kwari wato har da gupu
ko? Muneeba ta yi murmushi ta dan matsa daf da
140
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
shi tace, "Sannu da dawowa ya Ofis", ya amsa a
dakile "lafiya Lau" tasan ba wata hira da zata biyo
bayan hakan sai ta juya zata bar dakin sai ta ji ya ce
'Ina son daga yau ki ringa yin girki, don Suwaiba
ba zata iya ba kin dai san cikinta ya tsufa muna sa
ran haihuwarta ko yanzu ko anjima.
Ta juyo tana dubansa cike da bayyanuwar
mamaki a fuskanta ta ce "Amma a gabanka fa nace
ta hakura da yin girki zan dinga yi har Allah ya
sauke ta lafiya" tace in barshi zata cigaba da yin
abinta, ni to meye laifina ko kuma ta dauka girki da
mijin zan amsa gaba daya? Wallahi ni ba nufina
kenan ba, ko yanzu zanyi girki kaci gaba da kwana
a'dakinta ni bani da matsala.
Ta juya za ta fita ya sake magana, ki`je ki
sama muku abin da za ku ci don bata girka komai
ba bata jin dadi, ta ce "Allah ya sawwake żo mu je
Baffa" Ta kamo hannun yaron uban ya dubeta a
kaikace ya ce, barshi ki je ki yi aikinki tunda
namanshi za gutsura idan kin barshi ta dubeshi cike
da tuhumar kalamansa suna hada ido yayi saurin
dauke kansa itama sai ta dauke nata kan tare da
adiye kalaman da ta so furzarwa, taja jiki ta bar
masa dakinsa.
Tun daga ranar ita ke yin girki da hidimar
komai na gidan, amma maganar rujia kwana
dakinta kota kwana dakinsa duk bata danan sai
Suwaiba.
143
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Wannan karonma aiki akayi wa Suwaiba
data tashi haihuwa ta haifi diyarta mace mai
tsananin kama da ita, haihuwar an kashe kudi sosai
a asibiti saboda matsala da akayi ta samu da
Suwaiban taki natsuwa dinkin ya warke shi yasa
sau biyu yana budewa ana sake dinkewa saida tayi
kusan sati uku sannan aka sallameta a lokacin
Hajiyarta na Dukku bata da lafiya shi yasa Goggo
ceta karasa zama da ita a asibitin har aka sallamesu
suka dawo gida.
Shirye-shiryen suna Suwaiba ke tayi, hakan
ya tunzura zuciyar Goggo har ta 6ara tayi
maganawa Suwaiban 'Haba Suwaiba wane kuma
taron suna za'ayi ai kyaji tausayin mijinki irin
wadannan makudan kudi daya kashe a asibiti
sannan yanzu a sake kashe wasu a taron da bai
zama dole ba haba a dinga yin abu da tunani ana
tausayawa abokin zama".
Wannan kalamai sun kular da zuciyar
Suwaiba wato ita ga me da bata son ya kashe
kudinsa to wallahi bata isa ba kudin sai ya kashesu,
ko tana so ko bata so. Ba ta dubi ko inda Goggon
take ba tayi maganganun son ranta, "Tabdi kada ayi
taron suna, ai wallahi sai anyi tunda shi mai kashe
kudin baıyi kukan bashi da kudi ba, haka kurun sai
a ari bakinsa aci masa albasa, sai a bari yazo aga
maganar wanda zaiji" Goggo ta sake tunzura dama
ta 'ura da take taken Suwaiban kiris ya rage wata
144
Π
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ran ta lakucewa Goggon hanci tunda ta riga ta sami miji a hannunta, to bata isa ba za ta yi maganin
rashin kunyarta.
Ta ce, Lallai Suwaiba wuyanki ya isa yanka,
tunda kika iya zakalkalewa kina min rashin kunya
son ranki, uwarki ma Hajiya Harira za ki iya mata
tunda mun bi dare munbi rana mun samo miki
'yanci a gurin miji wato za ki juya shi nima ki
juyani to baki isa ba ni na haifi abina, na raini abina
na sha wahalar da gwagwarmaya har sai da naga
rayuwarsa ta inganta to ba kuwa zai yiwu rana tsaka
ace za'a wahalar min da shi ba don an ga yana da
abin hannunsa suna ne wallahi in ban amince ba ba
za a yi shi ba gara ma abini a sannu”.
