ta saukar masa.
Sai da ya natsu sosai sannan ya tashi ya
shiga bayinta yayi wanka a lokacin ita hr tayo nata
wankan tana zaune tana busar da gashinta da (Hand
Dryer) yana fitowa ya dubeta yana murmushi yace,
'Meye naki na busar da gashi? Ce miki nayi na
sallameki? To ni yanzu ma da na yi wanka sabon
karfi ne ya zo mini..Ni fa yau ina dakin nan sai
yamma zan fita.
Ta marairaice murya, 'Don Allah ka yi
hakuri kaje ka siyowa Suwaiba maganin, kasan dai
bata da lafiya, "ya dan kanne ido ya ce, Nima
ciwon ai ta jawo mini na rashinki kusa dani na wata daya, amma yau na warke garau tunda na samu magani, zanje in sami Goggo anjima bazai yiwu a
37
..aanon 7aria
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
cigaba da danne miki hakkin kwananki ba ana
kwararki sam bazai yiwu ba". Ta yi saurin cewa,
"Ni fa in don nice don Allah ka bar wannan
maganar na yafe har sai ranar da Suwaiba ta warke
garau" ya hada gira ya ce, wannan kawaicin naki na
cutar da kai ni ba zan yarda da shi ba, ni kina cutata
kema kina cutar kanki yanzu dubi yadda jikinki ya
dinga rawa da gani an san kina cikin bukatar
kasancewa da mijinki amma saboda kawaici kin
daure kina cutar kanki, to bazai yiwu ba daga yau
zan kashe wannan tsarin nasu tunda ba Shari'a bace
Muneeba ta ce “Au sharrin da zakaimin kenan wai
ina bukatarka har jikina na rawa, wato don na
tallabi bukatarka shine zaka yi min tsiya ko, in
halinka ne gobe ma zaka dawo, na daina rawar jiki
akan bukatarka zakaga irin amsan da zanyi maka ya
janyota ya rungume yana lallashi yi hakuri kada
kiyi min abinda zan gwammace bin kawo kaina da
bukatata gareki ba, ni kuma gashi daga yau na
daina hadiye kwalamata a kankihaka kurum ni da
halas dina ansa ni ina hadiyaryawu ai an yi an
gama. Miko min rigata ma ki gani inje in siyo
maganin nan in dawo ayi wacce za'a yi?.
Ya amshi rigar ya saka ya dan taje sumar
kansa dake kwance Lamban, ya gyara tsaf sannan
ya zura takalminsa yace zoki budemin kofar baya in
fita kuma ki sani yau anan dakin zan kwana
kadama Goggo ta tambayeki kice kin yafe
38
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
kwananki don wallahi nib a zan yafe maki ba, ai an gaya mini ina fita take yin wanka tayi kwalliya ta fito fakin Goggo suna hira suna dariya sai na dawo
ne take langabewa ita ga mai laulayi, kyale ta kawai nake yi".
- Muneeba ta rike haba cike da mamaki ya aka yi ya san abinda ke faruwa t ace "Kai
ammamutane da a ido suke, yanzu waye ya gaya maka wannan maganar?" ya ce 'Ina ruwanki da
wanda ya gaya mini tunda ke kinki gaya mini, ana yi mini ha'inci kun yi gum da bakin ki. Ta ce, "Ni
babu ruwa na yanzu kada ka fiddo maganar nan don
cewa zasu yi ni na fada al'alin ba nib ace, gara
kawai kabar maganar?.
Ya amshi makullin kofar ya bude ya fice ta baya, ya zagaya ya shiga kotarsa ya tada ta ya fice a
gidan. A daidai lokacin Goggo ta daga labule tana
kallon ficewarsa cik da mamaki, sannan ta juya tana duban Hajiya Harira t ace "Dubi yaron nan she
yana cikin gidan nan amma da na tambayi matarsa
tace bai shigo dakin taba lallai yarinyar nan
munafuka ce sai nayi maganinta, ita ga jarababba ko? Hajiya Harira tayi wani murmushin takaici tace, "Ai yarinyar nan sai kin tashi mata tsaye don
na lura ta kama miki da a hannu komai fa za'a yi a
gidan nan sai da amincewarta". Goggo ta yi kwafa
ta ce, sai na tashi tsaye ko sai mun tashi tsaye, ai abin da ya shafeni shine zai shafeki, tunda idan ta
39
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
mallake mujeebu tana juya shi yadda ranta ke so
kinsan Suwaiba ba zata kai labari a gidan nan ba.
