Gagarar da al'amarinta
da ya ke yi ko meye aibunta a rayuwatsa? Oho!ert
Ya matso ya amshi kofin shayin yace, bara
in hutasshe ki mama.ta mika masa yassomalba
muneeba tin. Haushin ya kama Goggo ganintyanda
bai ji kunyarta ba, ta mike tana cewa zoka kami
gida sai ka dawo Allah ya kara sauki ya karasarba
munceba tin duk da bata sakar masa fuskaba tamkar
yana bata madaci haka take hadiyar tin. sY
Ya fita ya kai Goggo gida ko'šhiga bai yirba
ya juyo kan motar ya koma asibitinA hanyarya
tsaya za saya musu duk wanni.abu nnigokatandon
sai da ya cika mazauain bayan motirsa dá' sayayya
sannan ya koma asibitin.
PAS IC SSIA
Tun daga ranar Mujceb ke sintirin zuwa
asibiti yana kashe kudadde wajen saye-saye har aka
sallameta suka koma gida. Wani abin mamaki tun
da suka koma gida sai al'amarin su gnaasibiti ya
sauya ya koma 'yar gidan jiya sam ya daina shiga
harkarta, sai dai abu daya dake damunsa idanıiya
fito offis shine kewarta, duk iya kokarin san a hana
faruwar hakan abin ya gagare shi. NUR EWOOL
A tunaninsa rashin Suwaiba ne ya sa yakeе
kawar Muneeban, tur da jego ta ke yi kuma aiki aka yi mata sannan ya rasa inda zai kaisbukatarsa, ga
177
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
lafiyayya yar mata yana da ita amma wani abu da
bai san ko mene ne ba yayi musu shamaki da juna.
Yau kam tunda ya shiga ofishinsa kewar
matarsa ke damunsa, a dadafe ya iya kaiwa azahar
suna dar da sallah ya shiga motarsa ya nufo gida,
daga waje ya tsaya don har mai gadinsa ya bude
masa get sai yace ba shiga zaiyi ba, ya dauki
wayarsa ya kira lambar muneeba, tayi matukar
mama kin ganin kiransa, ta katse tunaninta ta
hanyar amsa wayar tasa.
Ya ce, me kike yi yanzu? "Tace ina gida
ne" ya ce, eh na san kina gida, so nake in san
abin da kuke yi". Mamaki ya kamata na wadannan
tambayoyi tace, na fito wanka ne ina shafa mai"
Yace, " Good,to ki sa kaya ki fito waje ki same ni
zamu je wani waje "Ta ce to, tare da kashe wayar.
Wata lafiyayyiyar riga mai dan karenn kyau
ta saka, tayi fakin din gashinta ta daura dan kwalin
rigar ta sa hijabin rigar ta dauki wayarta ta fito.
،
Goggo na ganinta tace, " ina kuma za ki je ke da
baki da lafiya, ta ce nima yanzu baban Baffa yace
in fito yana waje ban san inda zamu je ba, Goggo ta
Gyada kai tace, yayi dai dai sai kun dawo", tana
wucewa suwaiba ta fito take cewa Goggo" ba
wani baban Baffa karya ne, tana dai son fita ne bari
in gani in da gaskene".
Isarta waje yayi daidai da juyawar kan
motarsa suka tafi, ta tambayoyi mai gadi waye
178
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
a
wancan. Yace Alhaji ne ya dauki Hajiya ". Tabbas shi dinne don motarsa ce. Tayi sauri ta fari wani
mai mashin tace ya bi bayansu ya ga inda suka je ya
dawo ya gaya mata zata biya shi. Mai mashin ya ji
aiki mai tsoka, yayi saurin bin bayansu.
