wayarsa ya ce idan sunje
ya nemishi ko da zai taimaka masa ta wani fannin
tunda yana da mata da 'ya'yansa.
Suna isa dakin da aka basu wanka suka yo suka
gabatar da salar da ke kansu, su ka yo odar abinci
suka ci suka koshi, sannan suka yi shirin tafiya
Ka'aba don su yi sallar Magriba da Issha'i a can su
yi dawafi kafin su dawo gida tunda a washe gari ne
Munecba za ta ga Likita da safe.
Muneeba ku san bakauyiya ta zama saboda
ganin kyawun kasar Saudiya wanda ke da tsarin
gine-gine masu kyau ga hasken lantarki lungu da
sako na ksar ko ina ka bi tamkar rana ba dare ba
saboda haske ga zirga-zirgar mutane a ko ina balle
idan kaje masallacin Madina ko na Ka'aba ba su
dawo masaukinsu ba sai kusan sha daya na dare, а
dalilin Muneeba ta makale tana ta dawafi tare da
zubarda hawaye a dawafi tana gayawa Allah
bukatarta don tun tana yi a zuciya har addu'ar ta
fito fili da kyar ya lallasheta, ya ce ta bari gobe idan
suka dawo sai ta cigaba.
Washe gari bakwan Safe a asibitin tayi
musu likita ya duba Munceba sosai ya basu wasu
gwaje-gwaje da za'a yi mata saboda yana son
tabbatar da lafiyar mahaifarta.
A ranar.duk aka yi mata gwaje-gwajen suka
it magunguna suka gaya mata ranar da zata davo
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
don amsar sakamako sannan ta sake ganin likita. Duk wasu abubuwa da ya kamata ayi an yi mata sakamakon ya nuna mahaifarta lafiya lau take ba ta da matsala wajen daukan cki a shirye take ta dauki cki ako wani lokaci idan Allah ya nufa wannan dalilin yasa shima Mujeeb said a suka yi masa gwaje-gwajen don ganin ko daga gareshi matsalar take tunda matarsa bata da matsala.
Nashi samakon shima ya fito irin nata,
komai nasa lafiya lau yake. Sun basu shawarar ci gaba da shan magunguna tare da sauraron lokacin
da ALLAH zai kaddaresu da samun ciki hankalinsu
kwance suka cigaba da gudanar da ibadarsu ba dare
ba rana sannan Mujceb ya soma nemar musu bizar
tafiya kasar Dubai don su shakata. Ana gobe zasu
bar Saudiyya zuwa Dubai da daddare suna zzaune
suna shan-shayi Munecba ta dubi Mujceb tace 'Wai
ya aka yi ka shirya mana tafiya Dubai, Alhali daga gida bamu yi shirin zamu Dubai ba? Ya kurbi
ruwan shayi ya lumshe idanu sannan ya, 'Yawon
Shakatawa zamuje kinsan Dubai tana daya daga cikin manyan kasashen Larabawa da ta zamo cibiya
ta yawon bude ido da Kasuwanci da Shakatawa ga Turawa, Larabawa harma da mu bakar fata, kuma
Kasace da ke da kyau sosai, ga baruwan wani da wani zaman lafiya yayi dirshan a kasar zamuje a
zaki gani sai kinji kamar mu yi ta zamanmu a can,
ba tsangwama ba mai sa ki kuka ko a gaya miki
21
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
maganar da zata bata miki rai balle gaki da
masoyinki, sai mun sha soyayya ta sati biyu a
Kasar sannan zamu tafi, In sha Allahu ba zamu
koma Kasarmu muba saida tsarabar Baby a
mahaifarki". “Ta yi murmushi ta ce, Allah ya sa
hakan ya tabbata don ni ina ji a zuciyata da jikina
kuma ina da yakinin Allah ba zai wofintar da
addu'arda rokon da muka yi ta yi masa ba ba dare
ba rana tamkar ma nasami cikin haka nake jin
jikina.
