ya zamo ina wuta
su Goggo su sakata cewa wai ta gama mallake
Mujeeb tunda har bai iya aiwatar da komai sai itace
mai aiwatar masa, baya shawara da kowa a
al'amuransa sai da ita to ba ita bace zata haihu, sai
ta bari tayi duk abin da taga dama a nata amma
wannan ta ja baya taba mai haifuwa fili ta yi yadda
take so lokacinta ne ita kuma sai ta jira nata lokacin
yazo.
Wadfannan maganganun sukansa Muneeba kuka, tunda ita tana yin komai domin Allah ne ba
don a sota ko a yabeta ba, amma sai gashi bita da kulli ne ke biyo baya ana zargin ta kuma tasan wani
55
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
abun in bata sa baki ba Mujeeb baya saya cewa
yake a bari ta haihu lafiya sai ya saya.
Kullum Mujeeb cikin lallashin Muneeba
yake yi akan ire-iren maganganun Goggonsa da
matarsa, don ma yana takawa Suwaiban birki a daki
yake wanketa da soso da sabulu batare da Goggo ta
san anyi ba tunda itace ke daure mata kugun yin
takama da duk iskancin dataga dama a cikin gidan
shi kuma a daki har bara zanar rabuwa da ita ya
keyi, a cewarsa don ya saketa ba wata tsiya bane,
ita kuma da taji Kalmar sakin sai ta shiga taitayinta
don a duniya babu abin da take so irin Mujeeb,
balle yanzu da take dauke da cikinsa, ita ta sanma
barazana yakeyi b zai taba iya sakinta ba, sai dai
wannan barazanar da ya ke yi tasa zata shaidawa
Hajiyarta a kansa tunda har yanzun basu mallaki
zuciyarsa irin yaddda suke so ba, ta na jin idan ta
haihu wani bokan zasu canza in har ba suga canji,
ba tunda suna so yaso jaririn da Suwaibar za ta
Haifa irin mahaukacin son nan da bai taba yiwa
kowa irinsa ba a duniya, shi yasa. duk inda zasu
sami asirin wannan soyayyar to za su je su bada
kudi komai yawansu ba su da matsalar kudi Mujeeb
na sakar masu bakin aljihu daidai gwargwado.
56
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
**** ***** *****
Cikin tsakiyar dare nakuda ta kama Suwaiba, Allah yasa Mujeeb a dakinta yake ihunta ya tashe shi ya farka a gigice ya ganta kwance a Rasa tana birgima
tana ihu ya diro daga gadon yana tambayarta
menene ta ce "Ciki na da marata da baya na ne suke
ciwo zan mutu ka taimakeni kả kaini asibiti wallahi
mutuwa zan yi ya zo ya riketa yana cewa "Ki dinga
yin Salati ne ba ihu za ki dinga yi ba bari in taso
Goggo ina jin haihuwa za ki yi sannu ki yi hakuri
yanzun za mu je asibiti." ya mike zai tafi kiran
Goggo, ta damko kafarsa ta rungume tana kuka
tana cewa "Ni mu tafi asibitin ba za ka fita ka barni
ba wayyoo Allah ka zo ka taimakeni" ya dawo ya
tsuguna gabanta ya ce ki yi hakuri ki daina ihun nan
sunan Allah kawai za ki kira shi ne zai taimakeki
sakeni in taso Goggon mu tafi "Da kyar ya banbare
kafarsa da ta danka ya fice da sauri ya je ya bugawa
Goggo kofa, jikinta na rawa ta tashi ta bude tana
tambayarsa abin da ya faru yace Suwaiba ce ba.
lafiya ina ganin haihuwa zata yi shine na ce bari in
gaya miki za a kaita asibiti.
