sa an tsire shi, in gari ya waye. Ai cewa aka yi
su kama barayi, ba a ce musu su kashe ba. Duk mu tsaya, in ya so
in za su kashe mu ne su kashe mu duka, tun da dai suka raba mu
da dan'uwammu. In ko suka kashe mu, ai lalle sur ma a kashe su,
don mu ma Musulmi ne, ba kafirai ba."
Da 'Yan Gadin nan suka ji haka fa, sai suka yi tsammani sun
kashe mutumin nan ne. Saboda haka suka fara shawarar su gudu,
kada a gan su. Suna cikin shawarar inda za su bi, sai suka ji
barawon nan na kwance, ya fara kakarin mutuwa, yana shakuwa
kikaf kikaf. Can sai ya ja wani kakari mai karfi, ya yi shiru.
Sauran barayin suka buga salati baki daya, suka ce, "Ya cika."
Ko da 'Yan Gadi suka ji haka, ba su tsaya su gama shawarwarinsu ba, sai kowa ya ce in ba ka yi ba ni wuri. Kazunzumi da
jin tif tif tif na 'Yan Gadi suna gudu, sai ya tashi ya shiga gaba,
sauran na biye har gida.
Da zuwa suka sami ruwa mai sanyi, suka kyankyama. Ka san
na gaya maka kafin su debi rogon nan sai da suka ci daya daga
cikinsu tukuna. Abinka da kayan zalunci, ko da suka sha ruwan
nan sai danyen rogon nan da suka ci ya taso, ya murde su, kowane
ya yi ta murde-murde abinsa, yana nishi. Kafin asalatu cikunansu
suka haye tim, sai amai sai zawo, gari bai waye ba, sai da duka
suka hauri arewa.
Da safe da aka tarad da su kowane cikin nan ya kumbura
kamar salka. Ga su kace-kace cikin amai da zawo. Rogo na fita
har ta hanci. Aka duba sako aka ga kwanduna cike da danyen
rogo, sai aka hakikance danyen rogo suka yi wa cin yunwa, ya
halaka su. Aka yi 'yan koke-koke, aka yi musu jana'iza, aka kare.
20
Garin nan ya faye yawa, 'Yan Gadin nan ba su san wannan
abin ya auku ba. Da suka gamu da hantsi sai guda ya ce, "Shin wa
ku ke tsammani ya harbi mutumin nan ne na jiya? Ni dai na
tabbata ba ni ba ne."
Na biyu ya ce, "Balle fa ni da na ke biye da ku daga baya."
Na uku ya dubi na fari, ya ce, "Amma ko da ku ke neman ku
maka mini laifi, ai ku kuka ce in harba."
Na fari ya ce, "I, gaskiya ne, amma ai kai ka san abin da na ke
nufi. Ka harba ta ketare kansa, ba ka same shi ba."
Na uku ya ce, "Ni ma tsammani na ke koli na harba ta. Ina
mamakin yadda ta same shi. Kaddara dai ce ta tarad da ajali
kusa."
Sauran suka ce, "Gaskiya ne, sai dai mu yi kurum, kada mu
tona kammu."
Daga'ran nan duk sa'ad da biyu daga cikinsu suka gamu sai su
ta da taďin, su rika kokari su lika wa wanda ba ya nan laifin. Suka
zauna kan hakanan dari dari har iyakar ransu, suna tsammani a
gane su yau, a gane su gobe, ba su ji magana ba. Suna son su
tambaya, suna jin tsoron kada son iyawa ta tona su.
Musa ya ce, "Wadannan 'Yan Gadi sun kuwa isa sakarkaru."
Aku ya ce, "Su ma ai suna da hankali bisa ga wani Bahaushe
wanda ya tafi fatauci cikin kasar Yarbawa."
Musa ya ce, "Har ya fi wadannan sakarci? Haba, wanda ya fi
wadannan sakarci, ai sai yanka."
Aku ya ce, "Bari ka ji gogan naka, ka san ko cikin Hausawa
akwai Yausawa."
