san abin Karin safe na na can na
jirana, ke da baki da lafiya me ye na wahalar da
kanki", tace,
"Meye na wahala don nayi abu zan ci na yi da
kai? Allah yasa dai ba ni kadai na soma yin haka a
gidan nan ba, da kanka ma zuwa kake ka ci ko girki
na ne ko na taba hanaka?" ya amshi filet din ya
debi cokali daya na naman ya kai bakinsa yana
cewa, "To sarkin korafi, na ci shike nan? Zuba min
kunun".
100
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ta juya ana zuba masa kunun a kofi
zuciyarta cike fal Da farin ciki, ita kam ko yanzu
ya ce ya koshi bukatarta ta biya sai ta dauki sauran
ta je ta yi fuioshin dinsa a toilket don kada danta ya
shigo ya ci, sa boda bata son ta mallake shi yanzu ta
dai fi son mallakar Ubansa, shi raba shi zata yi da
uwar goyon tasa kwata-kwata ya dinga gudunta.
Tana zaune tana kallonsa har ya kusan cinye
farfesun, ya mika mata ragowar ya cigaba da shan
kununsa. Ita kam tunda bukatarta ta biya sai ta ce
masa tana zuwa ta baro dakin nasa, kai tsaye bayin
dakinta ta shige ta juye ragowar farfesun a masai
tayi filoshin dinsa ya bi ruwa sannan ta sauke
ajjiyar zuciya tae da subucewar wani murmushin
mugunta a labbanta, "Mujeeb ka riga ka zo
hannuna, zan juya akalar royuwarka yadda nake so,
ta yadda za ka ji maganata ka bi umurnina fiye da
bin umurnin mahaifiyarka. Ke kurra Muneeba kin
kade har ganyenki don sai na maida ke abin
kwatance, zau raba ki da mujin da ki ke takama da
shi, in mallake shi ya zama nawa ni kadai, karyarki
ta kare."
*** *** ***
Kwana biyu kacal da faruwar hakan sai
Awakwalwar Mujeeb ta birkice wani sabon al'amari
ya bakunci zuciyarsa na tsanan al'amarin Munceba
haka kurum sai ya ii baya son ya genta, amma in
126
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
bata kusa da shi sai ya ji yana son ya je inda take da
zarar ya je kuma suna yin arba sai ya ji kunci a
zuciyarsa, ya rasa dalilin wannan abu.
Idan tunaninsa ya fara hararo masa zargin
ko Suwaiba ta bi halin Hajiyarta sunje sunyi masa
asiri sai kuma ya ji zuciyar tasa ta kasa gasgata
hakan sam zuciyarsa ba ta son ganin wani laifi na
Suwaiba ko aibu akan wani nakasu na halayyarta.
Kwana biyun da ya yi a dakin Suwaiba sai
yake jin tamkar ya zarce ya yi ta kwana mata ita
kadai ba tare da ya raba mata kwanan da wata ba.
Wata irin tsagwaron soyayyar Suwaiban ce take
ratsa zuciyarsa, sai yake ganinma bai taba jin so irin
haka a zuciyarsa ba sam ba ya son ya ga canji ko
yaya ne a fuskar Suwaiba sai hakan ya tada
hankalinsa.
Ita kam Munceba tunda ta lura da wannan
sauyin daga mijinta sai ta tsannanta tsayuwar daren
da take yi fiye da na da tana kaiwa Allah kukanta
don kuwa ta san an riga an tsunduma mijinta cikin
wani hali na halaka, sabo da a kwana biyunta da ya
dawo dakinta sam ya ki yarda su hada makwanci,
wanda in ada ne it ace ma ke yakice iribn kulaficin
da yake nunawa akan ta, amma sia gashi wai yanzu
shine ke gudun hada makwanci da ita, hakan bai sa
nayi fushi ba don ta san ba yin kansa ba ne, aikin
asiri ne tunda ta ji da kunnenta lokacin da Suwaiban
ke waya da Hajiyarta tana mata albishir da cewa
127
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
aiki fa ya yi dole aje a yi wa boka godiya da bayani
don har ya juyawa Muneeban baya, ko hada
makwanci ba ya yi da ita, kuma da ita Suwaiban
yake shawarar komai yanzu.
