dakinta, in Goggo na nan ne take fara shiga
gurin Goggo tayi sallama kusan sau uku ba'a
amsaba idan da sabo ta riga ta saba da wannan
aria
ita
rin
ar
ar
li
a
e
73
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
halayayyar ta Suwaiba idan tazo dakin tayi sallama
sai taga dama take amsawa ko kuma tace sam bata
ji ba.
Munceba na jin wasannin yaron can a dakin
baccin Suwaiban, hakan yasa ta kutsa kai cikin
dakin tare da kara yin wata sallamar jin Muneeban
ta shigo yasa ta amsa sallama can a kasan makoshi.
Muneeba na shigowa tasa hannu ta suri yaron ta
daga shi sama tana masa wakar Dan bOy na Mama
da Baba, inai timbidi boy dina" ya wangale baki
yana bangala mata dariya ya ganeta, ta dawo dashi
ta rungume a kirjinta tanawa Suwaibar magana.
"Ina ta sallama shiru na dauka ma bacci
kike yi, shi yana wasansa, ta wayance da kare kanta
'Sama sama naji sallamarki baccin nake son inyi ya
hanani, shi bai san komai ba sai wasa? Ta ce yi
baccinki bari mu tafi muyi wasanmu ko da yake
yau zama zai fora koya" Suwaiban ta ce "Na yi ma
babansa magauar Keke kullum sai ya ce ya manta
ni kuma wallahi bazan koya asa zaman ba indai
bui sayi keken ba" Munceba tayi murmushi ta ce,
"Yi hakuri kinsan Yayara da mantuwa ni na
fanshe shi, dana dawo makaranta yanzu.na biya na
siyo masa shikenan ko?
Suwaiban tadan bude baki cike da mamakin
Muneeba, kullum bata kyautata mata, bibiyarta take
da mugun kudiri amma ita ko a jikinta burinta a
yanzu bai wuce na ganin tayiwa Baffa abu ba, kudi
14
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ko nawa ne zata kasha masa san bata kyashi, ita
kuwa kishin banza ya hana ta saurara mata da irin
abubuwan da take kulla mata a gurin miji da uwar
miji da ma duk wani mai goyon bayanta bata fadar
aikhairan Muneeba sai dai tayi mata mugun kulli
kai jama'a inama wannan mugun kishin zai barta
tasawa zuciyarta Salama ta rungumi kaddara ta aje
duk wani mugun kulli su zauna lafiya kamar yadda
Muneeban ke so sai dai kash! Ba zata iya ba tana
tsananin jin kishin irin son da Mujeeb ke nuna
mata, shi yasa take biyewa ra'ayin su Hajiyarta da
Goggo na bin duk wata hanya ko wace iri ce don
ganin an kushe wannan son da yake nuna mata.
Muneeba ta fice rungume da Baffa tana
masa waka ta bar Suwaiban zaune tana saka da
warwarar abin da bazai kaita gaci ba. A falonta ta
iske jume ya gama kwaso kayan ya aje mata
makullin motarta bisa Tebur ya fita. Ta aje Baffa
akan kujera sannan ta dauko Keken ta fiddota a
ledarta, ta je ta duko batir ta sa a gurin da ya ke
wakoki sai ta kunna wakoki suka fara yi tare da
dan joji ta dauko yaron ta saka shi a keken ta
daidaita masa zamansa ya soma wasansa yana
kallon danjojin yana wangale baki sai ta barshi ta
shige bayi tayo wanka saboda zafin da ake zabgawa
ta dauro alwala tazo tayi sallar La'asar ta dawo falo
tana shafa mai tana kallon yaron.
75
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Sai ga Suwaiban ta shigo ganin Keken
Baffan ta ganshi a zaune yana 'yan wakokinsu na
yara na sauran tarkacen kayan was an da Munceba
ta siyo masa Ta dan dubi Munceban kadan t ace
"Ni fa tun dazu da kika barni a daki ina ta mamaki
da kika ce kin sayo masa keken zama ashe da gaske
no" Ta ce "Meye abin mamaki? Baffa fa jinina ne
wałlahi ko nawa nake dashi zan iya kashe masa ki
daina shakku nayi domin Allah sannan a
matsayinsa na dana ta 6angare biyu.
