Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 12
kula da ko jakin da ya ke ja ba. Daga nan sai wani daga cikinsu ya ce, "Yanzu fa ba ku sani ba, karbe wa muzin nan jakinsa bai sayi wuri ba, in ina so." Saura suka ce, "In ba kurarinka ba yanzu, yaya za ka yi? А buge dai ba ka iya buge shi ka karba, yanzu ko ba dare ba, balle ka ce ka sace." Sai dan birnin nan ya tashi ya bi bayan bakauye, saura na biye da shi sululu. Ya matsa, ya kwance igiyar da ke wuyan jaki ya daura wuyansa, ya mika wa 'yan'uwansa jakin, suka koro. Gagon naka tun da dai ya ke jin tsauri-tsauri a hannunsa, sai ya yi ta tafiya baki bude, yana kallon dan hoto. 32 Can da dan birnin nan ya ga 'yan'uwansa sun bace da jaki, sai ya ja ya cirje. Bakauye ya ja ya ja, yana has has has! Amma bai waiwaiya ba, yana jin kada ya dauke kansa dan hoto ya yi wani abin mamakin da bai gani ba. Da ya ja dai ya ji jakin bai biyo ba, sai ya waiwaya don ya buge shi su tafi. Dubawan nan da ya yi sai ya ga mutum maimakon jakinsa. Abin ya ba shi mamaki, ya ce, "Kai, me ya faru haka?" Dan birni ya ce, "Ni ne jakinka, tsaya ka ji labarina, domin abin na da ban mamaki. Tun asali ni da ma ba jaki ba ne, mutum ne dan'uwanka. Ina zaune da tsohuwata, sai ran nan kuruciya ta debe ni, na sha giya. Sai na zo gida, ba ta san abin da ya faru ba. Ta yi mini 'yar magana kadan, ba ma ta tashin hankali ba. Ka san wańda ya yi sha bai san inda kansa ya ke ba, sai na zage ta. Ta dafe kai ta dube ni, ta ce, 'Ni ka ke zagi? Ashe har Allah ya kawo mu lokacin da 'ya'ya ke zagin iyaye?' Ka san mai maye sai na ce, 'Na zage ki! Ke wace ce da ba za a zage ki ba?' Sai ta sa hannu kai, ta yi ta kuka, ta roki Allah ya mai da ni jaki. Tun ran nan na ke jaki har Allah ya sa na zo hannunka. Yau ina ga ta gafarta mini ne, ka ga na koma mutum." Bakauye ko da jin haka sai tausayi ya kama shi, ya kura masa ido, ya ce, "Don Allah ka rika bin maganar iyayenka, kada ka yarda kuruciya ta debe ka, ka yi kyalkyalin tsada. Ga ka kyakkyawan saurayi, amma zuciyarka ta munana." Dam birni ya yi sako, yana jin wa'azi, kamar wani mummuni. Da bakauye ya kare ba shi wa'azi ya ce, "To, na ko bi wa'azin nan da ka yi mini." Ya faki idon bakauye, ya yi masa gwalo. Bakauye ya kwance masa igiya ya tafi, ya nufi wajen 33 'yan'uwansa. Suka kai jaki wani gida suka daure, kafin ranar kasuwa su kama shi su kai su sayar. Bakauye ko daga nan bai isa kasuwa ba, sai ya koma gida ya gaya wa matarsa duk abin nan da ya faru. Suka yi ta jin tausayin dam birni, domin wulakantad da shi da suka yi suna tsammani jaki ne, ba dan Adam ba ne. Ran nan bayan kamar kwana uku, ranar kasuwa 'yam birnin nan suka kai jaki su sayar, su sami abin zaman gari. Sai aka yi muwafaka bakauyen nan kuma ya tafi neman jaka. Da ma don ya sami mace shi ya sa ya so ya sayad da nasa namijin. Ko da ya isa ya duba haka sai ga jakinsa na da, sai ya matsa kusa da shi, ya dube shi, ya yi tsaki mts, ya ce, "Allah wadanka! Duk wa'azin nan da na yi maka ba ka lura ba? Mai hali ba ya barin halinsa. Haka