in ka
tashi kayi wanka ka kunna kallon da ka keson
gani, rayuwa kenan ashe muma zamu samu
wannan?.
Yanzu tunda komai ya natsa bari na nemi
wanda suka rungumeni lokacin da ba ni da komai
bani da kowa, Hajia maman kalifa da Bilkisu, na
tashi naje bangaren mahaifinmu shi da inna suna
zaune suna kallo, na gaya musu bukatata na
-74-
L
kuma gayawa babana irin wahalar da suka yi da ni
a baya, yace "to idan Allah ya kaimu da safe na
shirya naje na samesu."
Gidan maman kalifa na fara zuwa, tunda
ko rasuwa karima bata sani ba ballan tana kо
shamsu zaije ya gaya mata amma nima nayi shiru,
ban boye mata komai ba na gaya mata duk yadda
abin ya kasance, na bata hankuri akan rashin gaya
mata rashin karima, hajia ta yi kukan rashin
karima ta kuma ta ya mu murnar komawa gaban
iyayenmu, ta yi min alkawarin zata ta yiwa inna
da baba gaisuwar karima ita da baba kalifa, ban
dade ba na kama hanyar zuwa gaidansu Bilkisu a
maitama take, ita ma tana ganina ta fara cakwadi
na dai dau laifina, na gaya mata karima ta mutu
bayan tafiyasu da kwana daya, sun ji mutuwar
sosia da ita da Abdul dinta, Hajiya Ramatu ta fito
itama tayi min gasiuwa, can muka shige daki da
Bilkisu nake. gaya mata mun koma hännun
iyayenmu, yanzu nai mata kwatancen gidan, ta yi
min alkawarin zuwa, sai mita take wai saura sati
daya bikinsu duk abubuwa sun cakude mata ta
rasa inda zata ganni ta buga waya taji shiru ta je
gurin Mairo, Mairo tace bata san ba gidan, na ce
"itama yanzu zanje, yau yawan zumunci nake da
kuma ba da hakuri," Bilkisu ta so ta rakani, ta ki
saboda Abdul ya'na zaune babu dadi Abdul ya
bani dubu biyar, na ce mata "yanzu idan ta o bugo
waya za ta sameni, daman a rufe ne saboda
-75-
mutuwa" tace "za ta zo ta daukeni na yi sallama da
mamata na wuce cikin sauri.
Ban zame ko ina ba sai gun mairo, wayyo
mairo bata nan, ta tafi Babura sai dai aunty Nafi, ta
gaya min ranar da zata dawo nace "zan zo na
dauketa zuwa gidanmu." Anty Nafi ma ta taya ni
murna, naso naje gun anuty Hafsat amma dare ya
yi, dan haka na koma gida.
Wani abu da ba mu saba dashi ba shi ne
kulle, ba ma fita nan da nan, san nan kuma baba ya
ce "kowa saita fitar da miji." Binta da take
yarsanda a maiduguri tace ba zata koma ba aure za
tayi, abin kunya duk cikin mu ba bu wata mai
takamaimai sai Hadiza, don yazu Alhajinta
bakano ya dawo ya tsaya tsakani da Allah zai
aureta tun da ya ga iyayanta, da Hadiza tana
neman taki, ni dai na bata shawara nace "gara ta
hakura tunda Baba yace idan ya gaji zai bayar
damu gun abokanan cinikinsa" ita matsalar
Hadiza mata, matansa uku don haka bata sonsa,
amma yace zai raba musu gida ita zai barta a
Abuja, amma ita Hadiza tana ganin kamar ida
anyi biki zai hadasu, sunansa Alh. Rabo dan,
kundila ne, irin mutanan da suka shigo Abuja da
sa'a ne a lokacin Abacha, ya dade yana wahala da
Hadiza kusan nace shine mutum na farko daya
bude mata ido, ban da shi ban ta ba ganin Hadiza
da wani ba.
To yanzu dai Hadiza ta yarda da shawarata,
-76-
1
1
1
don Alh. Rabo ya yi tambaya an kuma ba shi,
yanzu haka a wannan satin zai turo mutanensa
daga gida za a sa rana.
