sai ya koma ya debo fam
guda. Ya yi ta yin haka kullum. Nan da nan kafin wata takwas ya
sa aka debe dannin gidansa, aka gina masa na kasa. Aka yi
zauruka kamar goma sha biyu kafin a shiga gidan. Aka ta da
soraye. Ya kwashi kayan sassaka duk ya kona.
Cikin mako guda ya auri 'yam mata uku, ya gama da matarsa,
suka yi hudu. Duniya ta komo sabuwa, sai katta ke ta kaiwa suna
komowa cikin gida. Aka manta da kiransa Maikujera, sai aka
lakaba masa Maigida. Da ya yi magana sai a zabura a gama abin
da ya ce, kome ya faďi sai ka ji barori na cewa, "Allah ya kyauta
yin maigida."
Bai cika shekara ba sai da ya daure doki goma sha biyu a
bargarsa suna harbin iska. Da ya hau sai a bi shi tii, kamar Sarki.
Mutane suka yi ta al'ajibin yadda ya yi arziki haka. Suka ga ko ba
ya saye ba ya sayarwa, amma kullum abin nasa gaba gaba ya ke
90
ci. Da mai garin da wadansu sun fara hassadar abin, suna
kushewa. Amma daga baya, da suka ga hassadarsu ta zama taki,
sai suka saki, suka mika kai neman abin sutura.
Da ba ya girman kai da wannan abu, amma daga bisani mutane
da makada da maroka suka kumbura shi, har ya fara hura hanci
yana alfahari, tun ba in ya je dutsen kudi ya ga abin kamar ba
alamar karewa.
Ran nan yana zaune bisa kujera, sai ya ce a ransa, "Kai, ni fa
wahalar zuwa dutsen kudin nan kullum ta dame ni. Kullum,
gemai-gemai da ni, a ga na nufi daji saboda fam guda. To, ni ba
abin in ki zuwa ba, don ina so in kwashe kudin duka inda yana
yiwuwa. Gobe dai fam biyu zan debo gaba daya in gani.
Watakila dai Malam Dogo ya ki barina ne, don kada in huta wa
raina. Amma fa ina amfanin a ga kamata ya tashi ya shiga daji
don fam guda?"
Ko da magariba ta yi, sai ya tafi dutsen kudi, ya debo fam biyu,
ya fito. Sai ya ce, "Haba, na sanı da ma abin nan na Malam Dogo
ya rufe ni ne. Tun da ya ke dai nawa ne, mene ne na yi mini
haka?"
Ya yi kamar wata guda yana diban fam biyu biyu kullum. Sai
wata rana ya ce, "Shin me ya sa ne zan rika wahala da kaina don
'yam fam biyu tak? An ce ba sata na ke yi ba. To, ba na kawo
abina gida, kowa ya huta, ni ma ko in sami hankalina ya kwanta
in yi kiba, da wannan wahalar shiga daji kullum, sai ka ce
talaka?"
Sai ya sami buhunan gishiri ya ajiye, ya ce, "Gobe da
wadannan za ni, in rika cika su ina kawowa gida har in kwashe
sarai, in huta da shan dari kullum magariba."
Gari na wayewa, ko da magariba ta yi sai ya kwashi buhunan
ya nufi dutşen, yana takawa sai ka ce namijin agwagwa, don cikin
'yar shekan nan guda da rabi ya zama sai ka ce taiki don kiba.
Ni'ima da din dadi duk sun sa har furfurarsa ta koma baka. Ya yi
tsar, shuni ya huda shi, jikinsa sai kalli ya ke yi.
Da ya isa sai ya zauna ya huta, yana kulla abin da zai yi a ransa
in ya kwashe kudin nan duka. Yana cewa lalle ya buge gidansa ya
sake wani. Matansa kuma duk ya kamata ya sake su, don tun da
suka kai ga shekara guda da rabi a dakunansu ai sun tsufa.
Da ya gama kulle-kullen abin da zai yi, ya tashi ya shiga kogo
da buhuna. Ya ajiye su gefe guda, ya dauki daya don ya cika
yadda ya ke iya dauka, ya kai gida ya dawo. To, ko da ya duka ya
sa hannu zai diba, sai ya ga randar kudin ta yi kasa, ta bace.