Mujeeb ne ya shigo falon tare da sallama ya
bisu da kallo, sannan ya tsaida kallonsa ga Baffa
dake cikin Keke yace "Iye! Yaron mamansa Keke
aka yo masa Lonchin Dalleliya haka? Lallai yaron
nan ana ji da kai don Allah waye wannan taimakon
Mama Babba ko Mama Kurama? Ya tsaida idonsa
ga Suwaiban. Ta nuna masa Muneeba ta ce,
"Mamansa ta sayo masa tunda kai ka kasa siyo
masa harkar kasuwanci da Ofis sunsa har kana
mantawa da sha'anin danka daya tilo ranar da
sukayi yawa kuma sai Allah”.
Gorin da tayi masa yayi masa ciwo tunda
har ta nuna neman kudl ya fi ye masa da guda daya
da A'lah ya bashi bai nuna mata ba sai yiata
"Ko ni na' manta dashi ina da 'yar uwar da
bazata manta dashi ba zata dinga fansata wajenyi
masa duk abin da ni na manta ba tare dana bata ko
sisi ba" ta kada kai, Ai nakan yayi kyau shi dai ya
10
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
suri yaron yana cilla shi sama yana masa wasa. Ya dubi Munecba yana mata godiyar dawainiya ta harareshi sai ya kyakyale da dariya.
**** **** ****
Lokacin da Baffa karami keda watanni bakwai a
duniya har ya fara rarrafe yana ma kama abu ya
mike, a wannan lokacin Suwaibar har ta sami wani
dan karamin ciki wata biyu dama hudubar su
Goggo kenan wai kadata ta yarda da tsarin 'yan
asibiti da suka ce kada ta samu wani cikin sai ta
sami akalla shekaru uku da haihuwa adalilin aikin
da aka yi mata shine su Goggo na jin haka suka се
sam wannan ba mai yiwuwa bane, ko ta sami ciki
babu abinda zai same ta, shi yasa ta saki jiki har ta
sami cikin.
Mujeeb da ya fahimci cikin gareta ranshi ya
faci yayi mata fada kamar zai ari baki tunda tana
da matsalar operation da kansa ya amso mata wani
magani na addini ne da akesha duk bayan gama
al'ada to da izinin Allah mace babu abinda zai
shiga mahaifarta har wani watan yayi ashe bata sha
saboda su Hajiyarta sun zugata da cewar tayi ta
hainhuwa ta cika gidan da 'ya'ya tunda ita Allah ya ba.
Mujceb kuma yace babu ruwanshi idan ta
sami matsala gurin haihuwa, sannan gashi .cikin
77
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yazo mata da tsana in laulayi fiye ma dana Baffa
hakan ne vasa konai na Baffan ya koma hannun
Muneeba shan nono da kwanciyar bacci ne ke
hadasli da uw rsa, sai kuma idan zata makaranta to
zata barshi gurin Suwaiban wannan dalilin ne yasa
ma aka vamo musu wata 'yar yarinya da zata din ga
taya Suwaibar renon Baffan.
Kiriniyar Baffan da barnarsa ne yasa ake
kaffa-kaffa dashi tunda komai hannunsa ya kai
kansa to zai 6arar dashi ko ya barnatart dashi idan
abin na amfani ne sau biyu Suwaiba na barin reza a
dakin ta yana yanka hannunsa.
Ranar juma'a bayan saukowa masallaci
Baffan yana dakin Munecban yana ta sana'ar tasa
ya baro da wannan ya rarrafa ya damko soket idan
ta kwace sai ya koma can ko kuma ya saka kuka ta
dauko shi tana cewa 'Kai Babana wai kai wane iri
ne, idan an harka mai ciki sai ka fadawa- mai
goyo.
Mujeeb ne ya fito daga bayi yana musu
dariya y ace "Tun rannan nace don Allahki warware
min wannan Karin maganar ni har yau bangane me
alia nufi ba kinki” ta dora Ban bisa gadonta ya
tura masa tarkacen kayan was sai da yayi daidai
d su akan gadon sannan ta ce, Ai na gaya maka
nima bansani ba tunda ni ba Bahaushiya ba ce kaje
ka tambayi Hausawa ni fillo ce ya ce Fillo mai
karambanin aron yaran wasu kenan, ni dai don
ن
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Allah ki koya min Karin magana Hausawa na rasa a
ina kika koyo" t ace Ai makarantar Boarding kasan
akwai hausawa da yawa suma muna koya masu
fillanci kowa yana karuwa da dan uwansa". Da
gudu Muneeba ta isa bakin gado ta tare Baffa daya
ziro kafafuwansa wais hi zai sauko.