Munecba tana shiga motar, kawai ta ga a
juya kan motar ya hau titi ya soma tafiya. Ta dube
shi kadan tace," lafiya baban Baffa? Me ke
faruwane? ina zamu je? Ba tare da ya dube ba,
hankalinsa na kan titin da yake yace, Duka
wadannan tambayoyin na mene ne? kin san đai ba
zan siyar da kanki bane. To sa ranki a inuwa kuma
ki zuba min ido kawai kada ki kara tambayata
komai, hakan ta yi taja bakinta ta tsuke ta zubawa
sarautar Allah ido.
Mujceb bai dire su ko ina ba sai a wani
kebantaccen hotel. Abin ya bata mamaki an ma ba
ta ce masu uffan ba. Ya barta a motar ya fita, ya
dauki mintoci sannan ya dawo Ya bude mata
murfin kofar ya ce ta fito ta biyoshi. Tamkar
rakumi da akala haka tayi ta binsa har ya bude
dakin tabbacin cewa kama dakin ya yi.
A tsakiyar dakin kawai ta tsaya kikam tana
karewa dakin kallo, tare da kallon Mujeeb da ke
zaune bisa gadon dakin yana zuba ruwa a kofi. Shi
ma ya sauke idanunsa akan nata yace, ki zauna
mana, kin tsaya cikin tsoro kamar wacda na sato.
Ba zata iya yi masa musu ba shi yasa ta zauna a
179
WATA KUSAN 2 Ramatu Hassan Zaria
kujerar dakin yayi mata umuminh ta dawo kusa da
shi akan gado. Ita dai bin umuninsa kawai take yi,
amma zuciyarta cike take da wasiwasi musabban
kawo ta hotel da Mujeeb yayi.
Rabon da mujeeb ya taba ko da hannunta ne
har ta manta, balle ya taba jikinta ko aje ga yin
wani abu, sai gashi ya rungumeta tsan tsan a jikinsa
yana sauke ajiyar zuciyarsa tare da lallashinta, ki yi
hakuri akan abubuwa mara sa dadi waddanda sukai
ta faruwa sam yanzu ba kya gaba na, ba kya birgeni
irin da, bana ganin farinciki a cikin gidana, kullum
bakin ki na ke gani, ki taya ni addu'a Allah ya ye
mun wannan matsalan in dai na shiga hakkin ki.
Idanun Muneeba suka kawo ruwa sabo da
tausayin mijinta, ga dai bikin zuwa amma babu zani
daurawa, magana ce a bakinta to amma babu halin
furtawa don ba zai ji a bakinta ba wai kanwar sarki
da kwarkwata ta langabar da kanta a kafadarsa ta
ce, ni bana rikonka a zuciyata tsakani na da kai
addu'a ce, kaima ka dage da addu'a ka hana
idanunka barci In Shaa Allah komai zai daidaita.
Bata yi musu kan bukątu varsa ba akanta, ta
bashi hadin kai yadda ya kamata tunda ita ma kanta
cike take da begen kasancewarta da mijinta nata, a
dalilin lafiyayya ce ita, babu luwa abin da zai
hanata mararin mijin nata, kuma a hakika ta sami
gamsuwarsa da bata taba ji a ray uwarta aurensu sai
180
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
dai matsalar nan ta kunno kai a tsakanin su, shi yasa
muneeba ta yi Masa tarba mai kyau.
Yadda take jin nishadi ma sai ta ji tamkar su
yi ta zamansu a hotel din kada su koma gidansu, su
sake haduwa da matsalar da suka baro a gidan nasu.
Mujeeb za ma ya yi shiru a gefen gado,
bayan kammaluwar komai ya shiga zurfin tunanin
akan wannan al'amari kwata kwata idan ya sadu da
muneeba ba ya jin dadinta irin da wanda ya san a
da tafi suwaiba nesa ba kusa ba, amma yanzu an
wayi gari suwaiba tafi ta, in ma ya sami gamsuwa
ita ma ba wata azo a gani ba.