Dutsen kuma ko kasa ko bisa, sai aka bar Usuman jikan Usuman
nan tsugune yana sallallami, yana da na sani sa'ad da ba ta da
91
amfani. Ya kwashe 'yam buhunansa, ya nufi gida yana bakin ciki.
Da ma ai irin bukatarsa ka san ba tari ya ke yi ba. Kafin wata
uku dan abin hannunsa duk ya kare, ya sayad da dawakinsa,
barorinsa da suka ga abin na lalacewa suka watse. Da wadannan
kudi na dawaki suka kare, ya karyar wa mai garin da gidansa
araha, ya yi awo da kuďin.
Kafin shekara wannan dan hatsin ya kare, sai matan nan yara
suka fita, suka bar shi da tsohuwar matarsa. Da ma an ce tsohon
doki sai mai shi.
In gajarce maka labari dai, na rantse har da rawaninka, Allah
ya ba ka nasara, ba a yi shekara biyu ba, sai da ungulu ta koma
gidanta na tsamiya. Ka ji aikin zari. Kowa ya yi kokarin wai ya
sami fiye da abin da Allah ya ba shi, ya lalace.
Kafin aku ya kare ba da
labarin nan gari ya waye. Musa
ya dubi Barakai, ya ce, "Kin ga
irin halin nasa ba?"
Barakai ya ce, "A'a! Ashe
kana da gaskiya, ka ji abu
kamar na magani! Wallahi ko da
ya fara labarin sai na ji na manta
abin da ya kawo ni. Amma ba kome, na dawo da magariba." Ya
fita ya koma gida, ya gaya wa Waziri yadda aka yi. Waziri ya
fusata, ya ce, "Har kai ma watau tatsuniyoyinsa sun rude ka ko?
To, gobe ka fito ba da shi ba, ka ga abin da zai same ka."
Da magariba ta yi sai ga Barakai ya yiwo shiri ya dawo, ya се
wa Musa, "Zan sake kwana nan gunka, yau lalle mu fita. Suka
zauna suka yi ta hira. Da suka ji bayin nan sun yi shiru suka iske
aku, Musa ya ce, "Zan tafi, ga shi har na sami 'yar rakiya
kuma.""
Aku ya duba ta taga sai ya ga hadari ya taso, yaşce wa Musa,
"Haba, ko kuna hauka kwa fita yanzu cikin wannan ruwa?"
Barakai ya ce, "Ai ba a fara ruwa ba, ma tafi hakanan." Aku
ya yi ta jansu da 'yan tade-tade, har ruwa ya goce. Suka zauna
suna jira a dauke.
Aku ya dube su, ya ce, "Da zaman banza bari in gaya maku
dan labari."
Musa ya dubi Barakai, ya ce, "Ai ko kin san gaskiyarsa, ya
fada mana dan gajere."
'Barakai ya сe, "Kуale shi, ba mu so. Kullum sai ka rika tsai da
shi a kan surutun wofi, kai ba hadisi ka ke masa ba, kai ba
labaran Annabawa ka ke gaya masa ba, balle a san kara shi ka ke
yi."
92
Aku ya ce, "Abin da ya sa ba na ba da labaran Annabawa,
tsoron jahilai na ke. Kun san yanzu akwai mutane da yawa
wadanda su ba malamai ba na sosai, amma da sun ji mutum ya yi
wata 'yar magana game da irin wadannan, sai ka ga suna neman
daukar kafarsa, wai ya yi sabo. Amma fa im ba don gudun haka
ba, labarin Annabawa, tun daga Annabi Adamu-tsira da aminci
su tabbata a gare shi-har zuwa ga Shugaban Ma'aika, akwai
wanda ban sani ba?"
Musa ya ce, "To, in haka ne fara gaya mana labarin Annabi
Sulaimanu, wanda aka ce ya mallaki mutane da aljannu har da
tsuntsaye."
Aku ya ce, "Wannan ai sananne ne har yanzu ba ka ji shi ba?"
Musa ya ce, "I, na ji cikin dukan mutanen duniya babu wanda
ya fi shi arziki."
