An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
WATA KUSAN
RAHMATU HASSAN ZARIA (Mrs, Abdullahi S. Paiko)
こ
WATA KUSAN 2
******
Rahmatu Hassan Zaria
****** ******
D
uk wani abu da ta san zai gamsar da mai Gidan, shi ta yi a matsayin abin karyawa. Tayi
kunun gyada ta dafa ruwan ti wanda ya ji kayan Kamshi, sannan ta dama koko, saboda Goggo tafi
son koko, sannan ta soya kosai ta soya dankalin
turawa da plantain (Agada) can a gefe kuma ga
farfesun kayan ciki da farfesun kifin ruwa, ko wane
ta zuba shi a food flask, su kunun kuma ta zuba a
manyan jug masu rike zafi.
Gaba daya kayan abincin a kicin dinta ta
barsu, idan Allah Ya sa ya shigo sai ta kai falonsa
tunda a can suka tsara za'a dinga yin break fast. Ta
shiga bayi tayo wanka tazo ta zauna tana shafa mai,
sannan ta ji an turo kofar dakin baccinta tare da
Sallama. Mujeeb ne kallo daya tayi masa tayi
saurin kawar da kanta dalilin bacci da gajiya da ta
gano har yanzun basu saki idon ta ba, nan da nan
kumallon matan ya yunkuro mata, amma da ta tuno
shawarwarin Antin Zaria sai ta hadiye kishin da ya
tirniko mata, ta juyo tayi masa duban rahama tace,
"yayana yau ka makara ko da yake dole ayi ma
uzuri amarci ba karya ba ne." ya harareta yace "in
baki raba bakinki da zancen amarcin nan ba, sai na
tsaga bakin nan gida biyu". Ya sa hannu ya
mintsini bakin nata ta yi 'yar kara ta ce," yi hakuri
na daina kada ka yaga min bakin in rasa na
magana". "Yа сс, "Ba ki da kirki maimakon ki
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
tambaya lafiyata, tunda kinsan bana makara shine
zaki wani eearci". Ta ce, to dai yanzun ina
kwaria, ya kwanan amarya? Ya ce lafiya lau, ni tun
asuba da na awo Masallaci yaron Malam Kabiru
yake gayamın uban ba lafiya shi yasa bai fito
masallaci ba, dama jira suke ayi Sallah su kai shi
asibiti, shine fa na zo na dau mota muka kaishi
asibiti sai da na ga an bashi gado an sa masa (drip)
karin ruwa shine fa hankalina ya kwanta na yo
gida, nayi wa Suivaiba waya cewa ta gaya muku".
Та сс, "Oh! Allah Sarki me ke damun Malam
Kabirun jikin da sauki ko? Ya ce, "То
Alhamdulillah zamu ce, amma yana jin jiki malaria
ce ga hawan jinni, amma abin ya zo da sauki sai dai
fatan Allah ya bashi lafiya. Na kira wayarki in gaya
maki naji ta a kash, me yasa meta? Ta ce, "Jiya
hadimar jama'a bata barni nayi cajin wayar ba har
ta mutu, shi ne da zan kwanta na kasheta na sa
chaji, sai yanzur ne ma na kunnata.
Ya ce, Anyi abin brcak fast ko? Та се,
"Yes, kanwar ango tayi sai kuma me? "ya yi dariya
ya ce. "Yau dai na ga da zolaya kika tashi, ni zanje
nyi vanka ki kawo komai alo na sai mu karya
acan Lka muka ısara ai? "Ta gyada mas kai 'n
kanika gaya mata".
Yana fita ta tashi tayi shiri cikin wasu riga
da Siket na atamfa England mai ruwan ganye shar
da adon ja a jikinta, yar ayin kwalliyar ta fiddo ta
9
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
sosai, ta saka jan takalmi filat ta yafa fan karamin gyale ja mai shara-shara, don bai rufe komai na jikinta ba kawai dama ta yafa shi ne don ya kara fiddo da kyan kwalliyarta, hatta dan kunne da sarka da zobe da abin hannu jajaye ta saka, sai ka rantse ita ce amaryar, sai kamshin dadadun turaruka take zubawa. Ta dauki warmers din abincin ta soma kaiwa dakinsa bisa katafaren teburin cin abincin
dake falonsa, mai kujeru guda shida a gewaye ta jera komai, tana dada goge gurin ne ya fito shima cikin kananan kaya, riga shirt ce a jikinsa (Long sleeve) deep red sai wandon Chinos baki, suka kalli juna sukayi murmushi sannan ya ce, Kinyi kyau sosai". Ta rausayar da kai tace, Har na fika yin kyau kai fa ango ne dole kayi kyau, har wata kiba fa ka kara yi yau kadai. "ya kyakyale da dariya ya cc, "Rashinki yasa nayi rama, amma zaki yi min sharrin wai nayi kiba, ki ci gaba zan rama.