To yau ma hakan ce ta faru suwaiban ya
dinga rayawa a ransa sannan ya sami biyan
bukatarsa. Wannan abu yana daure masa kai, shi
yasa ma yanzu bai damu da kusantar inda
muneeban take ba ya fi na cewa Suwaiba sabo da
canjin da ya samu.
Ya mike ya shiga bayin dakin yayi wanka,
yana fitowa yace tayi wanķa su tafi, jikinta ba
kuzari ta tashi ta shigo bayin mamaki take yi na
yadda farat daya ya sauya mata ya shiga cikin damuwa, zuciyarta na ta hararo mata abubuwa da dama dake damunsa amma a canke-cankenta ta fi
cafko cewa yanzu baya jin dadinta baya gamsuwa da ita, saboda ta gano hakan ne a yanayinsa, idan ya
gamsu da ita tana ganewa a fuskarsa da irin
kalaman da zai yi ta mata na yabawa irin baiwar da
181
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Allah ye mata na mace mai ni'ima, sabanin yanzu
da bata sami yabon komai ba, sai ma kunci da ta ga
zuciyarsa ta shiga, sai dai abu daya kawai ta lura ya
rage karfin sha'awar da ke damunsa a dalilin ba shi
da madafa a yanzu kasancewar suwaiba tana jego,
in bayan haka da ba zai neme ta ba, wato rashin
uwa ne yayi uwar daki.
Suwaiba kuwa bayan tafiyar mai mashin
gida ta shiga ta shaidawa Goggo abin da ya faru da
bin bayansu da tas mai mashin yayi yaga inda za su,
suna kan tattaunawa ne maigadinsu ya leko yace
musu mai mashin ya dawo.
Ta fito ta sami mai mashin ya bayyana mata
cewa hotel suka je, bai baro gurun ba ma sai da
yaga sun shiga ciki kuma har tahowarsa baiga sun
fito ba, a takkaice ma yana jin daki suka kama don
ya ga shi Alhajin ya shiga ya fito da makullin daki
a hannunsa, sannan ta fito ta bishi cikin hotel din.
Taja dogon tsaki zuciyarta cike da tsananin
kishi ta mikawa mai mashin din naira dubu daya,
yayi godiya ya tafi ita kuma ta dawo cikin gida ta
labartawa Goggo abin da me mashin ya je ya gano
mata.
Goggo ta jinjina kai tace, 'iye' lallai yaron
nan to uban me ya dauketa zasu je su yi a hotel, sai
kace wata karuwa, suwaiba tace, 'Ai wallahi zai
dawo ya sameni sai dai ayi wadda za'a yi, zai gaya
minme hakan ke nufi. Goggo ta tare ta, Akul kika
182
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
tada jijiyar wuya akan wanann abun, ina ganin
al'amarinmu ya fara yin Sanyi, ina ga karyar zuwa
asibit zakiyi masa gobe kije kiga boka bamu ga ta
zama ba tun kafin al'amura su jagule mana.
Suwaiba tace, sai dai mu je da ke don ni
bazan iya kai kaina gurin ba, tace, ba zai yiwu ba
mu je tare ba sabo da zan sa ido na sosai a
al'amuran gidan nan, zan kira Hajiyarki inyi mata
bayani sai ku hadu a can kuje tare.
Da su ka dawo a waje ya aje muneeba inda
ya dauketa ya juya ya koma offis, ta sha habaici
gurin suwaiba har Goggo ma sai da tayi nata, abin
da ya ba Munceba mamaki yadda akayi har su
kasan hostel sukaje da abinda sukayi amma sai ta
share lamari taji dadi a ranta tunda har abin ya basu
haushi.
Washe gari Suwaiba ta sami nasarar
yaudarar Mujeeb cewa zata ganin likita asibiti ta
tafi da karfin guiwarta suka yi mahada da Hajiyarta
suka wuce kauyen da boka yake.