Aku ya ce, "Ai wannan daga baya ne. Domin sa'ad da aka nufe
shi da annabci aka ce ya zabi dukan abin da ya kę so a ba shi. Shi
ko ya ce tun da ya ke an ba shi mulkin jama'ar Allah, shi ba abin
da ya fi so sai hikima, don ya san yadda zai rike su a kan adalci.
To, tun da ya zabi wannan bai zabi dukiya ba, ko tsawon rai, ko
girman duniya, Ubangiji ya ba shi hikima fiye da dukan sauran
mutanen zamaninsa, ya kuma kara masa har da abubuwan nan da
bai roka ba."
Musa ya ce, "Haba, tun da na ke ban taba samun wanda ya
bayyana mini asalin wannan al'amari ba, sai fa kai yau."
Aku ya ce, "Ko labarin yadda ya yi hukunci tsakanin wadansu
mata biyu ba ka taba ji ba?"
Musa ya ce, "Wallahi ban taba ji ba. Wane irin hukunci ya
yi?" Aku ya matso kusa da Musa, ya kishingida a bisa hannun
rigarsa, ya fara:
93
Labarin Annabi Sulaimanu
Wata rana Annabi Sulaimanu-tsira da aminci su tabbata gare
shi-yana zaune, sai wadansu mata su biyu suka zo suka kawo
kara a gabansa. Guda ta ce, "Ya Annabin Allah, da ni da wannan
mace gida daya mu ke zaune. Na haifi da. Ana nan, bayan na
haihu da kwana uku wannan mace kuma ta haihu. To, duk gidan
ba kowa sai mu biyu kadai. Ran nan cikin dare ta kwanta bisa
danta ba ta sani ba, har ya mutu. Sai ta tashi da tsakad daren, ta
dauki dana ta mayar wajenta, ta dauko danta mataccen ta kawo
gabana, ni ko duk ban sani ba. Sa'ad da na tashi da safe garin in
ba dana mama sai na gan shi matacce. Da na duba da kyau, sai na
ga ashe ba dana ba ne. Na gaya mata haka, ta ce karya na ke yi,
maiaccen ne dana. Muka yi ta gardama. Da muka ga abin zai kaї
ga barna, muka zo gare ka ka raba mana gardama, ya Shugaba."
Waccan kuma ta ce, "A'a, karya ta ke yi, ya Shugabammu. Ni
na riga ta haihuwa da kwana biyu, ran nan da dare ta taka nata ya
muťu, ta zo ta musanya shi da nawa."
Jama'ar da ke nan suka ce, "Kai, wannan shari'a ai ba ta warwaruwa, sai gobe ga Allah."
Da Annabi Sulaimanu ya ji maganar matan nan sai ya sa aka
dauko takobi aka zare, ya ce, "Tun da ya ke abin ya rikice haka,
abu daya kadai za a yi a raba gardaman nan. Zan raba dan nan
biyu ko wacenku ta dauki rabi, kowa ya huta, ku dangana har
Allah ya sake ba ku wadansu."
Da mace daya ta ji haka sai ta ce, "Don Allah kada a kashe shi.
A ba ta, na yarda mata." Amma waccan ta ce, "A'a, daidai ne,
ya Annabi. A dai raba shi, kowa ya huta."
Da Annabi Sulaimanu ya ji haka sai ya ce, "Ku mika dan nan
mai rai ga waccan da ta ce kada a kashe shi. Danta ne, ita ta haife
shi.""
Da Musa ya ji aku ya yi shiru sai ya ce, "A'a! Yaya aka san
wannan ke da da?"
Aku ya ce, "Haba, ba ka ga abin da a ke nufi ba? In da waccan
ta haife shi ta ce a kashe shi tana kallo kiri-kiri?" Bai'tsaya su
94
Musa su sami damar fadin wani abu ba, sai ya ce, "Kafin ku kare
tunanin wannan, tsaya ku ji yadda wani Sarki ya yi nasa
hukuncin."
95
Ba Wahalalle Sai Mai Kwadayi
Da aka yi wani Sarki mai son nishaďi. Ana nan wata rana
zuciyarsa ta yi baki kirin, har ya kasa barci. Ya kira yaronsa ya ce
masa, "Maza ka tafi wurin Waziri, ka ce ina kiransa." Yaro ya
tafi ya gaya wa Waziri, suka zo tare, suka shiga wurin Sarki.