Ya kai hannu ya jawo ta ya hada ta da jikinsa yana dan sin sinanta, ita kuma tana zillewa ta ce "Don Allah ka bari kada amaryanka ta shigo ta ganınu bai kyautu ba." Ya ja tsaki yana harararta,
ya soma latsa wayarsa ya kira layin Suwaiban tana dauka ya ce "Ke fa muke jira zamu yi break fast ta ce, "Gani nan zuwa". Ta kashe wayar.
Mintuna biyu bayan nan sai gata tayi sallama ta shigo cikin dogowar riga ta bacci. Kallo daya tayi wa Munceba tayi saurin dauke kanta
7
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
saboda irin kwalliyar da taga ta cancanda sai kace it
ace amaryar, duk sai ta ji ta muzanta ta kunyata da
ta shigo haka, ba wanka su kuwa kowa ya dau
wanka ya tsantsara ado sai tashin kamshi suke yi.
Ta dubi Mujeeb ta ce, "Wanka zan shiga ka kira ni,
ko inje inyi ne?. ya ce, "No ba zai yiwu muyi ta
zaman jirann ki ba, ki zauna mu gama in yaso kyaje
kiyi wankan". Ita kanta ta san dai ta fadi zatayi
wankan ne don kada su ga kazantarta, amma ba
yanzu ta yi niyyar yin wanka ba.
Ta ja kujerar da ke kusa da Mujeeb ta zauna,
sannan ta gaishe shi, a dakile ta juya ta gaida
Muneeba, ita kam Munceban ba ta damu da yadda.
ta gaisheta a dakile ba, har ta bi bayan gaisuwar ta
ta da cewa "Ai na so in biyo ki da abin karyawar
dakinki tunda na san a gajiye zaki tashi saboda
kujiba-kujiba sai ogan ya ce gara a hadu". ta danyi
yarr da idanu ta ce, "Ai hakan ma ya yi".
Da suka kammala karin kumallon ne suka
koma kan kujerun falon suka zauna. Mujeeb yayi
musu nasihohi akan su zauna lafiya a tsakaninsu,
saboda shi ba ya son hayaniya a gidansa zaman
lafiya yake nema, kuma ya umurci Suwaiba da ta ba
Munceba girma a matsayinta na babba kuma uwar
gida a gareta, ita ma Munceban ya nuna mata da ta
kama girmanta sannan tayi mata adalci a matsayin,
karama a kanta, su rike junansu amana wanda ya
8
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
ha'inci dan uwan zamansa to ya san abin da zaije ya tarass a gobe kiyama.
Ya karkata ya dubi Muneeban ya ce, Kina da wani bayanin da zaki kara? Ta girgiza kai tace, "Babu wani bayani sai dai addu'ar Allah ya bamu
zama lafiya ya hada kawunan mu" ya amsa da "ameen" sannan ya waiwayi Suwaiba ya ce, "Ко kina da abin cewa? Ta girgiza kai tace, "Bani dashi" ya ce, to shi kenan tunda ba ku da abin cewa. Magana ta karshe itace rabon kwana zan dinga yin
kwana bibbiyu. Yayi ko? Suka hada baki gurin
cewa, "Ya yi"yayi addu'ah suka rufe zaman.
Muneeban tayi saurin mikewa ta soma hada kayan da suka ci abinci za ta fita da su, ya dubi Suwaiba da har yanzu ke zaune ya ce, tashi ma na ki tayata kwashe kayan".