Ta bangaren mu kuwa ni, Binta da Sadiya
ba bu bayani kwarama Binta tana tunanin
komawa gidanta na da, ni ko a lahira ba na son
Allah ya sake hadani da nawain ba wajen hisabi
ba, tunda mijinta yazo sau daya take tunanin
komawa kuma naga innama tafi son haka, wai
daman uwarsa ce, ta kuma mutu, yanzu komai ya.
rage min tunda sadiya yarinya ce, don haka ba
dole bane a matsa ma ta tunda gamu.
Washe gari da safe, maman kalifa ce ta fara
mana sallam ita da baban kalifa....bayan ya yiwa
inna gaisuwa, suka keba da baba a falon kofar
gida, sun sha hira sosai har sai da baban kalifa
yace "ya na so zai je unguwa, zai bar Hajiya a nan,
idan ya dawo zai zo ya dauke ta, itama ta tausaya
min, ta dau alkawari sakani a cikin addu'a Insha
Allahu kema zaki tashi dai dai dasu. Hajiya bata
tafi ba sai ga Bilkisu, maman kalifa ce ta kwashe
komai ta gaya mata, Bilkisu ta yi dariya tace
"daman wannan zance na ke son nayi amfani da ilimina, zan kuma nemo wanda nake son na ganki
da shi duk duniya." Ido kawai na kafawa bilkisu
ina kallon ta.
Hajiya tace "to Bilkisu Allah ya bada sa'a,
ai onasan aikin ki yafi da haka. Mutanan Alh.
Rabo sun zo neman aure kuma an basu an saka
-77-
rana, saura sati uku, sunkawo kudin komai da ake
kawowa. Binta ma dai abin ya kusa tabbata don
mijinta ya dage da zuwa, yanzu haka har sun
tsaida rana zai turo kanin babansa. Sadiya ma da
bata kula kowa yanzu ta dage don ihar tana
tunanin tsaida wani Tasi'u a matsayin mijinta.
Yanzu ya rage ni kadai a filin ko yanzu nayi rashin
karima don da tana nan da ni da ita zamu yi
kwantai.
Yanzu gidanmu shirye-shiryen biki suke
nima kuma ina ta faman shirye-shiryen- bikin
kawata, don yanzu saura kwana uku suka rage a
kaita dakinta, munje mun siyo anko gwar-gwaron
ne golden colour na kawayen amarya, kawayen
mama kuma na su fari ne. Bilkisu 'yar gata,
komai ya ji a bikinta, don Nicon Hotel aka kama
mana don yi dinar, launching kuma a Sheraton, a
Sheraton din ma a Ladi Kwale Hall, Hall din da
ake takama da shi a duk hotel din, duk wanda ya
hallarci bikin na ranar asabar, ya san bikin dan
gata. da 'yar gata ake yi, maman Bilkisu ita ta
kama'Sheraton ita kuma maman Abdul ta kama
Nicon, wanda aure kowa yana ji da kansa. Baban
Abdul shi ne Information Minister a yanzu ga
bilkisu ita kuma abar milk, amma an tara an aje
tuntuni, gata ita kadaice tilo, gwara Abdul naga su
na da yawa naga yayyansa da kannansa, duk sun
yi ankon wani jan leshi tunda nake da Bilkisu bata
ta ba fadamin Abdul dinta dan information
-78-
minister ba ne sai a katin Biklinsu na gani, gaskiya
duk halayen Bilkisu su na birge ni, ni kadai na je
wajen launch, saboda haka na dare na ce da su
Hadiza su taho muje gurin dinnar, da kyar ta bi ni
wai ita tana shirye-shiryen bikinta. Mu duka
muka je, ni da Sadiya, Binta da kuma mahaifinmu
ya ba mu lokaci kar mu wuce goma, Allah sarki,
duniya ba bu abin da ba zai wuce ba, in da ne ko da
kwana za mu yi ba bu ruwan kowa da mu. Ina
shiga hall din idona in ba karya ya nuna min ba
Aminu ne na gani mijin Yusra, wanda ya so muyi
aure Allah bai yi ba. Nan da nan na dauke kai na na
yi kamar ban ganshi ba, mun samu, guri mun
zauna nida 'yanuwana, ni kadai a zuciyata nake
cewa ko dama Aminu abokin Abdul ne, in ba haka
bamai ya kawo shi nan.
