gayawa ta sakaki cikin kunci
dabakin ciki idan ba zaki girmamata a matsayin
uwar mijin ki ba ai kya girmamata a matsayinta na
160
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yar mahaifinki, to shikenan tunda abin naji ya zama
haka Baffa ba zai dawo hanunki ba, ki barshi a
hannun mamansa, wannan umurni ne na
mahaifiyata bazan iya ketare shi ba, kuma dole ki bi
umurninta, in kuma ba zaki biba to baki isa ni ki sa
in ketare dokarta ba dole inyi mata biyayya don in
gama da duniyata lafiya.
Muneeba ta durkusa a gabansa ta soma
aikin Kuka, shikenan ta san ta rabu da Baffa tunda
har Mujeeb ya bada goyon baya shima ya bi sahun
masu son su kuntatawa rayuwarta ita kam da ta san
za'a raba ta da Baffa bayan sun shaku da juna da
tun farko bata amshi rikonsa ba, don kuwa shakuwa
akwai babban illa yayin rabuwarsu.
Kukan da take durkushe tana yi baisa ya ji
tausayinta ya lallasheta da kalamai masu dadi ba,
illa ma daga murya da yayi yana matsa sababi "Mе
ye haka ne za ki zo ki tasani gaba kina min kuka,
Sai kace na yi maki wani abu, yanzu in wani ya
shigo ai sai ya dauka wani shahararren abu na yi
miki, alhalin magana ce kawai nayi da ya zama dole
kibi yadda nace babu sauyi to meye abin yi mini
kuka?.
Bude kofar falonsa da aka yi shi ya maida
hankulansu ga kofar don ganin mai shigowa.
Goggo ce ta shigo falon tare da sallama ta dube su
ta ce, "Ina tsakar gida nake jin sautin Kuka na tashi,
lafiya wannan ke durkushe tana kuka? Wani abu
161
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
kayi mata" ya girgiza kai ya ce ni babu abin da na
yi mata magana ce akan amsar Baffa na riga na
gaya mata dole inbi umurnin abinda kikace shine
take min kuka da magiyar in dawo mata dashi, ni
kuma magana ba a hannuna take ba sai yadda kika
ce "Goggo ta tabe baki tana duban Munceba ta ce
ni na karbe shi kuma kina ganin banyi miki daidai
ba shi ne ki ka kawo karata gurinsa, to yanzu dai
kinji matsayi na a bakinsa inda baki yarda ni
uwarsa ba ce mai sawa da hanawa, mai yi masa
umurni ko in hana shi to yanzun sai ki yarda, na
maida Baffa hannun uwarsa babu mai dawo miki
dashi in kuma kina ganin wanda kika kawowa karar
zai maida miki shi to gaki gashi nan kinga tafiyata".
Goggo ta juya tayi ficewarta tabar Muneeba
a durkushe tana ci gaba da sharban kukanta na
rashin ina zata dosa da za'a share mata hawayenta.
Mujeeb ma biris yayi da al'amarinta ya sa hannu ya
dauki Baffan da ke rike a hannun Muneeba shima
kukan yake taya uwar goyon nasa suka shiga dakin
baccinsa ya barta anan.
Ta san idan ta bishi ciki da wata magana
akan Baffan zai iya yi mata wata tijarar, sai ta share
hawayenta, ta tashi ta tafi dakinta ta soma rera
sabon Kuka wanda ya dauketa a kalla fiye da
awanni uku ranar ko abin karyawa bata nemarwa
cikinta ba, har bayan kiran sallar azahar tana nade a
gado da kyar ta iya tashi jiri na dibanta taje bayi
162
WATA KUSAN 2 Rahmatu.Hassan Zaria
tayi wanka da ruwa mai zafi sosai sannan ta dauro
alwala tazo tayi Sallar a zaune don ba zata ita
tsayuwa ba saboda tsananin yunwa da jiri da yake dibarta.
