanzu haka sun bayar
da kudin a yi mata aikin a gani in babu sauki sai a
fita da ita. Yau alhamsi don haka yau saura kwana
hudu kenen a yi aikin. Mairo ta koma gida sai dai
tazo ta wuni, mu kuma mun dukufa ga addu'a
Allah yasa a da ce kullum Sadiya za ta zo ta wuni
amman Hađiza sam sai dai tazo ta gaishe da inna
ta wuce wai karta dauki ciwo, ba na ganin laifinta
don idan karima ce za ta yi mata abin da yafi haka.
Biliksu da iyayanta da masoyinta suna ta ci
gaba dayi mana dawainya. Har yau karima bata
san inna ta zo ba don tana bude idonta lokaci
lokaci amma sam ba ta gane mutane.
Ranr hittinin da safe aka shiga da karima
tiyata wanda a daren ni da inna kwana muka yi
59-
muna Addu'a. Abdul din Bilkisu shi ya biya kudin
duka, tun bakwai likita ya zo, muna zaune bakin
kofar dakin har san nan likita ya fito sauran
ma'aikata suka janyota aka je aka kwanatar da ita
a wani daki, suka ce mu kyaleta nan da awa biyu.
Karfe daya dai dai wata ma'aikaciya tayi kiran mu
muka zo muka tarar da karima tana ta faman
shure-shure na fita da gudu na kirawo likita yace
"babu komai za ta dawo dai dai, idan allurar ta
saketa" Bilkisu ta bugo waya "yaya jikin
karima?" nace "Bilkisu ga ta nan an mata aiki
amma bata farka ba" tayi mana Allah ya sauwake,
ba za ta samu damar zuwa ba saboda saura two
weeks, don haka za su wuce Dubai ita da innarta
za suyi kwana hudu. Na yi-mata godiya da fatan
Allah ya dawo da su lafiya.
Karfe biyar na yamma sai ga sadiya da
Muhammad, Usman, Isah da Ibrahim duk ta nemo
su ta gaya musu Inna tazo ga kuma halin da
karima take cik, i naka-naka ne inji bahaushe yace
ko ba zai baka kamai ba, duk kanin su duk da maza
ne sai da idanun su ya yi ja sobda halin da suka
sami karima duk da an yi mata allurar baccі,
saboda rashin dawowarta dai-dai shi ya sa har
yanzu ba'a cire mata rigunan tiyata ba, basu bar
asibiti ba sai da aka yi kiran sallar magariba,
munyi sallam da su akan za su da wo washegari da
safe.
Tun karfe ukun dare bacci ya kaurace
-60-
mana saboda bige-bigen da karima take likitocі
uku ne akanta, amma abin ya faskara, can wajen
biyar saura karima ta farka kamar ciwon ya tafi,
ba bu kowa sai ni da inna, ta budo ido tace "inna
yaushe kika zo, don Allah ki yafe min na san ban
kyautawa kaina ba, ni na kwasowa kaina ciwon
nan, na san mutuwa zan yi ba bu wanda ya iya
magana sai kuka, da karfi karima take magana
kamar nace mata rage murya, duk Kalmar
shahadar da nake mata wai ta fada, amma ya
gagara a bakinta iyakacinta da tace mu yafemata
karfe shidda saura dai-dai karima ta daina shureshure tayi shiru sai kunfa da take fita daga bakinta
na ruga na kirawo likkita, ya na zuwa ya yi 'yan
aune-aune yace "to Amina sai ku yi hakuri.
karima ta rigamu gidan gaskiya, Allah ya jikanta"
sai naji kunnena ya na gaya min ba dai-dai ba, don
haka yana fita naje na sake kirawo wani likkitan,
yana taba ta ya ce "oh Jesus karya ne, babu inda za
ta", shi ne kuma wanda ya yi aikin ya tsaya yana ta
faman ma ta Addu'a irin tasu. Hankalina ya dawo
jikina sosai na gane wan can doctor Muhammad
gaskiya ya gaya min, karima ta mutu shi wannan
yana son dulmiyar da ni ne, don haka na fita na
gayawa su inna babu karima, inna ta shigo da
sauri tasa zani ta rufe gawar, naje na sami doctor
Muhammad na ce "don Allah ya zo ya sa hannu a
bamu gawar kar ace sai ankaita mutuware," ba a
ata mana lokaci ba ya sa aka hada mana komai
61-
aka bamu, motar asibiti din ciki aka saka gawar.
