An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Magana
Jari Ce
Littafi Na Farko
Magana Jari Ce 1
Yaro Ba Da Kudi
A Gaya Maka!
Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E., C.O.N.
-Kámfanin Littafai Na Nijeriya Ta Arewa
ZARIA.
Mallaka (M Kamfanin Gaskiya Zaria 1945
Ba a yarda a kwafi wannan Littafi ba, dukkansa ko sashinsa
don bugawa ko sa wa a kowace irin na'ura, sai an samu izini a
rubuce.
An Fara Bugawa 1937,
An sake Bugawa Sau 17, daga 1954 - 1985.
Gyaran Farko 1993, 1997. 1998
An Shirya a
Kamfanin Littafai Na Nijeriya Ta Arewa
Lambar Gidan Waya 412,
Kamfanin Gaskiya, Zaria.
ISBN: 978-169-057-7
An Buga Shi a
Kamfanin Gaskiya, Zaria
Labarun Da Ke Ciki
Gabatarwa Shafi
Labarin Sahoro Da Sahorama
Magana Jari Ce
Labarin Wani Bororo Da Dan Zaki
Banza Ta Kori Wofi
Sauna Kira Mana Shashasha, In Ka Ga Sakarai Ku
Taho Tare
Labarin Auta Dan Sarkin Noma Da Naman Jeji
Labarin Wani Bakauye Da Wadansu 'Yan Birni
1
13
18
22
26
29
32
Labarin Wani Aku Da Matar Ubangidansa 37
Labarin Sarkin Zairana Da Sarkin Bokaye Gara
Labarin Kyanwa Da Bera
40
44
Labarin Wani Jaki Da Sa 49
Yadda Muka Yi Da Ubangijina Ojo 53
In Ajali Ya Yi Kira, Ko Babu Ciwo A Je 57
Labarin Wadansu Abokai Su Uku 61
Munafuncin Dodo, Yakan Ci Mai Shi 65
Abin Da Mutum Ya Shuka Shi Zai Girba, In
Hairan Hairan, In Sharran Sharran
68
Fara Koyon Mulki Da Baki, Kafin Ka Koyi Mulki
Da Hannu
71
Babban Mugun Abu Gun Da Ya Yi Hushi Da
Iyayensa
75
Banza Girman Mahaukaci, Karamin Mai Wayo
Ya Fi Shi
79
Labarin Sarkin Busa 62
Kowa Ya Yi Kokarin Ya Sami Fiye Da Abin Da
Allah Ya Nufe Shi Da Shi, Ya Ja Wa Kansa
Lalacewa
Labarin Annabi Sulaimanu
Ba Wahalalle Sai Mai Kwadayi
Saurin Fushi Shi Ke Kawo Da Na Sani
Raina Kama Ka Ga Gayya
Labarin Shaihu Mujaddadi Dan Hodiyo Da
Umaru Mu'Alkamu
Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Madugu
Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Wani Malami
Sauri Ya Haifi Nawa
88
94
96
99
103
107
110
113
116
GABATARWA
Wannan littafi, Magana Jari Ce, 1, yana cikin littattafai guda uku
da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa
a Zariya a shekarar 1936. Dalilin zaßo shi kuwa ya rubuta wadannan littattafai shi ne ya shiga wata gasa ta rubutun littafi a shekarar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'.
An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D
(Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin Kagara sa'an nan
tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a
Makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22
ya rubuta 'Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen kaga labari mai
ma'ana ya sa Dr. R. M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya
roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya.
Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta
wasu littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin
1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo
da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar
farko ta Arewa. Shi ne ma ya rada mata suna 'Gaskiya Ta Fi Kwabo'
aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.
Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta
wani littafi a lokacin 'Yakin Duniya Na Biyu' watau 'Yakin Hitila'
da ya ba suna 'Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da labarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa ta Yamma
zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943.
Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne 'Tarihin
Annabi da na Halifofi' wanda aka fara buga shi a shekara 1957
lokacin nan yana shugaban Hukumar Daukar Ma'aikata ta Nijeriya ta Arewa.
Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nadawa Kwamishinan
Jin Kararakin Jama'a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana
kiranta Arewa ta Tsakiya. Ya rasu yana da shekara 70 a duniya
ranar Juma'a 19 ga watan Yuni, 1981.
Alhaji Abubakar Imam ya rika cewa wannan aiki da ya yi, na
talifin 'Magana Jari Ce' ya yi masa amfani ainun. Ya kan ce wannan aiki shi ne ya ba shi damar zama tare da mashahurin Baturen
nan na talifin Hausa, Dr. R. M. East, O.B.E. Ya ce daga gare shi.
ne ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi.