A sani na Bilkisu bata san shiba, dan haka
babu yadda zance ita ta gayyato shi, to Allah dai
ya barwa kansa sani. Daga isar angó da amarya
wajen, don haka kowa ya je ya zuba abincinsa
bayan ango da amarya sun zuba nasu, mun je
muna zubawane ni da Binta sai naji ance "ki zuba
min nima madam" ban ma san da ni akeba sai da
na duba bayana ina cewa Binta to bismillah, sai
naga Aminu kawai, na kasa magana na mika
masa plate din nawa, wani irin yar naji har cikin
jijiyoyina tun da nake ban taba jin irin wan nan ba,
na kasa maga kamar an kafe min bakina gam,
haka naji lallai so masifane don ko ba komai duk
-79-
T
2
T
gabobin jikina yau sun nuna min na kamu da son
Aminu, gaba daya na yarda da zuciyata cew yau
na hadu da mijina wanda jikina ya tabbatar min
cewa duk duniya ba bu namiji da ya keburgeni
yake bani sha awa irin Aminu, na yarda ba ni da
miji isai Aminu. Ya ce "ki zuba wani" nace "na
koshi” ya sa dariya yace "haka har da saurin
sarewa, to zo mu ciwannan dinma." Mun gebe ni
da Aminu mun zauna muna cin abinci ko da yake
ni drinks na sha, tun muna zaune cikin mutane
hira ta yi dadi, muka kebe daga da kujeru muka
zauna.
Ni da Aminu kowa kokarin ba dan uwansa
laifi yake, shi ya na ni na koreshi, nima ina shi ya
koreni, shi kansa ya yi mamakin da na tambaye
shi ina ya san mijin Bilkisu, yace sam bai san shi
ba, Bilkisu ce ta kai masa kati har office dinsa,
lallai na yarda yau Bilkisu ‘yar jarida ce, ina duba
agogo na ga goma, na tuna da gargadin da
mahaifinmu yayi mana, don haka nace da Aminu
zan je neman su Binta don ance kar mu wuce
goma. Shi ma ya kalli agogonsa ya ce "da kyau,
muje in kai ku," hall ya kacame da kida kowa sai
rawa yake, amarya da ango suna tsakiyar makada,
mutane sun lullube su bama su san wanda yake
kansu ba, don haka ban bata lokacina ba wajen yi
mata magana, naja su Sadiya muka kama hanya
har kofar gida Aminu ya kaimu, mun da de a mota
muna hira, ba bu yadda banyi da shi ba akan ya
80-
do
ya
da
bi
k
A
b
k
d
ra
d
n
11
g
y
1
Π
A
t
K
66
1
C
1
a
Π
shiga su gaisa da su Inna, ya ce "sam zai zo zuwan
kansa ba yanzu ba. Mun yi sallama tare da bawa
juna lambar waya, na shiga gida cikin farin ciki da
walwala ba kamar da ba, tun da ko ba komai nasan
ina da matayin hira, nima a yau na yarda da
maganar Baraka tunda na fara gani da idona inna
ta fara canja min akan su Hadiza, abu kadan ka
ganta suna hira da na shigo sai ayi shiru, ina ji
haushi kawai ina dakewa ne, saboda na san yadda
zan yi da anga ba ni da kowa, to nima Allah ya
kawo min nawa ko bal aureni ba ya tayani hira da
haka har Allah ya kawo min abokin zama.
Na shi go gida, ban ko fadawa Inna abin da
nake cikiba, sallah kawai nayi na kwanta, da safe
da muke falon su Inna wurin gaisuwa take
tambayata "wa ye jiya ya kawo ku?"Nace "wani
tsohon sauray nane" ban ce Aminu bane, Baba ya
ce "to Allah ya zaba muku abinda yafi muku
alheri" nace "amin, nagode" Hadiza bata gurin na
tashi na koma dakinmu na duba wayata naga
missed call, Aminu na share na kira Bilkisu ta
dauka tana magana da kyar, da ka ji kasan akwai
gajiya nace "kiyi hakuri na katse miki rayuwa",
"a'a ba bu komai, wai jiya mai ya faru ko salama
ba bu?" nace "Bilkisu ko me ye ai ke za a
tambaya, wai Bilkisu ya akayi ki ka san office din
Aminu" ta sa dariya tace "Alhamdu lillah abin da
nake sonji kenan kuma na ji dadi tunda komai ya
yi dai-dai", "to naji wa ya fada miki office din?"