Ti mai kauri ta hada da zafinsa ta shanye
kusan kofi daya bat agama numfasawa ba ta soma jin duniyar na juya mata kafin kace haka amai ya
btaso mata gadan-gadan ta soma shekashi babu ji
babu gani, sai da ta amayar da duka tin da tasha
sannan ta koma yin wani koren amai tamkar zata
amayar da 'yan hanjin cikinta. Ta rarrafa dakyar ta
labo wayarta ta kira layin Mujeeb bai daga ba haka
tayi ta kira har sau goma bai daga ba.
Sai ta kyaleshi tayi masa uzurin kila baya
kusa da wayar ne nan da nan taji zazzabi shima ya
kawo mata nashi ziyarar a haka cikin jiri da
zazzabin ta shiga bayi ta wanke jikinta tazo ta gyara
gurin da ta bata da amai, sannan ta kwanta ta
kudundune kanta cikin bargo tana makyarkyata
zazzabi na kwankwatsar kashinta.
A makaranta Maman Dijab taji ta shiru bata
zo ba gashi zasu yi test tayi ta kiran wayarta tana
ringin amma ba a dauka ba har lokacin shiga Test
din yayi sai ta roki wata kawarta ta zauna tayiwa
Muneeba Test din, suna gamawa ta shiga motarta ta
nufi gidansu Muneeban don ta gani ko afiya bata
zo makaranta ba, sannan bata daga waya va.
163
WATA KUSAN 2
Rahmatu Hassan Zaria
Ko da Maman Dijah ta shigo gidansu
Muneeba bata wuce dakinta kai tsaye ba dakin
Suwaiba ta nufa tayi sallama suka amsa mata suna
zaune a falo da Goggo Baffa na zaune a gefe yana
kuka tare da watsi da kayan wasansa da aka tila
masa a gabansa.
Maman Dijah ta rusuna ta gaida Goggo
sannan ta gaida Suwaiba tare da tambayarta yaya
jikinta ta isa gaban Baffa ta daukeshi tana cewa
Baffa me kakewa rikici hala maman nasa bata nan
ne? (Muneeba take nufi) Suwaiba ta ce, "Tana nan
rikici kawai ya ke ji. Goggo tace tana dakin ta tun
safe dai da muka gaisa ban sake ganinta ba maman
Dijah ta ce, nima na biyo ne ingani ko lafiya bata je
makaranta ba, kuma nayi ta kirar wayarta bata
dauka ba bari in je in dubata ko lafiya.
Ta yi ta saliama a kofar fallon Muneeba ta ji
shiru ga Kofar falon a bude hakan yasa ta shiga
falon shiru babu kowa taci gaba da sallamar da ta ji
ba'a amsa ba tunda tasan mai gidan baya gida sai ta
wuce dakin Muneeba ta isketa kukudundune cikin
bargo tanata makyarkyata tare da numfarfashi, da
gudu ta isa gareta ta yaye bargon a tsorace tana
cewa, Innalillahi wa inna ilaibir rajiun Munceba
mcke faruwa? Baki da lafiya? Kina daki ciwo zai
kasheki ba wanda ya damu balle ya duba an jiki
shiru a daki. Wannan wace irin rayuwace.
164
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ta zauna kusa da ita ta kai hannu wuyarta taji zafi rau tamkar wuta ta kira sunanta ta amsa dakyar tare da kallon fuskarta tayi magana dakyar
Maman Dijah samomin maganin zazzabi da ciwon kai insha, tun safe nake kwance cikin mawuyacin
hali da ciwon ajali ne da kin iske na mutu Maman Dijah duk ta rude ta tayar da Muneeba zaune tana
cewa asibiti zan kira mijinki ya kaiki wannan ciwo
ya wuce asha masa magani a kwanta a gida dubi
yanda kikayi rama tamkar wanda ta yi shekara a
kwance tana jinya.
