mene ne?"
Kaza ta ce, "I, gaskiya ne, ya kamata kuwa ka yi alfahari bisa
ga godiyan nan taka. Amma da ka taba ganin mutane sun kama
'yan'uwanka sun yanka, sun fige suna soyawa, yadda na ke ganin
kullum suna yi wa dangina, da ran da suka tashi kama ka, bari ta
gudu kana fadawa shigifu, in ka balle daga nan ka shiga daji, ko
labarin inda ka ke ba a sake ji."
Burtu ya yi shiru, ya rasa abin da zai ce wa kaza bisa wannan
magana tata. Kaza ta harare shi, ta juya, ta ce, "In za ku yi
magana, ku rika tsayawa tukun kuna lura, kuna auna ta tukun
kafin ta fito bakinku har wadansu su ji. Ga irin abin da a ke gudu ke
nan, mutum ya fadi maganar da bai san kanta ba, bai san gindinta
ba, ta zo ta dame shi daga baya. Kai, Allah wadan zaman daji!"
Da Ojo ya ji haka ya bushe da dariya, har ya haure ruwan
alwallarsa bai sani ba. Da ya gama dariya, ya kare alwalla, ya
shiga daki ya yi salla. Da ya gama, sai karuwan nan ta zo ta ce
masa, "Maigida, yau ni marmarin shinkafa na ke ji, ita zan dafa,
sai a sayo tozo."
55
Zai ce to, sai ya tuna da maganar aku, yana tsammani da ya
yarda zai mutu, ga shi kuma ba ya son bata wa matar zuciya, sai
ya tuna ba abin da ya fi ransa dadi. Ya san yanzu da ya mutu sai
ta fita ta auri wani, shi ta manta da shi. Sai ya ce mata, "An ki, ni
yau tuwon dawa za a yi mini, miyar shuwaka."
Ta dube shi haka yatsine, ta watsar, ta yi tsaki, ta ce, "In wani
ke min da hannun, ba sai ya sa in yi na dawa ba? Ni na shinkafa
zan yi, in kama kazarka a yanka in ka ki sawo mini tozo. In ya so,
in na yi, ko ka ci, ko kada ka ci, ni ba abin da ya dada ni da
kasa." Sai ta tashi ta nufi wajen buhun shinkafa, za ta diba. Ojo
ya ga in ya bar ta ta yi abin da ta ke'so, watau shi zai mutu ke nan.
Sai ya tafi ya kama ta. Sai kokawa ta kaure kiki kiki. Ojo ya tuna
shi namiji ne, ya dauke ta ya kantara da kasa, ya yi ta bugu.
Da mutane suka ji kuwwarta tana cewa, "Wayyo Allah, na
tuba! Ba na kara yi maka musu, ka ji kaina!" Sai suka rugo, aka
zo, aka kwace ta da kyar. Ta yi yaji.
Bayan kwana uku Ojo ya bi ta, aka yi rarrashin duniyan nan ta
dawo, ta ce in ta koma gidan nan ya zama kabarinta. Ta tashi za
ta yi masa halinsu na karuwai, ta tona masa asiri cikin jama'a ya
ce ya sake ta.
Abinka da mai sule, kafin kwana bakwai ya nemi 'yam mata
uku 'yan gaske, aka ba shi. Da ya mila, sai ya ce a sà su lalle gaba
daya. Aka sa su, aka yi biki, aka gama. Muka yi zamammu lafiya
lau da matan nan nasa, ba sauran mai kuka da wani.
Da aku ya kawo nan, ya ga gari bai waye ba, sai ya dubi Musa,
ya ce, "Don Allah ka yi kokari ka yiwo abin da kowa zai yaba. Kа
tabbata wata dabara taka, da wani tsoro, duk ba su hana makaа
mutuwa, domin duk ran da ajali ya yi kira, ko babu ciwo a je.
Gama Sarkin Yaki yana zaune lafiyarsa lau, amma ran da ajalinsa
yà sauka, sai da ya sayo wa kansa halaka."
Musa ya ce, "Ai Sarkin Yaki ya sami lafiya har ya tafi tare da
Sarki."
Aku ya ce, "Ba Sarkin Yakinku na nan gari na ke magana ba,
ina zancen Sarkin Yakin Niraini ne."