ku ke shaye-shayenku, kuna sa mutane asara a wofi. Dubi duk wahalar da ka sha wajena, buga wannan kasuwa, dauki itace kai wannan kasuwa, duk ba ka daddara ba, sai da ka sake yin sha. Ni dai na gane ka. Sai ku yi can da wanda tsautsayi ke bibiya, mu dai muna tudun mun tsira." Ya hauri jaki ya wuce. Dan Sarki ya ce, "Ai ko wannan lalle ya isa bakauye!" Aku ya ce, "Ina ka san ya isa muzi tukun? Ai da sauran labari." Da ya duba bai samu wani jakin saye ba, sai ya komo gida yana kunne da dam birnin nan. Can zuwa maraice, 'yam birnin nan suka karyar da jaki, suka karbi awalaja. Da wata kasuwa ta kewayo, sai bakauye ya samo kuďinsa ya komo kasuwa neman jaka. Yana zuwa kusa da kofar gidan mai gari, sai ga fam birnin nan da ya ce shi ne ya rikide jaki, bakauye ya saya. Ya yi sitati za shi kasuwa, kayan nan sun dauki zargina tsar. Ko da bakauye ya gan shi sai ya gane shi, haushi kuwa ya kama shi, ya ce a ransa, "Kai, ba na dai yarda in yi asara a wofi don lalataccen nan!" Sai ya dubi dam birni, ya ce, "Ashe ka koma mutum kuma?" Dam birni ya yi biris da shi. Sai bakauye ya tasam masa ya kama shi, ya sa masa akumari, ya ce wai zai hau ya tafi da shi ya yi kwarami. Dam birni da yana tsammani da wasa ya ke, sai ya ga ya yi wuf ya haye kafadarsa. Ga shi ya fi dam birnin karfi, ya kuma fi shi iya kokawa, ya yi ya yi ya ka da shi, ya kasa. Mutane suka cika wuri su ga.ikon Allah. Bakauye ko bai kula da su ba, sai df1, dl, d'l, ya ke yi, yana has! kur! wai shi ya hau jaki, yana ta ba shi dudduge a ciki, yana duka. 34 Da dam birni ya ji ba dama, sai ya kwanta. Bakauye ya haye cikinsa yana duka, wai ya tashi su tafi, yana cewa, "Ai fa ko a janye sai na kai ka gida, ka daukam mini taki, ba na yarda in yi asara. Ka sha ka zagi uwarka, ta mai da kai jaki, na saya ban sani ba, ta koma ta gafarta maka ka koma mutum, na dauki asara, na sake ka. Ranar Talata kuma, da na zo cin kasuwa, na tarar ka sake yin wani abu ta mai da kai kuma jaki, wani ya saya. Ga shi yau kuma ina ga ta gafarta maka, ka koma mutum. Ka sa kuma wancan mutumin da ya saye ka ya yi asara kamata." Ya dubi mutanen da ke kewaye, ya ce, "Don Allah, jama'a, gaskiya fa kun ga wannan na yiwuwa? Kura da shan bugu, gardi da karbe kaya? Ai ka san ba abin da zai hana ni yin kwarami da shi, ko kuwa ya fanshi kansa:" Sai ya sake hau masa da bugu, wai ya tashi su tafi dai kauyensu. Suna cikin haka sai ga wani Dogari, ya kwashe su ya kai ga Alkali. Alkali ya tambayi bakauye yadda aka yi, duk ya kwashe ya fadi, bai rage kome ba. Da mutane suka ji haka, suka ce me za su yi ba dariya ba? Alkali ya tambayi dam birni in hakanan ne. Dam birni ya ce faufau shi bai ko taba ganin bakauyen ba, sai yau. Alkali da ma ya san halin irin mutanen nasa sa aika. Sai ya sa Dogarai su tambaye shi sai ya faďi gaskiya. Da masu fushi da fushin wani suka same shi, ya ji zafi, sai ya ce, "Wayyo Allah, ku tsaya, ku tsaya!" Suka dakata. Ya kwashe maganar bakauye, ya ce duk hakanan ne, mutane suka yi ta al'ajibi. Alkali ya sa ya biya