ta matsa min sai na dawo wai ba haka
muka yi da mijina ba, shi yasa na lalla6a haka nan
na dawo, idanu a rufe na shigo gidan nan shi yasa
ba ku ji dawo wata ba".
"Munceba t ace, "Subhanallah! To Kin kira
Baban Baffan kin gaya masa, kinga ai ya kamata ki
ga likita tunda ba ke kadai ba ce, sannan ma dare
ake tsoro". Suwaiban ta yunkura ta tashi zaune ta
na cewa
"Ai ina shigowa na sha magani, yanzu
haka ciwon ya lafa min.
Muneeban ta dora Baffa bisa gadon ta na
cewa, "Baffana baka ga mama ta dawo ba ne, je ka
yi mata sannu da dawowa". Tana aje shi, ya tsallara
ihu ya makalkaleta yaki yarda ya zauna shi ala dole
ba zai sauka ba, dole ta maida shi ta rike Suwaiba
haushi ya kamata na irin kuiyar da Baffan ke mata
ta ce, "Allah ya raka taki gona, ni dai ka ke wa
kuiya ko? Zaka ga nayi wani sabon yaron kwanan
109
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
nan saura in ga 'yar kafarka a dakin nan sai na kore
ka". Muneeba ta yi dariya ta ce, "Kar dai ki sa ya
janye sabon yaron mu barki ke kadai". Ta cc, "In
kuka yi haka ai bakuyi min adalci ba, gara dai a bar
min sabon ke ki rike tsohon". Duk suka yi dariya
Muneeba ta fice dauke da Baffa.
Suna fita Suwaiban ta raka ta da wata
muguwar harara tare da jan tsaki sannan ta yi kwafa
ta ce, "Idan na so ne za ki zauna ki dinga yi min
raino, idan kuma ban so ba, a yi waje road a bar
min gida ni da 'ya'ya na mu sakata mu wala, har
Goggon taku da take wani zakalkalewa kullum tana
yawon gidan danta duk sai na yi maganinku bari
dai miji ya zo hannuna, idan na mallake shi zaku
banbance tsakanin aya da tsakuwa".
Da dare ya yi tana jin dirar motar Mujeeb
tayi saurin barin abin da take yi ta haye gado ta
shige cikin bargo.
Bai shigo dakinta ba saida ya gama abin da
zaiyi a dakin Munceba, sannan ne ya nufi dakinta,
duk da cewar yana shegowa Muneeban ta gaya
masa suwaiban ba ta da lafiya baije dakin ba sai da
ya canza kaya.
Ya isketa sai kakkarwa take yi tana fadın
wayyo Allah zan mutu. Ya dan tsaya a kanta yana
kallon ta sannan ya sa hannu ya bude rufar da ta yi
wa fuskarta ya ce, "Kin san baki da lafiya me yasa
tun da kika dawo baki kira ni ba, da kuma ban dawo
110
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
da wuri ba fa?" ta yi Magana a sanyaye "Ka yi
hakuri na dauka maman Baffa ta kira ka ta gaya
maka". Ya ce "Ni ba a gaya min ba yanzu sai ki
tashi mu je asibiti". Ta sake marairaice murya tace,
"Ka ga dare ya yi kuma yanzu ciwon ya lafa min na
sha. magunguna" Ta yi saurin fadın hakan ne don
bata son zuwa asibitin tunda ta san ba ciwo ta ke ba,
tarko ne ta ke son dana masa don ya kwana a
dakinta, sannan ta bi duk wata hanya dà zata bi ta
yaudare shi zata bi, don ganin ta karasa aikin da
boka ya sata.
Ya sake dubanta ya ce, "Kin ci abinci ko?"
tace, "Eh, na ci" ya ce, "Allah ya kara sauki ni zan
je ina da ayyukan ofis da zan yi na cike wasu
takardu zan dawo kafin in kwanta" ya juya ya tafi,
to damarta ta kufce kenan? Ta yi saurin yin Magana
kafin ya fice."Don Allah dan dawo ina son yin
Magana da kai", ya juyo yana dubanta ya ce,
"Magana ? ina ga zai fi kyau ki bar maganar sai
zuwa gobe kinga na ce miki akwai aikin ofis da zan
yi, kuma gobe me zan yi (Submitting) takardun".
