gari ya waye ba mu
sani ba!" Sai ya tashi fuu ya shiga cikin gida. Tun safiyan nan kar
magariba bai sa ko loma bakinsa ba don bakin ciki.
Ko da wata ya fadi, tun ba a ko yi kiran sallar asuba ba sai ga
Musa ya shiryo. Ya zo ya ce wa aku, "Sai na dawo."
Aku ya ce, "Ka dawo lafiya." Ya sake duban Musa, ya ce,"А!
Kam ba Waziri ba, a dubi kakkarfan dan Sarki kamarka a ce za a
hana shi zuwa yaki? Shin halin Waziri wane iri ne?"
Musa ya ce, "Rabu da shi tsohon wofi! Ko da ya hana, ai ga shi
yanzu za ni yana gani."
Aku ya ce, "Tafi abinka, rabu da shi! Kome mutum ke
aikatawa dai ai, kul ba jima, kul ba dade, ya ga sakayya. Da
Allah ya sa ya ji labarin Hafaru da dansa, da ya rage wadansu
abubuwa."
Musa ya ce, "Wane labari ne na Hafaru da dansa? Gaya mini,
ko ni ma in karu.'"
Aku ya cе:
67
Abin Da Mutum YaShuka Shi Zai Girba, In Hairan
Hairan, In Sharran Sharran
Wata rana an yi wani mutum wanda ba shi da da, ba shi da jika.
Ya yi maganin duniyan nan don ya sami da, Allah bai nufa ba, y
gaji ya dangana.
Ran nan yana zaune a kofar gidansa, sai ya ga wani ya kama
dansa yana ta duka, ba ji ba gani, sai ya ce, "M, Allah mai girma!
Dubi wani Allah ya ba shi har yana bugu, ni kuwa ga shi ina nema
ruwa a jallo, Allah bai nufe ni da samu ba. In da ni Allah ya ba
wannan, kome rashin jin kansa, me zai sa in buge shi? Da da ya
yi jin kai, da kada ya yi, ai duk uwarsu daya, in ba dai don batan
basirar mutane ba."
A kwana a tashi, ran nan sai Allah ya ba matar mutumin nan
ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji. Aka yi suna, aka sa wa
yaron nan Hafaru. Yaron ya girma a sangarce, kome ya yi uban
ba ya ce masa kanzil. Ta kai dai fagen yaron nan ba ya jin kan
uban, balle ya taimake shi. Don son da uban nan ke yi wa dan har
abinci ma tare su ke ci, har ya kai ga aure ba su raba kwarya da
ubansa ba.
Da ubansa ya fara tsufa sai Hafaru ya rika kyamar cin abinci
da shi. In suna ci sai ya hana uban ya taba gabansa, yana cewa
wai uban ya faye kazanta, duk yana-barin majina a hanci, wai
kuma ga shi da yawan tari, yana zuba musu yawu a ciki. Uban dai
bai ce masa kome ba. Ana nan dai har ya kai ga fagen yana ci
hannu na rawa, na baka na fadowa cikin kwarya. Sai dan ya buga
masa tsawa, ya janye kwanon abincin, ya ce sai ya ci kana ya ba
uban.
Suna nan haka, sai ran nan Hafaru ya ce wai uban ba ya sude
kwarya, kullum sai ya bar kwano cakal, duk ya bata shi da yawu.
Saboda haka sai ya samar wau uban akushi, aka rika zuba masa
nasa abincin dabam. Ran nan yana ci garin makyarkyata sai ya
tuntsurad da dan akushin, tuwon ya zuba. Hafaru ya zo ya yi ta yi
masa fada, wai ya faye gidi-gidi. Saboda haka sai ya tafi kasuwa
ya sawo kwami irin na ban ruwan shanu, ya kawo gida ya rika
zuba wa uban abinci a ciki, ya ce, "Ture wannan kuma, mu
gani!"
68
Uban dai bai ce kome ba, sai in abin ya dame shi ya yi ta kuka
yana. cewa, "Wannan dai duk laifina ne da na ki kwabonsa tun
yana karami. Amma ba kome, Allah ya ba da mai rama mini."