bakauye kuďin jakinsa sule goma sha daya da taro, yadda bakauye ya ce ya saya. Ka san abu hannun barawo, shi fa dam birnin nan sule shida da sisi ya sayar da shi wannan kasuwar da ta wuce. Alkali ya sa aka daure dan birni. Bakauye ko aka ba shi kudinsa, ya tafi. Bakauye dai bakauye ne. Duk abin nan gogan naka har ya tafi bai san wayo ba dam birnin nan ya yi masa ya sace jakinsa. Shi har yanzu tsammani ya ke dai rikida ya yi. Musa ya yunkura zai fita, sai ya ji magana a babban zaure, wadansu daga cikin bayin sauro ya dame su, sun kasa barci. Suka farka suka yi ta taďi har gari ya waye. Musa ya koma gida yana jin haushi. Da shigarsa gida ka san ba abin da ke cikin idonsa sai barci, don duk cikin 'yan kwanakin nan bai runtsa ba. Ko da ya kwanta bai farka ba sai can zuwa la'asar, ya tashi ya yi salla, yana nan har 35 magariba ta yi, aka ci abinci. Bayi suka duka hira. Da Musa ya ji bayi sun yi barci, ya tashi ya shigo damaru, ya ce wa aku, "Don Allah yau kada ka tsai da ni, sallame ni in tafi. Kai, Allah ya kiyashe mu! Ban taba ganin tsuntsu mai surutunka ba." Aku ya tuma nan ya tuma nan, ya ce, "Ba kai kadai ba, Allah ya ba ka nasara, kowa na ganin surutummu, amma in kun lura da mu ba mu surutu a banza. Ko dai mu ba da gargadi, ko kuwa don rashin munafuncimmu mu bayyana asirin da muka gani ana kullawa za a cuci jama'ar Annabi. Don haka yanzu duk inda muka fi rashin fada shi ne wurin mata. Tsaya ma ka ji yadda wani aku ya yi da wata mace, don ka san dai al'amarimmu muna yi don Allah ne, ba don mutane su yaba ba." 36 Labarin Wani Aku Da Matar Ubangidansa Wata rana wani tajiri za shi fatauci, sai ya bar matarsa a gida. Yana kuma da wani aku. Suna nan tare, sai matar ta rika fita yawo, don ta ga mijin ba ya nan. Barorin gida da suka ga abin ya dame su, ba su da damar su yi magana, kada matan nan ta sare su wajen mai gidan in ya komo. Saboda haka suka zura mata ido. Ana nan ran nan sai mai gida ya dawo. Ka san al'amarin duniya ba shi boyuwa, sai wani ya tsegunta masa abin da matarsa ta yi ta aikatawa bayan ba shi nan. Da mai gidan nan ya ji haka, sai ya kira matar, ya same ta ya yi ta zagi. Ya dauki sanda kuma ya ba ta kashi. Da matan nan ta ga haka sai ta yi yaji, aka komo da ita. Ta ce a ranta, "Ba wanda ya fadi abin nan sai aku." Ka san mu, Allah ya ba ka nasara, bakin jini gare mu kwarai, tun ba game da mata ba. Suna cewa mun faye tsegumi. Saboda haka, ta bari mai gida ya tafi kasuwa, sai ta kama aku, ta fige shi da rai, ta wurga shi waje ta taga, ta ce, "Daga gare ni ka bar tsegumi!" Allah ya sa aku bai mutu ba, ya tsallaka har ya kai wani hurumi ya sami kabari ya shige, ya yi ta jiyya. Da mai gidan nan ko ya dawo, sai matar ta ce wai bayan fitarsa kadan kyanwa ta cinye aku. Ko da ya ji haka sai ya san karya ta ke yi, kashe shi ta yi, don tana tsammani shi ya gaya masa tana fita da ba shi nan. Saboda haka ya fusata kwarai da gaske, .ya same ta da duka kamar ba zai bar ta da rai ba. Ya kore ta daga gidan, ta tafi wajen hurumin nan tana kuka. Ashe