Tace to! Abin ya zo? To Allah ya raba su
lafiya bari in je dakin sai ka yi maza ka fito da mota
ta wuce dakin Suwaiban shi kuma ya nufi dakin
Munceba tana zaune bisa Sallaya tana addu'o'i
bayan ta gama nafilar dare ne ta ji ana bugun
kofarta gabanta sai đa ya fadi a tsorace ta zo tana
57
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
tambayar "Wa ye? Ya ce nine Munceba bude tana
jin muryar mijinta ta yi sauri ta bude kofar tana
tambayarsa abin da ke faruwa ya gaya mata
Suwaiba ce za ta haihu nan da nan ta soma jero
addu'o'i ga 'yar uwar zamanta na Allah ya sauketa
lafiya koma daki ta yi ta dauko wayarta dama da
dogon hijabi a jikinta ta yi saurin rufo dakinta ta
biyo shi zuwa dakin Suwaiban ta iske su da Goggo
suna kokarin daukota don a fita da ita zuwa waje
cikin mota.
Munecba ta ce, Ka fito da motar ne? Ya cе,
duk na rude wallahi na manta in fito da ita ga
makullin can kan (Side bed) dauka ki fito da motar
da dau makullin da sauri ta je ta fito da motar daga
inda take ta juyata ta fuskaci hanyar fita sannan ta
dawo suka kamata suka kaita bayan mota ta suka
kwantar da ita tana ta aikin ihu da kiran Mutuwa
Goggo na ta lallashinta da ta ji Mujeeb ya ce ta
daina ihu ta dinga Salati sai ta haushi da fada, Don
Allah ka kyale yarinyar nan in ma ta yi ihu ba laifi
bane saboda haihuwa tamkar zarar rai haka radadin
ya yake don dai baka san zafin bane, in ba za ka
lallasheta ba to ka kyaleta.
Muneeba na kokarin shiga gaban mota su
tafi sai Goggo ta ce A'a ba da ke za a ba, wannan
sabgar ta manya ce" Muneeba ta yi saurin ba
Goggo hanya ta shige motar Mujeeb ya matso
kunnenta yace "Yi hakuri bari mu tafi da Goggon
58
S
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ki tayamu addu'ah Allah ya sauketa lafiya, tunda kin tada hankalinki bana ma son ki je wata damuwar za ki karawa kanki" ya shafi kumatunta
ya zagaya ya shiga mota suka tafi.
Wasa farin girki, ashe ma nakudar somin
tabi ne wai maye ya ci jariri domin kuwa da a ka je
asibiti lokacin ne ma ta soma asalin nakudar wadda
ta kaita har wayewar gari bata haihu ba sai bakar
wahala da take sha tunda har ruwan nakudan an sa
mata amma ba ta haihuwa ba.
Muneeba tana gida hankalinta a tashe duk
da cewar suna waye Mujeeb na gaya mata duk halin
da ake ciki haihuwarta ta zo gadan-gadan har kan
bebin ya fara kunnowa amma sam babu hanyar da
zai fito Nosis din sun yi iya kokarinsu don ganin ta
haihu da kanta amma abin ya faskara hakan ne ya
sa suka yanke shawarar sai dai a yi mata operation
(C.S) a cire bebin domin kuwa ya wahala sosai za a
iya rasa ransa ko a rasa ran uwar tasa.
Hajiya Harira da ta iso da Goggo suna jin
maganar za a yi mata aiki sai suka hau kuka Mujeeb
sai ya kasance shine mai basu hakuri lokacin da ya
je ya sa hannu a yi mata aikin a ofishin likitan.
Tuni har an kammala shirye-shirye sun shiga da ita Mujeeb ya lalubo waya sa ya kira
Muneeba tana dauka cike da zumudi
Tace, "Hala ta haihu?" ya sauke ajiyar
zuciyar yace "Bata haihu ba yanzu haka ma (C.S)
59
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
suka ce zasu yi mata nasa hannu har an shiga da ita
sai ki taya ta addu'a Munceba ta dafe kirji ta сс C.S
ba za ta iya haihuwar bane za su yi mata C.S? Ya ce
yaron ya kunno kai amma babu kofar da zai fito sun
yi iya kokarinsu abin ya gagara, sunce za'a iya rasa
bebin ko ita shi ya sa ya zama dole ayi aikin" Ta ce
Innalillahi wa Inna Ilahiri Rajiun Haka Allah ya
tsara al'amarinsa sai dai mu yi addu'ar Allah yasa
ayi aikin cikin sa'a Allah ya basu lafiya ita da bebin
gaskiya ba zan iya zama a gida ba gani nan yanzu
zan zo asibitin.
