ko?"
Rufa'i ba saurin "Gaskiya zan yi yanke
hukunci ba, saboda Aminu dai nasan halinsa tun tuni
to ya kamata a ce nasan na matarsa itama tasan irin
matar da zata żauna da ita, kaga haka shi ne zai sa
zaman lafiya a gaidan, ni gakiya ban ji dadi ba da
Aminu ya boye min ya na da mata". "A'a Amina",
Aminu yasa hannu ya dakatar dani yace "ni ban
boye miki ba tun da ki ke kin taba tambayata, ace
kinsan ina da iyali, saboda mutum kamata ban rasa
ci da shaba ina da wadata gwargawdo ace na kasa
rufawa kaina asiri, don aure rufin asiri ne tunda yana
dadawa mutum mutunci idan za ki tuna dama inason
rufawa kaina asiri, tun da nace inason rufawa kaina
asiri tunda nace ina sonki, da aure na nemeki, don an
hana ni ne bayan nan ban dade ba na yi aure. na don
haka tunda yanzu kin kawo hujjarki ta son kiga
matata zan kaiki har gaidana kiga iyalina itama ta
ganki, Allah-ya kaimu Abuja zan kai ki har gida kiga
Iyalina, inyaso sai mu tashi daga inda mukatsaya.
Muka yi sallam da Rufa'i ya bani kyauta a leda
munyi sallama da Umma da mutanen gida munsha
tsaraba kya-kaya. Bamu bar mubi ba sai karfe sha
biyu na rana, tunda muka taso Aminu yake ta kwara
gudu ba mu tsaya a ko ina ba sai a Fadan Karshi,
mukaci abinci muka yi salloli nan ma muka kama
hanya, nan ma muka kama hanya, nayi manakin
zuwan Aminu da wuri mubi don ranar juma'a ne, nan
ya ce "wai ai ya fito biyar na asuba."Bamu iso Abuja
41-
ba sai karfe goma na dare.
Kowa ya gaji don haka sallah kwai muka yi kowa ya kama makwancinsa, kajin da Aminu ya siya mana babu wanda ya taba ko wanka kasa yi
muka yi, da safe Aminu kafin yaje office ya biyo ta
nan don ko tashi ba mu yi ba, mun yi sallar asuba mu
koma bayan ya sa an táshe mu yace daman yazo ne
ya gaya min na shirya idan ya dawo da yamma zai
zo ya dauke ni ya kai ni na ga iyalinsa, na ce Allah
ya kaimu, tun lokacin bacci ya kaurace min, ni kadai
na saka wannan na kwance wancen, wajen karfe
goma sai ga Baraka, nayi makmaki don da sauri na
tambayeta "me ya kawo ta? yanzu ina office din?"
tace "wai tana hutu taga kwana biyu" nace mata
'jiya muka dawo daga mubi," munsha hira irin ta
kawaye anan nake gaya ya mata Aminu ya ce zai
aureniduk da nasan Baraka bata son Aminu, na fada
mata ya na da mata da yara biyunan da Baraka ta hau
fadawai bani da hankali zan auri mai mata har da
yara biyu ai na daukowa kaina aiki, ina zaton zai so
ni ne ya na kai ni gidan sa shi ne zai fara tona min
asiri bacin ya san komai nawa ai ita ko ba shi ida
mata ba za ta aure shi ba tun da ya san asirinta ba bu
yadda zata auri wanda ya san sirrinta, wanda da
kansa zai zauna ya gaya mata sirrinki, gorima ya
isheki a tsakar gida duk motsi a ringa cewa karuwa
dan haka ni dai shawarata karki fara shi yasa ya
matsa miki ya rabaki da gidana don ya cusa ki
gidansa ya hada ki da wahala in aure ki, ki so ki nemi
wanda bai sanki ba. Ba wanda yasan kiba tun kina
-42-
yarinya.
