suka bar gawawwakin 'yan'uwansu nan, abin
sai wanda ya gani!"
Ko da Sarki ya ji haka, sai ya yi kamar ya ce kaka don murna.
Ya shiga ya gaya wa aku, ya yi ta gode masa, ya yi kamar ya
dauke shi ya hadiye shi. Nan take ya dauko jaka biyu ya ba
Balarabe, kuďin aku. Ya kawo ingarma taka hau ya ba shi, ya
kara masa da bayi bakwai, ya ba shi kyankyandi goma sha biyu
na tufafi, ya sallame shi ya tafi.
8
Cikin daren nan sai ga Barakai ya komo ya gaya wa Waziri abin
da ya faru, ya ce, "Mu ke kan gaba, sai kawai muka ga ana ta
zubo mana kibau, har aka sami dokina ban sani ba, sai na ga
kawai mun zube. Ni ko da na ga haka sai na kwanta karkashinsa
kamar na mutu. Na yini nan ba motsi, ana ta yaki bisa kaina. Da
dare ya yi tsaka, na ji sun yi shiru, sai na sulale na dawo."
Waziri ya yi masa barka, ya ce, "In ji ba a gane kai ne ba?"
Barakai ya ce, "Na tabbata ba wanda ya gane ni."
Waziri ya се, "То, madalla. Amma ina mamakin yadda Sarki
ya gane ta nan za su bullo."
Barakai ya ce, "Ni ma hakanan. Bakina dai ban yi da kowa
ba."
Waziri ya ce, "Lalle mutanen Sinari akwai munafukai. Amma
ba kome, gobe ma rana ce."
Bayan kamar kwana uku gayyar yaki ta taru, gari ya cika da
dawaki da dakaru har ya amaye, kauyukan rabe da birni ba
wanda bai cika ba. Da Sarki ya ga duk an hallara, tun da sassafe
sai ya kira Waziri ya bar shi tsaron gari.
9
Waziri ya duka, ya ce, "Na ko karbi amanan nan taka da
hannun dama." Yana 'yan koke-koken munafunci.
Sarki ya tashi ya shiga gida, ya kira wadansu bayinsa amintattu
guda goma sha biyar, ya bar su tsaron gidan, ya ce su lura kada su
Musa su fita waje sai sa'ad da Allah ya dawo da su lafiya. Ya
kuma tafi ya kira su Musa wajen aku, ya ce musu, "In kun
kuskura kuka fita wajen gidan nan bayan ba ni nan, ban yarda
muku ba. Kuma kome za ku yi ban yarda muku ku yi shi ba, sai
kun zo kun shawarci akun nan. Abin da ya ce muku kuwa, ko da
kuna tsammani kan kuskure ne, kada ku ketare shi."
Yara suka fashe da kuka suna cewa, "Baba, mun ji abin da ka
ce duka, ma ko bi."
Sarki ya juya wajen aku, ya ce, "Kai kuma, ga amana nan, in
ka ci amanata, to, Allah ya isa."
Aku ya ce, "Hakanan ne, ranka ya dade. In Allah ya so kuwa,
ka tarad da abin da ka ke so."
Sarki ya ce, "To, madalla." Zai tashi ya ce, "Af, jiya kuwa na
ga wani da wata macen aku, na saya don in gama ku tare, ta rika
debe maka kewa." Ya aika aka kawo ta, aka gama su. Aku ya yi
godiya, suka yi sallama da Sarki.
Walaha na yi, aka buga tamburan tafiya. Sarki ya taka ya hau,
sai Waziri ya zo ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ko ka sha'afa ne?
Ka yi alkawari duk yakin da ya fara aukuwa da Mahmudu za a."
Sarki ya kawo iya wuya, ga bakin cikin rabuwa da iyali, ga
kuma wata maganar banza. Sai ya sa baki ya kira Mahmudu ya
ce, "Ga doki nan, hau mu tafi, da kai za a." Mahmudu ya dare
doki.
Musa ya ce, "Ni ma zan tafi!"
Sarki ya ce. "Ba na zuwa da kai." Musa ya fashe da kuka, ya cę
ba ya rabuwa da Mahmudu. Sarki ya daka masa tsawa ya koma
gida, ya kira Sarkin gida da bayin nan da aka bari tsaro, ya ce,
"Ku lura kada ku bar Musa ya ko leko waje, in wani abu ya same
shi ina yanka ku!" Suka shiga da shi. Runduna ta dunguma, aka
taryi inda Sarkin Sinari zai fito.
