ya kai
karar babanta" Usaina ta kwala ido alamun bata
san komai ba, tana masa rantsuwa mamanta ta
fito tace: "mike faruwa? Nan bakasan gidan
matan aure bane? zaka shigo mana ko sallam
babu, da izinin wa ka shigo? To bari na gaya maka
kafin ka kai baban ussaina kara shi zai kai kararka,
6
tunda shi a tsarinasa ba'a shigo masa gida bada
izini ba". Mamanta ta juyo cikin bacin rai tace da
usaina: "ina bandake do shige-shegenki ma ta ya
ya za a yi wannan mara hankalin ya shigo mana
gida? Kai kuma ka fice ka bar mana gida ina
rowan mu da matarka da har zamu barta ta shigo
mana gida har mu boyeta? Kaje can inda ka kulleta
ka nemota, ka saba dukan 'yar mutane kullm har
'yan unguwa suna jin kukanta shine zaka zo kana
wani zare ido wai usaina ta nemo maka matarka, ai
masu son matansu basa dukansu lallashinsu
suke." ta nuna masa hanyar waje da hannunta, ya
fitajiki babu karfi.
Maman usaina mutunce mai mutunci
wanda babu ruwanta da ruyuwar kowa yadda na
fuskanceta koda yake ba fita nakeba amma yadda
usaina take bani labarinta duk wanda ya shiga
gonarta bata kyalewa don haka Nura yana fitowa
ya kama hanya ya tarar su Hadiza sun dawo ita da
Sadiya yace maśu wai su fito masa da ni, Hadiza
da yake mafadaciya ce ta tashi tace: "kaga karka
gaya mana maganar banza yaya zakace mufito
maka da Amina bacin mu a gidansu muka santa,
sau nawa muke zuwa gidanka sai dai muyi
Magana da ita ta windo mu tarar ka kulleta, ko don
kaga ba wanda yayi maka magana don da di ya yi
maka yawa za kazo kace wai mu fito maka da
Amina. Dan Allah malam ka fita, ka kuma fito da
'yar uwarmu don gobe zan zo gidan in har na tarar
1
1
bata nan, sai dai muhadu a station don bazamu
yardaba.
Nura ya fito yana huci yazo kamar zai
tambayi Shamsu ya tarar da masu siyan shayi
sunyi yawa don haka ya karasa can gun wata mai
kosai ya tambaye zulai mai kosao tace ita rabonta
da taga Amina tun kafin ayi mata aure. Cikin
sauri da zafin rai yaje ya hau motarsa ya koma gida yana neman mafuta har ya yanke cewar ya
daina neman Amina kawai, zai kaiwa yan uwanta
takardar sakinta ya dakko biro da takarda ya
rubuta saki uku har ya sa a embilan wata zuciya ta
gaya masa "idan har ya bar Amina tabarsa to zata
iya tona masa asiri tabbas hakan zai iya karshen
rayuwarsa, don yasan Amina ta gane sana'arsa
gashi kuma bai mata dadi ba, don haka haushin
abin da ya yi ma ta zai iya sawa 'yauwanta su
zugata ta kai karaarsa police station, don haka yau
operation din neman Amina zamu yi, an nan ya
dauko bindigarsa zuciya ta yanke hukunci.
Karfe ukun dare Nura da abokan aikinsa
suka dirkawa gidansu usaina cikin tsoratarwa irin
kaga barayi, aka bude musu ko ina suka duba babu
Amina, wanda basu nunawa masu gidan Amina
suke duba babu, sun nuna kudi suke nema duk da
cewa ga kudin amma basu daukaba, soboda bashi
ake bukataba, karfe hudu saura kwata suka dawo
gidanmu na Yanyan suka tarar hadiza, sadiya,
kasimu, duk suna nan suka ringa bi suna cajewa
8
ko zasu ganni duk da badda kamar da Nura ya yi
sai da hadiza da karima suka ganeshi yazo bakin
kofa zai fita karima ta bude zatayi Magana hadiza
tayi sauri ta rufe mata baki Allah yasa bai gani ba
ya juyo yasa kafa ya make hadiza yace: "daga
ganinki zakiyi tsiwa." wani daga cikinsu yace:
"yallabai wannan inaga bai kamata abartaba don
inaga kamar tana da magana kamata yayi kafin
tace wani abu ace mata" Ya daga bindiga zai
narkawa karima Nura yasa hannu ya kare, "rabu
da ita babu abinda zasu iya don basuda gata".