aku na nan kusa da ita cikin wani kabari, yana ji. Sai ya ce mata. "Yi shiru, bari kuka, in Allah ya so kya koma dakinki. Amma akwai sharadi guda, sai ki je ki aske kanki sarai, sa'an nan ki dawo nan, gobe zan taimake ki ki koma." Matan nan ta duba, ba ta ga kowa ba. Abinka da mace, sai ta yi tsammanin, wani matacce ne ke yi mata magana. Nan da nan ta tafi gidan iyayenta, ta sa aka aske mata kai kwal. Da gari ya waye, maraice ya yi ta nuho wajen hurumi, kai na kalli sai ka ce na namiji. 37 Da isowarta sai ta tafi wajen kabarin. Abinka da jahila, ta durkusa, ta ce, "Na asko." Sai aku ya ce, "To, kin san dalilin da ya sa na ce ki aske kanki, domin kin zalunci wani dan tsuntsu, kika targe shi a kan abin da bai ji ba bai gani ba, har kika fige shi da ransa, kika wurgo shi bayan gida. A wannan na yi miki sauki, na ce ki aske gashin kanki kawai, amma in kin kuskura kika sake yi wa wani tsuntsu haka, ki kuka da kanki. Amma akun nan da kika kashe zai komo duniya, yadda zan mai da ke dakinki, shi kuma zan mai da shi gare ki. To, ki lura da shi da kyau, ki sa mijinki ya ajiye yaro guda mai hankali wanda zai rika lura da shi, a rika ba shi ruwa da sukari. Kuma ki tsawata wa yara su bar kiransa aku kuturu." Matan nan ta kara dukawa, ta ce, "Na ji." Da za ta tashi sai aku ya ce, "Da saura. Yau kin ga sha biyu ga watan Safar. To, ko wace shekara sha biyu ga watan Safar ki aske kanki, don ya rika tuna miki aku dai da ki ke ganinsa banzabanza ba banza ba ne. Amanar Allah ce ya sa a hannunku 'yan Adam, ya fi kyau kuwa ku lura da ita da kyau. Watan duk da ya zo ba ki aske kanki ba, yadda na gaya miki yanzu, ki tabbata ba ki shekara. Shi ke nan, gobe kya koma in sha Allahu. Tafi gida abinki. Amma ki kiyaye gargadin nan da na yi miki, ki kuwa yi kirki, ki bi mijinki sau da hannu. Allah ya gama mu da alheri & Darassalamu!" Mace ta koma gidansu. Aku ya tashi yana tsalle, har ya kai gidan tajirin nan, ya ce masa, "Ka san ni?" Tajirin ya dubi aku ba gashi, ya ce, "Yaya zan yi in san ka, ban taba ganinka ba?" Aku ya ce, "Ba ka taba ganina ba? Ai ni ne akunka wanda kyanwa ta cinye." Tajiri ya ce, "Tun da kyanwa ta cinye ka, yaya kuma aka fara har ka yi rai? Da ma dai ba kyanwa ta ci ka ba akwai yadda aka yi." Aku ya ce, "Daga cikin kyanwar aka nufa in fito, don in shaida maka duk abin da matarka ta fadi na batun kyanwa ta cinye ni gaskiya ne. Kada ka zarge ta. Amma in kana sona, zan kara dakatawa kuma wurinka, in yi gashi in koma kamar da, har Allah ya kari kwanana gaba daya. Amma sai ka mai da matarka, ka yafe mata, ku yi zaman lafiya." Mai gida ya ce, "To." Ya aika matar ta dawo, ya gafarta mata, suka sake zamansu. Daga ran nan ta zama mazar kirki, duk gari ba wadda a ke so sai ita a kan kirki. Musa ya tashi zai fita, aku ya dube shi, a ce, "Wallahi, yallabai, ba ka ga yadda ka rame ba. Maza ka ta i kada zulumi ya 38 halaka mana kai a banza, yadda ya tashi halaka Sarkin Zairana." Musa ya waigo, ya ce, "Ina ne Zairana kuma? Zulumin mene ne haka ya sami Sarkin, har ya