A halin yanzu abinda Muneeba tafi maida
hankali a kansa shine karatunta da take a shekarar
karshe, don bata fatan damuwar halin da take ciki
ya shafi karatunta. Suna zaune a makaranta ita da
wata kawarta, wadda tunda suka fara karatu tare
suke, ita 'yar asalin garin Gombe ce kuma anan
take aure da yaranta guda biyu. Ta dubi Munecba
tace, "Wai Muneeba kwana biyu me ke damunki ne
sam kin daina wata walwala sai in dinga ganin ki
cikin zurfin tunani, ni kaina abin na damuna in na
tambaycki ki ce min ba komai, alhalin ni idan ina
cikin matsala kece abokiyar shawarata, kuma ba
kya bani muguwar shawara har in yi aiki da
shawarar taki inga na cimma nasara, amma ni sai ki
dinga nuna kokwanton amintakar mu ne?"
Munceba ta kada kai tana murmushi wanda ya fi
kama da yake ta ce,
"Wallahi sam ba haka bane Maman Dijah, don
matsala na shiga cikin gagaruma. matsala to amma
gani nake tunda na tsayu da addu'a matsalar zata
gushe da yardan Allah shi ya sı ma ban gayawa
kowa ba amma kiyi hakuri ba wai ina boye miki ba
ne, kina daga cikin aminai na gari abin ayi shawara
da su, ke din mutum ce da ba a cika samun masu
128
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
son mutuin tsakani da Allah irinki ba, wallahi ina alfahari da samunki a amatsayin aminiyata".
Maman Dijah ta cc,
"Bari fasamin kai, ke dinma ai baka kike da fatan
zamu ci gaba da rikon AMANAR JUNA (Sunan
littaf na gaba). Kuma ko baki gaya mini matsalarki
ba zaki iya ce mini in tayaki da addu'a yanzu ma
insha Allahu zan tsayu da miki addu'a Allah ya ya
kawo karshen abinda ke damunki har muma sauran
musulmi Allah ya yi mana maganin matsalolinmu,
kar ma ki gaya min matsalar don nima tada min da
hankali za ta yi. Amman ina fatan ba akan rashin
haihuwarki ba nc?" Ta girgiza kai tace,
"Ba wannan ba ne, maganar haihuwa ni kam tuni
na fawwalawa Allah, kila rashin haihuwar shinc
alheri a gareni, in kuma ina da rabo to ina rokon
Allah ya bani masu albarka. Wani boka na ji
Suwaiba na cewa Hajiyarta aje a gaya masa aikin
da ya yi mata ya ci baban Baffa ya juya mini baya
ko makwani baya hadawa da ni, kuma haka dinne
yadda ta fada, wallahi yanzu maganar arziki bata
hada ni da shi, ko dariya yake yi idan ya ganni sai
ya canza fuska yadda kika san ya ga bakin maciji,
yanzu kulum sai sun fita tamkar wasu sabbin
amare, saukin abinma basu kwace Baffa a hannuna
ba shi nake kalla in yi wasa da shi inji sanyi, in
suka amshe shi anan ne damuwata zata dada
129
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Karuwa". Ta kare maganar fuskarta kunshe da
tsantsar damuwa.
Ita kanta Maman Dihjah nan danan ta shiga
cikin damuwa a dalilin jin abinda ya samu
aminiyarta, sai take jin tamkar ita hakan ya sama.