in
Nura ya koma gida kamar tsohon
mahaukaci da takaicin bai sameniba bai kuma san
inda zai sameni ba don yama yanke hukuncin
ya ganni kwai kasheni zai yi don ya san na gudп
ne don na tona masa asiri, kwana nura ya tsananta
bincike a kaina
Wanda nikuma a bangarena ina cen a
hospital, nama fara samun bakin magana don
haka na sami dammar yiwa Hiajiya da baban
kalifa bayin halinda na tsinci kaina tunda nake
gidan Nura, ya rubuta tsaf ya kaiwa police report,
bayan ya kaine suka neni hoton Nura dan life
camp ya kai da haka suka rasa sauran police
station kuma sun tsananata bincike akan Nura,
sun sha kaiwa gidansa farmaki basa samunsa, don
haka aka baza matakan tsaro masu sanin yanda
za'a kama shi.
Ta bangaren Nura kuwa, bayan ya kaiwa
9-
su Hadiza farmaki da su Usaina bai sameni ba duk
da haka bai hakura ba sai ya rinka zagaya unguwa
akoda yaushe har gida, kai kace wani neman
arziki yake min don haka ya daukeshi har gidan
Hajiya Amara, yayi sa'a ya sami baban kalifa ya
fada masa gaskiya yace "Amina tazo amma
kwananta daya ta gudu, suma tashi suka yi da safe
suka tarar bata nan don haka su yanzu shawarar su
je police station su kai report da hotonta idan
anganta," har Nura ya yarda da shawarar baban
kalifa daga baya wata zuciya ta raya masa kamar
hadin baki ne ana son aikai shine.
Don haka ya tashi yace da baban kalifa zai
dawo gobe suje da safe, Allah ya kaimu. Ya fita
wata zuciya ta gaya masa lallai ya zo operation
gidan baban kalifa da daddare su tsanan tashi duk
inda take ya nemo masa ita, to shima baban kalifa
ya yi wannan tunanin, don haka yaje life camp ya
sanar da 'yan sanda. yadda suka yi da Nura da
yazo, sukace kar ya sami damuwa in dare ya yi za
su kai ma'aikatansu su tsare gidan don kar ya
kawo hari.
Dare nayi Nura da mutanensa suka shirya
suka farmaki gidan baban khalifa kiri-kiri Nura ya
tsare baban kalifa da bindiga wai ya gaya masa
inda nake in ba haka ba yanzu su aika shi ba shiri,
yana cikin wannan magana ne 'yan-sanda suka
fado wanda daman sunga sanda suka shiga sun
barsu ne saboda suyi musu saukin kamawa, ba
-10=
don Allah yasa 'yan sanda na da yawa ba da su
Nura sun kashesu don dan sandan da ya taba fada
Nura lokacin da ya sawa baban kalifa bindiga a
kunne yana juyawa ya harbi shi, take ya mutu ko
shurawa bai yiba.
Nan da nan police suka yo kansa duk suka
kamasu suka sa su a mota, da safe baban khalifa
da ya je asibiti yake bamu labarin yadda sukayi da
Nura, dòn haka a nan take muka nemi sallama
wanda zaman gudun kar Nuran yazo ya kasheni
ne yasa mukaci gaba da zama a hospital din, sai da
nura ya yi kwana uku a police station sannan aka
turo neman baban khalifa wanda bayan yaje ne
akace masa anan son ganina. A nan 'yansanda
suka sakani gaba da tambayoyi, tambayoyin uwa
sune: "mai na fahimta da sana'ar Nura? Na taba
sanin office dinsa?" Sannan sukace "suna son
nagaya masu abokinsa daya da na sani" daga
karshe suka tambayeni "shin ina son cigaba da
zama da shi?"
Nura Ibrahim shine sunana da naji ko nace
naga yana rubutuwa tun kafin muyi aure da
haduwarmu da Nura zuwa aurenmu har kawo wa
yau ina ga zai shekara daya da wata biyu, yallabai
kamar yaddan kuka nemeni tunda nake da Nura
ban sanshi da wani aboki ba wanda zan nuna tun
sanina da Nura shikadai na ganshi har muka yi
aure da Nura zan iya cewa lokcin da aka tsahi
bakin mu da Nura mutanen da sukazo basu wuce
11-
wadannan wanda naga an kamasu tare ba, amma
tunde nakeda shi bai taba kai mana suba gidansa
don haka nima tun a bikinmun ban kara ganin
suba inba yauba.