Ya hada masu surkulle iri-iri tare da
gargadin aiwatar da komai yadda ya tsara musu,
sannan da gargadi mai karfi akan kada ta yarda
kunnin mijinta yaji sirrin dake tsakaninta dashi,in
kuwa ta bari yaji duk abinda ya biyo baya kada tayi
kuka dashi tayi kuka da kanta.
Ai kuwa tun daga wannan zuwa da sukayi, biyo bayan ayyukan da suka zartas sai komai ya
183
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
cabe tsakanin Muneeba da Mujeeb har bacin abin
yafi nada muni ita kam a lokacin babu abinda da ta
sa agabanta sai tsananin addu'ah.
Cikin wannan halin ne Munceba taje Dukku
halartar wani biki da suke dashi kwananta biyu
ranar Lahadi tana shirin dawowa Gombe da misalin
Karfe biyu na rana Mujeeb ya kira wayarta yake
shaida mata wai ta zauna a Dukku kada ta dawo
Gombe har sai yazo.
Cikin mamaki ta tambayeshi wani abu ya
faru ne, ko nayi maka wani abu ne ban sani ba? Ya
ce babu abinda kikayi mini haka nan ne bana son ki
dawo nafi son zamanki anan Dukkun yana fadin
haka ya kashe wayar ta dade zauna tana jinjina
wannan al'amarin har innarsu ta shigo ta sameta
tayi zugum tana tunani. Ta tsaya a kanta tana mata
kallon mamaki ta ce, ke lafiya kike zaune cikin
tunani ke da zaki tafi shine kika zo kika zauna so
kike dare yayi maki ke da ba kyason tukin dare.
Damuwa ce karara a fuskarta ta bayyanawa
innarsu abinda Mujeeb ya ce, itama abin mamaki ya
bata, sai bata yi kasa a guiwa ba ta sa a ka kira
babansu Muneeba ta shaida masa abin dake faruwa
shima al'amarin ya girgiza shi har yake tunanin ko
wani abu Muneeba tayi masa, tayi wa babanta
rantsuwar batayi masa komai ba, itama ta
tambayeshi laifin da tayi masa yace batayi masa
komai ba.
A
184
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
D
tada jijiyar wuya akan wanann abun', ina ganin
al'amarinmu ya fara yin Sanyi, ina ga karyar zuwa
asibit zakiyi masa gobe kije kiga boka bamu ga ta
zama ba tun kafin al'amura su jagule mana.
Suwaiba tace, sai dai mu je da ke don ni
bazan iya kai kaina gurin ba, tace, ba zai yiwu ba
mu je tare ba sabo da zan sa ido na sosai a
al'amuran gidan nan, zan kira Hajiyarki inyi mata
bayani sai ku hadu a can kuje tare.
Da su ka dawo a waje ya aje muneeba inda
ya dauketa ya juya ya koma offis, ta sha habaici
gurin suwaiba har Goggo ma sai da tayi nata, abin
da ya ba Munceba mamaki yadda akayi har su
kasan hostel sukaje da abinda sukayi amma sai ta
share lamari taji dadi a ranta tunda har abin ya basu
haushi.
Washe gari Suwaiba ta sami nasarar
yaudarar Mujeeb cewa zata ganin likita asibiti ta
tafi da karfin guiwarta suka yi mahada da Hajiyarta
suka wuce kauyen da boka yake.
Ya hada masu surkulle iri-iri tare da
gargadin aiwatar da komai yadda ya tsara musu,
sannan da gargadi mai karfi akan kada ta yarda
kunnin mijinta yaji sirrin dake tsakaninta dashi,in
kuwa ta bari yaji duk abinda ya biyo baya kada tayi
kuka dashi tayi kuka da kanta.
Ai kuwa tun daga wannan zuwa da sukayi,
biyo bayan ayyukan da suka zartas sai komai ya
183
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
cabe tsakanin Muneeba da Mujecb har bacin abin
yafi nada muni ita kam a lokacin babu abinda da ta
sa agabanta sai tsananin addu'ah.