Ta yi Magana cike da kisisina fuskarta dauke da
yanayi na neman a tausaya mata tace
"Yi hakuri maganar ba mai tsawo bace
dama alfarma zan nema na yau kadai". Ya dawo
cikin duban fuskarta tare da nazarin kalamanta wai
na neman alfarma, sanan ya tambayeta,
111
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
in dai bata fi karfina "Wane irin alfarma ce fadl
ba sai in yi miki", Shi anasa tunanin alfarma ce ta
neman kudl tunda ya santa ya san halinta a kullum
sai ta kawo kokon barar rokan kudi a gurinsa, shi
sam bai saba ba saboda Muneeba bata rokarsa abu
ko tana da bukatar, sai dai shi ya kangano lokutan
da take da bukatar kudi, idan sha'anin 'yan uwa ya
tashi to tun kafin ta nemi ya bata yake bata, in ma
bai bata ba ta kan iya yin hakuri tayi amfani da dan
wanda ke hannunta, sabanin Suwaiba da har abin
nata ya ishe shi, don ko yau da za ta tafi sai da ta
matsa masa ya bata dubu hamsin wai Hajiya ce ke
da matsala za ta bata, kuma ba ayi sati biyu ba da ta
amshi wasu dubu hamsin din sune aka hada aka ba
boka dubu dari, ba su ci ba ba su sha ba ko da yake
idan bukatarsu ta biya za su ninninka fiye da haka.
'Ta dan soma inda-inda don ta rasa ta inda
zata bullo masa tunda ta san halinsa, ya ce "Ke nifa
zan tafi tun da ba zaki fada ba". Ta daure tace, "So
nake ka taimaka yau ka kwana anan don ni wallahi
idan ina ciwo in baka kusa da ni sai inji ciwon na
karuwa, amma idan kana tare da ni sai inji ciwon ya
tafi".
Ya yi dariya yana girgiza kai y ace,
"Wannan abin da zuciyarki ta raya miki sam ba zan
yuwu ba, tunda zuciyarki bata yi adalci ba da ta
raya miki yadda za a tauye hakkin wani saboda ayi
mata abin da take so, ko da can da kika ga a cikin
112
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Baffa na tare a dakinki ina kwana wallahi bisa tirsasawar Goggo ne, amma yanzu babu wanda zai tirsasani in tauycwa Munecba hakkinta, ai abin ya yi yawa don dai tana da kawaici da hakuri sai ayi
ta mata cin kashe Allah fa sai ya tambaye mu".
Ta marairaice murya, "ta na Magana da
nuna alamun zafin ciwo, "Wallahi ni ba don in
tauye hakkinta na roki wannan alfarmar ba, na rasa
yadda zan yi ne, wallahi ni kadai ne san irin azabar
ciwon da nake kwana cikinsa, ganinka kusa da ni
yana rage min radadin ciwon amma shike nan ka
tafi, dama tsiyar auren mijin wata kenan, ya zan yi
dole in yi hakuri".
Ta koma ta kwantar da kanta bisa filo, ta
soma zuraro da hawayen kinibibi, ya dan dube a ya
kauda kai sabo da tausayinta day a ja ya ji yana son
yayi tasirin rinjayar zuciyarsa. Ba tare da ya ce
mata komai ba ya sa kai ya wuce ya barta.
Ya gama duk abinda zaiyi a dakinsa sannan
ya nufi dakin Muneeba ya isketa kwance bisa 3 sita
tana kallon wa'azin kasa da aka yi a Zaria a tashar
Sunnah TV. Baffa kuma na kwance a ruwan cikinta
tana dan bubbuga shi ya riga da ya yi bacci.
Ya zauna a gefen fuskarta a kasan kafet
yace, "Uwar gida ran gida yau kasaitar ake ji ba a
biyo ni ba har na ci abinci na yi wanka kina nan kina riritar Baffa ni an watsar da kula da n”.