Musa ya ce, "Ina ne Niraini? Ban taba jih sunan wannan gari
ba, balle Sarkin Yakinsu. Me ya sa ya saya wa kansa halaka?"
Aku ya ce, "Yanzu kuwa ka ji."
56
In Ajali Ya Yi Kira, Ko Babu Ciwo A Je
Wata shekara mutąnen kasar Suraida suka kai yaki kasar
Niraini. Mutanen Suraida suka kori na Niraini suka kashe musu
jama'a mai yawa. Suna murna za su shiga garin, ashe Sarkin
Yakin Niraini ya shirya wadansu dakarai, suka biyo jama'ar
Suraida suka yi musu zobe, suka hana su gaba, suka hana su
baya. Da wani dakaren Suraida, wai shi Barde, ya ga za a halaka
su nan tsaye da yunwa ma kadai, sai ya ce wa 'yan'uwansa, "Ya
kamata mu yi kunar bakin wake. Kada mu mutu nan, mu bar
wa na baya abin fadi." Suka yarda, suka tasam ma mutanen
Niraini. Barde ya fara kaiwa, ya soki wani dan saurayi, ya mace.
Mutanen Niraini suka kashe yawancin mutanen Suraida, aka
kama Barde, har an fara sassare shi za a kashe, Sarkin Yaki ya ce
a kyale shi. Ya sa aka dauke shi aka kai shi gidansa, ya yi ta
jiyyarsa ba dare ba rana, kamar dansa. Kullum safe, da ya fara
iya magana, sai ya zo ya tambaye shi yaya ya kara ji.
Shi kuwa sai ya amsa masa, "Na gode Allah."
Yana nan gidansa, ba ya iya tashi har wata guda, sa'an nan ya
fara tashi da sanda yana doddogarawa. Sarkin Yaki na binsa,
yana-tare shi kada jiri ya kwashe shi ya faďi. Bayan 'yan kwanaki,
ya fara tafiya ba sanda. Ran nan yana tattakawa, ya dube shi, ya
ce, "Yi tsalle mu gani, in ka iya." Barde ya yunkura kamar zai yi
tsalle, sai ya ji ba ya iyawa. Ya dubi Sarkin Yaki, ya ce, "Baba, ai
ba na iyawa sai dai an.kara kwana biyu."
Bayan kamar kwana bakwai, da Sarkin Yaki ya ga lalle Barde
ya warke, sai ya ce ya yi tsalle ya gani. Ya yunkura, ya yi tsalle, ya
buga kafa, ya dube shi, ya durkusa ya ce, "Allah ya taimake ka
yadda ka taimake ni."
Sarkin Yaki ya ce, "Alhamdu lillahi, tun da ka warke!" Sai ya
nufi cikin gida, ya dauko masu guda biyu, ya fito da su wajen
Barde, ya ce, "Mu je bayan gari yawo, mu shawo iska." Barde ya
се, "То." Ya karbi masu ya rike, har suka isa bayan gari.
Da isarsu sai Sarkin Yaki ya ce masa, "Zabi daya." Barde ya
ce, "Me za mu yi da su?"
57
Sarkin Yaki ya ce, "Kai dai zabi daya, na ce." Ya zabi guda
gajere, ya mika masa dogon.
Ko da ya karba, sąj ya ce masa ya tsaya nan, shi ya ja da baya
kadan su yi yaki. Yaki ko na sosai, ba wasa ba, kowa ya sami
dan'uwansa ya kashe.
Da Barde ya ji haka, sai ya yar da nasa mashin, ya ja da baya,
ya ce, "Subuhana lillahi, Allah ya sawwaka in yi yaki da kai!"
Sarkin Yaki ya ce, "Ko kana kasa kana dabo, sai ka yi. Cikin
yakin da muka yi da ku watan jiya ina da da, kai ka sa mashi ka
tsire shi. Na neme ka kasa da bisa lokacin nan, na rasa, sai daga
baya har an yi maka raunuka za a kashe, na gan ka, na ga in na
kashe ka sa'an nan ban huce ba, don lokacin nan kusa da matacce
ka ke. Saboda haka na ce a kyale ka, na jiyyace ka, sai yanzu da
na ga ka warware, ka iya jin zafin da dana ya ji, na ke so in rama
masa, ko da ya ke ba shi da rai. Yana kan kokarinsa ka kashe shi,
saboda haka ni kuma na ke so in kashe ka bisa kokarinka, ba
sa'ad da ka ke ba wąni makami a hannunka ba. Yanzu ko kana
so, ko ba ka so, sai ka dauki mashin nan ka taso mini, sa'an nan
ni ko in tsire ka."
