'yan albashi ne
ga 'yar gudunmuwar mu don satin biki ba muyi
albashi ba" Bilkisu da Abdul suka yi godiya,
Abdul yace "kana son kayi mana tsiya ne kawai to
karka manta Amina ce bare duk kanawa ne don
haka za mu iya da kai" duk gaba daya aka kwashe
da dariya. Aminu ya tafi office, Bilkisu da Abdul
dinta suka wuce da niyyar karfe hudu Amina zata
je su yi bankwana.
-91-
Aminu ya kai ni gidan su Bilkisu na tarar
duk ta hada kayanta tsaf a cikin store, kayan sawa
kawai ta dauka. Bayan mun gaisa da mutan gidan,
Bilkisu ta dauki Aminu har falon babanta. Alh.
Usman ya yi mana nasiha yadda ya kamata, a nan
ne Alh. Usman yake ce mana "kar kuga Bilkisu
bata nan kuce baza ku fada mana zancen aurenku
ba", "Baba Insha Allahu zamu sanar da ku
komai." Bilkisu ta jani wani daki a cikin gidansu
kayane irin na mata babu abin da babu wanda ya
shafi kitchen da kayan jere ta ce "Amina wannan
gudummuwata ce, don haka ina son idan zaki tafi
ki nunawa Hassan gidan ku don ya kai miki in
yaso tunda ga babbar mota nan ta office din Baba
sai ya kwashe su a cikinta." "Kai Bilkisu na rasa
wanne irin godiya zan yi miki" "a'a Amina ba bu
godiya tsakaninmu ai wannan taimakon kai ne
tunda burina ya cika ai shike nan." Muka koma
dakin Bilkisu ta bani hotuna ita da Abdul babba,
ta dauko leshi guda biyu da shaddodi dinkakku ta
ce "to wan nan kiyi fitar biki da su ga wannan inji
Abdùl ya ce na baki ta shi gudummuwar" "haba
Bilkisu banda taki hadda ta Abdul?" "Don Allah
Amina kar ki saka komai ki dauka ni da Abdul da
ke duka 'yanuwa ne, karki saka komai a ranki,
kada kuma muna can idan kina da bukatar wani
abu ki yi shiru, ga lamba ta +1280678252 dan
Allah ki tambayimu komai ba wai ki ringa
tambayar mu lafiyarmu ba, don muma za mu
-92-
dinga kiran amarya da ango muji lafiyarsu" ita da
kanta ta kwashe da dariya mun yi sallama da Hajjiya su Bilkisu, Hassan ya dauke ni don na
kasa tsayawa muyi sallama da Bilkisu tunda
akace lokacin tafiyar yayi, wai jirgin karfe biyu za
su shiga amma tun shidda Abdul ya turo ta tafi gidansa, nima lokacin na fita na kama hanya shike nan na rabu masoyiyata mai kauna wadda ta nuna min kauna da iyayena basu nuna min ba, ba abin da zance da Bilkisu da ita da minjinta ban da nayi mata addu'a. Ina hanya Aminu yayi min waya wai ya tazo daukata nace "ia na taho gida". Hassan ya ajiyeni yace "idan Allah ya kaimu gobe zai rako
masu kawo kaya" nace "na gode"
Tunda Aminu ya kawo Yusra, don haka
yau ba ni da sukuni ina ta faman hidima tun kafin
nan, don ma bata zo da yaraba. Ina son halin Yusra
saboda dannewa da take, harda cewa "karma
yanzu ajamu a sake korarmu" nace "to ku dage da
addu'a kar a sake koraku". Ko a yanzu nasan
Aminu zai karemin mutuncina tunda lokacin da
bani da gata bai kwashi Yusra ya kai mini ita ba sai
a yanzu ina cikin gatana duk da ance ba a shedar
namiji to inganin zan shedi nawa mijin. Kamar
yadda yace, bai zoba sai bayan sallar Magariba, a
cikin irin kayan turarukan da Bilkisu ta bani tun
kwanakin na dau guda hudu na bawa Yusra, mun
rabu muna wasa da dariya. Bayan na idar da sallar
isha'I nayi addu'o'i na godewa Allah da ya sako
93-
min kunci lokacin daya ya kuma saka min waraka
lokaci daya, don yanzu duk inda na juya sai dai godiyar Allah komai ya zama tarihi, tundå duk
mai mace fargabarta da mai kishiya shi ne halin
kishiyar, ba dole ne ba kana son zama lafiya itama
tana so, amma ni cikin ikon Allah ita take son
zama lafiya, don haka dole duk fitinata nima na
zauna lafiya na kuma godewa Allah da Aminu ya
ce ba zamu zauna gida dayaba tunda idan gida
daya ne dole wata rana a bata, yanzu fa kullum a
marmarce zamu hadu.