Abin mamaki, shi kuma wannan Bature, Dr. East O.B.E., a
wajen 'Mukaddamar' da ya yi da Turanci tun farkon buga 'Magana Jari Ce', ga abin da ya ce: 'Muna godiya ga En'e ta Katsina,
saboda taimakonsu, da hangen nesa da suka yi, har suka yarda,
suka ba mu aron Malam Abubakar Imam. Suka yarda, ya bar
aikinsa, na koyad da Turanci a Midil ta Katsina, ya zo nan
Zariya, ya yi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadannan littattafai a cikin harshensa.
'Iyakar abin da mu ma'aikatan wannan ofis muka yi, na game
da talifin wadannan littattafai, shi ne aiki irin na ofis, na shirya
al'amuran, yadda suka kai har aka buga su. Ban da wannan sai
kuma taimakonsa da muka yi na tattara masa littattafai iri iri,
don ko zai kwaikwayi wani samfur. Sai fa,kuma wajen shiryawa
bayan da ya rubuta.
'Kai, in dai'har muna da wani abin da za mu yi kirari mun yi,
game da talifin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu
kawai, shi ne yadda muka yi har muka binciko wannan malamin
talifi'.
1982 N.N.P.C.
Magana Jari Ce
A wani gari a kasashen gabas an
yi wani babban Sarki wanda a ke
kira Abdurrahman dan Alhaji.
Rabonka da samun ko labarin
mai arziki irinsa tun Dankaruna,
mutum ko gidansa ya shiga ya ga
yadda aka kawata shi, ya ga
kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya rike baki kawai, don abin
ya fi gaban mamaki. Zaurukan gidan nan kuwa-kai! In ma
mutum ya ce zai tsaya ya bayyana arzikin Sarki Abdurrahman ga
wadanda ba su san abin da a ke kira duniya ba, sai su yi tsammani
shara ta yake yi.
Amma duk yawan arzikin Sarkin nan sai ya zama na banza,
don ba shi da 'ya'ya, ba shi da kane, ba shi da wa. 'Ya daya kadai
gare shi, an ko yi mata aure, Saboda haka Sarkin nan ya zama ba
wani wanda zai gani ransa ya yi fari cikin fadan nan tasa duka. Ya
ga in ya mutu duk dukiyan nan sai a raba a ba matarsa da 'yarsa
kadai, abin da ya rage a sa baitulmali. Kuma sarautarsa sai wanda
Allah ya ba ya ci. In ya tuna da wannan, duk sai ni'imomin
duniyan nan da Allah ya ba shi su yi masa baki kirin.
Ana nan ran nan sai 'yan nan tasa ta haifi da namiji, aka yi
shagali, aka sa wa yaron Maiımudu. To, amma ko da ya ke Sarki
ya yi murna kwarai da ya sami jika, duk da haka murnarsa
ragaggiya ce domin dan mace ba ya gado, balle har a ce ya yi
sarautaа.
Yana nan cikin wannan bakin ciki, sai ran nan wani shaihun
malami ya zo ya ce masa, "Na yi mafarki jiya, an gaya mini da za
ka tara malamai arba'in su yi ta yi maka addu'a har kwana
arba'in, in Allah ya so za ka haihu."
Sarki ya yi murna da wannan mafarki, ya dauko kudi da riguna
zai ba malamin nan. Malamin ya ce shi ba kuďi suka kawo shi ba,
ya zo ne ya isad da umurni, ya yi sallàma, ya tafi.
Ranar ba ta sake juyowa ba sai da Sarki ya sa aka tara masa
1
manyan malamai guda arba'in na kasarsa, ya gaya musu abin da
ya ke so. Suka ce, "To, Allah ya karbi rokonmu!" Mutane suka
ce amin. Suka yi shiri, suka shiga masallaci, suka duka.
Ubangiji ya nufe su da katari, ya karbi rokonsu. Kwanan nan
arba'in ba su cika ba sai da matar Sarki ta sami ciki, bayan wata
tara ta haifi da namiji, wanda kyaunsa ba shi da iyaka. Shagalin
da aka yi cikin kasan nan, da farin cikin Sarki bisa ga wannan
al'amari, ku da kanku kun san ba shi yiwuwa a bayyana shi cikin
wannan dan karamin littafi. Aka dai, rada wa yaron nan suna
Musa. Watau tsakaninsu da jikan Sarki abin bai ko yi shekara ba.