Sauri Mujeeb yayi ya aje kofin shayin da
yake sha ya janyo ta jikinsa ya zaunar da ita, ya
soma shafar cikinta yana cewa 'Lokacin al'adarki
yayi ne, Tace 'Bai yi ba ina ga sai nan da kwana
goma" yace ko kinji alamun cikin ne? ta ce 'Banji
komai ba kawai dai zuciya ta ce ke raya mini cewa
addu'armu ta karbu" ya ce "To ko mu je asibiti ne
tunda dare bai yi ba su duba ki don mu tabbatar
wallahi har kin san a soma dokin zan zama baba"
ta yi murmushi tana girgiza kai t ace "Ka bari har
in banga al'adata ba sai muje asibitin a lokacin
muna Dubai sai su duba ni.
A Dubai sun yi masauki ne a daya daga
cikin hotel mafi shahara a kasar Mujceb yayi haka
ne don su hole su wataya tunda abin da ya kawo su
kasar kenan, shi yasa ya saki bakin aljihunsa yana
son ne ya farantawa Muneeba rai ta san cewa zai
vin komai domin farin cikinta.
02
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
A kwana biyu da suka yi nan da nan fatar jikin Munccba ta sakeyin jajir tayi wani irin sheki wanda ta fara zargin kodai shigan ciki gareta sai dai ta kanyi saurin fatattakar wannan tunanin na zuciyarta don kada gasgata hakan ya yaudari zuciyarta ta sa ran samun abinda bata isa taba kanta ba sai in Allah ya kaddara zata samu.
A wani yammaci suka yi shirin su tsaf! Zasuje sayayyar tsaraba tunda baifi kwanaki uku ya rage musu su koma kasa Nigeria ba. Leshi ne a
jikin Muneeba riga da siket, sai ta kawo bakar abaya ta dora a bisa kwalliyarta, san nan ta kawo gyallen bayar ta nade fuskanta zuwa kafadarta tasa Pin ta matse gyallen saboda zamiyewa sai fuskar ta fara tas da tai luwai-luwai bako digon kurji fuskar kawai kake gani a waje ko ina ta rufe shi ruf, ta saka takalmi shim baki sawu ciki na (Toms) mara tudu ta fito tana rike da yar bakar jaka, tayi kyau tamkar wata Balarabiya er Kasar ta Dubai.
Shima MUjcebun yayi kyau cikin wani yadi dan asalin Indiya da aka yiwa dinkin (GOOD LUCK) aka hade halar ash da baki, idan ka gansu zaka dauka amarene a satin aurensu da suka zo
yawon shakatawa, don Mujeeb Makale matarsa yayi tsan a jikinsa a dalilin kallo da yag ana binsu
dashi, shine yake nunawa duniya ba Budurwansa bace matarsa ce ta Sunnah Halak Malak.
23
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Wani Shago suka tsaya suka yi sayayya mai
yawa, yana lura da ita duk abinda zata saya in indai
nata ne to guda biyu take diba a kala ne kawai ta ke
banbantawa, daya ta dauki mai haske daya mai
duhu, har dai ya kare ya tambayeta 'Wai ke dawa
kikewa sayayyar nan nc? Ta ce 'Ni da 'yar uwata
mana' Y ace 'Wa ce 'yar uwar taki? Ta ce Suwaiba
mana tunda na lura kai kanka kawai ka sani shi yasa
nima nake zabar mana namu "Y ace, "Au abin haka
ne Suwaiba ta fi ni shi yasa ko hankinci baki dauka
nawa ba ko? Ta сe, Haba Yallabai ka manta
kayayyakin dana zaba dominka a Saudiya kona
Dubai ne suka fi tsole maka ido, "Ya yi murmushi y
ace, "Ai zance yak are tunda naga kalar taki
Soyayyar kin fara mantani.
Ta rike haba ta ce, 'Ni na isa in mance
abokin rayuwata? Ai wallahi kaine komai nawa, yi
hakuri abokin rayuwa yanzun zaba me kake so, ya
make kafada tamkar wani dan yaro yayi magana
cike da shagwaba "Ni ke zaki zabar mini, ko ince
bana so, Gaba daya suka tuntsire da dariya har mai
shagon da bai san me suke cewa ba sai da ya tayasu
dariyar, har ya kare yana tambayarsu 'da Turanci
wai hala yawon amarci suka zo suka amsa masa
cewa eh yawon amarci suka zo yace Kai kun dace
da juna gashi kun iya soyayya don Allah kada ku
raunana Soyayyarku idan kun haihu naga haka kuke
vi mu kuwa Larabawa idan muka haihu da juna
24
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
lokacin ne muke kara son juna" suka cc Insha Allahu bazasu daina son juna ba".