Haka muka kare hirar mu da Baraka ta kama
hanya ta tafi, masifatuwa Hadiza tana jinmu, ina
dawowa daga rakiyarta tace "to ta kaiki ta baro, don
ita tarasa shine take son ta hana ki naki a renko? Ina
zaki?, zauna kiyi tunani gwara ki zauna Amniu shi
yafi kowa sanin sirrinmu, amma duk da haka bai yi
kyamarki ba yace yana sonki babu abinda
mahafinmu bai yi ba akan idon Aminu, amma yace
yaji ya gani, idan zai tona maki asiri tun yanzu zai
fara ga iri halin daya fito dake daga gidan duk da
haka yana manne dake don so kawai, banda husuma
irin na mutane menene aibun mai mata tun da ya
rike an gani ai yafi lalube a cikin duhu, duba duk
wahalar nan da Aminu ya ke miki bai taba cewa zai
dauke ki kuje yawon banza kamar sauran samari, ai
Wallahi Amina babu rufin asirin da yafi namiji yace
zai auri mace mai zaman kanta don ya rufa mata
asiri, don kuwa rufin asiri ne babba, banda rufin
asiri Aminu idan ya aureki har jahadi yayi, tunda ya
fitar dake daga kangi." Nasihar Hadiza ta shigeni
don haka ni yanzu na barwa Allah zabina kawai.
Kamar yadda mukayi da Aminu magariba
nayi sai gashi na yi kwalliya dai dai gwardwado
nasa wata Holland fara da Aminu ya yi min lokacin
da zamu tafi mubi nasa Hadiza ta shirya tsaf,
doguwar riga ta sa, ita ma Aminu ne ya siya mani,
tun daga nan na fara yiwa kaina fada nasan Aminu
gatan mune tunda daga ni har kannena mun zama
akarkashin Aminu, Rufa'i abokin Aminu a ledar da
-43-
ya bani turarrukane guda uku da man shafawa
"SoWhite" set na dauka cak da niya nima naba
matar Aminu. Bamu zame ko ina ba sai Asokoro
Aminu ya yi hon maigadi ya bude kofa, katon gida
harda gareji tun daga falon na fara tsorata ganin
yaran Aminu da suka zo tarare kai kace 'ya 'yan
turawane saboda kyau ga fara fat, tabbas kowa yaga
yaran nan yasan uwarsu mai kyau ce dan duk
cikinsu babu mai kama da Aminu, kamar ba 'ya' yan
sa ba ma wanda zai ce Fahad da Fairus ba yan biyu
ba ne, ina ta sake sake Yusura ta fito tace manyan
baki sannunku da zuwa ko gama gaisuwa bamu yi
ba har an cika gaban mu da kayan ciye-ciye, ba bu
ko shakka da kallan Yusura kasan ta hada iri da
shuwa ko fulanin asalin, don babu makusa a jikinta
doguwa fara siririya hanci kamar ka tureshi ya fadi,
da gani akwai natsuwa a tare da Yusura da alama
tana da zurfi ilimi.
Basai ka tambaya ba kana gani ka san akwai
tsaftatacciyar soyayya tsakanin wadanna
ma'aurata. Aminu ya kalli Yusra "Uwargida ga
amaryarki" ta kalleni tace "Allah ya bada zaman
lafiya, Allah ya sa mu zauna lafina idan ta zo", koba
har ranta take maganaba ai naji dadi, don kuwa idan
kissace ma to ta gwanance ida makirceine to
karatunsa tayi, gaskiya da duk mata haka suke
kamar Yusra da kudin boko ya huta, mun sha hira da
barkacwanci da Yusra da Aminu, Hadiza kuwa tana
ta fama da Fairu wajen tambayoyi, muna zaune har
tara tayi muka fito, nazo mota na dauki ledar dana
-44-
kawo mata naba Hadiza nace ta ashe itama ta na can
tana faman nata hade-haden tazo har mota ta kawo
mata tace "Amina ki rike amana karki yaudari
Aminu kinga tsakani da Allah yake sonki ina fatan
baza a same ki da rashin birki ba."