Ta dauki wayar Muneeba ta kira layin
Mujeeb din har tayi ta gaji bai daga ba Muneeba ta girgiza kai ta ce wallahi tun safe dana fara amai
yana gidan bai fita ba nayi ta kiransa bai dauka ba
har ya fita a tunanina bai kusa ne idan yaga kiran
nawa zai kira amma bai kira ba ki kyaleshi kawai
bazai dauka ba wannan ciwon nawa na rashin Baffa
ne, ina rokon Allah ya bani hakuri akansa.
Maman Dijah cikin rashin fahimtar inda
zancen Muneeba yasa gaba ta ce wani guri su kace
maki an kai Baffan? Na shiga dakin Suwaiba gaida
Goggo na ganshi yana kuka babu inda aka kaishi,
Muneeba tai yake kawai da hakura ta ce babu inda
aka kaishi daman Goggo ne ta amshe shi daga
hannuna ta maida rikonsa hannun riamensa tunda
wai ni bana zama wallahi da karatune ba zo karshe
ba zan iya hakura da karatun don tabarmın yaro ua
165
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
riga na shaku da shi bazan iya rayuwa in yaron
baya tarc dani ba shi ma nasan haka, duk da yake
yaro ne zai iya mantawa dani amma kafin ya
mantani zansha wahala, jiya kwana yayi kuka baiyi
barci ba nima hakana kwana banyi barci ba daukar
alhaki yayi yawa amma ba komai akwai Allah."
Ta maida kanta ta jingina da allon gado
hawaye na kwarara a idonta Maman Dijah ta
girgiza kai cike da tausayin aminiyarta ta ce, Ni
yanzun abinda nake so dake dan Allah ki kwantar
da hankalinki ki lallashi zuciyarki akan rashin
Baffan kar rashin nasa ya janyo maki wani
gagarumin ciwo tunda sun kwace shi ki kyalesu,
duk abinda mutum yayi don ya cusgunawa rayuwar
wani ai kansa yayi wa, muna nan muna yi maki
addu'a kema Allah ya baki naki, "Ai duk tsiya
bamai rabaki dashi balle ace bake ki ka haifeshi ba.
Bari inje in nemi izinin Goggon sai muje
asibitin, don ba zai yiwu ki zauna da ciwo a gida
ba, Maman Dijah ta je ta sami goggo tai mata
bayanin halin da Munceba ke ciki na rashin lafiya,
sai kada baki tayi tace ai da yake bata daukemu da
wani muhimmanci bashiyasa bata gayamana bata
da lafiya ba, ke yanzu da kika zo ai gashi kin sani to
ni yanzun meye matsayina a gurinta da har za'a
nemi izinina kafin a kaita asibiti? Sai kije ku jira
dawowar mijinta ni babu ruwana.
166
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Mamaki ya kashe maman Dijah a tsaye kai lallai zumunci ya lalace in bayan haka yaushe ne mutum zaiso bare ya wofintar da nasa 'yar da dan uwanka ya haifa indai da zumunci ai tamkar kai ka haifeta, amma mutane sam sunyi watsi da zumunci.
Ta sake rokon goggon a karo na biyu kiyi hakuri Goggo ki bani izini in kaita asibiti don tana cikin
matsanancin ciwo sosai, kuma muna ta kiran
wayarsa bai dauka ba, tunda ke uwace na tabbata idan kikace masa da izininki muka tafi ba zaice
anyi masa ba daidai ba Goggo kam fafur taki basu
izinin tafiya asibiti ta kafe akan lallai sai dai su jira
ya dawo Maman Dijah ta dawo dakin Munceba ta
isketa durkushi a kasa tana tawani yin kurin amai ta galabaita sosai.