Suwaiba bata sake tankawa Goggo ba amma
sai kunkuni take yi tana fadan bakaken kalamai
wanda wasu ma Goggon na ji amma ganin
Munceba ta shigo dakin ne ya hana Goggo tankawa
itama Suwaiban ta rage kunkunin da take yi amma
da kallon fuskantar ka san an ta6o ta.
Ruwan wan kan jaririyar ne Muneeban ta
shigo da shi, ta dau co bahonta ta juye shi sannan ta
dubi Goggon ta ce "Goggo kawo ta inyi mata
wankan yau in hutassheki" ta wani dubeta cike da
mamaki tace "Kiyi mata fa wankan kika ce? To ni
dai ban ta6a ganin wanda bata haihu ba ta yi wa
Jariri wanka ba, ki bari idan ki ka haihu "sai kiyi
abinki ba mai hanaki amma ki daina wannan
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zana
karanbanin akau jaririn wasu gara kiyi a naki in kin
samu.
Maganar Goggo ta Kona ran Munceba
amma sai bata nuna ba tace "Gani nayi Baffa ma
tun yana jariri nake masa shi yasa" ta cc, "Shi
dinma ai saida yayi Rwari kike masa kuma lokacin
na kom Dukku, wannan ma sai ki bari sai na koma
ba za'a yi a gabana ba".
Da Mujeeb ya dawo Suwaiba tayi sauri ta
tareshi a dakinsa da maganar yin taron suna, ta
lallaße shi har ta amshi kudaden da zata yi sayayya
ta dawo dakinta ta zura idanu don ganin yadda
zasuyi da Goggo, tunda sun riga sun gama shirya
komai.
Tana cikin dakin baccinta taji shigowarsa
faionta inda Goggo take. Tzna jin hirarrakinsu har
Goggon ta sako maganar suna ta nuna masa kada
ayi taron suna don zai wahalar da kansa ne, banda
wahalar kashe irdin asibiti da akayi ta yi ta kara da
cewa, Haka yınyar nan ta zakalkale tana min
fitsara don kawai nace a hakura da suna tunda ba
dole bane, kuďi kam ai an kashc su a asibiti tunda
ba hakosu ake a rami ba, su 'ya'yan yanzu sam
basuda tausayi su dai a kashe m1 kudi turda basu
zan zafin nemo su ba to baza a taro ba tunda ba
b huwar fari bune, a na Baffa ai anyi" ta kare
maganar cikin bashi umurmi.
L
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ya fanyi shiru, itama Suwaiba a daki shiru
tayi ta natsu sosai don jin amsar da zai ba Goggo ta
amincewa da umurninta ne ko akasin hakan, duk da
tana da tabbacin ba zai taba ketare maganar da suka
riga suka yi su ka gama ba har sun kai matsaya bata
ankara ba sai ji tayi yana cewa Goggon 'Ina ganin
Goggo hakuri zakiyi suyi taron sunan tunda ta
kwallafa ranta tana son tayi maganar kudi ki daina
damuwa bani da matsalar kudı sai muyi fatan ayi
taroň lafiya a gama lafiya.
Bakin cikin Goggo daya yadda Suwaiban
taci galaba a kanta lallai aikin boka na tasiri akan
danta tunda gashi yanzu kota bashi umurni,
Suwaiban na'bashi nata zai tsallake na Goggon ya
aikata na Suwaiban Tirkashi yau fa ta debo ruwan
dafa kanta, dama tsuntsun dayaja ruwa shi ruwan ke
yiwa tsinannen duka.
Anyi taron suna da kashe kudi na ban
mamaki wanda ba'ayi ba a haihuwar Baffa tunda
ragamar gudanar da komai na taron sunan Suwaiba
ya dankawa sabanin haihuwar Baffa da Muneeba ce
Jagorar komai.
Hatta da zannuwan da Suwaiban ta sa na
fitar suna rantsattsune (Super Exclusive) ne guda
biyu sai Lesuna manyan (Swiss) guda uku sai
Shadda`da suka sha aiki an jera stones dinkin yayi
kyau matuka guda biyu da Materiyal guda biyu
masu tsada.
147
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Haka ta d nga shiga sutura tana sauyawa
tambe wata amar kai da gani dai ta kama miji a
hannunta. Muneeba kuwa ko Ingila bai jefeta da ita
ba, Alla', yaca tana da sababbin dinkunanta su tasa
ranar senan sh. yasa babu wanda zai gane ko anyi
mata ko baıyi mata ba.
