zaranda Hotel, yasa aka kawo mana
kayan ciye-ciye, muka zauna muka sha hira
kasancewa matsi da kuncin da maihaifiyata ta
sani shi yasa na yi saurin amincewa da Alh.
Sunusi, tun daga wannan ranar na zama kamar
matarsa inna sami hutu yana daukata muna yawo
gari-gari yawon bude ido, da haka na sallama
gidanmu, sai nayi wata uku banje ba, abin
mamaki da naje ko mai ya sa baki zoba ba ace min
ba, ga dukkiya an ganni da ita, nayi dunkuna kala.
Na dinga yin abinda babu tsoro babu fargaba.
Tunda na san babu wanda ya damu dani banda
Alh. Sanusi, na sami wasu' abokan haraka, a
cikinsu a kwai wani Ali da kwara tantirin yaro ne,
Ali kowa ya san kwarori ba bu wanda ya kaisu
fitina, to Ali tasa fitinar har da shaye-shaye
haduwata da Ali ta sa na yarda duk samarina ta
haka ya koya min shan giya, tun ina sha ina jin
daci kamar yadda kikace yanzu, har na goge naga
babu abinda ya kaita huce takaici da sa zuciya
sukuni irinta, tun randa na fara shan giya babu
wani damuwa da nake kwana da ita, dan haka ina
baki shawara da ki sha giya ki kula kananan yara
-24-
ki huta da wahalar da kan ki wajen manyan
mutane."
"To Baraka ya ya aka yi ki ka dawo
Abuja?" Tun da nagama A.T.B.U Bauchi na
koma gombe naga baza mu shírya da Innata ba
tunda ita bata sa min idoba, amma abinda take
min gwara sa ido, ina da kayan biyan bukata a
gidan babu abin da nake nema matsalar duk
wanda yazo guna sai tace a kirawo shi yana zuwa
tace wai lallai ya je ya kirawo iyayensa, inba haka
ba kar ya sake zuwa, ko kuma in ta ga abin duniya
tace bata son wanda bai kawo ba ta fita tana zagezage, niko giya bata banani sha ba don inaga ko na
sha bata ganewa, to da irin wannan damuwar tasa
muka yanke shawara da wani saurayina Gali ya
samo min aiki anan Abuja ban sha wahala ba, da
nace mata zan dawo Abuja, to kinji dalilina na
zuwaAbujа."
"Yanzu haka kina zuwa ko bakya zuwa?"
"Ina zuwa ina kai mata kayan alheri ta na kuma
farin ciki bama tayi mini zancan aure ma."
Na yi shiru zancen Baraka ya ratsani, ita
kuma uwar tace ta matsa mata gashi ta sata ta
shiga wani hali kwara ni daman uba ban sanshi da
tausayi kamar uwa ba, tun da shi baya shan wala
kamar uwa, ita uwa itace mai daukar ciki, itace
mai shayarwa da reno duk da haka banda son abin
duniya irin na mutun, ya ya mutun zai wulakanta
dansa ya guje masa saboda abin duniya?, gaskiya
-25-
iyaye na sake wajen amanar da Allah ya basu, to
yanzu in sunje wujen Allah mai za su ce Masa
akan amanar da Ya basu ta mu, ranar lahira da
kallo kuma in ina ganin duk abinda mukayi su
Allah zai tuhuma don haka bari na sha giyata
kawai.
Tun daga ranar na fara shan giya da farko
na wahala daya baya na saba kullum da yamma
sai mun fita nida Baraka mashya, anan ma munyi
kawaye iri-iri kamar su Bashina da Maijidda
kusan nace kullum da yamma nan gidan Baraka
muke haduwa randa bama son zuwa sai mu bayar
a siyo mana mu zauna musha mubugu tare da
samarinmu. Don yanzu na bi shawarar Baraka ba na
kula manyan maza sai kananan yara dan na hadu da
wani yaro dan shekara ashirin da hudu har ya koyan
shan taba, kusan nace na bar gidan mu na dawo gidan
Baraka dan ko tafiya tare muke dan tsabar shakuwar
mu, yaron da ya koya min shan taba Misbahu, yaro ne
fari dogo kyakkyawan gaske dan naji dadin haka
kwarai da gaskiya da Musbahu, ta haka ya koya min
shan taba, na san na fishi nesa ba kusa ba, amman in
kinga shagwabar da nake masa kin san bariki ba kyau,
a wannan lokacin holewar rayuwa babu irin wanda
bamuyiba. Yan kannena Hadiza da Sadiya da suka ga
na canja sai suka ja baya da ni, na daina neman 'su
maman kalifa duniya ta yi dadi.