-81-
"Ki tambayi Hadiza ita ta fada min inda gidansa
yake ni kuma na je na tambayi mai gadinsa ya
fadamin office dinsa, shi ne na kai masa card
amatsayin kawarki, na kuma gode ya amsa kirana
yazo, don Allah Amina ki sawa kanki nutsuwa ki
auri Amimnu, kinga tunda yanzu komai yayi dadai, sai ku dai daita ni ina ganin Aminu ya so ya
samarwa 'ya 'yansa uwa tagari ne shi ya sa ya
dage, kinga yanzu za a yiwa kowa aure a gidanku
danda ke, ko ni ban ji dadi ba shi ya sa na nemo
Aminu don inganin duk duniya banga wanda ya
cancanci ya aureki in ba Aminu, kin san bature ya
ce true love never end don hakaki kwantar da
hankalinki kawata, soyayyarku da Aminu ba zata
kare ba, sai dai ta karu, bari na barki kar kudinki
ya kare zan kira in anjima, bye bye!.
Yau saura kwańa shidda bikin Hadiza da
Binta don haka kullum suna hanyar kasuwa, yan
zuma suna hira, ni kuwa yau shirin bacci bacci
zan yi tunda mun gama namu bikin, Bilkisu tana
ginta tunda a America za su zauna, don haka tana
ta shirye-shiryen tafiya, andai shirya musu gida
da komai da komai a Asokoro anan, bata tareba
saboda shirye-shiryen tafiyar da suke yi.
Har bacci ya fara daukata wani yaro yazo
ya kwan-kwasa dakin da nake wai gashi inji wani
abawa Amina, da saurina nace "yana ina?" Yace
"yana motarsa", Aminu ya na so ya canja hali, ba
zai so ya gaida su Inna ba? Gasgiya a rayuwata
82-
d
K
bana son na auri mijin da bazai girmama iyayena
d
H
D
1-
d
T
1
الا
1
i
t
1
ba, na bude ledar naga cards guda biyar da
turaruka, kowa ne card yana dauke da maganar
soyayya kala-kala, kan na gama karanta cards din
text message dinsa ya shigo, ya rubuta kamar haka
"Hi! Darling how are u, please take this before i
come back from office, bye" na ji dadin
wannantext din, saboda na san ko yanzu Aminu ya
na tare da ni, kai lallai zan yiwa Allah godiya ranar
da na ganni a gida Aminu, na yarda da masu iya
magana da suke cewa so baya tsufa Sai dai
masoya su tsufa, har yau Aminu kullum soyyaya
sabuwa ta ke dasuwa a zuciyarsa, naji dadi nace,
bari nayi godiya "Thank you sweetie, may Allah
give U a rainbow 4 every srom, a smile 4 every
tears, a blessing 4 each treail, a sweet song 4 every
sight and an answer 4 every question" ba aminu ba
ko makiyina na yiwa wannaň text din na san sai ya
saramin, shiru in cewa text din nawa bai shi ga,
sai da na duba Acct di na ga har sun cire kudin text,
zuciyata ta bani abu biyu, na farko na ce ko ya shi
ga bai gani ba yana aiki, na biyu na ce ko shi bai yi
masa dadi ba, na koma na ci gaba da baccina ban
farka ba sai salla, ni kaina nayi mamakin baccin
da nayi.lallai ba karamar gajiya na tara a harkar
bikin nan ba, bayan nayi sallah, naji wayata na
kara ashe Amaryace, mum dade akan layi take
gaya min an gama musu komai na tafiya sauran
kwana uku su tafi, wai tana so ta zo gobe ta yi
-83-
+
3
sallama dasu inna.
"Lallai ba kwanan za'ayi bikin Hadiza da
Binta, da", "suna cewa kwana shidda", "lalle
kam, to ke kuma yaushe kuka sa mana?, gaskiya
ina bakin cikin zaman AMERICA, naso na ganki
a dakin Aminu" "ba bu komai haka Allah ya
shirya", "amma Insha Allahu zan zama kamar ina
nan, don waya zata daukar min komai, inaga idan
na takura muku da waya har sai kun kasha," "haba
dai Bilkisu, Allah ya sawake, inaga a rayuwata ba
bu wani dadi da zai sa na manta da ke da Miro,
maman kalifa don duk mutumin daya rungumi ka
lokacin da baka da komai, to lallai zai goyaka
idan Allah ya yi maka arziki" "haka ne, to mun
gode bye."