Ni na rasa irin wannan jaraba wato tunda na hana
shi kwana a dakinta shine zaiyo satar hanya da rana
ya lallaba ya shige suyi abinda zasu yi sai tashin
motarsa kawai mukaji. Kyale almuri zai dawo ya
same ni, in banda taci darajar Suwaiban kada in
kwareta dana sa tsidugu ya hana a bar aiki sai inga
karyar jarabar ta". Hajiya Harira ta ce, "a'a kada ki
yi haka ko don Suwaiba din amma ai za mu iya sa
ya yi mana dan baka duk ranar girkin ja'ira mu
dana ba zai iya aikin komai ba. Ko ya kika gani?
Goggo ta yi dariya tace haka kuwa za'a yi aminiya
ai mu kowacci tuwo da mu miyar ma bai sha ba
balle ya ci tuwon. Sai dai ba yanzu za'a yi ba kin
san bata da kwanan girki sai mu bari sai idan ta
soma kwana da mijin sai mu yi mata lalata 'yar
tselen uwa jarababba suka sheke da dariya suka tafa
ita kam suwaiban tana kwance tana jin tuggun
iyayen nata wanda hakan da suka shirya yayi mata
dadi, dama kishí na ta nukursutarta tunda taji sunce
gashi ya fito daga dakin Muneeban har suna fallasa
abin da yaje yi dakin, sai take jin tamkar taje ta
shake Muneeban don haushi, itafa in son samunta
ne ace Mujeeb nata ne ita kadai babu wata mace da
zata rabar mata shi, saboda shi kyakkyawa ne na
shiga taro, gashi gwani ne gurin iya soyayya, ya iya
tarairayar mace ya mantar da ita duk wani bakin
40
D
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ciki na rayuwa ya san hanyoyin faran ta wa mace rai da yadda zai jiyar da mace dadi ta ko wane fanni, sai dai Kash! Duk wannan jin dadin da tarairaya tare ake raba mata da wata ita kam duk hanyar da zata bi sai abubuwan nan sun zama ita kadai ake wa, ba tare da wata ba.
Ta ja dogon tsaki tayi juyi saboda takaicin
Mujeeb ya je dakin Munecba kuma ta san mai yaje yi tunda daren yau sai da ya neme ta taki yarda dashi a dalilin ta nemi wasu kudi masu yawa bai bata ba wato shine ya kai bukatarsa ga matarsa lallai sai sun sa musu ido ta yadda bazai sake fakar
idanu ya je can ya yi wani abu ba (Kun ji fa karfin hali jama'a mutum da matarsa).
Bai dade da barin gidan ba ya dawo dauke
da ledar magunguna da ya siyo ya shiga dakin Goggo sai ya iske ita kadaice, Suwaiba da Hajiyarta
suna can dakinSuwaiban. Ko amsar maganin bata yi bat a rufe shi da fada 'Wato ka mayar da mu shaka tafi kana jina na je dakin Muneeba neman ka
ashe kana ciki kayi bülun bukui ta fito tace baka
nan ita barama na ganka ba, in ita bata maida ni a
bakin komai ba kaima sai kabiye tata to ka kyauta
tunda kayi yanda ranka ke so ni ka bata nawa ran
"ya zauna kusa da Goggo yana cewa "Wai nema na kika yi tayi a gidan to ai ni fita nayi gurin bako a
waje ina shigowa na shiga mota na tafi siyo maganin ita Muneeba ma bata san na dawo ba, can
41
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
kika je nema na?. ta gyada kai, can naje mana ai na
dauka kana can, ashe ba karya tayi min ba, sai ka
dauki maganinka kai mata tana daki.
Har ya mike sai ya dawo ya zauna ya ce
"Yawwa Goggo dama ina son muyi wata magana".