Kwance na ke akan three seater ina kallon
A.I.T suna English drama ina jin dadin wasan sosai
wata yariya ta shigo wai ana kiran Amina kafin na ba
-26-
ta amsa Baraka ta bata tace "ki ce wa mai sallama ya
shigo”. Ga kwalbar giya a gabanmu muna korawa, wa
zun gani, Aminu wanda mahaifina ya hana shi aurena
tun ina yarinya ko ince Aminun da ya koya min harka,
na kalle shi kallo irin na bugagiya yace "kwarai da
gaske, gaskiya Amina na sha neman ki tun tini na rasa
inda zan sameki, lokacin da na samu wanda ya nuna
min gidanku sai aka fadan kinyi aure, to yanzu kuma
nazo wucewa na shiga shi ne sadiya tace min auren ya
mutu kina ma nan gida."
Na kalleshi a buge nace "yanzu da wace ka
zo?" Aminu ya yi murmushi alamar ya san ba a cikin
haiyacina nake ba ya ce "Amina na zo da wacce kika
san ni" na mika masa kwalbar giya nace "to bismilla"
ya girgiza kai yace" na gode, żan barki ishan Allahu
zan dawo gobe kamar yanzu".
Washe gari da safe sai ga Aminu ko tashi bamu
yi ba sabanin yadda yace da yamma da alama Aminu
bai yi bacci ba, da ganin idonsa. Haka kwa akayi
dana fito na sami Aminu a falo, na kalle shi idona
cike da bacci na dafe kai nace "lafiya dai? da safe
haka kamar mai bin bashi" ya saki murmushi yace
"Amina ai bashin na ke bi tun da jiya banyi bacci ba, halin da na gan ki wai ke Amina ke ce ki ka
dawo haka", kallon shashasha nayi masa nace "Aminarka a ina?" Ina Magana ina busa masa hayakin taba, na lura bai kula ba da abin da nake,
ya sake kallona yace "Amina don Allah ina son kiyimin alfarma guda daya idan zan samu, ina son
ki shirya mu fita wani guri", nace "mai zai bana,
-27-
ina zuwa" na shiya cikin siket da riga ko dankwali babu nace "muje ko?" ya girgiza kai yace
"gaskiya Amina kisa mayafi, idan kuma da
doguwar riga kisa don bazan so a ganni dake da
wannan shigarba," na juya na dauko dan mayafi
wanda hausawa ke ce masa rakani karuwanci,
nace" doguwar riga kuma babu, in bazaka ba
shike nan" duk tunanina ya bani shi ma layata zai
dauka yace "to bisimillah" muna fita kasuwa
wuse ya zarce dani ya tsaya a wani kanti da ake
sayar da dogayen riguna yace na fito ya nunan
wasu guda uku yace ki dauka idan sunyi miki na
dauka ko godiyar kirki banyi masa ba tun da ba
wando da riga ya siya min ba, ni sunfi doguwar
rigar a gurina.
Na lura Aminu ya gane ban yi farin ciki da
rigunan daya siya min, amma duk da haka ya
kawar da kansa bai kula ba ya kunna mota ko
kallon ind nake bai yi ba, bai tsaya a ko ina ba sai a
Abuja Garden, inda mukaje muka zauna a fararan
kujeru da table fari a tsakiyarmu, ya tashi yace
"ina zuwa tunda ya dawo bai ce dani komai ba,
nima haka can sai ga wani mutun da leda baka ya
kawo masa, a raina da naji dadi ca nake wani
abinci ya bayar aka siyo mana don yinwa nake ji
banci komai ba.
Buda leda ke da wuya sai na ga' kwalbar
giya da ganyen wiwi da kwalin taba guda daya ya
kalleni cikin bacin rai yace "Amina ina son duk
-28-
kayan nan ki dauke su daya bayan daya kiyi min
bayani akansu, da amfaninsu ga shan su."jikina
ya yi sanyi sosai, abinki da zuciyar bariki wato
bushashiyar'zuciyar ban ko kalle shi ba, nace
"duk amfanin su daya, suna sa zuciya tayi sanyi".
