makami kusa da shi, sai ya ce, "Ashe ku duka mata ne, yaya
za a bar ku kumu ku rika zama ba mai ko sanda? Halal kun
manta da duniya." Bayi suka ga gaskiyarsa, kowa ya dauko
takobinsa ya zare ya ajiye a gabansa, aka shiga hira.
Can lisha sai ga bayin nan na Waziri su biyar, har da Barakai,
suka shige gida sai ka ce mata, aku kadai ya gane maza ne. Suka
sami wani zaure suka make, su ba su cikin gida, su kuwa ba su
waje. Suna nan suna jiran Musa ya shigo, don su tarye shi nan su
halaka shi, hira ta ki karewa. In aku ya ga za su dan dakata sai ya
yi musu wani abin dariya. Suka yi ta yin haka har asuba ta yi.
Da aku ya ga sun gaji da hira, wadannan sun fara gyangyadi,
sai ya ce, "Bari in yi muku wani labari mai daďi."
Musa ya ce, "Ai ko hakanan ne, ku tsaya ku ji fasaha wurin
dan tsuntsun nan nawa." Wadanda ke jin barci suka murje
idanunsu.
Aku ya sami ruwa ya kora, ya yi kaki ya zubad da yawu, ya
fara:
115
Sauri Ya Haifi Nawa
An yi wani Sarki nan arewa wanda ke da dan auta da ba a taba
ganin kyakkyawa irinsa ba. Da fari dai ga shi, shi bai cika
kyamushewa ba, shi kuwa ba kakkaura ba hakanan. Wuyan nan
nasa sai ka ce goran nono, idanunsa ko fari fat sai ka ce madara.
Gashin kansa ma abin kallo ne, don sai ka ce mai ya ke shafa
masa. In ko har ya yi dariya ka ga hakoran nan, wayyo Allah!
Kafafunsa kuwaMusa ya ce wa aku, "Kai don Allah in za ka ba mu labari ka ba
mu mu sha, in ko ba ka ba mu, ka kyale mu kowa ya san abin da
ya kama."
Aku ya ce, "A'aha! A bar ni in gyara labarina yadda zai yi
daďi."
Wata rana Sarkin nan ya hau duk da mutanensa, don ya
kewaya kasarsa ya buga musu haraji. Suna cikin tafiya sai
autansa ya janye wani baransa, suka rika ja da baya. Suna son a
wuce su kama labarin duniya. Ko da suka ga rundunar Sarki ta
bace, sai suka yi ta tadinsa suna kakkawa suna tafawa. Suna cikin
haka sai suka isa wani dan kauye wanda Sarki ya wuce tuni. Da
suka ga azahar ta yi sai suka sauka, don su yi salla. Baran nan ya
tafi gidan mai garin ya gaya masa ga dan Sarki nan zai yi salla a
garinsa.
Da bayin nan na Waziri suka ga ga shi har asuba ta yi Musa bai
ko motsa ba, balle su sami damar gama masa aiki, sai suka sake
shawara, wani daga cikinsu ya zo ya durkusa gaban Musa kamar
mace, ya ce, "Ana kira ciki."
Musa na tsammani baiwarsa ce, sai ya ce, "Je ki, ina tafe," ya
koma, Aku ya ci gaba da labarin da ya ke bayarwa, ya yi ta jansa,
don kada ya kare gari bai waye ba Musa ya ce zai tashi.
Da baran ya wuce, sai ga wata yarinya kamar 'yar Larabawa ta
fito daga wani gida kusa da masallaci. Tana leko kai sai duk
wurin ya haske, in ka dube ta sai ka yi tsammani ba ta cin abinci
don ba alamar ciki. Jikin nan nata kuwa na rantse har da
girmanka, yallabai, kamar in ka duba za ka ga bargo. Hancirta
116
ko sai ka ce ita ta yi wa kanta. In da ka dubi idanunta sai ka rantse
da Allah ba ta kifitawa, Gashi koMusa ya ce, "Kai, ya isa hakanan. Ci gaba da labari, ka ji ana
kirana gida."
Aku ya ce, "Ina zuwa." Ya yi ta tsawaita shi:
Dan Sarkin nan ya ta da kai, ya dube ta tun daga kasa har
sama, sai ya ce a ransa, "An ce dan Adam duk bai cika goma ba,
to, yau ga wadda ta kai goma sha biyu."