Cikin wannan halin ne Munceba tajc Dukku
halartar wani biki da suke dashi kwananta biyu
ranar Lahadi tana shirin dawowa Gombe da misalin
Karfe biyu na rana Mujeeb ya kira wayarta yake
shaida mata wai ta zauna a Dukku kada ta dawo.
Gombe har sai yazo.
Cikin mamaki ta tambayeshi wani abu ya
faru ne, ko nayi maka wani abu ne ban sani ba? Ya
ce babu abinda kikayi mini haka nan ne bana son ki
dawo nafi son zamanki anan Dukkun yana fadin
haka ya kashe wayar ta dade zauna tana jinjina
wannan al'amarin har innarsu ta shigo ta sameta
tayi zugum tana tunani. Ta tsaya a kanta tana mata
kallon mamaki ta ce, ke lafiya kike zaune cikin
tunani ke da zaki tafi shine kika zo kika zauna so
kike dare yayi maki ke da ba kyason tukin dare.
Damuwa ce karara a fuskarta ta bayyanawa
innarsu abinda Mujeeb ya ce, itama abin mamaki ya
bata, sai bata yi kasa a guiwa ba ta sa a ka kira
babansu Muneeba ta shaida masa abin dake faruwa
shima al'amarin ya girgiza shi har yake tunanin ko
wani abu Muneeba tayi masa, tayi wa babanta
rantsuwar. batayi masa komai ba, itama ta
tambayeshi laifin da tayi masa yace batayi masa
komai ba.
C
184
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ya je ya sami 'yan uwansa Baffa Adamu da
Baffa Audu ya gaya masu abinda Muneeba ta
shaida masa. Baffa Adamu ya lalubo wayarsa a
aljihu ya kira wayar Mujeeb din, bayan sun gaisa ne
yake tambayarsa meye gaskiyar abinda Muneeba ta
gaya musu. Babu kunya ko fargaba wani abu sai ya
ce "Eh haka ne nace ta zauna a nan Dukku Baffa ya
ce "Ko meye dalilinka na cewa haka? Ya ce, Babu
wani dalili ya cc "wani abu tayi maka" Mujeeb ya
ce "Ba tayi mani komai ba" ni dai nafison ta zauna
anan in yaso idan na warware matsalolin dake
gabana zanzo in dawo da ita? Baffa ya sake
tambayarsa "Ina kake nufin ta zauna kenan? Ya ce
"Na bata zabi duk inda take son ta zauna ko nan
gidansu ko gidan Goggo dakinta ai yana nan "Baffa
ya harzuka ya ce, Abin da duk ka yi yayi maka
daidai tunda da sanin mahafiyarka kake zartas da
komai to mun gode zamu rike yarmu kamar yadda
ka bukata zata zauna a gidan iyayenta, amma ka
sani idan muka gaji da jiran zuwanka baka zo ba, to
zamu kaika gaban alkali don ka bata takardar ta
tunda mu dai bamu isa mu tilastaka zama da ita ba
zamu tilastaka bata takardarta, tunda kai da uwarkа
bakusan muhimmancin zumunci ba, duk al'amuran
dake faruwa agidanka muna sane da irin cin kashin
da akc mata, hakan bai sa kaga irin hakurin da take
da ku ba har sai ka rabata da gidanka, to ka je
duniya ce tafi bagaruwa jima, ka da wadda
185
zauna
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
kake so zabin mahafiyarka indai yar Hajiya Harira
ce wallahi ba ba ki zan yi maka ba sai ta maida kai
abin kwantance kamar yadda uwarta ta maida
ubanta gashi nan har yabar duniya ana kwatancensa
a matsayin mijin ta ce mijin da bai da iko da
gidansa baida iko da 'ya'yansa balle matarsa data
rabashi da kowa nasa, to kai ma yana zuwa kanka
muna nan zamu ji labara har ita uwar taka in bata yi
sa'a ba sai sun raba ku zata ga sharrinsu.
