tun kuma ranar bai zoba balantana
musan matsayoin shi ya kyalemu ko kuma yana nan
70
akan baker sa nasai munbar masa giadansa akullum
gari na wayewa kowa zata kama gabanta neman
abinda zamuci ya yanmu maza kuwa tun wanda
akayir rigima nan muka rabu a gidan Baba Maryam
bamu sake ganin kowa acikin suba itama karima duk
tayiwa hudubara Inna kunnen Uwar shegu tun da
muka dawo randa Inna ta tafi wani saurayinta yazo
tabishi haryau yanzu dagani sai Hadiza muke ta fadi
tashiAllah ya taimakeni Aminu yace zai biya mini
kudi nayi karatun Computer don haka yanzu komai
inaga zai zo mini da sauki ina ta zuwa gida ina
wannan tunanin ashe facin rain a gabana tunda ina
zuwa kofar gida naga motar mahaifinmu ina tura
kaina cikin falon naganshi kwance a falo nayi
sallama bai koa amsaba na shiga a tsorace kamar
barayon da aka kamo yayi sata.
Na tsugunna a kasan kafet nace ina wuri
Baba ya wurgeni da mugun kallo wai ku wane irin
mayu ne ban ace kuabar mini gidana ba to karkubar
gidan ni nasan matakina da zana dauka akanku Allah
ya kaimu gobe. Ina shiga na tarar Hadiza tana dakia a
zaune tayia tagumi na tambayeta ko Baba yayi mata
wata maza na tace sam ita baisan tana gidan ba
saboda sanda yazo ina bandaki don haka inaga har
yanzu bai samba ina nan. Nace to tayi shiru mu
kwanta karya jimu in yaso in Allah ya kaimu gobe
Aminu yace zai bani kudi zan shiga computer school
in yaso idan ya bamu sai inje in nemo mana gida
haya ko ince daki koda a Nyanya ne.
71
To wannan shine dalilin dawo warmu yanya ita
kuwa Karima mun kusa wata daya a Nyanya bata
samba inda muke sai sannan Hadiza tazo wani kanti
sannan taganta ta gaya mata muna Nyanya ita Sadiya
a lokacin tana makaranta kwana don haka da akayi
hutu naje na daukota na nuna mata inda muka koma
shikenan shi kuma mahaifinmu muka rabu bama
ganinsa baya ganin mu, daki biyu muka kama kusan
nace diya kaganmu ne diya kuma anan muke kwana,
kayan fa bawasu kaya bane abinci cine da yar
tarkacan kwanika wanda Innarmu ta barmana, duk
mun samo inda 'ya'yanmu maza suke mun kuma
gaya musu inda muke koda yake suna sun kasu kowa
da inda yake Usman yana karo yana aikin gyaran
wuta Moh'd kuma yana makaranta Poly nasarawa
don haka yakoma ma nasarawa da zama wani abu
kinsane ya dauki nauyinsa wanda muke nan unguwa
daya don haka kusan ince yadawo gidan su abokin su
suke masa kome Ibrahim kuma yana nan gareji yabi
yana tuka mota Isah ma anan yake sai dai shi yana
aikin bada takardane a tashar yamin kunga kowa ya
watsu.
Ita kuwa Karima ta zama kyakykyawar
karuwa don in akazo aka dauketa sai tayi kwana uku
babu ruwanta da kowa tunda ko zuwa tayi to in wani
abuta samo babu wanda zata ba ko wahala zata
kasheka inta dafa abinci ba zata bayarba don haka
ban dogara da itaba sam kullum nafita zan samo
mana abinda ya samu da haka harna tara kudi na
shiga computer cikin wata tara na hada diplomer
duka don haka bansha wuya ba nasami aiki.