Ba tare da ta kalleshi ba ta ce, ina jinka ya rage
murya, "Ga ni nayi tunda suwaiban ta sami sauki
kuma ga Hajiyarta zan dinga yin kwana bibbiyun
yanda nake yi a dakin kowaccensu". Goggo ta
gyada kai ta ce 'Yaushe ne Suwaiban ta warke? Ina
ce jiya ciwon tashin ya yi har muke je asibiti yau
shine za ka kawo min wata tsirfa kokuwa ita
Muneeban ce tace bata yarda ba? Ya ce "Ba ta ce
haka ba nine dai naga dacewar hakan sabo da
gaskiya an shiga hakkinta ina tsoron Kada Allah ya
kamani da laifin na zalunceta". Ta ce to Meye abin
zalunci anan inace da yardarta aka zartar da abin
nan amma yanzun don munafunci zakace ana
zaluntarta. To shikenan kaje kayi ta kwana a
dakinta muna sa'ido muga abin da kwanan da take
so zai tsinana mata, bakin ciki ne sai ya kasheta, ita
ta hana kanta haihuwa wata tazo ta samu kuma bata
isa ta hana ba, sai na rike danka nayi masa rawa a
gidan nan yace "Goggo addu'a zamu yi itama Allah
ya bata don rashin haihuwa wallahi ba daga gareta
bane daga Allah ne kuma Insha Allahu zai bata
Muneeba ai 'yar kice duniya da lahira bai kamata ki
so wani fiye da ita ba".
42
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Tayi magana da zafin zuciya a kakkaushe, "ba zan so ta ba sai kazo kasa ni na sota, ita da
uwarta ai ba sona suke ba, basu mai dani wata tsiya
ba ki ya sa nima, na watsar da zumuncin na kama
masu sona, Hajiya Harira ai ta gama min komai
kaima ta gama maka komai har ta aura maka
diyarta gashi yanzun kana zaune lami lafiya har ga
karuwar zuri'ah nan ya baku, zuri'ah ma ba'a san
iyakarsu ba tunda yanzun za'a soma, ai kuwa dole
in sota ita da uwarta.
Mujeeb ya raunana murya yace "Shike nan
Goggo kiyi hakuri Allah ya huci zuciyarki". Tа се
kaine abin aba hakuri tunda an ta6o gimbiyarka ka,
mma ni ai banji haushi ba kuma babu abinda zai
bani haushi akan Muneeba, so ne baka isa ina nan
ka nuna kafi son ta da Suwaiba ba tunda bata fi
Suwaiban da komai ba a gidan nan sai ma suwaiban
da ta fita tunda itace tazo da albarkar haihuwa,
Ganin idan yaci gaba da zama a dakin zancen Goggon zai fi haka nuni kuma Muneeban na iya
shigowa ta riski maganganun Goggon kuma ko ta shigo Goggon ba fasawa zata yi ba, saima abin da zai karo shi yasa ya mike tsam ya ce "shi kenan Goggo ayi hakuri ni zan koma offis". Ta се " А
dawo lafiya kada ka manta ka siyoa Suwaiba Kankan. da Abarba har da mangwaro dan juyo yana duban Goggo yace Ni yanzun ban san indan zan sami mangwaro ba tunda ba lokacinsa bane"
43
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Та се "Ка dai dudduba ko ka aika kila a samu,
kasan mai ciki da kwadayi, ya za ka yi tunda Allah
ya baka abin da kake nema shekara da shckaru.