Suna gama waya da Mujeeb ya kira wayar
Goggo ya gaya mata abin da mujeeb ya yi. Kada
bakin da zata yi sai cewa tayi tunda yace ta zauna
anan sai ta zauna, mai daki ai shi ya san inda ke
masa yoyo, nidai bazan matsa masa ya dawo da ita
ba tunda ba sakinta yayi ba, kuma ai kila akwai
dalilinsa da yasa ya ce ta zauna anan" cikin jin zafi
Baffa y ace Abin da zaki iya cewa kenan ko? To shi
kenan mun barku da Allah ke dashi idan kunyi
hakan ne don musgunawa rayuwar yarinyar nan
wallahi Allah nasa ne kuma sai ya saka mata inma,
anan duniya ko sai anje Lahira, amma ki sani
Hajiya Harira da 'yarta da kika rika hannu bibbiyu
to zaki ga sharrinsu ki rike wannan a ranki.
Ya kashe wayarsa ya dubi 'yan uwansa ya
ce kun dai ji yadda mukayi dasu ko? To mu kyale
su mu zuba musu ido Muneeba zata zauna a gida
kamar ya ce kafin mu ga abin da allah zai yi amma
ina sonmu taya yaron nan da addu'a don kuwa
186
S
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
al'amarinsa yana bukatar addu'ah an riga an
farrakasu da yarinyar nan kuma sakacin duk na
shashashar uwarsa ne, amma zata gane kuskurenta
ranar da zasu raba ta da dan nata su sa ya koreta a
gidansa tamkar yadda ya yi wa matarsa.
Baffa Adamu da kansa ya tasa ta a motarta
sukaje Gombe gidansu yace ta bude dakinta ta
dauki duk wani da ta da ta san zata bukata tana
gamawa yace ta rufe dakin ta taho da mukullinta.
A gaban Suwaiba ya gaggayawa Goggo
maganganu masu tsayawa a rai ko ruwan gidan bai
sha ba suka juya suka koma Dukku kwananta
bakwai a Dukku su ka yi mata umurninta ta koma
gidan Mama Amina ta zauna don karashe karatunta
wanda watanni biyu ne kacal ya rage mata ta gama.
Zamanta gidan Mama Amina ya kwantar
mata da hankali sosai saboda Maman da 'ya'yanta
suna debe mata kewa basa barin ta cikin tunani ko
damuwa, ga mahaifinsu ya zama tamkar shi ya
kawo ta duniya saboda kulawar da yake nunawa
akan al'amarinta sarnan yayi tsaye don ganin
al'amura sun daidaita tsakaninta da Mujeeb ta koma
dakinta amma abin ya faskara saboda irin kalaman
da Mujeeb din yake gaya masa ne ya gano
al'amarin nasu na bukatar addu'a shi yasa bai matsa
masa ba ya Kyale sai dai yasa Malamai nayiwa
al'amarin nasu add'ah shima da kansa yana tayasu
addu'ar gidan ya koma daga Goggo sai Suwaiba da
187
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
'ya'yanta. A halin yanzu ma goggo bata son zaman
Dukku in dai ba wani sha'anin ake yi ba, kuma tana
zuwa bata dadewa da an gama sha'anin zata tattaro
ta dawo Gombe.
Baffa kuwa tuniya manta da wata Muneeba
a dalilin kulaficinta da yake yi ne Goggo ta amso
rubutu akayi ta dirkawa yaron har sai day a manta
da ita tun tana gidan ya daina yadda da ita sai
mamansa sai Goggo da Babbansa.
**** **** ****
Ranar da Muneeba ta kamala jarabawar ta
gama karatunta na Digiri a ranar sam bata cikin
kuzari naimakon ta kasance cikin farin ciki duk sai
tana jinta tamkar mara lafiya.
