baki su, kuma nawane. Hajiya dubu goma
sha biyune, a'a a'a a'ah! Hajiya yaya kike bude baki
haka? harda rausayar da kai? to Bilkisuce ta bani jiya
da amuka tafi daga nan na rakata gaurin babanta ta
karba ya bani dubu goma taban babanta kuma ya
bata dubu biyu yace ta bani na shiga mota.
kai! Kai! kai 'yata wadannan mutane masu mutunci
'yan wane garine? kuma a ina kika sansu?.
Hajiya kenan zaki shiga wanka amma har kika kagu
kiji labarin Bilkisu to ki bari sai kinshirya mana.
Ina Amina bawani shiri, kawai bani nasha, To
Hajiya.
Su Bilkisu dai mutanen kano ne, Alh. Usman Dan
batta shine mahaifin Bilkisu shi wannan bawanAllah
mutumin kirki ne kwarai fiye da tunaninki, Danbatta
wata karamar hukuma ne a jihar Kano, kamar yadda
14
ta taba gayamun waida Babanta Custom ne. amma
yanzu ya dade da barin aiki, yan zu ofisshin kansa ne
dashi a wuse II inda yake saida motoci inaga mafa
kamar zakisan wurin don kusa da office dinsu
Babana Khalifa ne, wani wuri da ake saida motoci an
rubutu USMANIYYA MOTORS, ke! ban tari
numfashinki ba shine babanta? Hajiya shine babanta
a ke ko dole tayi kyautar dubu goma Hajiya tana fada
tana kwantar da kai, nace wallahi Hajiaya har kin ban
dariya.
Hajiya Hafsatu itace mahafiyarsu itama
mutumiyar kanoce, babanta tsohon alkali ne anan
unguwar kan karokfi kamar yadda Bilkisu taga
yamun mahaifi yarsu tayi digirinta, anan B.U.K tayi
karatun tana Account don haka yanzu tana aikinta ne
a 'Bank of the North' su Balkisu su uku ne a gurin
Hajiya Hafsat da Alh. Usman. Bilkisu itace babba, sai
kannanta Hassan da Hussaini wandan da suna nan
suna makarantar sakandire yanzu haka Bilkisu yarin
yace data gaji arziki gaba da baya don haka tasan
darajar mutane, wani abu da yake burgeni da Bilkisu
tausayi, duk inda kike tunanin mutum mai tausayi
kika sami Bilkisu to koma ki zauna. don kwa nasha
garin haka muna tafe da Bilkisu idan taga Almajirai
sai ta tsaya yta basu sadaka, kin san wanbi abu
Bilkisu har kayanta na sawa take ajewa a mota don
intaga almajirai a hanya ta basu, wani lokacin kuma
ta kanje Area 1 wajen masallacin nan ta rabawa
almajirai kayan sawa da kudi, kar kice kayan tsafaffi
a'a masu tsada kuma basu yi komai ba haka take
rabar dasu.
15
Gidansu Bilkisu kuwa yana nana a maitama ta wajen
federal Housing in kinbi kamar zaki shiga kwanar
maitama store to sai ki mike kwanar farko shine
gidan Bilkisu, watan Hajiya gidansu sama da kasane
kuma bangare biyu daya bangaren Hajiya ce da
Bilkisu da 'yan aikin gidan mata, daya bangaren
kuma Alhaji Usman da Hassan da Hussaininsa,
gaskiya Hajiya tunda nake a cikin garInnan na shiga
gidaje da yawa amma ban taba ganin gida mai tsarin
gidansu Bilkisu ba, babu abinda babu a cikin gidan
nan, abinda yafi bani sha'awa sai yanda sukayi
wajensu dana yaransu, a bangaren Hajiya Hafsatu
itace a kasa dakin Bilkisu a sama haka nan shima
Babansus a bangarensa shine a kasa su Hassan a
sama. kinga wannan yana daya cikin tsarina Addini,
tunda kinga hakan tarbiyyace mai kyau. Hajiya
Hafsatu tana kula da shige da ficen Bilkisu, haka
Alhaji usman yana kula da shige da ficen su Hassan
da Hussaini wanda kinga in kika duba sauran gidajen
mutanenmu ba haka abin yake ba, sai ki tarar iyaye
sun ware nasus bangaren daban na yaranmu daban
don haka sai kiga yaran sun tashi da muguwar
tarbiyya sune shaye - shaye neman mata mugayen
dabiu dai kawai don babu ruwan kowa da shige da
ficensu, ba'a masan abinda sukeyi ba don tsabar
rashin kula irin ta wasu iyayen har yaro yakawo
budurwa ya kwana da ita a cikin gida sunanan da
safe ya fita da ita amma sam basu saniba.