Da suka shiga Sarki ya ce wa Waziri, "Yau zuciyata ta baci, har
barci ya gagare ni. Ina so mu tafi mu zaga rafi, ko zuciyata ta yi
sanyi."
Waziri ya ce, "To, shi ya fi, ranka ya dade." Da fad'in haka sai
yaron ya yi dariya.
Sarki ya ce, "A'a! Mene ne? Ni ka ke wa dariya ko Waziri?"
Ya ce, "Ranka ya dade, wane ni in yi maka dariya? Wani abu
ne ya fado mini a rai wanda na gani jiya, shi na ke dariya."
Sarki ya ce, "Wane irin abu ne?"
Yaro ya се, "Ranka ya dade, jiya ina yawo a bakin kogi sai na
iske wani mutum, mutane sun kewaye shi, yana ta ba su dariya."
Sarki ya ce, "Maza ka tafi ka kirawo shi, ya zo ya yi mini abin
da zai ba ni dariya, ko na samu zuciyata ta huce." Yaro ya tafi
wurin mutumin, ya ce, "Sarki yana nemanka."
Sai mutumin ya ce, "To, da kyau. Me ya sa Sarki ya ke
kirana?""
Yaron ya ce, "Yau Sarki yana bakin ciki, yana so ka zo ka ba
shi dariya, don zuciyarsa ta yi fari."
Sai mutumin ya ce, "Mu je."
Yaro ya ce, "To, sai mu yi sharadi, abin da Sarki ya ba ka duka
a kasa shi uku, kai ka kwashi kashi daya, ni in kwashi kashi biyu.
In ka yarda da haka zan kai ka, in ba ka yarda ba, yi zamanka, ni
kuwa in koma in ce ba:ı gan ka ba."
Sai ya ce, "To, shi ke nan, na yarda. Mu tafi." Yaro ya kai shi
wurin Sarki, ya fita.
Sarki ya ce wa mutumin, "Ina so ka yi mini abin da zai sa in yi
dariya. In na yi, in yi maka kyauta, in ban yi ba in yi maka
bulala."
Mutumin ya yi ta yin abubuwa masu ban dariya, da labaru iri
iri, har ya gaji. Sarki bai yi dariya ba.
96
Sarki ya ce, "Shi ke nan, ko akwai saura?"
Mutumin ya ce, "Shi ke nan."
Sarki ya ce, "Ga shi ban yi dariya ba. Kwanta in yi maka
bulala."
Mutumin ya matso, ya kwanta. Sarki ya tsala masa bulala da
karfi. Sai ya yi ta kururuwa, ya ce, "Tsaya, ranka ya dade! Na
karbi rabona, saura na yaronka. Domin mun sharada kome na
samu in dauki kashi daya, shi kuwa biyu."
Sarki ya kira yaronsa, ya ce, "Na ba wannan mutum rabonsa,
sauran naka, matso kusa ka karba."
Yaro ya matso kusa, yana tsammani zai sami kudi. Sarki ya
tsala masa bulala da iyakacin karfinsa. Yaro ya kwala ihu. Sarki
ya ce, "Tukuna, ai kashi daya kadai ka samu, saura daya."
Yaro ya ce, "Ranka ya dade, kashi dayan nan ma ya ishe ni, na
bar maka dayan."
Da Sarki ya ji haka sai ya fashe da dariya, bakin cikinsa ya
yaye. Ya kawo kyauta ya ba su, ya sallame su.
Kafin aku ya kare wannan
labari gari ya waye Barakai ya
koma yana cizon hannu, yana
neman hujjar da zai fada wa
ubangidansa.
Da zuwansa Waziri ya harare
shi, ya ce, "Ban ji an gama aikin
ba. Ina dalili?"
Barakai ya ce, "Ruwa!"
Waziri ya ce, "Ruwa? Wane iri? Ruwa da aka yi aka dauke tun
kafin a yi kiran sallar fari?""
Barakai ya ce, "Watakila nan wajen gidanka aka dauke da
wuri, wajen fada har rana ta fito ana ruwa."
Waziri ya cika, ya kawo iya wuya, ya zabura ya danne shi ya
shake, ya ce, "Fada mini gaskiya, in ba haka ba ko yanzu in kashe
ka, mutumin banza, munafuki! Lalle kai ne ka tona asirin da
muka kulla da Sarkin Sinari. Da ma ina shakkar haka."