Ya juya ya fita yana cewa "Allah yasa a
samu sai a siyo mata". A ransa yana kakabin yadda
Goggo ta dauki son duniya ta dora akan Suwaiba
balle 'yanda take da ciki ko yaya tai wani motsi sai
tayi mata sannu tare da tambayar ta mene ko me
take so in kuwa shagwabar ciwonya ya tashi to
Goggo hart a kanfi Hajiya Harira nuna damuwa da
ciwon koda yake ita Hajiyar ta san Lanbon 'yar ta
duk da dais u ne suke kitsa mata komai har yadda
zata marairaice cikin ciwo idan Mujeeb din yana
gida, amma sam bata nuna kulawa ga 'yar dan
uwanta yadda kason ba su hada alakar komai ba
haka take nunawa Muneeba duk da yake ita
Muneeban na yi mana tsananin kulawa a matayin ta
na Goggonta kuma sirikarta amma Goggon wannan
sam baya birgeta illama idan ta yi wani abun don
kyautatawa ta rikideshi ya zama rashin kyautatawa,
shine yasa Muneeban ta ja baya da yi mata wasu
abubuwan kyautatawa tunda Suwaiba tazo gidan
duk dadai ba dainawa tayi ba alhalin kuma ita
Suwaiban bata yi, kamar yi mata wanki, da goge
mata kaya, duk da akwai mai wanki, sannan ta
share mata daki ta gyara shi tsab ta sa turaren wuta
yayi ta kamshi, idan kuma tasan Goggo nason wani
avu ko da bashi ta dafa a gidan ba zata sake shiga
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
cikin kicin ta girka mata, ko wajen tarban baki da jama'arsu na Dukku Munceba ce kan gaba wajen kyautata masu, amma Goggon duk bata gani, ita dai burinta shine ganin gazawar Muneeba tafi son a
yabi Suwaiba. Wannan al'amari yana bashi mamaki yadda zumunci ya lalace yanzun kowa nasa ya sani
ba'a son 'ya'yan ‘yan uwa sai mutum ya nuna yafi
son bare kiri-kiri akan dan uwansa (Allah kasa mu
gyara mu'alamarmu ta zumunci Allah ka bamu
ikon son zumunci da son 'yan uwanmu na zumunci
amen, kada ka bamu ikon cutar da wani ma balle
mu cuci dan uwanmu na jini amin).
Bai shiga dakin Muneeba ba Ofis kawai ya
wuce don idan ya shiga zai karawa kansa da ita
wani laifin ne. Da dare ya dawo a dakin Goggo ya
iske su suna cin abinci amma babu Muneeba,
Suwaiba na nan kishingide tana ta yatsina ga kayan
abinci nan birjik a gabanta. Bayan ya gaida su
Goggon sai ya juya yake tambayar Suwaiban 'ya jikin na ki" ta yi wani far da idanu ta juya su wai
nan duk alamun tana jin jiki ne tace, "Jiki da sauki
ya ce kinci abinci ko? Ta girgiza kai. Goggo tayi farat tace "Kasan bata cin tuwo bata son shinkafa to
tuwo yau akayi tunda an san bata so". Mujeebu
yace "To ai Goggo kinsan ka'ida indai 'kina gidan
nan da dare tuwo ake yi tunda kinfi sce shi, itama
Suwaiban ai naga tana cin tuwon". Ta ce "In wa
tana ci to yau dai bata so sai a san abinyi".ya turawa
45
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Suwaiban ledojin da ya shigo dasu ya ce "Ga
abarba da mangwaron nan an samo sai ki sha, ga
gasassar kaza nan tunda bakya cin nama sai kici".
Ta sa hannu ta ja ledar tana dubawa, shi kuma ya
mike ya fita zuwa dakin Munceba.
A kicin ya hangeta tayi kwalliyarta da wata
doguwar rigar shadda Galila ya lallaba ya damke
kugunta ya rungume ta, tayi kara saboda tsoro tace
"Subhanallahi, haba abokin rayuwa wallahi ka ban
tsoro' Ya cusa kansa cikin wuyanta yana jan
numfashi ya ce, "In banda abinki wa zai cafke ki ya
rungume in ba ni ba me kike yi ne a kicin zaki 6ata
min kwalliya? Ta ce wallahi Suwaiba ceta ki cin
tuwo ni ban son kuma yanzun bata son tuwo ba,
shine nake mata faten (Arish) dankalin turawa da
hanta ina ganin zata iya ci tunda ruwa-ruwa ne.
Ya kara rungumeta cike da taiusayinta a
zuciyarsa na irin wannan hidima da take da
Suwaiba kuma tsakani da Allah takeyi amma su
Gogo basa gani y ace "Allah ya baki ladan abinda
kike yi dominsa, ya baki abin da kike so a duniya
da lahira, amma ki daina wahalar da kanki don
yanzunma wannan da kika yi ba Karamin aikinta
bane ta ce shima bata ci". Tayi murmushi ta ce ko
ta ce bata ci bazan damu da wahalar dana sha ba
tunda masu ciki suna fama da irin wannan larurar ta
rashin son cin abu kaza da kaza ni babbar matsalar
La da ta kwana da yunwa kasan babbar matsala ce
46
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ga jariri idan uwarsa ta kwana da yunwa" ya ce Ba
zata kwana da yunwa ba tunda ga su kankana can
da mangwaro da ta ce a siyo mata na kawo mata ko
su tasha ai zasu rikcta har gobe".