Wani abun ai sai shiru tare da Addu'a kawai
Amina amma tarbiyya kam ta gurbace sai gyaran
Allah kawai, hm! haka nefa Hajiya, kinga in kjiana
16
shiga banagaren Hajiya Hafsatu kina shiga falone
kato akwai wata karamara kofa daga cana cikin falon
in kinbi tanan ne zaki shiga kicin mai katon store a
ciki daga gefen falon dakin Hajiya, katon daki da aka shinfideshi da kafet na alfarma, gadon da yake dakin
baiwar Allah nan ko film ban taba ganin irin shi ba,
remote da kika sani Haijya shi ake dannawa gadon ya shige bango ya manne kamar ba'a taba yinsaba, idan
kuma aka sake danna remote in anason ya fito kenan
sai ya fito kamar ba'a taba komai a jikinsa ba, abindai
sai kin gain da idonki kawai don idan bakin gain da
idonki ba sai ki karyata. Dai dai kofar nan da zata kai
mutum kichin matakalar bene take itace ta haura hard
akin Bilkisu, dakin da take shima katon gaskeni don
yaci babban gado da kujeru set manya, komai najin
dadin rayuwa akwaishi a wannan dakin kan mudubi
Bilkisu turarukan da suke gurin da man shafawa ya
isa mai karamin karfi jari, a kowa ne daki da yake
gidan akwai toilet shi kansa kayan ban dakin ban taba
ganin irinsu ba, tunda randa na fara shiga kasa bude
famfor nayi, inkin fito daga dakin Bilkisu akwai
dakuna guda biyu a nan Hajiya take sauke bakinta.
Daga gefen gidan ne jikin bangaren Alhaji aka yi
dakuna masu aikin maza, duk da namijine yake musu
abinci amma duk da haka suna da masu aiki mata
saboda shara da wanke - wanke da gyaran
dakunansu.
Afilin gidansu Bilkisu akwai masallaci anyi
shine a tsakanin bangaran mata dana maza don haka
yazama dole idan anyi kiran sallah kowa ya fito, ata
gefen kichin din akwai dining anan aka shirya katon
17
dining table doncin abincinsu don haka da angama
abinci. Alh. dashi dasu Hassan za suzo nan
bangaren Hajiya don cin abinci.
To wai shin Amina a ina kika hadu da ita
wannan Bilkisunne? inji Hajiya kenan take
tambayata, nace Haj ya a inda muka hadu da Bilkisu
dai shine awurin aikina anan Abuja Shopping mall a
wani office na siyar da gidaje da filaye, shine Bilkisu
sukaje da ita da babanta da mamanta don siyan wani
fili. To agaskiya Hajiya Alheri yana da adadi don
kuwa lokacin nayi kokarin dana taimaka musu naga
na toshe duk wata kofa da za'a cucesu, kinsan
sha'anin fili ba abu bane da za'ayi rana daya har dai a
garin Abujan nan, don haka duk zuwan da za'ayi
Bilkisu ce take zuwa to da haka muka saba da ita
sosai, sai dai duk sabon danayi da ita ban bari tasan
labarina ba. kinga yanzu inaga mun kai shekaru uku
da ita amma sam ban yarda tasan labarina ba, duk da
haka Bilkisu tana burgeni koda wasa bata taba sonjin
labarin na don bata taba yimun tambayar da zata so
tasan mai nake ciki ba wannan ma yana daya daga
cikin abinda yasa nake sonta araina.