Barde ya yi tubar duniyan nan, ya ki ji, sai ya ce a ransa, "Da
ma ni kusan cikin matattų na ke, shi ya kubutad da ni, to, tun da
Allah ya nufa, don in kara shan ruwan wata guda ne kadai, aka
nufe ni da tsira da fari, ai sai in yi godiya." Ya dauki mashi ya
rike.
Ko da Sarkin Yaki ya ga ya rika, sai ya zaburo zai tsire shi,
yana tsaye yana Kalmar Shahada. Allah mai aikata abin da ya ke
so, wallahi, yallabai, kafin ya kawo gare shi, sai kafarsa ta fada
cikin wani ramin kurege, mashinsa ya kafe daga baya.
Yunkurawan nan da ya ke yi da fushi, sai ya fadi da baya bisa
58
mashin. Nan take ya tsire kansa, bai ko motsa ba. Da Barde ya ga
haka, sai ya rungume shi yana kuka. Ya sa hannu a kai, ya shiga
gari ya gaya wa Sarki yadda duk aka yi. Aka zo aka iske shi, aka
yi ta mamaki, aka rufe shi.
To, tun daga ran nan Barde ya dauki alkawari yana kawo wa
iyalin Sarkin Yaki abin da za su ci, har ya kan kawo musu awaki
su sayar su sayi hatsi, duk dai wai saboda alherin da Sarkin Yaki
ya yi masa.
Musa ya ce, "Wallahi in ni ne ko kasa ba na bada musu, tun da
ya ke ba da niyyar gari ya yi mini alherin ba."
Aku ya ce, "Ai ba kai kadai ba,
kowa ma ya ji wannan labari
haka zai ce."
Musa ya yunkura zai tashi, sai
ya ji an yi asalatu, ba damar ya
fita, kowa ya farka. Da azahar
tayi, Waziri ya ga ba zai sami
Musa ba, ta ya rude shi da
Mahmudu na can na abin kirki, sai ya sake dabara ya rubuto
takarda kamar daga Mahmudu, ya aiko tsohuwan nan ta kawo
wa Musa. Da ya karanta sai ya ga an ce, "Daga Mahmudu zuwa
ga dan'uwana Musa, rabin ransa. Gaisuwa mai yawa da so da
yarda. Bayan haka, Musa, yanzu kana da rai har ka yarda aka
raba mu ko? To, ga shi jiya na fada wani barde cikin mutanen
Sinari, ya yi mini raunuka abin ba ko masaka tsinke. Ga alamar
da na ke ji a jikina, ni da ganinka kuma sai Darassalam. Tun da
har ka manta da ni, ba ka iya kokarin da za ka zo mu nemi juna
gafara ba, to, shi ke nan, ba kome, ni na roke ka gafara. Mutuwa
dai ai kowa ka gani za shi ne. Musa! Musa! Tuna zumunci, Musa!
Haza wassalam."
Da Musa ya karanta wannan takarda $ai hawaye. Tsohuwan
nan kuma ta tsuguna ta yi ta yanka maså karya, wai a gidansu (a
ke jiyyar Mahmudu). Wannam takardar wai shi ya ba ta
hannunsa da nata. Musa duk ya dimauta, mutanen gida suka rasa
kansa, suka rasa gindinsa. Da
asubar fari, tun bayin nan ba su
yi barci ba, sai ya kintsa, ya tafi
wajen aku yana kuka, ya nuna
masa takardan nan da tsohuwa
ta kawo. Aku ya sa tabarau, ya
karanta, sai shi kuma ya fashe
da kukan karya, ko da ya ke ya
59
san takardar ba Mahmudu ya yiwo ta ba, makirci ne. Sai ya ce wa
Musa, "Sai ka yi shiri ka tafi."