Allahu Akbar rai bakon duniya muduba muga irin
sharholiyar da karima tayi lokacin rayuwrta,
babu wanda zai ce ya yi farinciki da rayuwarta. A
dalilin karima inna ta hadu da hawan jini, gaskiya
kukan da nake ba kowa nake waba sai kaina,
yanzu mutum ya yi mutuwa irinta karima, a
rayuwar duniya ace babu abin da ka fuskanta dan
gane da lahirarka?, to me zaka cewa
mahaliccinka?.
Ni dai abin da ya tsoratar da ni haushin
karan da na ji Karima tana yi ka fin ranata ya fita,
tun daga duniya ma ke nan a zatona karima ko
sallah ba tayi don tunda na ke da iťa ban taba ganin
tana sallah ba, gaskiya duniya ba abun shagala
bace, yanzu ta tashi tun tana karamarta tana
faman bin samari, to yanzu a sakamakon da suka
bata tunda sun hadata da ciwon da suka aikata
lahita ba shiri, abin mamaki inda zaka kara tsorata
da duniya tun da karima ta kwanta ciwo samarinta
har mugayen kawayen nata duk sun kai ta sun
baro.
Innace ta katse min tunani tace "to sakko"
muka sauka aka dauko gawar aka shiga da ita,
Hadiza da Sadiya suka kwalla kara, nan da nan
mutane suka cika gidan ana ta faman kururuwa.
Babbab abin da ya fara damu na a ranar, jahilci,
daga ni har inna babu wanda ya iya wankan gawa,
mutane kuwa da suka cika gidan duk yawancinsu
-62-
arna ne, da farko shamsu ya je ya kirawo wani
malami yazo ya gwanda mana, ya tafi ya siyo
likkafani nan fa ya tafi ya barmu da gawa ba mu
san yadda zamuyi mata komai ba.
Can sai ga kungiyar su muhammad gaba
dayan su kamar yadda suka zo asibiti, inna tace
kuzo kuyimata wankan gawa, muhammad ne ya
fara magana yace "gakiya ban san yadda ake
wankan gawa ba", su Ibrahim ma kowama
yagirgiza kai anan Shamsu yace ai akwai wata
tsohuwa ana biyanta dubu biyar, idan namiji ne
dubu goma, don haka idan da kudi sai ya je cikin
maraba ya kirawo ta. Inna ta dauko kudin taba shi
tunda kudin ragunnata babu abin da ta yi da su,
mun fi awa daya da gawa a gaba ba bu shamsu ba
bu mai wankan gawa, malamin daya kwadata bai
dawo ba daga dinkin likkafani ba, sai arna ke ta
faman yi mana ife-ifen, can muhammad yace
"yana zuwa" minti isirin bai yi cikkake ba, sai ga
shi da mahaifinmu, wanda gurin kowa ya yi tsit
har arna da suke faman ife-ife, ko baka sani ba
kasan shi ne mahaifinmu, tunda duk inda kama ta
ke to su na kama da Karima mai mutuwa da kuma
Muhammad, don haka duk arnan suka fita suka
bar dakin dagamu sai shi, sai kallon-kallo suke
shida inna, ya yi shigar manyan kaya shaddace
tasha aiki bulu, hularma kalar kayan, banda
siraran hawaye babu abin da yake, mu kanmu ya
samu kukan wiwi, yauwa da inna ta kawo masa
63-
را
ruwa mai dimi zai wanketa Muh'd ne ya hado
ruwan, yace “baba ka koyawa inna ta wanke ta"
yace "ai wankan gawa kamar wankan tsarki
yake, sai dai shi ba'a niyya, don haka ke da Amina
za ku iya." Sai da muka kusan gama wankan
gawar, sai ga matar wata wujiga-wujiga da ita,
ganina ko sallar ta bata cikawa, na godewa Allah
da mahaifinmu ya wanke mana jahilcinmu, ya
kawo turare ya gwada mana duk inda za mu
sakamata, malan mai likkafanin ya kawo aka
sakata, mun shiryata tsaf nida innata duk zuciyata
ta bushe kukama da nake na daina sai kokarin a
kawar da ita kawai nake.
Babu wasu mutane su shamsu ne da
abokan hirarsa, sai mahaifinmu dasu
Muhammad, sun yi shinfida za suyi mata sallah da
su kazo daukar gawar ne mahaifinmu ya dafa
makarar yana kuka yace,
"Karima Allah ya yi maki gafara".