Ya kara dubanta ya ce, "Yam mata, daga ina?"
Ta ce, "Daga Waila Fadama. Mun zo biki ne nan jiya, yanzu
kuwa da azaharin nan za mu koma."
Dan Sarki ya yi mamaki, ya ce, "A Waila Fadama? Wane gida
ki ke kuwa har ban sani ba?"
Ta ce, "Nan gidan mai garin. Ai ni ce babbar 'yarsa. Ba na fita
ne, daga biki sai salla, shi ya sa ba ka san ni ba. Amma ka ga, ni
kuwa na san ka. Ko kai ma ba ka rasa jin labarin Nana Yauki ta
Waila Fadama ba."
Dan Sarki ya yi shiru, ya ce, "Wallahi kuwa, na ji ana
labarinta."
Та се, "To, ai ni ce."
Da dan Sarkin ya ji haka sai ya takale ta da maganar aure, ya
ga alamar lalle tana sonsa. Wancan mijin da za a ba ta wai dattijo
ne mai gemu, ita kuwa ta ce ba ta auren mai gemu.
Bayan sun shirya da ita a nan sai ta tafi. Ya dauki buta a
masallaci ya yi alwala, ya shiga ya yi salla. Da yai sallama, ya yi
addu'a ga Fiyayyen taliki ya nufa Allah ya sa ya auri wannan
yarinya. Don dokin bukatar auren yarinyan nan har ya yi subul da
baka ya ce wai in Allah ya nufa ya aure ta ya kashe kansa don
murna.
Bayan ya fito daga masallaci sai ya tarad da mai garin ya kawo
masa sauka. Suka gaisa, ya hau, suka mika da baransa. Suka bi
Sarki har suka iske su. Yana tafe yana ba baran nan labarin
yarinyar.
Da aka kare kewayar kasa aka koma gida. Sai dan Sarkin nan
ya gaya wa Wazari yana son su neman masa 'yar Sarkin Waila
Fadama da aure. Waziri ya gaya wa Sarki.
Aka neman masa, aka ba shi. Aka yi biki aka kare.
Bayan sun yi kamar shekara uku da auren, sai ran nan Nana ca
ce tana son mijin ya raka ta ta gano gida. Dan Sarki ya gaya wa
ubansa, uban ya yarda. Ya sa wani babban bawansa ya raka su,
aka yi musu shiri, suka hau rakuma suka tafi.
Suna cikin tafiya har suka kai garin da dan Sarkin ya fara ganin
Nana, suka yi zancen aure, suka tsaya kusa da masallacin, don ya
117
yi alwala ya yi sallar azahar. Ko da ya shiga ya gama salla zai fara
tasbaha, sai ya ji kamar daga bisa an ce masa, "Ina alkawarin da
ka dauka, da ka ce in Allah ya nufa ka auri Nana za ka kashe
kanka don murna da godiya ga Ubangiji?"
Da dan Sarki ya ji haka, sai ya tuna da alkawarin nan da ya yi.
Ya duba gabas, ya duba yamma, bai ga mai magana da shi ba, sai
jikinša ya dauki rawa, ya yi salati, ya ce, "Lalle baki shi kan yanka
wuya!" Sai ya zare takobi, nan ya fille kansa. Ya fadi ya mutu.
Da aku ya kawo nan sai suka
ji assalatu. Wani daga cikin
bayin Waziri ya yi maza ya sake
zuwa ya durkusa gaban Musa,
ya ce, "Ana kiranka maza maza
ciki."
Musa ya ce, "Haba, su sai su
dami mutum da kira. Ina kika ga
zan iya tashi ban ji karshen wannan labari mai dadi ba? In wani
abu a ke so, Sarkin Gida, je ka ka gani."