Aminu ya yo min da waya wai "sunyi magana
Inna za a hada daurin aurenmu gaba daya da su
Hadiza, don haka ni tun dazu na bayar da aikin
buga kati, Amina ina son kema ki shirya next
week Sunday ki tare don kin san bazan iya hira ba
ace kina gida da aurena”. Ban bashi amsa ba don
maganar tasa ta daure min kai, wai har da cewa
yana ji kin ti shiru? Nace "Aminu mai kake so
nace maka tunda kariga ka zartar da abin da kake
so, ai ko kunyi magana da Inna nima ya kamata ka
nemi shawara ta" nan da nan ya zafita "Amina
idan ba kya so na ki gaya min, wace shawara zan
yi dake tun da nayi da nagaba da ke?" "Allah ya
huci zuciyarka." Kawai na kashe wayata. Na yi
shiru da waya a hannuna nace "idan bama zuciya
zamu ringa yi ba, in ba haka ba ai kamata yayi tun
da aure dai da shi ne ya nemi shawarata ba wai
yace shi ya je ya gama, ni sam na so ya nemi
94-
shawara yace da baba yaso a bashi nan da sati biyu
saboda zai yi shiri, in yaso su sai ayi musu nasu
tunda komai biyu aka tanada don haka bana son a
cusa kanmu a cikin harkar.
Binta ce tayi sallama, wai nazo inji Aminu.
Ko gaisuwata bai amsaba "Amina mai yasa kike
so ki mayar min da hannun agogo bayane? Kin
san dai bai kamata na nuna gazawataba, ba don
haka nema na zo akace an bani, don me zanyi
sanyi akan lamarin?" "ni bance ka yi sanyi akan
lamarinka ba, amma ni gaskiya anyi saurin
amince maka kamar wadda aka gaji da ita kawai
sai ace yau saura kwana hudu daurin aure, ai
kusan tayi yawa kamata yayi ace kayi kamar wata biyu sannan ace ka fito."
"Ni wallahi kin ban dariya Amina, ina son
ki kwantar da hankalinki in dai ni Aminu ne bazan
wulakantaki ba har abada, nasan kina tsoron
mazan nan wanda idan basu sha wahala ba suke
cewa dama ana neman kai ne da ke, to ni.Amina ki
ga ne duk namijin da zai wulakantaki to daman
can yana da niyya, idan kuwa mutumin kirki ne ko
ranar da ku ka hadu washegari aka daura muku
aure to zai rikeki, ni ina ganinki kamar mai wayo
ashe ba ki da wayo?, baki san idan aka dade ana
soyayya duk soyyayar karewa take a waje, ba gara
muyi aurenmu tun yanzu ba idan muje gida mu
karashe, haba amaryata dan Allah ki dai na taurin
kai." "ni wallahi har ka bani dariya naji na
-95-
fahimceka, Allah ya nuna mana lokacin", "yauwa
tawan, duk abin da nace aringa cewa to, kinji ko?"
"TO."