Ta sake gwada kirar wayar Mujeeb amma
ya kashe alamar yaga nacin kiran da Munecba tai
masa in yaso sai ta hakura da kirar nasa kawai sai ta
kira layin Inna Amina kara daya biyu ta dauka ta
се, Maтa nice maman Dijah ba Muncebar bace
ganinan a fakinta bata la lafiya sosai nayi ta kirar
wayar mijinta bai dauka ba saboda yazo a kaita sibiti, sai na je na yi wa goggo magana tabani izinin mu tafi asibiti tunda jikin yayi tsanani amma
wallahi taki wai sai dai mu jira shi ya dawo ita ba ruwanta, shine nace bari in kiraki in' gay maki ko
za ki zo kila idan ta ga idonki ta yarua akaita asibitin.
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Mama Amina ta harzuka tace, wai me
Goggo ke nufi ne da irin wannan kiyayya da take
nunawa Munceba tamkar ba jininta ba? In don
rashin haihuwa nc ai ba ita tayi kanta ba balle ta ba
kanta haihuwa inda siya akeyi wallahi sun san zamu
iya siyan mata ko don mu raye gorinsu kyale su
ganinan zuwa yanzun nan?.
Mama Amina na zuwa da taga halin da
Munceban ke ciki said a ta zubda hawaye ta je da
kanta ta sake yiwa Goggo bayani tare da neman
izini amma fur Goggon tace a bari Mujeeb ya.dawo
tunda shike auranta, ita kam bata da iko da ita.
Zuciyar Mama Amina ta sake yin zafi dama
ba wani shiri suke da Goggon ba a dalilin irin
matsin lambar da take yiwa Innarsu Munecba, sai
kuma gashi yanzun abin ya hadu biyu matsin
lambar ya hada da Muneeba har nata yafi na uwarta
tsanani da nuna kiyayya ta zahiri.
Ta dubi Goggon tace, "Shi ke nan zan nemi
izinin wadanda suke gaba dake don nasan su masu
kaunar tane ba zasu so a barta ciwo ya halakata a
gida ba, in banda kaddara ma mai zaisa mutum ya
auri jinin wanda bata kaunar uwarsa balle shi to
kaddarar aure ce haka Allah ya nufa" ta juya ta fice
abinta ta bar Goggo na sababi, "Eh bana kaunarta
din sai ki dauketa ki aurar da ita inda ake Kaunarta
ai ni duk wanda yace zai mallakemin da ko dan
uws to wallahi zanyi fito na fito da mutum in
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
gwadawa mutum karya yakcyi in a hanya yake
kwana to ni na riga shi don a can inda zashi na
kwana sai dai ya iskeni acan! Wallahi saidai mu
zuba daga nan har yaumul tanan-nade."
Mama Amina ta amshi lambar Baffa Adamu
ta gaya masa abinda ke faruwa tare da neman
izininsa cikin bacin rai yake magana. Haba Hajiya
Amina yaushe nema zaki tsaya biye ma hali irin na
Rahin na rashin sanin ina yake maka ciwo, don
Allah maza ki dauki yarinyar ku tafi asibiti idan ya
dawo tasa ya rubuta takardar Shika yaba Muneeba
dama ai fitina ke kaikata gidan tana zama ba wani
abu ba, ki barni da ita gobe zanzo Gombe sai ta
raina kanta kuyi azama ku tafi asibitin Allah ya bata
lafiya sai nazo goben.
Nan da nan suka saka Munceba a motar su
Mama Amina suka wuce da ita asibiti. Gado aka
bata aka daura mata Ledar ruwa saboda aman da ta
yi yasa jikinta ba ruwa.
A gwaje-gwajen da likita ya yi ya gaya
masu tana cikin matsananciyar damuwa wanda har
tasa jininta ya hau kuma hakan na baraza da taba
lafiyar zuciyarta.
