nunamin ababuwa
komai ya gane insha Allah aikin sati nan zai turo
mutanen gidan su, hakan kuwa akayi kwana uku da
magana Bello yaturo mutanen Hadeja akasa ranar
aure wata biyu. To fa hankalin kande ya tashi don
kullum kwanta da tashinta mai zatayiwa Maryam
wanda zata bata wannan aure da farko ta sata daukar
tafashahsen ruwan zafi a katon bokiti taje da ruwa
34
akanta ya zubo mata duk ta kone jikinta har kanta
yarinyar ta kwanta jinya ni da kaina bansan halin da
take ciki ba sati wajen biyu tana kwance babu abinda
take ko ina jikinta ya kwale banda fuskarta amma har
kanta duk da haka kande bata kyaleta ba tana cikin
jinyar taje ta cire mata wanda ta dauki kandir wanda
ake kunwa ta caka mata a matuncinta kamar yarda ta
saba caka mata danyatsa yanzu kuma kandir kaji
rashin imani irin na wasu jahilai don kuwa wannan
jahilci ne tsanatsa duk wanda yake da ilimin bazai
taba yiwa dan uwansa musulmi wannan izayar ba.
Kafin kace wannan, jini da mugunyar kuna
yana ta fita ajikin wannan baiwar Allah nunfashin ta
yana neman daukewa annan ne kande ta tsorata tasa
magajiya taje tayi kiran, tare muka taho da magajiya
kanin dake yana gida kafin mu karasa Maryam tuni ta
suma na rasa inda zana fiskanci ciwon ne farko dai ga
kuana duk ajiki to kuma wannan jinin na mai yake
kwarara haka? na tambayi kande wai itama haka ta
gani kwai yana fitowa shi yasa tace a kirawo ni
nasake tambayar ta dama ta kune tace wai da ruwan
zafi ta dafa zatayi wanka, naga dai duk zan batawa
kaina lokaci idan na tsaya ina saura rana karyar kande
nace da kanina ya shigo mu kamata muka kaita
babban Asibiti na nan aikin cikin garin babura nan da
nan aka bamu gado dakin da aka barmu mu kadai ne,
aka samata ruwa, suka sako kayan aikin su suka guge
wurin kunar suka satsaka magani tare da allurai.
Muna zaune da yarinya har magariba tun safe amma
bata farfaduba akwai wata ya rinyar kirki acikin yan
aikin zalamatu nace don Allah ta kirawo mini likita a
35
duba idan babu rai kamata yayi a abinne ta muyi ta
zama da gawa agaba, yazo yayi aune - aune sa yace
tana da sauran rai yanzun hakama tana jin duk abinda
ake cewa tana ji kawai magana ce bazata iyayi ba
saboda azabar ciwo saboda ta wahala sosai ana
magana sai ga Bello yazo yake gayamin wai murtala
ne yake gaya masa bata da lafiya shin kullun idan
yaje sai ace masatayi lafiya babu wanda ya taba gaya
amsa bata da lafiya, yake tambayar baba mai ya same
ta ance Bello banda wannan kuanar babu abin da zan
dara sai dai ina Allah yasa ta tashi ta fada mana
abinda yafaru. ya dafa kafadar likita yace likita kana
ganin zata tashi likita ya kalleshi. Ido yayi yajir yace
insha Allah ka kasa nace namiji karka karyawa
tsohuwa raia nia kwa Amina zuciyata ta bushe ko ka
dan banajin kuka araina tuni ma nasawa raina
Maryam ta mutu kawai dai muna zauna ne daga
wane. Don dai anki yarda ne kwai da salla insha'I
kenan ina jan carbaha nabar Bello nan zaune yana
kallonta sai naji yace Baba tana motsi kafin nada ko
kaina Maryam ta bude idon ta wanda yayi jajir ta
kalleni tace Baba mairo ki yafe min Inna kande tana
son ta kashi ni kinga abinda tayi mini bazan iya zama
ba ta kwaramin ruwan zafi yau sati biyu ko zama
banayi barai komai babuya wanda yabani magani
gashi kuma yanzu abinda ta saka mini sai ta kalli
Bello ta fashe da kuka shima Bello kukan yake ni
kuwa ido nane yayi jajir na kasa kukan, Bello ne
yakatse mana yace Maryam tashi yanzo ki sha koda
madarar nan nace wallahi bazan iya tashi ba
yakalleni yace baba mutasheta nayunkura
36
zan dagata
daga yadda bayanta ya manne kana ganni naman
jikinta gashi ta kasa hada kafafunta sai bude su takeyi
kasan cewar banason Bello ya gane domin a tunani
na ko kande wani katon ta dauko yazo ya burmata
da karfi dayaji don haka nace Bello mukeleta tunda
naman jikinta ta zalla ana ganin sa duk da maganin
da aka samata anan asibiti nai kukarin dagu kanta a
filo ahaka na danga bata madara da Bello yakáwo
mata har tace ta kushi na mayanta na kwantar.