An daura aurenmu ranar lahadi 27th Mar
2005, misalin karfe daya rana AMINU DA
AMINA, ALH. RABO.DA HADIZA, KABIRU
DA BINTA.Abin gwanin ban sha'awa, Alh. Rabo
ya yi kaya kai daya da mu da mazanmu duk
shadda blue, abin yayi tsari sosai. Alh. Rabo da
Kabiru sun hada party a Abuja Garden, sun sa
kaya iri daya Kabiru da Binta, Alh. Rabo da
Hadiza ni da Aminu ne ba muyi wani kwalliya iri
daya ba, saboda bamu san komai akan tsarin bikin
ko kuma nace na sune ba namu bane be.
Washe garin daurin aure aka kai ko wacce
gidanta, Binta Maiduguri aka kaita yabzu mijinta
a can yake, ita kuma Hadiza anan Abuja aka kaita.
Baba yayi kokari sosai don anyi musu gado na
gani na fada tunda kowacce gadonta ya kai dubu
saba'in, duk abin da akeyi a kicin an yiwa
amaran. Nan muna zaune a wurin party sai ga
Shamsu ya zo yace "Amina ga wata jarida ki
gani" ina budewa hoton Nura ne da abokansa wai
an kashesu, nan da nan naji duk garin ya isheni
nace da Aminu "Ina zuwa, wata kilama zan kima
gida" yace "lafiya kalau?" "babu komai" yace
"Amina ko mainene bai kamata ki boye min ba, in
wani abu ne zo muje daga cikin can ga wasu
kujeru can."
-99-
Mun zauna, to anan ne na nunawa Aminu
hotunan su Nura na kuma gaya masa dangantaka
da shi, don ada ba abin da ya sani, dalilin
kaduwata itace nina yi masa sanadiyar tafiya
lahira, Aminu ya ce "Amina, gaskiya gaki kamar
mai zuciyar maza amma kuma kina da tsoro, ke
kika san iyakacin mutanen da ya kashe, ke kanki
kika san niyyarsa a kanki, don haka karki damu
kanki ba shi da awani hakki a kan ki. Halinsa ne ya
kaishi ya baro shi." Gaskiya na gode da miji
gwarzo irin Aminu, ya kawoni yana yi min fada
akan shaye-shayen da nake, gaskiya Aminu miji
ne, Allah yasa mu zauna lafiya.
Ba a tashi daga gurin party ba sai karfe
shida na yamma, magariba ta kawo kai, kowa ya
kama gabansa. Amare kowa ta kama shiri, washe
gari duk suka watse saura ni kadai na rage, tun
washegarin da suka tare duk gidan ya gundire ni, naje dakin da kayan da Bilkisu ta bani na ringa
dubawa daya-bayan-daya naga duk wani
electronics na kitchen babu wanda bani da shi,
plates da cokula da tukwane, filas din cin abinci
duk masu tsadar gaske, gaskiya dolene na kara
godewa Allah nayi dace da mutuniyar kirki kawar
arziki, bari ma naje na duba gudummuwar da tace
Abdul,kai lallale ina da sake inda wani ya dauke a
gurin bikin nan, ashe check ne na dubu dari, lallai
masoya sun hutar min da iyayena. Don
yanzu zanje Yanyan na zabo gado da kujeru ne
-97-
kadai ya rage min masu gara kawai. Tunda muka
dawo daga wajen party Aminu bai sake zuwa ba
sai dai waya, don haka ni kadai naje na zabo
gadona da kujeru masu bala'in kyau, dama Baba
ya bani kudi dubu hamsin saboda siyan labule da
zanen gado, acan na bar gadon nace idan za а
kaini anzo a dauka, na wuce kasuwa na siyo
zannuwan gado da labulaye iri daya nasa aka
dinka min zanin gado da labulaye iri daya, pganin
yadda na shiryawa kaina kayan alatu naji har na
matsu ranar tarewa tayi.