Tabbas mata masu danne kishi irin su yusra
abin sone da dai nasan bazan iya ba ko banza yayi
amfani a illimnita ta daure kishin ta wanda ko wane
namiji zai yi alfahari da mace irin Yusra wanda take
daure fitinar ta, mun biya ta Natalizer mun yi take
awy na chicken shawarma da ice cream, bayan mun
dawo gida mun dade da Aminu muna hira yana
tambayata "yanzu yaya nake ciki tunda nace sai
naga matarsa, to naganta meye ra'iyina?" Na saki
murmushi "Aminu gaksiya na yaba da Yusra
matuka, dole ne kayi alfahari da ita, Allah yasa nima
idan na shigo gidan, nayi koyi da hali irin nata
sweetheart, kuma ba sai ka tambaya ba ka san ina
sonka tun tuni, na san bani da miji sai kai don haka
ka ya femin abin da nayi a baya in sha Allahu zaka
sameni mai ladabi da biyyayay a tare da ku" cikin
jin dadi yace "amin, amin, aminu" yace "gaskiya
Amina ba wani abu bane ya sa duk inda ki ke a
duniya zan neme ki in kin yarda zan aureki, saboda
tun tuni daman in kin tuna da aure na nemeki
mahaifinki da shedan sune suka sa har ta kai ni da
afka miki, dan haka na dade da yin nadama, Amina
hakan da na yi miki shi yasa bana tsantsanin duk
halin da na ganki, kullum ina zargin kaina dan ni na
jawo miki tunda ni na bude miki ido.
45-
Na riga na yi tunani naga babu abin da zan
miki ki ya fe min, irin na aureki don Allah Amina ki
rikeni da amana nida iyalina, don Yusra bana jinta
don ban boye mata komai akankiba da saninta na
dawo na nemeki, kinga yanzu in zakiyi tunani ni ne
mutumin da nafi kowa can-canta da na aureki duk
wanda za ki aura bayan ni basu san iyayenki ba, don
haka zasu yi miki kallan marar gata ni kuwa kin ga
nasan kina da gata.
Kinga idan kin zo zan saka ki a islimiya
kamar yadda na saka yar uwarki." wannan shi ne an
sosa min inda yake yi min kai-kayi nace "daman
Yusra bata aiki?" ya girza kai yace "sam bata aiki,
islamiya kawi take zuwa ta dai yi karatu kafin tazo
gidana, amma bata zuwa ko ina sai islamiya Monda
to Friday, yaushe Amina zan bar matata take aiki?
sam bazai yiyuba ina da kishi don haka bazan bar
matata ta ringa cakuda da maza tunda ina aikin
office ina ganin yarda akeyi".
"Amma gaskiya Aminu kana son kanka da
yawa, ai tunda kake kallon matan wasu kaima sai
kayi hakuri a kalli naka" "a'a Amina karki yi min
sharri bana kallon matan kowà, ni duk duniya
akawai dan gata irina wanda Allah ya yiwa baiwa.
kiga fa irin baiwar da Allah yayimin da mata
kyawawan mata kamarku, dan haka babu wasu
mata da suka isheni kallo", "Hm Allah yasa
maganar da ka ke fada har cikin zuciyarka", "Amina
ya kamata ace ke ce mutum na farko da zaki
shedeni" "hakane, ina maka wasane na yadda da
-46-
kai". Ina ga nin mun kai karfe goma da rabi muna
hira da Aminu na amince zan auri Aminu dari bis
dari don na auna naga duk wahala gara zama da
Aminu akan zaman da nake yi yanzu in da Aminu ya
kubutar da ni, bansan irin halinda zan sake tsaintar
kai na ba tunda gashi a dalilin Aminu Baraka ta
daina kulani, sam in ban da ta tsaneshi ne, da haka
nayiwa kaina fada tunda in zan tuna labrin Baraka,
rashin samun miji ne ya sa ta zama 'yar bariki, duk
kawayen mu wanda muka shekewa da su kowacсе
ta shirya ta kama gabanta, su maijidda tun yaushe
sukayi aure, ai naje auren kowacce duk cikin su
babu wacce ta samu miji irinAminu na.
Wata nayi Aminu yazo nace "na amince yaje
ya sami inna da mutanan sa ayi maganar aure" yace
"to nagode Amina sai dai akwai hanzari, ba gububa
ina son ace baba mahaifinki shi ya daura mana aure
ko ace bazai dauraba da yardarsa" "Hm!!!" wata
doguwar ajiyar zuciyar na yi kana nace "Aminu, kai
yanzu kasan inda zaka sami baba? Gaskiya ko ka
sani nasan abinda bazai yiyuba kenan, inaga aure
yanzu basai samu ba, tunda kai kafi kowa sanin
yadda muka rabu da mahaifinmu, don haka na
tabbata har yanzu mahaifinmu yana nan kan
bakansa, ni dai ina son ka janye zancen neman
mahaifinmu, idan Allah ya yi zamu hadu wata ran
zamu hadu, idan kuma sai a lahira to Allah yasa mu
dace."