Afuwan abokin rayuwa, yau rigimar Bafffa ta
113
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
4
!
daban ce lallai shi sai a jikina zai yi bacci, naga
baccin ya yi nisa idan na lallaba na maida shi gado
sai ya farka, shine muka dawo falo yanzu nake
tunanin in aje shi in bika sai ka shigo. Ya jikin
Suwiaban ya hanani ma in koma in dubota sai daru
yake yi". Ya shafi sumar yaron yace
"Tun dazun na bar dakinta, jikin nata dai har
yanzu shine ma nake tunanin ko zaki je can ku
kwana tare ko kuma inje gidansu karime in fauko
ta su kwana tare". Ta girgiza kai tace, "Haba dai
kaje dauko Karime da daren nan, ni meye amfani
na, sai dai kuma kai ya kamata ka kwana da ita
saboda ni ko munje can kwana Baffa ba zai barta
tayi bacci ba yadda yake jin rigimar nan yau, gara
kai ka je can ka kwana”.
Ya yi haka ne dama don ya sami yarda daga
gareta ba wai koda yaushe su dinga tirsasata suna
shiga hakkin ta ba, sai gashi ita da kanta ta bashi
dammar ya je ya kwana da Suwaiban shi yasa a ko
wace dakika a rayuwarsa yake jin son Munceban na
kara yin tasiri mai girma a zuciyarsa. (da ya san
gadar zare Suwaiba ta dana masa da bai je ba).
Ya gyara zamansa yana fuskantarta yace,
"Ba zai yiwu mu dinga' shiga hakkin ki ba, don bata
da lafiya, ya zama ina kwana ko da yaushe a
dakinta wancan karonma ganin idon Goggo sanan
da bin umurninta ne yasa na tare da kwana a can
amma yanzu ba zai yuwu ba Karime kawai za ta
114
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
dawo nan duk ranar da bana gurinta sai su kwana tare, tunda nima idan na kwana gurinta ai ba dauke
mata ciwon zanyi ba".
Muneeba ta ce,"Eh duk da haka ganinka kusa da ita zai dan rage mata radadin laulayin kasan sha'anin mata da miji, ko ni ce zan fi son
kana kusa da ni, yanzu dai dan yau abar maganar Karime, na amince ka je ka kwana mene ne abin damuwa don ka kwana can ba matarka ba ce ni wallahi bana zafin kishi a kan wannan sannan kuma
larura ai ta kori komai".
Nan da nan ya Gata rai ya ce "Au yanzu ke ba kya kishin in barki in je in kwana da wata?
Lallai ashe nine ke rawar jikin sonki tunda har ba kya kishin ina tare da wata. Dama nasan ba zaki taba damuwa da al'amurana ba balle har ki so ni,
tunda tun farko ba ni ba ne zabinki, ni kuwa gashi
na manta da son duk wata diya mace a duniyar nan
ke kadai ce ke mulkin zuciyata" ya kare maganar
tarc da sauke ajiyar zuciya.
Munceba ta tashi a hankali don kada Baffa
ya farka ta zauna idanunta kyar! Akan Mujeeb
domin maganganun sa sun soki zuciyarta tunda har
ya budi baki yace "Shine ke sonta ita bata sonsa
alhalin inda bata son shi babu yadda za ayi ta iya zama da shi na tsawon shekarun da suka vi, ita kam
in dai sai ta yi haukan kishi a kansa skane ba zata iya ba, zubda mutuncin kai ne da ragewa kai Kima.
115
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ta tausasa muryarta ta ce masa "Nice kuwa
ke kishinka, tunda ni kadai na san irin son da nake
maka, sai dai ni ba zan yi shirmen kishi ba nc,irin
na hauka yadda wasu matan ke nuņa wa,ku kuma
maza kuna son ayi ta haukacewa akan kisinku kuna
murna kuma jin dadi, idan kuka garo kan wannan ta
nan sai ku garo na waccân ta can, daga karshe sai
ku hado kawunan ku gwara a tare sai rikici ya balle
ayi ta yi, ku kuma kuna gefe kuna jin dadi ana
rigima akan sonku, wallahi maza kunji dadinku
'yan gatan mata ne", Mujeeb ya kyalkyale da dariya
ya ce, "Au nan kuma kika bullo? To ni dai ba na
gwara kawunanku, ni dai na sań nawa tsarin ta inda
baki ya karkata nan miyau yake zuba kin gane ai?"