Da bawan nan ya ga Sarkin Gida zai biyo shi sai ya ce, "A'a
zauna abinka, Sarkin Gida, shi a ke nema. In ba ya zuwa, bari in
je in gaya musu." Sai ya koma ya gaya wa 'yan'uwansa, suka yi
waje da sauri, suna wa juna barka da Sarkin Gida bai biyo ba, da
yau sun bakunci lahira. Suka tafi suka gaya wa Waziri abin da ya
faru. Waziri ya ce ku koma su sake kokari, zai kara musu fam
goma goma. Suka sake shiga irin ta maza, suka komo. Duk gari
an tashi, har rana ta kunno, aku kuwa sai jan labarinsa, ya ke yi:
Da Nana ta ga ya dade bai fito ba, sai ta ce wa bawan nan ya
shiga ya gani wane irin dogon wurdi ya kama, har yanzu bai gama
ba. Da shigarsa sai ya tarad da shi kwance male-male cikin jini, ba
kai, ga tokobi can gefe yashe. Ya dafe kai, ya yi salati, ya се,
"Yanzu in na fita na fadi abin da ya faru, lalle za a ce ni na kashe
shi, Ban ga wata hanya ba sai in kashe kaina nan tare da shi, in an
ga haka a san lalle sai da na yi kokarina har na kasa, abin ya faru
haka." Sai ya dauki takobin nan ya fille kansa. Ya fadi gefe daya
ya mutu.
Nana tana waje tana jira. Shiru shiru, ba ta ga wani ya fito ba,
ta ce, "Kai, yau fa ga inda na yi ma'aikin kibiya. Abin nan lafiya
dai?"
Ta kara hakuri dai har la'asar ta yi sakaliya, sa'an nan ta cе,
"Ko da mata ba sa shiga masallaci, lalle ni in je in ga abin da ya
auku."
Sai ta sauka, ta kutsa kai cikin masallaci. Da shigarta sai ta ga
mijinta da bawansa duk ba kawuna. Ta ja da baya, ta yi nan ta yi
118
nan, ta fadi ta yi ta kuka. Da ta ga dai kuka ba ya magani, sai ta
dauki takobi, ta ce, "Bari ni ma dai in kashe kaina, in huta da
wannan bakin ciki, raina dai ba shi da amfani gare ni muddin
mijin nan nawa ba ya numfashi."
Ta cira takobi za ta sare kanta, sai ta ji an ce, "Tsaya. Dauki
kawunansu ki lillika musu, duk sai su tashi."
Ta duba gabas, ta duba yamma, ba ta ga wanda ya yi mata
magana ba. Sai ta tashi da rawar jiki, ta dauki kawunan ta lillika
jikunansu.
Ashe cikin dokin ta ga mijinta ya tashi har ta kidima ta dauki
kan dan Sarki ta lika wa jikin bawan, ta dauki kan bawa ta lika
wa jikin dan Sarki. Sai suka tashi, dan Sarki da kan bawa, bawa
da kan dan Sarki! Kowane da mikewarsa sai ya rungume ta, ya ce
matarsa ce.
To, jama'a, wa kuka gani ke da mata?
Bayi suka tashi da gardama haya haya, haya haya, wadansu na
119
cewa mata ta kan dan Sarki ce, wadansu na cewa a'a, mata ta
gangar jiki ce. Suna cikin gardamar, ga bayin Waziri tsaye bakin
zaure, ba wanda ya san abin da su ke jira sai aku. Sai aka ji
tambura Sarki ya tinkaro. Kafin a yi haka, kofar fada ta fara
daukar 'yam bushara.
Bayin Waziri da suka ga ba dama, suka koma suka gaya wa
Waziri, ya yi ta cizon hannu don bakin ciki. Jim kadan Sarki ya
kawo, Mahmudu na gaba maroka sun daho shi, sai kirari a ke
masa, ana yi masa waka.
Mahmudu, jimre ka dau himma,
Sai an gwada za a san babba.
Zama ga daki na raggo ne.
Wan Musa, taso mu je gaba.
Mai son fada, duk ya zo nana,
Gun Mahmudu, yanzu ya bar wasa.
Sinari bana sun tabo wahala,
Wan Musa Allah ya jaya ma!
Sakaci da tsoro ka yashe su,
Duniyag ga ba tai mai wauta.
Sinari sun tuba, sun bi ka,
Sarkinsu ya zo, ka gafarta.
Kyaun saurayi duk ya dau mashi,
Don shi da mata a bambanta.
Ayyururui! Mutane, mu dau guda,
Mahmudu da mai kamar baba.
Allah ka dube mu kai rahama,.
Allah ka dube mu kai rahama.
Allah ka dube mu kai rahama,
Ka ji kan mahaifa, mu ce amin!
