gwanin wani mugun wani ne, sannan ni a
192
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
gurina kwace goruba a hannun kuturuba wuya
bane, ina nan ina jiran dawowarsa nima da bakinsa
zai gaya miki matsayina, na irin dawainiyarsa da
nakc dauka wanda a yanzu ke ba za ki iya ba duk
ikirarin sonsa da kike yi nidin nan nice zan iya, Da
Mujceb ya dawo Goggo ta kara zayyana masa
abinda ya faru ya kira wayar Suwaiba ya ce tazo ta
sameshi a dakin Goggo.
Ta shigo tana yatsina tana taunar Cingon ta
tsaya kerere a gabansa shi da Goggo ta ce "Gani
fadi maganarka don sauri nake yi ina hidimar
abincinka ne kasan hidimomin ka a kaina na da
yawa dana gama wannan zan yi wannan. Ya gyada
kai ya ce eh! Ai na sani sannu da kokari meya
hadaki da Goggo ne? ta kalli goggo tana tabe baki
Babu abin daya hadani da ita illa abinda ta kitsa
maka haka yake haka akayi, nace na gaji da girki
biyu hidimarka nazo yi gidan aure ba ta wani ba in
kuma dole ne inyi hidimarka in yi ta goggo sai in ji
"ya raunana mura ga Suwaiban ya ce a'a sam ba
zai zama dole kiy i hidimar Goggo ba ta wuce dole,
saboda haka kiyi hakuri babu mai tilastaki yi mata
dole "Ya juya ya dubi Goggo ya ce yanzu yadda
za'ayi Goggo kawai ki dinga yin girkinki tunda ta
ce ba zata iya ba indai ana neman zama lafiya don
ni banason abinda zai tada min hankali.
Tsoro da mamaki ne ya kama Goggo duk da
yake ba yau bane Mujecb ya saba bin duk wani abu
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
da Suwabar ke so, amma na yau ya fi ba Goggo
alajabi Lakika kowa ya debota da zafi bakinsa
kadai zai Kona.
fa juya ta dubi Mujeeb ta ce Mujecbu yanzu
irin b tkraeun da zaka iya yiwa matarka kenan, kai
keda il o akanta amma ba zaka iya sata tayi abinda
zai faranta ran uwarka ba. To wallahi ka sani
aljanarka na dugadugina sai na daga maka zaka
samu ka wuce. In ka manta bari in tuna maka ni cc
na haife ka bayan shan wahalar daukar ciki na wata
tara nayi nakuda na haifeka na shayar dakai nayi
rainonka har ka girma ka zama abinda ka zama, in
har kana ganin akwai wanda zai wulakantani a
doron kasar nan ka iya kyaleshi to kayi babban
kuskure kuma wallahi idan nayi maka baki sai ya
kamaka alhakin nono na da kasha don kuwa baka
isa ka iya biyana ladan wahalar dana sha a kanka
ba, kama daga haihuwa shayarwa zuwa rainonka
saboda hak wallahi ka kiyaye don wannan
shu'umar yarinya zata kaika ga halaka, ta Kare
rnaganar tana nuna masa Suwaiba da yatsanta
sabab.
Mujeeb ya numfasa sannan ya ce Ni kam
Goggo banga illar Suwaiba ba in ma har tana da
ata illa ai da baki hada aurenmu ba tunda kullum
alkhairinta ki ke fadi ita da mahaifiyarta, shi ya sa
n kuma bana son Gata mata rai a dalilin bin
umuninki kin ga kuwa ban yi laifi ba idan naso
104
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
९
Suwaiba fiye da kowa a duniya kuma ke cc ki ka
nuna min muhimmancinta a rayuwata a matsayinta
na uwar 'ya'yana saboda haka kii hakuri da ita
tunda kc cc sanadin aurenmu..
Goggo ta muskuta ta ce, oho! Wato don nice
sanadin aurenku ai ka kyalcta tayi mini cin kashi ba
zaka iya daukar mataki a kanta ba? Ita din in 'yar
halas ce ai ban cancanci wofintarwa a gurinta ba in
har zata iya tuna tsayuwar dakan da na ke yi a kan
zaman aurenku ya dawwama gata nan ai ta sani.