Ta girgiza kai, "Ni ban gane wannan hausar
ba, ka san ni dai ba bahaushiya ba ce". Ya ce,
"Amma Hausa filani ce ko?" it ace, "Eh, Hausa
fillo ce amma Karin maganganun suna da wuyar
fahimta ni dai dorani a hanya yadda zan gane".
Yace,
"Wace unguwar zaki sai in gano hanyar da zan
doraki". Ta watsa masa harara tace, "Yau dai na
lura raha kake ji, yanzu dai mu aje rahar nan sai
gobe ka tashi ka tafi ka taya kanwata kwana, ka san
halın cıwənta sai ka na kusa shi ma harararta ya yi
ya na dan murnushi yace, "Ni dai ki ke kora ko?
Vallubi zan rama, ki bari ki shiga gona ta sai na.
hoblala bayacki" Ta saki dariya tace,
116
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Lah, yaushe ka fara shuka? Ni me ma zai kaini
gonarka balle ka ce in taya ka noma. Ni dai na sallame ka don Allah ka tafi dare fa ya yi?" Yace,
"Au har korata ki ke yi kin kosa in bar miki dakin
in tafi? To wallahi babu inda zan je sai an yi mini
abin da nake so, don nima ina da hakkina a gurinki
kuma ina da muradin in amshe his kafin in kwanta,
yanzu sallame ni kawai sai in tafi".
Ta girgiza kai tana dan murmushi ta ce, "Kai! Abokin rayuwa ka cika rigima, wai kai baka
girma ne? "Ya kanne ido daya yana dubanta yace,
"Girma? Da yake ma har yau bani da siriki ba a
fara dukawa ana gaise ni ba ana ce min baba an
kwana lafiya ki bari idan aka fara min irin wannan
gaisuwar sai in san na girma in barwa yara, amma
yanzu da saura na, tunda ma ni nan kokari nake in
cikasa biyu kafin nan da badI, kinga ko ai sai
gwarzó ne zai aje mata hudu".
Ta zumbura baki tana harararshi ta ce, "In
ka so ma gobe a daura zaka fi birgewa sai a san kai
gwarzo ne kam da biyu ka karo biyu rana daya".
Ya ci gaba da zolayarta "Au Allah kun yarda a
daura gobe, ba zaku tayar min da yaki a gida ba?"
tana son tayi dariya sai dai ta kirne ta share shi, ya leka fuskarta ya ce, "Au har kin soma fushi tun yanzu? Lalai yarinya kina da aiki ni dai 'lame ni
ba ruwana fushinki".bata Ankara ba sai gani ta yi 'ya soma rage kayan jikinsa, yana gamawe ya wuce
7ין
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
dakin baccinta yana cewa "ina jiranki, gara ma ki
zo ki kwantar da wannan rigimamman dan naki,
karbi kin shagwaba shi yaro ba ya barin mutane su
yi baccin kirki balle wata harkar arziki, Dukku ma
zan maida shi gurin matansa ni ma ya barni da
nawa matan.
Ta mike safe da Baffan a kafadarta ta bi
bayansa tana cewa, "In ka kaishi Dukku ai ka kai
shi kusa ka kai shi Yola ko Jalingo ne, ko can
Manbila tunda yana da wata matar a Manbila". Bai
kulata ba ya haye gadonta ya latse fitila mai haske
ya kunna mai duhuwar kala. Ta je ta kwantar da
Baffa a gadonsa sannan ta isa gareshi tunda babu
yadda ta iya dolenta ta amshi tayinsa.