A kwana a tashi, sai ran nan Allah ya ba matar Hafaru ciki, ta
haifi da namiji, aka sa masa suna Ishiye. Da ya kai shekara hudu
ya yi wayo, sai ya zama ba shi da wajen wasa sai tare da kakansa,
ko abinci ma tare su ke ci. Uban ya yi ya yi ya hana shi cin abinci
da kakan, yaro ya ki. Saboda yaron nan har aka rika sa wa
abincin tsohon mai da nama. Kome yaron nan ma ya samo sai ya
nufo kakansa.
Ana nan har Ishiye ya kai shekara shida, ran nan suka tafi gona
da uban, yana rike masa da goran ruwa. Da suka isa uban ya yi ta
noma, har rana ta yi tsaka, sai ga matarsa, uwar yaron, ta kawo
masa abinci, ya kakkabe hauyarsa, ya zo ya zauna yana ci, matar
kuwa ta zauna kusa da shi. Sai yaron ya dauki wani dan guntun
gatari da ke nan, ya shiga gona ya fara saran wata 'yar itaciya da
ke ciki, kwas, kwas, kwas. Da uban ya hanga ya gan shi, sai ya се,
"Kai me ka ke yi nan? Ajiye wannan abin banza, ka zo ka ci
abinci. Haka ku ke yi har ku sare 'yar kafarku, ku bar mutane da
jiyya."
Da yaron nan ya ji haka, sai ya ce wa uban, 'Ci naka, ka bar
mini nawa nan. Ni ina nan sai na sare itacen nan tukuna, ina so in
gyara rassan ne in yi maka dan kwami da shi, in kai gida in ajiye,
don in ka tsufa in rika zuba maka abinci a ciki!""
Da iyayen yaron nan suka ji haka, sai suka yi nadama, suka
rike baki suka ce, "Ashe gaskiya ne abin da mutane ke fadi, kome
ka shuka shi ka kan girba."
Daga nan Hafaru bai sake dukawa noma ba, sai ya tashi, suka
kwashi 'yan hauyoyinsu, suka iza keyar yaron nan har gida. Da
isarsu gida Hafaru ya kama' hannun dansa har wajen kakan.a
durkusa, ya gaya wa tsohon abin da yaro ya ce a gona, ya kuma
sake durkusawa ya roki tsohonsa gafara, yana ahi da kuka bisa ga
abubuwan da ya yi masa. Yaro na kallo, bai san abin da a ke yi
ba. Tsohon nan ya ce, "Mhm. Ai duk abin nan da aka yi, ni na ja.
Je ká, na gafarta maka duniya da lahira."
Hafaru ya tashi yana murna. Daga ran nan bai sake, tozarta
ubansa ba, har Allah ya nufa ya cika a hannunsa, suka rabu da
alheri. Kullum in Hafaru ya ga dan nan nasa, in ya tuna da
maganar da ya yi, sai ya rike baki ya ce, "Ya'yan zamani,
saninku ba sanin halinku ba!"
Da Musa ya ji aku ya kai karshen wannan labari, ya cе,
"Wannan labari naka gargadi ne mai amfani ga wanda ya ji shi."
Aku ya се, "Ва wannan kadai ba, duk labarin da na ke
69
bayarwa, in ka lura, ka ga haka ya ke. Ai ba muni ga mutum da
ya fi ya kai muddin mutane bai iya bakinsa ba. Ga wani karamin
misali nan na kunkuru da gauraki:
70
Fara Koyon Mulki Da Baki, Kafin Ka Koyi Mulki
Da Hannu
Wata rana wadansu gauraki guda biyu suka gane wani itacen
baure a bakin wani rafi. Kullum suka tashi sai su nufi can su hau,
su yi ta ci. Gindin bauren nan kuwa ashe akwai wani kunkuru.
Kullum idan gaurakin na cin baure, wadansu 'ya'yan su kan
kucce musu su fado kasa, Da kunkuru ya ga suna fado masa yana
ci, sai ya yi tsammani gaurakin nan ke ba shi kyauta, don suna
sonsa. Saboda haka, da ya ga alherin ya yi yawa, ran nan sai ya
daga kansa ya dubi gauraki, ya ce, "Kai 'yan'uwana, na gode!
Kullum dai na kan ga 'ya'yan bauren da ku ke sako mini. Abin
naku ya yi yawa, wallahi har kunyar godiya na ke yi. Allah dai ya
saka da alheri!"