Ta gyara zama suka fuskanci juna sosai ita da
Munecba, ta soma bata shawara ta gari irin yadda
ya kamata aminin kwarai ya ba amini ba cuta ba
cutarva,
"Abu na farko da ya kamata kiyi, yanzu shine
addu'a don ita addu'a takobin yakin makiyi ne da
duk wani mugun halitta mutum ne ko aljan, kada ki
yarda zuciyarki ko wani ya baki shawarar bin irin
hanyar da su ka bi, domin irin hanyar da suka bi ta
fatattu ce kuma zuwa gurin boka yin shirka ga
Allah ne babba kuwa. Sanann abu na gaba duk wata
kulawa da kika san kina bashi kada ki gaza, kada ki
ce don ya juya miki baya kema bari ki juya masa
baya ki watsar da duk wani abu da kike masa na
kyautatawa sam kada ki daina ki ci gaba, har itama
kada, ki canza mu'amalarki da ita, ki ci gaba da
kyautata mata, balle kuma dai ta da rikonsa ke
hanunki, ki ci gaba da rikonsa tsakani da Allah
yadda kike masa wallahi ba zaki tabe ba, kuma
kada ki gaya ma sa kinji wayar da ta yi da Hajiyarta
ki kyalesu kwana dari na baraw ne amma kwana
daya tak ne na me kaya zai karna barawonsa (red
handed) dunu-dumu, in dai kin dage da addu'a to
130
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ba za a kai ko ina ba kome ta yi masa zai zo iyaka,
In shaa Allahu Allah zai warwarc kullin da suka yi
zamu dage da addu'a tunda babu abun da ya gagari
Allah, kuma shi ne da kansa ya ce, ku rokeni zan
amsa muku, kada ki saka abin ya yi ta damun
zuciyarki don zai iya haddasa miki wata cutar a
zuciya ki dage da addu'a da azumi wallahi sai kinga
karshen al'amarin". Zuciyar Muneeba ta sanyaya
da jin nasihar aminiyarta, ta sauke nannauyar ajiyar
zuciya ta cе,
"Madallah da samunki a matsayin aminiyata
wallahi ina alfahari da samunki a rayuwata,. Na
godc na gode da shawarwarin ki, wallahi tunda abin
nan ya sameni ban taba jin natsuwar zuciyata ba
irin yau, kasancewar al'amarin na ta gwaguyar
zuciyata, amma na gaza furta shi ga kowa, yau
kadai da na bayyana abin da na boye a zuciyar tawa
ga shi har na ji sanyi, lallai na yarda barin kashi a
ciki baya maganin yunwa". Aminan biyu sun
cigaba da tattaunawa har lokacin sake shigarsu aji
ya yi sannan suka shiga.
Koda suka tashi makaranta sai ta ji zuciyarta
sam bata son komawa gidanta tana son ziyartar
Mama Amina, don kawai ta je tayi hira da Maman
da su Khairat ko ta ji sanyi a zuciyarta na abin da ke
damunta.
Ta lalibo sunan Mujceb a wayarta ta kira shi
don ta nemi izinin sa ta kira sau biyar bai daga ba,
131
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ba ta yi tsammanin ba ya kusa ba, tabbas ta san
yana kusa da wayar dauka ne ba zai yi ba, dama
kuma a 'yan tsakanin na haka yake mata idan ta
matsu da son tambayarsa anguwa to fadin wata
maganar ko ta kira ba ya dauka sai dai ta tura masa
sako a wayar, to nan ne yake bata amsa shima a
rubucc.
Yanzu ma sai ta tura masa sakon neman
izini, ba a jima ba ya turo mata amsa, sai kin dawo,
da manyan baki a takaice.
Sun fito inda motoci suke da maman Dijah a
inda direba ke jiran MAman Dijan sai Muneeba ke
ce mata "Hanya daya zamu bi, zanje gidan Mama
Amina ne", ta dubi Munceba fuskarta kumshe da
tuhuma tacc, "Ba dai maganar nan zaki gaya mata
ba, ki tada mata hankali?" ta girgiza kai, "Zanje ne
kawai in gaishe su, inyi hira da su don inji sanyi a
zuciyata, ba wai don in gaya musu matsalata ba, na
san Mama da damuwa akan abin day a shafeni,
yanzu ina gaya mata hankalinta zai tashi ta yi ta
damuwa har ma ta fi ni damuwa, shi yasa ba komai
ba ne na damuwata nake gaya mata na fi gaya mata
abu na neman shawara".
"Yauwa kada ki fada mata mu cigaba da addu'a
babu abinda day a gagari Allah, Zai kawo mana
agaji". In ji Maman Dijah.
A gidan Inna Amina ta vi Sallar azahar ta ci
abinci duk da walwalar da ta samu a gidan amma
132
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
saida Inna Amina ta gano tana tattare da damuwa har ta tambaycta, ta ce ita babu wani abu dake damunta. Tace, "To amma kinyi rama kamar mara lafiya". Tacе,
"Karatun da na ke hana ido na bacci na yi inaga shi ya sa nayi rama, don bana samun isasshen bacci
hakan ke sa in yi ta ciwon kai ni kuma in ba da
daddare ba bana iya karatu don ko Baffa baya buri
na in ba bacci yake ba".