Sun gama sayayyarsu zasu tafi sai Muneeba ta hango wani shago na sayar da kayan karau na mata wato danginsu Zinarai, azurfa lu'u lu'u da yakutu, sai ta radawa Mujeeb yayana ga wani shago can ina son in duba 'yan kunne da sarka na Gold yan Dubai tunda gamu a kasar. Yace "Daga yau fa na tashi daga yaya na zama abokin rayuwa, bana son yayan nan ai kowama ya san ni yayanki ne ko baki fada ba". Ta yi murmushi tace "Au kaji dadin Dubai ka canzawa kanka suna ko? Ya ce ke kika canza mini nib a ruwana kuma ma idan nace banji dadin Dubai da Saudiyya ba a wannan tafiya
ai nayi karya saboda nayi kyakkyawan amarcin da ban tabayin irinsa ba, don bazan boye maki ba
wallahi kin jiyar dani dadi da kulawar da ban taba
samun irin suba a rayuwata komai naki ya canza ko
zamzam din da kike sha kulum ne yasa nake jin ki
zam-zam kinga kuwa ai dole a canza min suna
tunda na samu Sauyin Sabuwar Rayuwa" Dariya tayi tana nuna shida da yatsa tace "Kai ko ka saki baki kana ta zuba kamar fanfon da ya lalace a gaban
mutane don kaga basa jin yarenmu ni dai mu tafi". Mujeeb ya dubi mai shagon ya nuna masa kayansu da ke cikin manyan ledoji irin na shagunan Dubai ya ce "Ga kayanmu zamu bari zamu shiga
wancan shagon sai mun dawo zamu dauka. Mai
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
shagon yace "Aik » baku gaya min ba idan kuka tafi
zasu davo iele kayanku babu abinda zai same
su don babu wanda zai taba mu haka muke а
Kasatmu idaa ka aje abu da izinin Allah inda ka aje
nan zaka zo ka ganshi ko da an kwana ne. kuje
kawai babu abinda da zai sami kayan ku",
Su Muneeba suka tafi suna mamakin
al'amarin wannan kasa da babu 'yan sane balle
'yan fizge ko 'yan yankan aljihu sabanin tamu
Kasar da komai ya tabarbare ba tsaro ba tsari, kowa
na yin abin da yaga dama tun daga na sama har
zuwa na kasa. Allah dai ya shiryar mana da
Shuwagabanninmu da mu na kasan ameen.
Nan suka bar kayan suka tafi shagon kayan
Karau. Rudewa da ruwan ido ne ya sami Muneeba
a shagon saboda ganin idonta taga rowan gwalagwalai da lu'i lu' wato (Diamond) da bata taba
ganin irin suu a idanunta wasi mata da suka tadda
shagou sune suka tayata ta zabi dan kunne da Sarka
da zobe sai awarwarokwana biyu tal amma masu
*sananin kyau da ban sha'awa aka auna rnata
kudinsu ya tashi a Dubu Dari Biyu da Hamsin, ta
sake cewa a dauko wani setia wanda kucinsa zaiyi
daidai dana farko amma disin dinsu ba i
'n tafi suna dubo mata ne Mujeeb ya kalleta ya ce,
wanda kikace a dauko kuma na waye" Tana
mumushi t ace, "Na Kanwata ne Suwaiba" ya dan
daure fuska ya ce, kice s varshi don wallahi bazan
26
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
saya ba, ai na gaya miki Goggo ta matsa mini said a
na saka mata hark ala biyu a kwati da irin wannan fan Duban da wani dan Saudiya amma aike ban saya miki ba shine ke yanzun zaki ce in kara siyan mata garamå in kara miki wani ya zama biyu kamar yadda na saya mata biyu amma wallahi b azan siyan mata ba.
Ta shagwar-gwabe masa hard a dan kukanta irin na yaron da ke tsananin son abu yana son sai anyi masa tace 'Haba abokin rayuwa don Allah ka
sayan mata na nan sun fi design ma kyau, kuma
nima ai ina da wani ko" y ace, kinga yanzun idan na siya maki wannan kowa na da bibbiyu kenan" Duk
inda ta 6ullo masa yaki ya sayi na Suwaiban dole ta Kyaleshi ya biya kudin natan kawai tunda ta san yafı ta gaskiya suka yi shatar taxi ta maidasu masaukinsu.