Da Waziri ya ga an raba Musa da Mahmudu, ga shi kuma Sarki
ba ya nan, sai ya tafi gida ya yi ta murna, yana tsalle-tsalle. Ya
shiga tunane-tunanen abin da zai yi ya halaka Musa kafin Sarki
ya dawo. Domin in ya samu ya kashe Musa, kome ya faru wurin
yaki shi ke bisa. In Sarkin Sinari ya ci nasara, bukata ta biya, in
ko Sarki Abdurrahman ma ya ci, duk daya, don ko ba jima ko ba
dade shi ne zai gaje shi.
Da ya ga kurar yaki ta bace, sai ya kira wadansu katti hudu
cikin bayinsa wadanda ya amince da su, ya ce yana da wata
10
bukata, wanda duk ya biya masa ita zai 'yanta shi.
Bayin nan suka dauka gaba daya, "Fadi, yanzu ka ga aiki da
cikawa!"
Waziri ya ce, "Ina so ku kashe mini Musa. Yana nan cikin
gidan Sarki an kulle shi, an sa duk bayin gidan su tsare shi."
Bayin nan suka ce, "Af, in haka ne yaya za mu yi mu kashe
shi?"
Waziri ya ce, "In dai kun kasa kunne kwa ji, aiki a ke so ba
surutu ba. Yanzu duk hankalinsa yana ga Mahmudu dan'uwansa.
Na san lalle in kafa ta dauke, yadda aka yi duk saı ya yi kokarin
da ya fito don ya bi shi. Sai ku nemi buhu, in dare ya yi ku tafi
kofar gidan Sarki, ku sami wuri ku make. Da kun gan shi ku
kama shi, ku rufe bakinsa, ku tura shi cikin buhu ku daure, ku je
da shi kogi ku jefa."
Bayi suka ce, "An gama."
Musa ya yini ran nan sukuku. Mutane suna tsammani uban ya
ke tunawa, saboda haka ba su koma ta kansa ba. Da magariba ta
yi Sarkin Gida ya kulle kofofi duka, ya miko wa Musa mabudi ta
taga, yadda Sarki ya ce ya rika yi kullum. Ya koma zaure wajen
bayin nan da aka bari, suka yi ta hira har kusan asuba, sa'an nan
barci ya kwashe su. Duk abin nan kuwa Musa bai yi barci ba,
yana jira bayin nan su yi, ya je ya gaya wa aku ya bar shi ya fita ya
bi su Mahmudu.
Da ya ji sun yi barci, sai ya shirya, ya dauki mabudan nan, ya
shiga damaru, ya dauki garkuwa da mashi, ya nufi wurin aku. Sai
ya tarad da aku namijin, watau wanda aka fara saye mai sihiri,
yana barci. Sai ya ce, "Af, tun da wannan ke barci bari in
tambayi matar, da Bako da Tukura ai duk Umbutawa ne." Ya
tsaya gaban macen aku, ya ce, "Na zo in gaya muku ne don ku
sani, za ni bin Mahmudu, duk abin da zai same shi ya same mu
tare."
Da akun nan ta ji haka sai ta girgiza kai ta ce, "A! Wannan ko
kusa ba shi yiwuwa. Yaya Sarki zai bar mana amanarka, sa'an
nan mu saba?"
Ko da Musa ya ji haka sai duk ransa ya baci, ya harari aku ya
ce, "Har ke dan tsugunin nan naki kin isa ki hana ni zuwa wurin
dan'uwana? Karyarki ta sha karya!" Sai ya kama ta, ya murde
kan, ya yar. Yana jefad da ita sai mijin ya farka. Musa ya juya
wajensa, ya ce, "Kai kuma me ka ce? Na zo in gaya muku ne zan
bi Mahmudu yanzu.'