Shi ma yace "naji to kuma mai yake karawa a
jiki?" na dauke kaina nace "jinin mutum ya na
dawowa yana sa mutun lafiya, kyau" Amina
dama jinin mutum yana tafiya ya dawo, abinda
nake nufi da jinin mutum yana dawowa idan
mutum yana shan wadanna abubawan yana sawa
jini mai kyau ya dinga zama a jikin mutum.
Aminu ya daure fuskarasa yace "Amina
kar kiyi was dani kinji, kina magana son ranki, ki
duba kiga yadda ki ka dawo, haka kike da?
hunnunki da fuskarki da kafarki duk sunyi baki
saboda hayakin da kike busawa jikin ki, mufara ta
kanta, ita taba wanda mutane suke gani karamin
alhaki to illarta babba ce, na farko tun kafin ta je
ciki, fuskar mai shan ta musamman farin mutum
za ta yi baki kirin, hannunsa haka, tafin kafarsa,
kansa cikin bakin kuwa nanne farko da lebansa, to
anan ga uwa uba ciki duk wanna hayakin da
mutum yake busawa yana nan a zaune cikin
huhunsa, za kiga duk wanda taba ta yiwa illa yana
yawan tari musamman idan yana magana, dafin
da take sawa cikin huhunsa, shi ne ya ke fita a
fuskar mutum da tafukansa, ki yi tunani hayaki
shi kadai idan ana gobara ya na kashe mutun har
29-
lahira, ballan tana kiyi sheharu kan busawa
cikinki, don haka kullum likitoci suna cikakken
fadarkar da masu shanta, su kan su masu tallarta
suna mai da ku wawaye tunda kullum sukanyi
talla sai sun rubuta (The Federal Ministry of
health warns that smoking is dangerous to health)
shan taba harsarine ga lafiyar mutun, don haka
Amina, ina baki shawara tun ba ta kama kiba ki
bar ta.
Giya bari na hada duka don wannan na
ganki da gulder yau kuma naga kwalbar star don
haka ban san wanda kike sha ba, star, gulder
dandanonta kamar kanwa yake, to Amina tun ba'a
je kan wata ba miye amfanin kanwa in ba a miya
da duk wanda ya sha kanwa ta zame mai dole,
miya kanta idan aka samata kanwa sai ta yi kunfa
saboda zafinta amma Amina ace shi ne abinda
zamu sha yana kara lafiya ki yi tunanni.
Star wanda naga kulbarta a gurinki yau,
tafi kowace karfi kinfi kowa sani wata illar babba
da giya takewa mutane sai ka sha kwalba hudu a
lokaci daya, uku lokaci daya, giya ta na sa rashin
kunya, duk abin dan giya yake idan yasha yana
sane illa dai kawai bazai fasa ba saboda fitsarewar
da idonsa ya yi ba ya jin kunyar kowa, zata iya sa
mutun ya je ya yi zina akan titi ba tare da jin
kunyar kowa ba, saboda ya sha abind idonsa zai
bushe, kana ji kana gani za ka kasa tashi kayi
sallah, duk mashayi ya na barin sallah don babu
-30-
yadda za'ayi ya yi sallah, don haka Amina ki kula.
Stourt mai kamar maltina tana da daci,
amma ba mai kama baki ba, itace wadda likitoci
ke cewa tana kara jinni don wani lokacin akan
cewa kasha maganin fever, to bari na gaya miki
Amina, duk abinda Allah ya hana ya na da kyau
mu barshi, dan cikakken musulmi ba zai ce kije ki
sha giya ba, kin ce maganin jini ne, don haka duk
wanna yahudanci ne, kwara mu barshi, ita giyar
nan idan mukayi hakuri da ita anan an tabatar
mana da ita a aljanna, Allah (SWT) yayi
alkawarin duk wanda ya sha ta duniya ba zai sha ta
lahira ba, Amina mai ya sa zamu bari shedan ya
rinjaye mu muyi zuwan zomo kasuwa (ya zo a
guje ya koma a guje), don Allah Amina ki nemi
lahira kibar duniya, ki tuna matsayin da ki ke,
kamar marainiya ki ke, me ya sa bazaki rike
maraicinki ba, ki kama kanki har Allah ya baki
miji kiyi aurenki, ke bakya sha'awar yadda ku ke
da yawa, kema ki samu naki, sai ki zauna ki na
shirme duniyar nan babu wanda yazo zama, kowa
da ki ka gani zai tafi, don haka ki yi kokari kafin
lokacin tafiyar ki yazo ki figi wani guzuri da za ki
yi ikirari da shi acan.