Na tashi na fita na basu wuri Bello ne ma ice
mata Maryam kiyi hakuri ina tare da duk wahala
sanan duk wannan abubuwan yana samun kine
saboda ni Insha Allah idan munyi aure sai munzama
a abin su ga kowa kuma insha Allahu gobe zanje
kano zanyi magana da likita na, idan yace a kawoki
inyaso zan kai ki can Asibitinsa ya kalleta cikin
tausayi da kuncin zuciya in kana son bu kagan sa a
wani hali kiyi hakuri samu sauki don haka gobe
bazan zoba sai da yamma saboda zuwa kanon
gawannan kudin ko zasu ne mi wani abu Allah ya
baki lafiya ina dada fada miki ina tare dake duk halin
da kika ciki sai na dawo to bayan fitar Bello ne
Maryam take bani labarin abinda kande taimata da
kendir nadagata naga yadda baganta ya rure yayi
zajur har yanzu kuma bai dai na zubar da jinni ba
hankalina ya tashi sosai cikin sauri naje na kirawo
likita na nuna masa halin da take ciki nan da nan yasa
wata safar hannun sa yasaka hannunsa a matancinta
Maryam don zafi takasa buda bakinta sai hawaye
take zubarwa don azaba anan likita yaga shi
kendorden ya karye aciki ya janyoshi bansan lokacin
37
dana fashi da kuka da karfi kukan danake hankalin
likita ya tashi sosai yace Baba kiye hakuri zata samu
sauki akwai allurai da zamu yi.
Washi gari da safe Murtala yazo harda kayan
shayinsa bayan mun gaisa ya tambaye ni yaya mai
jiki lokacin Maryam tana ta sharar baccinta takaici
bai barni na bashi amsa ba nakalle shi kallon, banza
murtala ka cuceni akaci amanita wannan yarinyar
daka ke wulakantawa idon Allah ya tashi kamaka
mahaukacin kasuwa ma sai yafi ka daraja, tana
zamanta a gurina kazu ka karbeta kaje ka kunata kana
kwance a gida har sati biyu amma bakazu kace dani
komai ba ba ka kuma nemomata magani ka bata ba.
To yanzu komai ya kare Maryam tabar gidan
ka har abada kande ta satai duk kutun da ta dace ba
zata koma dagi don kada zama ba tana neman kasheta
kanji kana gani don ita takawo rashin imani duniya
shine ta dauki kendir ta sokawa wannan yarinyar a
matuncinta tana neman kasheta har lahira, to zamanta
a agiadanaka yakare sai dai taje da yawo yayi kasake
da kai yace babu damuwa Baba Allah yaba ta lafiya.
Washe gari har yamma sai wajen magriba Bello ya
dawo daga kano kamar yadda ya gaya mana zai
gayawa abokinsa a kano, to haka akayi don abokin
yace lalle a hanzarta kai Maryam ya ganta gari na
wayewa Bello ya kawo mota, muka kama hanyar sai
kano. Aminu Kano gurin abokinsa Dr Nasser inda
suka bamu daki mu kadai dagani sai ita.
Bello ya biya kudin komai da komai nan da nan ka
fara fesa mata maganin nika jikinta allurai kuwa a
kan lokaci badon kar nayi karyaba sai nace ammata ta
38
fi hamsin Allah cikin ikon sa kwana uku yarinya ta
sami sauk: so sai har tana zama, tana kuma cin abinci
sosai muna da kwana hudu ne maurtala ya zo duba
mu yace Bello ne yagaya masu tun randa muka tahu,
yanzu kusan nace komai yayi dai – dai a Maryam
banda tafiya bata iya tafiya nayi - nayi da ita sai tace
ba zata iyaba wai gabanta yana mata ciwo tana najin
kamar zai fado idan ta tashi zata taka. To anan na fara
fahimtar lahanin da kande tayi matane don haka nayi
amfani da basirar mu ta mata nan da na ringa gasata a
cikin rowan zafi sau uku arana kamar yadda a kewa
mai sabuwar haihuwa cikin ikonAllah Maryam fita
da ita filin Asibitin mu zaga ya, wani lokacin ma
Bello ke dauketa yazagaya da ita, a haka said a muka
shafe wata biyu cif a Asibitin Aminu Kano.