Da akun nan ya ji haka, sai ya dubi matar, ya ga abin da ya
auku gare ta. To, ga shi Sarki ya bar masa amanar yaro, in ya bari
ya fita, lalle ya ci amanar Sarki. Ya ga kuma in ya hana yaron nan
11
tafiya, lalle abin da ya auku ga
matarsa zai auku gare shi. Yana
nan yana tunanin wadda za ta
fisshe shi, sai Musa ya сe, "Ban
ji ka ce kome ba, ko kuma kai
hana nin za ka yi, yadda matarka ta tashi hana ni?"
Aku ya daga fiffike, ya duka,
ya ce, "Mamakin abin da ya sa
ka ba mace shawara na ke yi. Ai
magana irin wannan sai mu
tsakanimmu maza. In ba rashin
hankalin mata ba, ina mutum
zai ce za shi ga dan'uwansa, sa'an nan a hana shi? Yi maza ka
tafi, kada ka ji tsoron kome.
Ba shakka dai ka cika dan kirki, tun da ba ka saba abin da
tsohonka ya hore ka da shi ba,
da ya ce kome za ka yi ka shawarce ni. Ga shi ka san ni ba
kome ba ne, amma don ka cika
umurnin ubanka ka zo. Da ma
abin da a ke so ke nan kawai ga
dan kirki ya bi maganar iyayensa
da malumansa. Dan zaki da ya
bi halin 'ya'yayen zamani, ya ki
bin maganar magabatansa, ai ka ga yadda ya kare."
Musa ya ce, "Dan zaki? Wace magana ya ki bi? Su ma dabbobi
suna wata magana ne?"
Aku ya ce, "A! Suna yin irin tasu mana. Bari ka ji yadda suka
yi."
12
Labarin Wani Bororo Da Dan Zaki
Wata rana namun daji suka taru suna shawarar ta kofar da ya
kamata su rika fitowa 'yan Adam, don su kubuta daga
tarkokinsu. Kowa na kawo tasa ana kushewa, sai dila ya ce, "Ва
abin da ya fi, sai a yi makaranta nan dawa, mu da muka sha
gwagwarmaya da mutane, muka gane makircinsu, mu rika koya
wa na baya irin dabarummu." Sauran dabbobi suka yarda da
wannan magana.
Daga nan sai kura ta ce, "To, wa za a sa? Ai ka san wannan
aikin sai mu."
Zaki ya ce, "To, gaya mana irin dabarun da ki kan yi ki kubuta
daga mutane, sa'an nan mu gani in hanyoyinki na da amfani ga
sauran su bi."
Kura ta ce, "Ai ba wata dabara da ta ke raba ka da mutum, sai
idan wuri ya kure maka ka bude hakora ka tasam masa. In ko
akwai 'yar tazara, ka sanke ka yi ta kanka."
Zomo ya ce, "Allah wadan wannan dabara taki. In ke kina da
karfin tasam musu, mu muna da shi ne?" Ya dubi zaki, ya ce,
"Allah ya ba Sarki nasara, mafitarmu daya ce, idan kowa ya yi
rami a kasa, ya yi masa kofa kamar goma duk nesa da juna. Ka ga
in an rutsa ka nan sai ka bulle nan, in an datse nan sai ka bullo
nan."
Bauna ta dubi zomo, ta yi murmushi, ta ce "Kadai, yaro dai
yaro ne. Kana maganar a gina rami, ni ina ka ga ramin da zan iya
shiga?"
Dila ya ce, "Ce ma kya iya shiga, to, in kun gamu a wajen kiwo
fa? Ko kuwa don tsoro sai a bar neman abinci?""
Zomo ya ce, "Ai wannan sauki gare shi. Da kum gamu ya sa
karnukansa suka biyo ka, sai ka yi gaba kamar ka wuce, ka ta da
kura ka komo baya, ka sami gidan gara ka make gindinsa, sai ka
saje da shi."
Wannan magana ta zomo ta ba kowa haushi, har giwa ta tashi
take shi, ba ta sani ba. Ta harare shi ta ce, "Kai sakarai, in kai
kana iya makewa a suri, mu fa? Kai karnuka suka dame ka, me
13
aka yi aka yi karnuka? Cikin abubuwan ba tsoro har a gama da
karę? Wannan ba dan'uwammu ba ne, kwadayi ya kai shi cikin
mutane har ya yarda suna wulakanta shi kamar ba dan halas ba?
Kai ma zomo, ba ka san maganar da ka ke yi ba."