"Amina naji maganarki, amma sam ban
yarda da maganarki ba, ku mata tunaninku kadan ne
-47-
abinda nake son ki gane anan shi Uba Ubane don
haka abinda yayi muku dole ne ku nemeshi tunda ya
haifeku tunda ke kin taba ganin inda akayi ado da
uwa sam, Iba ki ji hausawa na cewa da ubanka ko
gyartai ne shi ne ubanka, Amina ba'a sake uba idan,
ana sake uba me ya sa ba'a kiranki da wani sunan ina
kowa ya tashi Abubakar din nan da shi ake amfani,
bari na gaya miki in ba dan na sanki tun kina
yarinyarki da ba bu yadda zan yarda na aureki band
san mahaifinki ba, don ko` kin ce min ya mutu
dolene ki nuna mini dangin mahaifinki ko sau dubu
ki ka nuna min mahaifiyar ki idan ba ki nu na min
mahaifinki ba babu-yadda zan amince, abinda zan
dauka ke 'yar-rariya ce baki da uba, to kinga duk
wanda yake son ya shiryawa kansa arziki dolene
yanemawa 'ya 'yan sa uwa ta gari mai Asali.
Dan haka Amina nida kaina zan nemo inda
mahaifiku yake, in ya so zan zo na dauke ku muje ku
kuma kuroke shi gafara duk da kuna ganin ya yi
muku laifi, tunda ya koreku, sannan muyi masa
zancen aure idan ya yarda to idan yaki kamar wance
sai mubi ta wata hanyar mu nemi wanda muka san
zai bashi hakuri har sai ya amince sannan muyi aure
ya kikace?" "Naji ban amince ba, inaso abani kamar
sati abin da na yanke zan fada maka", Aminu ya yi
murmushi yace "ba bu damuwa za'a baki ranki ya
dade ko wata kika ce za'a baki ballantana sati, Allah
ya kaimu". Ya mike ya je yashiga motarsa, nasan
ransa ya baci yá danne ne kawai, kamar yadda na
nemi sati guda, Aminu bai zoba bai kuma aiko da
-48-
wani dalilinsa ba, tunda duk bayan kwana biyu yana
aiko abokinsa da ya ke unguwar mu, ya kan aiko da kudi ko da kayan abinci da kayan cefane, amma
babu ko note ballantana wani bayani mai gamsarwa,
nasan dama fushi ya yi to ni dinma haka, don a cikin
satin nan na ziyarci maman kalifa inda nayi mata
karyar tafiya ce mubi ta sameni babu shiri shi yasa taga
shiru bana zuwa, a karyar tawa har da cewa jiya don
naga har tana tambayata ya umma nace tana nan lafiya
kalau.
Ban boye mata komai ba game da Aminu har
nemana da ya yi daga farko mahaifina yaki yarda
muka rabu dashi, yanzu yace sati amma sam ya share
tunda na dawo daga mubi yaki zuwa, don karta dagoni
nace tanda nadawo daga mubi. Hajiya kamar yadda ta
saba tace "Amina ina son ki gane aure nan shi ne
mutuncinki, kuma Aminu yana da gaskiya da ya ce
zaije gurin neman mahafinki, yanzu abinda na keso da
ke, ki kwantar da hankalinki, idan ya gano inda
muhaifinki yake to mu da baban kalifa sai muje mu
gan shi, muje masa da maganar auren, idan yace ya
amince, kema sai mu kai ki ku sasanta, idan kuma yana
nan akan bakansa sai a kyaleshi aci gaba da addu'a har
Allah ya kawo karshen abin sai azo baban kalifa ya
daura ko kuwa?, Idan kuma Aminun ya kafe akan sai
ya yarda zai aureki, to sai muzuba masa ido muga
abinda zai biyo baya ko ince muga yadda zai yi karki
damu Allah yana tare damu ke dai ki da ge da addu'a.