21
Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku
Taho Tare
Wata rana wani Bahaushe wai shi Wawa za shi fatauci, sai ya bi ta
kasar Yarbawa, Wawa ba ya jin Yarbanci, mutanen da ya tarar a
wannan gari su kuma ba su jin Hausa. Amma duk da wannan
Wawa bai lura ba. Yana cikin tafiya, ya kawo kofar gari, sai ya ga
wani katon garken shanu fari fat suna kiwo. Wawa ya yi
mamakin wanda ke da wadannan shanu masu yawa haka, sai ya
tambayi wani mutum nan kofa ya gaya masa ko shanun wane ne
wadannan.
Mutumin ya amsa da Yarbanci, ya ce, "Ni baı ji ba."
Wawa da ya ji haka tsammani ya ke "Ni ban ji ba" shi ne
mutumin da ke da shanun. Don haka ya ce, "Ni-ban-ji-ba lalle
yana da sukuni." Ya wuce ya shiga gari, sai ya kai ga wani
babban gida. Ya daga kai, ya ga lalle gidan nan ya amsa sunansa,
sai ya ce wa wani yaro da ke nan kofar zidar, "Don Allah,
samari, wa ke da wannan babban gida haka?"
22
Yaron ba ya jin Hausa, shi kuma sai ya ce a cikin harshensa
"Ni ban ji ba."
Da Wawa ya ji haka, sai ya ce, "Kai, ba shakka Ni-ban-ji-ba ba
wanda ya fi shi sule garin nan. Wannan irin gida sai ka ce na
Sarki. Da ganin wannan ai ko ba a gaya maka ba ka san wurin
nan sule ya zauna da gindinsa." Ya haura takalmansa ya wuce
faram, faram, faram, faram, har bakin kogin garin. Yana zuwa
sai ya tarad da wani jirgi ya zo, ana ta fid da kaya daga cikinsa.
Wawa ya dubi kaya, ya ce, "Oi! Wannan jirgi ya yiwo kaya!" Ya
dubi wani nan kusa gare shi, ya ce, "Dan'uwa, duk ko kayan nan
na mutum guda ne?"
Shi Bayarabe bai ji abin da ya ce ba, sai ya dube shi, ya ce, "Ni
ban ji ba."
Da Wawa ya ji haka sai ya rike baki, ya ce, "Masu gari!
Hakika Ni-ban-ji-ba ya huce haushinsa. Ina ma Allah zai sa in
gamu da wannan mutum, ko wajen adonsa ma in more ma
idona!" Sai ya zauna ya huta, ya debi ruwa ya sha, ya kama
hanya zai wuce. Ya kai kofar gari ke nan, sai ya ga wani matacce
an dauko shi, za a kai shi a rufe, wadansu na ta kuka. Wawa ya
tsaya yana dubansu. Tausayi ya kama shi, ya matsa wajen wata
tsohuwa, ya ce mata, "Wane ne wannan ya riga mu gidan
gaskiya?"
Tsohuwa ba ta ji Hausa ba, sai ta dube shi, ta ce, "Ni ban ji
ba.""
Wawa da ya ji haka sai ya dafe kai, ya ce, "Allah mai girma!
Ka san kowa samun nan na duniya ya ruda, ya shiga uku. Don
Allah dubi abin da Ni-ban-ji-ba ya tara. Ga shi yanzu ya zama sai
labari, kamar dadai duniya ba a halicce shi ba! Cikin duk abin
nan da ya tara, dubi dan kyallen da za a kai shi da shi. Tun da ya
ke al'amarin nan haka ya ke, to, ni yanzu me ya ruda ni har da na
rabo da gida don rashin wadar zuci? Ga shi Allah bai hana mini
abin da zan ci ba. Watau ba dai abin da ya fid da ni gida sai in
sami abin alfahari in kara sabo. Mhm, Allah ya kiyashe mu da
aikin Shaidan! Na gode Allah da ya kawo ni nan na sami gargadi
daga al'amarin Ni-ban-ji-ba. Ba sauran abin da ya fi, sai in koma
garimmu, in dangana da abin da Allah ke ba ni wajen 'yar gonata.
Da ma an ce, "Gani ga wani ya
isa tsoron Allah."
Musa ya tashi, har ya bude
zauren farko, sai ya ji bayi sun
farka. Sai ya kuta, ya koma.
