An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
MAHAIFINAH
NA
SARATU LAWAN NUHU
NASIHA
lyaye na mantawa da cew a duk wanda Allah
ya bashi 'da (ma'ana 'ya'ya) ba wai ya bashi bane
don yafi kowa, ko inche ba'an bashi bane don babu
wanda za'a bawa don haka don Allah ina nasiha wa
iyaye, su kula susancewa "da" amanace agurin Iyaye.
musamman ma iyaye maza don yawancin sai kaga
yaro idan har uwarsa bata gida, yana shan wahala
uban na kallo, ko kuma uwar don tana gidanma don
kawai ba'a ra'ayinta tana ta famanshan wahala ita da
'ya'yanta don cin amana da rashin sanin ashari'a ko
kuma inche don take sanin shari'ar Allah.
Don Allah maza a rinka adalci don duk
yawancin laifin daga kune don cuk uwar data haifi
danta tana sonsa bazataso taga abunda zai cuceshiba
sai dai in har finkarfinta akayi, to nan kuma sai
Addu'a.
Don haka iyaye kar muyi wasa murike
amanar da Allah ya danka mana na 'ya'ya yenmu don
dolene a tambayemu acan, don haka karmu yarda
mufadi anan don idon muka fadi anan, musanifa acan
akwai hisabi, In mun gyara anan ta gyaru, in ta baci
anan ta baci acanma.
GODIYA
Ina godiya daAllah subhanahu wata'ala daya
bani basira harna tsara wannan littafi nawa mai suna
MAHAIFINA warınan littafi nasiha ne ga Iyaye ina
fatan za'a kiyaye ayi amfania dı abinda yake mai
kyau da wanda bashi da kyau.
ii
Ina mika godiya ta ga Aliyu Shehu
(LAJE - LAJE / BAGGIO) wanda yake mini aikin
bugawa a na'uran Computer Allah ya taimaka
amen.
SANARWA
Ban yarda wani ko wata ya juyi wata hanya ta
wannan littafi ba sai tare da izinin murubuciya yin
hakan babban laifine.
iii
Kwance nake akan tsumman katifata wanda
ko zanin gadon kirki babu, babu komai a idona sai
hawaye dake kwarara wanda nayi - nayi na tsayar dashi na kasa.
Tunanin rayuwar da nake ciki ne yake
damuna, mu ba marayu ba mu ba masu iyaye ba,
babu wanda yake tausayin kowa, gashi dukkanmu
uwarmu daya ubanmu daya, balantana ace ko 'yan
ubanci ke damunmu, babu wanda yake tausayin dan
uwansa babu Imani sam a zuciyoyinmu kowa ta
kansa yake.
Gaskiya muna tare da kuncin rayuwa, gashi
yau natashi banida ko sisi, bani da abincin da zanci,
ga' yar uwata nan uwarmu daya ubanmu daya ta
dafa abinci amma ta hanani, to mai yakawo haka?
babu wanda yaja mana wannan matsalar sai mahaifin
mu.
"Assalamu Alaikum, sarakan zaman gida, kullum
kina daki kwance sai kace kasa, ke ko gajiya ba kyayi
da kwanciya, ko kina da cutar baccine, mu kaiki likita
ya dubaki?". Muryar Balkisu naji, na tashi zaune na
amsa.
"A lallai Bilkisu kinci abinci shi yasa kike mini
wannan tsiyar, bari in kawo miki ruwa kisha." "Babu
wani ruwa ni babu abinda zakice mini uwarcika
Alkawari kawai kin ce mini za kizo amma nasha jira
shiru.
Gaskiya Bilkisu ba zaki ganniba, ba don
komai ba sai don yau nafi sati banida ko sisi don haka
babu inda nake zuwa, "to kema Amina nace miki kiyi
aure kinki ina Alhajinki shima kin kore shi ko?"