Mujecb ya ce Kai! Wannan Baba na mu đa
karambanin tsiya yake saukeshi a kasan tunda
yafison ya sauka ko ki ba Karime shi don hutawa
nake son in yi ba zai barni ba". Ta sauke shi kasa
tana cewa yaro fa shi da dakin Mamansa ba za'a
kore shi ba Karime aiki takeyi tunda hutawa kake
sonyi sai ka koma dakinka kaga can ba mai hanaka
sakewa in munzo ma ka koromu".
Ya dora kansa bisa filo yana murmushi ya
ce, wane ni da zan koro ku kudai da kuke kora na
idan na zo yaci ace nayi zuciya na tafi inyi muku
yaji saikun nemeni kun kawo kanku tunda
nasan........? karar fashewar wani abu da Baffa
yayi shi ya dakatar da Mujeeb daga maganar. da
yakeyi suka nufi gurinsa dukansu wani madubi ne
babba da ke aje akan dirowar gefen gado (Side Bed
Drower) ya dafa durowar ya mike shine ya dauko
shi ya kwala da kasa akan tayes ya fashe kwatsakwatsa.
Munceba ta daukeshi don kada yaji ciwo ta
mikawa Mujeeb shi ta yi sauri ta fita ta dauko tsintsiya då abin kwashe shara ta shigo dakin ne ta
79
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
iske Mujceb ya kama 'yan hannuwan yaron yasa
nasa yatsun guda biyu yana bugasu a yatsun yaron
tare da masa fada wai ya daina barna in ba haka ba
sai ya zane hannuwanshi da bulala.
Muneeba ta kallesu tayi dariya ta ce wai
Baba na kake yi wa wannan fadan? Bai ki ma
yanzu ka sake shi ya sake wata sabuwar barnar ba
yadda kasan ana masa allurar doki haka yake jin
karfi don ko barnar zaiyi da karfinsa yake yinta
Hajiya dai tace idan zamu zo Dukku bata gayyarsa
in kuwa munzo da shi to Goggo tayi masa masauki
a gidanta.
Ya rungume Baffan yana shafa sumar kan
yaron wadda ta kwanta Luf Luf a fatar kansa yace
ita batasan dama haka Goggo keso ba idan yaje ya
sauka gidanta don ta fara amshe cefanen da ya je da
shi garin. Kinsan zuwansa na karshe gidansu daya
fasa mata randa sanda ya radawa randar cike da
ruwa ya fashe wai ta taho da gudu ita ma ya daga
sandar ya rada mata da karfinsa.
Muneeba tayi ta dariya hallayyar Baffa ta
kara da cewa, "Ai ba kakanni kadai Baffa ke
Musgaba har mu nan iyayeısa nima nan yasha
kwalamin wata ran idan naji zafi inyi kamar in
buge shi sai inga ban iyawa dole in kyaleshi" Ya ce
ai ke kike shagwaba shi saura keya fasa maki
wannan (Show Glass) din ta kayan turare inga
yadda zaki yi masa ranar" tace Ni burina idan ya
80
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
fasa kada su yanke shi ai ba abinda zanyi masa illa
abin kai zai shafa ka bani kudi in siyo wata insa ba
shikc nan ba.
a
Washe gari asabarce kowa yana gida
Mujeeb yana dakinsa yana aikawa da sakonni
Laptop dinsa dama in dai Suwaiba ce ke da Girki to
yawanci zaka fi samun Mujecb a falonsa nan ta kan
biyo shi idan tana jin tsiya kuma taki zuwa to balle
yanzu da take fama da laulayin ciki kuma suna
takun saka da mai gidan.