Da Waziri ya ga kwana biyu
sun wuce, kowace safiya bayin
23
nan da ya sa suka dawo sai su ce ba wanda ya ko leko zauren, har
abin ya dame shi, ya ce, "A'a! Da ko na yi tsammanin zai fito,
yaya haka! Amma ba kome, kada ku fasa aikinku, na san
dabara." Ya kira wata tsohuwar baiwarsa, ya bayyana mata abin
da ya ke so duka game da Musa, ya ce mata in ta yi kokarin ta
taimake shi har ta sa Musa ya fito waje, zai ba ta fam goma, ya
kuma 'yanta ta. Ya kawo sule goma, ya fara ba ta ta lasa.
Tsohuwa ta ce, "Ta kwana gidan Sauki." Magariba na yi, sai
ta shiga gidan Sarki da kayan talla, ta kaikaici idon mutane ta
yahuto Musa waje guda, ta ce, "Mahmudu ya aiko ni, ya ce a
gaya maka wai kai haka za ka yarda ka lalace cikin mata? Ya ce a
gaya maka fa duniya ba ta auren raggo."
Musa ya matsa kusa da tsohuwa, ya ce, "Don Allah iya, yana
can yana ta yaki ko?"
Tsohuwa ta ce, "Haba! Yanzu sansanimmu akwai wanda a ke
magana irin Mahmudu? Ni ma fa can na ke sansani, mu ke yi
musu abinci. Mahmudu ya shaku da ni, ya aiko ni gare ka."
Musa ya ce, "Koma maza ki gaya masa, gobe in Allah ya so ya
gan ni." Tsohuwa ta koma.
Da dare ya yi, Musa ya saurara ya ji barci ya kwashe bayin nan,
sai ya shigo damaru, ya zo wurin aku, ya ce, "Ka ji Mahmudu na
can sansani yana ta abin kirki, ni za ka sa in lalace nan cikin
mata."
Aku ya ce, "Yallabai, ina ruwana? Ni ban hana ka ba. Yaya
barde kamarka zai ce za shi wurin yaki a hana shi? Tun da ya ke
niyyarka ka yi abin da zai faranta wa tsohonka rai ne, ai kowane
24
hadari ka shiga Allah ya fisshe ka, yadda ya fid da Auta dan
Sarkin noma daga namun jeji."
Musa ya ce, "Wane rigima ta kai shi ga fadawa hannun namun jeji?" Aku ya karba:
25
Labarin Auta Dan Sarkin Noma Da Namun Jeji
Wata rana wani manomi ya ce wa dansa Auta kullum ya san
yadda zai yi ya harbo musu abin da za su yi miya. Auta yа сe.
"To." Kowace rana sai ya je daji, yau in ya harbo zomo, gobe ya
harbo batsiya ko gada. Kullum haka har ran nan bai samo ba,
uban ya yi ta yi masa fada har ya ba shi kashi.
Yana cikin haka, ran nan har namomin daji suka gaji da kisa,
suka kai kara gun zaki, Sarkinsu. Zaki ya ce, "To, yaya za mu yi?
Kun sani fa Allah abin tsoro ne, mutum ma abin tsoro ne."
Sai kura ta ce, "Ai, ranka ya dade, babu wata dabara sai mu yi
kokari mu kawo maka yaron nan, kai kuwa ka yi abin da ka ga
dama da shi."
Sauran dabbobi suka ce, "Ai kuwa haka ne, abin da kura ta ce
shi ne gaskiya." Suka sallami Sarki, suka watse.
Ran nan yaron yana yawon harbi sai ya ci karo da dila ya ja
baka zai harbe shi, sai dila ya ce, "Tsaya! Na ce ko abinci ka ke
so? Zo in kai ka inda za ka hųta da wahala."
Auta yana tsammani gaskiya ne. Ya bi shi, suka mika har wani
katon kogo inda zakin nan ya ke mulki. Da shigarsu dila ya ce ya
ajiye bakansa daga waje don kada a ce shi maharbi ne. Suka
shiga, sai dila ya komo da baya ya boye bakan yaron. Suka tarad
da zaki a zaune, duk ga namomin daji sun kewaye shi, ana
fadanci. Dila ya fadi, ya yi gaisuwa. Kura ta dubi yaron nan, ta
ce, "Kai, ba ka gai da Sarki?"
Auta ya ce, "Ke, me ya sha miki kai? Ke kika aiko ni?"