72
nawa property inda muka hadu dake kenan Bulkisu
inbiki muntaba ja haka na kame mutunci na,
narufawa kaina asiri dani da 'yan Uwana duk sanda
sa'adiya zata tafi makaranta babu abinda take nema ta
rasa inayi iya kokarina akanta don karta shiga wani
hali kamar yadda muka shiga haka Hadiza duk data
gama karatunta da tace tana son ta shiga aikin
dansanda nayi iya baki kokarInna na samo mata ta
tafi don haka da kowa ya kama gabansa dana dauki
kudi karshen wata nakama hanya naje mubi naga
mahaifiya tayi tausayin Innar mu saboda yadda naga
ta rame tayi baki babu alamar yinwa ko rashin kyaun
makwanci a'a sam babu tantama rashin ganin mune
da tunanin yanzu awane hali muke har kukan tausayi
nayiwa kanmu tunba da tace tunda tazo ni kadaice
nazo gurinta babu wanda ya taba zuwa a tunanina
'yayyanmu maza suna zuwa tunda naga kowa yana
da rufin asirin sa amma ina kowa ya kama
hanyarsaAllah ya shirya addu'ar Inna kenan.
Koda yake banga laifinsu ba irin renon da aka
bamu ne dole yasa kowa baya tausayin kowa haka
najiyo nadawo da tausayin Innata fal cikina nazo na
nemi kowa nagaya masa naje mubi Inna kuma tana
gaishesu nayi hakane don insun mantama da ita to
sutuna karkuma wataran wani yace ace ina zuwa suga
kamar ina musu wani zagon kasa ne.
Allah cikin ikonsa ina nan Nyanya ina kuma aikina
na kuma kama kaina don harnayi 'Istibira'l'Allah ya
hadani da wani bawanAllah Nura abinda yahada mud
a anura kuwa fili yazo siya nan office namu to tunda
yazo sau daya yasiya shi ken an kuma duk sanda ya
73
tashi neman fili sai yazo office namu yakan bugo
mini waya yace yana nan zuwa idan yazo mukan
gaisa amma babu wani wasa saboda shi nura mutum
ne shi mai jin kai, don haka ni kuma nake dauke
kaina idan yazo tunda na fuskance shi wani lokaci ma
idan ogana yana nan ko kalon inda yake banayi tunda
in bayanan dole aikin sai dani anna haka ashe shi
nura wai sona yake don haka ra'ayinsa in yanason
abu sai yaja masa aji .
Ni kuma ta bangare na ina sha'awar hakan
don banason mazan nan masu rawan kai don nasan
babu komai acikinsu sai neman mata hakan da nura
yake sai nake masa kalom kamili don haka kafin nura
ya furta min yana sona tuni sonsa ya dada a zuciyata
don haka nura ya furta mini yana sona ne ta hanyar
waya ya tambayeni numbers wayata a kan cewa yazo
neman oga nane bai same shi ba shine yace na basa
number office namu yana fita ya bugo mana waya
kasancewar yasan ni zana dauka ina dauka ne yake
bayyana kansa a wuri na yana sona da aure mun dau
lokaci muna hirar fahimtar juna tun daga nan dai
muka fara fahimtar juna don nura ya bayyana mini
bai taba yin aureba nima kuma naga hakan, don shi
namiji mai iyali in ka gansa kasan shi ba wani abu
bane ba yasa nura ya shiga raina lokaci daya sai
kwarjininsa nura ba fari bane bakine bakinmu irin
wulik yana da idanu kwala - kwala bashi da wani
kyau wanda zam fasalta muku nura bashi da surutu
bashsi da irin kananan maganganu duk matar da
takeson ta aje namiji mai kwarjini zata so ace nura
mijinta tane don kuwa kwarjini yanasa a mutunta
74
namiji cikin dan kankanin lokaci muka amince da
juna nida nura min yiwa juna alkawarin aure cikin
wata uku.
Lokacin da bikina ya rage saura sati uku
lokacin ne na rasa wa zai zamo mun Uba ko Uwa a
harkar cikin ikonAllah na nemi Baba Maryam yayi
mana ya kuma amince na dauki Nura na kaishi gidan
Baba Maryam da Hajiya Haliama da sunan sune
iyayena Nura yasan gidan da nake a Nyanya bai taba
tambaya ta ba ni kuma bance masa komai ba tunda ni
ai nafison hakan Hajiaya yarda akayi muka hadu da
Hajiya wato yaya Anty Ramatu anan Nyanya cikin
gidan da muke zaune dake dakuna ne har guda shida
mu munkama biyu Hajiya kuma suna zaune aguda
hudu ita da mijinta da yaranta guda biyar kusan nace
na dauki Hajiya tamkar Uwata tana da 'ya mai suna
na don haka take cemin 'yata son yarana ne ya dada
hada jininmu da Hajiya tsananin shakuwar mud a
Hajiya tasa duk wata damuwata inagaya mata don
duk wani sirrina kamar kudInna da abinda nake ciki
da samarina asalima Hajiya ita tabani shawara nayi
Istibira'I don haka babu abinda nake boyewa
Hajiyanema na da Nura babu abinda bata sani ba
Hajiya tasan labarina kusan nace tana farkon
dawowanrmu gidan da aurena ya tashi Hajiya tayi
Uwa tayi Uba ko ince baban Khalifa yayi Uba sun
tashi haikan don sharemin hawaye tunda nake a
duniya bantaba ganin mutane masu mutunta mutane
irin yau Babura Hajiya uwarta mutumiyar Baburace
uba daya suka hada da Anty Ramatu mijinta tama
mutumin Babura ne don haka naga karanci gurin
75
mutanan nan zo ku gansu sai kice bikin yarsu ta
cikinsu ake.
Ran aurena da Nura baba Maryam aure kawai
ya daura ya dako gudun mowa dubu Ashirin yabani
amma Hajiya da Baban Khalifa sune gado kujeru
kayan kichin duk wani abu da zaʼayiwa yarinya dai –
dai gwargwado bayin Allah nan sunyi ranar da za'a
kaini dakina ne Baban Khalifa ya zaunar dani kamar
yadda kowane uban kwarai yake wa yansa ya faramin
wa'azi kamar haka wajibine gareki yake yar uwa
musulma kiyi biyayya ga mijinki da kyautata masa
manzo Allah (S.A.W) yace idan mace tayi sallarta
biyar kuma ta kiyaye farjinta, tabi mijinta to zata
shiga aljanna ta kowace kofa take su daga aikin
kofofin aljanna to kinga anan babu wanda aka hala
tawa aljanna cikin sauki irin mata don haka Amina ki
kiyaye tunda ni aganina kin auri mutum kina sonsa
yana sonki to maizai hana ki kayutatta masa ko
bazaki sami ladaba saboda kaunar dake tsakanin ku
ballan tana banda lada harda aljanna.
Yaci gaba da cewa Amina bai halatta ga mace
tayi aure ba alhali mijinta yana tare da ita said a
izininsa kuma kada tabawa wani dammar shiga
gidansa sai da izininsa hakan manzonAllah (S.A.W)
yace idan miji ya kira mtarsa zuwa shinfidarsa batazo
ba har ya kwana yana fushi da ita, to mala'iku zasu yi
ta tsine mata har gari ta wayi. A wata ruwayan kuma
manzon yace babu wani namiji da zai kira matarsa
shinfidarsa sanan taki amsa masa face (Allah) wanda
yake sama yayi fushi da ita har sai mijin ya yarda da
ita.
76
To mata nagari masu biyayya ne gamazajensu kuma
masus kiyewa ne ga kansu da asirin mazajensu da
dukiyoyinsu lokacin da basu nan saboda kiyayewar
daAllah ya dora musu wanna yana wajabta wa mace
tayi biyayya ga mijinta a komai na hidima da tafiya
tare da shi, dab a da kanta gare shi da sauran
abubuwan kamara yadda manzon Allah tsira da
amincinAllah su tabbata agare shi ya nuna.
Allah madau kakin sarki yace mata ma suna
da hakkin akan mazajensu irin yadda miji yake dashi
akan matarsa acikin shari'a daga kyan zama da rashin
cutarwa ance maza masus iko ne akan mata to idan
mace bata yi masa hidima ba, maimakon haka ma
shine mai hidimar, ta zama itace mai ikon a kansa ke
nan Allah ya wajab tawa namiji ciyar da ita, da
tufatar da ita da samara da matsuguni gareta, akan shi
yafi dadi da ita kuma tayi masa hidima da abinda
al'adar zaman aure ta gudana a kai sannan kuma duk
wata yarjejeniya tsakanin mutane ana yinta ne aka
abinda al'ada ta gudana a kansa. Abinsa al'ada kuwa
mace itace take hidima da kula da ayyukan cikin
gida.
Ba dai - dai bane a dai - daita tsakanin mace
mai matsayi da wanda bata kai taba ko tsakanin mai
talauci da maiwadata gadai wadda tafi duk matan
duniya matsayi itace fadimatu, yaddar Allah ta
tabbataa gareta ta kasance tanayiwa mijinta hidima
har tazo wajen manzon Allah tsira da amincinAllah
su tabbata a gare shi ta kawo kukanta kan wahala da
take sha wajen aikin gida amma bai dauke mata shi
ba Amina ina shawarar ki daki nemi izni wajen
77
mijinki ki shiga islamiya don zaki fahinci abubuwa
da yawa zan iya ce miki ban gaya miki komai ba
gamai da zaman aure wannan na gutsura ne don
nasan baki san komai ba game da aure tunda baki
taba yiba. Don haka kid age ki nemi sani gurin wanda
suka sani ki rokeshi ya sakaki in kuma baya so to shi
ya koya miki in bashi da lokaci ya samo mai koyar
dake kinji ko na daga kaina jeki mutane na jiranki
Allah yayi miki albarka da Inna ta matar wanta da
take wurinsa a can Mubi da Hajiya sune mukashihe
mota kai amarya dasu gidana a garki II dan karamin
gida ciki da falo da bandaki a tsakar gida kichin da
sito duka a hade an shirya mini dakina da faloa duka
babu abinda Hajiya da baban Khalifa basuyi mini ba
tunda kusan sai nace kowa gudun mowa ya bayar
sune sukayi komai Innata daman dake ba komai gare
taba sai ido da godiwa Allah.
Inna tayi kuka har kuka wa Hajiya da baban
Khalifa kan abinda sukayi mini tayi musu addu'a da
fatan Alhairi Inna take gaya mini bata bakin ciki da
bacin rai irin na karima takaicin abinda karima take
Inna tace zata dashe bata zo ganin muba saboda
batason tazo taga yadda karima ta mayar da kanta,
Karima ta mayar da kanta mashayiya shangiya taba
kwaya a gaban kowa wani abu ban tsoro daf da
bikina Karima ta gamu da wani saurayin dan koken
nan day a mayar da ita yar koken shine abinda ayafi
daga wa Inna ahankali tunda ranar wurina duk
mutane sun cika gidan Karima ta shigo a buge tasha
koken ta bugu ko ince ta shaki koken din tana zaune
ido yayi mata jajir Inna sai kuka take yansanda sukai
78
mana sallama wai suna nemanta an kamasu da hodar
ibilis itada saurayin ta yanzu haka saurayin yana
hannunsu don haka itama zasu tafi da ita.
Inna tana kallo aka kada keyarta aka tafi da ita babu
kuma wanda zai bita donshi baban Khalifa daga shi
har matarsa basa harkar karima don haka har aka
gama bikina atana can a kulle da wannan bakin ciki
Inna ta wuce Mubi.
Zamana da Nura zama wanda tunda na shiga
gidan bangane kansaba matsalata ta farko itace nura
bai san addinin sa basa rigimar farko da muka farad a
nura baisan yadda ake kwanciyar aure ba yadda Allah
da manzonsa sukace miji ya kwanta da matarsa yasha
baban da yadda nura yakeyi duk dare sai naci duka
kafin nura ya kwanta dani sai yace sai dai ya nemeni
ta dubura wanda duk da bansan komai ba nasan
hakan ya sabawa addinin mu to idan naki yakan mini
duka ya nemeni ta karfin tsiya, Da safe idan ya tashi
fita yakan bani kudin abinci da zanci na safe ya auna
mini abincin rana da dare iya ciki na kwai idan nayi
baki sai daia nabasu na hakura idan yana gida
magana kadan ta hadani dashi duka, ya hanani aiki
sam bana fita ko ina bayason yaga kowa yazo gurina
idan ya fita ya dawo ya ringa tambaya suwaye suka
Zo.
Wani abu da yake bania haushi da Nura
wanda kuma na rasa fahimtara Nura baya fita yawo
sai karafe ukun dare yayi wata shiga yasa bindiga
ajikinsa ya fice idan yana shiri zai fita yasa son ko
kadan naji motsi nima yadda akayi nagane kullum
idana na tshi da asuba zanji sallah ko kuma idan na
79
farka zanyi fitsari naga baya nan shine arantan na
hana idona bacci ina ganinsa yana shiryawa don haka
ranar zuciyata ta bani Nura dan fashine, Asalima
Nura baya son maganar iyayensa sam yayi min
alkawarin idan munyi biki zai kaini garinsu yace dani
iyayensa sun mutu don haka da aka tashi bikinmu ma
abinda ya gayawa Baban Khalifa kenan sai wasu
dattijo ya kawo wan 'yan uwan Baban sane yanzu
kuma na gane karya ne dan fashi na aura tun sanda
Nura ya fita na tashi nayi alwala nake ta kuka kamar
an aikomini uwata ta mutu.
kamara Ni Amina ina zansa raina ina ganin
nayi aure na huta da yawan wahala ashe ba hutawa
nayi ba wahala nashiga zabuwa tunda gashi na auri
wanda zai gurgunta mini rayuwata yana nemana ta
inda zai lalatani gashi ya hanani aikina ya hanani
kowa yazo gurina kullum duka ga babban matsala
wannan fitar daren da yake yi wanda na tabbata fashi
yake zuwa tunda na taba kamashi ya dawo yana cewa
bacci nake ya zauna yana kirga kudi masu yawa na
tsorata tad a ganin yawan kudin nan nama rasa yadda
zanaga Hajiya in gaya mata matsalata idan kunan na
dage nace zanfita da karfi nasan bazai sakeni ba kar
kuma na gudu yazo ya kasheni hargida islamiyar da
baban Khalifa yace ya sakani itama ya kicincine to
shima bai yiba tayaya zai sakeni koya barni nayi.
Kawai wata yarinya makociyar mu kusan kullum
yarinyar inta dawo daga makaranta tana shigowa
muna gaisawa har takan kawo mini littafai na hausa
ina karantawa to ahaka rannan ta shigo nake gaya
mata inason ta kawo na addini inrinka karantawa
80
kona samu karuwa na kuma sami addu'oin d azan
ringa yi saboda dai kewar wani bakin ciki. Na kuwa
sa'a ta kawo mini harda wanda nake nema na addu'oi
da wani littafi mata muminai naji dadin littafin
tunkan na fara karanta shi dana duba abubuwan dake
ciki nazo kurin da aka rubuta.
IDAN MAСЕ ВАТA SON MIJINTA KUMA BA
TA SON CI GABA DA ZAMA DA SHI YAYA
ZATA YI?
Da sauri na tafi nemo inda topic yake fako
abinda marubucin yaceAllaha madaukakin sarki
yace idan kunji tsoron cewa ba za su tsaida doko kin
Allah ba, to babu laifi agare su cikin abin da ta fanshi
kanta dashi (Bakara: 229) Al-hafiz Ibnu Kathir yace
acikin tafsirinsa idan ma'aurata suka saba da juna
matar bat a wa mijin hakkinsa ta ki shi kuma ba zata
iyaci gaba da zama dashi ba, to ya hallata gare tat a
fanshi kanta daga gare shi, ta bashi abinda ya bat a
babu komai akanta idonta bashi kumashi ma babu
komai a gareshi idan ya karba wannan shine KHIR"I
sake - saken duniya suka cika min ciki nayi imanin
wannan mutumin na dako sadakinsa na bashi kasheni
zaiyi babu abinda ya damesa sai dai shima a kashe
shi.
Gashi idan ya fita da safe wani lokacin sai ya
dawo sau wajen hudu yanzu haka tunda yarinyar nan
ta kawo mini wannan littafin bata sake zuwa ba tunda
yanzu ya lura tana zuwa ta debai mini kewa don haka
idan zai fita sai yasa mukulli ya kulle ni.
Abin ya fara isata don ko na fara tunanin manfurta
wa rana laraba ya manta bai rufe gidan ba yafita ya
81
barni a bude nasa kayanaa ko wanaka banyi ban a
fada gidan su yarinyar nan sunan ta Usaina tana
ganina tana tsakar gida tana wanke - wanke tayi sauri
ta tareni tace lafiya Amina nace don Allah idan kina
da kudi ki dako mini dari biyu da sauri muna tsaya
mamarta ta fito tasame mu tace ina zaki nace mana
Asibiti zani Usaina tayi sauri yaje ta dauko mini dari
biyu batare da mamarta tasan halin da muke ciki ba,
mamar Usaina ta kalleni taga irin shigar da nayi ta
kuma lura kamar a tsorace nake tace Amina ina fatan
ba wani abu bane ta faru tsakanin ki damai gidan nayi
saurin wangale bakina nace, haba mama babu komai
asibiti kawai zani shi yasa nace bari na gaya miki zan
kuma ba Usaina mukulli in yazo ta bashi koda ban
dawo da wuri ba.
Mukayi sallama da mamar Usaina, Usaina ta
biyo bayana ta bani dari biyu muna lekowa kofar gida
ina cemata saina dawo juyawar nan da zanyi Nurane
a bayana Usaina ta fada gidan su da sauri da karfi
yasa hannu ya jawoni tundaga kofar gidan su Usaina
har cikin gidansa yana dukana da kafa tun ina bashi
hakuri harna galabai ta nayi shiru bakina jinni ke fita
idona ya juye ga yunwa na gallabata babu abinda
naci ya fita yabarni kwance niba suma nayio ba niba
mai raba yayi maganganu masu yawa bazan iya
maimaita suba saboda duk kunnuwana dasu - dasu
nake jinsu. Ban farko ba sai wajan karfe uku na
yamma na rarrafa naje kichin na dauki wata guntuwar
miyata ina dagarin kwaki na dauka na cakuda da
niyar ko ruwa ban saba ina kaiwa bakina taunuwa ya
kasa samuwa balantana hadiyewa bashiri na furzar da
82
abinda yake bakina nasan na shiga wani yanayi
wanda bansan dashi ba.
Na zauna zanyi kuka duk naji makoshina
yarike naga wannan bazata kaini ba tunda bashi da
magani don haka na tashi cikin mayen yunwa da
wahala ta duka na dago tagar dakina naga gilas ne na
duba agogo na ga karfe biyar na tabbatar Nura ya
kusa dawowa na tuna furucinsa wanda kunnena ya
jiyo mini wanda yace dukama sai nadawo na tabbatar
shi agurinsa wannan ba wani, abu bane, na zabura da
karfin zuciya na dako tabarya a kichin na daki gilas
din dakin ya fashe tatsatsa na zura kafata sai danaji ni
a kasa sannan na zura sauran jikina daman kudin da
Usaina ta bani na sashi acikin rigar nono na, nan da
nan na fada wani lungu wanda zanyi saurin bulla titi
ina zuwa bakin titi naga bus ana maraba yanya nan da
nana nafada na fito da kudin da Usaina ta bani dari na
mikawa mai karbar kudin mota bai tambayan ba ani
kuma ban gaya masaba ana zuwa Nyanya dai - dai
kofar gidan mu sai wata mata tace akwai na nan ina
dubawa naga nima inda zan saukane don haka na
sakko na karbi canjina.