Da daddare suna zaune suna cin abincin da sukayi Oda na dare, sai ga Kiran Isah kanin Mujecb
ya shigo wayar Mujceb yana ganin kiran yasan Goggo ke son Magana dashi kuma bazai wuce akan Suwaiba ba don da ya kirata da safe take ce masa
bata ji dadl to kila ciwon yayi tsanani ne don a
muryanta ya gamo lallai bata da lafiya.
Yana daga wa yaji Muryar Isah na masa sallama, ya amsa tare da tambayarsa komai lafiya
ko tunda Goggo da Isah din suna gidansa na Gombe tun ranar da suka baro Nigeria a cewar
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Goggon bazai yiw a Suwaiba ita kadai ba sai wata
yerinya da Hajiy: r tat a kawo ta tayata zama ba
gara itama tazo su zauna tare sannan Isah ma yazo
don gida ba namiji akwai matsaia.
Yaawa Goggo wayar yana cewa "Ga
Goggo zakuyi magana" tana amsa bata amsa
gaiswar da yake mata ba sai cewa tayi 'Wai
A ujcebu wannan wane irin ganin likita ne yau
k ısan satin ku hudu a Saudiya kila sai kunyi aikin
laji zaku dawo". (Bai gaya musu sun wuce dubai
ba) sai ya ce, Nan da kwana uku zamu dawo Insha
Allahu kinsan gari ba kusa ba garamu gama komai
sannan mu dawo ai Insha Allahu muna sa ran an
dace koga irin dawafin da mukayi a Ka'aba muna
Lawai Allah kukanmu sanna ga kwararrun likitoci
sun dubamu dukanmu sunce babu mai matsalar
rashin haihuwa a cikinmu lokaci ne bai yiba shi
yasa hankalirunu ya kwanta yanzu shirye-shiryen
dawowa gida kawai mukeyi.
Gogge tare kai kam bukata ta biya a
gurinka addu'arka ta karbu ga suwaiban nan dauke
da cikinka dan sati bakwai, dazu muka je asibiti in
so samu ne gobe ka dawo don wannan abin farin
ciki yaci, ace kana kusa avi arin cikin tare dakai
ktayata jinya don bata da lafiya ar góut
e mu koma idan aman da take bai tsaya ba
z. kwantar da ita su sa mata ruwa". Yayi farin
ciki to amma yana tsananin tausayawa Munceba shi
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
in son samunsa ne ace Munecban ke da ciki ba
Suwaiba ba to babu yanda zaiyi da tsarin Allah,
amma yana mata addu'ar itama Allah ya bata.
Ya cewa Goggo “Allah ya sauwake zan kira
da wayarta inyi mata sannu sannan duk abinda kuke
bukata dangane da asibiti ga Isah nan zaije banki ya cire muku kudi sai kuyi amfani da su Allah ya bata lafiya sai da safe". Ya kashe wayar yana Duban
Muneeba, ta rigashi cewa "Waye ba Lafiya? Ya ce
'Suwaiba ce wai har sun je asibiti ance tana dauke da ciki na sati bakwai". Ta riko hannuwansa tana
mai cike da murna tace "Kai Alhamdulillah ai
wannan zancen ya wuce wai abinda muke nema ne
Allah ya amsa addu'armu tun bamu dawo ba ya
bamu aini wannan cikin tamkar a jikina haka nake jin murnar samunshi tunda ni za'a haifowa bebin
wallahi koni bansamu ba idan Suwaiba ta haifo
maka tamkar ni ce na samu, tun da abinda zatra
Haifa jininmu daya.
Kira wayarta muji ya jikin nata". Jikin
Mujeeb duk sai yayi sanyi ya kara jin tausayin
Munecban a ransa sam babu kishi ko bakin ciki ita
Allah bai bata haihuwa ba yaba 'yar uwanta sai ma
murna da doki takeyi za'a haifo mata bebi tunda
dama yayi alkawarin zai bata abin da Suwaiban ta
haifan kyauta ta rike in dai Allah ya kaddara ta riga
ta haihuwa. Kuma murnar da furucinta har zuci tayi
29
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hasşan Zaria
sune tsakani da Allah hakan halinta ne ya riga уа
sani.