Yallabai, sana'ar nura kuwa lokacin kafin
na aure shi zan iya cewa suna'ar da na san shi da
ita itace siyan fili ya siyarwa don nima kusan nace
office din da nake aiki yake zuwa siyan filaye ta
haka muka hadu da shi mukayi aure sai naga abin
ya sabawa abin da na sani don kuwa baya fitar
sana'arsa sai dare yayi kullum karfe ukun dare
yake tashi yayi shiri da wasu bakaken kaya ba ya
wuce awa daya biyu yake dawowa sai ya tabbatar
ina bacci ni kuma bai san na taba kamashi ba nayi
shiru ne don saboda jin tsoron kada ya kasheni in
yaga na gane babu kuma hanyar da zan gayawa
wani tunda kullum in zai fita kulleni ya ke yi
saboda jin tsoron kada ya kasheni in yaga na gane,
babu kuma hanyar da zan gayawa wani tunda
kullum in zai fita kulleni ya ke yi saboda kar na
fita kuma kar wani ya zo wajena, yace "karma na
kara barin wani ya shigo masa gida”.
Wani daga cikin 'yansanda yace "ya taba
gaya miki wani abu game da gidan da ya sakaki,
misali ya taba fada miki na shi ne ko na office?"
"Gakiya a'a don tunda na zo gidansa wata bakwai
kenan babu wata magana ta arziki data shiga
tsakanina da shi". Daya dan-sandan yace: "kin
taba ganin wani makami a hannunsa?" nace:
-12-
"sam banda wata binidinga guda daya, ita kadai
nake gani kuma tun kafin muyi aure an nemi ya
turo iyayensa ya turo wasu mutum biyu manya ya
ce "daya babansa daya kanin babansa,
mahaifiyarsa kuwa yace ta mutu, yace min su
kauyensu yana wajen Kaduna, amma tunda
mukayi aure har yau bai kara yarda munyi
maganar data shafi hakaba."
"Yallabai maganar zama da shi kuwa ina
son araba mu daga yau bana son ko hanya mu kara
haduwa sai lahira in anzo mana hisabi." Suka yi
dariya gaba dayansu, 'yansandan suka tambaye ni
"yarinya yanzu kinji wahala kike son rabuwa
dashi da ai kudi ya nuna miki yace yana sayarda
fili ko?" Inji wani police duk suka sa dariya.
Duk maganar da nake yi Nura ya na zaune ya
na kallona wani lokaci ya sunkuyar da kai idan yaji
na fadi wata maganar ya dago kansa yanzuma tunda
nace ina son murabu kwala min ido ya yi har yanzu
bai dauke kansa ba daga kaina wanda nima kalon
nasa nake kallo na takaici da haushi ina masa Allah
ya isa a raina ta wani bangaren kuma ina masa
godiya ga Allah da zai rabani da kaya. Wani daga
cikin yansanda ya kalli Nura yace: "to kai kaji
yanzun matarka ta ce bata son zama da kai don haka
yanzu tana son ka saketa ya kace?" Nura cikin
karkarwa don kowa ya kalli Nura yaşan ya sha duka
ya ce: "to Amina na sakeki, Allah ya baki miji nagari
ba irina ba." nace "Amin", bafa don naji dadi bane
13-
don kuwa ina tsoron fitowar Nura daga police
station don haka nace da yansanda inason ayimini
tsakani da nura wanda ko ya fito babu ruwansa dani
sukayi dariya sukace ba zai fito ba wanda ya kashe
rayuka shima. kashe shi za'a yi Nura ya yi kwalakwala da idanu ya ji ance za'a kashe shi yasan kuma
babu mai fito da shi.