Tana dawowa gida ta shige daki tayi
kwanciyarta dama gashi tana fashin sallah, sai
kwanciyar tata tayi tsayi Mama Amina ta shigo
dakin ta sameta da waya a hannunta tana cewa'wai
Muneeba yau lafiyarki kalau kuwa" Ta tashi zaune
ta na cewa lafiyata kalau hakan nan dai nake jin
kasala da faduwar gaba bansan dalili ba, ta.cc Allah
ya kyauta amma fa ki kara dagewa da addu'a. me
ya sami wayarki Innarki na ta kira tana ringim ba ki
daga ba shine ta kirani taji ko lafiya.
Muneeba ta luluba kasan filo ta dauko
wayar tana cewa, "Na manta a (silent) take tunda
z ru biga yin jarabawa ban cire (Silent) din ba shi
138
量
8
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yasa banji ba bari in kira ta Mama ta ce "Kya iya
kiranta amma rashi ne akayi miki ta kira ta gaya
miki sai dai kiyi hakuri ki dauki dangana suma tace
min gasu nan har sun iso gomben". Munceba ta
dafe kirji cike da jin tsoron wanda za'a ce mata ta
rasa Allah ya saba Mujeeb ta rasa ba ko Baffa ko
kanwarsa ko kuma.Goggo ce, kai duk ba su bane. A
tsorace ta tambayi Mama Amina "Mama waye
nawa ya rasu? Ta ce kiyi hakuri Baffanki Karami
ne Allah ya yi masa rauwa wai yasha maganin
kwari za'asa a kicin din mamansa saboda
kyankyasai ta manta ta ajiye shi kuma ya dauka ya
sha ya dauka magani ne" Muneeba batasan lokacin
da ta kwarma wata irin kara ba tare da sakin salati
ta zabura ta mike ai ko taku biyu ba ta yi ba sai ta
yanke jiki ta fadi Allah yayi taimako daga gado ta
tashi data fadin sai ta fadi bisa gadon.
Mama Amina da gudu tayi kanta tana
girgiza ta tare da kiran sunanta amma shiru ba amsa
hakan ne ya tabbatar mata da Muneeba suma tayi
itama salati ta hau yi ta shiga bayin dakin ta debo
ruwa su Khausar ma ashe sunji karar Muneeba sai
gasu da gudu suka iske Muneeba warwa Mama
Amina na shafa mata ruwa tare da tofa mata addu'a.
su khausar suka tambayi Mama abinda ke faruwa ta
gaya musu suma sun tausayawaMunecba rshin da
tayi kasancewar irin tsananin son da takcyiva Baffa
180
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
wanda ko fan cikinta kila da kyar zata yi masa irin
wannan so mai tsanani.
Ganin ta dawo cikin hayyacinta yasa Mama
Amina ta dinga yi mata nasiha da tayi hakuri dama
iyakar lokacin yaron kenan a duniya ba zai taba
Kara koda dakika ba akan wadda Allah ya kudira
masa. Mama Amina ta kira mai gidanta a waya ta
shaida masa rasuwa ya ce su tafi can gidan har da
Muneeba shima yana nan zuwa don ayi jana'izar
dashi.
Gidan rasuwar ya cika da jama'ar Dukku
maza da mata dakin suwaiban suka shiga tayi kuka
har taba uku lada, sam bama ta cikin hayyacinta sai
surutu marasa kan gado take yi na yadda aka yi ita
da kanta tayi sakacin ajiye abinda ya zamo sanadin
mutuwar danta.
Sun shiga dakin Goggo sun yi mata gaisuwa
sanna suka koma dakin Munceba wanda ana duk
ilahirin danginsu da suka zo suke zaune Munecba ta
je falon Mujecb inda Gawar Baffa take ta bude shi
tana masa kallon karshe ganin yadda maganin ya
fatattaka masa baki da lab6ansa ne yasa ta saka
kuka har sai da aka riketa aka fita da ita.