Da Barakai ya ji haka sai jikinsa ya dauki rawa, ya ce, "Na
tuba Allah ya ba ka nasara, gaskiya zan gaya maka yanzu. Akun
nan sihiri gare shi, in ya fara ba da labari, sai duk hankalin
mutum ya rude, ya rasa abin da ya je yi. Muddin akun nan na
numfashi ba yadda za a yi a fid da Musa daga gidan nan, ko kai
ka je da kanka."
Waziri ya ce, "Rufa mana baki nan da karyar banza!" Ya
dauki bulala ya tsala masa har ya gudu.
Waziri ya koma ya zauna, yana ciccika shi kadai, yana cewa,
97
"Ina Wazirin kasan nan duk tsawonta da fadinta, ga shi dan abu
kadan ya rage da zan yi in zama Sarki, dan tsuntsu ya ce zai hana!
To, bar ni da shi."
Sai ya aika wajen Musa ya ce yana son aku ya zo yau ya debe
masa kewa da labaru. Ya ba da igiya, ya ce in Musa ya yarda a
dauro shi a zo da shi. Da aka gaya wa Musa, bai san abin da a ke
nufi ba ya ce shi ya yarda, zai tambayi akun kuma ya ji in ya
yarda. Ya tafi ya tambayi aku, aku ya ce, "Yallabai, tun da ka ce
in tafi, ai sai in tafi." Yaron da aka aiko ya jawo igiya zai daure
aku ya kai shi. Aku ya ce, "Mene ne na dauri? Ban saci kayan
kowa ba. Ba cewa aka yi ana sona don nishadi ba? Wuce, in hau
bisa kanka mu tafi." Suka tafi har gidan Waziri, suka tarad da
shi a kofar gida. Aku ya sauka, ya tsaya nesa kadan. Waziri ya
sallami mutane. Da shi niyyarsa, yana da wata katuwar sanda a
boye ya kashe aku, kowa ya huta. Da aku ya lura da sandan sunne
cikin rigar Waziri, sai ya kara ja da baya.
Waziri ya ce, "Matso mana."
Aku ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ina ni ina zuwa kusa da
kai?"
Waziri ya ce, "Ina so ka ba ni labari, kowane iri ka ke iyawa, in
na ji da dadi in yi maka kyauta."
Aku ya ce, "To, sai ka zauna in fara." Waziri ya zauna, aku ya
fara:
98
Saurin Fushi Shi Ke Kawo Da Na Sani
Wata rana Sarki yana kilisa, sai ya tarad da wani dan kwikwiyo
yana kwance, duk kiyashi sun cika bakinsa nishi ya ke yi dai dai,
zai mutu don yunwa, Ga shi ya faye kankanta, har ba ya iya ci da
kansa. Ko yaya aka yi ya rabu da uwarsa, Allah kadai ya sani.
Da Sarki ya dube shi sai tausayi ya kama shi, ya ja linzami ya
tsaya, ya dubi mutanen da ke biye da shi, ya ce, "A kakkabe wa
dan kwikwiyon nan kiyashi a dauke shi a kai mini gida. A ba
Sarkin Babanni ya lura da shi da kyau yana ba shi abinci, in yana
da sauran kwana gaba ya tashi."
Nan da nan, kafin Sarki ya rufe baki, bayi sun dira sun kama
karen, sun shafe masa baki da hannayen rigunansu. Wani ya sa
shi kan kwacciya, ya tafi da shi gida ya kai wa Sarkin Babanni, ya
gaya masa abin da Sarki ya ce. Ya saki hammadanci ya tarad da
Sarki. Da rana ta yi sanyi suka komo.
Bayan kamar kwana uku sai dan kare ya farfade, har ya fara
tafiya, Da ya sami kamar wata biyu sai ya zama kamar ba shi ba.
Ya yi bulbul, duk inda Sarki za shi yana biye. Da ya girma sai
kullum dare in Sarki ya shiga barci, shi kuwa sai ya zo kofar
turakar ya kwanta. Ba mai ikon gifta wurin sai gari ya waye.