Ya duka ya yi gaisuwa. Da suka zauna, zaki ya dubi dila, ya се,
"Shi ne wannan da ya dame ku?"
Kura ta amshe ta ce, "Shi ne, ranka ya dade. Kuzajje mai kaі
kamar kodago!"
Zaki ya ce ma Auta, "Kai samari, me ya sa ka ke kashe mana
'yan'uwa?""
Kafin ya amsa tambayar Sarki sai kura ta ce, "Ranka ya dade,
raina mu dai ya yi, dubi jikinsa, dan nema, jemamme!"
Auta ya durkusa, ya ce, "Ranka ya dade, shin kai ne Sarki, ko
kuwa kura?"
26
Da zaki ya ji hàka, sai ya yi fushi da kura, ya ce. "Kada in sake
jin kin yi magana a nan. Faďi jawabinka, samari."
Auta ya sake durkusawa, ya ce, "Dattijan garimmu suka ce in
zo in rika kashe ku, don mu ga idan abubuwan da kura ke fadi na
labarinka gaskiya ne."
Zaki ya ce, "Me kura ke faďi na labarina?"
Auta ya ce, "Mu da nufimmu mu fid da Sarkimmu na mutane,
don ba shi da hakuri, mu nada ka, ka yi mulkin dabbobi kuk da
mutane baki daya, mu gama kammu mu bi ka, duk abin da ka ce
mu yi, mu yi, abin da ba ka so mu bari. To, muna cikin wannan
shawara sai ran nan kura ta shigo gari ta ce ka aiko ta, wai ba abin
da ke tsakanimmu da kai sai kisa. Muka sake tambayarta, ta ce
duk Sarakunan duniyan nan babu azzalumi irinka. Wai da an yi
maka dan laifi kadan sai ka ce a kashe mutum. Saboda haka aka
ce in rika kashe ku, mu gani ko ka sa a kashe ni. In ka sa an kashe
ni, lalle maganar kura gaskiya ce. In kuwa ka yafe ni, kura ta
zama makaryaciya."
Zaki ya dubi kura, ya buga mata tsawa ya ce, "Wa ya aike ki ga
mutane?"
27
Ta zabura, zawo na fita, ta ce, "Karya ya ke yi, ban taba shiga
gari ba."
Auta ya ce, "Wa ke maki karyar, zaki da kansa? Kin manta har
muka ba ki kujera kika zauna, don girmamawar Sarki da kika се
ya aiko ki?"
Za ta yi magana zaki ya zabura, ya sa gaba ya banke ta, duk
namun daji suka hau mata, mai yaga na yi, mai cizo na yi, har
suka kashe ta. Zaki ya sallami yaron nan. Ya ba shi kaya mai
yawa irin wanda su ke kwacewa daga fatake. Yaro ya yi godiya,
ya ce zai je ya gaya wa mutanen gari abin da ya auku. Wannan shi
ya sa ko yaushe in ka ga zaki a daji ka durkusa, ka ce, "Ranka ya
dade," ba zai cuce ka ba.
Musa ya duba haka, sai ya ga gari ya waye. Bai ko tsaya ba ya ji ko labarin ya kare, ko bai kare
ba, sai ya yi tsaki, ya juya ya
shiga gida. Yinin ran nan duk ya
ki ko zuwa wurin aku, har
magariba ta yi. Bayin Sarki suka
ci abinci suka zauna hira, sai can
barci ya kwashe su.
Da Musa ya ji alamar bayi sun
yi barci sai ya tasam ma wajen aku. Da hango shi sai aku ya bushe
da dariya. Musa ya dube shi, ya ce,'Me ka ke wa dariya
haka, kai kadai kamar mahaukaci?"
Aku ya ce, "Ai ba ka san abin
da aka yi ba jiya da dare.
Shigarka ke da wuya, sai na ji
bayin can naka na babban zaure
suna hira, Sarkin Gida na yi
musa tatsuniya. Da na ga ba na
jin barci, ni kuma na tafi in taya su. Da Sarkin Gida ya kare
tatsuniyoyinsa, ni kuma na ba su labarin. wani bakauye da
wadansu 'yam birni."
Musa ya ce, "Ashe Sarkin Gida tsofai-tsofai da shi nan, har ya
iya tatsuniyoyi?" Labarin me ka tarar yana yi musu?"