Kowa ya yi ta kawo dabararsa, don a sa shi malamin dawa,
amma in saura suka bincika, sai su ga shi kadai ta ke wa amfani.
Can an rasa wanda za a zaba, sai dila ya yi tsalle ya fado gaban
manyan dawa, ya ce, "Allah ya kiyashe ka daga sharrin mutane,
ni za a ba malanta, domin duk makircin mutane ba wanda ban
sani ba."
Kura ta ce, "Ba a tambaye ka yawan magana ba. Ka fadi
dabarun da ka ke yi kana tserad da kanka mu ji, in mun yarda."
Dila ya dubi zaki, ya ce, "Allah ya daukake ka, na san kuka na
cikin abubuwan da ke tona mu ga mutane, saboda haka in na yi
kuka gabas sai in ruga in koma yamma, in na yi a yamma sai in
koma kudu. Ban taba tsayawa inda aka ji na yi kuka ba, balle a
biyo."
Zaki ya girgiza kai, ya ce, "Lalle kana da dabara a wannan
wuri, amma in ka yi barci fa? Ko kuwa kullum ba ka yi, sai ka yi
ta gudu ka je nan, ka je nan?"
Dila ya ce, "Allah ya ba manyan dawa nasara, ai ni ba na barci
sai tsakiyar ganyayen doka. In da ko fara ta fadi na ji kyamas sai
in farka, in na ga ta tsaya in tsaya, in zuciyata ba ta ba ni ba in
ruga."
Zaki ya ce, "Lalle kana da dabara."
Kura ta ce, "Manyan dawa, ai ko wajen shan ruwa mutane na
cutarmu. In ya ce yana da dabara a fili ta wajen shan ruwa fa?"
Dila ya ce, "Ai ni ba na shan ruwa yadda ku ke yi. In na ji
kishirwa sai in tafi rafi, in tsoma wutsiyata cikin ruwa, in fito
waje in tsotse, in koma in sake tsomawa. Haka na kan yi ta yi har
in koshi, amma ban gane wa in dukad da kaina ba. Irin wannan
shan ruwa da ku ke yi, ai ita ce baya ba zane. In wani ya lababo
daga baya, ai barna ta auku."
Damisa ta ji haka sai ta ce, "Mhm, ai ba nan mutane su ke sha
da arna ba, sai wajen yin tarko. Babban abin da ba mu san kansa
ba ke nan."
Dila ya ce, "Ni dai abin da na tsare, shi ne duk inda na ga itace
ya sarke, ba alamar ganye, ba alamar saiwa a gindinsa sai in sake
hanya. Na san lalle itatuwa ba su tsira sai da saiwa da ko ganyaye,
ko sun bushe a ga alamar inda su ke. In ko ina tafiya, na ga wani
abincina a inda ba safai ya kamata a same shi nan ba, sai in hade
kwadayina, in kewaya in wuce shi."
Zaki da sauran dabbobi suka ce, "Lalle, dila, mun yarda kai ne
14
malamin dawa." Suka tara 'ya'yansu a makaranta, dila ya yi ta
koya musu wayo iri iri. Kullum in darasi ya fado a kan dabarun
da ya kamata su yi su kubuta daga mutane, sai dan zaki ya tashi,
ya ce don mutum, wannan dan karamin alhaki, shi ba ya bata
lokacinsa ga jin labarin makircinsa ba.
In dila yana rarrashinsa ya tsaya ya karu, sai ya ce, "Ni dai don
mutum Allah ya kawo ranar da za mu gamu da shi, ran nan yá
kwashe kashinsa a hannu. In same shi in keta cikin, in karairaya
kasusuwansa, in cinye namansa, in sha jininsa in more!"
A kwana a tashi, ran nan dan zakin nan na yawo, da shi da dan
rakumin dawa, sai suka hangi wani Bararo tafe da kayan tsabgu
da igiyoyin dangwali mai yawa, sun yiwo tashi, ya bar
'yan'uwansa a baya, yana sauri ya riga su isa mashekari, ya fara
zaben wuri ya yi bukka. Yana tafe yana 'yan wake-wakensa da
Fillanci, yana kirari shi kadai kamar mahaukaci. Ko da rakumin
dawa ya hango shi, sai ya ga bayanin da dila ke yi musu na mutum
lalle wannan ya zama shi ne, saboda haka ya gudu ya shiga daji.