Maman Amina ta shiga cikin damuwa
matuka, anan Mama Dijah ta bayyana mata
musabbabin ciwon na Muneeba dalilin amshe rikon
Baffa datayi a hannunta Maman Amina ta zauna a
kujerar jikin gadon da Munceba take kwance tana
1
1
1
1
L
ப
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
mata agana a hankali cikin lallashi ki kwantar da
hankalinki, amsar Baffa da Goggo tayi a hannunki
ba atinsa rayuwarki ba ne, ko kuma kira ranki a
damuwa warda za ta zama musabbabin shigarki
cikin wani ha mawuyaci dubi yanzun halin dakika
sa kanki aanin shiga damuwa, rashin haihuwa ai
ba waa üla bane da har zasu dinga cusgunawa
rayuw aıki don Allah bai baki ba, kisa ranki a inuwa
Allan na sanc dake shin kina ina wanda ke da
sbekara ashirin zuwa sama da aure bata taбa
haihu-va ba zata samu bayan shafe shekaru? Ki
manta da komai na damuwa dake zuciyanki ki yi
fatan Allah ya baki lafiya.
Sai da ta sami bacci ne Maman Dijah tayi
sallama da Mama Amina ta tafi gida amma tace
zata davo tare da mijira da daddare Maman
Amina iayi waya dukku ta shaida masu an kwantar
da Muneeba har ana mata karin ruwa sannan tayi
waya ta shaidwa mijinta su Khairi ma ta gaya
masu tare da mmin su talio masu da abubuwan
bukata da abinci, cikinsu kuna wata zata kwana da
unceba.
Har garin Allah ya waye babu Mujecb
ballantana kunia Goggo duk la mama Amina ta
same shi da wayarta ta sh ua inasa suna Asibiti da
uneebar an kwantar da ita ana mata karin ruwa,
ya nuna damuwa yace yanzun zai shiga gida ne
170
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
amma yana nan zuwa a lokacin tana jin kila Goggo
ta hanashi zuwa nc.
Yan Dukku mota guda sukayo suka zo
Gombe, kai tsaye asibitin suka wuce suka duba
jikin Muneeba, yanayin da suka garta yaba
Baffansu al'ajabi tayi, rama sosai tamkar wanda ta
shekara tana jinya Baffa ya tambayeta mujeeb yazo
asibitin, ta gaya masa daga shi har goggo ba wanda
yazo.
Baffa Adamu ransa ya baci sosai ya dubi
dan uwansa Baffa Audu yace, kaji halin tsiyar
Rahina har ta koyawa danta ko? Yanzun in banda
rashin mutunci ace diyar kaninki kuma surukarki
tana gadon asibiti ba lafiya, ki ki zuwa dubata
shima mijinta kin hanashi yazo ko laifi tayi maki ai
kyayi hakuri kizo don zumunci balle babu abinda
Munceba zatayi mata, halin tsiya ne irin nata. Baffa
audu ya ce halin tsiya kona dabbanci aiko dabbarma
tasan nata kuma tana sonsa, balle mutum mai
hankali in banda raşhin hankali da rashin sanin
muhimmancin zumunci yaushe zaka wofintar da
danka na zumunci harka fifita bare kafi sonsa akan
naka. Tashi muje can gidan ai makaho bai san ana
harararsa ba sai an zungure shi cikin ikon Allah da
sukaje gidan Mujecb ma yana nan aiko gaba daya
da dan da uwar suka hada suka zage su tas akan
abunda sukayi na rashin kyautatawa Baffa Adamu
ya kara da cewa duk abinda ke faruwa a gidan nan
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
muna sane, Duk waa cusgunawa da batanci da
kuke mata keda fank, muna sane kuma lokaci yayi
da zamu fara kwatar mata 'yan cinta don ba baiwa
nuka baka a zumunci ne yasa mukaga ya dacc ayi
wannan a kuma kana ganin da kwara a
al'amarin toka sallamo mana ita ta dawo gida,
bawai ku taru ka matsawa rayuwarta ba, kuna mata
cin kasbi a tsakarka don kawai Allah bai bata
haihuwa ba, ko kai daya baka rawar gwanancewa
kayi masa da ya baka?.