tashi halaka?" Aku ya ce, "Yallabai, me ka mai da zulumi ne?" 39 Labarin Sarkin Zairana Da Sarkin Bokaye Gara Akwai wani Sarki a Zairana wanda Allah ya nufa da kiba, abin har ba iyaka. Idan ka gan shi sai ka ce giwa, in ya zauna ba yadda zai yi ya ga cibiyarsa, dokin duniyan nan duk ba mai iya daukarsa. In ya tashi daga zauren gidansa zai shiga, mutum ya yi tafiyar loko biyu Sarkin nan bai isa ba. Sarki fa duk abin duniya ya dame shi bisa ga wannan kiba, shi kuwa ba abin ya ki cin abinci ba ya mutu. Saboda haka ya tara bokayen kasarsa, ya ce su yi kokari su samam masa maganin da zai sha ya rage kiba. Bokayen suka shiga aikinsu. Kowa sai ya sassako wannan itace, ya gino wannan sauya, ya kai wa Sarki. Ya yi ta sha, amma a banza. Maimakon ya ragu sai karuwa ya ke kullum safe, sai ka ce ma maganin ya kara kiba su ke ba shi. Da Sarki ya ga haka sai ransa ya kara baci, ya yi kamar ya kashe kansa don haushi. Ga duniya Allah ya ba shi, kiba ta hana shi jin dadin cinta. Yana nan haka sai ya ji labarin wani boka wanda a ke kira Gara Mai Aburkuma. Sarki ya aika aka kira shi, ya bayyana masa bakin cikinsa. Ya ce in ya warkad da shi kuwa zai yi masa kyauta har ya kasa godiya. Gara ya се, "Tо, Allah ya taimake mu. Amma in ka yarda,. ranka ya dade, ina so a ba ni kwana uku in je in shawarci Aburkuma, Inna uwa ma ba da mama, abin da muka yi da ita duka zan zo in gaya maka." Sarki ya ce, "To, je ka, na ba ka iznin kwana uku, amma kada ka wuce haka." Gara ya yi ban kwana, ya tafi. Ya yi ta tunanin inda zai fito wa Sarki ya yaudare shi. Ya san dai, in ba wautar Sarki ba, wane boka ne zai iya ta da hukuncin Allah? Bayan kwana uku sai Gara ya komo wajen Sarki, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, na dawo." Sarki ya ce, "To, ina labari?" Gara ya ce, "Allah ya daukake ka, ai sai a bar kaza cikin gashinta, al'amarin ya tayar mini da hankali."" 40 Sarki ya ce, "Me ka gani, na ce. Fada mini mana in ji." Gara ya ce, "Allah ya ja zamaninka, ai ba na iya fadin abin da Inna ta gaya mini. Saboda bakin cikin al'amarin, jiya, na rantse har da rawaninka, ban yi barci ba. Abin da na gani ya fi sai a bar wata wahalar neman magani, a tasam ma istingifari." Sarki ya fusata, ya ce, "Yau ga zancen banza. Na ce ka gaya mini abin da ka gani, ka tsaya kana kewaye-kewaye." Gara ya ce, "Allah ya yi wa Sarki rahama, Inna ta ce saura kwana arba'in ka riga mu gidan gaskiya." Sarki ya fusata, ya ce a kama shi a daure. Dogarawa suka cafe shi. Gara ya ce, "Da ma abin da na ke gudu ke nan da gaya maka gaskiya." Aka dai iza keyarsa zuwa gidan kurkuku. Sarki ya shiga zulumin abin nan da Gara ya fadi, ya ce, "Na san Gara fa shahararre ne bisa ga al'amari da aljannu. Ba abin da ya fi dai sai a rika kidaya kwanakina da ya fadi. In sun cika arba'in na ga ban mutu ba, na san Gara karya ya ke yi. In kuwa na ga bayan kwana talatin da takwas, ko talatin da tara, na fara 'yar mashasshara na san ni tawa ta kare."" Wannan zulumin da ke ran Sarki fa ya sa ya tsunke. Ko abinci ba ya iya cin