Saboda haka Sarki ya rika sonsa kwarai da gaske. Ba mai ikon ya
buge shi, ko ya yi masa wata katuwar tsawa, don tsoron Sarki.
Ana nan, ran nan safiyar Salla Sarki ya yi shiri zai fito ya hau
zuwa idi, sai karen nan ya biyo. Sarki ya waiwaya ya gan shi, ya
buga masa tsawa, ya koma daki ya kwanta, don ya san haka a kan
yi masa in ba a son ya bi.
Yana nan kwance dakin Sarki, can an kusa saukowa daga idi,
sai aka kare toye-toyen Salla. Wata sadaka ta fara dauko kwano
guda ta kawo cikin dakin nan ta ajiye. Amma maimakon ta rufe
abincin yadda ya kamata sai ta bar shi a bude, don ta san ko da
zai rube karen nan ba shi tabawa.
Karen nan yana kwance, sai ya ga wani kumurci ya biyo
matakin soro, ya sauko daga kan azara, ya sa baki cikin abincin
yana ci. Kare ya fita waje yana haushi don mutane su zo. Ba
99
wanda ya kula da shi. Da mata suka ji ya dame su da haushi, sai
suka dauki dutse suna jifarsa, don sun ga Sarki ba ya nan. Da
karen nan ya ga ba su gane abin da ya ke nufi ba, sai ya kyale ya
shiga daki ya kwanta. Maciji kuma da ya ga ya koshi, sai ya sulale
ya koma cikin azara abinsa ya shige.
Can an jima Sarki ya dawo. Da shigowarsa iyali suka yi masa
barka da sauka. Bayan sun tashi, ya nufi wajen abincin nan zai ci.
Kare ya bi shi yana kada wutsiya kamar ya ce, "Kada ka ci,
maciji ya zuba dafi a ciki." Allah bai ba shi ikon magana ba.
Sarki ya wanke hannu ya sa cikin abinci,ya yanko. Kare kuwa
sai ya kai nan ya kai nan, Sarki na tsammanin son abinci ya ke yi.
Ya jefa masa ya ki ci, sai haushi ya ke yi wa Sarki.
Sarki ya bude baki zai sa wannan lomar sa'an nan ya dauki
sanda ya kore shi, sai karen ya yi farat ya buge hannun Sarki,
loma ta fadi kasa. Sarki ya dunkula hannu ya shiga dimar kare,
amma kare sai gurnani ya ke, bai kula ba. Ya sa baki ya cinye
loman nan da ta fadi daga hannun Sarki, ya kuma hau wa sauran
abincin duk ya cinye sarai. Tun Sarki na dukansa, har haushi ya
kama shi, ya gaji ya bari. Ya tsaya kuru ya ga ikon Allah.
Ko da kare ya cinye abincin nan, sai ya koma gefe guda ya
kwanta. Kafin Sarki ya kare ciccika, kare ya ınimmike nan ya
mutu.
Ganin wannan abu fa ya kara ta da hankalin Sarki, ya се,
"Lalle akwai wani abu game da abincin nan. Watakila sadakar da
ta kawo ta yi mini sammu ne in ci in mutu."
Sai Sarki ya fito ya kira ta, ya tambaye ta, ta rarise da abin da
zai kashe ta ba ta sa kome ba ciki. Ya tanta mba:ta ko ta bari
100
gaban sauran kishiyoyin, ta ce a'a, da karewa sai ta zuba cikin
wannan kwano ta kawo.
Sarki ya ce, "To, da kika fita ba wadda ta shigo bayanki?"
Sadaka ta ce, "Mts, bayana ba wadda ta shigo. Ba na daukan
alhakin wani, ni kadai na dawo na bude, don ya sha iska da na ji
kuna tafe."
Sarki ya yi shiru, ya ce, "Lalle karya ku ke yi. Munafincinku na
mata wane ne bai san shi ba? Ba shakka ki gaya mini abin da kuka
zuba, in ba haka ba kuwa in sa a yanka ki."
Sadaka ta fadi tana ahi, tana rantse-rantse tana cewa ba ta sa
kome ba ciki. Ya dube ta, ya ce, "Ke ar, munafuka!" Ya aika a
kira bayi su zo su yanka ta. Nan da nan suka shigo, aka cafe ta
tana kuka, aka yi waje da ita.