Sannan ace yarinya na asibiti tun jiya babu
wanda ya lekata cikinku in ita bata lekata ba, kai ai
dole kaje tunda matarka ce hakkinta yana wuyarka
idan ka zalunceta daidai da Kwayar Zarra sai Allah
yı saka mati ko a duniya ko a lahira idan munje,
saboda haka lada ka yarda wani ya sakaka a hanyar
sabama Allah ka biye masa ko waye, koda uwarka
ce gata nan, don ba'a bin abokin halitta wurin
sabama mahallic sai ka kiyaye, kuma maza ka
tashi ka tafi asibiti wurin maʼarka kayi komai da
ake bukata duk da Hajiya Amira ta biya kudin
koai tana can tsayc da al'amarinta, wannan ai
abun kunya ne ka bar dangin uwarta da dawainiya
al'hali kana dashi, rashin zuwinka ma ai shine
abban abin takaici, ya kare naganar tare da jan
tsi ya dubi Baffa Audu yace, "Tashi mu tafi rana
172
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Mujecb yayi saurin cewa," haba Baffa tun
yanzu zaku tafi, ku tsaya abaku abin karyawa, sai in
sa direba ya maida ku dukkun, Baffa Audu yace,
mun riga mu karya tun a gida mun gode, suka
mikc. ya biyo su yana cewa, to bari inzo in maida
ku asibitin. Baffa Adamu yace, "ka Kyalemu
yadda ka ganmu, a motar haya muka zo daga
asibitin yanzu ita zamu hau mu koma daga can mu
koma Dukku a motar damu ka zo dan bamu kadai
bane masu zuwa dubiyar? Ya juya ya dubi Goggo
yace, da kuma da ubansa ya bata riko ance kin mata
gori kin amshe shi a hannunta, to ku rike abinku
dama naku ne ba nata ba Allah yaga irin rikon da
tai masa na tsakani da Allah ne kuma saboda
zumunci, saboda haka muna rokon Allah muna
tawassali da irin rikon da taimasa dominka Allah
itama ka azurtata da 'ya'ya masu albarka don
alfarmar annabinka da Al'kur'ani mai girma, inma
bai bata ba babu kaico zamu bata da a dangi ko
guda nawa takeso ta rikesu amatsayin ya'yanta har
abadaba shikenan ba kafin Goggo tayi wata magana
don kare kanta har sun fice a gidan suka nemi mota
suka shige suka koma asibiti shi kanshi Mujeeb
jikinshi yayi sanyi ya kuma san bai kyauta ba
abinda yayi tun jiyan yaso zuwa asibitin amma da
ya dawo gida Goggo ta gaya masa wai su Mama
Amina da Maman Dijah sun ci mata mutunci akan
tafiya da Munceba asibiti don kawai tace su jirashi
173
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ya dawo shine abin ya bashi haushi yaki zuwa
asibitn.
Yana shiga dakinsa yayi saurin yin wanka
ya shirya kansa cikin lallausar farar shadda mai
shicki da aai ya fesa turare ya dauke wayoyinsa
da maullin mota ya shiga dakin Suwaiba yace
masu zaije asibitin ya na Lura da Suwaiba yanda ta
hada rai tana cin magani daga ya ambata zaije
asibitin ba ta san yanda yake jin zafin rashin
kyautatawar da yayi koda Goggo zata hanashi zuwa
asibiun a yanzun bazai hanu ba yanda yake
kambama girman laifin da yayi balle ita fushinta
bazai hanashi zuwa ba.
Goggo ma dauko mayafi tayi tace masa su
tafi tare da ita. Baffa na ganin zasu fita ya saka ihu
sai ya bisu, Mujceb ya dauke shi ya mikawa
Suwaiba yace lallashe shi don bazai yiwu muje
dashi ba, idan ya ganta rigimarsa karuwa zatayi
gara ya zauna gida.