abin kirki, balle ma ya faranta ransa da wadansu kawace-kawacen duniya. Saboda haka kullum sai ramewa ya ke don zulumi. Duk mutane suka rasa kansa suka rasa gindinsa. Bayan kwana talatin da wannan magana sai tashin hankalin nan ya yi masa yawa, har ya sa kansa ya rika ciwo. Rana ta talatin da tara da ya ji ciwon kan na karuwa, sai ya kira dansa ya danka masa mabuďin taskoki, ya yi ta yi masa wasiya, yana gargadinsa yana cewa su tasu ta kare. Yaro bai san abin da ya ke nufi ba, tsammani ya ke don ya fara tsufa ne ya ke so ya nuna masa al'amuran mulki. Ana nan dai kwana arba'in suka cika, Sarki na jiran mutuwa, bai ga ya mutu ba. Kwanaki dai suka kai kwana arba'in da biyar, Sarki bai ga ya mutu ba. Sai ya áika aka zo da Gara daga gidan sarka, ya се, "Ка сеe bayan kwana arba'in zan mutu, ga shi yau kwana arba'in da biyar da maganar, ban mutu ba." Gara ya ce, "Da ma maganin ka rage kiba ka tambaye ni, to, karyan nan da na yi na ce'saura kwana arba'in ka mutu ita ce maganin. Ka tambayi kowa nan garin ka ji in ba ka rage kiba ba."" Da Sarki ya ji haka, sai hankalinsa ya kwanta, ya bushe da dariya, mutane suka yi kyakkewa baki daya, suka ce, "Lalle Gara ya isa dan duniya." Gara ya ce wa Sarki, "Ba abin dariya ba ne, sai ka ba ni abin da ka alkawarta." 41 Sarki ya sa aka yi ta kawo masa riguna da zannuwa da wanduna, ya kuma ce duk mai kaunarsa ya yi wa Gara kyauta. Mutane suka yi ta zuba masa kudi, tun yana godiya har ya fashe da kuka don murna. Sarki ya sallame shi, ya kwashe kayan da aka ba shi duk, ya tafi. Kullum in an ta da labari, sai Sarki ya yi ta yi wa kansa dariya in ya tuna abin da ya yi daren da kwanan nan arba'in za su cika, da ya yi ta yawo tsakar gida shi kadai, ya kai gwauro ya kai mari, yana ta salati ga Fiyayyen talikai. Aku na kare wannan labari, sai Musa ya ji zakara na ta cara, gari ya waye. Ya rasa abin da zai ce wa aku ya huce, sai ya shiga gida, ya yini ran nan bai ce wa kowa kome ba. Magariba na yi, sai ga 'yar tsohuwan nan ta dawo, Waziri ya aiko ta da takarda wai daga Mahmudu, ta kawo wa Musa. Musa ya karba ya karanta, ya cе, "Allah wadan dan abin nan da ke hana ni fita." Tsohuwa ta ce, "Yanzu haka, yallabai, duk karkaran nan da mace da namiji ba ka jin wani abu sai Mahmudu. 'Yam mata ma yanzu ba su da wata waka sai ta Mahmudu." Musa ya ce, "Har waka 'yam mata suka yi masa? Don Allah, in kin iya, rera mu ji." 'Yar tsohuwa ta karkace kai, don iya kissa ta fara wakan nan, ba da ko ta taba jinta ba: Jama'a ku zo ga kallon Mahmudu, Wanda ya wuce wargi. Ya fi karfin sai gobe, Ya wuce mai wargi. Shi ne ya kori Sinarawa, Har ya kashe musu Sarki. Ya fi karfin sai gobeе, Ya wuce mai wargi. Mahmudu wa ga Musa, mazaje, Da sunka kawo karfi. Ya ki wargi dattijo, Ba ya son mai wargi. Zaman gida na raggo, Sai dan da ke gudun mai karfi. Dan Sarkin da ke cikin mata, 42 Shi da su ana nan daidai. Ya fi wargi, Mahmudu, Ba ya son mai wargi. Da Musa ya ji wannan waka sai idandunansa suka jujjuye. Tsohuwa ta tashi, ta tafi wurin Waziri ta gaya