Jikinsa a sanyaye ya kira layin Suwaiban
tana dauka yi masa Magana cikiu sanyin Murya
Kiris ya roge ya ta saka masa kukan Kisisina
saboda ta matsu ya dawo ya ce, "Ya jikin naki?
Gorgo ta gayamin sunce cikine to Allah ya baki
lafiya sai ki dinga daurewa kina cin abinci saboda
abinda ke cikinki kuma cin abincin ko yaya ne zai
rage miki wahalar ciwo ya baki kuzari sosai kina
jina ta ce Eh ina jinka zanyi kokari, amma idan
naci amai nakeyi ko ruwana sha sai nayi amai”. Ya
ce haka nan zaki dinga daurewa ga Auntynki zata
gaisheki da jiki ya mikawa Munecba wayar ita ta
soma gaida Suwaiba ta kara da cewa, "Sai mukaji
abin farin ciki to Allah ya albarkaci abin da za'a
haifo, ke kurna Allah baki lafiya ki daure ki dinga
cin abincin don a lhaifo mana Bebinmu kato, idan
kika haifo лana dan Kuculi ba zamu yarda ba gara
kawai ki daur ki dunga cin abinci da yawa."
"Mhm" kawai tace saboda ba haka ta so Muneeba
ta amshi al'amarin cikin ba, ita kam koda tazo
gidan a baya ace MUneeba ada ciki ita bata dashi
ana jin ranar sai ta kusa Ladiye zuciya saboda
di ciki, ammına ita sai gashi murnama akeyı wata
2ta haitowa mijinta da, Allah yasa ba Kisisina
Lae dama Goggo tace balinta ne baka taba ganin
30
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
bacin ranta akan abin alherin wani ta iya duniyanci tamkar tsohuwar Karuwa
Babu wani almashi a kalaman da take
mayarwa Munecba, shi yasa Munecban ta datse hitar tasu tunda ta lura tamkar ta matsawa Suiwaban
ne bata son Surutu a yanda take amsa mata a dakilė
tana cikin zafin ciwo ne, bata san haushine ya tabi zuciyar Suwaiban ba kuma haushinma ita muneeban ne tunda bata nuna kishi da haushin Suwaiban ta sami ciki ita bata samu ba.
Mujeeb tashi yayi tsam daga inda yake
zaune ya dawo kusa da Munecba, ya zauna yasa
hannu ta bayanta ya riko kalauunta ya rungumeta a
jikinsa ya soma yi mata Magana cikin kulawa da
tausayawa a sanyaye". Muneeba kiyi hakuri kullum
addu'ata da fata inga na fara haihuwa dake sai gashi
Allah bai nufa kece zaki fara Haifa min 'ya'ya ba watanki ce zata fara haifamin to ki dauki hakan
amatsayin wani iko ne na Aliah da mutum bai isa
ya chanza shiba amma kamar yadda nayi miki alkawari idan Suwaiba ta haihu na baki abinda ta
Haifa duniya da lahira, itama zan gaya mata ko da
na mutu kafin ta haihu to abinda za ta Haifa naki
ne". Hawaye ne ya soma zarya a kumatun Muneeba
ta soma magana, wallahi ni bana kaico ko in nuna damuwata `akan Suwaiba ta haihu ni ban haihu ba,
tunda nasanbawai Allah ya manta dani bane, yana
sane dani to don me zan nuna masa garnjen hakuri
31
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
nada gazawar hakuri na alhalin bansan hikimarsa ta
hanani haihuwar da yayi ba. Kuma ba tilaswa
Suwaiba zakayi ba wajen yardanta ka bani abinda ta
haifa, kabi abin cikin hikima don ba dole bane su
Goggo su yarda gara inma zaka bani to muyi abin
cikin hikima babu maganar tilastawa.
Ranar Kwana sukayi yana lallashin
zuciyarta cikin tausayawa da dadaddan kalamai
duk daba wai ta damu bane amma shi sai abin yana
bashi tausayi kuma hakan da ta yi ya kara masa
kaunarta tare da wani matsayi mai girma a
zuciyarsa.