Daga kicin Suwaiba dakin Goggo ta shiga.
sai a lokacin ne za ta je gaishe ta, tana shiga bayan
ta gaida goggon sai ta dubeta sama da kasa tace, me
zan gani haka, Baki yi wanka ba ne na ganki ba kwalliya? Ta ce ban yi ba yanzu dai zanje inyi Goggo ta jinjina kai ta ce, "Lallai sai kin zage
damtse a gidan nan ta fannin kwalliya ko baki ga
matar Gidan bane yadda tun Subahi tayi wanka ta dau uban gayu tamkar zata je amsa liyafa fadar shugaban kasa, sai uban kamshi take zubawa.
amma ke kin zauna kina fama da kayan bacci a
matsayinki na amarya ba ki ji kunya ba da ki ka
9
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
jeru da ita? Haba Suwaiba tun yanzun karki bada
mu ta fanni kwalliya sai fa kin dage don yarinyar
nan tankar karuwa take wajen iya tsara ado, shi
yasa shi kuma sakaran ko a gaban uban waye ba ya
jin kunyar saki baki yana kallonta kamar zai
hadiyeta ko ni nan kwalliyarta da tururrukan da
take sawa suna birgeni balle shi da akayi dominsa
tashi maza ki wuce kije kiyi wanka ki tsantsara ado
fiye da nata.
Suwaiba ta mike jiki a salube ta wuce
dakinta zuciyarta cike da tunanin kishin Munceban
kuma hakika zancen goggo gaskiya ne tunda itama
taga zahir, da suke karyawa bai da abin kallo da ya
wuce Muneeban lallai kam dole ta mike tsaye da
kwalliya sannan ga uwa uba abubuwan da zata yi
amfani da su wajen kwanciyaarsu da turaruka na
jan ra'ayin miji da wanda zata sa masa a abinci da
abin sha tana fatan idan ta fara amfani da su
kwalliya ta biya kudin sabulu.
Ta dana masa tarko jiya don tayi wa kanta
shiri sosai kamar yadda Hajiyarta ta tsara mata sai
dai kash! Wanda akayi dominsa din bai fada tarkon
ba yana gama shirin bac.insa a dakinta
kwanciyarsa ya yi ya hau sharara barci wai a gajiye
yake, to amma in kere na yawo zabo na yawo wata
rana dole a hadu. Ta aje wannan tunanin ta fada
bayi ta hau Sallah wankan kece raini.
10
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Z2
hannunta
Muneeba ta shiga fakin Goggo da Sallama. fauke da Filet da ta yanka kayan marmari ta iske Goggon kishingide a gado ta ce "Goggo sannu da hutawa, ga kayan marmari sunyi sanyi, naga kina son kankana da sanyi”. Ta tashi zaune tana gyara daurin kallabin ta ta amshi filet din sannan tace nagode, amma wannan ba zai hanani in gaya maki gaskiya a cikin gidan nan ba. Don haka dubi yadda kika rangada kwalliya sai kace kece mai girki, irin wannan bashi da kyau saboda kwalliyar
nan sai ta sa shi ya biye maki ku shiga hakkin yarinya ku aikata sa6o, daga zuwanta jiya-jiya, ko ita da mijin ke hannunta bata yi irin wannan adon
na daukar hankali ba ki dai yi amfani da iliminki na Muhammadiyya ni kada a jefa dana ga halaka ranar Lahira ya tashi da shanyayyen 6arin jiki.
Gaban Munceba sai faduwa yake yi, jikinta yayi sanyi wai wannan 'yar kwalliyar da tayi ita се abin surutu har ake ganin ta yi adon jan ra'ayin miji
zuwa garcta, alhali kowa ya santa da kwalliya, ko ita goggon ta san haka, amma yau kadai za'a lauya mata zance ace tayi ne dan yaudarar miji. Ta dan rausayar da kai tayi magana а
ladafce, "wallahi Goggo ba da wata manufa nayi kwalliyar nan ba, kawai dai ni na riga na saba da yin wanka da wuri ne inyi shiri na, ba na son zama ba wanka tunda shi ma yaya Mujeeba na san baya
son ganin mutun cikin kazanta, shi yasa nake
11
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
kiyaye abin da baya so, amma ni banyi da wata
manufa ba".
Goggo ta dan ja gajeran tsaki tace, "Ai gara
ki gaya mini keme son miji ce mai bin umurninsa
da kiyaye dokokinsa, ita ma Suwaiban da ta shigo
cikinku yanzu zata yi abinda da yake so, in dai
kissa da kissisina ne kowa da su ake haihuwarsa sai
dai mutum ya ki yi, ballema Suwaiban diyar Hajiya
Harira ai babu abinda za'a layance mata sai ku zuba
aga wadda zata amshi miji a hannunta.