Suna nan suna hira har ta gama ta juye a
filet yadda zai huce sai tiririn kamshin dadi ke
tashi, kai da ganin faten kasan zai yi dadi sosai
tunda ya ji zallan hanta. Mujeeb ya dubeta ya се
"Raina ya biya ni ba za'a sammini ba? Та се,
Gaskiya banyi da kaiba, tuwonka na can bisa tebir
wannan don mai ciki nayi shi ita kadai, sai ka bari
idan ta rage sai a baka"
Ya gyada kai ya ce, 'kwarai yanzu dai na
lura kinfi kula da al'amuran Suwaiba akaina,
shikenan nima zan rama" tayi gaba dauke da Filet a
hannunta tana cewa, "Allah ba zaka iya ramawa ba,
sai dai ka rame".
A tare suka shiğa dakin Goggo ta wuce har
gaban Suwaiba ta aje mata Filet din tana cewa "Ga
fatan dankali da hanta nan nayi maki shi ruwa-ruwa
yadda zaiyi maki dadinsha" Suwaiba ta dubi faten a
yamutse ta ce "B azan iya sha ba nasha abarba da
mangwaro sun isheni" Muneeba ta risına gaban
Suwaiba tana lallashinta, tana jujjuya faten da
cokali don ya huce tana cewa Ki daure I sha ko ba
yawa, gara ki dinga cin abinci balle irin su hanta da
dankali za su saki dinga jin karfin jiki.
47
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo tayi karaf ta ce "Ke kuwa da naci
kike tunda tace bata sha ki kyalcta mana sai kace
dole, ina dalilin wannan naci ko so kike tasha ranta
baya so ta kwana tana amai" Ba Munceba ba hatta
Mujeeb sai da ranshi ya baci akan wafannan
surutan na Goggo, amma sai basu nuna ba, Mujceb
mai sai ya maida abin wasa don ya gusarwa da
Munecba bacin ranta ya dauke filet din ya soma
sha yana cewa," Ai ni gara da kika ki sha tunda kin
ki sammani wai sai dai idan kinsha kin rage sannan
kya bani, tunda ni an watsa ni a kwandon shara ke
kadai ake tattali a gidan nan?
Ya dibi faten da cokali ya kai bakinsa ya
tauna ya hadiye ya lumshe ido ya ce "wonderful!
Yarinya dadi ya barki wallahi, kin kuwa ji dadin
faten nan gaskiya zaki cuci baby na in bai sha faten
nan ba, oya bude bakinki in baki, da yake Hajiya
Harira ta fita Goggo da Muneeba ne a dakin sai ta
bude bakinta ita a dole miji na soyayya da ita gaban
kishiya, don taba Muneeba haushi ne ya sa ta bude
bakin bata san shi kuma yayi haka ne don Munceba
taji dadin wadda tayi abu dominta tasha ba.
A haka yayi ta bata suna sha tare, Muneeba
na musu dariya, har suka shanye, ai dole ta shanye
tunda yayi dadi girki ne na kwararru ba irin nata na
'yan kwiya ba nan dà nan ayi girki a gama sannan
b bu wani dadi Goggo dai tana gefe tana wa
Mujecou tsiyar bashi da kunya a gabanta yake ba
X
WATA KUSAN 2
3
Rahmatu Hassan Zaria
matarsa abinci a baki mujceb yana barin dakin Goggo, dakinsa ya wuce yaje yayi wanka, ya gabatar da Sallar Isha'i da shafa'i da wutiri saboda
bai samu jam'i ba, ya yi shirin sa tsaf! Ya nufi dakin Muneeba ya iske har yanzun bata koma dakinta tana dakin Goggo sai ya haye gadonta yayi kwanciyarsa yasa hannu ya latse fitíla mai haske ya bar mai duhu ta bacci.
Bai dade da kwanciya ba Muneeban ta shigo, yana jinta ta mayar da kofarta ta rufe, ko da
ta shiga dakin baccinta taga fitilar bacci bata dauka
wani ne ya kunnaba sai tayi tunanin ita ta kunna kafin ta fita, kawai sai ta wuce bayi tayi abinda zatayi ta fito yana kallonta ta hau abin sallah ta
kabbara sallah har ta gama duk yana kallonta.