BAYAN MUN DAWO GIDA
Da sati daya Bello yazo yasameni yace baba
ina son nan da sati biyu zan aiko komai. asa Bikinmu
amma banason asa da yawa inason kamar sati uku
idan ta kayan da za'a kaiwa Maryam ne zan saka
mata komai agidan ta don inason na waresu banason
hadasu saboda banason fitina inma zan hadasu sai in
sun saba, duk wannan maganan da yakeyi ni dai nayi
zugun na zuba mai ido ina kallonsa a raina inata sake
- sake anya inyaji abinda ya samu Maryam zai yadda
ya aureta kuwa? amma bania dai inji ta bakin shi
tunda dule in gaya masa abinda ake ciki aure yawuce
wasa.
Na numfasa nace dannan dama akwai wata magana
inaso ingaya maka (akan wannan yarinyar) watau
wannan konewan da tayi banda ita akwai wani ciwo
39
daban da na rula ban gaya maka ba, ya dago kanshi
da sauri yace wace magana ce Baba?. Na numfasa,
kamar ka na fada to amma na riga na fara zancen
kawai sai naci gaba, ai Bello ita, wannan mata da
kake gani kande. .nan na kwashe labari
irin mugun abinda tayiwa Maryam, kafin in kai
karshen labarin bawanAllah sai naji kamar yana
sheshekan kuka, naja dogon numfashi nasa gefen
zanina na goge kwalla da suka tara mua idona nace
sai fa hakuri. Bello.
Ya dago kanshi yace mun Baba idan ahar a
duniya tayi haka don ta rabani da Maryam ne tayi a
banza don bazan taba daina sonta a raina ba, ita kuma
muguntar ta Allah ya mayar mata kayanta Inna
shiriyane kumaAllah ya shiryeta. nadago kaina nace
amen bawan Allah, Allah yayi maka Albarka.
Bana wata gudu da maganar mu da Bello
akayia biki Maryam da Bell wanda kowa yayi
sha'awar Bikin banda makiyarta, kande da murtala
babu abinda ya fita na gudunmuwa saboda tsoron
kande sai kudin sadakinta atana daya rinke wanda
ranar daurin auren Maryam wanda baisan abinda ake
bama ya sani saboda har ana daura auren akan sadaki
dubu goma Murtala da kani na su suka fara shi ga
aikin gida su Maryam budar bakin kande malam
nawa ne sadakin yace dubu goma da saurin ta sai
catayi koma kace sai dubu ashrin ya juya da sauri sai
kace wani karamin yaro wai zaice a dawo ya fasa ya
mayar dubụ Ashirin nan da nan akanina ya zuciya
yace baza'a karaba abinda kiyi niyyar bata koa fasa
mu Allah zai huremana yadda zamuyi to abinka da
40
sai wanda sai yadda akayi da shi haka mukayi iya
kokarinmu duk na sayar da kiwona muakai mata kaya
duk da Bello yace kar aje da akomai amma said a
aka samu wani ta wajen dangin ubanta, wani kaninsa
mai zuciya, kuma babban ma'aikacin gwannati yace
in hara aka kaita ahaka ai sai a sai amata agori koa
mun mance tanadaa akishiys ne? shine ya sanya mata
duk wani abu da za'a gain adakian kowace ayargata.
Nidai da naje naga dakin Maryam naga irin dukiyar
ada aka shirya mata sai danayi kuka na kuama ce
Allahamdulillahi.
Zaman Maryam da Bello zamne mai tsafra
wanda duk wanda yagani zai yaba tunda Maryam
tana masa biayayya dai - dai gwargwado, Maryama
ta samu tarbiyya maia kyau a wurina tunda bana
sakara mata hasalima bana mata wasa irin na jika da
kaka, ata wajen kande kuwa zan iya ce ta samu
tarbiyar aiki tukuru da rashin son jiki, koa karkani
bata dauki aikace aikacen cikin gidanta bakiana
komai ba.