Muneeba kuma tana dakinta suna ta gogegoge ita da mai rainon Baffa Karime, yawanci ranar
hutun karshen mako ne take samun lokacin zama
tayi hidimar dakunanta sosai Sarkin kiriniya Baffa
na nan yana ta 6arnarsa don har sai da ya zubar
musu da ruwan goge gogen bokiti guda Allah yasa
sun cire Kafet din tsakiyar dakin akan tayals ya
6arar Karime Kaman zata bugeshi don haushi
Muneeba na lura da ita ta katse mata hanzari da
cewa yi hakuri karime mu sake Gogewa kinsan dan
nawa dan gwalne ba'a dukanshi idan yayi 6arna
kiyi hakuri Karime ta ce "Anti Allah da kin barni
na dan bubbugi hannunsa za ki ga ya natsu ya
daina, ji fa hannunsa kamar kaikayi yake masa idan
baiyi barna ba. Rannan fa na aje ruwa a baho a
bayin mamansa zan yi masa wanka na je in debo
ruwan da zan sirka sai ganinsa na yi zai shiga cikin
81
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ruwan bahon kuma tafasasshe ne Allah ya soni bai
shiga ba na ganshi.
Munecba ta rintse ido ta ce ke! Karima ki
dinga kula sosai da yaron nan kada yaja maki fitina
wata rana kinsan uwarsa ba zata dauki hakan a
matsayin kaddara ba kiyi taka tsam-tsam kada ki
rasa aikin ki kinga kina taimakon iyayenki.
Jikin yarinyar yayi sanyi ta ce zan kiyaye
Insha Allahu Munecba ta ce, yi sauri mu gama
gogewa ki tafi Islamiyya bana son kina yin latti
kinsan na gaya miki idan kina aiki ki dinga yi kina
duba agogo da kinga lokaci yayi ki aje aikin kona
waye ki tafi Islamiyya idan kin dawo sai ki cigaba
da aikin dan zama ba karatun addini ba zai yiwu ba
ga dan Musulmi kinji ko? Ta gyada kai.
Muneeba ce ta sakata a makarantar ta
'ya'yan masu hannu da shunin unguwarne akwai ta
matan aure da akeyi duk ranar Asabar da Lahadi da
safe akwai ta rana karfe biyu zuwa hudu ita
Muneeban ke zuwa tayiwa Suwaiba magana ko za
ta shiga tayi kemadagas tace bazata shiga ba wanda
tayi a gidansu ya isheta sai Muneeban ta nuna mata
ai ilimi ba a gama shi ana nemansa ne (Minal
Mahadi Ilal Lahadi) daga tsumrnan goyo har zuwa
kabari, sai in ka mutu ne neman ilimi ya kare a
kanka da Muneeba ta lura abin yana neman zama
tashim hankali sai ta kyaleta tunda tace kowa tasa
ta fissheshi inji Suwaiban.
82
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Tana falo tana karasa goge-gogen ita kuma Karime hart a wuce Isla miyya sai taji kakarin Baffa da ke wasa a dakin baccinta ta yi sauri da gudunta
ta isa dakin baccin saita same shi yana aman jini ta saka salati tayi kan yaron da gudu ta sungumo shi, tasa hannunta a bakinsa don a tunaninta wani abu
ya hadiya ta kwakula bata ji komai ba illama aman jinin da ya ci gaba da bulbulowa ta fita dashi da gudu ta nufi dakin Suwaiban don a tunaninta
Mujeeb na can ko sallama batayi ba ta fada dakin
tana kiran sunan Mujeeb.
Suwaiban ta taso a aguje ta fito ganin danta
nata aman jini yasa ta kwarma ihu ta fita da gudu
tayi dakin Mujeeb ita ma Muneeba ta biyo bayanta
suka isa fallonsa a tare shima yana ganin yaron ya
mike jikinsa na kyarma ya amshi yaron a hannun
Muneeban yana tambayarta meya sani yaron tayi
magana cikin kuka wallahi bansan me ya same shi
ba ina falo shi yana wasa a bedroom dina shine naji
kakarinsa ina shiga na iske yana aman jini "Suwaiba ta sake kwarma ihu tana cewa shikenan
za'a kashemin yaro dama son da kike nuna masa
bana Allah da Annabi bane don ki cutar dashi ne shi
yasa ki ka jashi a jiki ya saba dake baya yarda da
kowa sai ke tunda Allah ke bai baki ba bari ki dinga
yiwa abinda na Haifa kisan mummuke ta yadda
babu wanda zai yarda zaki cutar da shi in aka ga
83
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
irin so da kulawar da kika masa wallahi idan ya
mutu bazan yarda ba kotu ce zata rabamu dakc".