To 6angare Sobeniyos din da Suwaiban ta
raba ma wanda ta ga dama shi ta ba, haka nan 'yan
uwa na Dukku wanda take shiri dashi shi taba duk
wanda bata shiri dashi to ko kallon arziki bai isheta
ba balie ta bashi.
Wannan iskancin na Suwaiban ya tunzura
Goggo matuka har ta yunkuro zata je dakin
Suwaibar don ta ji dalilin hana wasu da tayi taba
wasu, su fadima sunsan idan taje rashin kunyar
Suwaiba zata iya mata shi yasa suka hanata zuwa
har Zuwaira ta kara da cewa "Kinga waccan
haihuwar ta Baffa da yake komai na hannun
Muneeba ai wa ya samu, wasu ma har da kari
wannan ko ya damka mta komai ai dole tayi
wulakanci, in jinta da akace tava matar kawu Lawal
da za su tafi, wai taron sunnan da aka bana ayi
shine yanzu za a dameta taba mutane abin suna, ita
fa taro don jama'arta tayi ba on jama'ar wasu ba
naso in fita inci nutuncinta Goggo Hinde ta hanani,
r iskar yarinya wato ta samu wuri shine zata baza
shanyarta yadda takeso, to wallahi zan gyara mata
zama.
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Adda Fadima tayi murmushi tace "Habawa
kuma dai ai zaku gani indai halin wannan
matsiyaciyar yarinyar ne dama ku kukc goyon
bayanta, sannan ta samu Goggo na daure mata
kugu tayi tsiyarta yadda take so yaushe Munecba
za'a zo gidan nan ta hana mutum abu balle har ta
gaya masa bakar magana ko da yake Goggonma
bata kyaleba balle wani banza, ni shi yasa ba ma
shiga shirginta balle ta rainani, wanda ko mijin
daya ajeta bai isa ya rainani ba balle ita".
Kowa fa a dakin yayi ta tofa albarcin
bakinsa akan irin share guri da Suwaiban tayi ta
mike kafa take baza abinda taga dama babu mai yi
mata birki Goggo dai bata ce ta tafasa a sauke ba,
saboda ita fa har yanzun bata san ana aibunta
Suwaiba duk da irin rashin kunyar da take zubawa a
gidan tafi sonta fiye da Munceba duk da cewar son
da takewa kishin Mujeeb yana wa Muneeba yanzu
babu shi, amma hıkan bai sa ta sassauta mata ba,
sam babu gurin wa nda Muneeba ke jin dadi a gidan
nan a halin yanzu.
***** *****
Wata sabuwar tashin tashina da taso a gidansu
Munceba kuma tace kwace rikon Baffa a hannunta
da Goggo ta yi bata mai da shi hannun uwarta,
acewar Goggon tunda Muneeba bata zama kullum
149
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zara
tana ysakaran to ba zai yiwu ba a dinga
barinawer yaro a hannun Karime mai rainonsa,
alhalin ga uwarsa a gida don tana takamar ance an
bata shi, in gaskiya ne ita uwarsa ce kamar yadda
lake iKirari toa dunga tasa shi a gaba tana zuwa
dashi makarantr in kuwa ba haka ba to dole da ya
dawo g rin u varsa.
Muneeba sam bata gasgata zancen Goggo
zai tabbata ba sai da ta dawo makaranta ta iske
Goggo tasa Karime ta debo kayan Baffa tas dake
dakinta wadanda tayi masa dirowa guda na komai
nasa data dawo ta iske Karime zaune a falonta ta
zuba uban tagumi fuskantar kunshe da damuwa, da
ganinta zaka san wani abu na tashin hankali ya
sameta kvi tsaye Munecba hayi ta shiga said a ta
fito ne, sapuan ta lura da hulin da Karimen ke ciki.
Ta matso kus. da ita tace, Karime lafiya na ganki
haka? Ina Baffa? Don nasan in ba dalilin Baffa ba
zan ganki hak. 'a?.