Shi kuwa Bello, sai son barka tunda bai rageta da
komaiba najin dadin rayuwar duniya, yana tattalinta
ya kuma saketa a islamiyya anan unguwar tasu, gidan
Maryam can dutse jihar Jigawa yake ita kuma
kishiyar Maryam tana Hadeja garinsu Bello, saboda
Bello ya koma can dutse da aiki yabar Babura.
BAYAN WATA TAKWAS DA BIKI
A lokacin Maryam nada ciki wata bakwai ciki
mai laulayi mai wahalarwa da gasken gaske ganin
haka Bello yazo ya dauki ni kullum Maryam cikin
wahala take tayi baki ta rame batacin komai sai
41
madarar ruwa irin ta bature shima sai nam a mata
take sha cikin na da wata takwas ne ciwo yayi ciwo
bata ko zama batayin komai sai na mata, kofi,tsari
zatayi sai na kaita. Bello ya matsu tuntuni muje
asibiti nace naga asibiti bashi da amfani tunda anje -
anje babu sauki to amma duk da haka Bello sai da
yarinja yeni mukaje asibiti a daren wata Alhamis da
ciwon yayi tsanani cikin yarina yin sama yana turowa
mata kirjinta idon ta duk ya kafe ni dai salati da kuka
duk nake hadawa saboda na tuna yadda mahaifiyata
tatafi muna zuwa asibitin babban asibiti ne a dutsen
suka turata a wani gado suka shiga da ita wani daki
shikenan Maryam ni dai a wannan daki suka ye tsoke
sokensu wannan ya wuce da farar riga wannan yasa
safa a hannua duk ina kallonsa suna hada baki sona ta
turanci sai dai wannan ya leko yace sannu Hajiya tun
inajin Maryam har na dai na ji, muna zaune munyi
zugum ni da Bello wata tazo tayi masa turanci ya
tashi da sauri ya shiga dakin da aka kai Maryam ashe
Maryam rai yayi halinsa. Allah yaji kanta yakauta
zuwan mairo na kano dana share hawaye. Amina
nace mai cewa ina labarin kande mairo aka ninfasa
kande kowa itace mai labari don Lami ta haife musu
da namiji ta gudu tabar musu ita kuma ta zama
kasuwar gida kinga alhaki kwukkwuyo ana cewa
Maryam yar iska anga iskanci ita kanta kande hakkin
bai barta haka ba tunda ta zama abin kyama ga kowa
tunda wasu kuraje ne suke fito mata sai suyi ruwa
banda doyi babu abianda take don wani zuwa da
muka yi bayan mutuwar Maryam gidana kansa ya
cenfa tunda shi murtala sakamakon kulawa da
42
yasamu daga Bello tacan yin gurin aiki tasa ya sake
aure ya kama wani gidan don haka yanzu sai yaga
dama zai kalli gidan da kande take.
kullum makota cikin rabon fada ita da magajiya babu
wanda zaki tausayawa shin yaron da lami ta bari
saboda baya samun kulawa ko kadan ita kakar wato
kande kenan tana fama da kuraje yadda kuma ta
mugunawa "yan uwanta babu wanda yake zuwa inda
take tunda dama abinmda yake kawo su sabodaa
murtala yana musu to itama ya barta, shi kansa
murtala duk da cewa asiri kanade tayi masa akan
Maryam din daban rokar masa Maryam ta yafe masa
ba, da ya shiga wani hali.
Shi kuwa kanina shine ya sami cigaban aiki ya dawao
nan ita kuwa matar gidan nan Hajiya Rahma ita
kawai matar kanin nawane Nafisa don haka da tace
tana son wadda zasu zauna tare na amince don kawai
na ringa motsa jikina tunda ita amatar ganina nawa
bata barina nayia komai akinji dalilina na zuwa nan
gidan Bello kuwa har yanzu yana zuwa gurinmu don
yaso naci gaba da zama dashi nice taki tunda dai
wanda ta hada ta mutu. yanzu haka mun kaia shekara
rabonmu da Babura don haka bazan iya ce miki ko
kande ta mutu ko tana da rai murtala yakan zo
mugaisa amma ban taba tambayarsa kande ba saboda
bana son komai sunan tan a karaji balan tana ita.