Ban dawo gida ba sai karfe biyar nayi
salloli da wanka don na kasa cin abinci saboda
gajjiya. Ina bude wayata naga missed call har
biyar, biyu Aminu ne daya kuma Hadiza sauran
biyun Bilkisu. Ba shiri naje nasa-credit a wayata
na buga mata, cikin sa'a kbugu daya na sameta,
tana tayi min tsiya wai na manta da ita, nace ba
haka bane muna shirin tarewa ranar Sunday
"lallai abin ya matso, yau saura kwana uku, ina
angon?" nace "nima sai waya yake min
kawai"tace kila yana shirinsa ne" nace "nima ina
ganin haka" mun dan sha hira har katin ya kare.
Ranar tarewa tun da wuri su Mairo da
maman Khalifa suka iso don suje suyi je da wuri,
amma har sha biyu Aminu bai turo mota ba, da
muka gaji da jijra muka yi masa waya yace muyi
hakuri yana zuwa, da ya zo babu wata motar kaya
babu komai. Ya ydauki Mairo da Maman Kalifa
-98-
wai suje su ga gida, gaskiya gidan ya tsara komai
nasa, babu dakin da ba gado, daki uku da falo duk
ya cikasu da kaya, falon kansa ya cika shi da
kujerun alfarma, babu abin da bai šaka ba na a
cikin gidan, yadda Haj Mairo suke fada har
kitchen an shirya masa komai don haka Aminu
yace da kayan sawata kawai yake son naje
gidansa. Nama rasa abin da zance, to yanzu ya
zanyi da gadon da na siya hadda kujeru, idan naje
nace su bani kudina ai baza su yarda ba, da na fadawa Aminu cewa yayi "ki bawa Inna ta sa
gadon a dakin ta kujeru kuma ta sa a falonta, na
falonta ki sayawa Isa, kinga don son kai naku sababbi shi kuma nasa sun tsufa.""to duk abin da
kace haka za a yi" "daman ina son in gaya miki
yau da daddare su Hajiya za su zo su kawo kayan lefe, ko ya kika ce?" "yaushe su Hajiya suka zo
daga Kano?" "ai tun washegarin daurin aure, abin
day a hana su zuwa saboda dasu ake ta faman
shirye-shiryen dakin naki."
Akwatina uku Aminu yayi min cike da
kaya masu tsada, set din gwal hudu aka saka, 'yar
zobe dozin biyu ta kwance biyu duk dubai, kwal
fasion kala biyu da warwaro mai shida, kai komai
kiyayyar da kakewa Aminu sai ka yaba da kayan
da yayi. Na tare ranar Lahadi kamar yadda akayi,
amma sam naki yadda ayi wani party, don gaskiya
wahalar da Aminu yayi tayi yaw. Baban Bilkisu
ya bada dubu dari biyu a siyamin wani abu, buhu
-99-
ashirin akayi min goma shinkafa biyar masara
biyar gero, maja garwa hudu man gyada ma haka,
macroni kwali biyar taliya biyar maggi kwali
gishiri buhu biyar shima, dan Baba cewa yayi
komai ya yiwa Aminu bai biyashiba.
Ranar tarewa yini muka yi da Bilkisu a
waya kamar yadda muka yi da ita, anyi mini
alkaki, nakiya, tsatssafa, dubulan, aljacagis da
tayota. 'yan uwanmu na Mobi duk sun zo saboda
sun ji haushi ba a aika musa da na su Hadiza ba.
Yau ni Amina, na godewa Allah daya nuna
min wannan ranar don ko a mafarki ban taba
zaton zan tsinci kaina a cikin wannan halin ba,
yau gani ga Aminu na, wanda ya bude min ido,
yau ga shi ya aureni ya rufa min asiri, da duk maza
haka suke irin Aminu na da sai n ace babu matar
barikin da zata wulakanta, to amma an sha
bambam, don mazan yanzu idan sun ci moriyar
ganga suna yadda ita, sai kaga yarinya karama
namiji ya koya mata bariki ya yadda ita tana ta
faman wanga ririya daga nan kuma hanya ta bud
eta zama abar kyama a gurinsa, bayan kuma shine
ya buda mata ido baya ko tunanin tasa 'yar, yanzu
wanda ya yiwa Karima ciki ga shi ya cuceta tunda
gashi ko saninsa ba a yi ba, kuma gashi su Inna
suje nemanta, 'yar matar da Inna ta sani to yanzu
babu wanda ya san ko wace ce, sai dai in anje
lahira Allah yayi hisabi muga ko waye uban acan.