A'a, har mesege ya shigo muna ta faman
suruto, dana duna lokacin na ga sha biyu ya shigo,
lallai yau nayi bacci ban ko ji kara ba, "sweetie
thank you very much, God belss you, I was given
a heart only 2 love u, my hrt beats only 4 U, I was
given Eyes only 2 u, u know I can't help my
feelings it tought 2 live without you" cikin sauri
na bashi amsa.
"Oh! My baby I luv U, luv ur smile d way u
call me! Oh Aminu just luv every tin about u take
care and b mine 4ever."
Karfe hudu dai dai sai ga amsar text dina
daga Aminu "yes my baby I am on my way, I'll b
with you soon. How prepared are you for." Nan fa
-84-
dУdЫKAHdrd1111d1a
na fada wanka da sauri, na dauro alwala la'asar,
ina idar da sallah na shiga shafe-shafe, yanzu
kuma na mayar da dove maina, sahibata Bilkisu
akwati biyu ta kawomin satin bikinta na kayan
sawa harda set din dubai da abin hannu, duk
akwatunan nan daga super sai less da kuma irin
materials din nan masu tsada, banyi mamakin
kyautar Bilkisu ba, don kuwa irin kayan da aka
dankaromata da gwala-gwalai, abin kamar almubazzaranci koda yake naira ta isane shi yasa.
Don haka na dau wani less pink kala na dau
passion sarka pin kala itama, nasa jan bakinma
kalar kayana, na san ni da kaina nayi kyau, don
duk wanda yayi kyau ya sani basai an gaya masa
ba, yaro yayi sallam da ni, lokacin biyar dai dai, ba
sai na tambaya ba, nasan Aminu daga office yake
direct, don haka naje kicin dinmu na zuba dambun
shinkafa da akayi a kula, wanda na san ko inna da
ita take yi tund da ita suke sakawa baba idan yana
da baki, naje falons u inna don nasan ba'a rasa
zobo a fridge dinta, na dauko a babbar robar
swam, na shirya a babar folon, na wuce falon Isa
na hanyar kofar gida na aje komai, sannan na fita
waje gurin motarsa. Wani kallo da Aminu yayi
min sai da naji yar a jikina, daga ni harshi kowa
jikinsa ya tsinke babu wanda yayi magana, da
kyar ya yi karfin hali yace "madam, har na dade
ina jira", sai ni ma nace "don Allah ka yi hakuri,
ka shigo daga ciki ko?" Ya biyoni a baya muka
-85-
C
wuce falon Isah, sai ga su Hadiza da Binta sun
dawo daga kasuwa da kaya niki-niki suna fama.
Sai da na zubawa Aminu abinci san nan muka
gisa yace "gaskiya madam, komai yau ya kai min,
don inajin babu wanda ya kaini gata, ga abinici da
na dade banciba, wanda nakeso, gaskiya idan ma
baki iyaba wallahi ki tambayi inna ta koya miki
tunda wurin." "balantam na iya" "to madalla
tunda kin iya, don ina son sa, karfa kice santine"
"a'a ba bu komai tunda dai akan kujera kake
nasan zata kare min kai."
"Yanzu dai mu ina wuni? Ya ya gaisa,
aiki?" "Lafiya kalau rayuwta! Gaskiya Amina
kinyi kyau kamar yau za a kai ki dakin nawa, kai!
wannan randa aka kaiki kuma ai sai na sume,
tunda yanzu jikina duk rawa yake." "Allah!"
Nayi masa wani far da ido, dan nasan duk namiji
idan akayi masa sai yaji a jinkisa, ai kasa daurewa
yayi yace "don Allah karki sake min wannan
kallon sai munyi aure, ai sai kisa naje ayi abin da
ba shike nan ba," yace "to, saura kuma idan mun
yi aure kiki yi min, don yawanci matan hausawa
soyyayarku a waje take, inason duk abin da ake
min a kara don nima karawa zanyi ba ragewa ba”
"to Allah yasa da gaske ka ke, tun da ku maza
haka ku ke, kuyi kamar zaku cinye mace a
gidansu da zarar taje kun aureta shike nan sai
kaga kamar baku ba." "to naji maganarki amma
ina son daga ganki muga darasi duk muba mutane
-86-
masu irin wannan halin mamaki suma su daina."