Muneeba hakuri ta dunga ba Goggo har ta
samu ta baro dakin tayi saurin wucewa nata dakin,
ta wuce can dakin baccinta ta haye gado ta soma
zuba hawaye na irin wannan rashin kauna da
Goggon ta keyi mata, wanda har ta gwammace ta so
bare a kan ta, alhali ita ce jininta itace dolenta
duniya da lahira gashi tana auren danta ai kuwa
KUSANCIN ya kai karshe, kuma zumunci mai
kyau ka dauki danka ka hadashi aure da 'yar dan
uwanka, jinni ya gauraya da jini, zumunci sai ya
dada karfi in dai ba'a sa son zuciya ba.
Tayi kukanta mai isarta tana mai jinjina
zaman Goggo a tare da su, irin ınatsalolin da zata
dinga fuskanta, a dalilin tsananin sa mata ido da
tayi akan al'amuranta ita kam tana rokan Allah ya
rage kiyayyar ta a zuciyar Goggo domin zuciya
bata da kashi, tana tsoron kada wata rana a wayi gar
ta mayarwa da Goggo amsa mara kyau akan irin
12
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
zarge-zargen da ta ke mata tare da bita da kulli akan al'amuranta da mijinta, fatanta suyi zama nesa da juna da Goggon tunda idan suna zama a tare akwai guma-guman matsaloli.
Bacci ya fara fizgarta kenan Mujeeb yayi sallama ya shigo yazo ya zauna daf da ita, ya soma tabata yana tashinta,, "Muneeba wai bacci kike yi
ne? Tayi lamo takI tashi din bata son ya ga halin da
take ciki, amma babu yadda zata yi dole ya matsa
mata ta tashi don cewa yayi yazo ne suyi magana
yana ganin canzawar idanunta ya kidime da
tambayar ta, "me kuma ya same ki? Kuka kikayi?
"ta girgiza kai tace, Ba kuka nayi ba baccin da na
soma ne", y ace, wannan ba barci bane kuka ne, ga
ragowarsa nan a idonki. Me ya faru gaya min don
naga shigarki dakin Goggo? "Ta ce babu abin day a
faru". Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, ni na san wani
abu ya faru sai dai ki 6oye min amma don Allah ina
rokonki kiyi hakuri, ki manta da koma mene ne ya
faru ki tayani mu cigaba da yi mata biyayya mu
lallaba muyi abinda take so har zuwa lokacin da
zata koma".
Muneeba tayi murmushin yake tace, "Babu
komai Goggo uwa ce a gareni, duk abinda zata yi
mini bana daukansa a batanci, illa gyara take mini,
ko nasiha ko yanzu ma abin data gaya mini hakika
gaskiya ne kuma Insha Allahu zan gyara". Ya kafa
mata idanu cikin Tuhuma ya ce, 'Me ta gaya miki?
13
-
WATA KUSAN 2
Rahmatu Hassan Zaria
Ta girgiza kai, wannan zancen mune ni da uwata ba
sai ka ji ba, ya Langabar da kai yace, "yi hakuri ki
gaya mini, indai gyara ne akan wani laifi to na san
har dani a ciki kinga sai mu taru mu gyara "Ta cc,
"Don Allah kayi hakuri ba sai na gaya maka ba,
garan nawa ne ni kadai bai shafe kaba".
Ganin ransa ya baci akan kin gaya masa da
tayi ya sa ta gaya masa yadda suka yi da Goggo.
Murmushin takaici yayi, "Wannan ba shari'a bane
ace mace ta daina yiwa mijinta kwalliya sai ranar
da take da girki, ita in ba zata yi kwalliyar ba sai ta
zauna da kazantarta, in kuma gyara Goggo keson yi
ita ya kamata tayiwa fadan abin da ya kamata tayi
bat a dinga tayata kishi ba, ke ya kamata ta taya
kishi ke jininta ba Suwaiba ba ba diyar aminiya".
Muneeban ta ce "Mhm! Ni dai zan gyara abinda
akace in gyara, in ma ance in daina kwalliyar ne
wallahi sai in daina zama lafiya ai yafi zama đan
Sarki. "Y ace 'ke! Ba fa zai yiwu ba ki daina abinda
ke faranta mini rai, haka kurun daga zuwan yarinya
jiya-jiya har an fara kananan zance, wallahi in ma
kinibibin tane zanyi maganinta, gara ma ta daina.