Har suka shiga mota suka tafi suna jiwo
kukan Baffan haushin da take jine yasa taki
lallashinsa hauchin motarsu Goggo na cinna kai
harabar asibitin suka hadu da motar yan Dukku
asu flo asibitun zasu tafi Mujeeb yayi masu alamar
sttraya ya fita suka gaisa da sauran jama'ar motar
suka paisa da Goggo sannan suka tafi kai tsaye
da Munceban take suka nufa tundama jiya
Mama Amina a gaya mısu dakin Muneeban ke
170
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
kwance hannunta dauke da abun karin ruwa, Mama
Amina ke zaune a kujcra Dab da Gadon shigowarsu Mujecb yana Muneeba tai saurin rufe
idanuwanta tamkar mai yin barci batasan Mujeeb
yaga lokacin data rufe idonta ba.
A mutunce suka gaisa da Mama Amina
tamkar ba su yi mata wani abu na 6acin raiba suka
tambayi ya mai jiki tace da sauki sun bata shiru
babu wanda ya sake yin magana. Da kyar Mujecb
ya iya bude baki ya ce mama dan Allah kiyi hakuri
da abinda ya faru sharrin shaidan ne. tai dan
murmushi ta ce, Haba babu komai ai ya wuce sai
dai a kiyayi gaba ya sake cewa sun bada bill din
abinda za'a biya ne? ta cc, Eh, sun bada har an biya.
Ya ce No, mama bazai yiwu ba kibani Bill din zan
maido maki da abunda aka bada hakkina ne. tacе,
kai mijinta ne ni kuma diyata ce karfin zumuncin
dake tsakanina da mahaifiyarta shi zaisa in kashe
mata ko nawane don neman lafiyarta ka kuwa san
girman ladan mutumin da yayi abu don Allah kuma
a dalilin zumunci to ni ina girmama zumunci
saboda Allah dakansa ma sai da yayi maganar
zumunci don idan mutum yayi watsi dashi to zai iya jefashi a wutar Jahannama a Lahira idan akazo ketare Siradi zumunci da amana duk wanda bai rikeshi da kyau ba sune kugiyoyi guda biyu da zasu finciki mutum su wugarshi cikin wutar kaga kuwa mai zai kai ni ga hallaka rayuwar Lahira ta ina ji ina
175
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
gani saboda haka kaima ka kiyaye hakkin aure da
hakkin zumuncin yar uwarka.
Ya ce na gode Insha Allah zan kiyaye
Goggo dai na zaunc tana jinsu tasan maganar
Mama Amina jirwaye ne mai kama da wanka,bada
Mujeeb kadai take ba harda ita.
Likita suka shigo da Nurse ya duba
Muneeba da zai fita ya dubi Mama Amina ya сe
Hajiya ko wannan ne mijinta? Ta ce, Eh! Shine
mijinta Likita ya dubi Mujeeb ya ce tun jiya da aka
kawota naso in ganka ka biyoni Offis zan yi
magana dakai. Mujeeb yabi bayan Likitan zuwa.
Offis dinsa.
Likita yayi masa bayanin ciwon Muneeba
kamar yanda yayi wa Mama Amina sannan ya kara
da bawa Mujeeb din shawara ak an a kiyaye wajen
6ata mata rai kuma a kula da yanda take cin abinci
don kuwa abinda ke damunta yasa har bata cin
abinci, kuma hakan zai iya jefa rayuwarta cikin
matsala.