Karime ta dan goge guntuwar kwallar dake
idanunta tace "Dazun ne muna zaune a tsakar gida
11 Baffan yana ta yawonsa, sai Goggo tazo ta
Jaukeshi suka shiga dakin mamansa sun dade a
car., shine ta fito tace in kwaso tnasa kayansa dake
dakinki kada in bar ko wando in kuma na rage ko
aya Saya ne sai taci mutucina, shine na kwaso
mala duka har da pampers dinsa data kalmansa da
salabbin kayan da kika siyo masa duk na bata, wai
150
WATA KU'SAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
daga yau ya koma fakin mamansa, wallahi ni banyi
masa komai ba.
Nan da nan hawaye ka cika idanun
Muneeba, tausayin kanta mai tsanani ya kamata
Allah sarki duk fa akan rashin haihuwa ake mata
wannan wulakancin da nuna iyaka, itama Suwaiban
ai ba rawa tayi wa Allah ya bata ba ganin damarsa
ne tana fatan itama ya bata masu albaka.
Tayi saurin goge kwallar da tazo idanunta
don bata son ta nuna butulcewarta ga Allah akan
bai bata haihuwa ba alhalin ya bata wasu ni'imomi
masu dimbin yawa da mul manci a rayuwarta,
wanda in aka dauki guda daya kacal ya fi ni'imar a
baka 'ya'ya misali lafiya kadai idan Alleya baka
ya baka babbar ni'imar da ta wuce ka sami 'ya'ya.
Takaicinta daya na yadda ake ce son rabata
da yaron alhalin sunyi shakuwa irin ta da da uwa
shakuwar da idan aka za'a rabashi da ita hakika an
zalunci yaron itama an zalunceta saboda zasu shiga
wani hali ko da yake so'akeyi aga iyakarta to amma
zata bari wanda ya bata kyautar dan yazo taga
hukuncin da zai yanke.
Sam kasa cin abinci Muneeba tayi saboda
rashin Baffa a tare da ita hakan ne yasa ta aje
abincin ta nufi dakin Suwaibar sallamarta kawai
Baffa yaji ya taso da gudunsa har yana faduwa yazo
ya kankameta yana fadin (Maama) da na abinda ya
iya fadi kenan sai wani lokaci yake fadìn Baba.
151
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ta dauke shi ta rungume a jikinta wani
sanyi ta ji ya ratsa zuciyarta hakika kauna ta jini
daban take, ita kam tana jin a duniyar nan babu dan
da zata so ta kaunace shi irin Baffa kai ko dan da
zata haifo ne, sai dai soyayyarsa ta biyo bayanta
Baffa.
Ta risina gaban Goggo dake sakawa
takwararta Rahina kayan sanyi tace, Sannunku
Goggo kun wuni lafiya? Ta amsa a dakile tamkar
mai ciwon hangui, Lafiya Lau. Muneeba ta kai
hannu ta shafi kumatun jaririyar tace "Goggonmu
har anyi maki wanka, ina kuka ana nan anayi? Daga
Goggon har Suwaiban da ke gefe tana ninke kayan
shanyar Jaririyar babu wanda yace mata ci kanki.
Ta aje Baffa tana cewa Baffa na zaune in
goya Goggo, Sarkin Kishi yanzu zakace baka yarda
sai dai kai a goya ka "Ta dubi Goggon ta ce
"Goggo tunda kin gama shiryata kawo ta in goya ta
"Goggo ta girgiza kai tace A a ki barta kawai bana
son a fita da ita a kwasar mata sanyi mura take yi
shima wannan da ake gararamba dashi a hannun
mai aiki yau na amso shi ya dawo hannun uwarsa
đon ba zai yiwu ba ke ba kya zama shi a barshi
hannun waccan yar yarinyar ca itama bata wuce
ayi nata rainon ba, suna walagig a tsakar gida to ba
zai yiwu ba, ko ta kama ta rufe su a daki ita dashi
kamar wasu masu laifi shi yasa ni yau na dawo
152
이
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
dashi gurin uwarsa kuna babu wanda ya isa ya karya umurni na che!.