"Ya Allah ka daukaka darajarta a cikin
shiryayyun bayi, ya Allah ka gafartawa karima
zunubanta wanda ta sani da wanda bata sani ba, ya
Allah kar ka tuhumi karima da laifin da ba ta da
masaniya aka shi, ya Allah ka haskaka mata
kabarinta, Allah duk sabon da karima ta yi maka
ni na jefata ciki, ina rokon ka da ka yafe mana baki
daya, ya Allah ka wanke karima daga laifuffuka
kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga dauda, ya
Allah ka tseratar da ita daga fitinar kabari da
-64-
3
t
Π
1.
+
f
L
azabar wuta."
Mahiafinmu yana wannan addua'ar yana
kuka haka su Muhammad, suka fita da gawar, aka
yi mata sallah. An dau karima zuwa gidan
gaskiya!, Allah! Ka kyauta namu zuwan, Allah
kasa mutuwar karima ta zama sanadiyar shiriyar
danginmu baki daya. Mahaifinm shi ke jigilar
kawo abinci kullum, tun bakwai na safe yake
zuwa sai bayan sallar Isha'i ya ke komawa gida,
ban da akin kuka ba bu abin da ya ke, na san kukan
ba ya wuce mutuwar Karima, minti ashirinashirin yake shigowa ya na tambayar inna me
muke bukata.
Ranar sadakar uku, ranar Binta ta zo, kuka
ya dawo sabo don ta dawo da mutuwar kamar
ranar aka yi ta, tunda ita tafi kowa dadewa ba ta ga
karima ba. Mutum ba'a bakin komai ya ke ba,
jahilci shi ne ya sa muke daukar kanmu komai,
kalli duk yadda karima ta shiryawa kanta jin dadin
rayuwa, ta sa kayan da taga dama, kullum kanta
cikin gashin doki, don kwalliya kawai Jakarta
cike take da kayan kwalliya, ba ta awa daya ba ta
fito da madubi ta yi kwaliya ba don jin dadin
duniya, yanda karima ta jiyawa kanta dadi ba ta
cin abinci in ba mai dadi ba, dai kusan karima sai
tayi wata ba ta cin abinci in ban a restaurant ba,
babu abin da ta tsana irin zafi, kullum cikin raba
take, don in ka ganta a gidanmu 'to şamirin nata
basa nan ita kuma bata da kudin zuwa Hotel din,
-65-
yadda kawaye suke binta kai kace wata matar
wani sarki ce. Amma abin mamaki, karima ta
kwanta ciwo har sati biyu ba wanda yazo, gashi ta
mutu har yau daga samrin har kawayen babu
wanda ya leko, ni abin da yake bani mamaki ma
shi ne, irin kayan da karima take sawa masu
tsadar gaske, amma yanzu babu ko daya ina
kyauta ta zatona kawayen nata suka kwshe, tun
dama komai nata yana gurin kawarta Habiba, tun
dama ta kawo man ita har yau bata dawo ba.
Gasikiya duniya gaba daya rudu ce, ga shi
dai yadda ta rudi karima. Babana ya katseni yace
"Amina sai hakuri, kunyi rashin 'yaruwa, Allah
ya ji kanta" Sadiya tace "Baba yanzu kana ina?
kasan gareji kawai muke haduwa", ya ce "Sadiya
mantawa ki kayi nace nan bayan garejin gaidana
ya ke, ai ranr bakawi duk zamu tafi can Insha
Allahu." Mahaifinmu yake tambayar Inna ina
'yar ginda karima? Inna tace "tana can gidan
marayu, da na daukota daga baya na ga wahala
tayi min yawa na mayar da ita, idan tana nan zan
ganeta".
Ranar kwana bakwai da sassafe
mahaifinmu ya zo akayi Addu'a kowa ya kama
gadansa, ya rage daga mu sai baba da inna.
Mahaifinmu ya shigo ya zauna kusa da inna ya
ringa kuka sosai wanda ko randa ta mutu bai yi
irin sa ba, duk muna zaune muna kallonsa, inna ta
tashi tace ita zata wuce Mubi kar dare ya yi ma ta.