To nima Aminu na haka ya yarda dani, ai Allah
-100-
kadai yasan halin da zan shiga.
Dan haka babu kakkautawa kullum zan
yiwa ioyalan Aminu addu'a ta musamman, Allah
yak are masa su kamar yadda ya nema, irin
maganin matan da Aunty Nafi ta ba su Mairo ta
hado min yasani jin kaina kamar ban taba neman
mazaba, sai yau zan san namiji, Allah ya sakawa
masoyana da alheri don duk da taimakonsu ne na
sami wannan matsayin da nake ciki.
Yanzu wata na bakwai kenan, hadiza tana
da tsohon ciki ita da Binta ni ko batan wata ban
yiba, amma kwanciyar hakali tasa na yi fari nayi
kiba, idan naje naga yadda Inna da Baba suka
canja dadin da nake ji ya isa, yanzu daga su sai Isa
da Sadiya a gurinsu, yanzu Isa yana level 3 а
university ita kuma Sadiya ta gama secondary
school, tana son ta shiga school of nurse, Baba y
ace tayi kokari ta fito da mijin kafin ta gama. Ina
cikin kwanciyar hankali don Aminu bai taba
damuwa da rashin haihuwarmu ba.
Yau kwana biyar baya nan, ga gurin da ya
tafi babu service din Glo, don haka sai na bude
waya na ringa karanta text message din da ya
rubuto min, ina karantawa ina jin dadin kalaman
nasa, kna farko -naci karo da wannan kalamin Hi!
Baby let me tell you a story of how lonely I used to
until you come into my life and set my sprit, free U
always there when I needed U, U made me real
special when I was felling blue. Thanks
-101-
Baby 100% I care, 20% I nid, 30% I love
U, 40% I cherish you, 50% I think of U, 60% I
dream of U, 70% 1 admare U, 80% I missed U,
90% I luv U am missin U again. Wannan text din
washe gari a gidan nan yayo min da ya fita office.
Bari na ga akwai wani da nake so sosai yace "hi!
Baby life is like a book which day is a new page,
may ur book a best sellers with advantages 2 tell,
lessons 2 learn and takes of good dead 2
members. Whatever is meaningful, whatever is
beautiful, whatever u desire, whatever brings u
peace & joy be yours 2 day and forever" ina jin
dadin kalaman da Aminu yake turo min kullum
idan ya tafi office, don tsabar text din Aminu har
memorin wayata ya cika saboda haka sai na goge
wasu san nan wasu su shigo.
Na bugawa Bilkiosu waya tana ta faman yi
min mita wai cikinta yana damunta da motsi, nayi
tayi mata dariya "wace irin mai rikicice ke, an
gaya miki a sama mama ta sameki, kwara ku dandana kuji yadda aka haifeku", "ke kin huta" "a'a
ba hutu tunda nima so nake, sai dai likita yace
bazan haihuba wai mahaifata baza ta iya rike
cikiba."
Ina ta zuwa Fiad Islamiyya nida Yusra
kullum Asabar da Lahadi, abin mamaki wata rana
mun'tashi ita kuma Yusrå bata fito daga ajinsu ba
ina waje ina jiranta sai naga Baraka da uniform
itama tana zuwa makaranta, ban san lokacin da na
-102-
je na jawota muka rungume juna tace "ta yi aure ta
auri daya daga cikin samarinta Ali, anan zone 3
take da zama" "Baraka, kin haihu?", "a'a likita y
ace bazan haihu ba wai mahaifata baza tad au
cikiba", "daman ina kin taba haihuwa ince ki kai
ni inda aka baki magani nima a bani, don na san ko
meye tare muka yi, kin san ina jin kokain din nan
ita ta lalata mana mahaifa" "nima ina zaton hakan
abinda yasa ni abinma baya damuna sosai don
Aminu baya Inuna mini damuwarsa." "To ni Alina
ya damu amma yanzu yaya zai yi sai dai in aure
zai kara" "lallai Baraka kinji haushi tunda kike
tunanin kishiya, in da ne ai ba zaki yarda ba amma
yanzu baki damu ba."