****** ******
Sun dawo Kasarsu lafiya sun tarar jikin Suwaiban
ya danyi sauki har tana dan iya cin abinci, amma ba
da yawa ba sannan ba kowane abinci take ciba. Ta
rame sosai tayi fari duk daba fara bace, daka ganta
kaga mai shigar ciki sai zuba shawagaba takeyi
tunda iyaye sun yayyabeta ga Goggo ga Hajiyarta
itama tazo jinya, kasancewar abun nema ya samu
matar falke ta haifi ja ki jira kawai suke Mujeeb ya
dawo suga irin murnar da zai yi tunda neman
haihuwa yake ido rufe bai samu ba, gashi nan ma
har wata kasa suka tafi don maganin neman
haihuwar, sai gashi wadda ta zo kwanan nan ita ce
Allah ya ba wadda ta dade din ba.
32
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Murnar da ya nuna ba yabo ba fallasa, su kansu abin ya daure masu kai kuma ya basu mamaki to amma fa ya nuna damuwarsa akan ramar
da ya tarar tayi don zama sukayi suka tasa ta gaba shida Muneeba har Muneeban ta kawo shawarar ya kamata a koma da ita asibiti ko akwai wani abu da zasuyi mata tunda har yanzu tana aman kuma bata cin abinci sosai.
Kamar dama jiranta Goggo take yi, ta na
gama kalamin kai Suwaiba Asibiti Goggon ta dirar
mata, Babu wani asibiti da za'a kaita, ai munje babu abinda suka tsinana mata sai da muka dawo
gida aka yi mata jike-jike sannan ne ta fara samun
sauki babu inda za'a kaita, shi sauki an sai
hankali ake samunsa cuta ce ke shiga farat daya.
a
Tunda Goggo tace haka Muneeba bata sake
maganar kai Suwaiba asibiti ba da daddare
Muneeba tana shirin bacci ne Mujeeb ya shigo yake
mata sai da safe wai Goggo t ace tunda ya dawo sai
ya amshe su jinyar da suke yi ya dinga kwana da Suwaiba. Muneeba ta ce 'Ai ya zama dole ka dinga
kwana da ita, tunda bata da lafiya su Goggo ai sun
nasu kokarin ba za'a bar mana tsofaffi da jinya ba
sanda kuka yi abinku basa ma gurin”. Ta mayar da abin wasa saboda ta lura ya shiga damuwa akan
wannan tsari dasu Goggo suka shirya su a nufinsu zaiyi ta kwana gurin suwaiba har sai ta warke, ita kuma Muneeba tayi alkawarin Insha Allahu ba zata
33
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
nuna damuwar komai akan haka ba in dai don su
kwareta suka yi to ba zata nuna an kware tan ba
zata bisu a duk yadda suke s.
Tun daga ranar sai ya kasance Muneeba
bata da rabon kwana a gidan Suwaiba ke da kwanan
duka, amma girki Munceba keyi tsakaninta da
mijinta sai dai da rana dare nayi zai kasance a dakin
Suwaiba tunda bata tashi amai da numfarfashi sai in
taga ya dawo daga Offis amma da zarar ya fita da
safe zata yi wanka tayi kwalliya ta fito dakin
Goggo su hadu da Hajiyarta da Goggon suyi ta hira,
har kyakyale dariya, zakaji tana yi ita dai Muneeba
ba ta kawo idanu ta zuba musu taga iya gudun
ruwansu, tunda duk wani lanbo da Kissa su suke
shirya mata-yadda zatayi gashi nan kuma sun sami
sa'a a kansa tunda har ya biye musu yana danne
hakkin Muneeba ba tare da damuwarsa ba ita kuma
ta dukufa kaiwa Allah kukanta akan wannan
danniya da Mulkin Mallaka da ake yi mata babu
halin tayi Magana.
A wata safiya jikin Suwaiba ya matsa mata,
suka shirya da Hajiyar ta da Goggo su ne 'yan
rakiyarta zuwa asibiti Mujeeb ne zai kaisu, sunje an
duba ta aka rubuta magunguna sai ya dawo dasu
gida yace idan ya fito zai sayo maganin ya bayar a
kai masu. Suna shiga dakin Munceba ya isketa tayi
wanka ta saka kaya tana tsaye gaban madubi tana
gyara daurin kallabinta.