-66-
Babanmu yace "dan Allah Amina kiyi hakuri
karki wuce, yau kukan da nake na godiya ga Allah
ne da ya sa ban mutu ba ku ma baku mutuba, zan
rokeki gafara akan abinda nayi muku, nasan na yi
jahilci kai na kuma na yi sabo babba na wulakanta
baiwar da Alah ya bani na rungumi wacce ba tawa
ba. Amina cuta na san na cuce ki kuma duk wanda
ki ka ji ance ya yi hakuri to an cuce shi ne, don
haka nasan na cuceki don Allah ki yafe min, nina
batawa yarana rayuwarsu, saboda na barsu cikin
yunwa, rashin sutura, kishirwa duka don haka
dolene suje suyi ko meye, babu yadda mutum zai
rayu babu daya daga cikin waddan nan ballantana
su babu duka ma. A rayuwata arziki bai karamin
komai ba sai halaka, don haka kullum Addu'ata
Allah yabarni da talucina saboda na samu rabo
babba.
Annabi (SAW) da kansa yace "Mu nemi
tsari da talauci don haka to ni ban ji dadin arzikina
na fi jin dadin talauci don haka zan iya cewa
talauci shi ne arzikina tunda shi ne na ke sa ran zan
sami rabo babba dashi, Amina na wulakanta ki ke
da 'yanuwanki lokacin da kuke tsananin bukata
ta, amma da Allah ina rokonku da ku yafe min,
rudin duniya ne da sharrin shedan yanzu na canja
nagane na sake halina.
Kowa ban ji kowa ya yi magana ba sai Sadiya ce tace "baba yanzu baka da mata?" yace
"Sadiya bani da mata, mum dade da rabuwa da
67-
Igala, wanda itace sanadiyar rabuwa daku gaba
daya, tun lokacin da aka koreni daga aiki, ta
kwashe min kudi masu yawa, kafin ta kwashi
kudin sai da ta siyar da motocina, duka san nan ta
kwashe mini kudina na America, wanda sune
arzikina, inaga da Kudin nan suna nan ya isa nayi
wani company nawa na kaina, a garin komai sai
da ta rabani da komai, duk da gidan da take ciki
siya ma ta nayi, ta siyar ta gudu garisu, har dan da
muka haifa su duka, baifi sati uku da suka wuce ba
ta aiko wani dan uwanta da ya ke garin nan da
wasu wai dan ya mutu."
Yadda aka yi na sai gidan da nake ciki don
lokacin duniya juya ta min baya kuma kay abasa
tsada don na siyar da kujeruna da kayan kallona,
gadona kawai na bari nazo na siyi wannan gidan,
abokai na duka sun guje ni duk cikinsu babu
kamar. Buba, tunda shi ya fi kowa sani na, don
haka, da ya ga yadda na yiwa iyalina ya fita
harkata, ya na gani aka koreni daga aiki shi kuma
sai da lokaci gama aikisa ya yi, don haka na tsane
shi, nace ko yaje ya fadawa manyan mune, sai
daga baya na gane sam ba haka bane hakkin
iyalina ne ya kamani.
Na dawo abin tausayi a cikin Abuja tun da
abincin da zan ci ma ya gagare ni, yanzu dubi
yadda na dawo, ni ba almajiri ba ni ba mahaukaci
ba, sai na yi kwana biyar ban yi wanka ba, bani da
kudin sabulu bani dana abinci. Haka na ringa
68-
rayuwa sai da nayi kusan shekara a haka naga
zama ba zai kaini haka ba kullum ina cikin gidan
ina kuka kamar mace na fito gareji gurin masu
mota, a nan naje na sami ogansu nace ina son ya
taimakeni ya bani aikin da zan ringa yi ya na
biyana, yace shi gaskiya na yi girma duk
ma'aikatansa yara ne, don haka ba zai daukeni ba.
Makocina wanda gidana ya ke jikin nasa, yana da
shago a kasuwa naje na zauna a kofar gidansa ina
jiran ya dawo, yana zuwa ya ganni a kofar gidansa
yace "malam Abubakar lafiya?" nace "ba kalau
ba", ban boye masa komai ba na gaya masa
bukatata ta son na ringa binsa kasuwa nayi masa
yaron kantinsa, yace "ai ni ca nake ka na da aiki"
na ce "gaskiya da ina da aikin yi, ritaya suka yi
min, shi ya sa nazo na sai gida acan da kudin da
suka bani gaba day."