1
Hm! Bilkisu kenan kewai ce miki akayi nice nake
korarsu, ni tunda nake ban taba korar kowaba. Allah
ne dai bai kawo mini miji naba .Allah nayi farin cikin
ganinki sosai, Don Allah ki ajeni a gidan Hajiya
mana, yanzu sai muje mu dawo nan cikin
mararrabane." Tace haba, babu damuwa amma kidan
gyara mana ko zamuci koro da Alhaji tana fada tana
kyalkyacewa da dariya Bilkisu nace miki kinci abinci
kinki yarda, ni ko wallahi na riga na hakura da
maganar aure domin kuwa nasan babu wanda zaizo
yace zai aure'ni a wannan gidan, don kowa kallon
marar mutunci yake maka, don haka na barwa Allah
lamarina kawai. Tace Haba Amina kina magana
kamar ba musulma ba har kice baza kiyi aure ba, kisani fa aure sunnace ta manzonmu don da kansa ya
ce muyi aure mu hayyayyafa zai yi alfahari damu
ranar tashin kiyama ace dukkanmu Al'ummansane,
aiko ko don hakama bazakia sakeba ki zauna babu
duniyar ace lahiaranma babu, ni dai shawarata aa
cikin masu sonki ki samu daya kar ki duba wani abu
wai shi so a'a, yanzu duk lokacin wannan ya wuce,
yanzu kince kinfi sati baki da abinci, to inda kina da
aure da duk ba ruwanki da wannan dole abincinki
suturan ki duk suna wuyansa. Don haka wallahi
Amina kiyi aure, nima yanzu bakiga ba Allah -Allah
nake December nan tazo Abdul ya dawo muyi
aurenmu."
Kinga Amina idan kinada mijinki, cinki, shanki,
sabulun wanka dana wanki duk kudin kashewa da
duk wasu abubuwaa na rayuwa dolensa yayi miki
tunda zamansa kike, Amina ta nisa, tace hm! idan
2
nayi sa'a kenan," To ai daman sa'ar ake nema inji
Bilkisu, lallai ke yarinyace Bilkisu akan rayuwar
aure, tunda har kike tunanin namiji zai baki kudin
kashewa to ni tunda Allaha ya halicceni ban taba
ganin namijin bahaushe daya ke bada kudin kashewa
ba, ban saniba ko akanki zan fara gani. "To wallahi
kullum idan baba zai fita kullum sai ya bawa mama
kudin kashewa," inji Bilkisu, To banda shirme irin
naki kya hada baba damazan zamanin nan namu
wanda yanzu idan kika samu ya baki abinci sutura
sabulun wanka dana wanki ma sai ki godewa Allah.
Ni duk kin cikani da surutu, tashi mutafi kawai. Na
saka atamfata Java Wax jah na dauko mayafi ja
shima, jakata da takalmina farare nace to malama
Bilkisu mutafi ko. Tace amma kinyi kyau Allah ya
baki miji na gari, Amina ke kyakkyawa ce nace Allah
ko? nagode, har kin sani murmushin dole, amma kin
san duk kyauna ban kaiki ba ko? wane ni wallahi
Amina kin fin kyau, don haka ki kara yanga akan
tada kinji ko? hm naji muje.
Mun fito bakin titi, daga gefen titi Bilkisu tayi
parking din motar dake gidan namu lungune, mota
bata shiga ina zuwa gurin motar sai naji sha'awar
Bilkisu ta kamani, Motar Bilkisu 306 ce kalan motar
lemon green, kalan kayan jikinta ma lemon green ne,
duk wanda yaga Bilkisu yaga fentin motarta zaice
motar ta zo da kayan jikintane don haka ba maza ba
ni kaina da nake mace tayi matukar burgeni, takalmin
kafanta golden colour ne da jakarsa, nadai kare mata
kallo nace Allah kayi mana arzikin duniya da lahira
ta ahanya mai kyau. Ina cikin tunanin duniya ne
3
Bilkisu ta tabani tace Bismillah ko inaga tayita
tadinta taji shiru shine ta tabani.