Da suka iso duk gari aka dauki alo alo. Musa ya tafi ya taryi
Mahmudu a kofar gida, ya rungume shi, suka yi ta murna. Ya
tambaye shi kwana nawa ya yi yana jiyya, ya ce shi ko kaya ba ta
taba sukarsa ba tun fitarsa, balle ya yi jiyya. Musa ya yi ta
mamaki. Ya tambaye shi batun takardar da ya sha yiwowa, ya се
shi bai aiko kowa ba. Musa ya tafi dauko takarda, ya tarar ba ko
daya, ashe duk aku ya kwashe su ya boye.
Waziri ya zo yana 'yan dararraku, wai shi yana murna. Da aka
natsa, aku ya ce wa Musa, "Na ji kana neman takardun da
Mahmudu ya aiko maka sa'ad da su ke wajen yaki, ai suna nan na
ajiye maka." Ya tafi ya dauko ya kawo musu, suka yi ta
karantawa suna tu'ajjibi, suka boye takardun suka kyale.
Da gari ya waye, sai suka dauki takardun nan suka kai wa
120
Sarki. Ya duba, ya ce, "Wańnan ai hannun Waziri ne."
Mahmudu ya ce, "Hannun Waziri! Karanta ta ka ji."
Sarki ya karanta takarda, sai ya rike baki, ya ce, "Me ya ke
nufi da wadannan?" Ya juya ga Musa ya tambaye shi yadda aka
fara, har aka aiko masa da wadannan takardu.
Musa ya ce shi bai san abin da a ke ciki ba, tsammani ya ke
Mahmudu ke aiko da su. Ya kwashe abin da aka fara aikowa, da
dukan abubuwan da suka auku, da yadda aku ya yi ta rudinsa da
labaru har bai sami fita ba, duk ya fada wa Sarki.
Da Sarki ya ji haka, ya ce, "Ba shakka akwai magana. A kira
aku." Nan da nan aka zo da shi, Sarki ya tambaye shi. Aku ya
zauna ya kwashe yadda aka yi duka har da abin da suka yi da
Waziri sa'ad da ya aiko a je da shi, da labarin bayin nan da a ke
aikowa suna yiwo shirin mata suna zuwa, da abin da ya faru
daren da Sarki zai dawo, har ya są suka komo cikin bayin da aka
bari tsaro ya rika ba su labari don kada su yi barci, da yadda ya yi
ta fama da Musa don kada ya fita, duk ya fadi.
Da Sarki ya ji wannan abu, sai hawaye suka zubo masa don
tausayin aku, ya dauke shi ya rungume, yana cewa, Yaya za mu yi
mu fito wa wannan al'amari?"
Aku ya ce, "Duk wadanda a ke aikowa, ko ina suka shiga, in
na gan su na gane su. Bari in kewaya wajen gidan Waziri in na ga
daya daga cikinsu a kira shi ya zo, in an matsa masa ya fadi abin
da suka yi niyya. Da zan sami ganin wata tsohuwa da ta fara
zuwa, da ta fi bayyana abin sosai." Sai wani bawa ya sa shi a
wuya, suka yi ta yawo unguwar Waziri, da wadansu katta uku
kuma suna biye. Suna kawowa kofar wata 'yar rusasshiyar
bukka, sai aku ya leka cikin bukkar, ya ce, "Ga ta!"
Kattan nan da ke biye suka kutsa kai ciki, suka jawo ta, suka
iza keyarta har gaban Sarki. Da Musa ya gan ta ya ce, "I, lalle ko
ita ce, wannan aku abin nasa sai a yi shiru."
Sarki ya tambaye ta abin da Waziri ya tashi kullawa game da
Musa. Tsohuwa ta gigice, ta ce, "Iye, na'am! Allah ya ba ka
nasara, wallahi tilasta ni ya yi."
Mahmudu ya mike, ya dube ta ya kashe ta da mari, ya cе,
"Sarki ke tambayarki, ki gaya masa abin da aka tilasta ki yi."
Tsohuwa ta durkusa, ta fede wa Sarki biri har wutsiya. Da
Sarki ya ji haka sai ya aika duk dogarawansa suka zo ya ce, "Ku
jeku kamo mini Waziri!" Dogarawa suka ruga.
To, ashe tun sa'ad da aka kama tsohuwań nan wani ya tafi
wurin Waziri, ya ce, "Ranka ya dade, na ga wadansu bayin Sarki
guda uku da wani aku sun zo sun kama tsohuwar baiwarka ta nan
bayan gida, ko lafiya?"