Ihu Suwaiba keyi tana buga bango tana kara
fadar muggan kalamai Muneeba ta matsa ta riko
hannunta tace "Ki yarda dani Suwaiba wallahi ban
taba tunanin in cutar dake ba balle in cutar daBaffa
bawan Allah baisan komai ba sai in cutar dashi
wallahi nib a hali na bane kila wani abun yasa a
baki ya yankashi wallahi bansaniba kiyi hakuri,
tana maganar tana kuka Wiywiy.
Mujeeb dai yana rungume da yaron yana ta
kokarin kwakuloo ko meke bakinsa, amma abin ya
faskara sai ma aman jinin da yake cigaba da yi gaba
daya kayan jikinsa da na jikin MUjeeb din sun rine
da jini, itama Muneeba kayan jikinta duk jinine.
Suwaiba ta suri wayar Mujeeb ta kira
Goggo tana dauka ta ce, Goggo ku taho Gombe
yanzu ga Baffa nan sai aman jini yakeyi zau mutu
Muneeba c eta bashi wani abu a dakinta bamu san
ko meye ba so take ta kashe shi tunda ita bata haihu
ba.
Goggo ta rafka Salati tace A' kuwa idan ya
mutu ita ma sai na kasheta, gamu nan zuwa yanzu
ni da Hajiyarki gata nan muna tare.
Mujeeb ya tsare Munceba da idanu yana
mata kallon tuhuma yace "Ni fa banji komai a
bakin yaron nan ba wai me yaci ne? Muneeba tazo
gabanshi tace, wallahi babu abinda na bashi, nima
84
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
shiga kawai nayi na iske yana aman jini? Wata mika da yaron yaja tare da yin kara sai ga jini ta hanci da baki hard a guda guda, shikenan sai jikin yaron ya saki yaraf ba zakace akwai sauran rai a
tare dashi ba.
Wani kakkarfan Salati Mujeeb din ya saka, Muneeba ta kai hannu zata amshi yaron bata
Ankara ba sai ji tayi ya zabga mata wani bahagon
mari wanda yayi sanadiyyar daukewar
numfashimta tare da ganintana wucin gadi ta fadi
can gefe.
Bayan ta farfado daga jinyar radadın marin
ne ta nemeshi da Suwaiban a dakin ta rasa da gudu
itama ta fito ta iskesu har sun shiga cikin mota ta
suri hijabi a igiya cikin wadanda Jume ke wanke
mata a harabar gidan ko bushewa baiyi ba ta fada
motar suka nufi asibiti.
Suna isa aka amshi yaron aka shiga dashi
Emergency, su kuma suka tsaya a waje cirko cirko
har a wannan lokacin Muneeba kuka take yi
fuskarta a kumbure idanunta sun tara jini saboda
marin da Mujeeb yayi mata.
Ita marin bashi ke sata kuka ba kukanta na
tausayawa halin da Baffa ya shiga ne shin zai rayu
ko ba zai rayu ba, saboda jinin da ya amayar ba kankani bane zai iya sa jinin jikinsa ya kare. Hajaran majaran jume ya rako su Goggo asibitin suna zuwa basu bi ba'asin komai ba sai
85
a
C
1
1
1
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ruwan ba'la'in fada da suką hau yi wai za a kashc
musu jika. Muneeba ta tsananta kukanta ta durkusa
a gaban Goggo tana mata bayanin yadda abin ya
faru ta kara da cewa wallahi Goggo ko ban hada
alaka da Baffa ba bazan iya cutar da dashi ba, balle
Baffa fa dana ne duniya da lahira ko wani naga zai
cutar dahsi sai inda karfina ya kare balle kuma ni in
cutar dashi ribar me zanci idan na cuceshi me
zancewa ubangijina ranar gobe kiyama. Allah shine
shaida na, ina rokon ya fitar dani daga zargin da ake
mini.
Ta dan rage kukan sai ajiyar zuciyar da ke
zuwa mata lokaci zuwa lokaci idanunta na kallon
kofar shiga imajensin don ganin fitowar wani ko
zasu ji wane hali yaro ke ciki. "Duk surutun dasu
Goggo ke yayyafawa Mujeeb bai ce komai bat un
bayan da ya gaishe su ya na daga bakin kofar
imajensin yakai mari ya kai gwauro ya kasa zaune
ya kasa tsaye.
Wani likita ya fito daga dakin da saurinsa
zai shiga wani dakin Mujeeb ya tare shi da
tambaya, "Don Allah Dakta yaron yana raye ko ya
mutu? Likitan bai waiwaiyo ba kawai ya gyada
masai kace yace Yana raye" Kawai abin da ya fada
masa kenan ya wuce.