Ganye wiwi kuwa nata daban da sauran,
don ita tana tafarfasa kwakwalawa, da zarar kasha
zakaji yunwa ta kamaka to idan ba ka yi kokari
kaci abinci ba shine ka ke dawowa kamar
mahaukaci, don ita lokaci daya take kama duk
-31-
was jijiyoyi na jikin mutum ta kuma kama kansa
da ido yai jajur kan mutum ya ringa bugawa tana
sa rashin kunya kamar giya itama.
Amina don Allah don Annabi ina son ki yi
min alkawarin kin daina shan wadan nan
cuttukkan duka. Ki tuna Baraka tafiki gata, tana
da kudin kanta ko ciwo ya kamata kafin takai ga
halaka zata iya yiwa kanta magani ke kuwa
Amina daina kulaki za tayi ta koreki don karki
mace mata a gaida". Maganganun Aminu .sun
shigeni, sai kuma idan na daina wannan harkar
duk abokan harkar tawa gudu na za suyi to wazai
kula dani da da bana wanna harkar kullum cikin
roka da bashi nake, yanzu fa ba bu abinda da na
nema na rasa wasu ma yi musa nake adalilin
wannan haraka.
Dan haka yanzu in na ce da Aminu na daina
a gaskiya karya ne ban daina ba. Na kalli aminu
nace "to na gode da shawarar da ka bani, Insha
Allahu zan daina shan komai daga yau, amma ina
fatan zaka taya ni da Addau'a" Aminu yace "ba bu
damuwa Allah shirye mu baki daya, Allah kuma
Ya sa wanna maganar har ranki in ma karya ki ke
Allah ya sa mala'iku sun ams", haka muka rabu da
Aminu lafiya ya dawo dani gidan Baraka, na san
dai Aminu ba aurena zai yi ba sai dai ina mamakin
yadda ya ke mini kullum da yamma idan ya taso
daga aiki ya na tare dani amma kuma ko hannuna
bai taba sha'awar ya rike ba, duk kuma abin da ya
-32-
san zan nema na bukatar yau da kullum ya na
kokarin kawo min, a haka ya fara korar samirina.
Hakan da yake min ya sa na ke shakkarsa sosai
don in zanyi shaye-shayena nakanyi da daddare
ne kamin safe komai ya bar jikina.
Kawai ranar da Aminu yazo da safe ya
kamani da kwalbar giya a hannuna kallo da yayi
mini nida kaina na tsorata na rasa inda zan sa
kaina, ya fito da ni ina tangadi nazo na tsaya a
jikin motarsa nace "don Allah Aminu ka yi hakuri
ba zan sake ba." ya daka mani tsawa yace matsa
daga nan mayaudariya banza, ni zaki rainawa
hankaki ana son a taimake ki, kina lahantar kanki,
daga yau karki yi tunanin kin sanni, ki je ki yi ta
barikin, tun da ki na ganin shi ne ya fi miki". Na
kwanatar da kaina ina ba Aminu -hakuri, don
nasan Aminu gata na ne, ko banza duk wanda ya
san sirrina a baya bai kai aminu ba. Amma bai
wulakanta niba, nasan duk irin mutanan da na ke
ma'amala da su da sun san sirrina kamar Aminu
da walakacin da za su ringa yi min yafi wanda
suke mini ko banza nasan Aminu a gaskiya yake
mani tunda banda wulakaci mia yake faruwa
daren jiya said a aliyu saurayina yayi mini dukan
tsiya bayan ya ya biya bukatarsa wi ina zagezagana irin na bugaggu shine na zageshi yanzu
haka bayana du ciwo yake min ibabu kuma
abinda na isa nace masa gobe ma idan yaga dama
saiya sake ko kudin kwana bai biyanda, haka
33-
(
rayuwar take watarana da sa'a wataran babu wani
inyazo yabiyaka hakkika wani kuma yayi maka
duka ya kama gabasa dolene nabi shawarar
aminu idan inason rayuwa ta dawo irinta da.