Musa ya ce, "Ina fa ka ga taflya yanzu, ga bayi can ba su yi
barci ba? Da ma abin da ya sa ka ga na zo tun da wuri haka, don
in kawo maka takardan nan ne ka gani. In kuma kana da wani
labari wanda zai dan faranta mini rai, ka gaya mini tun yanzu, ko
na ji dan sanyi-sanyi a zuciya, kada in taho an jima in sun yi barci
ka ce za ka tsai da ni, har in zo in makara."
Aku ya ce, "Haba, ranka ya dade, in tsai da kai bayan na
karanta wannan takarda, mahaukaci ne ni? Tun da dai ka ce kana
son in gaya maka wani dan labari wanda zai sa bakin cikinka ya
ragu, wannan shi ya fi kome sauki gare ni. Ga kujera nan, zauna,
don tsayuwa ba ta da amfani."
Musa ya haye kujera ya zauna zugudum. Aku ya yi kaki, ya
tofad da yawu, ya fara:
60
Labarin Wadansu Abokai Su Uku
Wata rana wadansu samari su uku, abokan juna suka tashi daga
garinsu za su wani gari neman aure. Kowane ya yi wankin
kayansa, suka yi ado, suka kama hanya. Suna cikin tafiya, sai
karamin ya ce, "Ku ci gaba, na iske ku ni zan ratse.
Suka wuce, shi kuwa ya ratse, ya rabu da hanya kadan sai ya
tarad da wani dan akwati, barayi sun sato ya fadi. Ya duba
gabas, ya duba yamma, bai ga kowa ba, ya duka ya dauki
akwatin, ya ji da nauyi, ya nemo wani dutse ya fasa. Da
fashewarsa sai ya ga kuďi ciki cunkus, sulalla. Ya durkusa, ya sa
hannun rigarsa ya kunshe, ya fito da gudu ya bi 'yan'uwansa yana
kira. Da suka ji kira, suka tsaya. Ya ce, "Albishirinku!"
Suka ce, "Goro."
Ya ce, "Kun ga abin da na tsinta." Kowane da ya kyalla ido ya
ga kuďi, duk suka yi ta murna, suka koma gefen hanya suka
kidaya, suka ga fam ashirin da hudu ne da sisi. Wanda ya tsinto
kuďin na kirki ne, saboda haka ya ce, "Sai a raba, kowa ya sami
fam takwas takwas, sisin nan kuwa mu sayi abinci da shi mu ci."
Da babbansu ya ji haka sai ya сe, "To, madalla, mun gode,
Allah ya bar mu tare! Amma abin da ya fi, sai ka tafi gari maza
ka sawo mana tuwo da tsire da sisin nan namu. Mu kuwa mu ajiye
kuďin, in ka dawo sa'an nan mu raba."
Yaron da ya tsinci kudin ya tashi, ya nufi gari da gudu. Da
bacewarsa sai babban ya ce, "Abin da ya fi sai mu yi dabara mu
karbe kudin nan, mu raba mu biyu, watau fam goma sha biyu
biyu ke nan."
Daya abokinsa ya ce, "Lalle gaskiyarka. To, yaya za mu yi ke
nan?"
Babban ya ce, "Ina da dabara. Ga wani maharbi can, mu
kirawo shi mu ce ya shiga kogon itacen nan, in an yi magana ya
rika amsawa."
Suka kira maharbi, suka gaya masa duk abin da su ke so ya yi
musu, da abin da su ke so su karbe wa dan'uwansu, har suka ce sa
ba shi lada. Da maharbi ya ji batun kudi haka ya yarda. Ya shiga
61
kogon ke nan sai yaron ya komo. Da hango shi, sai suka fara
kuka. Ya ce, "Lafiya?"
Suka ce, "Ina fa lafiya, itacen nan ya kwace kudi duka!"
Yaron ya dubi itace, ya ce, "A'a karya ne, itace da ba ya
magana ma, ina ya kai ga sata? Ku dai ku sake shawara."
Daga nan sai mutumin da ke cikin itace ya ce, "Wace shawara
za a sake? Ni na dauke. Kuma in kana tsammani kai ka fi
'yan'uwanka jaruntaka, to, zo karbi. Matsiyata 'ya'yan zamani,
wadanda ko iyayensu ma ba su san girmansu ba, balle wani!"
Ko da yaro ya ii haka sai ya garzaya, bai zame ba sai gidan
Sarki. Ya gaya masa duk abin daya faru tun daga farko har
karshe.