121
Da Waziri ya ji haka, sai ya ce, "Lafiya mana." Bai sake wata
magana ba, sai ya shiga gida, ya sa aka daura masa sirdi, ko
rawani bai tsaya nema ba, balle bara. Sai ya hau, ya sulale ta
bayan gida ya fita gari, ba wanda ya gan shi.
Da dogarwa suka zo, suka fada cikin gida suka tarad da
Jakadiya, suka ce, "Ina Waziri?"
Jakadiya ta ce, "Lafiya, har cikin gida ba sallama?"
Dogarawa suka iza ta, suka ce, "Je ki, ki yi mana iso."
Jakadiya ta shiga cikin gida. Jim kadan ta fito, ta ce, "Ai ba ya
nan." Dogarawa suna tsammani karya ta ke yi suka bazu cikin
gida, wadansu suka tsare kofar zaure. Da suka yi nema ba su
same shi ba, suka kama duk bayin gidan suka kai wa Sarki, suka
ce ba su ga Waziri ba.
Sarki ya ce, "Ya gudu ne." Ya sa 'Yan Doka su hau su bazu
ko'ina, duk inda suka same shi su kamo shi.
Aku ya dubi bayin nan na Waziri da aka zo da su, ya се,
"Ranka ya dade, ga ko shaidu da suka san abin da aka yi."
Sarki ya ce, "Ka san su?"
Aku ya ce, "Na san bakwai daga cikinsu, har ma ga wanda aka
aika gun Sarkin Sinari."
Sarki ya ce, "To, nuna mini su."
Aku ya tashi ya ce wa wani dogari, "Da wannan da wannan,
kai su nan. Wadannan, ku ku komo nan. Kai, wancan da ke noke
kai, komo cikin wadannan." Ya dubi Sarki, ya ce, "Ga su.
Wadannan, su aka ce su boye nan kofar gida in Musa ya fito su
kashe shi. Wadannan, su suka wo shirin mata suka zo
shekaranjiya, daren da za ka dawo. Wannan ko," (ya nuna
Barakai) "shi ne babban munafukin, shi aka fara aika wurin.
Sarkin Sinari ya nuna musu hanya. Shi kuma ne ya, shigo cikin
gida bayan tsohuwan nan."
Da bayin nan suka ji haka sai suka dauka. "Wallahi, karya ya
ke yi. Allah ya ba ka nasara, mun rantse har da rawaninka ba mu
taba shigowa nan ba."
Sarki ya dubi dogarawa, ya ce, "Ku tambaye su."
Dogarawa suka same su da duka, suna ihu. Sai Barakai ya се,
"Ni zan fadi gaskiya, na sai da raina don ubangijina ya yaba, ban
sami kome ba sai duka, nan kuma in zo haka?" Sai ya kwashe
duk al'amarin ya gaya wa Sarki. Sauran da suka ga ba dama, su
ma suka faďi gaskiya. Sarki ya sa aka daure su cikin gidansa.
Aka kwana biyu, rana ta uku da azahar sai ga 'Yan Doka sun
zo da Waziri, sun kamo shi can kan iyaka, ya kusa ketare kasa, ya
nufi Sinari. Da aka zaunad da shi gaban Sarki, sai ya bata fuska,
ya tashi da fada ya dubi Sarki yana cewa, "Na mene ne za a aika
122
'Yan Doka su kama ni, ban ci kayan kowa ba?"
Sarki ya tashi da mamaki, yana tafa hannu yana cewa, "A'a!
Ashe kamo ka suka yi?"
Waziri ya harari 'Yan Doka, ya ce, "Kamo ni suka yi mana."
Sarki ya ce, "Ni ban ce su kamo ka ba, cewa na yi su kira ka, in
ji ko lafiya, don tun shekaranjiya waccan rabona da ganinka.
Da Waziri ya ji maganar lumana sai ya ce a ransa, "A'a! Ashe
da ma asirina bai tonu ba na ke son tona kaina a wofi. Da ma na
san Sarkin nan gabo ne, ba ya gane kome. Kuma ko ma ba wawa
ba ne, irin makircina ai ba mutum duka zai gane shi ba." Sai ya
ce, "Af, ashe Shamakina bai gaya maka ba?" Ai na tafi ganin
wata goggona ce da aka aiko mini ba ta lafiya. Amma dai, Allah
ya ba ka nasara, 'Yan Dokan nan sun karya mini irli."