Saida ya yi wanka a nan dakinta sannna
suka yi sallama ya tafi dakin Suwaiba, wadda har ta
fidda ran bukarta ba zata biya ba ta rufe kofarta,
amma sam ta kasa yin bacci tana dan kwance ne
tana sakawa da warwara akan ya zata yi in dan ban
kwana a dakinta yau ba, shike nan cikar burinta ya
wargaje?. Ta yi zurfi a duniyar tunai ne ta ji alamun
ana dan bubbuga kofarta, sai ta kasa kunne sosai
sannan ta tabbatar lallai kofarta ake bugawa, ta yi
saurin tashi ta je ta leka ta window ta ga Mujccb ne
tsaye wata irin wawuyar ajiyar zuciya ta saukar duk
da bata da tabbacin ko kwanan ya zo yi, amma ta
sha alwashin ko ma me ya kawo shi to za ta
yaudareshi har sai ya sadu da ita don dai ta samı ta
118
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaría
kammala aikin boka a yau dinnan kamar yadda ya umurceta da aikatawa.
Ta bude masa kofar ya shigo ta maida kofar
ta rufe sannan ta bi bayansa. Ganin ya zarce kai
tsaye dakin baccinta sai dadi ya lullubeta lallai yau
hakanta zai cimma ruwa.
Bayinta ya shiga ya dauro alwala ya fito, ya
isketa zaune a gefen gado ta zuba uban tagumi, ya
dan dubeta ya ce, "Meye kuma na tagumi tunda
gani na zo taya ki kwana ko in tafine tunda na ga
kin sami sauki?" ta girgiza kai sannan ta ce, "Та
amince ka taya ni kwanan ne?" ya warware
dardumar Sallah sannan ya amsa mata, "Da bata
amince ba ai da baki ganni ba, don ba zan tauye
hakkinta ba". Shiru tayi a ran nata tace "Tauye
hakki ko? Yánzu kuwa za ka fara tauye hakkinta,
ka bar wani ikirari ka dau bari ka shigo tarkona
zaka san shayi daga ruwa aka samo shi. Amma a
fili sai tayi 'yar ajiyar zuciya tace,
"Nima ba zan so a tauye hakkinta ba. Bai sake ce
mata komai ba, ya tada kabbara Sallar nafila.
Kwanciya ta yi lamo tana kallonsa har ya idar da
sallolnsa, yayi dogayen addu'o'l, ya shafa. Bacci na
son daukar ta amma tana gaddamewa idanunta
yiwuwar hakan, don in ta bari bacci ya sace ta to ta
yi asarar nasarar ta ta wannan ranar, nan take
dabara "ta zo mata sai ta fara mirgine daga farkon
gado zuwa karshen gado, alamu ne da ta yi masa
119
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
nuni da ciwonta ya motsa, dama tallen zani ne
kadai daure a jikinta, sai ta tattara shii ta yaye daga
cinyarta tana fidda nishi a ħankali.
Mujecb ya taso ya za bakin gadon ya zau
yana tambayarta, "Mene ne kuma? Ciwan de? t
gyada masa kai tare da miko masa hannunta, ya kai
nasa hannun ya riko hata lhannun tare da yi mata
sannu cikin tausayawa sannan yà ce, "In kina ganin
ciwon nan ya matsa mikf sosai ki tashi kawai mu je
asibiti, don ni ina tsoron tashin ciwo da daddare in
ji Hausawa sukace ko bai yi kisa ba zai hana bacci".
Ta kankame cin cinyoyinsa da ta mirgina ta
yi filo da su tace, "Mu bari zuwa har da safe in sha
Allahu zai lafa mini. Ka gyara kwaciyarka idan nå
ji ni kwance a jikinka zan dan sami sa'idar ciwon".
Ya murmusa yana kada kai cike da mamakinta ya
ce, "Kai Suwaiba wannan laulayi naki yana bani
mamaki, kina son ki yi wa kanki sabo da abinda ba
na ki ba ne ke kadai, kin san dai ni na ku ne ku
biyu, ba zai yiwu kama in mallaka miki kaina ke
daya ba".