Sarki ya ce, "An tasam ma munafunci. Yaya za a ce itaciya ta
yi magana? Ina 'yan'uwanka?""
Yaro ya ce, "Suna can gindin itaciya."
Waziri ya dubi Sarki, ya ce, "Ranka ya dade, ai sai ka sa ni in
tafi in ji in gaskiya ne. Ka san ikon Allah ya fi da haka.
Sarki ya ce, "To, sai ka tafi ka gani."
Yaro ya shige gaba har gindin itaciyan nan, suka tarad da
'yan'uwansa can suna 'yan koke-koke kamar da gaske. Da ganin
Waziri suka ce, "Alhamdu lillahi!" Suka faďi suka yi gaisuwa.
Waziri ya dube su, ya ce, "Ku ne itaciya ta kwace muku kuďi?"
Suka ce, "1, mu ne, ranka ya dade. Daga mun zauna nan
gindinta muna kidayawa, sai muka ga guguwa ta tashi ta murtuke
wurin, duk kura ta buce mu, muka rasa inda mu ke. Can an jima
sai ta natsa, muka duba kudin da ke gabammu, suka ce dauke
mu. Muka shiga tonon kasa, don muna tsammani kura ce ta rufe
su, ba mu ga ko kwabo ba. Muka tashi za mu yi fada da juna, don
kowa na tsammani dan'uwansa ne ya boye kudin, sa'ad da mu ke
ta kammu yayin da guguwa ta buce mu. Da muka fara zage-zage,
sai muka ji kamar daga sama an ce, "Kada ku zargi junanku, ni
na dauki kuďin. In kuwa kuna jin wata-wata ne ku zo ku kwata.
Muka duba babu kowa, sai dai magana mu ke ji na fitowa daga
itaciyan nan."
Da maharbin nan na cikin itace ya ji haka, sai ya nisa, ya се,
"M, wannan dahir ne."
Waziri ya dube su, ya ce, "A'a! Ai kuwa ashe da gaske ne."
Itaciya ta ce, "Af, da kana tsammani karya ne? Sai ka zo ka
kwatam musu.""
Ko da Waziri ya ji haka sai ya rike baki, ya ce, "Ki yi mini
gafara, ni ba ruwana, aiko ni aka yi."
Nan da nan sai ya aika aka fada wa Sarki ya zo da kansa ya
gani, domin an ce gani ya kori ji. Can an jima ya tinkaro duk da
62
mutanensa. Da isowarsa Waziri ya ce, "Ranka ya dade, ka ga
'yar itaciyar da a ke markabu kanta."
Da maharbi ya ji haka sai ya ce, "Wai, wai, wai, ni ce 'yar
itaciya! Kai ne wa tukun da ka ce mini 'yar itaciya? Har dan
tsugunin nan naka ka isa zagina? Daga yau ba ka sake duban
kamata ka ce mata 'yar itaciya ba!"
Da jin haka fa, sai hantar Waziri ta kada, ya fadi ya yi sujada
yana ta ahi, yana rokon gafara. Sarki ya tsaya tsayin daka, ya
dubi kogon itaciyan nan, ya ga lalle mutum na iya shiga. Ya lura
da gindinta kuma ya ga sawun mutum kamar ya hau ta, ya dubi
takon nan ya ga dai bai yi daidai da na ko daya daga cikin
samarin nan masu kudi ba. Ya tuna tun da ya ke bai taba jin ma
wanda ya ji maganar aljannu haka a fili ba. Kai, karewa ma dai
tun da Annabi ya kaura aka bar jin irin wannan al'amari. Ko da
ya lura da haka sai ya hakikance makirci dai aka kulla, don a cuci
yaron nan da ya tsinci kudi. Sai ya dubi Waziri da ke ahi, ya ce,
"Kai, tashi! Kwaure ka ke wa sujada?" Ya juya wa itaciyar, ya
ce, "Yanzu dai ko ki ba su kudinsu tun da girma da arziki, ko
kuwa in sa a kone ki. Da mutum da aljani ni duk wanda ya tasam
ma zalunci cikin kasata sai na ga iyakarsa!"
Sai itaciyar ta ce, "Kai dai tsaya kan mutane. In ka fada
aljannu sai kai a ga iyakarka."
Sarki ya dubi mutanen da ke nan, ya ce, "Duk ku saro kirare."