Hajiya tayi wani goron ajiyar zuciya lallai
"yata wannan yarinyar 'yar mutunci ce ta haifu
kwarai don haka ake son harka da mai arziki don shi
duk wanda ya gaji arziki to zakar same shi dan
mutunci. Kinga babu abinda yasa Bulkisu ta hada duk
halin da ake so sai Ilmi don da bata da ilmi zata
kasance mai kyashi da kudin nata tana ganin kamar
tafi kowa tanama wanda basu da shi kyashi sai kiga
18
ma tana neman ta rabaki da naki komin kan - kanton
sa, gaskiyane Hajiya
Assalamu alaikum gaba dayansu suka juya
dan amsa sallama da akayi musu Anty oyo! yo: itama Anty da fara'arta tasha wani material mai fari da
baki abinka da farar mace tayi kyau ba kadan bata
karaso falan Hajiya inda suke zaune Amina kinzo
lallai na makara wallahi dana mika yara makaranta
shine na tsaya shan mai anan na bata lokaci, Hajiya
ina kwana lafiya kalau ya yaran duk suna nan lafiya?
iyi, lafiyarsu kalau, Hajiya ke tanbayar kanwar tata
wai a kawo masa tace a'a wallahia na kosher nake
kawai so nake na koma gida sabaoda abinci kafin
lokacin tashinsu yayi". To shike nan ai babu wani
abua iya kaci dai zan dan muku "yar nasiha Ramatu
ga Amina nan Amana inason ki riketa tamkara kanwa
ki uwa daya uba daya ban yarda ki rinki wulakantata
ba kada ki dauketa tamkar 'yar aikinki domin bamuyi
haka dake ba kinga dai ke kika zo har gida kika
nemeta don haka inason ki rike ta amana idan kika ci
amana wallahi sai Allah yaci amanar ki kina ji da
kyau ko Anty Ramatu ta kyada kai tare da cewa insha
Allahu zaki sameni mai rike amana Amina fiye da
tunanin ki.
Abu na biyu da nake son na gaya miki shine
dole ki iya bakinki da kawayanki duk wanda ya
tambayeki Amina kice musu yar uwarki ce idan ba
haba ba kuwa babu inda zaman ku zashi don nasan
sharin kawayen nan naku, wallahi Ramatu idan naji
wani abu daga gareki ranki zai baci don kuwa babu
abinda zakia sake zuwa ki nema kuma na shige miki
19
gaba. Ta juyo ta kalleni ni tace Amina ke amanace
agurin Ramatu. Ramatuma amanace agurinki don
haka inason ki duki Ramatu kamar 'yar uwarki Uwa
daya Uba daya. idan har Ramatu tayi miki wani abu
wanda ya bata miki rai da ita to babu fushi tsakaninki
da ita ki gaya mata shine zama na gaskiya, kara kice
zaki tsan gwami nna wa 'ya'yantta don kinga dai
wannan abu taimıkon kaine koma nace ke ka rufawa
asiri don haka idan kikace zakai daga mata ahankali
babu dole.
Duk da irin mutıncin da Hajiya take min sai naji
zafin wannan maganar amma bakomai ba abinda ya
jawo haka basai sanin sirrinn da tayi tunda da bata
san sirrina ba babu abinda zai sa ta fadamun irin
wannana maganar don haka yanzu tasa naji babu
wanda zan sake yarda yasan sirrina ji abinda ta fada
yanzu wai rufamin asiri za ayi itama da nake ganin
tana share mini hawaye ma kenan, gashi akan 'yar
uwarta don haka zaman nan ko zanyi shi bazan saki
jiki dashiba tunda tun yanzu Hajiya ta fara nunamin
banbanci akan 'yar uwata kwarama nayiwa kaina
fada tun wuri nayia hakuri da 'yan uwana tunda duk
tsiya babu wanda zai min gorin ya rufa min asiri ni
yanzu ma na daina yarda da kowa tunda Hajiya tafara
haka. Hajiya ace ta katsemin tunanina da cewa
yakamata inwuce ina fatan dai babu wani naga kinyi
shiru "yata inda akwai ki fada tunda ga nan na bata
amsa da wallahi babu komai lafiya, mu wuce ko Anty
tana fada tana duba mayafiyata tare da sakala Jakarta.