Ya mike ya sauya kayan jikinsa zuwa na
bacci, ya zo ya kwanta ta mirgina a hankali ta fora
kanta bisa kirjinsa ta ja bargo ta rufe su, ya soma
bacci sama-sama ya ji ta ta soma wasa da gashin.
krjinsa, wanda yin hakan ta san yana haddasa masa
mo:sawar sha'awarsa, ya yi saurin dakatar da ita da
nasa henan domin ba shi da jimirin jure i
120
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
wadannan wasannin kasancewarsa lafiyayyen namiji. Hakan bai sa ta yale shi ba har sai da ya
magantu, "Wai dama abinda ke ranki ke nan ki ka
matsu in zo in taya ki kwana kawai don ki hana ni
bacci?" magarsa ta soki zuciyarta wato ma
jarababba ya dauke ta, shi ma ya san ba halinta ba
ne zubar da aji ta nemi namiji ko shi ya zo da
bukatarsa sai ta ga dama, yanzu ma don tana da
kudirin da take son cimma ne da bata neme shi ba
amma zata bi shi har ta sami biyan bukatarta.
"Ni fa in dai kina son in hada jiki da ke ki
tashi kije ki yi wanka, kin san ka'idata bana
kwanciya da mace sai ta yi wanka, don na san baki
yi ba". Wani tsami da wari ne ya ji yana tashi a
jikintya wanda bai taba jin irinsa a tare da ita ba
kuma ba komai ya kawo hakan ba sai janabar boka
da gauraya da jikinta, wanda kila shi-kanshi bokan
bai san iya adadin kwanankin da ya dauka bai yi
wanka ba, ita kanta ta san ba karamar juriyar hada
jiki ta yi da shi ba. sannan kuma ta karashe wunin
ba tare da ta yi warka ba ai dole aji tsami da wari a
jikinta, kazantar kam ta yi yawa duk dalilin cimma
mummunar manufa.
Ta mike ta shiga bayin nata tare da
tararradin ya za ayi ta yi wanka tunda boka yace
kada ta kuskura ta, wanke janabarsa har sai ta
gauraya ta da ta mijinta in dai tana son biyan bukat. Hoda ta rurare ta dauka ta goggoga hodar a
121
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
hammatarta wadda ke cike cinkus da gashi kamar
gonar shinkafe sam Cama ia bata aski, sannan ta
bulbula turare duk don ta ragewa kanta warin da ita
kanta ta san tana yi, to ya zata yi tunda boka yace
bata wanka sai an kwana in cai tana son biyan
bukatara. (sason Allah ne dai an riga an tafka sai
dai Allab ya shiryi masu hali irin na Suwaiba da
Hajiarta ta sirikarta).
Tuk da wankan hoda da turaren da Suwaiba
a yi b. lana ijeebu jin warin jikinta ba, ganin ta
hana shi bac i da tsokane-tsokanen ta na tado masa
sha'aw yasa babu yadda zai yi ya biya mata
bukatar ta,. Shi kansi yau ya sha mamakin kansa na
yadda ya ji sam ya kasa saurarawa Suwaiba don ya
ji ta fiye da kullum sai ya rayawa ransa lallai wani
maganin mata ta je ta sha don ta gigita shi kuma ya
gigitan ita kanta yana jin tsumuwar maganin, a
jikinta ne yasa ta kasa juriyan har sai gobe ta amshi
girkinta yasa ta yi karyar ciwo. Lallai zai gargadeta
kada ta kara shan wani magani domin sa baya so.
Ya tashi ya je ya yi wanka ya dawo ya yi
I wanciyarsa, sai a lokacin ne ta tashi ta dauki
agan da boki ya bata ta je bayi tı yi fitsarin da ya
mata m 2t2 0 ta vi tsar'i mma sa ta ji tsron
in 'sarkin tunda ya ce mata babu taba ruwa har sai
ashe garı. Haka nan ta dauki naman nan ta tura
af1 gabanta sannan ta maida wandonta ta sa ta
dawo ta kwanta.
2
1)
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Tun da ya fita sallar subahi bai dawo dakin
Suwaiba ba fakinsa ya wuce a dalilin bashin bacci
da ke idanunsa tunda ko baccin awa biyu cikakku
bai samu ya yi a dakin Suwaiban ba.