Mujeeb ya sauke ajiyar zuciya ya yi
hamdala ga Allah, sannan yazo inda su Goggo suke,
ya shaida masu abinda likitan ya gaya masa suma
86
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
godiya ga Allah sukayi Munceba ma dake rakube a
gefensu Godiyar tayi ga Allah tare da fatan fito da yaron lafiya kuma a gano abinda ya sababba masa aman jinin.
Kusan mintuna talatin da komawar likitan
sai ga yaron ya fito dashi a hannun shi babu sutura
a jikinsa ya mikawa Mujeeb shi da yake shi ne a
bakin kofa dakin sannan yace gashin nan ya sami yin bacci idan ya farka a bashi nono ko baya sha? Mujeeb yace yana sha Likitan yaci gaba da cewa "Idan yasha nono gurin da yaji ciwo zai dasashe sai
a bashi wadannan magunguna kada ku damu da kukan da zai dinga yi saboda makogoronshi ya yanke da yawa kun ganshi guntun madubi ne ya dauka ya hadiye sai ku dinga kulawa ku daina aje abubuwa na jin ciwo a kusa.
Ya mika masu wani tiren silba dake dauke
da ballin madubin da aka cirowa yaron duk sai kunya ta kama Mujeeb ya kasa hada ido da Muneeba sai su Goggo yakeyiwa bayani wallahi jiya garin kiriniyarsa shi ya fasa madubin a dakin Muneeban kuma tas aka share gurin kunsan kwalba da tsalle ina ga wani tsalle tayi ba'a share ba ba shine yau ya ganta ya dauka yasa a baki abin dai ya zo da tsausayi Allah ma ya tsare".
Ya mikawa Goggo yaron ta saka shi a cikin gyalenta ta lullubeshi suka mike don tafiya ya kai kallonsa fuskar Mneeba har yanzun hawaye ne ke
87
a
3
C
1
1
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
zirarowa a kuncinta hakika yasaņ kukan da takeyi
yanzun na nuna rashin yarda da amtinci nè da ya
nuna mata idanunsa sun rufe yabi ra'ayin matarsa
na cewa Munecban zata kashe masu da alhali ya fi
kowa sanin halin Muneeban ko giyar wake tasha ba
zata iya aikata abinda suka zargeta da shi ba.
Kai! Subhanallahi Wallahi shi yasan baiyi
mata adalci ba a irin tattali da kulawa da kaffa-kaffa
da takeyi da yaron nan sam bai kamata in wani ya
zargeta shima ya bi sahun, masu zarginta bay a
kamata ne ya kyautata zato a kanta, to amma ba
komai yasan tana da laushin zučiya suna komawa
gida zaije ya lallasheta ya nuna mata lallai yayi
kuskure tayi hakuri ta gafarta masa.»
Basu dade da dawowa gida ba Baffan ya
farka Goggo ta mikawa Suwaiba shi tace ta bashi
Nono yana fara shan nono sai ya sak ya soma kuka
duk yadda yake son yasha nonon yakasa sha
Mujeeb ua shigo rike da ledar magungunansa yake
tambayarsu "Au ya farka ne" Goggo tace Eh ya
farka amma ya kasa shan nono sai dai Kuka.
Ya mika hannu ya amsheshi yace 'Bari
kawai in bashi magungunan akwai na kashe zugin
ciwo da na bacci kila idan ya sake yin bacci ya
farka zai iya shan Maman ya bude magungunan ya
soma baashi, yana sha yana kallon fuskar baban
nasa yana dariya dama in dai za'a bashi magani
daga babansa sai Muneeba su kađai ke iya bashi ta
88
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria a
dadin rai in kuwa Suwaiba ce bata iyawa sai an rirrike shi ba a jima ba bacci yayi awon gaba da
yaron yaje ya kwantar dashi a dakin baccin Suwaiban.
Su Goggo suka ce tafiya zasu yi tunda abin
da sauki, Allah yakiyaye gaba yace "Haba Goggo b
zaku bari sai gobe ba, sannan gashi ko abinci fa
baku ciba Hajiya Harira tace 'Ba zamu kwana ba
tunda jikin Adamun ai da sauki amma dan Allah ku
dinga kiyayewa a daina barin abin jin ciwo a kusa
ta yadda ba zai dauka yayi wasa dashi har yaji masa
ciwo ba kunsan yaro ba hankali gare shi ba bai san
abin da zai yi masa lahani ba shi komai ya dauka to
shi agurinshi abin wasa ya dauka.