Sarki kuwa ya dauki ransa ya kallafa bisa kan yaron nan. A ma
tsaya a kwantanta son da Sarki ke wa dan nan nasa, abin ya zama
kauyanci ke nan.
Kwanci tashi, bayan shekara biyu aka yaye yaron. Sarki kuma
ya aika aka kawo jikan nan nasa Mahmudu, aka yaye su gaba
daya, don su rika wasa tare. Suka tashi sai ka ce tagwaye, ba abin
da ke raba su.
Da duk abin nan burin Waziri,
tun da Sarkin nan ba shi da da
namiji, in ya mutu shi ya ci
sarauta. Yana alla-alla Sarki ya
mutu bai haihu ba, sai Allah ya
kaddara haihuwar wannan yaro.
Tun ran da Waziri ya ji gudar
haihuwar Musa, zuciyarsa ta yi
baki kirin, daga ran nan ya zama
ko mai suna Musa ba ya so ya
gani, ya shiga kulle-kulle kullum
na yadda zai yi ya kashe Musa,
ko kuwa ya sa ya bi uwa duniya, abin ya gagara. Har yara suka yi
kamar shekara goma sha biyar biyar, ko ina Sarkin nan za shi da
su ya ke zuwa.
Ana nan ran nan, ina ya Allah babu ya Allah sai Waziri ya sami
wata dabara, ya ce a ransa, 'Alhamdu lillahi, ko-da-ya-ke ba
yadda za a yi in sami Musa wani
wuri shi kadai ba tare da Sarki
ba, balle in san abin da zan yi
masa, ai in na yi kokarin da na
raba Musa da Mahmudu, kome
ya yi kyau. Domin yadda suka
shaku haka, lalle in aka raba su
hankalin Musa zai tashi, ta
wannan hanya zan san yadda
2
zan yi in sa shi ya sulale da dare ya bi dan'uwansa." Sai ya yi
dariya, ya buga kafa a kasa.
Kashegari, ko da ya tafi wajen fadanci aka fara 'yan tade-taden
duniya, sai ya takalo maganar yaki, ya ce, "Mu dai mun saki jiki
da duniya yanzu, ba mu shirin kome."
Sarki ya ce, "Me ya kawo wannan magana, Waziri? Muna
cikin sulhu haka, me ruwammu da wani shirin mayaka?"
Waziri ya ce, "Ai ka san ba a san abin da sauran kasashe ke ciki
ba. Gwamma ko mu zauna da shiri, don ba a fafa gora ranar
tafiya."
Sarki ya ce, "Wane shiri ya fi wanda mu ke da shi yanzu? Ga
Sarkin Yaki, ga Barde, ga Madawaki, cikinsu kowane ya yi kukan
kura sai a ba shi hanya."
Waziri ya ce, "Wadannan ai duk sun tsufa, ga Sarkin Yaki
yanzu a kalla ya ba saba'in baya. Wanda ya ke haka, tun da Allah
ya nufe shi da samun magaji, ya kamata ya huta. Dabarata sai
Mahmudu ya koma gidansu, ubansa ya rika koya masa al'amuran
yaki."
Musa da ke nan sai ya tsolma baki ya ce, "In dai don a dauke
Mahmudu ne, a bar ni ni kadai, ni ban yarda ba, sai dai mu je a
koya mana tare."
Waziri ya kau da kai ya kuta, ya ce, "Ina ruwanka da koyon
yaki, kai da za ka sa a je a yi maka?"
Musa ya ce, "Ni dai ban yarda mu rabu ba."
Sarki ya ce, "Tun da Musa bai yarda ba, dabararka ba ta yi ba
ke nan, Waziri."
Waziri ya bata fuska, zai fara wata magana sai ga wani ya zo ya
fadi gaban Sarki, ya ce, "Ga Wazirin Sarkin Sinari ya zo da
wadansu manyan garinsu, ya ce a yi masa iso." Sarki ya ce ya
shigo. Da ya shigo ya yi gaisuwa, ya mika masa takarda.
Magatakarda ya karba ya buda, sai ya ga an rubuta:
3
"Takarda ta fito daga Sarkin Muminai, Sarkin Sinari,
Abdul'azizi, dan Shaihu Muhtar, zuwa ga masoyinsa amininsa
Sarki Abdurrahman, gaisuwa mai yawa, da so, da yarda, da
aminci. Amma bayan haka ina so in karfafa zumuntan nan da ke
tsakanimmu, saboda haka na ba dana Musu 'yarka Sinaratu, in
sun kara girma a yi biki. Sai mu shirya a gama su tun muna da rai.