"Aiko dole ki daina karatun daren da rana sai ki
dinga kaishi gurin Suwaiba ko mai rainon shi ba
tana nan ba?" tace,
"Eh tana nan amma ba ya zama a gurinsu in dai ya
san ina gida, in kinga ya zauna a gurinsu to ya neme
ni ya tabbatar ba na gidan shi ne yake hakura ya
zauna a gurinsu" inna Amina ta ce,
"To shi babansa bay a fada akan hana idonki
baccin da kike yi shima ai kina shiga hakkinsa ni
banga amfanin karatun dare ba ka dauki hakkin
idon ka, ka dauki hakkin mijinka".
Munceba duk sai ta diririrce saboda ta san
bata shiga hakkin mijinta shine ma ke tauye nata
hakkin, shine dalilin ranarta tun da har yau ta kasa
gano kuskurenta a gurinsa da ya juya mata baya. Inna Amina dai duk hikimarta na son sanin
abin da ya ramar da 'yar tata bata sami wani haske
daga Muneeban ba, don har su Khairat tasa su bincikar mata Munecban tunda sune abokan
133
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
shawararta, to suma sun binciketa ba su sami wani
haske ba haka suka kyaleta.
Tana yin Sallar la'asar ta baro gidan Inna
Amina, saboda zata je ta yi girki. Tana cinna hancin
motarta harabar gidansa ta hangi Mujecb a jikin
motarsa tare da Suwaiba za su shiga motar tasa ga
dukkan alamu anguwa za su je. A bayan motar ne ta
hango Baffa shi ma an yi masa kwalliya da shi za
su je kenan tunda ta ganshi a motar.
Tayi saurin zuwa tayi fakin din motar ta
fito, ta nufo gurinsu, kafin ta karaso har sun shiga
motar dai-dai da isowarta gurin a lokacin Mujecb
ya ta da motar suka fice a harabar gidan suka barta
tsaye rungume da jaka. Ta juya tana jan kafarta da
kyar saboda nauyin da ta ji kafar ta yi mata,
idanunta cike da hawaye a dalilin wannan
wulakancin da Mujeeb ya yi mata, Allah dai yasa
mai gadinsa bai fahimta ko ya ga wannan cin
zarafin da aka yi mata ba, dan ganin hakan zai iya
rage mata kimarta da suke gani.
Zaune a tsakar gida a barandar kofar dakinta
ta ga karime ta zuba uban tagumi. Ganin karimen
ya sa ta yi saurin goge hawayen da ke idanunta, ta
isa gurin Karime tana tambayarta, "Me ya faru kike
zaunc anan kin yi tagumi?" Ta sauke tagumin da ta
yi ta soma yi wa Muneeba sannu da dawowa
sannan ta ce, "Babu komai, dama dawowarki na ke
jira sai in tafi gida".
134
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Munceba ta mika mata makullin motarta
tace, "Je ki bude gaba gefen da nake zama ki dauko
min wani filas da na manta da shi". (kunun gyada
ne Mama ta zuba mata tace ta taho da shi dan ta ga
bata wani cin abincin kirki).
Ta dauki makullin dakinta a inda take ajew
ata bude dakin ta shiga Karime ta yi sallama ta
shigo ta mika mata makulli da filas din tace, "Kunu
ne idan zaki sha ki diba, in kin gama sai ki zo ki
taya ni aikingirki sannan ki tafi".
Dama yunwa ce ke kwakular Karime, don
rabonta da abinci tun wanda Munceba ta bata da
safe kafin ta tafi makaranta, da rana tana gani
Suwaiban ta yi iya cikinta ita da danta suka ci ta
hanata ko albarkacin dawainiyar datake da danta
bai sa ta bata ba. Har baki ta cika kofin ta kafa kai
tanakyankyana, Muneeba ta dubeta cike da mamaki
tace, ", ba ki ci abinci bane? Tace "Eh ban ci ba, na
duba kicin dinki ko zanga ragowa ban gani ba".