Ita kuma sai wajen takwas sauta na safe ta
tashi, sai a lokacin ne ta yi wankan isarkin đa ke
kanta tun jiya sanhan ta zo ta yi ramakon Salfolin
da ta yi sakacinsu da gangan tun daga azahar din
jiya har zuwa subahin yau ba kunya har tana iya
daga hannu ta na rokon Allah wai Ya yafe mata
rashin yin Sallah akan lokacinta da laifin da ta yi
masa na fasikanci da boka (kunji fa jama'a shi
kuma mijita da da sauran laifukan da ta riga ta nada
gammo za ta yi dakonsa na mallakar miji a
wulakanta 'yar uwar zama yaushe za ta roki
gafararsu? Ko kuma sai an je kiyama? Dadin abin
ma bayan duniya akwai kiyama wata shari'ar tafi
karfin duniya sai an je gaban Allah. Allah ka tsare
mu fi karfin zuciyarmu amecn).
Ta shiga kicin ta shirya lafiyayyen farfesu
da wannan naman, ita ce har da yi wa miji kunun
gyada ta san yana so, alhalin sam bata damu da yi
masa abin da ya ke so ba sai in ita ce ke so, idan ya
ci shi ke nan in bai ci ba babu ruwanta ta san zai je
gurin Munceba ya ci.
Ta yi shirinta tsaf kamar ba ita bace ta yi wa
kanta karyar ciwo. Ta debi kayan bisa tire ta tafi
1
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
dakinsa a falo ta ije tiren don ta ji alamun zubar
ruwa a bayinsa ta san wanka yake yi.
Yana fitowa ya ganta zaune a falonsa ya
dut ta suka wa juna murmushi ya dan "hareta
ya ce, "wa Suwaiba ke wace irin mai kunnen kashi
ce?" 1 1 dan kashe ido ya ce, "Me kuma na yi baban
Bafía, ni dai sarkin laifi ce a gurinka". Ya ci gaba
da goge jikinsa da tawul yana Magana, "Wai sau
nawa zan ce miki ki daina sa min tarkacen
inagungunan ku na mata idan zan kwanta da ke
amma ba kya ji abin naki ma na ga ya dada shahara
ki na neman ki zautar da ni". Ta yi wata 'ya dariyar
mugunta ta cc, "Yanzu don Allah mene ne laifina
don jiyar da kai dadi, koko ka fi son ka jinni
tamkar an dafa kaza da ruwa ba magi ba gishiri? Ai
dai ba ni kadai nake sha ba ita ma tana sha wa ma
ya san irin wanda take sha", ya daga mata hannu,
"Ya isa! Bar ambaycki zancen wata ba, in ma tana
sha ni ban ta ji ko gani ba, yadda na santa haka
take ba ke ba ynu a ji dai-dai gobe kuma a ji akasin
haka". kalamnsa ya tinzirata. A tinzira tacе,
"Amma in tana sha ai ba bari za ta yi ka sani ba,
nima yanzu ai baka ganni na sha komai ba korafi ne
dai kawai, kuma mace mairon ciki ai ance kara
'imu take yi, sai ka zargi cikin jiki na". yace,
"kunsai dai na taba ganin kulli kullin magurguna a
dakinki ranar da zaki haifi Baffa kuma da kanki
kika ce mini magungunen mata ne, ko ma dai na
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
meye kc kika faďda da bakinki ko ba a yi haka ba?"
ta san anyi hakans shi yasa tayi shiru. Ya ci gaba da
cewa,
"Sabo da haka daga yau ki daina banso, sabo da
irin wadannan magunguna sai su halakar da ke
nima ki halakar da ni, tunda bana so ki hakura da su
ki watsar da su in ace akwai ababen sha masu kara
ni'ima irin su madara zuma, nono, ya'yan itace da
sauransu kuma duk baki rasa su ba, in ma babu а
gaya min zan siya".
Ta mike tana cewa "Ai shike nan tunda
baka so na daina,",", amma a zuciyarta sai ta cе
"halaka kuma ai sai dai kada a kuma, yanzu kam ka
riga ka zo hannu bari ma ka ci naman nan shine
cikon aikin da zan kaddamar akan mallakarka"
Ta zubo farfesun a filet ta mika masa ta се,
"Ga farfcsu haka nan nayi sha'awarsa nayi, ga
kuma mutuminka kunun gyada", bai amshi filet din
ba sai ya ce, "Kin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 12