Suka ruga nan da nan suka cika gindin itaciyan nan da itatuwa da
kirare.
Ya ce, "A kawo ashana." Aka mika masa. Ya tasam ma
itaciyar zai kunna mata wuta, duk kowa ya rike baki. Maharbi ya
ga dai in ya kyale minti biyu, lalle zai halaka. Sai ya yi kara ya се,
"Don Allah, ranka ya dade, kada ka sa wutan nan. Ni ba kowa ba
ne, mutum ne. Bari in sauko don Allah!""
Nan da nan sai mutum ya tsirgo daga kogo, da kudin rike a
hannunsa. Ya fadi ya gai da Sarki, ya tsuguna nan, ya fede masa
biri har wutsiya.
Sarki da mutanensa suka yi mamakin wannan al'amari.
Mutane suka yi ta cewa, "Lalle Sarki shi ma aljani ne." Nan take
Sarki ya sa aka yi wa yaran nan biyu azzalumai, da maharbi,
bulala hamsin hamsin, ya sa aka kai su gidan kurkuku su yi wata
shida shida, ran da za su fito kuma a kewaya da su gari, kowa ya
gan su. Ya dauki kudin duka ya ba yaron abinsa. Yaro ya fadi ya
yi gaisuwa, ya tashi ya koma gidansu. Sarki kuma ya koma gida.
Kullum in an ta da tadi, in ya dubi Waziri, ya tuna da yadda ya yi
goho da katon bujensa, sai ya yi ta dariya.
Musa ya yi murmushi ya ce, "Ai ba Sarkin nan kadai ba, kowa
63
ya ji wannan labari ya yi dariya. Munafunci dai ba shi da
amfani."
Aku ya ce, "Ina ka san munafunci ba shi da amfani, tun da ba
ka ji labarin Kado ba, da wadansu 'yam fashi guda uku?"
Musa ya ce, "Har ya fi wannan daďi? Ban yi tsammani bа. То,
yaya suka yi? Fada mini mu ji."
Aku ya ce, "Wannan d'in me? Kasa kunne ka ji."
64
Munafuncin Dodo, Ya Kan Ci Mai Shi
Wata rana wani bakauye wai shi Kado ya dauki gatarinsa, ya
shiga daji zai yiwo itace. Dawan nan kuwa da 'yam fashi,
mutanen dan kauyen nan duk sun san da su. Can bakauyen nan
ya yi nisa cikin daji, sai ya hango wani abu tsibe yana daukar ido,
ya matsa ya ga ko mene ne, sai ya tarad da sulalla ne tsibe. Ya
waiwaya baya, ya waiwaya gaba, bai ga kowa ba. Sai ya duka, ya
cika aljihun taguwarsa fal, ya saba gatarinsa, ya sheka da gudu ya
nufi gida.
Ya rabu da wajen da ya debi kudin nan ke nan, sai ya gamu da
'yam fashi su uku. Suka ce masa, "Kai, tsaya! Me ya koro ka?"
Kado ya tirje yana kaduwa, yana tsammani kudin nan da ya
debo nasu ne. Sai ya ce, "Iye! Ni? Na'am. Mutuwa ce na gani a
fili, shi ya sa na ke gudu."
'Yam fashin nan suka yi dariya, suka ce, "Mutuwar da kanta
ka gani, ko kuwa maciji dai?"
Kado ya ce, "Iye! Ni wallahi mutuwar ce da kanta na gani a can
tsibe, shi ya sa ban ko tsaya wurin ba, don kada a ce na gan ta, na
sheko da gudu."
Da 'yam fashi suka ga lalle ya tsorata da su, sai suka ce masa,
"To, mu je, ka kai mu mu gan ta mu ma."
Kado ya wuce gaba suna biye, har wajen da kudin nan su ke.
Ya ce, "Ga ta! Na rantse da Allah kuwa ban diba ba, kada ku ce
ko na ďiba ne." Yana boye-boyen aljihu yana tsammani ajiyarsu
ce, shi ya sa ya kara rudewa haka.
Da Allah ya sa ba su dubi aljihunsa ba sai suka ce, "To, tafi. In
ka fadi kuwa, muna zuwa da dare mu yanka ka."