Aku ya ce, "Ba wani labari mai dadi ba ne, tun ina yaro na san
shi. Kokawa da aka yi cikin labarin ne, in na tuna ta ke ba ni
dariya."
Musa ya ce, "Yaya suka yi?"
Aku ya ce:
28
Labarin Sahoro Da Sahorama
Wai akwai wani saurayi ne wanda a ke kira Sahoro. Kullum bá ya
tabuka wani aiki sai ya kora akuyarsa, ya kai ta bakin rafi ta yi
kiwo, da maraice ya kwanto ta. Nonon akuyan nan shi ne
abincinsa, ko ya sayar ya sayi wani abu, ko ya sha hakanan. In
akuyar ta yaye kuwa, sai ya sayar da ita, ya sayi wata mai da.
To, ba abin da ya miskile shi sai kiwon akuyan nan. Kullum ya
dawo gida sai ya ce, "Wash, ba shakka kiwon akuya ba aikin da
ya sha kansa kan wahala! Haba, lokacin nan yanzu akwai abin da
ya fi mutum ya sami inuwa mai sanyi, ya kishingida, ya yi ta
barci? Amma ba dama, dole ne mutum ya bi ta, in ko ya ki, ta
fada wata gona ta shirga barna a ci mutum tara, ko kuwa ta ki
dawowa kura ta sami kalaci. Kai, ya kamata dai in tuna yadda
zan sanyaya wa raina daga wannan azaba. Rai fa an ce dangin
goro ne, ban iska ya ke so."
Yana nan kullum yana zulumin wahalar kiwo, sai ran nan ya
ce, "Ah! Na san dabara, ba abin da ya fi sai in auri Sahorama. Ga
ta da akuya daya ita kuma tana kiwo, ka ga in na aure ta sai ta
rika gamawa da tawa, ni ko in samu in rika taba dan kailula."
Sai ya nemi Sahorama aure. Iyayenta suka ce, "Am ba ka. Dа
ma da Tukura da Bako duk Umbutawa ne."
Aka yi aure, ta tare, ta shiga hidimar kiwon awakinsu biyu.
Don ba su da wani abinci sai wanda suka samu daga gare su.
Sahoro ya yi ta shara barci a natse.
Ba a dade ba kuma Sahoroma ta ce wa Sahoro, "Maigida, ni fa
na gaji da wannan irin wahala, kudaje na cizona, ina tuntube.
Don Allah, dubi jikina. Da na zo nan gidanka ina sheki, duk
yanzu na fara kirci don cizon kudaje. Kai, ba na yarda in tsofad
da kaina tun ina gabar kuruciya, sai mu sake dabara."
Sahoro ya ce, "Wannan batu naki ba makankara. Ni ma fa na
ga kin fara baki, ni ko dubi yadda na fara ajiye taiba. To, yaya
zan yi da su?"
Sahorama ta ce, "Sai mu ba Dabo, ya ba mu amiya guda, mu
ajiye a bayan gida, in zuma ta shiga ta yi saka, mu rika diba muna
29
samun abinci. Ka ga ba ruwammu da kiwonsu, balle mu wahala."
Sahoro ya ce, "Kai, ai ko kin samo dabara, ga shi kuma ko ba a
faďi ba zuma ta fi nono dadi." Sai ya sa matar ta je ta yi magana
da Dabo. Ya yarda da musayar, don ya ga da riba. Ya ba su
amiya guda, suka yi ta samun zuma daga ciki suna sha. Suka sami
wani gora suka cika, suka rataye.
Sahoro dai in ya kwanta tun da dare, ba ya tashi sai rana ta
take. Ya kan ce wai tashi da wuri shi kan hana gira tofo, kuma ya
kan sa dundumi. Ran nan ya farka daga barci da rana tsaka, sai
ya ga matarsa ta dauko goran zuman nan, za ta diba ta yi musu
gari su sha. Sai haushi ya kama shi, ya ce, "Ku fa mata barnarku
ta fi ku! Dubi goran zuman nan har ya kusa karewa. Watau
zuman nan ta kare ne, har za ki fara dibar ta gora? Abin da na ga
ya fi sai mu sayar da goran zuman nan mu sayi kaji da zakaru, su
rika yi mana kwai suna kyankyashewa."