Sarki ya yi zugun cikin daki, yana mamakin abin da ya yi wa
sadakan nan har da ta ke so ta kashe shi, ya rasa. Can sai ya ji
dakin ya gume da wani wari kamar na gwano. Ya tashi ya duba
inda ya ke zaune, bai ga gwano ba. Yana kakkabe rigarsa ko ya
shiga ciki, sai ya ji ka-ka-ka-ka-ka a bisa rufin daki. Ko da ya
daga kansa sai ya ga wani katon kumurci a cikin azara. Da ya gan
shi sai ya san lalle barin abincin nan da ta yi a bude ne, macijin
nan ya zo ya ci. Saboda haka ya tashi da sauri,ya tafi inda bayin
nan za su yanka sadakar. Ya tarda su har sun kayad da ita, sun
dandanne za su yanka, sai kuka ta ke tana salati. Sai ya ce, “Kai,
ku tsaya, ku tsaya!"
Bayi suka tsaya suna kaduwa, suna tsammani Sarki ya raina
saurinsu ne. Sarki ya ce a sake ta. Ya kira bayin, ya tafi da su
turakarsa, ya nuna musu kumurcin. Ya gaya musu kuma da abin
da zai sa a yanka sadakan nan. Ya sa bayi nan da nan aka fyado
kumurcin kasa, aka fid da shi waje aka yar.
Sarki ya tara dukan iyalinsa, ya gaya musu wannan al'amari,
ya kuma gargade su kada su sake barin abinci a bude. Nan
gabansu kuma ya gafarta wa sadakan nan, suka koma
sha'aninsu.
Ya sa aka fita da karen nan zaure, ya gaya wa fadawa da
Sarakunansa abin da ya auku cikin gida duka. Ya sa aka gina dan
daki a kofar gidansa, aka yi wa karen nan kabari a ciki aka sa shi.
Ya yi bakin ciki kwarai saboda mutuwar karen nan. Ya kuma
gargadi mutanensa da abu biyu. Na daya, ya ce kada su rika
saurin fushi, kowane al'amari ya auku, kafin su zartad da
hukunci su tsaya sai sun bi cikin al'amarin. Ya ce domin da bayin
nan sun yi saurin cika umurnin da ya bayar a yanka sadakan nan
da ya yi da na sani daga baya. Na biyu, ya ce su kyautata tausayi
da jin kai ga dabbobi da tsuntsaye, ko da ba su da dabara
101
kamarmu, ba a san inda rana za ta fadi ba. Kowa ku ka gani a
duniya, yana da ranarsa. Ko ba don wannan ma ba, ai an ce
aikata alheri ga kowa, sakayyarka tana wurin Allah.
Da Waziri ya ji haka sai ya ce a ransa, "A'a! Me ya ke nufi da
wannan labari? Dan tsuntsun nan fa rigima gare shi! Yana
tsammani ni yaro ne, balle ya ce ya yi mini wa'azi?" Sai ya hadiye
fushinsa, ya yi murushi, ya ce, "Wannan labari naka iyaka ne.
Bari in yi maka kyauta." Sai ya zaro wani zobe na zinariya ya rike
a hannun hagu, ya nufo aku wai zai ba shi, hannunsa na dama ko
na cikin riga. Aku ya rika tsalle yana ja da baya, Waziri na binsa
yana cewa, "Tsaya mana ka karba!"
Aku na ja da baya dai yana cewa, "Ai sadaka na yi maka
labarin, ba don ka biya ba."
Da Waziri ya lura aku ya gane shi, sai ya zabura gaba daya ya
kai masa bugu, aku ya goce, buje ya tadiye Waziri ya fadi, ya
daushe baki har hakorinsa guda ya fita. Ya tashi ja wur cikin jini,
nan da nan baki ya haye.
Da aku ya ga haka sai ya haye cediyar kofar gidan, ya kaikaici
idon Waziri ya yi ta dariya. Da ya ga Waziri ya dubo, sai ya
kanne, ya ce "Sannu bawan Allah! Ba ka sani ba, Waziri, ni kuwa
ban ji zafin ba. Da ka taba jin labarin yautai da wani mai keke, da
ba ka kulla wannan niyya ba game da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12