"To Baraka sai gobe kinga kishiyata can ta
fito za mu tafi", "gidan ku daya?" nace"a'a muna
tahowa tare ne saboda ni ban iya mota ba, sai na
zauna a gidan da yamma Aminu ya mayar da ni
gida wani lokacin ya na koya min mota, Baraka
Allah ya kara shirya mu" "Amin Amina".
Yau aurenmu da Aminu shekara biyu,
Hadiza ta haifi 'ya mace Amina sunan Inna, Binta
ta haifi namiji sunan uban mijnta Ibrahim, Bilkisu
ta haifi twins Hassan da Hussaini sun sa musu
suna Muhammad da Ahmad, ta aiko min da
hotunan yaran renon turawa kamar turawa
manya-manyadasu kamar sun fi shekara. Ni kuwa
da nawa angon kullum soyayya kara karuwa take,
yanzu na iya mota babu inda ban a shiga, don haka
-103-
ya sai mini mota irinta Yusra 206, ni da Yusra
babu wani sabani don ta sake haihuwa ta samu
mace, ansa mata sunana ana kiran Mimi,yanzu
haka ta kusa dawowa gurina saboda shakuwar da
muka yi da ita, munje dinnar ni da sweetie, ina
waigawa kawai, sai ga Samira tayi baki ta lalace
kamar ba ita ba, tayi kamar zata yi min Magana ko
kunya taji ta fasa. Shi ne naje na same ta ita da
sauran kawayenta ana ta faman shan giya, na
gashesu saboda yanzu na san na fita duk da a buge
take, kunyata take ji don ta san yanzu bad a bace
"ina aunty Hafsatu?" "tayi hatsari kafarta ta fita,
don haka ta koma gida da zama yanzu haka ita a
gidan" daman na tambaya ne don na ji komai,
nace "to Samira Allah ya sauwake, sai anjima.
Ban ko ce mata ga mijina can ba, don nasan halin
matan bariki ko ita ko ukawayenta.
Yanzu na dawo da Shamsu mai sahayi
gidana ya na yi min wanki da guga ni da sweetie
na, muna biyansa dubu goma don na san yafi
shayinsa da kwanan titi.
Allah na gode maka da halin da na tsinci
kaina don yanzu babu Surar da bazan iya
karantawa ba a Qur'ani, addu'o'i kuwa ba a
magana, bana yafa mayafi sai hijabi don haka ko
yanzu nasan babu abinda yafi aure daraja, gaskiya
Bilkisu tunda ta rabani da jahilcin da nake fama dashi,
tunda idan naji ana wa'azi a makaranta, idan naji an
tabo irin abinda nayi a baya na kanji tsoron lahira
-104-
babu wanda nake tasuayi irin karima, kwara ni yanzu
na sani na kuma tuba, Allah ka shiryemu baki daya,
kasa masu hali irin na mu za su daina kar ce sai an
samu miji irin Aminu a'a indai aurene, kowama aka
samu ayi hakuri dashi Allah zai bada lada, komi kuma
lalaceawarsa yafi bariki, ba zai ki baki abinci in zai
barki ki nema to ki aure shi, sakamakon ki yana can
lahira, don ita ce madauwami duniya duk ruduce. Allah ya sa mu gane.
Zan so naji ra'ayin makaranta, wa yafi baku
haushi, tausayi, burgewa da kuma me yayi muku dadi sosai.
Na gode masoyana ku saurari littafina mai suna
DUK HALINSU DAYA
08035803200 MATA KAWAI
-105-
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels