zuwa suka tarar da tana ta sahrar barci sai matar
kanin ce take ta kaida komowa tunda ganan ma nasan
Allah ne ya kaddara zamu hadu da mairo shi yasa
taga gidan Anty amma sam duk wanda yaga gidan da
50
mairo take ciki da irin makwaneinta kasan tana
zaman gidan Anty ne don mutunci badon kudiba.
Anty Nafisa itace matar kanin na mairo don haka da
ita muka zauna muka gaisa har suka taba yar hira aita
da Anty kasancewar su kawaye to ganin Anty
Rahama najin kunya ata kasa maganar Mairo shine
nace da Anty Nafi mun biyuo sawun mairo ne don
bana nan na tarar bata nan koda yake Anty ma tace
bata koyi mata sallama ba itama dubawa tayi ta tarar
bata nan don haka shine muka zo mu bada hakuri
tunda dai babu maganra buncike ansan dai duk
wanda yatafi baiyi sallama da abokin zamansa ba to
lallaa bau lafiya don haka mudai muna rokon arziki
ko mai akayi ma ayi hakuri insha Allahu baza'a kara
ba.
Harna gama magana ta Anty Nafi bata tanka
mini ba, sai dana kai aya sannan ta kalleni ni kai na
nasan kallon na bacin rai ne tace ke Amina ya rinyace
ba kuma ke kika zo kika karbi yaya mairo ba Rahama
bari na gaya miki gaskiya abinda kanwarki Samira
tayi mini bata kyauta ba ayaya mace kamar yaya
mairo ace har ana zagin iyayenta mai yayi zafi abin
haushin kuma shine kina gidan yaya mairo tazo
ayimiki ba kema kinsan alfarma kika nema tunda da
kar dan uwanta yafita don ta nuna masa tana sonme
tunda hakane ta dawo kenan kiji ki nemi 'yar aiki
wanda 'yan uwanki zasu zaga ahar su gaji babu inda
zata tunda kudi take nemi Anty Rahama da saurinta
tasa hannu ta dakatar da Anty nafia tace haba Nafisa
gaskiya banyi zaton zakiyi mini mummunar fahimta
haka tunda tun tuni muke tare dake kuma matsalar
51
samira babu wanda baki sani ba kinsan dai nima bana
wuce abinda yafi haka agunta kawai da ina kyaleta
ne saboda iyayanmu sun mutu kuma nice gaba da aita
dole nayi hakuri da ita fatana dai kullum Allah ya
shiryeta.
Anty Nafi ta taba baki tace to Rahama kema
kin san dai kece dole ke tashafa don haka yanzu kece
kawai zakiyi hakuri amma banda yaya mairo bazata
komaba idan Anty Nafi tace bazata koma basai naji
gabana ya fadi zuciyata san bana yinin dadi ba Anty
Nafi tana cikin hakikancewa tana fada mairo ta fita
daga dakin da take bacci duk fuskarta abin bacci tazo
ta zauna kusa dani duk muka gaisheta nida Anty
Rahama ta amsa babu alamar canjin fuska ko kadan
hakan yasa naji dadi sosai duk da haka Anty Nafi
bata daina fadan da take aba.
Mairo ce ta dakatar da ita tace mairo ai duk
wannan abu ba abun fada bane nidai girma da
arzikine ya kainia gidan ki don haka mutunci ne zai
rabamu da girmana da shekaru na ace ban wuce
zagiba nice nayi magana ce wai mairo akan mai har
samira ta zageki mairo ta juyo tana daga hannu tace
wallahi tsautsayi gani nayi kawai ta balla jakarki tana
kwasar miki kaya tana zubawa a tata jakar naga ta
kwashe duk kayan shafe - shafe nan naki takalma ta
sake a ajakarta tsaf zata wuce dasu shine nace mata
ke kuwa baiwar Allah ko so kike ai kyabari tazo
tukunna amma ba bata nan ba ki daukar mata kaya
daga wannan bana karaba sai kuwa ta fara dura mini
ashar wanda ko ina yarinya ban taba samun wanda
yayi mun irin wannan zagin ba don haka ki nemi mai
52
cikin ki daman ni taimakone don bana son zama haka
in dama Nafi tana barina Ina kama abubuwa aida
haka bata samu ba tajuya ta kalli Nafi tace to kinga
yarda kayi mini yanzu sai ki ringa barina ina aiki inba
so kike naje wata ran a dakeni ba.
Anty Ramatu ta kaicine, haushi duka suka
tarar matar ta kasa gane a'inatake don ko magana
bata sake ba don tasan duk abinda zata fada baza'a
fahimce taba don haka ta durkusa har kasa tace don
Allah mairo ki gafarceni nasan na miki laifi tunda na
kasa hana samira ta zage ki ni kuma nayi hakane don
nina banfi karfi hakan ba amma nayi miki alkawari
insha Allah haka bazata sake faruwa mairo ta kalli
Anty Ramatu cikin tausayawa tace babu komai
zankoma tajuyo tace Nafi babu koma ki bari na koma
idan ta sake ai kuma shikenan daman tasan karshen
zancen.
BAYAN MUN KOMA L.G.E. Da Mairo daki muna
hira Mairo ta matsamin da tambaya akan sai na
gayamata meye tsakanina da Anty Ramatu da hara
kanwartaa ta tsaneni hakla ita azatonta nima 'yar
uwarAnty Ramatu ce ta yanzu daga bayanin samara
nasan babu wata dangan taka inda akwai ma bamai
karfi bace don haka inason nasan tsakanin ku in
akwai abinda zan iya taimaka miki donni kafin
dawowata gidan nan saboda ke nadawo don nadade
banga abinda ya batAmina raiba kamar yadda naga
yarinyar nan tayi miki akan me zata daukar miki
kayanki? Atunaninta yar uwartace tayi miki nikam
ba tsaya kyam ina kallon mairo har tausayi ta bani
don ganin yarda ranta ya baci a kaina.
53
shinkafa ko wake ta dafa manato duk sa. nuka
samu wannana murna mukeyi.
Wataran takan sirfa masara akai mata anika injin tayi
mana tuwo muci da rana da dare babu abin day a
damu babanmu damu muna zaune muna kalonsa
zaizo da giyarasa ya zauna fato yasha ya koshi in'yan
fadan suna kusa yayiwa Innarmu duka wani lokaci
kuma ya wuce yayi kwanciyarsa. Makaranta ko da
mukeyi makaran tace mai arha da kafa muke tafiya
babu abinda yayi masa zafi da littafi ko Uniform
namu kowa da kansa yake nasan za kuso kusan yadda
mukeyi ni Amina tun ina yarinyata ina da sanyasa
sosai don haka akwai wata mata maman Nabila muna
shiri da naibilan sosai akullum idan na taso ina zuwa
ina mata renon nabilan ina kuma mata wanke
wanke to anan nake samu nake cin abinci kudin da
take bani na wanke - wanke dasus nake siyan kayan
makaranta dasu nake siyan littafi hara kudin
makaranata takan bani sabulun wanka daman
shafawa mijinta kuma yakan mini dinki dake kowa
yasan halinda muke ciki agurin namu
To muna nan har mukaje aji hudu na firamare
muna tare da maman Nabila kasan cewar na fara
girma budurcina ya fara fitiwa don haka mutane suka
fara zuga mamana nabila wai lallai idan bata wareni
daga gidan taba mijinta zau aureni saboda gaskiya
baban nabila yana kyatatat mini ni kuma nasan ba
wai yana sona bane yanyine don yana tausayi na
tunda kowa yasan yarda babanmu yake mana.
Abinda kuma ya dada yan matsala shine Karima
babbar yarmu aka koro daga makarantar kwana tayi
ciki to wannan abun kunya data ja mana yasa anata
tsanatsAmina mu idan kika koma ta bangaran
babanmu shi babu ruwansa hakan baisaba ya canja
halinsa ko kadan. To yana daya daga cikin abinda
yasa maman Nabila tadau zigar mutane a kaina ta
koreni daga gidanta.
Naso na shiga wani hali saboda kusan nace
duk kusan abubuwa da dama bani da damarsu tunda
dai - dai da abinci bana cin na gidanmu kusan nace
har mamanmu ina kawowa to yanzu fa ina zansa
kaina don wannan damuwar har rama ata sani ina na
cikin damuwa don Uniform dina duk ya yage Innata
kuma bata da kudin da zatayi mini wani har Allah
yasa naje aji biyar naje yin jarrabawar fita daga
makaranta cikin ikon Allah nide Innata da yaya
Moh'd biga bigarsu aka biya mini komaia da
makaranta suka buakata har naci jarabawata, wato
alokacin da muka zauna a gida kafin jarrabawata ta
fitoAllah ya hadani da wani Amini yana zaune anan
cikin shiyarmu ne yake kullum yana gidan mu gurin
yaya Usman ashe shi sona yake ana nan har Allah
yasa muka saba ko ince muka shaku tunda a lokacin
duk muna maganar aure don haka aya tsayamin kaida
fata yasamo mini makaranta tudun wada anan zone 3
ya kashe kudi sosai akaina kafin na fara zuwa
makarantar harna fara ya bani kudin mota watan
kuma idan zai kai yayan wanasa makaranta yazo ya
hada dani ya kaini daya wansane yake aiki anan
bankin su babanmu din ko a office kowa yasan halin
babanmu yadda yake mana don haka wani lokacin
idan wasu kudi suka fito nasa a office sukan hana shi
57
matsalarsa domin kwanaki na gayawa yayanku don
haka daga yau bazan sake fadawa ki gayawa yan
uwanki inba hakaba zan koreku daga gidan daga ku
har uwar taku, kaji mutum babu abinda kake mana ba
ruwanka da cinmu shanmu suturanmu dai - dai da
sabulun wanka baya siya mana ita kanta Innar tamu
tsoron bangarensa take koda yake dai falo dayane
daga ka shiga sai ka wuce dakunan guda uku to biyu
namu daya Innarmu daya namu shi kuma yana cikin
daya mai hade da bandaki daga gefen falo kicin yake
tanan ake bi aje baskwata anan 'ya'yanmu suke
komai na mahaifinmu yana dakinsa to wannan gida
da muka cika masa ya tsaya masa arai akullum
fadansa mu barmasa gidansa muncika masa gida ana
masa kazanta banda abin baba ai dole ayi maka
kazanta tunda ka cika gida da jama'a kuma ga talauci
ka barsu dashi idan kuka shiga dan mahaifinmu zaki
zaci munfi kowa jin dadi don kina shiga faloa zaki
tarar to karki ga abinda aka shirya a falon kujeru jah
- jaye kafet jah labulayen du jah- jaye T.V Vedio,
Vedio. C.I.D. Redio C.D gidan talabijin din kansa
abin kallo ne idan kinga yadda ya shirya table din cin
abinci gidan ke kyace ko restaurant bai fimu abinci
ba amma ina duk da wannan dukiyar daya zuba bamu
isa mu zauna a falo ba balantana mua taba abin kallo
bamu isa ba wannan faloa shine yake zama da abokan
sa.
Inna dake ita mai gudun zuciya ce bata ko
zuwa gurin ma don kartayi abinda za'a bata mata rai
ko girki zata yi acan baskwata take dora kayanta akan
idace bata ko taba masa kuka gas dinsa.
60
A times nakan zauna nayi tunani ko haihuwace baya
so amma daga baya na lura ai bamu kadai yakewa ba
har iannar tamu kawai rashina sanin hakkin iyali ne
shine yasa yake binda yaga dama banda abinsa ai
mata da duk wanda Allah yaba ya basa amana ne
baya bashi bane don yafi kowa. To irin wannan isar
tasa idan na nemi aminu ya taimaka mini musamman
lokacin jarabawar karshe din nan yaki nuna sai dai in
zan bashi jikina ni kuma a lokacin damuwa ta sheni
gani nake kamar idan na bashi ya bani abinda nake
nema ai yafi kaci dai nasa idan nayi ciki baba zai
koreni kauye kamar yanda ya kori karima taje ta
haihu tabar yar acan ta dawo to nasa raina bazan
haihuwa zambi duk hanyar dazan hana kaina ciki da
wannan tunanin nayi amfani na ba Aminu jikina sosai
kamar mijina don lokacin da Inna ta gane damuwa ta
sake karuwa akanta da take da ita a dai – dai lokacin
nema Hadiza ta gamu da wani Alhaji bairni mutumin
kano yake tayi mata dawai niya karatunta ta ashe
itama tabi hanyar da nabi nida Aminu ko ince ta
rigani bin wannan hanyar.
Nasan Inna abin na damunta, amma babu
yarda zatayi tunda inta hanamu ai babu abinda zata
iya mana itama bata dashi, tun ina boyewa har nazo
banajin kunyar kowa tunda akwai ranar da bani da
lafiya na tattara na koma dakin Aminu don kawai ya
kula dani magani na da abincina kwanana uku acan
Inna ta damu don nasan a zaton ta nima ciki ne dani
don haka Inna ranar ta cire storo, nauyi taje ta samu
mahaifina har dakinsa tace abinda kake mini ya isa
kasani cikin masifa inda 'ya'yana duk na kyaleka
61
saboda nasan Allah zai saka mini to naga bakaan
shiru kawai nayi maka magana duk ka mayar mini
daya ay karuwai saboda azabar yunwa da rashin
kulawa wa kuma wai don haka dashi ba a'a don
kawai butulci da rashin sanin hakkin iyali inda kasan
'ya'yanan mace agurin ka sam ka manta zaka koma
ga ubangijinka zai muku hisaba ko ince zai mana
baki daya kar ka manta komu dade komu jima zaka
mutu suma zasu mutu ku hadu agurin mahalaicin mu
atamabaye ka yaya ka rike amanar da Allah ya baka
wato yaya ka raini'ya'yana ada ana abaka to ranar
zakasan abinda zaka fada kace ka turasu karuwanci
ko? Innarmu tana magana tana huci idonta yayi jajur
tana tsaye tana ta karkaji alamar babu tsoronsa ko
kadan a zuciyarsa tun lokacin da ta shiga dakin
mahaifinmu ni kuma na shigo.
Inna taci gaba da cewa ni duk abinda kake
mini baya damuna akan wanda kakewa yaran nan ai
duk da a duniya yana alfahari da gidan ubansa amma
sam banda 'ya'yanka su a rayuwar babu inda ake
azabtarsu sai gidan ubansu kullum ka shigo gida
kamar malaika ya shigo motsin kirki yara basa sonyi
saboda tsoranka haka Allah yace ka rikesu to yanzu
yau Amina kwananta uku agun saurayi tunda anzo
neman aurenta ta gaya maka kace baza ka aurar da
itaba to idan yayi mata ciki ka bashi itama Hadiza ta
tafi gun nata saurayin kafin Inna take karshe
maganar da take masa yasa kafa ya doke bakinta ta
fadi kasa ya bita ya take mata rowan cikin ta da
kafarsa yana fadin ni za'a yiwa iskanci har zakizo
dakina kina gayamin maganar banza wai na mayar
62
miki da 'ya'ya karuwai tubali na gina nasakasu ciki
to bari na gaya miki daga yau kada 'ya'yan naki
kuttara yanaku ya naku kubar mini gidana tunda naga
rainin wayon naku yayi yawa wato har daki zaki zo
kina zazzaga mini magana to daga yau na sake ki saki
uku ki ki kwashi yayanki gaba daya bana so kubar
mini gidana mutanan banza.
Inajin haka na fada dakin mahaifin namu don
naga halin da Innar tamu take ciki natarar da ita a
kwance duk bakin jinni yana fita tana ganina ta miko
mini hannu alamun na taimaka mata ta tashi na
dagata da kyar taka kafarta muka fito yana tsaye yana
kallon ta naje da ita bandaki na wanke mata baki da
fuskarta duk inda ya taka da takalmi har ya fara
kunbura na dawo da ita dakin ta tace naje maza na
nemo yayanmu maza duk inda nasan suna zama.
Dukuk da taurin zuciya irin na masu suna
Amina amma sai da Amina ta tsaya tana zubar da
hawaye su mairo da bilkisu kuma sai ince tun labari
bai yi nisa ba suka fara zubar da hawaye Amina ce
dai ta katse nata hawayen taci gaba da cewa bansha
wahalaba na samosu don duk suna cikin kwatas din
na hado kansu batare dana gaya musu komi ba kafin
mu karaso karima da Hadiza sun iso Innarmu ta
kwashe komai ta gaya mana yanda sukayi da
mahaifinmu tace mana ita gobe idan Allah ya kaimu
zata tafi Mubi amma gaskiya kun san bazan tafi daku
ba tunda kunga bani da uba bani da uba nima zanje
na kasu gidan kanina ne tunda kunga gadona tun
babanku bashi da komai na siyar na bashi kunga
63
kuma yanzu yadda yayi mini bani kurna damai
kwatar mini dukiyata sai Allah don haka kunga yadda
zan kwasheku zuwa gida kunsan dai halin kauye zan
tafi ingayawa yan uwansa in sunga zasu rokar muku
ya barku ku zauna dashi to in kuma yaki to Allah ya
shiryar mini daku ni dai na barku a hannun Allah
daman can a hannunsa kuke don dai ba ganinsa muke
ba don Allah ku sake kan ku ku kama kanku ina nufin
aike mutunci kanki kunga wannan dabi'ar da kuka
dauka tabin maza ba abin arrziki bane yanzu abinda
ya sami karima ai ya isheku ishara kuna gani taje taba
wani banza jikinta yayi mata ciki tazo ta haihu yaki
karbar 'dan kinga damun kaita kauye kun kanwar
babanku kuna ganin ta dawo da ita yar munaji muna
gani ankaita gidan yara to yanzu wannan da dine
kana da 'da bai sankaba harya girma a haka inaga
tunda karima takai yarnan bata sake zuwa taganta
ko? tana fada takali Karima, karimace ta daga kai
alamar bata taba zuwa ba kaji wata masifar kai da
yarka kanaji kana gani ka saba da ita saboda babu
yanda zaka yi.
Duk kanin mu kuka mukeyi lokacin da Innar
tamu take mana magana can karima tace Inna nidai
nasan ko baba ya hakura yabar kowa agidan nan
bansani don kuwa ayanzu daga area one nake naga
karuwar baba igalan nan da ake bamu labari ya kama
mata gida a area one naganta da tsohon ciki ina
kyautata zaton na baban ne ma tana tuka shohuwa
motar nan tasa yah to kunsan ya sanni agidan na area
one inacikin wata mota muna hada ido da ita tayi
mini wani kallo hada bugar motar da nake ciki da
64
karfi shine ni kuma na fito nayi mata dukan tsiya
yanzu haka tafi ta dako mini yansanda to mun taho a
hanya naga baban a wata gidan nata ina zuwa gida
kuma naji abinda ya faru don haka yanzu nasan baba
idan yazo korata zai yi don Allah Inna ki tafi dani
inyaso in kura ta natsa yadan manta ana dawo kafin
karima ta rufe bakinta baba ya shigo yarufe da suka
kamar Allah ya aikoshi ya dake ta kamar bazai barta
da rai ba don ko police station ya kaita iyakacin
dukan dai za'ai mata kenan mu duka mun tausaya
mata mun mata kuka Inna kam ko daga kanta bata
yiba yanda take kwance bata motsa ba bayan ya gaji
da dukan karima ne ya juyo yace da Inna to kuma
zaman me kike ko baki jiba abinda nace ba, nace na
sake ki saki uku kinga irin masifar da kuke jamin
keda ya yanki ko Inna kamar ma bada ita ake ba a
juye ya kalli 'ya'yanmu maza yace kafin na dawo
inason naga filin gidan karma ga kowa idan kuma
nadawo natarar da wani a gidan nan kuma kunsan
sauran. To anan ne Inna ta bude baki tace ni zan tafi
su kuwa babu inda zasu tunda nan ne gidan ubansu in
kuma baka sonsu kace ba yayanka bane ka kaisu
bola, yajuyo da zafinsa da karfi yace karsu tafi suga
abinda zan musu nace ki kwashe 'ya'yanki ku tafi
tare nagama magana ta. ya fice abinsa ya barmu da
karima akwance kowa kuka.
Inna ta nunfasa tace to kunga tunda hakane ni
yanzu zan dau kayana na tafi gidan Maryam da asuba
zan wuce ku, kuma ku zauna idan yazo inyaga dama
yayi rami ya saka ku ke kuma karima zancan tafiya
dake bai taso ba tunda dai abinda ake gudu yafaru ni
65
dai zan tafi da yar auta ta Binta. Haka kuwa akayi ta
tashi ta shirya kayanta tsaf muka rakata gidan
Maryam mu duka banda karima saboda ba zata iya ta
shiba yayanmu maza sukayi sallama da ita da niyya
zasuje can mubi su same ta mune dai muna gida har
magariba muna ta faman kuka wanda yafi mutuwa
ciwo tunda ina mutuwa ce zakace kai maraya ne to
suna dare waharlar da kake sha ko maryan baya sha
kamarmu su yaya Moh'd can su kayi kwara ta huta
da wahala mu suke'yi ta daman mune abin yi tunda
mune mata inar zamu, muna nan tare da Inna da
matar Maryam Haja. Halima har Maryam ya dawo
wajan karfe takwas yazo yasa me mu da mummunan
labari take gun ko zama bai yiba ya hau motarsa yaje
yasami baban mu a area one idan gurin yarsa 'yar
igala ya lullube mahaifin mu da fada ya kuma sanar
dashi babu inda zamu daga mu bar Innar tamu ai
daman ba zaman aure yake da itaba mai yake mata na
aure da har zai kore ta ita da yaran ta ina zasu babu
wanda zai rabata da 'ya'yanta zata zauna anan
gidansa inya so in aure yakeson yayi ai yasan ba zata
hana sa abin sa ba ina ruwanta dakai duk abinda
zakayi ba hauka ka take shigaba yanzu ai kai Habu
baka kajin kunya ace ka daki yarka ta cikin ka akan
karuwanci to ita wannan cikin dakayi mata kana
tunanin shine danka ko 'yanka ko? mahaifina ya
kullawa Maryam wata muguwar harara wanda
Maryam tuni yayi shuru da maganar da yake yi tunda
yaga alamar bamai tasiri bace ya kalleshi sosai yace
kaga bubu nasha gaya maka kafita daga harkar gida
na amma naga sam baka da niyya to ayau zaka gane
66
kuskuren ka tsaya nazo daga yau na daina kace ka
kara shiga harkar gidan wani ka sake, Baba Maryam
da yaga haka ya kama gabansa kafin ya fito yazo
yabamu wannan labarin Innarmu da Hajiya Halima
sukace da yagaya musu can zashi da baza su barshi
ba yaje koda yake gara da kaje kagani da idon ka.
Maryam yayi shiru idonsa yayi tagumi alamun ran
maza yabaci ya kasa cewa komai wurin karfe goma
muka kama hanya mu kace za muje gida mu kaje
muka kwanta da asuba karfe biyar muka fito mu kazo
gun Innarmu tunda munsan karfe shida zata koma
munkwana lafiya lau mu kadai don mahaifin namu
bai dawo ba, biyar da wani abu muka bar gidan baba
Maryam shine ya tuka motar har tasha muka raka
Innarmu munyi kuka mai tsananin gaske wanda ko
wane bacen rai mutum zai shiga wannan shine sila
mahaifinmu bai shirya mana rayuwa mai kyau ba
yaci amanar ubangiji tunda ya basu mu ya
wulakantamu inda mahaifinmu yasan baiwar da
Allaha yayi masa ga dukiya ga 'ya'ya da bai
wulakanta muba amma aina sai yayi amfani da
dukiyar da Allah ya bashi saboda dararjarmu ya
wulakanta mu ya tuzarta mu to yaje yace da Allah
me, duk aikin mu babu wanda ya samu ilimi daya
kwakkwara tsakanmin bokon da arabin tunda muna
ganin islamia acikin kwatas namu amma bama zuwa
tunda biya akeyi bamu damai biya mana don haka
dukkanin mu haka muka taso bamu san muhimmacin
addini muba sallah ka wai, kowa ya iya itama don
Innar tana koya mana don haka kuka ga duk dabi'un
'ya'yan kabilu mun iya tunda dasu muka girma
67
sannan samun kulawa wajen iyayansu tabbas nasan
kabila inyamuri ko baya rabe bazai taba wulakanta
dansa haka ba, me yasa?
Gaskiya mu musulmai muna fatar da abinma da
addinin mu ya shirya duk duniya babu Addini mai
sau kin Addini musulunci amman abin mamaki
musulman mu ke falalai da tsarinmu shi yasa har a
matan hausawan mu ke shawa'ar kabila zai yi wuya
kaga inyamiri ko baya rabe yace yana son yar
hausawa cikakiyar musulma har yafi sha'awar zama
musulmi saboda ita amma sai kaga inyamuri ya aure
ba haushiya har tana neman tabar addinin ta saboda
shi. inda zaka ga yadda inya miri yakewa matarsa da
ya'yansa sai kaga inyamurin mutum ya fasa zuwa
aiki yarike wa matarsa 'da sunje asibiti kabilan
mutum tun wanda matarsa ta haihu to har dan
yagirma tare suke nan da abinda baza kaga ba haushe
yana yiwa matarsaba ba kuma koma me yasa haka ba
sai girman kai gaskiya abinda mazan hausawa keyi
yana bana mamaki babban matsalarsu kuwa itace
jahilci tunda banda jahilci muda muke da dashi duk
wanda yake da addinin musulunci ai shine mai dahir
amma saboda rashin kulawa irin ta hausawan mu
tunda in muka duba kabilu su kullum cikin neman
ilmi suke church din nan fa da suke zuwa bafa saboda
addu'a suke zuwa ba kadai a'a harda karatu kullum
suna duba mai Allah yace tunda akowa yasami Arna
sun yarda da Allah. Annabin mune basu yarda dashe
ba.
Amma sama banda ba haushe shi girman kai
bazai barsa ya nemi abinda bai sani ba, kunga wata
68
babban cuta da iyayen mu suke mana shine su kabilu
tun suna 'yan yara ake koya musu kuma duk
makarantu da suke dashi babu abinda su kafi koya
masu cikin kashi dari ilimin sune amma don rashin
hankali irin na bahaushe wai wannan itace
makarantar da muke saka 'ya'yanmu kaje yaro ya
tashi da wake - waken kiristonci duk ya koyi yadda
suke addau'oinsu tunda ko nida nan kafin na koyi
karaturn Alkur'ani mai girma sai dana dade da koyan
karatun kiristoci kinga mai yafaro haka hada mu
makaranta dasu ana dankemu an kaimu makaran
tunsu wanda su koda wasa ba zasu taba kai 'ya'yansu
makarantu mu ba kunga ko anan mun nuna musu
muba kishin kan mu tunda sus basu hada addinin su
da komai ba. Mairo ce tayi magana tace duk abinda
kuka fada Amina gaskiya suma kansu iyayen naku
zaman bariki ne yasa duk suka yarda dabi'unmo
nagida tunda inba wanda yayarda dabi'unsa bat a
yaya mutum zai zauna cikin iyalinsa sai yasha giya
ya nemi mata ace kuma yayi abu da zuciyarsa babu
wanda ya isaaya sakashi babu wanda ya isa ya bashi.
banda rashin kishi ta yaya za'ace kana musulmi kana
da matarka da 'ya'yanka kaje kana neman wai Igala.
Tabbas da mahaifina sai Allah duk da irin abinda
mahaifina yAmina maganar na da mairo ta fada sai
naji dana sanin ta nawa mahaifin sai dai kash bakin
alkalami yariga ya bushe nariga na fara nakumayi
alkawarin zan gaya musu komai gaskiya Bulkisu dai
batayi wata magana ba sai kallona take da fuskarta ta
nuna tausa yi don koda yake itama mairon batayi
hakanba donta batamin rai kadan ta tazo tashi nasan
gaskiya take fada.
Mairo tayi shiru da fadan da ta keyi tace
inajinki Amina cigaba da bamu labari tunda kinga
Bulkisu zata tafi gida to naci gaba Inna nashiga mota
Baba Maryam yaki fitowa daga mota nasan yaya
hakane saboda bacin rai Inna tamu ta kallemu tace
kuyi hakuri ku kanku kunsan ina sonku ina kaunarku
Allah yayi albarka don haka banda dole babu abinda
zai rabani daku a tunanina mutuwa itace zata rabani
daku ko da yake yanzuma ganianku ne bazan yiba
akan lokaci donAllah ina rokonku ku kama kanku
kubar hanyar da kuka dauka ku rike addininku don
abinda kuka sani kuyi amfani dashi inason naja muku
kunne donAllah idan kuka sami miji ku kawoshi
mubi nasan ko babanku yace bazai muku aureba 'yan
uwansa wanda suka rage zasuyi masa aure. Don
Allah abinda ya sami Karima mu dauke shi kaddara
ina fatan babu wanda zata sake fatan haka ta faru
akanta kuna gania itama faduwa tayia ba ribaba taci
gaban da cewa don Allah kar wuya ke yinwa yasa ku
dauki nawani ku nemi na kanku dukkannin mu
hawaye muke tace mu tafi saboda Baba Maryam
yana jiranmu muka juya gaba dayanmu shima ya
kwantar da kansa akan sitiyari daga gain kasan
damuwa tayi masa yawa, muka sallama da ina da
kanwarmu Binta muka wuce - tare da Baba Maryam
nida Hadiza ranar don kuka har zazzabi mukayi.
Kwanan Inna hudu da tafiya muna nan acikin
gidan mahaifinmu