Sahorama ta ce, "In ko haka ne sai mu sami wani yaro wanda
zai rika zuba musu ruwa da hatsi. Ni dai ba na iya wannan jidali
kullum kwanan duniya."
Sahoro ya ce, "Lalle kiwon kaji wahala ne ja wur. Yaran yanzu
kuwa kowa ya san su a kan ragwanci. Yanzu ko, ko mun yayo
wani yaro don ya rika lura da kajin, in mun saya sai ki ga wasa ya
dauke masa hankali, ba ya wani abin kirki."
Sahorama ta ce, "Ko wane yaro muka dauko in ya ki yin aiki
sai in dauki sandan nan" (ta sa hannu ta dauki wani guntun itace),
"in sheme shi, tau a kai!" Sai ta kwantara wa gora ice, Gora ya
fashe, 'yar zumar da su ke takama da ita ta tsiyaye.
Sahoro ya ce, "Shi ke nan, ta faru ta kare, an yi wa mai dami
30
daya sata! Da kajin da za mu saya, da yaron da za mu dauko, duk
ga su nan sun malale a kasa. Amma dai na isa barka, da sakainan
nan da ta yi tsalle ba ta fada mini a kafa ba." Ya dubi matar, ya
ce, "Sa hannu, kwashe wannan da ke gudu kasa kafin kasa ta
shanye, don mu sami na farawa, kada yunwa ta sa in gintse
barcina tun ban koshi da shi ba."
Sahorama ta shiga sa hannu tana kwashe zuma, tana zuba dan
abin da ta samu cikin wata kwarya, tana lashe rabi tana ba mijin
labari tana cewa, "Abin nan fa da na yi yanzu amfanimmu zai yi
nan gaba. Don na taba jin wata rana an gayyaci kunkuru wajen
aure, don rashin saurinsa da ya tashi bai kai gidan ba sai bayan
watanni. Da ya isa ya tarar ana sunan dan amaryar da ya zo
bikinta ta haifa. Da aka gaya masa ya ce, "Ba kome, sauri shi ke
haihuwar nawa!"
Sahoro na kwance bisa gado yana kallonta, tana ta shan zuma
da wayo, tana zuba masa surutun banza. Sai haushi ya kama shi,
ya ce mata, "Wane labarin banza ki ke ba ni haka, ba kai ba
gindi? Wayon a ci an kori kare daga gindin kanya! Ga shi
ragwancinki ya jawo mini asara, wai ba ki iya kiwon kaji biyu sai
kin nemi yaro. Mutuniyar banza, sullutuwa!"
Sahorama ta ce, "Kai ne mutumin banza, wanda in ya kwanta
da magariba ba ya tashi sai gari ya waye da rana tsaka!"
Sahoro yana dai daga kwance ya ce, "Wa ki ke zagi,
Sahorama? Ka ga lalatacciyar banza, Kafira!"
Sahorama ta ce, "An je an zage ka, kai dai ne Kafiri, ba ni ba.
In kai da ne, ba shege ba, ka gina rami ka tsattsage ni!"
Sai zuciya ta turnuke Sahoro, ya tashi daga kwance ya sauko,
ya tarad da matar, sai kokawa kici kici, kica kica. Can Sahoro ya
gaji, ya ga bai ka da matar ba, sai ita ke neman tandara shi da
kasa. Sai ya ce mata, "To, sakan ni, kin kayar. Na ce ko iyakarta
ke nan?"
Sahorama ta ce, "Af! To, in sake ka, ni in fadi?"
Musa ya ce. "Lalle ne wannan kokawa tana da ban dariya. To,
kai gogan da ka je, wane labari ka ce ka ba su na bakauye da
wadansu 'yam birni?"
Aku ya ce, "Wannan shi ma yana da ban dariya."
31
Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yam Birni
Wata rana wadansu 'yam birni na zaune, sai ga wani bakauye
tafe, yana janye da jakinsa zai kai kasuwa ya sayar. A gaban
bakauyen nan kuwa akwai wani dan hoto, shi kuma za shi
kasuwar ya yi wasa. Ana tafe ana yi masa kidi, yana jefa garma
yana cafewa.