Munecba idanunta cike da hawaye ta
gurfana gaban goggo ta ce “Kiyi hakuri goggo don girman Allah in dai wannan shine dalilin amsar
rikon Baffa a hannuna to zan dinga goya shi ina
tafiya dashi makarantar, tunda ma na kusa gama
karatun". Goggo ta kyabe baki ta ce, ai ko fasa
zuwa karatun za ki yi saboda rikon Baffan ya dawo
hannunki ba zai dawo ba, in fitsari banza ne kaza
tayi mana in haihuwar a sama ake samu ki je ki
haifi na ki sai ki mallake abinki baki mallaki na
wasu ba ni na taba ganin inda akai haka:
Gwiwoyin Muneeba duk sai suka saki tana
durkushi gaban Goggo ta kasa mikewa saboda
kalamanta sun soki zuciyarsa, shikenan ta san tun
da goggo ta raba ta da Baffa to zance ya kare,
Mujecb bai isa yace zai dawo mata da yaron ba,
amına duk da haka zata kwatanta kai masa kokenta,
ko Allah zai sashi yayi nasarar canza ra'ayin
Goggon tunda shi ne ya bata kyautar yaron.
Ta mike tana sharan kwalla rungume da
Baffan zata bar dakin Goggo ta dubi ta tace, Aje shi
kada ki tafi dashi yazo ya hanamu bacci anjima,
duk da yanzu m ganinki da yayi ba zanıu iya tsayar
da kukan da zai yi ba idan kik tafi ni na rasa jarabar
da kike durawa yaron nan da har ba ya kaunar kowa
sai ke, uwar ma da ta tsuguna ta haife shi baya
153
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Kaunar zama da ita balle mu wallahi kiji tsoron
Allah!.
Muneeba ta ce, wallahi ni ban taba bashi
wani mugun abu don ya manta da wani ba, balle in
bas hi ya guji uwar data haife shi, son da nake masa
na jini ne kuma na tsakani da Allah. Ni kuwa meye
ribar da zan samu idan na raba da da uwarsa? Ai da
in zamo silar haka gara Allah ya dauki raina.
Au sau nawa kuma akayi haka, ni nan da
ban tashi tsaye ba ai da tuni kin rabani da nawa dan,
sai Allah yasa kurwata tafi taku keda uwarki, to
jikana yafi karfinku! Kamar yadda nafi karfinku.
Muneeba ta kai iya wuya da wannan irin
muggan kazafi da Goggo ke dora mata ita da
uwarta kazafin yin asiri wanda a rayuwarta bata
taba jin ko sanin Innarta na yawon asiri ba, amma
kullum Goggo sai ta jefeta da mummunar Kalmar
nan ta yin asiri bata san lokacin da bakinta ya furta
kalmomi masu zafi ga Goggo ba" "Masu dai son
rabaki da danki suna nan tare dake amma ni bana
fatan in rabaki da danki tunda banyi gadon yin
hakan ba da inga ranar gara Allah ya dauki
rayuwata inje in hadu dashi satin-alin ban dauki
hakin kowa ba".
Ita kanta Munceba ba a san lokacin da
bakinta ya iya furta wadannan kalamai ba kuma
tana fadan su ta juya tayi ficew rta, tana ji Goggo
na cewa, Dawo ki aje mata danta, tunda bake kika
154
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
haifar mata ba, ai shi yasa ma Allah bai baki
haihuwan ba na wani ma kin mallake kina iko a
kansa ina ga naki da kika Haifa vallahi ko kin tafi
da shi zan zo in dauko shi tunda dakin naki ba bako
na bane?
Da Munceba bata dare da Mujecb ya dawo
tunkare shi da maganar ba, saida ya dade da
dawowa don a tunaninta Goggo zata yi masa
maganar sai taga alamun bata yi masa ba, shine ta
same shi a dakinsa tunda yanzu bata cika zuwa
dakin nasa ba a dalilin ya kafa mata dokar in ba
wani abu zata kai masa ba ko zata amsa ko wata
magana to tadan saurara masa da biyo shi fakinsa
da sunan kwana in yana bukatarta zai kawo kansa, a
haka suke zaune kuma tun daga lokacin bai biyo ta
dakinta ba balle yazo don bukatuwarsa sai ta zube
masa ido kawai tare da Addu'ar Allah ya iyakance
wannan matsala da suke fuskanta yana zaune bisa
kujera mai zaman mutum uku (3 seater) tayi
sallama ya amsa mata da kyar, kallo daya ya yi
mata ya dauke idanunsa bata damu da hakan da ya
yi ba, domin idan da sabo ita kam har ta saba da irin
wannan ko'in kular na mijinta a gareta.