Ranar da kwana bakwai yana cika Aminu yazo
yace dani "ya ya nake ciki don shi yana nan akan
bakansa". Haushi ya zomini wuya nima nace "ina nan
49
akan bakana, inaga bai kamata ka matasa aka
maganar babana ba tunda ni bashegiya bace,
idanzaka tuna da shi ne ya koreni bani na kori kai na
da kainaba, don haka da yana bukatar mu yasan inda
zai nememu don haka idan har in da gaske ka ke
tsakani da Allah kakesona ai ni zaka aura ba
mahaifina ba, abu mai sauki ina ganin ka je ka nemi
baba buba ya daura mana aure nidai tawa shawarar
kenan."
Aminu yace "to naji taki shawarar sai dai
munsaha ban ban ana, amina kamar yadda kike ganin
babu wanda ya isa ya cenja maki ra'ayinki haka nima
don haka zabi ya rage naki, in kina ganin kin kafe
nima haka na riga na gayamiki bazan aúre ki ba
saida yarda mahaifinki kinga tafiyata wacce kike
ciki kya nemini".
Haushi ne, takaici ne duka babu wanda
babu, don haka na yi kuka na share, nayi
alkawarín nabar Aminu har abada, tunda tun
yanzu haka har tana faruwa a tsaknin mu, nasan
idan munyi aure abin haurshin sai yafi haka, don
gwara da ya nuna min tun anan nasan idan aure na
ya yi, akan kankanin abu zamu ringa batawa
dashi tunda yana da kafewa ni dai nan na fishi
gaskiya, da ace baisan iyayena ba in ya fadi haka
to ba zan ga laifinsa ba, idan ba ya sona a fasa
auren, ya dada cewa daga bangeran mahaifina
aka samu matsala, mai yasa zai kafe, to yaje na
hakura, Allah ya kawo mini rabona, don ma
banda kaddara ina zan iya da wannan makirar
-50-
matar da shi ni ba kowa ba, ba kuma 'yar kowa ba
na cusa kaina inda akafi karfina, ni daman a
tsorace nake dan na san ina aurensa, zai koma
gindin matarsa da 'ya 'yansa, ya zauna ya ajiye ni
a gefe, tunda ni na şan ba haihuwa zan sake yi ba,
ko haihuwa zan yi yaushe zan haifi 'ya 'ya kamar
wadannan yaran masu kama da 'ya 'yan
larabawa.
Duk kukan da nake Hadiza da Sadiya su na
kollo na ba bu wanda ya ce da ni ci kanki, haka na
ci gaba da rayuwa kamar da, don yanzu kusan
wata duga Aminu bai zo ba, bai kuma aiko komai
ba, don haka mun koma buga-bugar mu, tun da
bakin da Allah ya tsaga ba zai ha na shi abinci ba,
irin kudin da Aminu ya ke ba ni na hada dubu
goma na siyo indomie da kwai kiret goma na ce
shamsu ya rinka sayarwa yana aje mana riba, to
wannan ma yana taimakon mu sosai tunda muna
cin abinci ko ba dadi kamar da.
Hadiza ce muna cin abincin dare tace "wai
don Allah Amina yanzu me ya hadaku da Aminu?,
Kusan wata guda ba labarinsa, ni da na san office
dinsa da naje na bashi hakuri, na sanki da zafin
zuciya, don haka ba sai na bincika ba, na san
halinki, tunda Aminu tun kafin ya aureki ya ke
son ki, idan kuma zugar Baraka ne har yanzu, to
ita ta zagaya ta aure shi ta samu tsuntsu daga sama
gasasshe Allah ya bata."
"Hadiza na gaya miki ke yarinya ce, ba bu
51-
wata Baraka da zata zugani akan Aminu, yaushe
rabona da naganta ma, kamarki ki alhakinta ki
rage mata kaya, Aminu halinsa ya hadani da shi
tunda shi idan ya kafe akan abu ba bu wanda ya
isa ya canza masa ra'ayi, don haka ya sauka lafiya
Allah ya kawo min wanda zamu zauna lafiya mu
ringa ba juna shawara."