Haza wasalamu.”
Da Sarki ya ji abin da takardan nan ke ciki sai ya tashi da fada,
ya fizge takarda daga hannun Magatakarda ya kyakke ta. Ya
tashi ya kama gemun Wazirin Sinari, ya jefad da shi gefe guda.
Sarakunansa suka shiga tsakani, suna "Hucewa mai duniya!
Rashin hankali ne na yara."
Sarki ya сe, "Ko Musa ya lalace ya auri Sinaratu? Me aka yi
aka yi Sarkin Sinari, balle 'yarsa Sinaratu?"
Ya dubi mutanensa, ya ce, "Ku yi ta dukansu sai sun bar
kasata!
Wazirin Sinari ya ruga, ya haye dokinsa, mutanensa suka dafi
bayansa. 'Yam birni suka bi su eho, eho. Fada duk ta rude,
fadawa suka yi ta duban juna. Liman ya ce, "Allah ya ba ka
nasara, abin nan da aka yi, a aika lafiya dai?"
Sarki ya ce, "Me ya firgita ka? Don dai mai garin Sinari ko
cewa na yi a mare shi, ya yi magana?"
Barde ya ce, "Ai Sarkin Sinari yanzu ganin kansa ya ke daidai
da kowa. Ban yi tsammanin abin nan da aka yi masa zai kyale
ba."
Sarki ya ce, "Kai ma ka karai ne, kamar Liman?"
Waziri ya ce, "Ba karaya ba ce, ai gaskiya c abin da na ke fadi
yanzu na kan ba mu da shirin kome."
Mutane suka ce, "Gaskiyarka, Wazir, ga Sarkin Yaki yau
4
kwanansa kamar ashirin ke nan sai a kwantar a tayar, ba shi ko
da magaji."
Sarki ya kara fusata, ya ce, "Ba shi da magaji? Watau kun
shiga maganar tsohon banzan nan? In dai maganar Mahmudu ku
ke wa mita, na dauki alkawari, ko bai iya kome ba, duk yakin da
ya fara tashi nan gaba, shi zai zama jagaba." Aka gama fadanci
aka vatse, suka tafi suna zunden Waziri.
Waziri ya koma gida da fushi, ya kama shawarwarin abin da
zai yi wa Sarki ya huce haushinsa. Daren nan ya kasa barci, ya
kulla wannan ya kwance, har asuba. Da gari ya waye sai ya
rubuta takarda zuwa wajen Sarkin Sinari, ya ce, "Kada wani bu
ya ba ka tsoro da Sarki Abdurrahman, shirim ne ba inuwa.
Muddin ka dauki alkawarin za ka naďa ni Sarkin garin nan, ni ko
na san yadda zan yi in taimake ka ka ci kasar. Domin duk
mutanen kasar sai abin da na ce musu. Da farko sai ku dauri
niyya maza ku zo kafin su shirya. Ku biyo ta kadarkon Kimba,
don ta wannan hanyar har ka shigo birni kowa bai sani ba. Ku
taho tare da wannan yaro ya nuna muku hanya, domin ko ban da
shi nan kasar ba wanda ya san wannan hanya." Sai ya ba wani
amintaccen bawansa, wai shi Barakai, ya gaya masa yadda zai yi,
ya sallame shi.
Sarki Abdurrahman kuwa bai sake komawa ta kan Sarkin
Sinari ba. Ana nan ran nan ya sa aka daura wa dawaki sirada, ya
hau tare da yaran nan suka tafi shan iska, har suka kai wata
fadama, suka sauka suna hutawa, sai ga wani Balarabe dauke da
aku cikin keji. Ko da Musa ya daga ido ya gan shi sai ya ce, "Alo,
alo, ga aku a saya mana!"
Nan da nan wani bawan Sarki da aka je da shi ya kira
Balaraben nan, ya tambaye shi kuďin akun. Balarabe ya ce, "In
ba jaka guda ba, ba na sayad da shi."
Da bawan nan ya ji haka sai ya ce, "A'a! Da Sarkin za ka yi
ba'a? Kana tsammani Sarki ya tambaye ka karin magana ce?"
Da bawan nan ya fusata Sarki haka, sai ya cika ya ce a kama
Balaraben nan. Bayin da aka zo da su suka tasam masa kamar za
su cinye shi danye, da shi da tsuntsunsa duka.