Sun danyi shiru na wasu sakonni sannan ya
kutso maganan da ta kawo shi, 'Dama maganan
zuwa ganin Likitan da zaki yine a Saudiyyya, yanzu
ta internet na sami sanarwan ranar appointment din
da zkai ga likita 'Daya ga watan gobe, kinga nan da
sati hudu masu zuwa kenan sai mu fara shirye14
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
a
shirye tare da addu'ar Allah yasa a dace, idan munje can ma addu'ar dacewa zamu yi tayi ka'aba don ina tsananin son in ga kin haihu bana son in fara hailiuwa da kowa sai ke".
Ta sauke ajiyar rai cike da damuwa ta cc, "Ya zaka yi da abin da Allah ya tsara, in sai wata ta haihu tare da kai sannan ni zan haihu, sai muyi wa Allah godiya in ma ya kaddaro min kwata-kwata ba
zan haihu a rayuwata ba ya za mu yi sai hakuri".
Ya yi saurin sa hannu ya toshe bakinta ya
ce, yi shiru bana son irin wannan maganar da kike yi. Insha Allahu sai kin haifo min 'ya'yaye dozin a
gidan nan har da ‘yan biyu da 'yan uku". Ta gyada kai cike da farin ciki addu'arsa ta ce, Allah ya sa
amma ina rokon alfarma in har Suwaiba ta rigani
haihuwa ka bani kyautar abinda ta haifa, zan rikeshi
tsakani da Allah tamkar ni na Haifa", ya ce 'ya'ya
na mallakinki ne duniya da lahira wannan kada ya dameki, gashi can ma na hangoki cikin yaran da
naki da nata kina koya masu karatu sukayi murmushi dukansu.
Kwanaki bakwan da ango keyi a dakin
amarya Muneeba a wannan lokaci hakuri kawai ta dinga yin a wasu al'amura dake faruwa a cikin gidan nasu, wasu ta fannin Goggo wanda dama su
ta riga ta sabá da su ta kuma san hanyoyin da take bi na hakuri da lallashin zuciyarta. Matsala ta biyu
kuma irin takun da amarya Suwaiba keyi a gidan na
15
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
takun Kasaita da nuna Gadara da yin komai cikin
isa da iko ala dole ita amarya da bata laifi amma
inji 'yan iya Magana, sannan wadda keda fada a
cikin gida gurin uwar miji, shi yasa ma Muneeba da
ta ga irin abubuwan da ta ke yi na Gadara, yasa ta
tattara al'amuranta gefe, tunda ko magana tayi mata
kafin ta bata amsa sai taja fasali tayi yatsina kafin ta
bata amsa, haka dai tayi ta binta don bata san ace ga
wata matsala daga 6angarenta ta fito amma da ta ga
abin ya wuce gona da iri sai ta kyaleta tunda babu
lallai ba tilas zaman jika da kaka.
Shima ta 6angaren uban gayyar Mujecb taga
abubuwan da Suwaibar keyi na damunsa amma
baya iya tsawatar mata tunda Goggo ta dau idanu ta
maka masu, idan yayi Magana saita dirar masa da
fada tace zai matsawa Suwaibar, shi yasa duka suka
taru suka zuba mata idanu take yin abinda taga
dama a gidan amma ya sha alwashin zai yi mata
saiti da zarar Goggo ta wuce dukku suka saura su
uku a gidan.
Muneeban ta maida hankali ne yanzu kan
tafiyarsu Saudiyya, sannan ga bikin babbar diyar
Hedmasta da za'ayi, itama nan Gomben za'a
kawota, za'a yi bikin ne ana saura sati daya su
Munceba su tafi jin cewan Munceban zataje Dukku
biki yasa Goggo itama ta soma shirin komawa gida,
a cewarta sais u tafi tare.
16
스
2
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ana gobe zasu tafi duk suna dakin Goggo ana hira sai Mujceb yake dada gayawa Goggon Maganar tafiyarsu sati mai zuwa, sai cewa tayi, wannan tafiyar ya kamata ace da Suwaiban akayi itama sai taje ta yi UmAra". Ya ce "Ai in zan tafi da wani kece ya kamata in tafi dake kije kiyi Umara
to amma sai naga gara in bari in biya miki Kujerar
Makka, ko me kika gain?" Wata uwar guda Goggo
ta rangada a maimakon tayi hamdala ga Allah ko tayi Kabbara ta kara da cewa "Ai gra inje aikin Hajjin haihuwa mai rana, yau nice zanje aikin Hajj lallai haihuwa ta biya ni, habawa yaushe ne za'a ce
ba'a son haihuwa ko don abin da ka Haifa ya huce
maka takaicin duniya idan Allah ya azurta shi, mu
kan muna son haihuwa kuma mun samu gashi nan
muna ganin amfaninta bamuyi ta a banza ba".