Mujeeb ya gyada kai wallahi Hajiya muna
kiyayewa tunda mun sanshi da kiriniya Muneeba
ma har tafimu kiyayewa kasancewar ko da yaushe
yana can gurinta ba ma yason zama nan dakin.
Goggo ta wani tabe baki tace kai nan har wani dadi kake ji da baya son zama gurin uwarsa, tunda can an wanke rubutun mantuwa an dirka
masa ya shanye harda manta dangi gaba daya an wanke an bashi irin yadda tayi maka, don ma a
tsaye na ke da kila inda nake sai an mantar dakai sai tayi rashin sa'a nafi karfinsu ita da uwarta yaro baisan kowa ba sai ita har kai ance ba ya yarda da uwarsa mai bashi nono na balle kai wannan ai abin dubawa ne, amma ba komai zanyi maganinta
89
a,
a
1a
la
ta
1
a
a
a
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
wannan karon sai nayi nasara akan kinibibinta da
surkullen ita da uwarta, sai na nuna musu nawa
surkullen yafi nasu taja kwata ta hau jijjikai nuna
alamun lallai wannan karon matakin da zata dauka
ba zaiyi kyau ba.
Mujeeb ya risinar da kansa kasa muryarsa a
tausashe yace "Don Allah Goggo kiyi hakuri kada
kice zaki dau mumman mataki akanta wallahi zan
iya rantse miki Muneeba bata yi wani asiri, ni na
san ladabi da biyayyar da take min shine matakin
nasararta na mallakar zuciyata ba wai asiri ba`ne,
shi kanshi Baffan wallahi kaunar 'yan uwantaka ne
take masa balle kuma ga ubansa a matsayin mijinta
kinga ai in dai mace mai sanin ya kamata ce ko ba
'yan uwartaka tsakaninta da mijinta dole ta so
'ya'yansa tunda tana ikirarin son ubansu, yanzu da
nunawa tayi bata sonsa bazan taba ganin farinta ba
kuma ba zaku ga farinta tunda bata son jikan ku don
Allah ku cire zargin asiri a al'amarina da Munecba.
Goggo ta daka masa tsawa Kai ! tafi can,
sakarai talasuru mijin tace kawai in banda ta wanke
ta baka kasha har ka dubi ido na da tsabar idon
sirikarka uwar matarka ga matarka duk a gabanmu
kace wai ladabi da biyayyar ne yasa ta mallaki
zuciyarka wato kama san ta gama mallakar
zuciyarka kenan, to sai ka gayamin ita Suwaibar me
take maka da har ta kasa mallakar zuciyarka? Bata
maka ladabi ne? bata yin tsabta ne? ko bata iya
90
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
girki banc? Ko kuma bata biya maka bukata ne, koko bata iya bane tunda ku mazan yanzun fitsararrun ne wai har da wata mace da ta iya gamsar daku itace 'yar gaban goshinku, sai ka gaya
min meye Suwaibar bata iya ba har Muneeban ta fita iyawa ta mallake zuciyarka.
Ga koshi ga kwanan yunwa sannan ai idan
ana dara fidda uwa ake yi, in bayan ga Hajiyar Suwaibar da daga shi sai Goggo da Suwaibar ne to
zai gayawa Goggo cewa duk abinda ta zano Suwaibar bata masa na farko dai bata masa wani
ladabi ga tsa-gatsa take gaya masa magana, sannan
babu biyayya idan yace tayi abu sai taga dama takeyi sabanin Muneeba wadda bama sai yace tayi ba in dai ta san abin da yake so to kafin ya
umurceta zata aiwatar.
Suwaiba batasan ta tsaya ta gyara girkinta
yayi dadı ba, ko yayane zata kwaba abinta ko su ci
ko kada suci babu ruwanta, sannan gurin tsaftar jiki data muhalli duk bata damu dayi ba ko danta bata
damu da tsaftarsa ba, Allah ya taimakeshi Kulawarsa ba'a hannunta take bad a wata rana sai
ya kwana bata yi masa wanka ba tunda ita dinma takan kwana batayi ba, balle idan tana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12