Sarki ya ce, "Sai ka yi hakuri da su. Da ma ina gaya maka
sakarkaru ne, kai ke cewa suna da kirki."
Waziri ya harari 'Yan Doka, ya ce, "Na rantse har da
girmanka, ba na iya yafe musu, tun da suka ci zarafina haka. Su
duk sai a daure su yanzu. Ko mahaukaci ai ya san abin da ya
kamata.
Sarki ya ce, "Ai kai ne da mulki, sai ka yi abin da ka ga dama
da su. Amma bari in tambaye ka abin da ya sa na kira ka tukun.
Tun da na dawo ban sami damar tambayarka wani abu ba game
da gidana da na bar maka amana."
Waziri ya ce a ransa. "A'a! Ka ji tsohon banza da wata irin
tambaya." Sai ya dube shi, ya ce, "Ka tarad da wani abin tashin
hankali ne? Ai ni ban yi wasa da gidan nan ba, da kaina na ke
fitowa da tsakad dare in kewaya."
Sarki ya ce, "Na san haka. Amma wadansu takardu ne aku
ya nuna mini wadanda ban gane kansu ba." Ya dubi aku, ya се,
"Je ka, kawo su."
Aku ya tashi ya kawo su, ya zube gaban Sarki.
Da Waziri ya ga takardun nan, sai cikinsa ya ba da kulululu. Ya
dauke su yana budawa, yana dariya, yana cewa, "Wani ne ke
kwaikwayon hannuna. In ka bibiya ma shegen akun nan ne.
Amma, Allah ya ba ka nasara, ya kamata a tsawata masa, in zai
yi wasa, ya rika yi da tsarar-rakinsa su ungulu da jemage!" Ya
fashe da dariya, wai shi gwanin ba'a. Ya daga kai ya dubi Sarki,
ya ga shi bai yi dariya ba. Ya dubi Musa, ya ga shi ma hakanan.
Ya juya ga Mahmudu, ya ga kowa kinne. Aku ko ma, sai wasansa
ya ke yi da kwayar gyada, kamar bai ko ji abin da a ke fadi ba.
Sai idonsa ya raina fata.
Sarki ya dubi Sarkin Dogarai, ya ce, "A zo da mutanen nan."
Dogarawa suka duru da gudu cikin gidan Sarki, suka fito da
123
bayin nan na Waziri, kowanensu an bankare shi.
Da Waziri ya gan su sai gabansa ya fadi. Ya gyara zama, ya
duba gabas ya duba yamma, ya ga kowa ya kura masa ido.
Sarki ya dube shi, ya ce, "Ka san wadannan?"
Waziri ya ce, "Allah ya ba ka nasara, na tuba, na bi Allah, na
bi ka!"
Sarki ya ce, "Me ka yi mini na tuba? Cewa na yi ka san su?"
Waziri ya ce, "Ka ji kaina, ka yafe ni, ba don halina ba!"
Mutanen gari da aka tara suka yi ta duban Waziri, ba su san
abin da a ke ciki ba.
Mahmudu ya tashi, ya kashe Waziri da mari, ya ce, "Sarki ke
tambayarka, ka san su, ka dame shi da magiyar banza!"
Waziri ya dubi Barakai, ya ce, "Kai ne amintaccen bawana,
don Allah bayyana musu sosai, su san ba ni da laifi cikin wannan
al'amarin."
Barakai уa сe, "A'a! Ba ka da laifi? To, wa ke da shi?"
Makirin banza!" Ya gusa gaba, ya daga murya ya fadi duk
makirce-makircen da Waziri ya kulla game da Sarkin Sinari, da
game da Musa, bai rage kome ba.
Da mutane suka ji haka sai suka yi salati, suka taso wa Waziri
gaba daya kamar za su cinye shi danye, sai da dogarawa suka
shiga tsakani.