Aminu yasa hannu yatureni daga jikin
motarsa ya ja kayansa na shiga cikin digan
Baraka ina kuka na sami kwalabar giyar tawa na
fartsa na dawo kamar maharkaciya ita kuwa
Baraka tana can tana. aiki na shiga bandaki nayi
wanka na kwanta baci mai karfi ya kwasheni irin
na mashya giya tayi Musu kai tun sha daya na
safe nake kwnce ban farka sai karfe ukku shima
Baraka ta tasheni, nashiga kicin naci abinci nayi
sallah ban yaga mata na yadda muka yi da Aminu
daon nasan bata son sa don ko gaisuwa arziki
basa yiwa juna tund ta gane inda ya nufa ina idar
da sallah na sau jakat nasaka daya daga cikin
dogaen rinunan da aminu yasaya mani ban zame
ko inana sai din su aminu don nasan baya tsahi
shidda yana zaune na kwankwasa kofa ya mansa
batare da yasan ko wanene ba yana dago kansa da
yaga nice ya bata ransa nagashe shi ya amsa a ciki
na daure tunda na san bani da gaskya nace
aminuy don Allah don son Annabi kayi hakuri
kayi mini Addu'a Allah yarabani da wannan
harka insaha Allahu bazan sakeba daga yau ya
kalleni yace Amina karki sake yardarata kinji
koke kanki kinsan ba ina yi donki bane inayi don
Allah don kuma sanaya dake tsaknina dake don
-34-
haka amina yarage naki koki daina ko kici gaba
tunda kema kin fison a ringa kwatace a kanki
kamar karima wanda duk wanda yasanta yasan
sunnata to shi ne kema kike son ki nadawa kanki
wannan sunna tunda ita mai wannan sunan bata
cika sai ta hada da wadannan abubuwan naa
shaye-shaye sannan ta cika kasuwa.
A durkushe nake a kasa nace "don Allah
karka kaurace min, na san na yi maka laifi"
Aminu "naji, Allah ya shirye ki, amma ina son mu
yi da wajewa daga yau laraba in na sake ganin ki
da kayan maye ba ni ba ke, kin gane?, saboda
haka ki kula ba bu wani dan Allah don son Annabi
ina son daga yau ki tattara kayanki ki koma gurin
su Hadiza 'yan uwanki da ki ka gudu saboda
shedanci.Amina kin cuci kan ki, kin yiwa kanki
tabon da ba zai warke ba kije daddare ina zuwa
gidanku ba gidan Baraka ba in har naga abin da
nake son gani shi kenan zamu shirya."
Na fita daga office din jikina a sanyaye da
zulumin ya ya zan ce da Baraka daya kenan, 'yan
uwana kuma wanda na wofantar dasu tun barina
gida dawowata gidan Baraka, wane ido zan kallesu
tunda sun sha zuwa ba na kula su, asali ma Hadiza
har korar kare nayi mata don tayi min nasiha akan
shan giya yanzu, idan na je za su saurareni ko suma
za su koroni kamar yadda na yi musu.
Yanzu abin da zan fara yi naje gurin su
Hadiza kamar na kawo musu ziyara don naga yadda
-35-
6
zasu karbeni, na yi sallama, na iskesu a waje, ta
amsa a dakile kamar dole waton Karima tayi mini
kalon sama da kasa tace "Amina daga ina, ko kuwa
abokan harkar sun korcki shine ki ka lekomu?" ban
ko kulaba tunda ba bakuwata bace in da sabo na
saba da bakakar maganar Karima, na wuce kaina
tsaye gun su Hadiza da Sadiya tunda su nakeyi ni
sam ba na yin karima, ko ta kulani ko ta kyaleni, na
wuce na yiwa kannena sallama, Sadiya da fara'arta
ta amsa, Hadiza kuwa ta yi kamar barci take na
zauna a sanyaye kamar mai jiran hukuncin alkali,
nace "Sadiya, Hadiza barci take?" Sadiya ta girgiza
kai tace "idonta biyu tana jin ki nasa hannu a
tsaorace nace "Hadiza kina jina ki ka kyaleni?" bata
ko motsa ba ballantana tace wani abu ko naji sanyi,
nace "sadiya bari naje nayi alwala nayi sallah"
Sadiya ta zuba mini abinci ina ci ne Hadiza ta juyo
tace "Amina ki biyo mune kici mana wani
mutuncin?"