Dan zaki kuwa ya tsaya, yana kallon wata irin halitta dabam da
wadda bai saba gani ba.
Da Bororon nan ya yiwo kusa, sai dan zaki ya ce masa, "Kai,
tsaya! Cikin namun daji, kai ne wa? Tun da na tashi ban taba
ganinka ba. Kai ko gaisuwa fada ba ka zuwa?"
Bororo ya ajiye kayansa, ya fadi gaban zaki ya ce, "Ni ne
Kuzajje. Abin da ya sa ba ka ganina fada, kunya na ke ji, ga kowa
da kafa hudu, ni ko sai biyu, ga kowa da wutsiya, ni ko fimfirin.
Dubi gashinku layalaya, ni ko tik da ni, kamar na fito daga
wuta."
Dan zaki ya ce, "To, ina za ka da wadannan itatuwa?"
Bororo ya ce, "Kura ta kira ni in je in yi mata gida, don tana
tsoron mutum."
Dan zaki ya ce, "Shin don Allah ina zan bi in gamu da mutum
yanzu? Shi na ke nema ruwa a jallo, kwana da kwanaki ban gan
shi ba."
Bororo ya durkusa, ya ce, "Yau da gobe dai ai ka gan shi,
yallabai. Amma ai tsoron karo da irinku ya ke yi. M, kada ka tsai
da ni, ina sauri in je in yi wa kura aikinta, ko ba don tsoron
mutum ba ma, ga rana ta fara zafi. Ba abin da ya fi gida dadi."
Dan zaki ya ce, "tsaya ka yi mini gidan tukuna in ji, sa'an nan
ka wuce wajen na kura."
Bororo ya ce, "A'a, yallabai ai ba ni da dama tun da muka yi
alkawari da ita, da ba ya magana biyu. In dai na yiwo mata na
dawo, na yi maka don amfanina ke nan kawai wajenku."
Dan zaki ya ce, "Zancen banza. Mece ce kura, har ka ce sai ka
15
yi mata gida za ka yi mini?" Ya taso wa Bororo, ya sa dagi ya
keta masa dan warki.
Bororo ya dubi warkinsa sabo ful, an yi masa karantsaye, sai ya
kume, ya dai hade bacin ransa, ya ce, "Tun da ka ce kana so,
manyan dawa, ai sai a tsaya a yi maka tukun."
Dan zaki ya ce, "Dole. Ashe ana tsoron Inna, in ji 'ya'yan
mayya."
Bororo ya tsuguna ya shirya tsabgunan, ya yi tsaikon daki mai
karfi tsakar wadansu itatuwa. Ya bi tsaikon nan ya daure tam da
itatuwan nan, sa'an nan ya samo ciyawa himi guda ya tara, ya
samo kirare tuli ya tsiba gefe daya, kamar mai shirin gashin
tukwane. Da ya tara su duk, ya yi ta diba, yana jitawa bisa
tsaikon nan. Ya bar'yar kofa wadda za ta isa dan zaki ya shiga. Da
ya gama aminta shi, ya durkusa gaban dan zaki, ya ce, "Shiga mu
gani in ya yi daidai da kai."
Dan zal:i ya shiga cikin bukka, nan da nan Bororo ya mai da
itatuwa, ya kulle, ya buga kyastu, ya kewaye bukka da wuta. Da
hayaki ya murtuke, dan zaki ya kasa numfashi, sai ya yi neman
fitowa, ya kasa. Da ya ji ya matsu, sai ya yi kara ya сe, "Kai
Kuzajje, wannan daki naka ya faye kunci, kuma iskar ciki ba ta
shakuwa. Fid da ni."
Bororo ya ce, "Haba, me ka ce? Kara fadi in ji? Ka makara. Ni
ne mutum wanda ka ke fartar kasa ka ke cewa sai kun gamu.
Kafin ka fara shan alwashi, da ya kamata ka tambayi iyayenka,
ka ji yadda mu ke murtuku da su."
Da dan zaki ya ji wuta ta kama ba ba ba, ya ce, "Na tuba, don
Allah ka fid da ni!?"
Bororo ya ce, "Haba, da ma ka dangana. Alkalami ya bushe."