Da gauraki suka ji haka, suka duba suka gan shi, sai suka gane
abin da ke aukuwa. Da har babbar za ta ce masa su ba a kan sonsu
bauren ke zuwa gare shi ba, sai karamar ta hana ta. Ta dubi
kunkuru ta ce, "Don mun ga kai ba ka iya hawowa, shi ya sa mu
da Allah ya ba fiffike mu ke taimakonka. Don dan wannan abu
kada ka sa wa kanka wani jin kunya ciki. Allah dai ya bar
zumunci."
Kunkuru ya ce, "Amin! Na ko yi godiya." Suka zauna kan
haka. Da abu kamar wasa, har ya zama aminci na gaskiya.
Gaurakin nan da sun zo da safe, ba abin da su ke fara yi sai sun
tambayi kwanan kunkuru tukun. Suka zauna, ba su son abin da
ya taba shi, shi kuma ba ya son abin da ya taba su.
Ana nan, bayan kamar wata guda baure ya kare, gauraki suka
koma neman kwadi da tana. Bayan kamar wata biyu kuma dan
sauran ruwan rafin ya kafe. Wurin ya koma sai ka ce dadai
duniya ruwa bai taba zama nan ba. Da gauraki suka ga haka, sai
suka yi šhawarar su tashi su sake wuri, don ba su iya zama sai
inda ke da danshi-danshi.
Ran nan har za su wuce, sai karamar ta ce, "Ya kamata mu je
mu sallami kunkuru, kada ya ga shiru hankalinsa ya tashi, ya yi
zaton wani abu ne ya same mu." Suka tashi, suka tafi wajen
kunkuru, suka gaya masa za su yi kaura.
71
Da kunkuru ya ji haka, sai ya ce, "Af, to, ai ba ku barina, sai
mu tafi tare. Abin da ya yi Goje, ai shi ya yi Kaura. Ni ina na ke
iya zama inda babu laima?"
Da gauraki suka ji haka, sai suka ce, "Yaya za ka yi ka bi mu,
alhali kuwa kai ba ka da fiffike?"
Kunkuru ya ce, "Sai ku dauke ni, in kun ga kwa iya kokarin
hakanan."
Babbar gaurakar ta ce, "Wa ka ke zato cikimmu zai iya daukar
kato kamarka? To, ce ma muna iyawa, ina za a kama, ga ka jiki
duk kwarya?""
Karamar ta ce, "Bar shi, mu ji tasa, watakila yana da dabara,
Kin san an ce mai rai ba ya rasa kokari."
Kunkuru ya ce, "I, ina kuwa da wata 'yar gurguwar dabara, in
kwa iya. Sai mu sami kara mai karfi kamar zira'i biyu, ni in cije
tsakiyar, ku kuma kowace ta kama gefe guda dá baki. Kun ga da
haka sai ku tashi da ni har inda za ku."
Babbar ta ce, "Wannan dabarar ban ga za ta yiwu ba ga
kamarka, mai surutu."
Karamar ta ce, "A'a, in ya ce dai ya iya kyalewa, ai sai mu
72
daúke shi." Ta tashi, ta tafi ta samo karan dawa mai karfi, ta
dauko, ta zo ta ajiye gaban kunkuru. Ta dube shi, ta ce, "To, don
Allah in ka kama, ban da yawan magana."
Kunkuru ya ce, "Haba, wannan ma sai an dankwafe ni kansa,
sai ka ce yaro? in yi surutu mana, in ina so!"
Gauraki suka ce, "To, madalla!" Suka kama kara suka tashi
da kunkuru yana cije.
Suna cikin tafiya, sai hanya ta daukè su ta bisan kasuwa. Suna
kaiwa tsakiyar, sai mutane suka daga kai suka hange su, suka ce
"Eho, eho, ku zo ku ga inda gauraki ke daukar kunkuru! Kai
jama'a, abin mamaki ba ya karewa nan duniya!"
Da kunkuru ya ji haka, sai ya fusata ya ce, "Kai, Allah ya tsine
idandunan nan naku mutane, da ba su iya ganin abu su kyale."
Bai gama fadin abin da ya ke nufi ba, sai da ya kawo ķasa kum.
Duk da karfin kokon san nan, ya haure, bai ko motsa ba.