Ban ce masa korata aka yi ba, don kar ya ce
wani laifi ne ya ji tosron taimaka mini, yace "babu
komai malam Abubakar, Allah ya kaimu gobe, sai
ka shirya muja kasuwar a gwada a gani, ka san
komai sa'a ne, idan Allah ya sa anan abincinka ya
ke shi kenan."
Washe gari da safe muka tafi kasuwa,
sunansa Alh. Idris, shagonsa ya na cikin babbar
kasuwa, ya na siyar da atamfofi da shaddodi, idan
an zo ni na ke dauko kayan ina siyarwa, a haka
nake samun kudin da zanci abinci da sutura. Mun
kai wajen wata shidda dashi a haka, har ya fara
-69-
bani kudi ina zuwa kano ina masa sarin kaya, to
yanzu duka baifi wata hudu ba da ya bude min
wani shago anan kasuwar Garki, yanzu hakanma
yadda muka yi da shi idan Allah ya buda nim,
kantin ya na son na ringa biyansa kayansa na
mallaki kanti. Tun da muka hadu da Alh. Idris
yadda ake zuba masa abinci a gidansa haka nima
nake da kwano, dan haka ba bu abin da zan ce
masa sai Allah ya saka masa da alheri." Duk gaba
dayanmu mukace Amin.
Mahaifinmu ya kalli inna yace "Amina ya
kamata kizo muje gidana gaba daya in ya so sai ki
koma mubi, ku kuma kowa ta kwaso kayanta mu
koma can", ya kalli mazan yace "haka kuma
akwai dakin maza banda kải Muhammad da
Ibrahim tun da kuna da mata" Usaman yace "baba
nima ina da mata"yace "to me ya sa baka kawota
gidan mutuwa ba" ya sunkuyar da kai yace abin da
yasa ba musuluma bace" mahaifinmu ya dafe kai
yace "usman bą ta sallah kwata-kwata" ya daga
kai alamar E baba yace "to mai ya sa ba ka yi
kokarin ka ga ta musulunta ba? 'ya 'yanku
nawa?" yace "yaron mu daya Salwa ko shekara
biyu bai cika ba", baba ya ce "ba bu komai muje
dai can gidan nawa zanyi bincike baba yace babu
komai muje dai can gidan nawa zanyi bincike
akan abin." Inna tayi shiru abin ya bata mata rai
sosai, don kowa zai ji a ranasa sai ya zo ya sami
Inna ta zo bikin amma babu wanda bai kai matarsa
-70-
Mubi amma ban da Usman, ya na da aure har da
da, a gakiya abin ya bata mata rai don haka ko
magana ta kasa. Mun rankaya gidan mahaifinmu
da kafa tund nan cikin Yanyan ne, ni kadai ce
daman ban san gidan ba sai Binta da bata gari,
cikin rufin asiri ba bu abin da bai saba a gidan,
dakuna ne guda hudu, biyu a hade da falo da
bandaki, kitchin ya waje a tsakar gida, da kansa
yace "duk ginin nan daga baya ya yi su, don haka
kullum addu'arsa Allah ya kawo masa ranar da
zai hadu da iyalinsa.
Ya sa aka je gidan abinci aka kawo mana
abinci har da lemu, kowa ya fadi abin da ya ke so
aka kawo masa, dadi ya ke ji ko Inna ma da take
daure fuskarta nasan tana jin dadi a ranta, tana
haka ne don karta nuna masa ko kuma ta tsoro ne
kar a kuma, bayan munyi sallah ne Inna tace "ya
kamata mu tafi", to anan usman yace wai gidansa
yana nan bayan gidan mahafinmu, Inna ta so mu
je, muka kama hanya mu duka Allah ya jikan
karima da tana nan da yanzu tayi fada da wani.
Takun da muka yi kadan ne, matar usman
mai suna larai, daga ganin matar kasan suna
wahala, larai mutuniyar kirki mijin ne dai,
Asalinta 'yar kaduna ce arniyace, saboda usman
ta musulunta, inda Allah ya kama usman mun
sameta akan abin sallah, duk 'yan uwanta sun
gujeta saboda ta koma musulma, don haka yanzu
bata zuwa gurin kowai sai usman, tabbas ba sai
-71-
mutum ya tambaya ba ka san usman ya na
zalintar larai, daga ganin aikin Usman
makanikane, tun yana yaro ya ke da tabe-tabe,
har Allah ya hada shi da wani uban gida na kirki
ya koya masa aikin sosai, Usman yana samun
alheri sosai amma da gani baya wadata iyali,
babu wata alama anci abinci a wannan gidan,
daga dakin kadai zaki tabbatar, saboda ba bu ko
shimfidar kirki a cikin dakin, ciki daya ne da falo,
falon ko leda ba bu, bạn da halin tsiya irin na
usman tun da ka rabata da kowa nata aika san
baza a yi mata Komai ba, shi ne ka barta cikin
wahala. Ba dan yana son Salwa ba ya sata a
makaranta mai kyau ya siyamata kaya masu
tsada, da sai nace Usman ya gaji mahafinmu.