Dan zaki ya cinye wuta kurmus. Bororo ya kama hanyarsa ya yi
gaba.
Wanda ya raina maganar na gaba gare shi, ya yi abin da ya ga
dama, kome ya same shi babu kaito.
Musa ya ce, "Me na ke ji haka kamar kiran salla?"
Aku ya saurara, ya ce, "Kiran salla ne kuwa! Kai, wannan
ladani ya yi sauri. Har asalatu ta yi?"
Musa ya tashi ya shige, bai ce masa kome ba, don ya ga ba
damar fita, duk mutane sun
farka.
Musa ya yini ran nan yana ta
cizon hannu, bai sami fita ba har
dare ya yi. Ya zauna yana allaalla bayin nan su yi barci, suka
ki, sai can asuba. Da ya ji sun yi.
16
barci suna minshari, sai ya tashi ya taho wurin aku neman iznin
tafiya.
Aku ya ce, "Yallabai, ina ni ina hana ka abin da ka ke so?
Alhali ko ma abin da a ke so ne ga dukan dam Musulmi, zumunci.
Sai ka yi hanzari, ka ga alfijir ya keto."
Musa ya juya zai fita, aku ya ce, "Yallabai, sai ka dauki fitila.
Jiya na ji an koro wadansu barayi daga gidan Kakaki, na ji 'Yan
Gadi na cewa kowa suka gani ba fitila sa kama shi."
Musa ya ce, "Yaya aka yi ban ji ko kuwwa ba, ga shi kuwa ban
runtsa ba?"
Aku ya ce, "Hankalinka ne ba ya nan, da ka sha dariya. Wani
barawo ne ya shiga taskar Kakaki, ya shinfida bargo yana shirin
daure kayayyakin da ya sata, sai wani barawon kuma ya fado
dakin, bai san wannan gudan ya riga shi ba. Yana sawo kafa ciki,
sai wannan barawon da ya fara zuwa ya yi tsammani Kakaki ne
mai gidan. Saboda haka ya yiwo kofa da gudu. Shi kuma wannan
da ya zo yanzu, da ya ji an nufo inda ya ke, sai ya yi tsammanin
shi aka biyo, shi kuma ya yi baya ya zura a guje. Banza ta kori
wofi, yadda 'Yan Gadi suka yi da suka kori barayi daga gonar
Madaki."
Musa ya ce, "Jiya har sata biyu aka yi? Sun ga Sarki ba ya
nan!"
Aku ya ce, "A'a, nasu dabam ne."
17
Banza Ta Kori Wofi
Wata shekara aka yi tsananin yunwa a wani gari, har abinci ya
zama ba mai ganinsa sai mai dalili. Talakawa da matsiyata ba su
da wani abinci sai rogo, rogon ma bai wadata ba. Saboda haka
wadanda ba su da ko dalilin samun rogon sai suka rika zuwa
gonakin rogo da tsakad dare suna satowa.
Ana nan cikin wannan hali, sai wadansu mutum uku suka yi
shawarar su tafi gonar Madaki su sato rogo. Suka dauki
kwanduna, da dare ya raba suka nufi can. Daya daga cikinsu ana
kiransa Kodago-a-taka-a-kare, guda kuma ana ce masa Kadanmai-ban-haushi, daya kuwa sunansa Kazunzumi-a-gan-ka-аraina. Da shigarsu sai suka yi wa juna rada suka ce ya fi kyau su ci
tukun, sai sun koshi sa'an nan su diba, gobe su kai kasuwa su
sayar. Saboda haka suka debo, suka sami wuri suka zauna suna
ci. Kodago ya dubi saura, ya ce, "Kai, ai ko rogon mutumin nan
duk zako ne."
Kadan ya ce, "Haba, ai zakin ba magana a ke yi ba, in ka sa
baki sai ka ji kamar sukar."
Kazunzumi ya ce, "Ai Allah ya buda mana kofar arziki." Tun
suna raďa har dadi ya sa suka koma magana sosai, kamar suna
cikin gidajensu. Da suka koshi suka yi ta tuga suna cika
kwanduna.
Ka san dare in ya yi tsaka, da an yi 'yar magana ko da sannu
sannu ce, sai ka ji ta da nisa. Saboda haka waďansu 'Yan Gadi
suka jiyo su, suka lababo, suka tasam musu suna cewa, "Kada su
kai! Biyo nan, harbar su! Kowa ka gani, kashe shi!" Sai suka yi ta
bara da ka, suna harba kibiya cul cul.