Da dai tsuntsun nan ya ga haka, sai ya kada fifike, ya се,
"Allah ya ba ka nasara, kada ka yi hushi bisa ga gaskiyar ubangijina. Ni ma a jaka gudan nan da ya fadi a ganina ya karya mini
daraja ne. Kamata ai bai kamata a sallama ni jaka guda kadai
ba."
Sai sarki ya ce wa bayi su tsaya. Ya dubi dan tsuntsu, ya ce,
"Kai kuwa dan tsuntsun nan mene ne dalilinka na wannan cika
baki haka?"
5
Sai aku ya dukad da kai, ya ce, "Akwai kuwa, Allah ya ja
zamaninka, takamar da na ke yi ba don saboda kyaun jikina
kaďai na ke yi ba, ba ko don saboda dadin bakin nan da Allah ya
ba ni ba, amma saboda baiwa wadda Ubangijimmu ya yi mini ta
wajen iya duba. Har yanzu ta kai ni fagen ina iya ba da labarin
abin da za a yi nan gaba, balle ma a tambaye ni wanda aka yi ya
wuce. Kuma a cikin bokanci, sanin da Allah ya ba ni ba shi da
iyaka. In kuma labaruruka ka ke son ji, ko na aljannu, ko na
barayi, ko na Sarakuna, in ka saye ni in ya so ma kada ka sake
batad da kuďinka a banza garin sayen Alfulaila, ko wadansu
littattafai na Turawa wadanda ba su da wani labari daga na
tafiye-tafiyen gano kasashe, sai fa na tarihe-tarihe da na lissafelissafe, da na kiwace-kiwacen lafiya, masu gundurad da mutane.
In kuma karuwa ka ke nema wurin arziki, in ka saye ni bukata ta
biya."
Sarki ya ce, "Ta wajen suruntun naka na wofi?"
Aku ya ce, "Surutu ba abin rainawa ba ne. Magana ai jari ce."
Da yaran nan suka ji ya iya ba da labarai, da ma abin da su ke
so ke nan, sai suka yi ta tsalle-tsalle suna murna. Sarki ya rike
baki yana mamakin wannan tsuntsu. Sarki ya ce wa aku, "Tsaya
mene ne na wannan irin fafarniya? Yabon kai jahilci. In kana da
hikima, gaya mini yau shekarun Musa nawa?"
Sauran mutanen da suka zo tare da Sarki suka fashe da dariya,
suka ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara, ka ko kashe mana
bakinsa! Ya fadi mu ji, kan ba karya ba."
Aku ya dubi Musa, ya ce, "Yau shekarunsa goma sha hudu da
wata biyar da kwana uku."
Mutane suka ce, "A'a! Ai ko, Allah ya ba ka nasara,
gaskiyarsa!"
Sarki ya ce, "Kai, ji ya yi wajen wadansu ana fadi. Labarin
Musa yanzu ina ne bai kai ba?" Ya sake ce wa aku, "To, mun ji
ka rike wannan da ka ji mutane ke fadfi, amma wace rana ce aka
haife shi?"
Aku ya sake duban Musa, ya ce, "Ranar Jumma'a da la'asar."
Sarki ya ce, "A'a! Ai ko gaskiyarsa." Ya dubi aku, ya ce, "Da
ya ke kana da hikima, sai ka gaya mini me za: fara aukuwa gare
shi?"
Aku ya ce, "Ba za ka so ka ji wannan al'amari ba, don zai bata
maka rai kwarai. Ya fi kyau a bar kaza cikin gashinta." Sarki dai
ya nace sai ya gaya masa, in ya ki kuwa yanzu ya sa a hura wuta a
babbaka shi da rai.
Da aku ya ga Sarki ya fusata sai ya ce, "a yi mini gafara bisa
ga abin nan da zan fadi. Musa zai zama snad.n cuce-cuce, da
6
raunuka, kai har da halakar rayukan mutane kamar dubu na
kasan nan. Wannan al'amari kuwa ba da daďewa ba zai auku. Da
ma kana ganewa, ka sake shiri tun da wuri."