Dajin wannan kasan shagube ne take yiwa
Muneeba, kuma kowa yaji yasan da ita take, nan da
nan idanun Muneeban suka kawo ruwa, duk iya
kokarinta na maida hawayen said a suka silalo suka
zubo mata tayi saurin sharesu, Mujeeb ya lura da
haka sai ya ce " Ai Goggo ba naka daka Haifa ba, rikon dan wani ma idan kayi tsakani da Allah sai da
yayi maka abinda dan da ka Haifa ma baiyi maka
ba, duk wanda bai haihu ba ai baya cire rai da
Rahamar Ubangiji kawai addu'armu Allah yasa 'ya'yan da zamu Haifo a rayuwanmu su zama masu
albarka, su zamo 'ya'ya na gari.
17
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Washe gari Juma'a bayan saukan Juma'a
Mujeeb din ne da kansa ya kai su Goggo Dukki,
gida ya zama na Suwaiba ita kadai da mijinta tunda
a Kalla Muneeba za ta yi kwanaki uku ko hudu a
Dukku da ace ya bar ta ma sati taso tayi sai yace bai
amince ba kwana uku zuwa hudunma da kyar ya
barta.
Kai tsaye gidan Goggo suka cuce suka
sauketa tare da himilin kayayyakin da Mujeeb ya
saya mata a Gombe, da kayan abincin da ya saba
saya masu, a tunanin Goggo Muneeba ma nan
sasansu zata sauka inda komai nasu yana nań yadda
yake idan suka zo nan su ke sauka, amma yau tun a
gida Muneeba ta rokI Mujeeb alfarmar ya barta ta
sauka a gidansu tunda shi komawa Gombe zai yi ba
zata ji dadin zama ita kadai babu,shiba, shi yasa ya
amince mata da suka sauke Goggo suka yi mata
sallama suka wuce gidansu Munecban.
Jama'ar gidan murna sosai suka, yi da
zuwansu Munecba, a dalilin sun san indai tazo tana
masu yayyafin kudı balle kuma ace tare take da
mijinta to ranar sun warke talauci don kuwa ba
manyan gidan ba kawuninshi hatta mata da yaran
gidan kowa nada kason shi koda baka nan zai bada
a ajiye maka, shi yasa yanzu- suka rage yiwa
Muneeban tsegumin da suka saba, sai dai tarairaya
da nan nan da ita.
18
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
Ya dade a dakin Inna suna hira da Inna da
Mustapha da ya shigo akan aikinsa da aka yo masa tiransfa daga Yola yanzu ya dawo nan Gombe. Da Mujeeba zai tafi ya debo kudi masu tsoka ya ba
Inna acan Kogar gida ma ya dade da baffaninsa
suna tattaunawa akan noma da akc masa anan
Dukkun wanda Baba Adamu ne ke tsaye akan
komai gashi Allah ya sanyawa noman albarka sosai
ya shaida musu maganar tafiyarsu Saudiya don
zuwa ganin likita. Baba Adamu y ace "Aiko don mahaifiyarka ma data sawa 'yar uwarka kahon
zuka tana ganin taki haihuwa sai kace ita zata ba
kanta wallahi gara kuje kasa mai Tsarki ku nemi
magani, sannan kuyi dawafi ku gayawa Allah Insha
Allahu za'a dace. Allah yasa ku je lafiya ku dawo
lafiya ya sa aje a sa'a". Ya yi musu alhairi sosai
sannan ya tafi dauke da farin cikin addu'o'insu.
***** *****
Mujeeb da Muneeba sun saka a Saudi Arabia
Lafiya kai tsaye daga filin jirgi suka dauki shatar
taxi ta kai su Hotel inda sukayi masauki kuma sun nemi hotel ne wanda ke kusa da asibitin saboda su
samu saukin zirga-zirga, kuma da yake wai wani abokin Mujeeb din da ya taba zama yayi aiki Saudiya shine yayi masa bayanin duk yadda zasu yi idan suka zo da shawarar Hotel din da zasu sauka
19
a
V
U
WATA KUSAN 2 Rahmatu Hassan Zaria
har ma ya hadashi da wani abokinsa dake nan
Saudiyan ya basu number
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12