masa. Waziri ya yi mata kyauta. Da asubahin farko, Musa ya yi damara, ya dauki wata babarbara, ya tafi wajen aku, ya ce, "Zan tafi, ko ka yardá, k ba ka yarda ba." Aku ya duka, ya ce, "Yallabai, ina da ikon hana ka? In dai ka fita, ka sami dan kwabo ka yi sadaka. Allah ya ba da sa'a!" Musa ya ce, "To." Ya juya zai fita, aku ya ce, "Af, yallabai, ko za ka dakata kadan in fita ta taga in samo maka wani maganin karfe da na gada daga kakana? Ka san fa mazaje ba a tasam musu ba shiri." Musa ya ce, "Gaskiyarka. Yi maza ka debo, amma kada ka tsaya." Aku ya fita ta taga, ya sami wata itaciya ya haye, ya yi zamansa. Can da ya ga asalatu ta kusa, ya debo ganyen itaciyar, bai san ma ko wace irin itaciya ba ce. Ya taso fir ya kawo wa Musa. Musa ya karba, ya се, "Amma kuwa ka tsai da ni."" Aku ya ce, "Ba ka san iyakar inda na tafi ba ne, da ba ka zarge ni kan dadewa ba. Ka sa a dafa maka, ka yi wanka da shi, ba dai karfe ba, sai wani abu." Musa ya ce, "Ka ji asalatu ta yi." Aku ya cе, "Bа kome ka tafi gobe, zuwa da wuri ai ya fi zuwa da wuri wuri. Kafin a kare kiran salla bari in gaya maka wani dan labari guntu." 43 Labarin Kyanwa Da Bera Akwai wata itaciyar kuka a bayan wani gari. A gindin itaciyan nan akwai wani bera, a cikin kogonta kuma ashe akwai wani muzuru na kwana. Kukar kuwa cikin gonar wani mutum ta ke. Kullum dare sai muzurun ya fito ya je ya yi ta wa mutumin nan barna. Da mutumin ya ga haka, sai ya samo wata raga ya yi tarko, don ya kama kome ke shiga ke yi masa barna. Allah ko ya ba shi sa'a. Da asalatu ran nan muzurun ya ga beran, ya zabura zai kashe, sai ya fada cikin tarkon, ya yi ya yi ya fita, ya kasa. Bera kuwa da ya waiga ya ga tarko ya kame muzurun, sai ya yi rawa yana murna. Yana nan yana murna, ya duba haka cikin kara kusa da raminsa, sai ga wani maciji nan yana jira ya rabo da muzuru ya hadiye shi. Ya duba sama don ya hau, sai ya ga shirwa na kewaya, tana jira ya motsa ta fyauce shi. Bera ya tsaya, ya rasa inda za shi. Abu ya zama masa gaba siyaki baya damisa. Yana nan sai ya tuna wata dabara, ya ce, "Na san dai da maciji da shirwa ba mai iya zuwa kusa da muzuru. Yanzu ba abin da ya fi sai in je wajen muzuru, in ce ya rantse ba zai sake cutata ba, ni ko in cinye igiyar ragan nan in sake shi."" Sai ya tafi ya tambaye shi. Muzuru ya ce, "Ina za a fara wannan aiki? Ka fid da ni daga halaka, sa'an nan in cuce ka? Ai ka kubutad da ni, mun zama abokai ke nan har abada." Bera ya ce, "Bari in jarraba alkawarin nan naka in gani, in gaskiya ne. Zan kurda tsakanin kafafunka in gani in ba ka cuce ni ba. Amma fa ka sani in ka halaka ni, ka halaka kanka ke nan." Muzuru ya ce, "Ai ni ba na magana in tayar." Bera ya kurda ko'ina, muzuru bai motsa ba. Da maciji ya ga haka sai ya sulale, kada muzuru ya sami kubuta ya gama masa aiki. Shirwa ita kuma ta yi nata wuri, don tana tsoron muzuru. Muzuru ya ce wa bera, "Aboki, yi maza ka cinye igiyoyin nan, ko na tsira. Ko yaushe na motsa sai in ji sun kara daure ni." Bera ya ce, "Yi hakuri

Chapter 4 of 12