Ba'ayi cikkaken wata biyu da rabuwar mu
ba, naje gidan maman kalifa na gaya mata yadda
mu kayi da Aminu da dalilina na saurin yin fushi,
tayi min fada sosai akan na ringa hakuri, muna
zaune ne baban kalifa yazo ya ke gaya mini ai
yanzu daman zai sa a nemoni don ya samo mini
aiki. Shi ne office din da muka hadu da Bilikisu,
shi kuma wannan gurin abin da ya sa nabar gurin
saboda ogan nawa yana matsa min, lallali yana
sona yana son ya mai dani matarsa, matarsa ta
rasu ni kuma na ki sam, dan bana son irin wannan
rashin kama kan kullum in ganin 'yammata kala
kala ana fita dasu, don haka nan danan muka fara
fada da shi, tunda na kwanta rashin lafiya sai ya
aiko min da takardar kora daga aiki, nima kuma
ban je ba ballantana na bashį hakuri.
Duk da cewa ya na jin haushi na naki bashi
hadin kai, amma ya hada baki da wani
bazawarina, wani tsahon mutum a kalla zai kai
shekara sittin da biyar, haka a yadda ya gaya min,
matarsa ta mutu ta bar shi da 'ya ‘ya, yana zaune a
kaduna, anace masa Ambasada, ya nuna kamar
-52-
zai aureni, to shedanci yasa na afka cikin wannan
wahalar, don watarana yazo Abuja ya sauka a
Nycon, na san dakin da yake sauka don haka dana
tashi daga aiki sai na wuce gurinsa na gaya masa
ba ni da lafiya na sha magani, ina son zan kwana a
gurinsa. Ransa bai soba don haka ya bar min dakin
ya dawo falo yana karatun Al-Qur'ani, a haka
muka kwana, washe gari sai na dada langwabewa
tun da babu in da zani ya dada komawa falo, sai na
biyoshi falon na ringa aibatarsa har na sami kansa
ya afka min, to tun daga wannan lokacin ya mayar
dani kamar matarsa, duk lokacin da shedan ya
gaya masa sai ya kirani idan yazo Abuja, ko
kwana nawa zai.yi tare za muyi sai ya tafi zan
dawo gida, hartakai ta kąwo idan bazai sami zuwa
ba yana turowa in je Kaduna weekend ya kama
min daki, saboda yaransa ba na zuwa gidansa, to
da haka sai ya sa ni a gaba kullum yana cikin waya
office din mu kar na fita, yasa aka samin ido ban
isa na kula kowa ba sai ya ji, mu yi ta bala'i ya sa
ye wani abokin aikina na zama bani da sukuni
nawa na kaina, da haka ya samu ya shiga gurin
ogan nawa, to daman abinda yake nema, don haka
ogan ya danne kishinsa ya sani a gaba ko waya aka
bugo min sai ya ji wa ye, sannan zai bari na dauka
to da haka suka koreni daga office din, yanzo
kuma ya gujeni bai aureni ba don yanzu bana
ganinsa sam".
"To Mairo da Bilkisu kun ji dalilin su
-53-
Samira suke mini wulakanci, su ma gani su ke su
suka dace d asu zauna da aunty Rahma ba ni ba,
ita kuma ta ki saboda shaye-shayensu", Bilkisu ce
tace "wai sannu Amina kin wahala, babu laifi
amma wani abun hadda zuciyarki don in nice ke
ba bu abin da zai hadani da Aminu, zanbi
shawararsa, sai dai mahaifinki tunda shi ya
haifeki ke ya kamata ki nemeshi bashi ba, don
yansu ina da abin yi akanki idan harkin yarda, na
farko kibar gidan nan dole, na biyu ni da babana
zamu biyo sawo dole a nemo inda mahaifinki
yake, ko da ba za ki auri Aminu ba ya kamata kiyi
aure, ballantan Amina kin yi kuskure Aminu shi
yadace daki aura tunda ya fada miki. gaskiya duk
mutumin daya ganka a wannan yanayin yace
yana sonka haka toba karamin masoyika bane."
"Bilkisu mahaifina kuwa nasan inda yake
har gidansa na sani ka wai zuwa ne bazan yi ba, su
sadiya idan sun hadu suna gaisawa, amma ni
gaskiya ban taba haduwa da shi ba, yanzu dole ne
na koma Yanyan da zama don Karima tana nan
bata da lafiya duk wasu kuraje sun fito mata tana
fama da mugun ciwo ciki, don haka na ke son in
koma don in taya su Hadiza jinyarta, tunda baka
kula ta mutum, ko yanzu idan za tayi bankali ai
tayi tunda tafi wata shida bata je Yanyan ba,
amma da ciwon ya kamata sai suka dauke ta suka.
kaita cen."