Don haka Amina a duniya kayi gaski karka
dauki wani ba naka bane inhar kana da tunani shine
naka don sai kaga baka mori naka ba kamori nawani
wallahi mata mu kulla don irin wannan kuskuren
daga gurinmu yake tasowa idan kin to zarta danwani
43
kin wulakanta shi to kanki kikewa kunga da kande
don sharrin son taga Maryam taje iskanci babu irin
azabar da bata mata don kawai taje ta nemi maza ace
yar iskace daya keAllah ba ruwansa kinga duk da irin
gatan da takewa "ya"yenta sai mugun nufin da tajefi
Maryam ya koma kan "ya'yanta alkairin da ta nufi
'ya'yanta ya koma kan Maryam da tayi gaskiya tad a
duk haka bata faruba don haka mata mukiyaye mu
saniAllah baya barci.
Yana jinmu yana ganin yana kallonmu duk
inda rauke karmu yarda duniya ta rudemu ta kaimu ta
baromu don komai kika samu ko kike dashi anan zaki
barshi babu inda zaki dashi daga ke sai likafaninki
zaki yan uwa ayi tunani a kiyaye. Gaskiya Mairo labarin Maryam labarine da yake da
abin tausayi, amma duk da haka zan iyace miki
labarin yafi na Maryam ban tausayi, al'ajabi,
mamaki don ni duk wanda yaji labarina zaiso ya
ganni ido da ido.
Nikuwa badan babu kyau bincike bad a zance
zanso nasan labarin ki don inaga ci yan dubarun mu
na tsofaffi ba za'a rasa shawarar dazan baki ko kuwa?
ina fatan ba zakiyi tunanin idan nasan sirinki ko zan
yi miki wani abu kamar juya baya ko tona asiri in
zaki duba ki gani ina da hankali, sannan yarda ita
take kawo komai don kuwa yarda dake da nayi ita
tasa na kwashe labarInna nida jinina wato Maryam na
baki. Haba Mairo duk wadan nan tunanin ma bai
kamata kiyi ba domin kuwa idan har banyi niyar baki
labarin ba da bazan fara furta miki ina da wani siri a
zuciyata, don haka mairo zan baki labarin zuciya
44
daya babu komai araina dake sai dai inason ki bari sai
jibi don kinga yanzu dare yayi tunda ana kiran sallar naje gidan kanwata Bilkisu saboda inason tasan nan
gidan don tunda ta dawo nan bata zo nan ba saboda
rashin sanin gidan inaga kuma zankai yamma don
haka labarin sai jibi idan Allah ya kaimu.
To Amina ta Allah ya gwada mana ganin jibin Mairo
ta fada cikin sanyin murya da gani kasan badan taso
ba dadin manya kenan duk yanda kake dasu sun ya
danne damuwarsu komin dacinta hakan Amina kota
kula ta tashi na nufi bandaki don daura alwala
magariba.
Washe gari Amina na tashi wajan tara bayan
tayi sallar Asuba ta koma sai karfe tara ta tashi ta
share dakin da take kwance ta gyara katifara data
atashi a akanta ta wauce bandaki tayi wanka tazo ta
cada kwalliya da wata atamfa jah sabuwar fitowa mai
suna three elephant tayi kyau ta kara tunda daman
duk wanda yaga Amina yasan kyaukyawa ce don
haka yau ta kara akan nada ta wuce kichin ta dako
dumamen tuwo wanda yasha man shanu da yajin
daddawa ga kuma rowan shayi bunu daman can
Amina tun tana karama ba sem da safe taci komai
inba tuwo ba don ita batason wani dankali ballai
kwai. In babu sauran tuwo ne take siyar masa gurin
wata mata ya Bauchi.
Amina ta zauna cikin nutsuwa ta gama cin
abinci ta mayar kwanan kichin ta wuce dakin Anty
Ramatu ta sameta a falonta suka gaisa. Anty cikin
fara'a ta kalli Amina gaskiya kinyi kyau sosai fita
zakiyi ko kokuwa sirikin namune zaizo. Amina cikin
45
jin kunya ta rufe idonta haba Anty sai zanko
zanyi bako zanyi kwalliya zanje gurin Bulkisu ne
kinsan an kusa bikinta kuma haryau bata san nan
gidan ba, ah ya kamata ki akaita nima fitar zanyi
zanje har wuse II hanyarmu daya? Amina cikin
dariyar farin ciki tace wallahi Anty harnaji dadi don
banason zuwa gidan su Bilkisu a Taxi don tafiya
lungu cikin maitamane, Anty ne maia cewa babu
komai bari na doko jakata, itama Aminar cikin sauri
ta shiga daki ta dako Jakarta da takalminta bakake da
mayafinta jah kalar atamfata.