Ni da baban khalifa haka muka fito muka
kama hanya da niyyar zuwa gidan baba Buba mu
sanar dashi halin da ake ciki, muna zuwa muka tarar
wasu ne a gidan ba shiba wai ya yi ritaya ya koma
mubi, muka jiyo duka babu kwarin jiki. Su Hadiza
kuwa sun rasa inda zasu same ni don itama hadiza
tun sanda Nura ya kai musu ziyara suke ta faman
nemana matsalar basu san gidan Hajiya ba don haka
babu wnda ya dòshi can, da muka dawo da baban
khalifa yace: "ya kamata ki tsaya kiga 'yan uwanki
ki gaya musu abinda kike ciki in yaso koda da
yamma ne sai ki dawo" yace: "ga wannan kin sayi
wani abu in kuma zaki dawo kya shigo mota kin
dawo." nace: "to na gode."
Ina zuwa na tara Hadiza da Sadiya suna
zaune, sai suka bani tausyi saboda halin da na
samesu, ina sallama duka suka taso suka rungumeni
har hawaye nayi don tausayin mu. Bayan na zauna
ne suke bani labarin halin da suka shiga saboda
rashin sanin inda nake da kuma irin shigar da Nura
ya yi ya zo musu har da police din da Hadiza taje ta
gayawa, nima na kwashe duk abinda yafaru har da
zuwa gurin Baba Buba da na yi. Bayan nan nace
-14-
musu yanzu ni da Nura mun rabu. Bayan komai ya
lafa, na tambaye su ina karima? Shi ne sadiya ta се
tun sanda nura ya zo bata sake kwana ba tana gidan
samarinta, sai dai ta zo ta kwashi kyanta ta wuce, ina
zaune har la'asar wajen karfe hudu da rabi 4:30
Shamsu yazo daukar kayan shayinsa, da yake dama
cen a nan ya ke ajjiyesu, shi ne ma dadin
dangantarkar mu da shi, shi ma ya zauna yana
jajinta min har yake gaya min ai shi Nura ya
tambaya gidan Hajiya, yasa shi a gaba ya raka shi
har gidan nan dai na gayawa Shamsu mun rabu da
Nura don haka ko gaba yazo nemana kar ya sake
yace zai nuna masa inda nake.
Biyar da rabi dai-dai nayi sallama da su
Hadiza na wuce maraba muka rabu da niyyar zasu
kawo mini ziyara tunda ni ina idda kuma kowa
yasan a ka'idar musulunci anason mace in har ta
rabu da mijinta ana son ta zauna a guri daya har sai
ta gama iddarta, badan komai ba aka gindaya mata
hakan don cika ka'idar iddar tun ba'a son wani ya
gan ki kuyi zance idan kunyi haka kunyi zance kan
aure don haka ko tagama idda babu aure tsakanin su.
Nayi zama na jindadi da kwanciyar hankali a
tsakanin Hajiya da baban kalifa wanda duk iyayen
da suke son 'ya'yansu haka za su yi musu, jikina ya
dawo nayi fari nayi kyau ranar da iddata ta cika
ranar nayi sallam dasu baban halifa halifa sai mubi
don gano innata itama innata naga tayi farin cikin
ganina don a zaton ta ina nan a gidan mijina don
haka abinda akeyi bata sani ba, inna take bani
-15-
labarin itama daman za tazo Abuja ta ganni ta kuma
gaya mana zata yiwa binta aure nan da sati biyu
harta tambayeni Nura nace: "yana nan lafiya ban
gaya mata kome nake ciki ba har nayi wanka nayi
sallar magariba sai dana tabbatar duk kowa na gidan
ya kama gabansa ya barni dagani sai innar tawa
saboda tausayawa da ya ke tana cikin matan 'yan
uwanta don haka tana tare da habaince-habaince irin
na matan kauye don gudun haka nema yasa sai na
yiwa kowace mata tsaraba da kudin da baban kalifa
ya ba ni.
Na kalli innar tawa a karo na farko na tausaya
mata nace a sanina yanzu idan na gayawa innta nima
aurena ya mutu, don haka dole ne na gayamata ban
gama tunanina ba ta kalleni tace "kuna dai zaune
lafina ko?", Inna babu abinda zan boye maki gakiya
yau watana uku kenana rabona da Nura don nagama
iddah na kwashe komai nagaya mata tun farkon
aurena da Nura har rabuwarnu inna tace: "Allah ya
zaba miki abinda yafi alheri”. Inna tace ni yanzu babu
abinda yake damuna irin karima tunda nazo garin nan
yarinyar nan bata taba kawo min ziyaraba sai dai ni
naje kinga yarinyar nan bata taba aika sabulu saboda
ita ba balanta ni duk da haka ban tunzur inna ba nai ta
bata hakura da kuma shawara duk abin nan da take ta
ringa yi mata addu'a Allah ya shiryeta, ki daina sa
bacin ranta, fishinki zai iya sawa takara fandarewa.