Kwanan Muneeba uku a dakinta a dalilin
umurnin da iyayenta da Baffaninta suka bata na ta
zauna ayi kwana uku, sannan ta koma gidan Mama
Amina duk safiyar Allah Mueeb yana shigowa
dakinta don gaisar da 'yan uwansa dake dakin
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
amma ita dashi har yau babu wanda yaccwa dan
uwansa Uffan sai dai in ya shigo zata bi gaisuwar
da jama'a ke masa amma batayi masa ita kadai ba
tunda sam yaki yarda su hadu, yadda ta lura ma
kamar kunyarta yake ji shi ya sa ya ke kaucewa
haduwarsu su biyu.
Tun bayan rasuwar Baffa sai al'amura suka
soma sauyawa tsakanin Goggo da Suwiaba yanayin
zamantakewar su ya fara canza salo, Goggo bata da
iko akan al'amarin gidan danta yanzu Suwaiba sai
ta nuna mata bafa zata takura mata ba ita da gidan
Mijinta, sannan Goggon bata da ikon yin sirri da
danta sai taji wannan sirri a bakin Suwaiba, Mujeeb
din zai gaya mata in wani abu takeso yayi mata to
sai ya nemi izini Suwaiba idan ta yarda sannan ayi
mata in bata yarda ba to sai dai tayi hakuri ko kuma
ta kaskantar da kanta ta roki Suwaiban sannan ayi
mata.
Abin duniya fa ya damu Goggo yadda ta
dauko ruwan dafa kanta gashi kiri-Kiri ruwan na
konata kuma babu yac da zatayi ba halin ta gayawa
wani sai ayi mata dariya da Allah ya kara ai dama
duk wanda yaja ruwa shi ruwa zai yiwa dukan tsiya.
Saboda hawan jini da Goggo ke dashi yasa
tun Munceba na gidan girkin Goggo daban aka
koma ana yi mata, in miyace ma tata ta musamman
ake mata, amma sai Suwaiba tą da ta yi, ds
Goggon tayi magana sai Suwaiban ta ce, ni fa
191
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
a
C
gaskiya Goggo ki daina matsa mini da wanne zan ji
da hidimar yara ko da ta ubansu koda taki gaskiya
kawai ki dinga yin girkinki in dai ba zaki ci me
gishiri ba wannan takura ne ace mutum duk lokacin
da zaiyi girki sai ya dora tukunya biyu, nifa ba dole
bane inyi miki abu in kuma kinga baki iya zama
dani ki koma gidanki.
Goggo tace, kwarai dole kiyi mini rashin
kunya tunda nayi tsayuwar daka na hada aurenki da
dana kin sami wuri kin baza shanyarki yadda kike
so yanzu nice abin wulakantawa to zai dawo gidan
nan da bakinsa zai gaya miki matsayi na idan kin
manta ni uwarsa ce da na dau dawainiyar wahalar
nakuda na haife shi nayi ta ba shi nono na ina
rainonsa cikin kulawa har ya ya shekara biyu na
yaye shi, sannan na ci gaba da kula dashi har ya yi
girma ya shiga makaranta yayi ilimi daya sami aiki
yayi kudın da kike takama dasu ya aureki, shine ni
zaki wofintar da wulakanta masa saboda ke butulu
ce, na fifitaki akan 'yar kanina na soki fiye da ita
sai gashi kin watsa min kasa a ido tun ba'aje ko
inaba to shi kenan ki sani akwai ranar Kin dillanci
ranar da hajar mai gari zata bata".
Suwaiba dariya tayi ta ce to ai Goggo kece
baki sani ba ruwa cikin cokali ya isa mai hankaii
yin wanka sannan ai ba kowa bane zai iya gane
dingishin kwaďo sai mai tsananin hankali da basira
kuma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 12