Suwaiba ta tabebaki tana yatsina "Ni fa
Goggo in wani taimako kike min a kan aurenmu ya
kamata daga yau ki daina tunda ke bakya amfana da
komai ni kadaice ke amfana, amma fa ko ba komai
ni da danki duwaiwaine ya riga ya dame da kashi,
babu yadda za'a yi sai hakuri.
Mujeeb ya dubi suwaiba ya ce "Ya isa haka
wuce kiyi aikinki magana ta kare kiyi girkinki
itama za ta yi nata shi kenan Suwaiba ta juya ta yi
ficewarta ta barsu tana fita Goggo ta rushe da kuka
tana cewa, kaico na ni Rahina! Na dauko ruwan
dafa kaina, na riga na yi babban sakaci a rayuwata
wanda kafin in gyara wannan al'amarin zan sha
wahala. Yanzu Mujeebu a gaban idona ka iya fifita
matarka ka nuna ta fini matsayi ka lallasheta a gaba
na amma ni tsakanina da kai ba Kalrnar lallashi
balle ka bi umurnin ka yi abinda nake so sanin
kanka ne hawan jinin nan ba zai barni in iya yin
195
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
girki ba sai ka nemo min mai aiki ta dinga mini
girka da 'yan ayyuka tunda matarka ba zata iya ba.
Mujeeb ya ce, shi kenan zansa a nemo maki
zama kan yayi tsamari tsakanin sirikan guda biyu
don kuwa kiri kiri Suwaiba ta hana a nemowa
Goggo mai yi mata girki dole da kanta take miyarta
in an yi abinci a kawo mata goyonsa taci da
miyarta.
Muneeba kam tana nan gombe hankalinta a
kwance har ta fara bautar Kasarta a nan Gomben ta
cire damuwar matsalar aurenta da Mujeeb a ranta
tana nan tana addu'aba dare ba rana kan Allah ya
daidaita al'amuransu, in kuma rabuwarsu ce alheri
to Allah ya kawo sanadin rabuwar aurensu cikin
saukI ba tare da tashin hankali ba don yadda su
Baffa Adamu suka so sun so ne su je har Gombe su
tsitsiya shi a gaban uwarsa ya bata takardárta da
suka nemi shawararta sai ta ce su kyaleshi tana nan
tana addu'a Allah zai kawo Karshen al'amarin
saboda duk istiharar da ta ke yi a kan aurensu sai ta
ji sam zuciyarta bata son rabuwar aurensu zuciyarta
ta fi karkata akan son zama da mijin nata, kuma
kullum kwanan duniya dada kara sonsa ta ke yi har
bata son ta ji an fadi laifinsa ko ace ya yi ba daidai
ba akan lamarin aurensu hakan ne ya ke bata
tabbacin lallai akwai wani 6oyayyan alhairi da żai
biyo bayan aurensu to amma. fa sai an yi namijin
hakuri kafin a kai ga nasara kuma zata yi hakuri
196
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
tana addu'ar har sai an kai ga nasarar da take hararowa a wannan lokacin ne suka sha bikin khairi
da Khausar, an kai ko wacce gidan mijinta duka
anan Gomben sai fatan zama lafiya.
**** ***** *****
Ranar litini Mujecb tun sassafe ya bar gida zuwa
Ofis a dalilin neman gaggawa da aka yi masa a Ofis
din wajen misalin sha biyun rana Suwaiba tayi
bakuwa wata kawarta ce da suka hadu a asibiti
gurin'awon cikin Baffa tun daga wancan lokacin ne
suke zumunci da ita suna kuma ziyarar juna.
Sun baje a falon Suwaiban suna ta hira da ciye-ciye har lokacin Sallah ya yi bakuwar ta nufi
dakin baccin Suwaiban tayi sallah tana zaune a
gaban madubi Suwaiban ne bayan ta idar da sallah
suwaiban ta shigo dakin dauke da walida diyarta
zata canza mata kaya.
Tana zaune bisa gado suna hira da
bakuwarta inda bakuwar ke tambayarta, wai ni
maman Walida meye sirrinki ne yadda mijinki ke
nan nan da ke, ga gida kin zama ke kadai ba kishiya
kin kadata uwar miji ma naga lallaßaki take tamkar kwai, sai yadda kike so ake yi wallahi zanso haka a
gidana nima, ko don ni mijina hutsu ne ba'a sanin gabansa balle bayansa.