Da irin wanan dadadan maganganu nayi tayiwa inna
har ta dan saki ranta muka cigaba da hira kwanana uku
a Mubi nadawo Abuja.
Tunda na dawo Abuja na gaji na dawo gidan
-16-
1
Hajiya don na huta, don haka ina son Bilkisu da Mairo
suma su huta, "Bilkisu kin ga magariba ta yi, kin san
kuma mama bata son kiyi dare, yanzu sai ki tashi ki tafi
gida in ya so kya dawo gobe na karasa muku ko in
nasami dama sai kizo na karasa baku labarin ko kuwa
Miaro?"
Mairo tace: "gakiya haka ne, don ya kamata a ce
יי munyi sallah tunda magariba ta yi kafin ki wuce.
Bilkisu tace: "Mairo ina hutu" ta na fada ta na
dariya "gobe idan Allah ya kaimu karfe goma
zanzo don jin karshen wannan labari". Da Mairo
dani muka yiwa Bilikisu rakiya har bakin mota.
Gaba dayan mu ni da mairo muka yi alwala
muka yi sallar magariba muka zauna wuridi har
aka yi Sallar Isha'i, san nan Mairo ta je ta dakko
mana kula da faranti ina gama cin abinci nace:
"mairo gaskiya zafi nakeji, bari naje nayi wanka."
Da na fito ne daga wanka kafin nä shiga dakinmu
na leka nace da aunty sai da safe, anan ne ta
tambaye ni "ina bilikisu?" nace "ta wuce tun dazu
mun leko kina toilet" "to baza ki yi kallo ba?" na
girgiza kai nace "gaskiya aunty na gaji bacci nake
ji".
Washe gari tun karfe goma Bilkisu tazo
don ni ko tashi ban yi ba, sai naji ana dukana, na
tashi naga Bilkisu, "gaskiya kin fiya sammako"
"ai dole nayi sammako, don kuwa na matsu nasan
abinyi akanki, ai ni kin cuceni, tunda duk tsawon
zamana dake baki bani wannan labarin ba."
17-
Amina ta tafi ta yiwanka, bayan ta shirya
tace da Bilkisu "zo muje mu gaisa da Anuty" da
muka dawo daga dakin aunty ne Bilkisu ta wuce
mota ta fito da kuloli guda biyu da flask na tea,
kulolin waina ce masa, daya kuma farfesu kifi ne
shi kuma flask din tea kuma kunun gyada ne
hadadde mai makon rowan shayi. Amina tace "ke
ki ce da abincinki ki ke tafe." Bilkisu tace "mai ya
yi min zafi tunda ina son labarin, dole na cikawa
mai bani labari cikinta da abinci ta koshi don kar
yinwa tasa ta ringa bada labarin gaibu."
Na dauko flate da kofina na zubawa Aunty
nata da Mairo, ni kuma na zuba mana namu nida
kawata Bilkisu. Bayan mun gama mairo ta
kwashe kwanikan ta kawo mana ruwan sanyi,
bilkisu tace "wai Amina kafin ki fara bani labari
zanyi miki wata tambaya, mai yasa har yanzu
bakya gidan Hajiya?"
"Kwanana biyar a gidan Hajiya, bayan na
dawo daga Mubi na tattare kayana na koma asalin
gidanmu Yanyan, inda sauran yan uwana suke,
Hajiya ta so ta hanani komawa yanyan don dai
babu yadda za tayi tunda ba gidanta bane dole ta
hakura nida kaina nasan baban kalifa bazai
tasheni ba, amma a tsari ya kamta na koma inda
nafi wayo, ba dan komai ba don su Hajiya su ci
gaba da zama a matsayinsu na iyayena kar wani
abu ya hadani dasu."
Kafin na tafi na roki baban kalifa daya
-18-
samo min aiki, Hajiya ta hada min goma ta arziki,
kayan abinci kala-kala. Baban kalifa ya bani dubu
biyar tare da nasiha nayi hakuri da halin dana sami
kaina kada na yarda shedan ya auręni na koma bin
samarin banza, duk abinda nake so nazo gurinsu in
Allah ya yarda za su yi min dai-dai iyawarsu. Nayi
godiya nakoma cikin yan uwana da zama.