Ko da Kado ya ji haka sai ya ranta cikin na kare, bai zame ba
sai gida. Ya kai yana haki, kamar ransa zai fita. Ya boye kud insa,
ya kama bakinsa ya tsuke.
Da 'yam fashin nan suka ga ya wuce, sai suka yi ta mamakin
kudin nan, suka ce, "Watakila wadansu barayi ne suka sato, da
suka ga sun yi musu yawa suka zubad da sashi nan. Allah Sarki!
" Bakauyen nan fa tsammani ya ke, namu ne.
65
Babbansu ya ce, "Kai, ai ko ya firgita. Yanzu fa ya dade da
kaiwa gida."
Sauran suka ce, "Haba, tuni. Sa'ad da ya garzayan nan, ai ko
mota ba ta kamo shi." Suka bushe da dariya.
Sai babban ya dauki sule guda ya ba karamin, ya ce, "Ruga
maza kasuwa ka sawo mana abinci mu ci tukun, idanummu su
bude, sa'an nan mu san yadda za mu yi kasafin wannan kudi."
Karamin ya karba, ya sa riga kamar ba barawo ba, ya yi nadi,
ya tafi kasuwa, ya nufi wajen mai tuwo, ya sayo, ya kuma biya
mahauta, ya sayo musu tsire ya dora kan tuwon, ya dauko ya
nufo daji. Yana kulle-kullen abin da zai aikata da kuďin nan, da
nasa ne shi kaďai. Sai ya ga itacen tinya, ya ajiye kayansu, ya ce,
"Alhamdu lillahi! Bari in debi ruwan tinya in zuba wa abincin
nan, in kai musu. Ni kuwa ko sun ce in ci, sai in ce na ciwo daga
kasuwa. Ka ga da sur ci duk sai su mace, ni kuwa in kwashe
karfena, in shiga gari in yi ta kece raini." Ya karya tinya ya zuba.
Shi kuma ashe kafin ya dawo 'yan'uwansa sun yi shawara da ya
zo su kashe shi, su kwashe kudi, su raba su kadai. Suka ce ai haka
abin ya fi auki.
Can sai wannan karamin ya iso da kayan abinci. Ko da
ajewarsa sai suka hau masa da bugu, bai san hawa ba, bai san
sauka ba, suka kashe shi. Suka fada abinci da ci, in sun gama
sa'an nan su kwashe kudi su san inda suka nufa. Da gama cinye
abinci, sai kowanensu ya fara kaduwa, yana faduwa yana tashi,
kafin kiftawa da bismilla duk suka kai takarda.
Can bayan kamar kwana bakwai sai Kado ya ce a ransa, "Bari
in koma wurin nan, in na tarar suna kwashe kudinsu in tsuguna in
yi kala, ko Allah ya ba ni dan taro. In kuwa na tarad da su sai in
ce na zo ne in gaya musu Sarki zai aiko da dogarai a kama su
gobe, abin da ya fi kowa ya yi ta kansa. In ce kuma abin da ya sa
na gaya musu don haka, sun ji kaina ne ran nan. Ka ga watakila
ma sa ba ni dan sule. Kuďin dai ga su nan tsibe kamar ba su so, ba
su da alamar karewa."
Da isarsa wurin sai ya tarad da su duk sun mutu. Ya yi juyayin
abin da ya kashe su, ya rasa. Da ya lura har kuraye sun ci su, sai
ya yi zaton su ne suka kashe su. Ya rasa abin da zai yi don murna.
Ya shimfida gwadonsa, ya kwasa. Ya yi 'yan kirare ya dora, don
kada a gane, ya kai gida, ya gina rami ya binne. Magariba na yi
kuma ya kira dansa, suka tafi suka kwashe saura. Ya zauna ya yi
ta cin kudinsa sannu kan hankali, da shi da dansa, ba wanda ya
gane.
Musa ya bingire da dariya, ya ce, "Allah mai girma! In rabo ya
rantse, sai mai shi!"
66
Ya Saurara haka sai ya ji
kiran salla, ya ce wa aku,
"Wancan kiran sallan fa, na fari
ne, ko na biyu?"
Aku ya ce, "Sai dai na fari.
Amma bari mu ji." Sun yi shiru
suna saurare, sai suka ji ladani
ya ce, "Assalatu!"
Musa ya ce, "Subuhana lillahi, ashe har
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 12