Da Sarki ya ji haka sai ya hasala, don aku ya ce dansa zai zama
sanadin mace-mace. Ya dauki kejin ya jefar. Ya tashi zai je ya
take dan tsuntsun nan ya mutu. Bayi kuma suka zaburam ma
Balarabe, duk wurin ya harmutse. Sai kwaram suka ji kuwwa. Su
waiga haka, sai ga wani mai doki sukwane, ya zo ba ko sirdi, duk
jikinsa jina-jina, abin ba kyaun gani. Ya fadi gaban Sarki, ya ce,
"Wayyo Allah! Wayyo Allah! Ka yi mana agaji! Ai ga Sarkin
Sinari can ya shigo kasarka da yaki, 'yan garuruwammu na nan
kan iyakar arewa duk sun zama toka. Na rantse har da girmanka,
ni kadai na tsere!"
Sarki da mutanensa duk suka yi sako, kowa na duban
dan'uwansa. Sai kawai daga bayansu suka ji wani abu, ha ha ha!
Duk suka waiga firgigi, sai suka ji daga cikin keji an ce, "Ai ga ta
nan. Da ma na gaya maka, ka tashi kashe ni, kai ne ba ka sani ba,
ba irin magana kamar tamu a ke rainawa ba."
Sarki bai sami ta cewa ba. Aku ya ce, "Ko yanzu in ka bi
shawarata allah ya kyauta, ba wani abin da zai bata maka rai.
Sarki ya dubi aku da fushi, ya ce, "Ka rufa mana baki nan!
Wata shawara gare ka?"
Musa ya sa baki ya ce wa Sarki, "Allah ya ba ka nasara,
matambayi ai ba ya bata, ya fadi mu ji."
Sarki ya ce, 'To, fadi, in ko shawarar taka ba ta fita ba, ina
murde maka wuya, kowa ya huta."
Aku ya ce, "Yanzu Sarkin Sinari ya kusa kawowa kadarkon
Kimba, nufinsa ya biyo ta tsakanin dutsen Kimba da na
7
Ubandawaki ya kewayo ta gabas ya fada wa birni ta inda ba a
tsammaninsa."
Sarki ya ce, "Cikin 'yan gari ma akwai wani mahalukin da ya
san wannan hanya, balle Sarkin Sinari?"
Aku ya ce, "Kai dai ka ji abin da zan gaya maka. Yanzu maza
ka koma gida ka aika da 'yan kwarbai su tsare makurdin nan da
ke tsakanin dutsen Kimba da na Ubandawaki. Kome yawan
rundunarsa, ko mutum goma masu karfin zuciya sa iya mai da shi
baya a wannan wuri, kafin ya kewayo ma ka shirya uwar yaki."
Sarki ya yi tsaki. Musa ya ce, "Dan akun nan ya san abin da ba
mu sani ba, sai a bi shawararsa mu gani." Ko-da-ya-ke abin nan
da aku ya fadi Sarki na jinsa kamar tatsuniya ce, duk da haka tun
da Musa ya sa baki sai ya hau, suka koma gida, ya zabi 'yan
kwarbai guda dari ya aika da su inda aku ya misalta masa. Ya
kuma ta da manzanni ya aika da su kudu da arewa, gabas da
yamma, a gaya wa mutane su yiwo harama su zo maza da shirin
yaki. Makera kuma suka shiga gyara makamai.
Ana nan bayan kamar kwana biyar sai ga wani daga cikin 'yan
kwarban da Sarki ya aika ya zo a sukwane da bushara, ya ce wa
Sarki, "Allah ya ba ka nasara, ai wannan dabara da ka yi ta fita.
Shekaranjiya da hantsi muna nan mun yi kwanto inda ka ce
mana, sai muka hangi kura ta toshe sama, sai tsinin masu kawai
ka ke gani suna wal wal wal. Ga masu dawaki da dakarai
bilahaddin, muka hanga har iyakar ganimmu, ba mu ga
karshensu ba. Muna nan dai sai da muka bari goshin yaki ya
kawo dab da mu, sa'an nan muka yi ta sako musu kibau kamar
ruwan sama. Na gaba suka juya da baya suka gamu da wadanda
ke biye, abin ya cude, ga 'yar hanya karama, dawaki suka yi ta
zallo suna fada wa junansu. Mu ko dai sai zuba musu kibau mu
ke, na bisa na ta sullubowa kasa, dawaki na tattake su. Cikin na
gaban nan sai dai dai suka sami komawa wajen uwar yaki. Jim
kadan kuma sai ga wadansu suka taso wai za su yi mana sukuwar
salla. Ba dama, don hanyar ta cika matsatsi tsakanin duwatsu.
Muka yi musu yadda muka yi wa na farko. Aka yi ta aiko
wadansu, muna yi musu hakanan, har la'asar ta yi. Da suka ga ba
dama suka koma,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12