Ta leka inada mairo take wanke - wanke tayi
sallama suka fita, suna tafiya Amina nayiwa Anty
nuni da hannu har zuwa kwanar gidan su Bilkisu ana
zuwa bakin gate Amina tace to Anty koma daga nana
ga gidan nan sukayi sallama da nufin inta gama hirar
ta zata koma da kanta basai ta biyu mata ba.
Amina na shioga get din gidana su Bilkisu tun a
bakin masallaci taci karo da mutumin nata Hassan ya
tabbatar mata da kawar tata tana nan kafin ta karasa
ya rigata dan ta tsaya anan kasa tana gaishe da Hajiya
Innar su Bilkisu bata bar falon Hajiya Bilkisu suka
zo ita da malam Hassan nan da anan kawayen suka
rungume juna don murna Hajiya hafsatu ta tsaya tana
murmushi na ganin kawayen yadda suke son junansu
nan dai suka hau saman Bilkisu, suna shiga suka taba
hannu Bilkisu ce mai tambayar Amina ya Anty aid a
gain nasan tana kular mini da ke yadda ya kamata
kinga kika zama wata katuwa Bilkisu har yanzu dai
kina nan da zolayar ki ke kuma fa itama Amina ta
rama nan dai suka ringa yiwa juna tsiya kande mai
46
aíki gidana su Bilkisu ta shigo da kayan abinsha kaka
- kala dana tandar baki irin dai na masu hannu da
shuni.
Haka kawayen suka wuni hira lokacin sallah
yayi sukayi masallacin gidan sukayi sallah suka wuce
kan table nacin abinci nan ma suka ci suka kuma dasa
wata hirar sai wajan biyar sannan Amina ta yunkura
tace zata tafi, shine Bilkisu da yanzo mota ita da
Hassan suka tafi kaita gida lugue, unguwar dana
koma kenan da zama yanzu gidan aAnty Ramatu.
Muna zuwa na tarar da mairo ita kadai a tsakar gida
tasa kujera 'yar tsygune tana ta sakatar hakorinta ita
kuma Anty tana falonta tana kalon wani sabon wasan
Hausa sansani, mairo da saurinta ta taremu duk da
bata taba ganin Bilkisu ba abinda tayi mata a rannan
naji dadi sosai tunda ta nuna kamar da dade da
saninta har ita kanta Bilkisu yadda ta amsa taryar
mairon naji dadi sosai.
bayan sun gaisane muka wuce fakon Anty ni kuma na
wuce kichin na dako mana ruwa sha da kunun aya,
muka zauna muna tay Anty kallon film din yadda
Aunty take jan bilkisu da hira yayimin dadi sosai, ko
da yake dai daman banyi zatron komai daga Anty ko
kare na kawo gidan inaga zata karramashi a yarda
nake gani muna cikin hirarmu akayi kiran sallar shine
muka tashi muka yo alwala nayi mana shinfidar abin
sallah a dakina don a lokacin mairo harta idar da
sallah tana lazumi.
Ina idar da sallah naga wata katuwar jaka na ke
tambayar mairo ko munyi bakune shine take gayamin
Maryam ce kanwar Hajiya da kawarta suka zo amma
47
sunje cikin gari su dawo ta kaici yas. kasa
daurewa said a na nuna bacin raina a fili don kuwa
zuwan Maryam gidan nana yana dagamin hankali ita
da kanta mairon ta gane banji ba dadin zuwan
Maryama din don haka tace wania abine na dana saki
raina nace babu komai.
Bilkisu tana idar da sallah tace zata tafi gidan don
bata tukin dare daddy ya hanata nayi - nayi dasuma
su tsaya suci abinci sunce a'a na kaita sukayi sallama
da Anty muna zuwa bakin mota Bilkisu tace Amina
naga zuwan zakin anan ya tayar miki da hankali ko?
akwai wani abune idan har kina ganin akwai wata
fitina mu koma gidanmu da zama in yaso idan kuka
tafi kya dawo a'a babu komai, ke dai Amina kina
sonki rinka boyemin damuwar ki meyasa wallahi ba
haka bane Bilkisu kina daya daga cikin mutanen dana
yarda dasu haka kullum kike cewa Amina Allah yasa
har ranki da gaskene to shike nan zan tabbatar miki
insha Allahu acikin satin nan.