Wadannan 'Yan Gadin wadansu sakarkarun kauyawa ne,
sabon shiga. Da jin yadda suka tasam ma barayin nan da hauka
haka, ka san gaulaye ne, tashin kauye. Ka san in da 'Yan Gadi ne
na sosai, Allah ya ba ka nasara, sai su lababa da ya ke ana duhu,
su kama su a hannu ba su sani ba. To, ka ga yadda suka bata
al'amarin.
Ko da barayin nan suka ji haka fa, sai suka kwashe 'yan
18
kayansu suka runtuma da gudu. 'Yan Gadi kuma suka dafo su
suna cewa, "Kada su kai!" Ko da ya ke ana duhu, har ba mai
ganin kowa, duk da haka 'Yan Gadin nan na ta kurari, suna bin
motsin barayin. Barayin nan suka yi ta gudu kamar ransu zai fita.
Suna cikin gudu dai, sai Kodago ya yi wa saura rada ya ce,
"Kai, ni fa na gaji, ya kamata mu yar da kwandunan rogon nan,
mu yi ta kammu.""
Kadan ya ce, "Ni ma da abin da na ke shiri in gaya muku ke
nan."
Da Kazunzumi ya ji haka, sai ya ce, "Kada ku yi saurin karaya.
Ku dai dan jure kadan, ku ga tawa dabarar." Sai ya fadi rica, ya
ce, "Wayyo Allah, ya kashe ni! Ashe, harbin nan da na ce an yi
mini, sai yanzu dafin ya narke. Ku ji kaina, 'yan'uwa, ku yi mini
rai." Ya rada wa sauran abin da za su ce.
Sai suka ce, "Tashi don Allah, mu isa gida, watakila ka sami
makari, in ka sha ka amaye shi."
Kazunzumi ya ce, "Ni tawa ta kare. Ina maganar tashi?"
Kodago ya ce, "Lallabo dai, in fa ka mutu ai lalle mu je Gidan
Sarki da su, su gaya masa dalilin da ya sa suka kashe ka, don mun
debi saiwar rogo za mu ci, kada mu mutu da yunwa."
Kazunzumi ya marairaice ya ce, "To, mu tafi in gani, in na
iya."
Ko da barayin nan suka ji wannan makircin, sai suka kara mai.
Da 'Yan Gadin nan suka ji haka, sai guda ya dubi dan'uwan, ya
ce, "Ka ji abin da suka fadi?"
Dan'uwan ya ce, "Ai na ji." Shi kuma ya dubi na ukun, ya се,
"Kai ka ji abin da suka.ce?"
Na ukun kuma ya ce, "Na ji mana, ai kome ya same su halas
ne. Mu matsa, ko sun yar da abin da suka sato, mu gani." Suka
dai yi ta bin su.
Da Kazunzumi ya ji suna tafe sai ya sake faduwa, ya ce,
"Wayyo, ni kaina! Da dai na ce ko zan kokarta in kai gida, don in
sami inda za a lura da ni, kada in kumbura kafin safe. Amma na
ji dafin ya ci karfina. Ku ku yi ta kanku, ku kyale ni, ashe da ma
kasa ke kirana. In kun isa ku ba mata da iyalina hakuri, su tuna
dukan mai rai mamaci ne.""
Da'Yan Gadi suka ji haka, sai suka cirje, suna saurare. Ya sake
cewa, "Ku lura da wasicin da zan yi. Ku shaida na ce a ba da
sadakar sule talatin daga cikin kudina da na bari. Kuma ku na ba
ku amanar 'ya'yana, ku lura da su da kyau, kada su sangarce. Ni
tawa ta kare." Ya yi kalmar shahada. Da'Yan Gadin nan suka ji
haka sai wannan ya dubi wannan, wannan ya dubi wannan.
Kodago da Kadan kuwa sai suka yi ta tafa hannu, suna
19
sallallami, suna cewa, "Kada ka gakamar ka yi mutuwar kare, ka
ji. Yadda aka kashe ka duk wanda ya yiwo harbin nan ta same ka
shi ma sai Sarki ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 12