Ina shiga naga dakin Hajiya Wasu kabilune
namu dakuna na duka a kulle da makulli na bude baki
zanyi magana inason na tambayi kabilun inasu
Hadiza suke naji bakin ya rike wuyana ya rike sam
bazan iya magana ba to anan hankali nay a dawo
jikina na fashe da kuka na tabbatawa kaina wannan
mutumin ya fasamin wani abu a wuya na nayi kuka
kamara raiana zai fita tunda nake ban taba kuka
kamar haka don tun ina gania har nazo bana gani
83
idon ya zama dusu - dusu dolene nayi kuka waje zai
tsayamin na sami magani? shin wai waye zai bi mini
hakkina akan nura? su Hajiya da nake takama dasu
bansan inda suke ba to in nagansu ma yazasu dani
tunda ba iyayena bane dole suma suna da nasu
"ya"yan.
yanzu idan na tsaya anan nasan dole Nura yazo nema
na idona - idon Nura kuwa zai iya kashse ni don haka
dole na tashi naje neman inda zan fake ko naje wajen
Baba Maryam in kuma nemi su Moh'd duk da nasan
ba zuminci zne damu ba baran tana wani yayi tunanin
wani zai taimake shi koda yake banga lefinmu ba
ukubar da mahaifinmu yasamu ita tasa kowa baya
tausayin kowa.
Na sake komawa kan tunanina nada dolene ko
bazan iya magana da za'a gane ba bari naje gurin
maman iyabo in yaso ko rubuta mata ane nayi ta gaya
mini inda su Hajiya suka koma don inaga ko zan
nemi Baba Maryam ya kamata na nemi su Hajiya
tunda su nasan zasu boyenin in yaso Baban Khalifa
yayi mini jagora zuwa gurin Baba Maryamn.
mairo ce ta nunfasa tace turkashi lallai Amina kin sha
wahala to ya akayi.?
84
Nagode mu hadu a
MAHAIFINA NA 2
SARATU LAWAL NUHU
GSM-08028405320
wannan littafin goron sallah ne ga dukkanin dauka cin musulmi Allah kasa abinda mukayi
karbabbene kuskuren da mukayi Allah ya yafe mana
amen.
85
MAHAIFINAH
2
ANA
SARATU LAWAN NUHU
'YANKANNENA
Aishatu Lawan Nuhu
Farida Lawan Nuhu
Balikisu Usman
Ummatu Sabo
Samira Nasiru
Usaina Usman
Ina ba makaranta Littafin Mahaifina 1 hakuri
akan kura-kuran da aka samu daga Na'urar Computer ne, misalin
-Amaryakar maimakon Abubakar
- Baba Maryam maimakon Babura
da kuma wanda baza'a rasaba.
-3-
Na duba naga biyar saura kwata na
tabbata dai idan Nura yazo yaga bana nan zai
taho nemana gashi kuma bani da bakin da zanyi
magana, na fito bakin titi gurin Shamsu mai
shayi tunda nasan ya iya karatu najashi gurin
kasa na rubuta masa INASON KAKAINI
GIDAN HAJIYA MAMAN KALIFA. Shamsu
yagigice sai hawaye yace "Amina yaya
maiyafaru? yaya naga kin dawo haka bakya iya
Magana?" Na daga kaina, anan yace tsaya ina
zuwa, yaje ya sallami mutanen dake siyan shayi
ya sami wani yaro yace ya tsare masa yana dawo
wa.