34
WATA KUSAN 2
Rahmatu Hassan Zaria
Yana shigowa ta soma tambayarsa "Lah" kun dawo ne? sam ban ji tsayuwar mota ba ya mai jikin ya ce gata can taji sauki Lanbo ne kawai ki kyaleta, Likita ma ya gaya mata ta dinga motsa jikinta tace, Kai abokin rayuwa wane. irin Lambo
don dai cikin ba a jikin ka yake ba da munga irin
naka Lambon ya janyota suka fada kan gado yana
cewa "Zo nan kiji tawa larurar wallahi nima bani da
lafiya". Ta ture shi tana cewa 'Don Allah sake ni
kada ka yamutsa min kwalliya ciwon me kake yi, Y
ace Ciwon rashinki nakeyi wata daya ai ba wasa ba,
na takura da wannan jinyar ana daukan hakkinmu
yau kam ba zan iya ba na azabtu da rashinki.
Abinka ga masu kewar juna ba musu ba
gardama ta sakar masa jiki, suka soma wasassinsu
na ma'aurata, sun kai kololuwar wata duniya ne
suka ji ana buga kofar falon Muneeban bugu mai
karfi bana wasa ba da kyar suka lalubo hankalinsu
da ya gushe suka saisaita shi sannan Mujeebun ya
tashi da kyar yana rangaji zai fita sai kuma ya dawo
domin a yanayin da yake ko waye zai iya gano
halin da yake ciki ya dawo ya dubi Muneeba ta
tallabe kanta tana jingine da allon gado ya ce, "Je ki
gani ko waye, in Goggo ce kice ban shigo ba" zata
yi magana ya daga mata hannu alamar ta yi shiru ta
bar maganar. Ta tashi ta suri dankwalinta ta daura
sannan ta je bude kofar falon, ilai kuwa Goggon ta
gani tsaye, ta dubi Muneeban ta ce 'Mujcebu yana
35
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ciki ne? muna nan muna jiranshi ya zo yaje ya siyo
wa Suiwaba magunguna ya shanyamu". Muneeban
ta ce "Bai shigo ba, ni ban ma san kun dawo ba,
sannunku ya mai jikin" Ran Goggo ya baci ta amsa
a dakile 'Da sauki" ta juya ta koma tana sababi.
"To ina ya shiga ga motarsa a waje dakinsa kuma a
kulle ita dai Muneeba ba tace komai ba ta biyo
bayan Goggon zuwa dakinta don ta duba jikin
Suwaiban tunda dama nan ne dakin jinyarta.
Da Muneeba ta dawo ta zo ta zauna a gefen
gado da yake kwance lakadan abinsa ta dube shi ta
ce, Goggofa na nemanka ashe jiranka suke ka
siyowa Suiwaba magani shine kazo nan ka kwanta,
don Allah ka tashi ka tafi kada ka jawo mini laifi ni
babu ruwana.
Kansa na jingine da gado yana kallonta har
ta gama maganar ta sannan ya ce je ki rufo kofar
falonki da key kizo in gaya miki matsalar da nake
fuskanta a 'yan kwanakin nan, ina fatan zaki
magance mini su ba zakibi sawun masu sani cikin
wata matsalar ba".
A tunaninta wata gagarumar matsalace ta
same shi duk sai jikinta yayi sanyi da saurinta taje
ta sawa kofar makulli ta dawo ta zo ta zauna kusa
dashi tana cewa 'Wace irin matsalace kai kuwa ka
shiga da har ka kasa gaya mini tun tuni sai yanzun
ne zaka gaya min", ya kai hann ıwansa duka biyu
ya rungumota zuwa jikinsa yana cea, ki bani
36
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
lokacinki ko yaya ne in dan sami natsuwa, sai inyi miki bayani matsalar tawa". Zata yi magana yasa bakinsa a nata ya hadiye maganar da take son yi, cikin kwarcwa irin tasu ta nagartattun maza da sukan mantar da matansu duk wata damuwa ta
rayuwa ya bi ya shagaltal da ita da wasanni irin na
ma'aurata hakan yasa ta manta da komai ta rungumi mijinta itama dama tana bukatar abinta daga ita har
shi jukkunansu rawa yake yi saboda kewar junansu,
sai da ya sami natsuwa ya tabbatar ya samu
gamsuwa irin yadda yake so sannan ya sassauta
mata amma duk da haka yana rungume da ita tsamtsam a jikinsa ya sauke ajiyar zuciyar a hankali dalilin natsuwar da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 12