Na shiga mota na zauna a kujerar mai zaman banza,
Bilkisu ta zagaya ta shiga mota ta tasheta sai maraba,
muna cikin tafiyane kafin mu isa take tambayata,
wai shin Amina ina Ambassador ne, wai yaya akayi
kuka rabu dashi ma, ko kece kikace ba kya sonsa,
meye laifinsa? nace No'karki ga laifina, kar kuma
kiyi saurin yanke hakunci a kaina don kuwa daidai da
rana daya ban taba kin Ambassador ba, shi ne dai ya
gujeni, don da a tunani na bantaba zaton ina da wani
miji inba Ambassador ba, tunda yadda ya nuna mun
kauna, lokaci daya kuma ya chanza mun ya daina
zuwa inda nake ya daina waya, idan na kira shi
awaya ya rinka yawo da hankalina, duk maganar
guda da yace yaga banida gata ya akuma ganni a
wannan gidan ba uwa ba uba. kinga fa kofar gidan,
Hajiyan nan zaki wuce, ko kin mance ne, Bilkisu tace
sam Hankalina yayi gaba, bakiga yadda na matsu
naga kinyi, aure ba, nace to mubar wannan maganar
sai mun fito.
Salamu Alaikum a'a 'yata wa'alaikum salamu
ai da nayi fushi dake ne kin yardani, Haba! Hajiya
babu abinda kikayi mini banida lafiyane mama ne,
tana fada tana shagwaba, meyasame ki? wallahi
Hajiya banida kudine, kuma ma dai kin san sauran ba
saina fadaba, ayya bansaniba ai dakin ganni nazo.
Hajiya Ina kwana, tunda shabiyu saura yanzu, inji
Bilkisu, lafiya kalau inji Hajiya yaya mamanki tana
lafiya? lafiya lau Hajiya, tace karmu shagala, Amina
bude firjin can ki dauko kunun zaki ki hado da ruwa,
4
la! Hajiya haryanzu kina kunun zakin nan naki?"
wallahi to me za'a fasa tunda ana saidawa, zama
hakanne bashi da amfani barima kiga in tashi inaga
da sauran cin - cin da na yi jiya ku dan taba kafin
ingama abinci.
Bayan Hajiya ta kawo cincin din, ta zauna
Bilkisu take ce mataa daman inason in kawo miki
karar Amina yanzu a yadda take dInnan mezesa
bazatayi aure ba, bayan ba manema ta rasaba, amma
Amina sam bata son zancen aure jayayyar da muka
rinka yi da ita kenan a hanya, na kıma gaya mata
aure nan shine darajan ta, don kuwa babu abinda yafi
aure mutunci, amma sam taki ganewa na rasa dalili.
"Eh,to, gaskiya kina da gaskiya amma inda zakiji
labarin Amina ba wai taki aure bane ba, kusan sai
ince ai abinda nake ta gaya mata kenan tun a gida
amma taki fahimtata, Hajiya ya za'ayi zuwa zance
wajenta, duk cikinsu ace tarasa wanda zata aura?", To
Bilkisu yanzu dai sai mu tayata addu'ar Allah ya bata
miji na ganri mai kaunar ta don Allah, to amin
Hajiya.
TO ke yanzu Amina ya za muyi dake nabarki anan
ko kuwa zaki gama mu koma tare? kawai kibarni
anan don sai anjima zan koma. Kar in bata miki
lokaci." "Babu wani bata lokaci inji Bilkisu, don
gurinki kawai na taho, nace to mu zauna. Ni kuwa
nayi ahakane don idan mun koma yanya bani da
abinda zan bata taci.
Hajiya abinda yasa nazo don naga ya miki
gaskiya ya kamata a sake shawara akaina don gaskiya
5
nagaji da zaman da nakeyi a gidan nan namu, kinga
kwanaki dana kwanta ciwo irin wulakancin da
Karima tayi mun ina kwance bai faduwa, ina gani
zata dafa abinci tahana ni ba sannu bare ayaya jiki, ki
duba kiga irin muguwar rayuwar da takeyi ta yaya
wani mutumin kirki zaizo ya aureka, tunda kaima haka ake kallonka ba mutumnin kirki ba?