Muneeba ta cika da mamakin halin mugunta
irin na Suwaiba, ace yarinya ta wuni cir tana miki
rainon danki amma don zalunci ki hanata abinci
alhalin ke kinci, wannan wace irin rayuwa ce.
"Shi Baffa me aka ba, shi?" ta ce
"Mamanshi ta amshe shi ta bashi abinci". Munecba
ta girgiza kai cike da al'ajabi ta ce, "Yayi kyau" sun
shiga kicin ta shirya lafiyayyen abinci kala biyu.
Tuwon semo da miyar kalkashi ta yi, miyar ta ji
135
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
nama sosai sabo da ta san Mujeeb na son tuwo
miyar kalkashi, balle idan miyar taji manshanu,
idan ta yi masa har santi yake yi, amma yau bata
sani ba ko zai yaba mata, tunda ya daina yabon ko
me zata yi masa na kyautatawa. Tayi lafiyayyen
salat sannan ta yi farfesun hanta da koda nan da
nan gidan ya dau kamshi. Kafin magriba sun
kamala komai, har sai ta ji dadin tafiya da Baffa da
akayi don da yana nan ba zai barta ta kamala
komai akan lokaci ba, da kam har ta ji haushin
tafiya mata da suka yi da shi.
Duka abinda suka yi sai da ta zubawa
Karime ta ce ta tafi da shi gida, son bata son gari
yayi duhu bata tafi ba duk da ba wani tazara ba ne a
tsakaninsu, kasancewarta mace akwai hatsari ga
fitar mace a irin wannnan lokacin da ake Sallar
magriba a dalilin 6ata gari sunfi amfani da wannan
lokacin na daukewar sahun jama'a su bi duhun
magriba su ja'ya'ya su lalata su, tun da su ba su da
mu da zuwa yin jam'i ba.
Tana fitowa daga wanka ne ta ji motsi a
falonta, ta lekawa ta ga Baffa zaune da leda babba
a gabansa ga robar ice cream da ya fiddo yana ta
zubarwa a jikinsa, yana ganinta ya kyalkyale da
dariya yana kiran sunanta "Mama, Mama". Ta iso
gare shi tana mamakin da yaushe aka shigo da shi
bata ji ba, sam bata ji dirin motar su ba, saukar
ruwan wanka a bayi ta san shi yasa ata ji da
136
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
dawowarsu ba. Ta fauke shi ta goggoge masa jikinsa, ta bude ledar da ke gabansa ta ga kayan ciye-ciye ne sai pampers dinsa da mota da jirgi
masu batir da ka siyo masa tunda duk ya lalata wadanda yake da su.
Ta dauke shi suka shiga ciki ta kunna masa
motar yana wasa da ita sannna ta tada ikamar
Sallah. Tana idarwa ta yi kwalliya a gaggauce don
kada Mujeeb ya shigo ba ta je ta kai masa abincinsa
ba. Ta so ta je ta shirya abin cin a dakinsa sai ta
iske bai aje makullin dakinba da abinsa ya tafi,
wato ba ya son ta shigar masa daki abin ya sosa
zuciyarta, amma sai ta lallashi zuciyar ta da kalmar
hakuri.
Har ta gama shirya abincin bai dawo daga
masallaci ba, sai ta koma ta dauki Baffa tayi masa
wanka ta samasa pampas ta canza masa kaya shi ma
ta feshe shi da turare sannan ta dauke shi suka
koma dakin babansa
Sun tarar ya dawo har ya sauke da abincin
da ta kawo kan kafet ya zuba yana cin abinsa. Ta aje Baffa a gefensa itama ta zauna a kusa da shi ta
na masa sannu da dawowa, da kyar ta iya jiyo yauwan da ya furta can a kasan makoshinsa. Ta
dauki kofi ta zuba masa ruwa ta aje a gabansa, ta sake daukan wani kofin ta zuba masa lemun abarba
da kankana da ta hada ta aje masa, tana kallonsa a
tsanake yadda baya son wata mu'amala ta hada su
137
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
amma yana son mu'amala da abincinta, to ko don
matarsa bata iya banc yasa yake cin nata a dole?
Oho!