Suiwaba tayi dariya cike da nishadi tace, "Ai wannan siriin nawa na rike miji ba kowa zai iya
197
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ba, kuma sirrine a gare ni, in har kinsan zaki iya in
gaya maki in yaso sai in kaiki gurun da aka yi mani,
wallahi zaki mallake mijinki tamkar dan da kika
Haifa a cikinki zaki juyashi tamkar waina a tanda
ke wallahi idan kika ce ya zauna anan kada ya tashi
sai kinzo to ko motsi ba zai yi ba ina mai tabbatar
maki ko fitsari yake ji bazai iya tashi ya je yayi ba
sai dai yayi shi a wando saboda bin umurnin ki
haka nake da baban walida ko uwarsa sai na bashi
izini yake mata abu, in kuwa ina fushi dashi to
tamkar mahaukaci yake komawa sáboda lallashi
kuma kinsan wani abu wallahi da mamansa muka je
akayi komai amma tana waje bata sani ba na amshi
lakanina na zo na aiwatar ita a tunaninta idan na
mallake shi zan raga mata, sai kace wata uwata in
kina so in kaiki boka ne ai kinsa tamkar yankan
wuka ki mallake miji ki kore kishiya kuma har
abada bazai iya sake auren wata mace ba ke ko
macen banza a titi ya nema ba zai ji dadinta ba
kinga ko ai dole ya kyaleta tunda don lada ake yin
sallah yanzu me kika gani zaki iya.
Larai (Bakuwa) ta ce "Me zai hanani iyawa
ni da nake neman yadda zanyi na rasa tun tuni ma
ai da anyi an gama gaya min sirrin "Suwaiba ta
gyara zama ta ce "To saurara kiji aiki ne na neman
duniya kuma zaki samu amma akwai kauce hanya
sai an danyi sa6o in yaso sai ki tuba daga baya
(Kunji fa jama'a aikin sabo har da da, sannan idan
198
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
anyi a tuba tamkar amsar tuban a hannunsu takc,
kilama kafin sutüban su mutu. Allah ka tsaremu
amen).
Ta soma zayyano mata irin fasadin da ake yi
idan akaje gurin boka tun daga abin da za'a yi a
bukka ta farko cite sutura kama daga dan kwali har
wando sai a shiga gurin boka tsirara shima a same
shi tsirararar har zuwa masha'ar da zai aikata da
mutum umurnin hada najasar janabarsa data miji
kafin a wanke gurin sai an kwana ake yin wanka da
naman da za'a saka a farji ya kwana ayiwa miji
miya yaci to idan fa yaci shikenan anyi an gama.
Larai ta jinjina kai ta ce yanzu duk kinyi
wannan aikin? Ta ce, kwarai kuwa duk nayi shine
kuma jigon nasarar da kika ga na samu a gidan nan.
Wani irin kakarin amai suka jiyo daga falo
tare da amon salati mai karaji wanda ya cika falon
Suwaiba da gudu suka fito falon don ganin waye a
falon Mujeeb suka gani dafe da bango yana tafiya
cike da tangadi zai fadi a dalilin tsaf ya ji kalaman
Suiwaba tun shigarsu dakin ya shigo daidai lokacin
da Suwaiba ke cewa sirrinta na rike miji ba kowa
zai iya ba shi kuma ya labe don ya ji sirrin shine fa
ya jiyo sirrin .daya gigita shi ya zautashi inda ya ji
wai har ya taba cin naman da ya kwana a gaban
mace bai sani ba.
Kafin su iso gare shi ya zube Fasa warwas
bayan ya yi wata kara mai firgitarwa Suwaiba ma
199
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
yanka ihu tayi tana fadin 'Shi kenan ya ji sirrina da
boka ya ce kada in bari ya ji in har ya ji to kada in
yi kuka da kowa akan abinda zai biyo baya shi kc
nan na shiga uku don bansan me zai biyo baya ba.
KASH TO NIMA SAI KUYI HAKURI
KU BIYONI DON JIN ABUBUWA DA DAMA
DA ZASU BIYO BAYAN WANNAN
BADAKALA.
RAHAMAN ZARIA CE
08068895555, 08028434948.
PRINTED:- BY
ZAZZAU VENTURES PRINTING PRESS
08035336868, 08028401199
200
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 12