Banyi mamakin halin danaga Shamsu ya
shiga akainaba, don shakuwar da muka yi da shi
kuma a dalilina yake aje kayan shayinsa a
dakinmu. Asalima nina bashi jarin shayin da
yake yi, don haka akwai dangantaka mai karfi
tsakanina da Shamsu. Banyi mamakin kukan da
naga Shamsu yanayi don ya ganni cikin wani
haliba, munje bakin titi mun shiga motar
maraba, bamu dadeba tunda babu nisa
tsakaninsu yace "akwai na nan”, Shamsu yana
rike da hannuna kamar wata yarinya har cikin
gidan. Shamsu yana yin sallam maman kalifa na
tsakar gida tana shara ta taso ta rikeni "lafiya?
yanaga haka? mai ya faru?" Shamsu ya sake
fashewa da kuka yace: "Hajiya yadda kuka ga
-4-
Amina haka naganta, inaga ko Magana batayi
don nima rubutamin tayi tace na kawo ta nan
gurin ki." Hajiya ta kalleni tace: "lafiya? mai
yafaru baki Magana?" Na dagawa Hajiya rigata
ta fashe da kuka mai ruri, duk da lalurar danake
fama da ita sai da naji tausayin Maman kalifa a
raina, naji wani farin ciki ya kamani don ni na
san ina da gata tunda na sami uwa mai tausayina
ha tana kuka saboda ni, ga kuma Shamsu kanina
shima na samu, tunda dole nace shamsu kanina
nasan shekarunsa bazasu wuce ashirin da uku
ba.
Shamsu ya koma da niyar gobe zai zo
yaga halin da nake ciki. Yana fita hajjiya tace:
"bari baban kalifa yazo muje Asibiti" kafin ta
rufe bakinta ya shigo, maman kalifa tayi masa
bayanin abinda ta gani yace: "ai babu zama sai
asibiti." Duk ta rude tana cewa "Amina ai
dukane" haka baban kalifa ya daka mata tsawa
yace: "wane irin rashin hankali ne haka uwani
kibari ta samu baki mana komai zata ansa"
Mun iso general Hospital da misalin
karfe bakwai na yamma, munyi sa'a likitan
yamma bai tafiba don haka ya bamu gado ya
shiga dubani ko ina. Dr ya yi kokarin yaga nayi
magana kona daga wuyana, kafin Dr ya bar kai
na, sai da ya tabbatawa su maman kalifa duka ne
kuma yana kyauta zaton an taka mini wuya ne
5-
don haka yanzu zasu rinka min allura za kuma
su sa mini ruwa, saboda bazan iyacin abinciba.
Baban kalifa yace: "don Allah likita ina so ka
rubuta duk ciwon da kagani ajikinta don ina son
na kaiwa police report." Baban kalifa ransa ya
baci fada yake yana cewa "wallahi ko waye
bazan yarda ba", ina daga kai na nan baban
kalifa ya da da harzuka yace: "wallahi sai naga
wanda ya tsaya masa". Ni dai ina kwance abinda
ya dameni shi ne ko ina ciwo yake mini ina son
na gayawa Hajjiya idan Şhamsu yazo ta gaya
masa kar ya sake ya gayawa Nura inda nake,
amma dole na hakura babu yanda zanyi tunda
ko na rubutawa Hajiya ba zata iya karatawa ba.
Saboda alluran da aka yi min da ruwan da
aka saka mini a maimakon abinci, nan da nan
bacci ya dauke ni ban farkaba sai da safe.
Bangaren Nura kuwa karfe bakwai na
yamma ya dawo ya tarar bana nan yaga ta inda
na fito, nan da nan ya fada gidan su Usaina ko
sallama babu ya tarar da Usaina a tsakar gida
yace: "lallai sai ta fito masa dani ko kuma