Ta nemi gefensa ta zauna tare da yi masa
sannu da hutawa ya amsa a dakile hankalinsa na
kan jaridar da yake nazari ta (Blue Print) ta dan
dube shi tace ni kam đai har yau na yi iya bincike
na na kasa gano laifin da na yi maka, tunda kullum
155
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
idan na tambaycka sai kace ban yi maka komai ba,
in kula shin an taba nuna wa mutum halin ko
alhalin bai yi laifi ba? Wallahi ban jin dadin irin
wannan zaman da muke yi nafi sabawa da zaman
auren rayuwanmu ta bava cikin so da kaunar juna
da kulawa da tarairayar juna ka tausaya mun na
rame na futa hayyacina duk a dalilin juyamun baya
dakayi shin da wanne zanji da matsalar data kunno
a tsakaninmu ko kuwa da yanayin zamanmu da
Goggo, na rasa mai na yi wa Goggo a duniyar nan
ta tsaneni, tamkar ni ba jininta ba ce, tafison
Suwaiba dani alhali nice dolen ta, duk irin rashin
kunyar da take mata bata gani, sai ma dada fifita
takeyi akaina, kuma hakan bai sa na daina yin mata
biyayya ba, sannan yanzun ban san mai na yi ba ina
makaranta ta ce Karime ta hado kayan Baffa a daki
na wai ta maida rikonsa hannun uwarta, tunda ni
ban zama sai dai in barshi gurin 'yar aiki, alhali ko
da can haka ake yi tunda ko muna gida daga ni sai
ita Karimen yafi yarda damu, da can duk ba'aga
cewa da matsala ba sai yanzun da ake son rabani
dashi alkawari ne ka riga kayi cewa ka ban Baffa,
saboda haka ina rokonka daka dawo mun da shi, na
yi mugun sabo da yaron ta yan la ba zan iya rabuwa
da shi ba, kafi kowa sanin shal uwarmu don girman
Allah ka tausaya min.
Tun da take maganarta ai dube ta ba har sai
da ta kai aya a sannan ya daga danu daga jaridar da
156
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yake dubawa ya dubcta yace, Duk na ji bayananki,
yanzu kin kawo mun karar Goggon ne a kan ta yi maki ba daidai ba ko mc?.
Tayi saurin girgiza kai tace, Ni ba kararta na
kawo ba, ina dai rokonka arzikI ne kasa baki a
dawo min da Baffa wallahi yaron shine farin cikin
rayuwata a halin yanzu, yana debemun kewa yana
sani cikin nishadi da farin ciki rashinsa tare dani zai
jefeni cikin Kunci da rashin walwala wallahi zan
iya kamuwa da ciwo dalilin rashinsa kusa dani.
Cikin maganganunta ya lura tana cikin
matsanancin kunci saboda halayyar da suka shiga а
zamantakewar aurensu, wanda shi baisan me ya
same shi ba sam, sam ya ji bata cikin zuciyarsa ko
kallonta yayi sai ya ji bakinciki ya taso ya tokare
masa, a kahon zuciya, idan ta matso jikinsa kuma
sai yaji tamkar ya hankadeta ko ya shaketa saboda
tsanarta da yake ji, balle kuma aje ga batun
kwanciya a tare har ya sadu da ita, sam baya jin
sha'awarta dukkanin sha'awarsa nakan Suwaiba, ko
da ta haihu yanzu baya jin sha'awar kusantan ta,
duk da a matse yake gashi bai iya neman matan
waje ballantana yaje ya rage zafi, shi kam ya rasa
dalilin takamamen abun dake masa yawo a
kwakwalwa, ko da yake ya taba gayawa wani
amininsa a gurin aiki sai yake shawartar sa da ya dage da Sallar dare yana kuma addu'a da sadaka insha Allahu kullin da ke
157
tattare da zuciyarsa zai
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
warware, to amma matsalar da yake fuskanta sam
baya iya tashi cikin dare yayi Riyamul laili balle
addu'a, azumin Na fila da suke yi na litini da
Alhamis ya daina yi dama muneeba ke tunatar
dashi, sadakama idan zai bayar sai yaji zuciyarsa na
hanashi, shi kam yana cikin tasku bai kuma san
yadda zaiyi ba.