Itama Anty Rahama, haka ta bita harda Hajiya tayi
musu rakiya suna zuwa Amina ta zauna a mazaunin
20
mai zaman banza ita kuma Anty Rahama taja motar
(CARINA 11) yah kai tsaye lugube muka nufa. gidan
Anty Rahama gidane ma dai -dai ci kana shiga tsakar
gida sai dakuna guda uku daya yana dayan kuma shi
Anty ta nuna min da niyyar yazama nawa, dakin da
Anty ta bani babu komai a cikinsa sai ledar tsakar
daki ina ciki dakin ina gogo ledar. Rahama tacе
abinda yasa na baki wannan dakin don ki sake inaga
kamar idan na hadaki da yara kamar na takura miki
Amina tace a'a babu komai Anty zan zauna acan
dakin da kayana amma zana ringa kwana da yara, na
fadi hakane dan nasan ina da kudina da Bilkisu ta
bani, itama Anty ta amince da hakan na tambayi Anty
abinda za'a dafa nan take tace dani taliya ta nunamin
duk inda kayan dafa taliya yake na shiga kichin cikin
minti arbain na hada taliya da busheshen kifi ina hada
komai a cikin tukunya na wuce (toilet) na sheka
wanka na fito dai - dai lokacin karfe daya dai - dai
don haka na daura alwala nayi sallah naje na juye
taliya a babban food flask na shirya tsaf cikin
doguwar riga na dako karamin mayafi na yafa naje na
sami Anty na sanar da ita inason zanje kasuwa, tace
babu damuwa nima yanzu zanje dauko yara don haka
bari na ajeki inda zaki samu mota.
nayi godiya na wuce kofar gida gurin mata ina jira ta
kulle gida mu wuce.
Anty Ramatu ta ajeni gurin da zan samu mota
nah au mota zuwa New Market. Ban zame ko inaba
sai gurin "yan katifa muka rinka ciniki dasu su taya
na taya harda muka dai - daita da wani aka dubu uku
da dari biyar, nabar katifa anan na wuce gurin masu
21
zuba uban tagumi nace mairo kinajin karya ko ai
ansan wannan kwai littafine yaya mutum zai yi haka
lallai Dijon nan ta cika muguwa nasan akwai masu
Kaman irin wannan amma ba haka sak, ba. Mairo ya
naga kin kafa min idon ko kiftawa ba kya yi?"to mai
zance miki Amina ai yau na san ke yarin yace tunda
kika ce wai bazata yi haka ba to bari nagaya miki
wannan nata mai sauki ne akan na wasu don idon
kikaji labarin tawa jikara zaki sha mamaki don sai
kice tatsuniya ne domin kuwa izaya da wahala ba
wanda yarinyar bata shata ba ni har kinso narufe
littafi ni kuwa zanzo naji wannan labarin ina da kawa
maru buciya idan har kin yarda zanbata ta fadakar da
jama'a wannan aia mai saukine yanzu ma idan
kinshirya nima ana shirya, nikan mairo a shirye nake.
Maryam shine asalin sunan ta don sunana ta
ci kasancewar nina haifi mahaifiyar da ta haifeta bata
ko daga kai ta kalleta ba ta ko ma ga ubangiji ta ta
zauna ahannun na, na shayar da ita har takai shekara
bakwai da can mahaifiyarta su biyune a gun mujinsu
don haka tana isa amakaranta babanta yasa hannu ya
karbeta ranar da zai karbita yarinyanan naga tashin
hankali mutuka don kuwa nasan mugun halin matar
nan kande.
Asalin mu matanen Babura ne a wani kauye
da ake kira kulfe Babura tana farkon karkashin
jigawa State don haka ita mahaifinta yana nan garin
Babura yarinyan nan ne don bani da ikon hanashi ita
tunda ya fini iko akanta. Malam Murtala Malamin
makaranta ne shine mahaifin Maryam mahafiiyar ta
itace Laure nina haifeta itace yata ta biyu, tana da wa
24
shine ya mutu kafin ita kande matara uban Maryam
tana da yaya uku amma a wani gidan ta haifesu sai
dai tana tare dasu a nan gidana Maryam ita kadai
malam murtala ya haifa don haka ya dora rai akanta
muruka Maryam kwanan ta hudu a Babura gurin
babanta ta fara fuskantar sabuwar rayuwa tana
kwance tsakar dare kande ta tasheta ana nuka
nukun sanyi irin na Babura matarnan haka ta dauko
ruwa mai sanyin tsiya ta kwara mata tace wai
tayimata fitsari kaji zalunci haka yarin nan ta kwana a
tsugune da kaya a jike shi kuwa uban yana can bai
san, bama abinda akeyi, to wannan ya zama jiki
kullum al'adane da kullum indai anyi ruwa dole ne a
tashi Maryam cikin duhu ta share ruwan gidan tas
kamar yadda na gayamiki da sanyin nan kuwa tana
barci za'a dauki ruwan tulu mai sanyi a kwara mata
haka kawai, duk wani aiki da kika sani shara da
wanke - wanke duk Maryam keyi daukar ruwa duk
itace take yi.