Hajiya yaya kike ganin abinan nifa zanbar gidan nan
don kuwa inason nasami gurin da zan kasance mai
mutunci ko nayi aure hankali kawata ya kwanta ina
fada ina kallon Bilkisu Ina dariya, Bilkisu tace wai
naga abin naki harda tsokana ma, babu wani tsokana
ko Hajiya? don bazan kara aure a wannan gidan
namuba don kuwa nayi banji dadiba kinga kowa
kallon da yake min banida mutunci, ai kuwa yanzu
baruwana da kowa, tunda Ambassador yasani nayi
istibra'I babu ruwana da kowa don haka nema banida
akudi, tunda kowa yazo gudu yake tunda daman
abinda ya kawosa kenan, duk wanda yazo yana son
ya rabi 'yar ni'imar da Allah yayi makane, maganar
kenan yanason jikina idan ka hana shi ken an soyayya
ta kare, daman ba soyayyar gaskiya bace, Hajiya
duniyar nan ta baci to ta yaya matan aure za suyi
daraja? don haka wallahi tsoron aurenma nakeyi, sai
kiga matansa biyu koa uku ga 'ya'ya manya manya
amma sam baya son ya tsare kansa daya baiwa
matarsa ta sunna kudi, gara ya bar matar nan tasa da
tsumma, yaje ya kashewa matan banza makudan
kudaden da in kuka ji abun zai baku mamaki, ga
zunubi ga asarar kudi ya bar lada don haka hakki tun
daga nan duniya, wallahi Hajiya duk mazajen da kika
6
ga ana kora daga aiki hakkin matarsa don kuwa suna
zalintarsu, idan kina bin gidajan matan aure zaki
tausaya musu kiga mace da 'ya'ya biyu ko biyar an
barta babu abincin kirki yara babu suturar arziki,
babu karatun kirki, amma in anje gurin matan banza,
indai zaki bada hadin kai sai a baki ko a kashe miki
dubu dari baiko damu ba kuma karkice wai ko tafi ta
gidan kyau a'a sam kyau da ni'imar Allah duk sai dai
ta gidan ta gwadawa na wajen, don baki kaita ba bare
ki fita, kawai masiface irinta maza, don Allah yaya
mutum zaiyi sha'awara aure. yana ganin yadda ake
wulakanta matan auren?.
To bari na gaya miki wannan duk ba ceke dai kiyi
Addu'a Allah ya hadaki da mijin kirki daman idan
kace zaka dubi wan to babu abinda zakayi, a duniya
tunda shi kansa karuwanci idan kace zaka duba wani
ai baza kayi ba tunda zaka ga wata ansai mata mota
an kama mata gida an bude mata hanya tana zuwa
kasashen duniya.
To ashe idan kina ganin irin wadannan matan sai kice
bari kuma ku daina tunda kai wahala kake sha don
haka Amina kiyi aure, babu wata hujja da kike da ita
akan maganar aure namiji ko dukanki yake da safe
idana zai fita aiki, idan ya dawo ya sake dukan ki
baka da hujjar da zakace bazakayi aure ba iyakaci
kice zaki sake miji, idan kuma kiyi hakurin dukan
naki Allah zai baka lada, wataran ko ance yada keki
bazai dake kiba.
Wannan fa duk dadin da kike yi a karuwanci
wallahi zuni bine inda za kiga irin azabar da Allah
yake rubuta muku da ko ance kiyi ba zaki yi ba don
7
haka duk abinda kika samu ta wannan hanyar bazata
yi miki albarka, ba kosu masu fita kasar wajen inda
zaki kula sai sun gama wahallarsu kiga wani abu
yazo ya afkawa dukiyar tasu gaba daya sun dawo
abin tausayi. Don haka idan zaki nemi lada komin
kankantarsa ki nema. Bilkisu kenan duk abinda ki
kaga mutum yanayi to ba lallai bane yazama ra'ayinmsa don haka ni da kika ganni nan dole ce
tasa na shiga wannan halin. Ato nidai na gaya miki ki sake tunani. "Bilkisu ke baki san rayuwa ba shiyasa kike fadar haka ihm haka kike gani ko bai faru a kaina ba ai ya faru akan dan uwana ko kuma nagani a littafi ko T.V Duk surutun nan da mukeyi Haj kalanmu kar takeyi can ta nun fasa tace to gaskiya rayuwar Amina abar tausayice don Amina dolece ta sata ayin wannan haakar ba wai tanayi bane don son ranta. Don haka duk wannan surutun ba magani bane abinda nake gani a matsayinmu na
masoyan Amina mu tayata Addu'ar Allah ya bata miji nagari.