Usman kuka ne kawai bai yi ba ranar,
saboda fadan da mahiafinmu ya yi masa, babu
abinda ya batawa mahaifinmu rai irin yadda ya
bar falonsa babu ko leda don shi babanmu tunda
yakema ya na son tsafta, wata al'adar banza da
yake kullum idan zai fita sai ya bada kudin abinci
'yar iţa kuma uwar gari zata jika tasha, 'yar kuma
a siya mata abinci mai kyau uwar kuma oho, ka ji
azzalimi.
Ranar dai yaga fada iri-iri don saida baba
yace ya je ya dauko duk kudin da ya aje ni kuma
ba haka ya nuna masa karuwa sa, yace shi baya
nema mata, da aka matsa masa yaje cikin dakin
matar ya bude cikin kayansa ya dauko kudi har
-72-
1.
Π
1
1
1
dubu dari da goma, kaji macuci nanfa akan karkashi daga Muhammad aka rubuta komai, kujeru,
leda, kayyan abinci, sabulun wanka dana wanki,
katifa tun da gadon babu katifar kirki itama laran
kayan sawa, ya na ji ya na ga ni aka ba muhammad
da Isa suka tafi siyayya, muka kama hanya
mukabar gidan, matar har kuka take don murna,
baba ya ce "daga yau ni ne ubanki, ki rabu dasu,
kar ki fasa yi musu biyayya addininsu ne dai kar ki
yarda ki shiga", har muka fito inna bata yi magana
ba. Muka kama hanya zuwa tsohon gidanmu da
niyar washe gari zamu je mubi mu duka, karfe
bakwai Muhammad da Ibrahim sun zo da
matansu, matar Muhammad Rashida da man mun
santa ta na zuwa zaman makoki, yaran ne bamu
taba ganinsu ba, Abubakar da Amina watau baba
da inna, daga ganin Muhammad kasan yana
rayuwa mai tsafta da iyalinsa.
Ibrahim ma ya kawo matarsa umaimatu ita
ma daman mun santa kyakkyawar gaske ga kunya
kamar mijinta, don kullum tazo bata iya hada ido
da inna, duk tsokanar da za muyi mata bata
tankawa, baba ya zo da Isah tun da daman tare
suka tafi, har an hakura da jira za'a tafi abar shi sai gashi yazo da matarsa Usman, inaga haushin
kudin sa ne ya sa da bazai zo ba oho masa.
Duk mai sonmu yayi murna da ganin mu a
mubi, baba yaje gurin manyansa, anzo an hadu da
kannan inna wanda take gurinsa, an mayar da
73-
AUREN INNA DA MAHAIFINMU, ranar
asabar da safe kofar gidan su inna ko in ce kofar
gidan kannenta duk murna muke, ita dai inna
gata nan ni na tambayeta nace "inna me ya sa
bakya murna?" tace "gaskiya uwani ba dan ku
ba, ba bu abin da zai sa na sake auren wannan
mutumin, ba bakya ganin idan kudi suka shigo
masa zai sake wulakantamu?" Ni na rufeta da
nasiha na ce "inna kamar ki kawo wannan a ranki
da fa ace ya ji dadi ne, kigafa-har yanzu ba da
hakuri ya ke, ya na nadamar abin da ya yi, ki ji fa
irinwahalar da ya sha a baya, insah Allahu wanna
zaman na har abada ne, muma mu koma gidan
ubanmu muyi aure koma samu namu 'ya 'yan",
har na sa inna tayi murmushi tace "Allah ya kawo
na gari", su Hadiza suna can suna faman yawo,
mahaifinmu ya shiga dakin inna, na tashi na bar
shi da amarya da ango su sha hira. Kwananmu
biyu a mubi, san nan muka koma gidan
mahaifinmu, ya yi mana dinkuna daga mu har
inna, abinci kala-kala ba ka tunanin matsala