Wani abin kuma da yake bani mamaki matar nan
bata bawa Maryam abinci sosai! da safe idan aka
dama koko zai tasa yaran nan nata kowa yazo ya
zuba yawun sa da majinarsa sannan ace da Maryam
gashi tasha sauran yawun haka zata sha tana sha taje
tayi amai amma babu wanda zai kula.
wannan abubuwan da Kande ke mata babu wanda bai
sani ba amma ankasa mata magana har shi kansa
murtala sai kaunar zuci kawai yake don kuwa koshi
bai fi karfin hakan ba agurinta don tsoronta da yake
yi.
25
kwananta biyar kenan rabonta da wanka tun randa ta
dai na talla bata karayin wanka ba.
Duk wannnan bayani da nake miki Amina
kande ce da bakinta take gayamin wadannan tun da
kwana biyar ban ganta ba sai na biya nida matar
kanina tawa nace muje mugani ko lafiya shine da
muke je take gaya mana wai don rashin kunya harda
cewa abinda yasa ta hana ta talla tana zuwa gurin
wani ne a kasuwa mai lemo ita kuma tana tsoron kara
taje tayi ciki ace don ba 'yarta bace. na kale ta kawai
nace kinyi dai - dai amma ina ganin ai Maryam har
yanzu yarin yace tunda bata wuce fadaba don haka
ina ganin ai za'a iyayi mata fada a kuma je a
tsawatarwa da mai lemon ba'ace ta fasa tallar gaba
daya ba ko kuwa ni anawa ganin, ta wani yatsuna
fuska to wazaije yana bin wani mai lemo kinsan shi
Murtala babu ruwansa tunda ta fara wancan lokacin
yace ba ruwansa da ita don haka ko magana baya
mata, kwara su lami da magajiya sau dubu da
Maryam gun murtala tunda ta nuna ita bata mada
mutunci, kuma wannan abu Maryam dashi tazo gidan
nan tunda tun farko zuwanta take kula gali mai shago
yara suke cemin sun gansu tare nake karyata wa ashe
da gaskiyarsu.
Bansan sanda na harzika nahau fadaba nace
dole murtala yace ba ruwansa da ita mana tunda ya
sami wansa suka fita kuma iskanci gada tayi shi yasa
take yinsa tunda ga uwata nan da 'ya'ya har uku ba'a
taba ganin ubansu barantana danginsu kullum cewa
ya mutu ake, ko ca kuke bamu san komaia bane
shiyasa aka sami bakin gayamana maganan banza
28
nan danan idonta yayi zazur tace ni Inna in har
maganar dana gaya miki ta baki haushi kiyi hakuri nib a haka nakenufi ba. bansan abinzai bata miki rai
haka ba.
Na tashi rai abace na je ni dakin garki na
janyo Maryam tana hura wuta nace muje ko mayafi
babu a ajikinta nace idan murtalan yazo ace nazo na
dauke ta ni inasonta haka da iskancin nata tunda shi
bayaso har baya mata magana akan kande tayi wata
magana nabar gidan. Ina zuwa nasa salamatu matar
kanina daura rowan zafi nasa Maryam ta tube
kayanta na dauko sabullun gana nahada da ruwan zafi
nan mai zafi so sai naje da kaina na gurje mata jikinta
tunda ga kanta na fara har kafarta wallahi idan kinga
kafar yarinyar nan kyace kullum a gona take wuni
bukiti biyu nayi mata saida na tabbatar tafita tas
sannan na kyale ta na dawo na dauki komai da
ruwanka na mitsitsika mata duk jikinta na ci ka
kwano da abinci tuwo shinkafa miayar Agushi nace
maza cinye, amma sam ta kasa cinyewa saboda
yunwar taci tacinye ta dole haka na kyaleta na bata
fura ta kara akan meye wannan ta fara kyan - kyali
don haka nace ta kwanta Maryam dai bacci harda
munshari.
Haka muka zauna cikin kwana uku ta murje
har tayi fari kiba a binka da mai doguwar fuska nan
da nan kyaunta ya fito na sakata a islamiyya kuma
karatu sosai sallah bata wuce ta wanda da ko sallati
bata iyaba ma. Babu maganar tallah in kinga Maryam
ta fita to taje makarantar islamiya ne yarinya mai
hazaka nan da nan tayi nisa a akaratun ta.