"To karki manta nan gidanmu ne ba gigan
Baraka ba, don haka a kara gaba a gaida Baraka da
sauran mashayan." Sai naji gabana ya fadi don kasa
tauna lomar dake bakina na kalleta nace "don Allah
Hadiza ki yi hakuri sharrin shedan ne ba bu kuma
wanda ya fi karfin kaddara, ke kin taba zaton zanbar
gidan nan har na zauna da wasu?, ki tuna yadda
nake sonki ki tuna kaunar da na nuna muku a baya.
Gaskiya Hadiza ba ki yi tunani ba, don ni yanzu
Inshal Allah na shiryu yanzu nake son kwaso
kayana zan dawo cikin 'yan uwana yanzu haka idan
-36-
na gama ina son Sadiya ta rakani na kwaso kayana
gaba daya daga gidan Baraka na dawo nan.
Marar kunya tayi shiru da maganganu da
take tace "Amina, dama ai ke ki ka ja ban da haka
muna nan kamar marayu, maimakon mu rike
maraicin mu amman kowa ya kama gabaansa bacin
kuna manya kun zama manyan banza kenan, karima
ta kama gabanta kema da muke ji da ke muna
faduwa muna tsahi kin kama gabanki kin bi sahunta,
in har kin shiryu muAddu'ar kenan kullum" Hadiza
ta bani tausayi saboda kukan da take tana Magana.
Bayan na gama cin abinci muka je da Hadiza
da Sadiya, na yi sa'a Baraka ba ta nan ta fita, ita da
saurayinta don haka na kwashe yanawa-yanawa
nace da 'yar aikinta tace nayi tafiya kawai don ma
kar ta biyo ni, kamar yadda mukayi da Aminu dare
nayi sai ga shi da alama ya ji dadin gani na a gida
cikin yan uwana, ni kaina naji dadin canjin rayuwar
don ya kawo mana kayan abinci har da su kaji da
kayan shayi ya kawo mana, mun sha hirar duniya da
Aminu da kannena baki daya, bayan ya tafi Hadiza
tace daman ya na yawan kawo musu kayan abinci
dana shayi, naji dadin hakan na fuskanci Aminu ya
mayar damu kannansa ne kawai don ya sa idonsa
akan tarbiyarmu, hatta shiga mutum ya yi sai ya lura
da irinta idan ya ga bata dace ba ya hana shi.
Yanzu da dawowar Aminu ya kai wata
takwas, amma sam bai taba nuna min wani abu na so
ko na fasikanci ba, a zatona ma Aminu yana da mata
don dai bana son ya san na damu da nufin zuwansa
-37-
na barshi a inda ya tsaya.
Kwana goma da komawa gidanmu, idan na
ji kishirwar giya hankalina yakan tashi na rasa in da
zan sa kaina na yi ta neme-neme wani lokaci na kan
sha lemun kwalba haka mai dan gas, abin ya dan
lafa min, idan kuwa damuwar tabace tafi komai
daga min hankali, saboda duk lolacin da naci abinci
ba bu abin da nake son nasha wan da ya wuce taba,
daga baya dabara ta zomin nake cin goro na mayar
dashi kamar tabar, da na fadawa Aminu cewa ya yi
na dinga fadin Inna Lillah Wa Inna Alakim Raji'un
isha Allahu abin zai zo da sauki, to kusan kullum
haka na ke ta fama da innalillahi da haka har sati
biyu ba tare da shan komai ba.
Ina da kwana goma sha bakwai ne Baraka ta
zo gaidan mu wai an ce mata nayi tafiya sati biyu,
san nan har yanzu shiru nace "tun jiya na dawo, naje
mubi ne, ina son na dawo nan da zama saboda su
Sadiya ba ta da isasshiyar lafiya, tana fama da ciwon
mara, idan ya tashi sai Hadiza ita kadai ta rasa inda
zata saboda haka Inna tace in dawo kusa dasu."