Babu wata hira da ta gilma tsakaninsu illa
dansa da yake yi wa Magana idan ya rarumo wani
abun zaiyi 6arna,ita kam ko kallonta ba ya son yi
sai kace wata abar kyama ko an aje masa danyen
kashi. Yana gama cin abincin ya mike tsam ya
dauki Baffa suka koma kan doguwar kujera suka
zauna ya daukki remote yana canza tashoshin
talabijin.jikin Muncebaa sanyaye ta mike ta soma
tattara kayan abinci taje ta kai kicin dinta sannan ta
dawo dakin, suna nan zaune har dare ya yi sosai, ya
mike ya je ya yi wanka ya saka kayan bacci ya zo
ya yi Magana ba tare da ya dubeta ba “Ina son zan
kwanta ki dauki Baffa ku tafi dakinki”ta dube shi
cike da mamaki tace, "Mu tafi fa kace? Ko ka
manta ni ke da girki yau?" yace, "Ban manta ba
tunda har kinyi girki na ci". Tace, "Amma gąni na
yi ka daina zuwa daki na duk da ko ka je ba kulani
ka ke ba, shi ya sa yau ni na karya yanci na na
biyoka, kuma ai yin hakan ba aibu ba ne”.
Ya dan dubeta ganin sun hada ido sai ya yi
saurin dauke idonunsa a kanta yace, "Ina bukatar
kadaici ne yanzu in ina da bukatarki zan neme ki ko
in kawo kaina yadda na saba, amma yanzu gaskiya
ban son a dame ni!" zuciyar Muneeba ta sosu
kwarai da Kalamansa amma babu yadda zata yi
138
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
kawai sai tasa hannu ta dauki Baffa da ya riga ya yi
bacci ta dube shi ta ce, "Shi ke nan sai da safe". Bata jira amsawarshi bat a baro dakin. Tana bada baya ya rufe kofarsa har da makulli.
Tana shiga dakinta ta aje Baffa a gadonsa,
ta zauna a bakin nata gadon ta yi kuka mai isarta
har sai da ta ji kanta ya sara mata da wani
azababben ciwo, sannan ta saurarawa kanta, ta tashi
ta rufe kofofinta, ta wuce bayi ta yi alwala ta zo ta yi nafilfili ta yi ta kaiwa Allah kukanta akan
wannan al'amari da ya zo wa rayuwarta wanda ta
dauke shi a matsayin jarabawar rayuwa, kuma In
Shaa Allah zata cigaba da yi wa al'amarin juriya da
hakuri har Allah ya kawo iyakarsa, don komai na duniyar nanamai faruwa ne kuma ya wuce in dai an yi hakuri, yanayi daya ba ya dauwama a rayuwar
mutum za a iya samun sauyi daga fari zuwa baki
ko daga baki zuwa fari iyakaci dai mutum ya yi ta yi wa Allah godiya idan rayuwar ta yi masa fari, idan ta bakanta a gare shi kuma sai ya yi godiya
tare da jin istigfari ga Allah, sai da ta yi Sallar subahi sannan ta kwanta.
1 Rashin baccinta shi ya haddasa mata tashi a
makare, hakan bai sa ta yi kasa a gwuiwa ba, ta shiga kicin ta shirya masa abin Karin kumallo lafiyayye. Sai da ta yi wanka sannan ta dauki kayan abincin ta nufi dakinsa tsayuwa ta yi tiris dauke da
tire a hanntmta sabo da jin kofarsa a rufe har ya fita
139
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
kenan, ba tare da ya neme ta ba, hakan ya dada
tabbatar mata da lallai baya bukatar ta na shiga
rayuwarsa.
Juyawar da za ta yi ta yi arba da Suwaiba da
ke tsaye a bakin kofar falonta, Suwaiban na
tintsirar dariyar mugunta sannan tace, "Kai
shishshigi dai bai yi ba a rayuwa in banda rashin
zuciya na wasu matan, yaushe ne zaka yi ta bibiyar
miji yana wulakantaka ya na korarka amma don
jaraba gobe ma ba zuciya ki dawo ko dan irin jan
ajin nan na mata babu, jiya kin zo ya kore ki yau
ma kin dawo, to tuni ya fita don ba ya son ganinki",
Munecba sam bata iya fadi in fada ba shi ya
sa sai ta rasa me za ta ce wa Suwaiba, kawa sai ta
juya ta koma da tiren abincin dakinta ta hau sana'ar
da a yanzu ta fi iyawa wato kuka, sabo da bakin
cikinta daya ne yadda Suwaiba ta sani komai da ke
wakana a tsakaninta da mijinta, wato har zuwan da
ta yi dakinsa jiya da korar Karen da ya yi mata duk
ya gaya wa Suwaiba, in ma bai gaya mata ba to tana
bibiyc da al'amuran da ke faruwa a tsakaninsu.