Da 'yam birnin nan suka lura da bakauye, sai suka ga ya bude
baki yana ta kallon dan hoto, bai kula da ko jakin da ya ke ja ba.
Daga nan sai wani daga cikinsu ya ce, "Yanzu fa ba ku sani ba,
karbe wa muzin nan jakinsa bai sayi wuri ba, in ina so."
Saura suka ce, "In ba kurarinka ba yanzu, yaya za ka yi? А
buge dai ba ka iya buge shi ka karba, yanzu ko ba dare ba, balle
ka ce ka sace."
Sai dan birnin nan ya tashi ya bi bayan bakauye, saura na biye
da shi sululu. Ya matsa, ya kwance igiyar da ke wuyan jaki ya
daura wuyansa, ya mika wa 'yan'uwansa jakin, suka koro. Gagon
naka tun da dai ya ke jin tsauri-tsauri a hannunsa, sai ya yi ta
tafiya baki bude, yana kallon dan hoto.
32
daya sata! Da kajin da za mu saya, da yaron da za mu dauko, duk
ga su nan sun malale a kasa. Amma dai na isa barka, da sakainan
nan da ta yi tsalle ba ta fada mini a kafa ba." Ya dubi matar, ya
ce, "Sa hannu, kwashe wannan da ke gudu kasa kafin kasa ta
shanye, don mu sami na farawa, kada yunwa ta sa in gintse
barcina tun ban koshi da shi ba."
Sahorama ta shiga sa hannu tana kwashe zuma, tana zuba dan
abin da ta samu cikin wata kwarya, tana lashe rabi tana ba mijin
labari tana cewa, "Abin nan fa da na yi yanzu amfanimmu zai yi
nan gaba. Don na taba jin wata rana an gayyaci kunkuru wajen
aure, don rashin saurinsa da ya tashi bai kai gidan ba sai bayan
watanni. Da ya isa ya tarar ana sunan dan amaryar da ya zo
bikinta ta haifa. Da aka gaya masa ya ce, "Ba kome, sauri shi ke
haihuwar nawa!"
Sahoro na kwance bisa gado yana kallonta, tana ta shan zuma
da wayo, tana zuba masa surutun banza. Sai haushi ya kama shi,
ya ce mata, "Wane labarin banza ki ke ba ni haka, ba kai ba
gindi? Wayon a ci an kori kare daga gindin kanya! Ga shi
ragwancinki ya jawo mini asara, wai ba ki iya kiwon kaji biyu sai
kin nemi yaro. Mutuniyar banza, sullutuwa!"
Sahorama ta ce, "Kai ne mutumin banza, wanda in ya kwanta
da magariba ba ya tashi sai gari ya waye da rana tsaka!"
Sahoro yana dai daga kwance ya ce, "Wa ki ke zagi,
Sahorama? Ka ga lalatacciyar banza, Kafira!"
Sahorama ta ce, "An je an zage ka, kai dai ne Kafiri, ba ni ba.
In kai da ne, ba shege ba, ka gina rami ka tsattsage ni!"
Sai zuciya ta turnuke Sahoro, ya tashi daga kwance ya sauko,
ya tarad da matar, sai kokawa kici kici, kica kica. Can Sahoro ya
gaji, ya ga bai ka da matar ba, sai ita ke neman tandara shi da
kasa. Sai ya ce mata, "To, sakan ni, kin kayar. Na ce ko iyakarta
ke.nan?"
Sahorama ta ce, "Af! To, in sake ka, ni in fadi?"
Musa ya ce. "Lalle ne wannan kokawa tana da ban dariya. То,
kai gogan da ka je, wane labari ka ce ka ba su na bakauye da
wadansu 'yam birni?"
Aku ya ce, "Wannan shi ma yana da ban dariya."
31
Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yam Birni
Wata rana wadansu 'yam birni na zaune, sai ga wani bakauye
tafe, yana janye da jakinsa zai kai kasuwa ya sayar. A gaban
bakauyen nan kuwa akwai wani dan hoto, shi kuma za shi
kasuwar ya yi wasa. Ana tafe ana yi masa kidi, yana jefa garma
yana cafewa.
Da 'yam birnin nan suka lura da bakauye, sai suka ga ya bude
baki yana ta kallon dan hoto, bai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 12