Zama na cikin su Hadiza na fuskanci
matsala da bakin ciki iri duk kayan abincin da naje
da shi har da kudin dake hannuna muka hada muka
halaka har da karima, tunda a 'yan kwanakin bata
fita ko ina ba, a satin ne karima ta sami aiki munyi
farin ciki kamar ba zamu mutu ba saboda lokacin
dana same su suna cikin yunwan don babu mai
aikin yi duk abinda naje da shi gidan ba'ayi sati
biyu ba ya kare, muka dawo kamar almajirai,
muna faman cin bashi a gurin shamsu, don ma
hadiza tana da wani saurayi bakano to idan yazo
muna samu mu biya Shamsu a haka muka zauna
duk abinda muka samu mukaci sai mu ragewa
karima komai kan-kantarsa ta zo ta samu, amma
abin mamaki wata na cika karima ta karbi
albashita muka nemeta muka rasa kwana biyar
duk hankalinmu ya taşhi sai ana shida sadiya ta
ganta a kofar wani guest house ita da saurayinta
suna hira, ta karasa kusa da su wai ita mai 'yar
uwa, amma mai zai faru, karima sai tayi kamar
bata santa ba, sadiya da sauri tace "karima baki
ganeni ba? nice sadiya" ta juyo a yatsine tace "na
19-
ganeki, menene?" Suka hada ido ita da saurayinta
suka kwashe da dariya, sadiya yarinta sai ta tsaya
tana kuka, da suka ga zata tara musu mutane suka
tashi suka bata wuri, da ta zo gida tana bani
labarin abin da karimatu ta yi mata banyi mamaki
ba saboda ta yiwa uwarta mu kuma su waye?
Kwanci tashi har na kai. shekara guda
rabona da aure babu aiki babu kuma miji sai
samari yan taya hira, lokaci-lokaci ina zuwa ina
gaisheda maman kalifa wata juma'a akan hanyata
ta dawowa daga gidan su maman kalifa muka
shiga mota daya da wata baiwar Allah muna
zaune zaman mota, har muka fara hira itama take
gaya min anan yanyan take, yadda ta kwatanta
min gidan da take babu nisa da namu gidan, tana
fadin gidan da take na gane marar gata ce ko ince
mai zaman kanta ce irinmu, don gidan babu wata
mai aure, gwara ma namu mu kadai ne. Mun rabu
da Baraka akan zamu ringa kaiwa juna ziyara, ita
ta fara kaimin ziyara tun washe garin da muka
hadu; Baraka irin mutanan nan ne masu kirki, don
haka Allah ya ke wasu, tana son mutane, ga
kyauta tun haduwa ta da ita bata barni ba na biya
kudin mota ba, haka da zata kawo min ziyara sai
da ta ciko leda da kayan shafe-shafe hadda
alawowi, munsha hira har la'asar ta gayamin ta na
aiki a kamfanin lemo, ba ta da aure amma a yadda
ta nuna mini bata taba yi ba, a yarda na fuskance ta
shekarunta zai kai talatin da uku, don haka nasaki
-20-
jiki da ita tunda komai ta fini don haka bana
tsammanin mummunar shwara daga gareta.
A cikin sati guda mun shaku sosai da
Baraka kamar mun yi sheharu, in ka ga ba ma tare,
to Baraka ta tafi aiki da zarar ta dawo za ta zo,
kwanciyar bacci ke rabamu.
Wani abu dana fuskanta da ita tana son
kula samari kala-kala sannan kananan yara
wanda basu kaitaba, kusan nace kannanta 'yanyara wasuma ko sakandare basu gama ba, kirkin
da Baraka take min yasa bana son na yi mata
mummunan fahimta, sai dai kawai zan iya cewa
munsha bam-bam tunda irin samarin da Baraka
ke ma'amala dasu narainasu, dan ni ko duniya
banza tsakanina dasu aike, aiki lokaci-lokaci idan
muna hira da ita, ina bata shawara akan kananan
yaran da take kulawa, amma Baraka taki sam, da
hakan takance da ni wai kula manyan-maza shi ne
ya ke tsofar da mace da wuri, duk da haka ban
yarda ba, ban kuma yarda na biye mata ba, sai ran
nan da la'asar an gama ruwan sama mun zauna
kowa ya takure saboda sanyin daya shigo na
yamma ga ruwa.