Baraka fuskarata a bace ta ce "haka ne amma
ai ya kamata ki ringa zuwa koda da yamma ne
munaa hira, ba dauke kafaba kamar mun yi wani
abu" nima na bita da kissa nace "babu komai
kawata, Insa Allahu zaki ringa ganina" ta fito da
taba ta busa ta miko min guda daya, nan da nan naji
yawuna ya tsinke, na shiga addu'a ba bu shiri har
Allah ya taimákeni na cewa Baraka bana jin shan
taba yanzu, na gode da haka muka sha hira ban nuna
-38-
mata komai ba don zamana da Baraka ba bu abin da
zance mata tayi min mutunci yadda ya kamata, dan
haka Baraka ba kashin yarwa bace.
Hadiza suna ta fama dani akan naje gaida
Hajiya maman kalifa, amma sam naki saboda
yanayin da na jefa kaína lokacin da na sheke ayata,
ban taba kula da yadda jikina ya dafe, koda Aminu
ya fada jinsa nake kawai inaga yana fada ne kawai
don na daina kawai, amma yanzu da hankalina
yadawo jikina naga fuskata ta yi baki, idona ma
sunki su dawo fari tas, kamar da saboda dafewar da
sukayi sosai, don yanzu na shiga shafe-shafen babu
gaira ba bu dalili akan jikina ya dawo dai-dai
dalilina daya Hadiza tace Hajiya tazo nemana sau
biyu sunce mata ina mubi.
Soyayya ce, mutunci ne, kauna ce har yanzu
ban fahimci ko daya ba nida Aminu, duk lokacin
daya dawo daga gurin aiki yana manne dani har
magariba, babu abinda muka nema muka daga ni
har kannena kusan nace har Innata, don Animu
yanzu yasan mubi yakan je shi kadai ma ba tare dani
ba, a wannan satin ne ma yake cewa mu shirya dasu
Hadiza zai kaimu muga inna muyi sati idan sati ya
zagayo zai dawo ya daukemu. Haka kuwa akayi
satin daya a mubi, zama irin wanda ba a taba yin
irinsaba tunda bamu daurawa inna nauyin komai ba,
Aminu daya kawomu sai da ya ciko mota da kayan
Abinci ya kuma dauko dubu biyar ya ba inna yace
saboda cefane munzaga mun gaisa da dangi yadda
ya kamata mu ringa ya wadanda basu sanmu ba
-39-
yanzu sun sanmu don har dangin babanmu inna ta
kaimu a wannan satin.
Ranar juma'a gobe Aminu zai dawo muna
cin tuwa mu uku inna tana gefen mu a dakinta
hadiza tace "inna ya kamata kisa baki mu bamu san
matsayin Amina da yaya Aminu ba kullum suna tare
har yanzu kuma munji shiru babu alamar maganar biki", Inna ta dan yi murmushi tace "to Hadiza ku
zaku zauna mata bakwa ganin irin matsayinsa yace
shi yana da mata da yara biyu idan tana sonsa haka
zai aureta nace "gaskiya inna Aminu yaso kansa don
tunda muke tare da shi babu wata magana ta
soyyaya da ya taba yi min ballan tana takai ga
zancen aure don ni inba yanzu bama ban taba sanin
Aminu yana da mata bama."
Washe gari tun karfe daya Aminu ya karaso
amma cike da kayan Abinci kamar sanda ya kawo
mu, bayan yaci abinci ya huta ya je masaukinsa
gidan wani abokinsa mutumin kano, wanda aiki ne
ya kawo shi mubi tun da ya tafi saida safe suka dawo
shida abokin nasa, bayan sun ci abicin safe ne muna
zaune dakin umma daga ni sai shi da abokinsa mai
suna Rufa'I, shi ne abokin ya ce min, "to Amina
ranar wanka ba'a boyen cibi, kin riga kinsan abinda
ya hadaki da Aminu tun tuni don haka yanzu ma ya
dawo sai dai da iyali don yanzun Aminu yana da
mata da yara guda biyu Fahad da Fairus yanzu haka
suna zaune a Abuja, a Asokoro, ina fatan za ki yi
joining dinsu as Amarya" gaba daya muka sa dariya
Rufa'i yace "ba dariya za mu yi ba kin san dai nan
-40
gida a kazo, don haka idan kin amince to mukara
shiri akan na da