Maganar tashinki kuwa tazo gidan sauki don kuwa Anty ki Ramatu tana neman wanda zasu zauna tare
don tunda ta gaya mini ban tuna kowa ba sai ke don
haka gobe in Allah ya kaimu zata zo zan gaya mata
ke kuma kisan yadda za kiyi dasu Umma, don ba na
son su san za ki guje sune kije wani guri, don haka a
hankali zamu bi abinda zaki rinka yi shine da kadan -
kadan har kibar gida kije can ki kwana biyu kije can
ki kwana uku da haka har kibar gidan gaba daya ko
kuwa yakike gani?. Hakan yayi Hajiya. Abu na biyu
kuma shine inason ki rika mutuncinki kamar yanda
8
kika ce kina yi to kici gaba da rike mutunci ki ki dauki Aunty Ramatu kamar 'yar uwarki Uwa daya Uba daya don nasan ita ma zata rike ki da haka don
nasan halinta, Inason duk wanda yazo agurinki
magana daya biyu inason ku tsaida maganar aure dashi. Idan baya yi yayi gaba.
Abu na karshe shine maganar Bilkisu dale kiyi yaki
da zuciyarki kidage da Addu'a, Sallah Azumi duk
don Allah ya baki mijina gari to Hajiya nagode, babu
komai kibi abin a hankali gobe idan Allah ya kaimu
kizo da safe da kayanki koda kala biyune ko uku,
kice da Umma kina son zuwa nan wajena daga nan
din sai ku wuce da ita Ramatu, Luba don kinsan ita
Umma halinta sai ita, saia da dubara don hakaa mubi
a hankali idan kina son kiga 'yan uwanki sai kizo
donni banson susan inda kike ko kuwa kina ganin su
sani ba wani abu? an ko ni zanso su ganni kawai ba
tare da sun san inda nake ba, tunda yadda Umma
takeyine bana so tana kara zubar mana da mutunci
don duk wanda ya ganka da ita zai dauka kaima haka
kake. bama ya kwanan gidan nan da take zuwa yana
bata mun rai don dai babu yadda zanyi da itane
ayanzu ni dai zan koma sai in Allah ya akaimu goben
zanzo nagode Hajiya, Allah ya kara kauna, babu
koma: Amina da na kowane, mu dai fatanmu Allah
ya cika mana burinmu ya kuma shirya mana
mahaifinku ya name ku don kansa,” hm! anya Hajiya
amma dai Amin Allah ya amsa addu'arki.
Bilkisu mu koma ko? don Allah Hajiya ki gaya wa
baban Khalifa zancan neman aikin nawa, karya
manta, to yata sai goben, ga wannan dari biyar ne ki
9
rike don karki rasa kudin motan zuwa goben ko?
Inason goben ki sanarda Umma bazaki kwana ba a
gidan don kar suga shiru idan kin kwana a lugbe
kwana kamar uku sai kije Nyanya ki kwana biyu ki
rinka musu karya da nan gidan kinga koda zasu
nemeki in sunzo nan ni nasan yadda zanyi dasu haka
har ki kwashe kayanki gaba daya, ke kuma Bilkisu
kinki cin abinci ko? a ba haka bane wallahi na koshi
ne ainasha kunun zaki da cin cin shi yasa na koshi
mungode Hajiya.