Ya ce "Yauwa gara ki taho, sai ki shiga
dakin Suwaiban ki hado kayan bebi da duk wani
abu da kika san za'a nema bayan an fiddo bebin sai
ki hado ki taho da su, ta danyi jim sannan ta ce,
'Kana ganin ba matsala idan na shiga dakin? Don
gaskiya ina gudun abinda zai je ya zo, ya ce ba wata
matsala tunda zuciyarki Fes za ki yi abinda na
umurce ki tace, shike nan, a ina makullin dakin ya
ke? Ya dan yi shiru yana tunanin inda ya saka
makullin lokacin da Goggo ta je ta rufo dakinta
mika masa makullin, sai ya laluba aljihunsa saboda
tunawa da ya yi kamar anan ya jeia shi ilai kuwa sai
ya ji makullin ya ja tsaki ya ce k n ga ma makullin
nan a aljihu na yanzun ya za'a y shi ya sani ba na
son ana wani rufe-rufen kofa ko ne za'a dauka ko
ayi mata a daki ban sani ba, g shi mun taho ba
kayan bebi yanzun idan sun fiddo shi sai dai uwarta
60
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ni
ta
ban
circ lullubin ta ta bayar a rufe mata jikan ta don san yadda zan yi ba" Abin dariya abin takaici
duba
Muneeba ta cc, yanzu ka yi sauri kawai kazo sai mu kayan idan muka dauka sai mu tafi tare" Ya ce shike nan gani nan zuwa".
Ya je shaidawa su Goggo zai je gida ya dauka kayan jariri Hajiya Harira tayi Karaf ta се, "Bari in zo mu je sai in duddubo tunda kai ba sanin abubuwan da za'a dauko ka yi ba" ya ce a a ku
zauna bari kawai in je ai Muneeba na nan sai ta taya ni mu duba". Goggo ta yi saurin cewa, Muneeban
ce za ka sa ta shiga ta yi mata bincike a daki,
wannan ai ba daidai bane in dai ba kai za ka dubo
ba to ba zai yiwu ita ta shiga ta duba ba ehe! Ta kare maganar a zafafe kuma cikin bashi umurni.
a
Ba da son ransu ba ya tafi ba tare da wata a
cikinsu ta bishi ba ya shiga gidan ya iske Muneeba
tsakar gida tana ta aikin mai kawo cikin damuwa
take sosai. Ta yi saurin ta zo ta rungume shi tace
har yanzun basu fito da ita ba? Ya ce basu fito da
ita ba amma muna sa ran za'a yi nasara ki kwantar
da hankalinki mu je mu dibo kayan".
Ya sa makullin ya bude dakin Suwaiban
falon tsaf tsaf suka wuce d'akin baccinta nan fa suka
iske fakin kaca-kaca tamkar me 'ya'ya goma sai
karni dakin ke yi a zuciyar Muneeba tace kila shi
yasa Mujeeb sam baya zuwa dakinta kwana sai dai
kullum ita ke binsa nasa dakin ita kuwa kusan koda
61
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yaushe a dakinta yake kwana a cewarsa yafi sakewa
a dakinta a dalilin rashin dabi'ar da Suwaiban ke
gwada musu sai ta bari Muneeba na dakin ranar
girkinta kawai sai su ganta tsulum tayi sallama ta
shigo babu ruwanta da bin dokar Musulunci na
cewa sai an baka izini sai ta kutsa kai tace tazo
daukan abu kaza ne idan yayi mata magana sai ta ce
ita da dakin mijinta ba me kafa mata dokar idan
zata shiga sai ta nemi izini. Tun daga ranar
Muneeba ta kudiri niyyar sai ta shayar da ita
mamaki in dai takamarta rashin kunya da nuna isa
da Gadara aka kuwa yi sa'a wata rana ta kutso
musu har dakin baccinsa tayi kyakkyawan gani don
ba zancę mummuna ba dama
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 12