Munceba ta katse masa tunani da cewa,
"Don Allah kayi wani abu akan al'amari na, ka
tausayamin kasan ni abin a tausaya min ce ya ce shi
kenan tashi ki tafi zan san abinda zan yi zan
nemeki. Ta mike jikinta a sanyaye ta tuna da
dakinshi shine makwancinta, amma yanzu da aka
shiga tsakaninsu har umurnin ta bar maşa dakin
yake bata, babu ruwansu da ko wani hali zata shiga
a dalilin kaurace mata da yayi na wata da watanni,
ga ta lafiyayya ta ci mai kyau ta sha mai kyau ta
kwanta a mai kyau aiko dole ta bukaci mijinta kusa
da ita, amma ya zata yi dole ta cigaba da tausasar
zuciyarta tana ba zuciyarya hakuri har Allah ya
kawo daukinsa a garesu.
Tana isa dakinta zuciyarta ta kasa hakurin
rashin Baffa ga uwa uba rashin mai gayya mai aikin
uban Baffa wanda idan daya baya tare da ita zata
kasance da motsin daya akusa da ita koma su
kasance su uku a tare sai gashi ita kadai tal a
dakinta yanzun shikenan haka zata rayu ita daya
babu mai debe mata kewa? Wani babin kuka ta
158
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
bude wanda saida dare yayi nisa sannan ta hakura a
dalilin ınatsanancin ciwon kai da zazzabi da sukai
maya rubdugu suka rufcta, duk da haka bata iya
kwanciya ba sai ta gabatar da sallar Nafila. tayi
addu'o'i sannan tasha magani ta kwanta lokacin
Uku da Mintina biyar na dare.
Ga dukkan alammu kwana Baffa ya yi yana
masu kuka, don kuwa tunda ta tashi yin sallar
subahi take jin kukansa har tayi sallah tana zaune
tana lazimi bata daina jin kukansa ba zuciyarta ta
soma yi mata zafi don bata son ko yayane ta ji
kukan yaron, sai taji kukan nasa yana sukan ranta
tana jin lokacin da Mujeeb ya dawo daga masallaci,
ya shiga dakin Suwaiba ya gaida Goggo ya amso
yaron suka fito zuwa dakinsa. Tabbas tasan kukan
da yaron yake na rashin ganinta a kusa dashi ne,
musamman irin gatar da takeyi wa yaron idan ya
tashi daga barci wanka take fara yi masa ta wanke
masa baki idan ta shafa masa mai ta sa masa kaya
to zata hada masa lafiyayyan Ti yasha, yana
gamawa zata goya shi ta soma ayyukan dake
gabanta, duk abinda zatayi yana bayanta tunda har
mamansa ta haihu bai cika shekaru biyu ba kenan
bai wuce a goya shiba.
Tasan kukan da yake yi bai wuce na yunwa
dana goyo ba, tun da daga Goggon har Suwaiba
babu mai goya shi, balle Suwaiba da aka yi mata
aiki jinjirarta ma sai dai Goggo ke goya ta kasa
159
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
hakurin jin kukan nasa tayi, ta tashi sanye da
hijjabin da tai sallah ta nufi dakin Mujeeb din A
falonsa ta iske shi tsaye yana ta safa da marwa da
Baffan a kafadarsa yana lallashinsa. Ta isa gare shi
ta soma gaisar da Mujeeb, ai Baffa na jin muryanta
ya yi saurin dago kansa daga kafadar uban ya dubi
inda yaji muryarta, yana ganinta ya sake saka ihu ya
soma zamewa daga jikin Mujeeb yana mika mata
hannu don ta dauke shi, bata yi jinkiri ba tayi saurin
amsan shi tana cewa, "My boy yi hakuri banje ko
ina ba ina nan tare da kai har abada, babu mai iya
rabamu sai Allah".
Yaron ya kwantar da kansa a kafadarta yana
sauke ajiyar zuciya. Ta dubi Mujceb ta na cewa
"Gaskiya an dauki alhakinmu ni da yaron nan
kamar yadda na kwana banyi bacci ba saboda
kewarsa shima ina jin kukansa, don kwana ya yi
yańa kuka kuma nasan rashin ganina tare da shi ya
sa shi kwana kuka. Gaskiya kayi wani abu akan
al'amarin nan, duk da dai anyi ne don a saka ni
cikin kunci da bakin ciki a dalilin Allah bai bani
haihuwa ba, alhalin ba laifi nayi masa ya hanani ba
jarabawa ya ke yi mini, in ba'a tausaya mini ba ai
ba za'a kuntata mini ba”.
Ya dubeta fuskarsa a daure ya cе,
"Mahaifiyar tawa kike
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12