29
WATA UKU
cur babu wanda ya biyo bayan ta daga gidansu nima
ban damu ba da hakan don haka kanina ya bani
shawara na rinka tura Maryam gidan yan matarsa
safiya baza ta yi zaman ban zaba tunda mu a aganin
mu yanzu Məryamu ta wuce musata a firamare don
haka naringa tura Maryam gun safiya tana koyan
dinki da yarinya mai hazakace nan da nan ta fara
hada riga da farin karatun boko kwa tafara koyan
wasika.
A gida itama matar kanin na wa takan koya
mata turanci abinka da mai hazaka nan da nan
Maryam kamaninta suka canja tana samun ilimin
boko tare da na sana'a nai kyauta nayi. cikin wata
shida na siyar da ragona nahado da kudin hannuna na
sai mata keken dinki duk tsawon watanin nan babu
wanda ya waiwayo Mairo daga gidan muma haka
yanzu kan mairo ta zåma buderwa tunda she karunta
sha shida take aiki yanzu haka tana da izu arba'in da
biyu a Qur'ani mai girma ta fanin boko tana iya
rubutu duk binda kika ce ta haka takan karanta
abubuwa da yawa.
Ni kuwa duk wannan labarain da mairo take
ina tausayawa Maryama amma ina gani nafita shan
wuya tunda ita tana da wanda zai taimaka mata harya
karbar mata yancinta na 'ya mace mairo ce ta farko
dani daga tunani na da nake tace Amina duk har
yanzu bangaya miki karshen tsiyarmu da kande ba.
don kuwa saida kande tabani Maryam ta zama
mutum sosai kowa yana sha'awarta yana yabawa da
kyaunta da tarbiyarta mutane sun fara kai hari ana
30
sonta duk da dai bana barinta fita barkatai zance da
samari saboda ina lura da ita Maryam din inda
hankalinta yafi kwantawa akwai wani yana aiki nan
local government, din Babura daraktane a wannan
lokacin bakone ba hadejene to naga hanakalin
Maryam din ya kwanta da kusan kowa dake garin nan
yasan da mutumin yana neman ta.
To abu kusan wata biyu har ya nemi yaturo
iyayen sai nace to zanturashi yaje ya tambayi babanta
tukuna, turashin nan da nayi gurin babanta Malam
Murtala shi yajawo rigima da kande ta tayarwa da
Malam Murtala hankali kan larai sai ya kawo
Maryam gida wai sai ta dawo gidan ubanta da ke
shima sakarai ne babu kunya babu tsoron Allaha yaje
wai Maryam ta dawo gida yanaso idan ma auren zai
mata yayi mata agabansa. Nayi niyar maye kanina ya
hanani yace sam ba yarsa bace baiji kunyar duk
shekarin da tayi ba baizo ko son yarsa ya dauakata
amma da ga ita sai kayan jikinta.
Har Maryam tasa takarmi zata bi shi nace da safe
tazo inason ganinta ba komai yasa nafadi haka ba sai
don inason kafin safe na taushi ganina akan don mun
mata kaya ba wani abu bane.
Kamar yadda nayi niyyar nasami shi kanin nawa ne
masa magana akan kayenta yace shi bayana nufin ya
hanata kayanta bane ba a'a yana son idan zatayi
amfani dasu tazo ta dauka don yasan yaran kande
sune zasu saka ita Maryam din baza bartaba ta saka
ba nun ma naga gaskiyarsa nabata kekenta nace zan ringa aika mata dinkuna idan sun zamu kudin kuma
zanci gaba da aje mata kamar sauran.
31
To wai mairo ita kande ina yayan nata suna 'nan?'
ita lami an kai ta makarantar kwana tana aji hudu aka
korire tada ciki wata biyu wai malamin sune yayi
mata acan a makarantar.
Magajiya kuwa ita da Jummai suna nan su
suka maye gurbin Maryam na talla ai mairo da gaji
kasan yaran nan babu wanda zatayi wani abun arziki
ko wace ko sunan kirki ba'a akiranta da shi, wanda
kowa a duniya anason dansa ya amsu suna nagari don
nasan ran koyi dasu sunan nagari amma ita duk tabi
ta bata yaranta da sunan banza to ni yarda kikaji
nafadin nan haka nasani bansan suna sun agaskiya ba.