Gauraki suka wuce abinsu suna bakin ciki, suna cewa "Wanda
duk bai iya mulki da bakinsa ba, lalle yana tare da halaka."
Musa ya saurara haka, sai ya
ji wani daga cikin bayin nan na
ta da 'yan'uwansa, gari ya waye.
Ya bata fuska. Aku ya ce, "Ai
ko yau ba ka yi zaman banza ba,
don na yi maka gargaďi."
Musa ya çe, "Gargado!"
Aku ya shiga shashatad da shi,
har ya 'ciwo kansa. Suka yini nan suna 'yan tade-tade.
Da rana ta fadi, lokacin fitar Musa ta yi, sai ya taho ya ce wa
aku, "Yau, don Allah ba ka kyale ni in wuce baki alaikum?"
Aku ya ce, "Sai ka dawo."
Musa ya ce, "Kai, yau wace rana ka kyale ni ba ka yi min wani
surutu ba!" Ya sa mabudi ya bude zaure na farko ya taka zai
shiga ya buda na biyu, aku ya biyo shi, ya ce "Yanzu wani babban
abu ya fado mini a rai. Kwanaki na bä ka maganin karfe, na
manta ban ba ka kau da bara ba. Ko kuwa ba ka so ka iya
gociya?"
Musa ya ce, "Ban iya gociya ba, in kau da baran na kusa ka
kawo mini. Ba wanda ya ki taimako."
Aku ya ce, "Wani kauci ne nan kusa, bari in fita in kawo
maka." Ya fita fir ta taga.
Musa ya ce, "In kana wa Allah, ka yi sauri!"
Aku ya ce, "Shi babba." Ya tafi ya sami wani lambu, ya yi ta
satar baure yana ci. Da ya koshi, ya ga kamar asalatu ta yi, ashe
farin wata ne, ya debo ganyen bauren ya taho, ya ce wa Musa,
73
"Ga shi, ka sami saki ka dfinke shi da shi, ka gama cikin
damarunka, ko ana ruwan kibau, ka tabbata ba dayar da za ta
same ka. Amma da sharadi guda, ya kamata ka koyi gociya,
domin kau da bara duk ba ta ci sai ana gamawa da 'yan zukezuke."
Musa ya ce, "To, madalla." Ya bude zaure na biyu, aku ya
dubi gabas yà gani ko asalatu ya yi, ya ga ashe bai yi ba, farin
wata ne ya rudo shi ya dawo da wuri. Sai ya tashi da 'yan tsalletsalle yana bin Musa, ya tarad da shi har ya bude zaure na uku, ya
ce, "Bari in gaya maka wani labari mai daďi. Wata rana akwai
دو wadansu 'yam makaranta
Musa ya ce, "Kai, tafi ka ba ni wuri! Ni na gaji da labarun nan
naka." Ya bude zaure na hudu.
Aku ya yi tsalle ya bi shi, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni dai
wallahi kana kayatad da ni, tun da ba ka wuce maganar iyayenka
ba. Dubi abin da Sarki ya gargade ka da ni, ka ga har Allah ya
kawo mu rana wa ta jiya kana nan rike da abin nan da ya се."
Musa ya waiwayo ya ce, "Rana wa ta jiya kadai, ranar yau
fa?"
Aku ya ce, "Ai kullum kana rike, da ma dai ai-."
74
Babban Mugun Abu Gun Da, Ya Yi
Fushi Da Iyayensa
Ina tsammani ban taba gaya maka ba, wata rana aka yi wa
wadansu 'yam makaranta jarrabawa. Daga cikinsu akwai dan
limamin garin, ana kiransa Ilu. Ba ya kula da aiki ko kaďan.
Kullum in ana koya musu aiki, shi sai ya yi ta wasa. Saboda
haka da aka yi jarrabawan nan bai ci kome ba. Sai ya sami
sifiri. Malaminsa ya yi fushi kwarai da ya ga haka, ga yaro dam
manyan mutane ya lalace. Saboda haka ya je ya gaya wa liman
abin da dansa ke ciki, don kada nan gaba a kore shi, uban ya bata
rai.