"To ku ga idan tana da tunani bata da
-54-
kamar mu, tunda abokan harkar ta ta kowa ya
gujeta, yanzu ma idan naga komai ya yi zafi zuwa
zan na dauko Inna, tunda babu yadda za ta yi da
ita, ita ta haifeta dan haka yanzu ina son duk wata
magana a barta mu gama da shifin karima tukuna"
Bilkisu "tace gaskiya."
Mairo ta nunfasa tace "Amina saboda
kaunár dake tsakanina da ke, zanje can na taya ki
kula da karima kafin innarki tazo", ban san
lokacin da na fada kan Mairo na fashe da kukan
murna, mum samu uwa, na hada sauran abin da
aka bar min na koma Yanyan ni da Mairo. Bilkisu
ta ajiye mu ta shiga ta ga yadda Karima ke birgima
akan katifa, tace za taje gida tunda dare ya yi zata
dawo da safe. Abin mamaki shi ne koda was aunty
Rahma bata nuna damuwarta na barinmu gidan,
ba wai daman ta sani tunda taga kwanan nan
kullum muna daki muna kus-kus harda cewa
"mairo ai sai ki bari na mayar dake inda na
daukoki tunda daman amana aka bani", Bilkisu
dake yar bokoce tace "a'a babu komai aunty
Rahma na ajeta, na hutarsheki" muka biya muka
yi wa aunty Nafisa matar kinin Mairo bayanin
komai sannan muka wuce Yanyen.
Karfe takwas na safe sai ga Biliksu tazo
don ni ko tashi ban yi ba saboda ina fashin sallah
gashi mun kwana bamuyi bacci ba saboda ihun da
Karima take. Bilkisu na zuwa ta ce "to kuzo muje
Hospital, National Hospital ya kamta a kaita" nan
55-
kuwa muka dosa da karima, ko taka kafarta bata
yi, sai da ma'aikata suka zo suka dauketa.
Nan da nan aka shiga daukan jini, fitsari,
kashi, harda yawunta sai da aka auna ckin minti
talatin aka zo da result wai tana dauke da wani
ciwone a cikinta, shi ba HIV ba, yawanci mata na
daukar ciwone a wurin mazajensu, don haka ta
samu ne wajen mijinta. A raina nace "wajen
samarinta dai" duk mun damu, likita yace zai yi
iya kokarinsa amma wai abun ya dade ajikinta
don haka saukinsa sai a hankali. Duk kuraje sun
cika mararta ganin yarda take faman ihu a hospital
din sukayi ma ta allurar bacci duk wahalar da ake
yi Bilkisu ta ke yi, don mu babu mai ko sisi a cikin
mu. Abincin da zamuci damu da karima duk
Bilkisu ta kawo mana, 'yar isaka Hadiza ko kusa
da mu bata zoba wai tasan HIV ce, dan haka bata
aike taba, tun a gidata bar mana daki da ta ho
Asibiti, Sadiya ce ta fito da komai na dakin ta
wanke komai wasu kuma ta baza a rana wai karta
dau ciwo.
Mun wuni muna sintiri a Nationa Hospital,
asibitin da inba dalilin Bilkisu ba, sai dai na shiga
dubiya don duk Abuja babu hospital mai kudinsa
da kyauta. A hospital din gwamnati kwanan mu
uku sai ciwo ya yi kamar ya tafi sai ya dawo, likita
ya yi kirana yace "idan muna son ta warke sai anyi
mata operation an yanke inda ciwon yake don ya
dade a tare da ita, amma sai mun bada kudi dubu
-56-
dari da hamsin", nace "to naji na dadi ma da
Bilkisu bata nan ya fada, da na rasa inda zan sa kai
na", don haka da safe Bilkisu na zuwa na ce"
zanje mubi na kirawo Inna don ta ga halin da
karima take ciki, san nan itama Mairo ta samu taje
gida," Bilkisu bata gaji ba ta dauko dubu biyar ta
bani tace "sai kin dawo". Ban je mubi ba sai karfe
tara na dare, Inna ta ce "Amina da daren nan, har
hankalina ya tashi", nace "Inna babu komai motar
dare