Ta cire kayan jikinta ta saka 'yar guntuwar rigar bacci sannan ta haye gado ta soma karanto
addu'ar kwanciyar bacci, har ta yi ta gama bata fahimci da mutuma dakin ba sai da taji alamar
saukar numfashi ne tatsorata, ta yi saurin kai hannu
ta kunna fitila mai haske, kawai sai taga mutum
kwance lakdan yana kallonta cike da murmushi a
fuskarsa ta sauke ajiyar zuciya itama idanunta a
kasan tace, Kai abokin rayuwa ka tsorata ni sosai
yaushe ka shigo dakin nan? Sannan me ya kawoka
har ka haye mini gado ka kwanta? Ni dai so kake
kawai ayi ta dora mini laifi a gidan nan, ana ce min jarababba wai ni nake jawoka da ire-iren kwalliyar
49
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
da nakeyi" yayi dıriya yana girgiza kai yace "Ai ni
ya kamata su kira jarababbe tunda nine nake biyoki,
haka akeso mace tayi abin da zata janyo hankalin
mijinta gareta, kinsan Allah nu jan bakin nan da
kika sa yayi miki kyau nake ta kallo Allah ya so
kima ban tsotse shi a dakin Goggo ba don wallahi
ina kallon bakinki ne ina dada tsuma yau in ban
tsotsa bakin nan ba ai sai na kwana ina mafarki da
sumtatu shi yasa na nunawa Goggo gazawata tunda
rana na gaya mata yau zaki amshi kwananki
gaskiya ina shiga hakkinki kada Allah ya kamani in
shiga uku, duk da dai amincewarki nake kwana
dakin Suwaiban to amma wallahi na san kawaici
kawai kikeyi kuma aka tialasta zuciyanki kika
amince na dole amma ni nasan yadda ki ke ji da ni
ba yadda za'ayi ki barwa wata ni, to yau na dawo
na nuna musu nine jarababbe, kwalamata ta motsa a
kanki bazai yvu du an lasamin zuma in hakura
da ina ba".
Ta t hi zaune tace, "Kayi hakuri ka tashi
ka tafi in don nice har ga Allah na yafe, ka cigaba
da kwana dakin Suwaibar har sai ta warke yadda
yakamata" shima tashi yayi ya zauna yana mata
"wani duba na baki isa ba yce "Wannan abin da
akayi bafa tsari bane na Musulunci, an dai yi son
raine saboda a farantawa Suwaiba ke kuma ko oho,
in ba son rai ba me ye amfinin zuwan Hajiyarta da
zaman da take yi anan tunda ba za ta kwana da
JU
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yarta ta yi jinyarta ba, sai ace dole ni zan dinga kwana da ita ina jinyarta wato tunda ni nayi mata cikin dole ne inyi jinyarta ko? To daga yau na daina daukar hakkinki duk randa nake dakinta nayi jinyarta in kuma banasan Hajiyar tayi itama ai
tanason jikan.
Duk yadda Muneeba ta lallashe shi akan
yayi hakuri ya koma dakin Suwaiba ita ta yafe, sai
ya nuna mata sam hakan ba zai yiwu ba, in ita bata
bukatarsa kusa da ita to shi yana bukatarta balle ma
yaga zahiri lalle tana bukatansa ko ga yadda tayi
saurin amsar tayinsa na dazu da yadda ta dinga
rawar jiki yasan tana cikin kewarsa, amma don
gulma shine yanzu za ta koreshi shi kam ba inda
zaije.
***** ***** *****
Cikin Suwaiba a halin yanzu ya sami watanni biyar
kenan, don har ya fito, kuma ta sami lafiya garau su
Hajiyarta 'yan jinya da Goggo tun yana wata kusan
hudu duk suka koma Dukku, tun bayan komawarsu
Mujeeb yace tunda ta sami sauki ta amshi yin girki
don ba zai yiwu a barwa Muneeba hidimr girki
wata da watanni ba, in ta yi mata lokacin tana ciwo
to yanzun ta sami sauki sai ta amsa, in kuma ba zata
amsa ba, to ba ta da kwana, in har ba zata amshi
..girki ba, don ba zai yiwu Munceba tayi mata girki
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ba idan darc yayiniya zuwa dakin miji ko da baije
nata ba, ba kunya ba tsoro.