Da aka gaya wa uban, sai ya kira shi wai ya yi masa fada ya
kara kokari. Ya zazzage shi yana cewa in bai yi kokari ya yi
karatu ba, ba shi da wani amfani, sai fa ya je ya yi tallan tsire.
Yaro ya tashi yana ta hushi, wai uban ya ce in bai yi kokari ba,
zai ba da shi ga mahauta ya je ya yi tallan tsire. Ya koma karamin
zauren gidan, ya zauna. Yana nan yana ciccika, lokacin cin abinci
ya yi, kanensa Ibrahim ya zo ya kira shi su je su ci. Sai Ilu ya dube
shi da hushi, ya ce, "Je ka, ci! Ni ban ci."
Ibrahim ya bushe da dariya, ya ce, "Kana tsammani wani ya
kula don ba ka ci abinci ba? Je ka, huta." Ya tafi ya gaya wa
iyayen.
Liman ya ce, "Fushi ya ke yi, don na yi masa fada? To, kyale
shi! Don cikinsa."
Matar ta ce, "Ya da ta ki auren Sarkin Noma ba?" Ko da ya
ke uwar ta ce haka, duk da wannan hankalinta na Wajen Ilu. Та
kaikaici idon liman, ta tafi wajensa tana rarrashi, ya ki cin abinci.
Ta yi ta yi, sai ya dube ta, ya ce, "Ina ruwanku da ni, ni da kuka
ce ba ni da amfani sai ga masu tsire? Ina kokarina, don malam ya
ki jinina ya zo ya ce ba na kokari. Na ko san duk ajin nan ba a
samun yaro goma gabana."
Sai uwar ta tashi, ta ce, "Bari mu je mu ajiye maka."
"Me za ku ajiye mini? Ni ko kun ajiye, ba na ci. Me za ku yi da
mai tallan tsire?"
Da liman ya duba, bai ga matar ba, sai ya yi tsammani tana
75
wurin Ilu ne, saboda haka ya sa baki ya kira Ilu, ya ce, "taso ka ci abinci, kada ka yi sakarci."
Ilu ya ce, "Ba sakarci na ke yi ba, karatu na ke yi. Kuma ni mai
tallan tsire, yaya zan ci abinci da ku?"
Liman ya ce, "Ho lalatacce, d'an banza, mai taurin kai! Allah
wadan yaron zamani!"
Ilu ya ce, "Na kuma zama dan banza, lalatacce, bayan da fari
ga ni bawan mahauta?"
Ibrahim ya dubi uban, ya ce, "Ya yi fushi ne, baba."
Ashe Ilu ya ji, sai ya ce, "Kai kuma me ya sa bakinka ciki? Cin
danko har da kaza?" Sai kuma fushi ya koma kan Ibrahim, ka
san da ma an ce zomo ba ya fushi da makashinsa sai maratayi. Ya
ce, "Wa ya tambaye shi ma ne, da ya sa bakinsa? Ka san Ibrahim
ya raina ni." Sai ya tashi, ya shiga dakinsu na kwana. Da zuwa
sai ya tarad da wandon Ibrahim bisa gadonsa, sai ya jeho shi
waje, ya ce, "Raini ke nan ya sa kazamin wandonsa bisa gadona,
ya sa mini kyaya." Ya haye gadonsa ya kwanta, yunwa kuwa ta
fara dafa shi.
Yana nan kwance, wai don ya fito sai Ibrahim ya zo ya ce masa,
"Ka yi bako."
Ilu ya harare shi, ya ce, "Fita, ba ni wuri!"
Ibrahim ya yi murmushi, ya ce, "Abokinka ne ya zo."
Ilu ya ce, "Na gaya maka ka tafi ka ba ni wuri tun da girma,
ko?"
Ibrahim ya wuce, yana cewa, "Na san dai yunwa ta sa ka
wannan hushi, ba kome ba."
Ashe fa gaskiyar Ibrahim. Ilu ya tashi ya rasa inda zai sa kansa
don yunwa. Ya yi shawara ya koma ya ce a ba shi abincin da aka
ajiye masa, ya ga in ya yi karaya haka a yi masa dariya. Saboda
haka ya jure dai. Can zuwa la'asar ya ji abin ba dama, sai ya
dauki wandonsa, ya sulale zai kai kasuwa, sai ya ji motsin ubansa
a zaure. Ya ga in ya gane zai ba shi kashi. Saboda haka ya komo
ya kurda ta kofar damfami, ya fita. Ya nufi kasuwa wajen 'yan
tsumma. Ya tarad da wani mai dinkin mashimfidi, ya ce masa
"Kana sayen wandona?"