Daga nan muka fita daga gidan Hajiya muka
shiga motar Bilkisu, To malama Amina yanzu sai
ina? sai gida mana Bilkisu daman nane kawai zanzo
gaskiya Amina Hajiyan nan tana kaunarki sosai ko ita
ta haifeki sai haka, nifa har kunya naji dana
hakikance miki daga baya naga ita manufarta tafi
tawa baki ga nayi shiru ba, ko abincin ma ai kunyace
ta hanani naci don yadda nayi miki, araina nace ni dai
zuwana na uku kenan amma bansan tsakanin kuba da
itaa halan yar uwarkice? Gaskiya Billkisu ina jin
bakya jin hausa sosai, tunda dai da kinbi
magananganu da mukayi da Hajiya da bazakice 'yar
uwata bace." "A'a yaza kaji Amina da wata magana
yaya zakice banajin hausa aifa ba sauraranku nakeba
kuma ma ai yawanci hirarku bana gurin naje yin
sallah. Ito hakane nayi shiru, don Allah Amina inason
ki rakani wuse II zanga Babana kinga ma biyar ta
kusa sai dai muyi sauri, bara in dana kara gudu, ni dai
gaskiya Bilkisu bana son gudunnan garamu tafi a
hankali, don ke wani lokacin sai ki rinka gudu kina
kuma kokarin yin over taking karfi da yaji, ni ko idan
10
naga haka tsoro nakeji. Amma Amina har kin ban
dariya sai kace wata bakauyiya? a'a a'a ba wani
zancen kauyanci rai dai guda dayane don haka dole
mutum ya lallabashi, to kice bazaki iya tukin motaba,
gaskiya bazan iyaba shi yasa koda wasas ban taba
gwadawaba, to ni kuwa insha Allahu saina koya miki
mota kafin kiyi aure, hm!Allah yasa.
Amina kinki ki gayamun tsakaninki da Hajiya
ko? Bilkisu kiyi hakuri zan gaya miki tsakanina da
Hajiya amma bayanzu ba, okey ba damuwa muka
karya kwanara shiga cikin farfajiyar ofis din, wani
make ken waje ne mai kayatarwa, yasha tiles masu
dan shape mai kyan gain, ina ta kale - kale na sai naji
Bilkisu nacewa kinga sa'a ko? ga Babanma can yana
kokarin fita gashi can zai shiga mota, bari musha
gabarnsa. kowa yasa dariya dagani har baban ganin
yadda muka sha gabansa da mota, daga ina haka? ya
tanbayemu uwata harda ke? don baya fadan sunana
haka yake cemun, Uwata gaskiya Baba muna da sa'a
inji Bilkisu yayin da ni kuma na tsuguna ina
gaisheshi, bayan mun gaisa na koma cikin motar na
zauna ina kallon Bilkisu da Babanta, abin yana bani
sha'awa kwarai da gaske, ina tunanin nawa mahaifin.
Ina cikin tunaninne har ta dawo ta zauna a mota ban
saniba, saida ta tabani sannan na danyi firgigit, nace
har kingama? shine take cewa a'a shin lafiya? nace
"lafiya kalau ina sha'awarku keda baba don kuna
birgeni sosai. kasancewar Bilikisu 'yar boko ce kawai
sai cewa tayi Allah ko? tabar maganan anan, ni kaina
naji dadin hakan don banason tasan sirrina, inaga
kamar zata gujeni, Bilkisu ta dada katsemini tunanina
11
tace yanzu bari r a kaiki gida, nace a'a babu inda zaki
kaini, ki ajeni at an gangare zone 4 nan Bus Stop in
shiga mota zuwa Nyanya, yaushe zaki daukia hanyar
A.Y.A a wannan kurarren lokaci ki kuma dawo
maitama? ki san a bus kawai in tafi." Gaskiya nefa
Amina mama ma zata mun fada don ban taba kaiwan
har wani lokaci haka a wajeba, amma bazan sakaki a
bus ba, barina tarar miki drop tunda kin kafe, yanzu
to six, gama taxi cana Hey, drop mai Taxi yazo ya
tsaya don Allah Nyanya. Gaskiya Hajiya bazani
Nyanya yanzu ba domin dare yafarayi, shikenan
jeka, gawani cana ssssss drop Hajiya inane? donAllah
Malam Nyanya, dari biyara in kin yarda, Bilkisu tace
na yarda kai daiAllaha ya akiyaye hanya, amin
Hajiya nace kinga abinda nake gaya miki ko? da kin
barni naje na shiga bus dina naira dari ta kaini, a'a
karkice haka Amina dari. biyar ma ai bus babu
mutunci bare da magaribar nan, to shikenan nagode
bari inje mai taxi na jirana kar yaji haushi ya tafi.