To kuma Mairo ta barta ta auri wanda take son a'a
bari dai tun da kin matsu na kara samiki nakara
samiki labarin kafin lokacin sallah ya yi shi mai
naiman nata Moh'd Balle ke nan wanda nace miki
mutumin Hadija ne duk da walakanci da kande ta
dinga yi masa bai damuba dak Allah yasa masa son
wannan yarinyar sannin kanki ne duk mai suna Bello
Allah yayi su da kwarjini da kuma bakar zuciya
amma sanin halin matar ubu bai kula da halin mairo
ba tunda idan tsiyarsa ta tashi idan yazo ai ta hana
Maryam din fita ya gaji da jira yatafi da aka ga
wannana bazai yiyu ba sai ta fara bin abin da kissa.
Idan yazo sai a turo magajiya da kayan abinci da
ruwa tazo tayi ta masa hira ita kuma Maryam din an
hanata fita ana cusa mata wai yace ya fasa yace
yanzon magajiya yake so don jahilci irin na kande
kayan Maryam masu kyau wanda mukai mata za'a
sawa magajiya tasa tafe take tana kararraya kusan
akullum haka kande kewa Moh'd Bello ita magajiyar
32
tana amsa kayar wai Maryam an mata alkawarin aure
da wani har ansa rana shiya sa ba zata fito ba.
Da Allah yasa ba azzalimin bawan sabane ana da
masa haka sai yazo ya sameni dayake ya saba dani da
zuwa yace kaka kinji abin da akace dani a gidan su
Maryam daman tafi sati bata fitowa zance sai dai
magajiya ta fito ta tayani hira. kinsan namiji duk
wanyonsa idan mace ta kulla masa wani makiraci sai
kiga ya zama wawa, don haka wannan makircin ya
samu karbuwa agurin Bello tunda yazomin da
maganar ya janye zai koma gun magajiya tunda mun
yaudareshi.
Nasan dai karshen alawa kasa amma duk da
haka bance masa komai ba naba shi hakuri nace yazo
gobe zanyi bincike na yi alwala nayi sallah nafila na
rokawa yarinyar nan abinda yafi alheri a rayuwarta
nashafa mairo na zuwa gurin naji idona yacika da
kwalla domin kuwa Maryam 'yar gatace tunda har
tana dama wata addu'a gaskiya nafita shiga kuna'a
rayuwata, Mairo tacigaba da labarinta a tunaninta ko
labarin da take bani ne. ya sani kuka. Tunda harda
acemin ihma kukama tukuna Amina.
Watan! Amina na dauki mayafina sai gidan Malam
Murtala muka gaisa da kande Malam yana tsakar
gida a kwance dama yazo maka yasa nayi kirana
Maryam nace Maryam haka zaki yimin ki ko yaran
nan Bello kice karya kara zuwa ko? Maryam ta bude
baki ta ce ta dafi kirji tace ni sam ba muyi haka dashi
ba. asalima idan yazo ya daina kirana sam sai
magajiya kuma inaga ni ya kamata nayi korafi da shi
tunda abin da yamin cin fuskane mai nayi masa zaice
33
baya sona wai magajiya yake so ai babu abinda ya
hadani da shi amma yace ya fasa kuma shine yafi
yace miki nace bana sonsa tana fada idonta duk sun
cika da kwalla nace duk maganar bata kuka bace,
juya kan kande nace kande ya ishiki akan yarinya nan
abinda kuke mini ya ishiki haka karkiga kinsa
Murtala yazo ya dauki yarinyan nan ki dauka don kin
isane dama munafarki kenan don ki rabata da mai
sonta ko? to kinyi karya don kuwa Allah yafiki na
kalli barinta wanda lami take kan keken Maryam tana
ta jagwalgwalawa kawai don mugunta na tashi da
sauri nace tashi mai uwa na kalli kande kici ga da
yiwa yarinya nan mugunta zakiga yadda Allah zai
mayarda don kuwa ba azzalimin bawarsa bane duk
wannan fitinar kece kika hada to ki sani ai Bello
mijin Maryam ne, sai ya aure ta akina arzukinsu in
gama fadar wannan kande ta rushe da kuka mai karfi
ba don komai ba sai don taga malam murtala yana
nan kafin yazo ya batamin rai na dade dabarin masa
gidansa don nasan yadda yake tsoaran ta duk abinda
tace yayimin zai min.
Washe gari da safe Bello kafin yaje aiki yazo
muka gaisa nayi masa bayanin duk irin kuke - kulen
da kande takes a tsakaninsu ya