Madinki ya karba ya duba, ya ce, "Kai, karbi abinka" kyallen
ai namuzu ne. Tir! Ko Ingila ba sayenka a ke ba, sai Turawa su
watsar sadaka. Amma to, nawa za ka sayar mini don in rika kara
wa jakina wajen laheru?"
Ilu ya ce, "Nawa za ka biya?"
Madinki ya ce, "Kwabo hudu. Ko ma na zura jiki ne?"
Ilu ya ce, "An ce in bai yi kwabo takwas ba, kada in bari."
Madinki ya bude baki kamar zai yi hamma, ya mika wa Ilu
76
wando, ya ce, "Lalle in ka kewaya a sami mai sayensa sule ma.
Duba shi, ai sabo ne."
Ilu ya lura ba'a ya ke yi masa, sai ya mika masa wando, ya ce,
"Kawo kuďi."
Aka mika masa awalaja, ya runtse a hannu, ya shiga kasuwa
neman abin da zai ci, Magariba ta kusa, kowa ya watse, bai sami
kome ba. Sai ya nufi tukubar tsire ya tsuguna, ya sa aka zare
masa wajiya ta kwabo huďu, ya ci ya ci har ya koshi. Ya nemi
ruwa ya sha. Ya tasam ma gida yana cewa, "Tun da aka zazzage
ni, sai na sayad da kayana duka na ci abinci. Ba na sake cin
abincinsu sai sun zo sun rarrashe ni."
Yana zuwa gida, sai ya tarad da fura mai zuma uwar ta kai
masa dakinsa. Ya bude, ya duba, ya diba kadan da ludayi ya
kurba, sai ya ji ta coin. Ya ce, "Yau ga ni ina son furan nan,
amma in na sha lalle a yi mini dariya." Amma bari in kurba
luddayi uku, na san dai ba a ganewa. Ya tsuguna ya sha. Ya gama
ke nan, sai ga kanen ya shigo, ya ce, "Ina ka tafi, ga Inna ta ce in
kawo maka fura?""
Ilu ya ce, "Ina ruwanka da in da na tafi? Me ka ba ni ajiya?
Dauki furarku, ba na sha. Ni sakarai, dan banza, me ruwanku da
ni? In je in mutu mana."
Ibrahim ya fita ke nan da fura, sai wajiya ta yi ta taso wa Ilu,
sai amaí. Nan da nan ciki ya murde shi, ya yi ta murde-murde bisa
gado yana kugi,
Da uwar ta ji, ta kira Ibrahim suka rugo su ga ko mene ne. Suka
tarad da shi sai amai ya ke yi, duk idanduna sun jujjuye, suka
tambaye shi abin da ya ci. Yà če, "Na-na-nama."
Nan da nan uban ya се a пеmo tsamiya. Uwar ta ruga. Ilu sai
kuka ya ke yi yana murde-murde, ya kasa kwance ya kasa tsaye.
Nan da nan uwar ta kawo, aka jika, aka dura masa ya sha. Sai ya
barke da zawo. Kafin lisha ya sami sauki. Gari na wayewa ya
warke sarai. Sai ya tafi wajen iyayen, ya roke su gafara, ya сe
daga yau ba ya sake yi musu musu. Aikin makaranta kuwa, su
saurari abin da zai faru in an sake yi musu jarrabawa. Daga ran
nan ya koma dan kirki, duk ajinsu aka rasa kamarsa.
In ka ki jin horon iyayenka, ka ji na Mahaliccinka.
Musa ýa duba, ya ga har rana
ta kunno, sai ya ce wa aku, "Ка
ga dai da zan yi tafiya, ka tsai da
ni a wofi, ga shi ka sa na
makara." Ya koma ciki da
hushi. Duk yinin nan ya hana a
kawo wa aku wani abinci sabo.
רר
Da rana ta fadi, asuba ta yi, aku ya kura ido hanyar da Musa ke
fitowa. Ko da ya hango shi tafe da takobi tsirara, sai ya ce,
"Daukan ni mu tafi tare."