Sarki ya ce musu, "Ku dakata tukuna, ai ba a kare ba." Shi
kuma ya kwashe labarin yadda aku ne ya yi ta kokari ya kubutad
da su daga zama bayin Sarkin Sinari. Ya kuma gaya musu yadda
ya hana Musa ya fita waje, don ya gane abin da Waziri ke
kullawa. Da mutane suka ji haka sai ya ga kowanensu ya yi ta tafa
hannu, suka dubi aku, suka dubi Waziri. Sai suka fara dibar kura
za su yi masa ature, sai da Sarki ya tsawata.
Da suka dakata ya sake dubansu, ya ce, "To, jama'a, ku dubi
laifin nan na Waziri. Wanda ya aikata haka me ya kamata a yi
masa?""
Jama'a suka dauka gaba daya, "Sai a tsire shi! Da shi ai halaka
mu ya tashi yi, don Allah ya ki nufinsa. Da ma ba mai kaunarsa
garin, don mugun halinsa."
Sarki ya ce, "Na ji tasa. To, wadannan mutanen ko fa?"
Jama'a suka ce, "Su ma sai a tsire su, abin da ya ci Doma ai ba ya
barin Awai."
Musa ya ce, "A'a, tun da dai Allah ya ki aniyarsu, ya gama
fuskokimmu da Mahmudu lafiya, ga shi kuma Sarki ya ciwo
nasara, sai a yafe su."
Sarki ya ce, "Gaskiya ne, Musa. A kwance su." Aka sake su,
suka zo suka fadi gaban Sarki suka yi godiya, don da sun tabbata
124
za a kashe su. Mutane suka yi mamakin Sarki a kan wannan
nasiha.
Sa'an nan Sarki ya tashi tsaye, ya ce wa jama'a, "To, mun ga
inda wadannan tasu ta kwashe. Amma ina tambaya, shin don me
a ke yin Waziri?"
Jama'a suka ce, "Don ya rika taimakon Sarkin gari shawarа,
yana kwabe abin da zai cuci jama'a, ba kamar wannan ja'iri ba.
Allah ya kiyashe mu da halinka!"
Sarki ya ce, "In don haka ne, na nada wannan aku Wazarina.
Da shi zan rika shawara." Ya dubi mutane, ya ce, "Ko kuwa kun
ga bai isa a yi shawara da shi ba, don yana tsuntsu?"
Jama'a suka ce, "Wane irin isa? Wanda ya yi wadannan
abubuwa a ce bai isa ba? Wannan tsuntsu ai baiwa ce Ubangiji ya
nufe mu da ita, wa ke da ikon jayayya da nufin Allah? Mu dai
wallahi mun so, mun so."
a
Sarki ya dubi dogarai ya ce, "A kama Waziri, a daure shi cikin
jaka da ya bayar a sa Musa, a tafi da shi a jefa cikin kogi, yadda
ya yi niyyar yi wa Musa. Ku kuwa Sarakunana da makada, a tafi
kai Waziri Aku gidan Waziri, a fid da matansa na aure, sauran
ko duk abin da ke gidan an ba shi." Sarki ya tashi ya shiga gida.
Duk fada ta yamutse, wadansu suka nufi wajen da za a kashe
Waziri, wadansu suka bi sabon Waziri, ana ta goce ganguna da
kakaki. Aku kuwa yana bisa wata karaga ta zinariya, an sa laima,
katta na dauke da shi. Sai makada ke ta binsa suna waka:
Haba jama'amu, ku zo mu yi caffa,
Gunsa Waziri, mazajen aiki.
Masu rabo da yawa mai ba mu!
Sannu da sirdi, tsuntsun kirki!
Da ba don shi ba, masu fasaha,
Da yanzu da muna Sinari.
Ga wani sauna, don sakarci,
Ya yi butulci, ya bashe shi.
Ikon Allah wa zai ki shi?
Kowas saba yai jahilci.
Ka sai mana doki, baba Waziri,
Muje mu gwada wa mutan Sinari.
In ba donka ba, mai cika aiki,
Da wani mun ga irin bautanshi.
Masu fasaha, masu basira,
Mai tauhidi, Sarkin ilmi!
Ga ni a durkushe, na roke ka,
Ya Allahu ka gafarce ni.
125
Aka kai aku gidan Waziri, ya debi dawaki uku daga cikin
wadanda ya samu gidan Waziri, ya ba makada da suka rako shi.
Ya sa bayi su yi ta gadinsa. Aka yi ta shagalin sarauta har kwana
bakwai. Da aka natsa,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 12