Sanin halinsə yasa a ranar ta amshi girki ta
soma sai Muneeban ta sami saukin hidindimun
gidan, con ma wasu abubuwan yaron gidansu Jume
yanayi kamar wankinsu da guga da sharar gida da
wajen gidan.
Suwaiba fitowar cikin jikinta yasa take
yanga da cikin take takun kasaita a cikin gidan, don
ta nuna wa Muneeba cewa yanzun it ace da gidan,
tunda ita ce mai haihuwa, ita kuma bata haihuwa sai
ta taya ta rainon abinda zata dinga haifowa.
Ganin jikin Suwaiba yayi garau har taje
Dukku biki ta kwana biyu ta dawo, ya sa itama
Munecba ta roki Mujeeb tanason zuwa Dukku ta
kwana ko daya ne, saboda zasuyi shirye-shiryen
bikin Murjan Hedimasta da yayan Muneeban
Mustafa.
Tana sa Dukku Mustafane ya dauketa a
mashin dinsa suka tafi gapin gidan da Mustafa ya
gina a nan Dukkun a unguwarsu ta sego babu nisa
sosąi tsakanı da gidan iyayensa gidan sasa guda
biyu ya gina na gaban gidan shine nasa da
amaryarsa, na ciki kuma shine na iyayensa, don
yana son ya rabasu da zaman gidan gandu, ya raba
imnaisu da matsi da Takura dasa ido irin na jama'ar
gidansu, ko da yake yanzu wannan halayyar da
suke nunawa innarsu duk sun rage a dalilin
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Lokacin biki ku-va ji tayi tamkar kafafunta
zasu tsinke saboda zirga-zirga tsakanin gidansu da
gidan Hedimasta. Ba ita ta huta ba hankalinta ya
natsu har said a aka kawo Murja gidansu a daren ta
shiga sasan nata tana mata tsiyar irin wahalar da
ciwon jikin da bikin su ya haddasa mata "Murja ta
hau bata hakuri da cewa, "Yi hakuri 'yar
Kanwarmu, ai dole ki wahala Kanwar Ango kuma
babbar kawar amarya bri in baki Panadol Extra
kisha ki watsattsakc.
Ta balla mata harara ta ce, ki rasa abin da
zaki bani sai Panadol Extra Hmmm!! Allah Sarki
duk rashin abokin rayuwata ne a kusa da banji
wahala haka ba, idan dare yayi zai yi mini tausa nan
kuwa ba maiyi mini sai ma kara mini zirga-zirga da
kuke tayi". Murjs tace, "Kr wannan abokin
rayuwa yaji dadi motsi kadan a yabeshi nima dai
gobe-gobon nan z radawa nawa yayan sabon
suna" ta i murmusai ta ce, Au abin gasa ne? to ko
kin rau. musa ba zai yi dadin da yaya naba" ta
mike tana cewa Linza ba zaki cikani da surutu ba ki
kara min ciwon kai dama fansar wannan ciwon kai
kaza. amarcinki ta daren yau in b naka ba bazan
yarda ba sai na gayawa abokin raytwa kun wab
nile da mijinki".
Murja tana murmushi tace kwamtar da
hankalinki kanwata kazar duka zan baki, harma da
duk abin da zai kawo, kinga kura da shan bugu
54
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
gardi da amshe kudi kenan" suka kyalkyale da dariya suka tafa. Muneeba tayi mata sai da safe ta fita.
Da kyar Munceba tayi kwana biyar a
Dukku, saboda yawan waya da Mujeeb keyi mata lallai lallai zai turo a dauketa da yaga taki bashi
hadin kai ta dawo sai ya biyo sawunta, ita kuma
dama sati daya ya bata tayi shi yasa tace sai tayi
satin zata dawo shi kuma yace gidan ba dadi a
dalilin bata nan, dole yazo ya dauketa suka koma Gombe.
Cikin Suwaiba a halin yanzun ya tsufa har
ya kai watan haihuwa duk wani shirye-shiryen daya
kamata ayi na tarar jariri anyi shi, Muneeba ce ya
wakilta takeyin komai hakan sai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 12