Hajiya ina jin, don Allah mallam kayi hakuri muana
zuwa, kinga Amina wannan dubu goma nina baki kije
kisayi abinda kikeso in zaki koma lugba dubu
biyunnan kuma babane yace in baki, kai Bilkisu
wannan wace irin dawaini yace haka kika sa kanki,
kai don Allah bana son irin haka Amina baki san
yadda na daukeki a raina bane shi ya kawo wannan
dogon zancen, nayi shiru Bilkisu nagode Al;lah ya
bara kauna, zanzo insha Allahu ki gaida mama ki
shafa mini kan mutumina Hassan, a'a Hassana yayi
fishi dake, tunda kinki aure ki Haifa masa mata. To
yayi hakuri rai dai Allaha ya kawo, sai nazo nagode
12
na shiga mota mai nai taxi yana ta kunchi yana
fisgata kamar zai yardani, ni dai farin cikina daya
wannan kudin da Bilikisu ta bani, sai tunanin iri - iri
nakeyi nace a raina nama rasa wane irin kauna
Bilkisu take mini, don ban dauka na kai har hake a
zuciyar taba, Allah kenan mai yin yadda yasos ya
hjada ka da wani dan uwanka ba, baima saankaaba,
amma ya rinka maka kauna na tsakani daAllaha
rayuwa kenan.
Muna isa Nyanya mai Taxi yace inane Hajiya
nace kabi kwanar can ta gaba da haka dai hara
mukaje gefen tititn da ya kamata ya tsaya don mota
bata shiga lungunmu, ina isa gida ınagariba tayi na
wuce daki na a'je jakata na tube kayana, kaina tsaye
toilet nayi daman bana sallah don haka na shirya na
fito gurin mai shayin unguwarmu, yana kofar gida na
sayi indomi guda biyu da kwai shima biyu da madara
peak milk na bashi kudinsa nayo gida, Ina zuwa na
dauki tukunya na dan soya kwai ca attarugu nasa
albasa kafin nan da nan na jika indo nie na da ruwan
zafi don haka na tsame na zuba na soyata ta soyu
yarda nakeso daman inda sauran milo na da sikari na
hada rowan tea, naci na sha nai tab dani nahau gado
sai bacci don daman na gaji.
Gari na wayewa wajen karfe goma na shirya
tsaf abina, ko karyawa ban tsaya yiba, don dama idan
haka ina period bana iyacin a binci da safe. Don haka
nace da Umma zani maraba amma bazan dawo ba sai
nayi kwana uku na dauko wata 'yarkaramar jakata
mai cin kaya kala uku zuwa hudu, na zuba kaya na
kala hudu harda rigar barci na dauko kayan
13
kwalliyata na saka duk a jakata, na sami jakarleda na
saka takalma kala biyu da slifas na uku duk na hada
komai na sami atamfa ta Ghana wax na fito bakin titi
sai maraba.
Ina shiga Hajiya ta karbeni da waina (masa)
nace haba Hajiya mu gaisa mana tukun, tace ai
inason na shiga wankane, kafin in fito kin gama,
Hajiya labarinda yake bakinane yafi karfin masar
kinsan dai ance ciyana gaba da komai, amma gaskiya
yau ina tafe da labarin da nake jin yafi ciin dadi a
ganina wannan maser kuma insha Allah nacii da rana
can.
To ai nima kinsa naji na fasa wankan sai naji
wannan labarin daya faranta miki rai, Hajiya kinga
wannan kudin kirga kiga nawane? aiba saina kirga
ba, waya