A irin wannan yanayin ne Goggo ta zo
Gombe ta iske al'amuran gidan dan nata gabadaya
sun sauya ragamar komai na gidan ta koma hannun
Suwaiba, duk abin da tace shi ake yi a gidan, dama
ab nda Goggo da aminiyarta Hajiya Harira ke so
kenan to sun samu bukatarsu ta biya
140
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaría
Abu biyu ya soma ciwa Goggo tuwo a
Kwarya yanzu, na yadda Mujecb ya rage zuwa Dukku, sai dai in tana bukatar wani abu ta yi masa waya ya ce ta aiko Isah, kuma duk abinda zai bata ta hannun Suwaiba ake amsa don akwai zuwan da Isan ya yi da ya amshi sakon ya kaiwa Hajiyarta kayan sun ninka na Goggo biyu har da kudi cikin ambulan wanda Isan bai san ko nawa ba ne, sai da Goggon ta sa shi ya buda ambulan din ta ga kudi tsabar su dubu talatin 'yan dubu-dubu sababbi fil babu ko kari.
Wadannan kudi sun ciji zuciyar Goggo don
ta tabbata daga aljihun danta suka fito, amma ita gashi ko ficika bai aiko mata da shi ba, sai kayan abinci.
Abu na biyu dake damunta irin hidimar da ya ke yi wa Hajiya Harira, har Umrah ya biya musu suka tafi su uku, shi da Suwaiba da Hajiyar da ta yi
masa magana me ya sa bai biya da ita ba sai cewa
ya yi su ai ya biya musu Aikin Hajji sun je shekarar da ta wuce da Muneeba da babanta da Baffaninsa,
bai biyawa Hajiyar da 'yarta ba saboda ita ta taba
zuwa, Suwaiba kuma na shayarwa shi ya sa yanzu
ya biya musu umura tunda ita Suwaiba bata da ciki
ita abinda ya fi ci mata tuwo a akushi, si ne rashin
zuwa Dukku da ba yayi kamar da, a halm yanzu ya kan shafe fiye da wata bai zo ba, bata san wasa farin girke kenan ba kadan ta gani inji Suwaiba".
WATA KUSAN 2
****
Rahmatu Hassan Zaria
****** *****
Shirye-shiryen haihuwar Suwaiba shine abinda
Mujeeb ya fi maida hankalinsa akai kenan yanzun
da watan haihuwarta ya tsaya ma sai ya koma da
kwana dakinta kacokan ba tare da shawarar
Munecba, ita ma sai ba tace masa komai ba ta
kyaleshi tunda Hausawa na cewa kowa yayi nagari
yayi ma kansa, kuma ko wa66ata ya sani ko
wagygyara ya sani.
Tana zaune da wani yammaci ta ji
dawowarsa, sai da ya shiga gurin Suwaiba ya
dubata sannan ya wuce dakinsa ba tare da ya
waiwaye ta ba, idan da sabo ta riga ta saba da
wannan juyin baya da yà yi mata. Ta tashi ta nufi
dakin nasa don ta yi masa sannu da dawowa hakan
ce take kasancewa a tsakaninsu in ya dawo bai
nemi inda take ba to ita zata kaskantar da kanta ta
bi shi tunda ita ke kasansa kuma zamansa takeyi
hudubar da Inna Amina tayi mata kenan shi yasa
take amfani da ita.
Baffa ne ke rike a hannunta yana dan dagara
Tafiyarsa da batayi kwari ba, har süka isa dakin
Mujecbun yaron na gani Babansa ya saki hannu ya
fara gudu yana faduwa tare da murna zaije gurin
babansa. Ya taso ya tari yaron ya daukeshi, yana
cowa "My boy" tafiya tayi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 12