Mujeeb ya yi godiya tare da jaddadawa
likita cewa zai kiyaye Insha Allahu lokacin da ya
dawo dakin tana zaune a bakin gado Maman Amina
nabata ruwan Ti data hada mata a kofi Munecba na
hada ido dashi tayi saurin kawar da kwayar idonta
ya matso dab da ita yana mata sannu ta amsa tare da
dubansa a fakaice yayi mata kyau sosai tamkar
wani jinsin Larabawa haka ya zama ya kara fari sai
176
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ramar da yayi ne abin ke bata mamakin abin da ke
sa shi rama hakan baisa taji tausayinsa baMaema
kara jin haushinsa da tayi na Eagarar daar'amarinta
da ya ke yi ko meye aibunta a rayuwarsa? Oholm
Ya matso ya amshi kofin shayin yace,bara
in hutasshe ki mama.ta mika masa ya somiba
muneeba tin. Haushin ya kama Goggo ganinsyanda
bai ji kunyarta ba, ta mike tana cewa zo:ka vkaini
gida sai ka dawo Allah ya kara sauki ya karanarba
munceba tin duk da bata sakar masa fuskabatamkar
yana bata madaci haka take hadiyar in. sY
Ya fita ya kai Goggo gida ko šhiga bai yirba
ya juyo kan motar ya koma asibitin A hanyanıya
tsaya za saya musu duk wanni abu naieukatandon
sai da ya cika mazauain bayan motırşa da şəyayya
sannan ya koma asibitin. swclnIES
Tun daga ranar Mujeeb ke sintirin zuwa
asibiti yana kashe kudadde wajen saye-saye har aka
sallameta suka koma gida. Wani abin umamaki tun
da suka koma gida sai al'amarin sugnanasibiti ya
sauya ya koma 'yar gidan jiya sam ya dainaishiga harkarta, sai dai abu daya dake damunsa idamiya fito offis shine kewarta, duk iya kokarin san a hana
faruwar hakan abin ya gagare shi.Uz Bwослм
A tunaninsa rashin Suwaiba nerya:saryake
kawar Munceban, tunda jego ta ke yi kumai aikiaka yi mata sannan ya rasa inda zai kaicbukatarsa, ga
BADG EETBJOM
177
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
lafiyayya yar mata yana da ita amma wani abu da
bai san ko mene ne ba yayi musu shamaki đa juna.
Yau kam tunda ya shiga ofishinsa kewar
matarsa ke damunsa, a dadafe ya iya kaiwa azahar
suna dar da sallah ya shiga motarsa ya nufo gida,
daga waje ya tsaya don har mai gadinsa ya bude
masa get sai yace ba shiga zaiyi ba, ya dauki
wayarsa ya kira lambar munceba, tayi matukar
mama kin ganin kiransa, ta katse tunaninta ta
hanyar amsa wayar tasa.
Ya ce, me kike yi yanzu? "Tace ina gida
ne" ya ce, " eh na san kina gida, so nake in san
abin da kuke yi". Mamaki ya kamata na wadannan
tambayoyi tace, na fito wanka ne ina shafa mai"
Yace, " Good,to ki sa kaya ki fito waje ki same ni
zamu je wani waje "Ta ce to, tare da kashe wayar.
Wata lafiyayyiyar riga mai dan karenn kyau
ta saka, tayi fakin dın gashinta ta daura dan kwalin
rigar ta sa hijabin rigar ta dauki wayarta ta fito.
Goggo na ganinta tace, ' ina kuma za ki je ke da
baki da lafiya, ta ce nima yanzu baban Baffa yace
in fito yana waje ban san inda zamu je ba, Goggo ta
Gyada kai tace, yayi dai dai sai kun dawo", tana
wucewa suwaiba ta fito take cewa Goggo" ba
wani baban Baffa karya ne, tına dai son fita ne bari
in gani in da gaskene".
Isarta waje yayi daidai da juyawar kan
motarsa suka tafi, ta tambayoyi mai gadi waye
178
WATA KUSAN 2
Rahmatu Hassan Zatia
2
ramar da yayi ne abin ke bata mamakin abin da ke
sa shi rama hakan baisa taji tausayinsaoba:IHama
kara jin haushinsa da tayi na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 12