Baraka ta zuba wani abu a kofi daga
kicinta ta kawo mana tace "Amina ku sha wannan
maganin sanyin da muke jine", na karba ina
kaiwa bakina wani irin wari da daci, na furzar
nace "Baraka meye wannan" "ke dai ki sha in ta
fara yi miki aiki kya ji", raina ya baci nace
-21-
"Baraka giya ki ka bani gaskiya baki kyauta min
ba, don ni ban taba shan giya ba", tayi wani
murmushin da ya bata min rai "inda kin san
maganin da ke dauke da giya da baki ce na cuceki
ba, kin ga dai tana maganin tunani ko wane iri ne,
ba wanda zai saki damuwa da rashi aure, tunda
kinga ni kaina inda ba dan wannan ba zaki ganni
haka ba, ga yadda kika rame, kin damu duk kin
zama kamar wata tsohuwa, kin sawa zuciyarki
damuwa, mace bata da ranar magani kin zauna
baki da aiki sai kula tsofaffin maza, wanda ba za
su kare ki da komai ba Sai cuta, banga amfanin
namijin da ba zai yi min magani ba, tunda kinga
tsohon namiji daga gare ki ya ke neman lafiya, to
daman zan je gun wanda zai karu dani, a'a kina
wahalar da kankine, Amina duk namijin da ya ce
min aurenki zai yi karyane, wanda ma yaron in
kina dabai-bayeshi koya aureki, shifa babba
tsohon dan iskane kawai so yake yayi amfani da
yarintarki na murje ya kara lafiya.
"Inda kin kai shekuru irin nawa, da baki
hanani hulda da kananan yara ba, don yazu
zancen da nake maki shekarata arba'in da biyu,
babu wanda zai ce na girmeki, duk kin tsufa".
Na yi kwanto ina kallon Baraka na
faman lakca, ina rike da kofin giya ni ban sha ba
ni ban aje ba. Ita kuma ko a jikin ta ta ci gaba da
cewa "ni Baraka Mansur kaunace ta hadani da ke
na ji ina kaunarki kawai a raina, mahaifina Alh.
-22-
Mansur da mahaifiyata Haj. Basira duk kanninsu
mutanen Gombe ne, babu talauci ko rashin gata a
tare da ni, don mu uku ne kacal a gurin iyayenmu,
mahaifinmu ya taba rike controller na costom a
nan Abuja, Allah ya bashi dukiya mai yawa
yayata wadda na ke bi yanzu haka tana aure a
Legos, tana auren tsohon gwamnan sojoji,
kanwata itama tana aure a Kaduna, auren
manajan kamfani ... yanzu haka ni kadai ce
Allah bai ba mijin aure ba, mahaifayata ta
tsangwama min, kullum cikin gori duk abin da na
dauka a gidan nan sai anyi min gori ni da
gidanmu, ba ni da izinin na saka abincin da zan ci,
tsoron zubawa na ke, ina karatu a A.T.B.U Bauchi
duk san da nazo gida weekend kafin na tafi sai
raina ya baci, ni ina son na ringa zama a can amma
innarmu bata son ta bani kudi da kayan abinci
isasshe, don haka kwana biyu komai ya kare inna
dawo karba wani a ringa yi min fada ana fada min
magana wai ni mai bakin jini har yau na kasa
samun miji, sai in masu miji sun kawo abu na kafa
zalama, kinji kamar ba ita ta haife mu ba.
Ire-iren wannan takaicin yasa kullum nake tunanin barin gida to keda kan ki kinsan bariki ba
kamar aure bane, babu wahala samun abokin yi, Alh. Sanusi shi ne mutum na farko da ya karbi
budurcina ta-hanyar zina, yana da mata uku ban
san iyakacin yawan 'yaʻyansa ba, yana yawan
zuwa makarantarmu wata rana na zo fita a bakin
-23-
get din fita anan muka hadu ya rage min hanya
zuwa cikin gari gidan yayata, a unguwar lemon
Hauwa'u, da dare yayi yazo ya daukeni yake tayi
min siyayya tarkacen kayan ci, ya kawo kudi dubu
goma ya bani, naji dadin kudin nan don haka ko
zance gombe banyi ba, washe gari da yamma yazo
ya kaini