Bilkisu tasa hannu a cikin mota ta mukowa
Amina leda cike da kaya atace gashi inji Hajiya
wannan kuma Handset ne nina hada miki saboda
inason mu ringa magana numbarki 08034477288
insha Allah zanzo jibi in duba lafiyar ki zanzo miki
damai gidana tunda ke kinki aure ta shige mota tana
dariya na bita da godiya nace a araina Bilkisu sarkin
zolaya
Na shiga gida da farin cikin kyautar da akayi
mini da akin cikin zuwa Samira don kuwa nasan irin
masifar da take hadamin don nasa komai Allah zai
shige mini gaba.
48
Ina shiga daki na saura sallar insha'I don na tarar
mairon ma sallah take bayan na idar ne na bude ledar
da Bilkisu ta bari naga ashema yikan shafawane da
turaruka na jikia dana hamata nayi farin cikin kyautar
Hajiya Hafsatu korai don duk abubuwab banita bani
shine lokacin danake bukatarsa.
Har muka ci abinci muka gama hirar mu
muka kwanta nida mairo su samara basu dawo ba sai
can wajen karfe sha biyu harda rabi naji su suna buga
gida shine mairo taje ta bude musu suna shiga kasan
a buge suke sunsha giyarsu sun koshi suna zuwa
samira tazo bayan ta kwanta harda cewa wannan
shegiyar maiyar haryanzu tana gidan nan ashe itama
kawar tata haka ta sharbu a kasa mairo dai sai kallon
ikon Allah kawai take tunda ita agurinta sabon a
bune. Dana lura barci irin na mashaya ya kwashesu
Maryam sai na tashi cak na koma dakin su.... tunda
daman basa nan sunje hutu gurin dangin babansu.
Tun asuba natashi nayi wanka na shirya don nariga
ba yanke zan koma Nyanya da zama har sai sunbar
garin zan dawo kafin ma su tashi naje na dumama
tuwo na dauki karamar aakata na zuba kaya na kala
uku da kayan shafe - shafe suma nadau wanda zanyi
amfani dasu na sanar da mairo inason zanje Nyanya
amma bazan dade ba zan dawo ko kadan mairo ba
taji dadin tafiya ta ba, na leka nace da Anty an aiko
nazone ana nemana da sauri na nuna mata wayata na
sanar da ita number na wuce sai Nyanya.
Ina zuwa nayima Bulkisu waya na sanar da ita
idan dan ana nema na ina Nyanya kwanana biyar
acan sannan na dawo 'don nasan iskacin Maryam ta
49
taji ina zuwa na tarar ta wuce amma tabar min sako
don kuwa ta kwashe mini kayan manshafawa da
Bilkisu ta kawo mini ta bude jakata ta dauki duk wani
kayan sawata sabo ta kalma na bata bar su ba,yaba
suma ta dauki wanda taga yayi mata, jakatama ta
ratayawa guda biyu ta dauka ko miye dalilinta
nayimin haka?
Na duba gurin kayan mairo ban ga komai ba jikina ya
bani lallai mairo ta kula Maryam akan daukar mini
kaya harta bar gidan ai kowa yau komin dare zanje na
nemo mairo na wuce falon Anty na tarar tana cikin
daki nayi sallama ta amsa tacce na shigo ko gaisuwar
kirki ban mata ba nace ina mairo shine take gayamin
wai tun jiya da safe lokacin su Maryam zasu tafi ita
dai batasan taka maimakon abinda ya hadasu ba taji dai samira tana ta zagin mairo.
To kinsan nima ban karfin abinda yafi haka
ba agurin Samira don haka naba mairo hakuri nace ta
kyaleta ita kuwa samira sai kara zaginta take don
haka na komo dakina na zauna bacin sun tafine na
duba na tarar mairon ma tabar gidan don haka yanzu
tunda kinzo ina ga yakamata muje gidan su mairo mu
bata hakuri don nasan zatace na koma daki na kiwa
samira magana kema kuma kinsan nima banfi karfin
hakan ba.
Amina da Antyinta suka dunguma gidan su mairo
suna