Musa ya harare shi, ya ce, "Ka yi mini amfanin me wurin yaki,
dan tsurut da kai haka? An ce maka labari a ke so?""
Aku ya ce, "Ko ba don labari ba, dabara aì ita ce yaki, ba karfi
ba. Ina zaton ba ka taba jin labarin yadda bunsuru ya yi dabara
har ya kori kura ya gaje gidanta ba ne?"
78
Banza Girman Mahaukaci, Karamin Mai
Wayo Ya Fi Shi
A cikin wani daji akwai wata kura wadda ke da gidanta mai kyau
kwarai da gaske a wani kogo, ta kawata shi da kyau, babu abin da
babu a ciki.
Sai kuran nan ta sami wani biri, ta sa shi ya rika tsaron gidan
nan kullum in ba ta nan, don kada wani abu ya fasa in ba kowa,
ko kuwa a zo a yi mata sata. Kullum birin nan ba ya rabuwa da
gidan. Ran nan yana zaune sai wani bunsuru da mata tasa da
'ya'yansu uku suka fado nan gidan. Dalilin zuwansu kuwa, kiwo
suka tafi har dare ya yi musu, suka rasa hanyar komawa gari,
suna kuwa tsoron kada su gamu da zaki ko kura.
Da biri ya gan su, sai ya ce, "Kai daga ina? Su wane ne ku? Nan
fa gidan kura ne, ku rufa wa kanku asiri ku koma, in ba haka ba
kuwa, in je yanzu in gaya mata ta zo ta hau doronku dai dai."
Akuya ta dubi bunsuru, ta ce, "Maigida, yau fa abin da mu ke
gudu ya auku, mun kawo kammu ga halaka. Da ma mun sani mu
dangana da ciyawar da ubangijimmu ya ke zuba mana kullum
dare! Ga shi kwadayin son danya ya sa mun kawo kammu a
mahalaka."
Biri ya dubi bunsuru, ya ce, "Ni fa na gaya muku ku gudu, in
ba haka ba, yanzu in tafi in gaya mata."
Bunsuru ya harari biri, ya ce, "Mutumin banza, wannan gidan
tun daga kakan kakana, Sarkin Masu, na gaje shi. Ba wanda zai
kwace shi daga gare ni duk fadin duniyan nan. Je ka, gaya mata
mana, ina nan ina jiranta."
Biri ya zabura, ya tafi wurin kura. Bayan ya tafi akuya ta ce wa
bunsuru, "Mu yi ta kammu, kafin kura ta zo!"
Bunsuru ya ce, "Ke ar, mara hankali! Ai yanzu idan muka
nuna alamar mun ji tsoro mun kade, ba mu da wurin tsira ko mun
gudu. Idan mun ga kura tafe, sai ki ce wa 'ya'yammu su yi kuka
gaba daya, in na tambaye ki dalilin kukansu, ki ce suna jin yunwa
ne, wai suna son naman kura su ci, ba su cin na jiya, ya rube."
Akuya ta amsa ta ce, "To, amma dai ni ban sa wannan za ta fid
da mu bа."
79
Da biri ya isa wajen kura ya ce mata, "Ga wani abu nan da
iyalinsa, ya zo ya ce wai gidan nan ba naki ba ne, wai na kakan
kakansa ne, Sarkin Masu. Na ce ya gudu, kada ki zo ki cinye su.
Ya ce ke din me? Ba irin zagin da bai yi miki ba."
Kura ta ce, "Ka san shi?"
Biri ya ce, "A'a. Amma barewa ta ce wai bunsuru ne."
Kura ta ce, "Ko da ban gan shi ba, lalle ba bunsuru ba ne.
Bunsuru ba yadda zai yi wannan aiki. Yaya kamarsa ta ke? Ya kai
girmana?"
Biri ya ce, "Ko kusa, ni ma kadan ya fi ni. Wani irin launi gare
shi ja ja, da gasusuwa zaro-zaro, da 'yan kofatai kamar na
barewa."
Kura ta ce, "In ka tabbata bai fi ni karfi ba, mu je mu gan su.
Shin su nawa ne?"
Biri ya ce, "Har da 'ya'yansu su biyar ne.duka."
Kura ta ce, "Nawa?
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 12