Muna cikin hira yace baiga karima ba nace
"ay karima ta dade da mutuwa", Aminu ya yi shiru
bai sake magana ba yace "to lallai na shiga na
yiwa inna gaisuw ya kama ni, don koda wasa ban
sani ba." Bayan ya fito daga gurin inna ne ya ke ce
min ashe su hadiza suma aure za'ayi musu, wai
yau saura kwana shidda inji inna, to ko muma
muce ahada damu ne, Amina?" "A'a kabarsu sun
tsara kayan su kawai muyi musu katsalandan,
muma mu kirkiri namu" gaskiyarki fa."
Sai shidda saura yayi min sallam ya tafi gida da niyar zai dawo bayan sallar Isah'i,. Na shiga na tarar da su Hadiza anata faman raba
kayan da aka siyo a kasuwa, banko kula suba na
shiga na cire kayana, Sadiya ce tace wai inje inji
inna, nasan maganar bai wuce maganar Aminu ba.
Amina yaushe Aminu ya fara zuwa nace "inna tin
ranar bikin Bilkisu", "to yanzu da wacce maganr
yazo" "da aure mana" "ai gara kiyi masa Magana
yasa himma aiba tsayawa za a yi ba ana wasa
dama ba ba bakone ba, don haka gara kawai ayi
maganar aure idan yazo kice ina nemansa” nace
"to inna amma ina maganar aure zakiyi masa da kinbari nima zan yi masa" "shi ke nan in dai za
kiyi masa, ai daman ga ni nake kamar baza ki yi
masa ba."
Bari naje na je na yi sallah, inna idar da
sallar magirba na yi wanka, nasa siket da riga,
-87-
siket din har kasa, na dauro alwalar Isha'i ko tashi
ban yi sallar ba, wayata ta yi kara ina ganin
lambar, nasan Aminu ne, don ina dauka cewa yayi
"ranki ya dade ina waje" na dauki dan karamin
mayafina na rufe jikina, yana jikin mota ya ce
"wai yanzu wata sabuwa kira mai kyau aka yi
miki ne, Amina gani nake kamar ba Aminar da na
sani ba, komai nata ya canja sai kyau take karawa,
anya kuwa zanbari su Hadiza su tashi su barni a
gidan nan. Gaskiya gara naje na gayawa inna ina
son a daura mini aure da matata hankalina zaifi
kwanciya." "Haba dai ai idan aka yi haka an yi
mini shigar sauri, ko aunty Yusra ma ba a kyauta
mata ba, irin wannan shigar sauri" "a'a, ita abin da
ya ke bakonta yanzuma ba gida daya zaku zauna
don ke zaki zauna a gidana na Kwarinfa ne, kinga
kuwa ai tarewa bata shafe ta ba" "haka ne amma
ta na da hakki da hakkinta za a ba ta mana", "tun
sanda muka hadu na gaya mata na sake haduwa
da Aminata kin san kuma yušura ma ai bata da
damuwa, yanzunma idan naje zance tazo ta yiwa
inna da baba gaisuwar karima insha Allah gobe da
safe idan zan wuce zan ajiyeta idan nadawo aiki
sai na biyo na dauketa.
"To mun gode, amma don Allah ina neman
alfarma a bari sai jibi ta zo, don gobe idan Allah
ya kai mu ba na nan, don Bilkisu za ta zo yiwa
Inna sallama, nima kuma zan bita mu yi
bankwana insha Allah, ka san jibi za su tafi",
-88-
“wan nan ba zai hana Yusra zuwa ba don kuwa ba
gurinki zata zo ba gun Inna da Baba za ta zo" "ya
kamata ace idan tazo na ta yata hira, tun da ka san
baza ta sake da Inna kamar ni ba, ba ka son mu
saba ne?, ai ko ba gida daya zamu zauna ba ya
kamata ace muna zumunci." "Na yarda da maganarki ranki ya dade, don haka a hukuncin da kika yanke ya nuna sai jibi Yusra za ta zo. Amma
ni zan so idan Bilkisu ta zo a kira ni mu yi sallama,
ko ba a son sallamar da ni?" "a'a, ni nace, Allah ya kaimu goben".
Ina shiga gida na saka rigar baccina na kwanta, ban yi minti talatin ba bacci mai karfi
kamar wadda ta wuni ta na aiki, lallai na san gajiya ba bu kyau, duk gajiyar bikin nan ce taki barina, har yanzu ina da aiki tun da ga wani bikin a
gaban mu yana tafe.
Ai ko da safe na rigå kowa tashi daga bacci, tun kafin nayi sallar Asuba sai da nayi
wanka don naji karfin jikina wajen sallah, ban bar kan abin sallar ba har karfe takwas na safe, ban da istigfari ba bu abin da nake, a lokacin abubuwa da
dama sun fado min, na tuna muguwarrayuwar da
na yi, yanzu ko ina su Baraka da Maijidda?, Allah sarki duniya, Allah yasa suma sun shiryu
iyayensu suma su gane kamar yadda iyayenmu
suka gane, nan da nan kuma lahira ta fado min,
tunanin yanzu ya Karima take a lahira?, Duk da
cewa ko yaya aikinta mai kyau yake, to itafa
89-
Karima mun sani duk cikin abubuwan da aikata
babu mai kyau, an kuma ce idan kuma har ka
mutu to babu zance tuba, to yanzu kenan Karima
tana can tana faman shan azabar kabari?. Ban san
lokacin da kuka ya kamani ba na ringa rokon
Allah da ya gafartawa Karima laifinta wanda ta
sani da wanda bata sani ba, inda ma naji zuciyata
ta dan yi sanyindan aka ce Allah ba ya kama
mutum da bai sani ba, Allah ya sani rabin laifin da
Karima ta aikata bata sani ba, Allah mun gode
maka da ka shiryemu, Allah ka shirya 'yan bayan,
idanuna sun yi hulu-hulu saboda kukan dana yi da
na tuna da Karima.
Na shiga gaishe da Inna take gaya min
gobe idan Allah ya kaimu za su je gidan renon
yara ita da Baba don neman inda yarinyar Karima
take kamar ta san yau nima da Karimar na tashi
nace "Inna inaga kamata yayi kiba Baba shawara
duk karshen wata ya dinga sawa ana mata saukar
Qur'ani don neman sauki akan zunubanta ko?"
Tace "haka ne" bayan wannan ne ma yasa ake
karanta mata hailala dubu saba'in duk karshen
wata, saboda zunubinsa shima, Allah ya jikanta,
amin.
Dama ina son in tambaye ki, ya aminu bai
ce komai ba?" "Shima ya ce shi a shirye yake, sai
dai ni Inna ina neman alfarma kinga yau saura
kwana biyar kuma ni babu abinda na shirya tun da
kinga su babu shirin da basu yiba, don haka inga a
-90-
yi nasu ni nawa ko nan da sati daya ne a yi tunda
dai ba wani biki zan yi ba ko Hajjiya da Mairo ma
sun isa su rakani" "amma babanku yace yana son
ya hada daurin auren gaba daya" "to ba damuwa
zan fadawa Aminu ina yazo, Inna kisan gobe
Bilkisu za ta zo ta yi miki sallama, ko bata samu
zuwa ba ina son naje."
Kafin ace na mayar da hankali na ci
abincin safe har Bilkisu ta zo ita da Abdul, wai yau
tana da abubuwa dawa, Inna da Baba sun yi musu
addu'ar Allah ya kaisu lafia, nace "bari nayi
flashing din Aminu ya zo ku yi sallama" Bilkisu
tace "haba flashing ai harkar talauci ce, bari ai
kiransa sosai ya zo", da wayar Bilkisu muka
kirasa yace daman yana kan hanya, muka fito
falon Isa gaba daya saboda abdul yana can, ba a yi
minti arba'in ba ya karaso, an zauna ana
barkwanci, muna musu tsiyar kar su je su manta
da mu, suma suna mana tsiyar kar mu tashi biki
muki nenamsu. Aminu ya dauko wani abu a kwali
ya bawa Bilkisu ya ce "kin san mu