Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 12
dai kadan, igiyoyin ke da karfi." Don wayo sai ya takarkare, kamar yana cin igiyar da karfi, amma sannu ya ke yi, yana cewa a ransa, "In na yi maza na kwance shi, AA ban yi tsammani zai bar ni ba. Amma in na ja aiki sannu sannu har mai gona ya zo, sa'an nan in yi da sauri in na hange shi, da ya kubuta sa'an nan sai ya kama gabansa, ba zai nufe ni ba." Muzuru ya rika duban bera, yana cewa, "Don Allah yi maza, gari ya waye, yanzu mai gona ya zo ya ga abin da ya faru. Kasan ko, in ya same ni nan, na lalace." Bera ya ce, "Gabanka ya bar faduwa, iyakar kokarina na ke yi. Ban da ni ba beran da zai yarda da kai ya taimake ka." Ya ci gaba da tauna sannu sannu, yana barin wadansu. Can sai suka hangi mai noma tafe, yana sabe da bota. Muzuru ya ce wa bera, "Ga shi can tafe, ga shi can tafe, don Allah yi maza."" 45 Bera ya kama aiki da karfi. Manomi ya kusa kawowa, ya tsunke raga duka. Muzuru ya gudu ya fada daji. Bera ya ruga ya shiga raminsa. Manomi ya rika tafa hannu yana cewa, "Kash! Ya cinye ragar, amma bari, gobe na sake dabara." Ya kwashe, ya koma gida. Da gari ya waye kashegari muzuru ya zo bakin ramin bera, ya ce, "Abokina, abokina, fito mu yi tadin abota." Bera ya yi dariya da ya ji wannan zance na muzuru, ya ce, Wane aboki? Ai muddin kana nan ba ka ganina na leko. Da ma kaddara ta sa mu aminci, ba wata abota ce mai dorewa ba, ta fatar baki ce, tun daga jiya kuwa muka babe. Yadda ruwa ke abokin gabar wuta, haka na ke abokin gabarka. Da ma ka dangana. Wannan hadari mun haye shi, sai wata rana." Da muzuru ya ji haka sai ya tsuguna nan, ya yi ta rantse-rantse, ya kalallame shi da baki, yana cewa, "Fito, mu sami wurin zama, ni ba zan cuce ka ba. Kuma da ya ke ni na fi ka karfi, ko wane abu na ga zai cuce ka na yi kokarin in tsare maka shi." Ya dai sami dan beran nan, har ya yarda da maganarsa, ya fito. Ya kewaya, bai ga ya yi masa kome ba, sai ya ce, "I, ashe dai gaskiyarka, ko cikin kyanwoyi akwai 'yan halas da yawa." Muzuru ya ce ya kwashe kayayyakinsa da ya tara, su koma cikin kogon kuka inda ya ke, don can ya fi yalwa. Bera ya yi ta kwaso kayayyaki masu yawa wadanda ya ke tarawa, domin lokacin dari ya yi kwanciyarsa cikin rami, ba ya fitowa, balle ya sha dari. Da muzuru ya ga kayan da bera ya tara, ga su daddawa, ga mai, ga nama, ga fura, ga cuku, ga kayayyaki barkatai, sai kunya ta kama shi, don ba shi da wani abu gidansa. Ya tambayi bera inda ya samo wadannan kaya cikin daji. Bera ya ce, "Wajen mai gonan nan da ya kama ka. Kullum matarsa ta kawo masa a nan gona, kafin ya kai kunyar da ya fara ya zo ya ci, ni ko sai in yi ta diba, ina kawowa gida da gudu, ina komawa. Wadansu ko ma ta wajen ubana na gaje su." Muzuru ya ce, "Sai haka." Shi kuma ya shiga nasa kokari, bera kuma ya sake ta da himma, suka kara bisa ga abin da ya zo da shi. Da suka tara, sai suka tsaya shawarar inda za su boye. Muzuru ya ce, "Ba inda ya fi nå masallacin can na bakin kofa." Suka dauki kaya, suka sami wani wuri can suka boye suka komo gida suka shiga hidimar ci da kawunansu kullum. Suna nan zuane, ran nan muzuru ya ji kasala ta kama shi, ga shi kuwa yana jin yunwa, dari kuwa bai kama ba, balle a duba ajiya. Sai ya tafi wurin bera, ya ce, "An aiko mini daga cikin gari 46 wai wata kanwata ta haihu, yau kuwa ne suna. Ina so in tafi yanzu, kai sai ka zauna ka share gida, don ba za mu tare ba, gama halin 'yan Adam ba iri daya ba ne. Abin da wani yə gani ya kyale, in wani ya gani, ba ya kyalewa." Bera ya ce, "Hakanan ne, amma fa kada ka manta da ni cikin kayan suna." Muzuru ya ce, "Haba, in na manta da kai, in tuna da wa?" Ya nufi gari. Da ma karya ya ke yi, ba wanda ya gayyace shi suna, wajen ajiyarsu ya ke so ya je ya ci. Da ya ci ya koshi, sai ya sami wuri ya kwanta yana lasar gashi, yana gurnani. Can da rana ta yi, sai ya komo gida. Ko da bera ya hango shi, sai ya tarye shi da murna, yana tsammani ya rago masa wani abu, ya fara cewa, "Me aka samu?" Muzuru ya ce, "Namiji." Bera ya ce, "Me aka sa masa?" Muzuru ya ce, "Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba." Bera ya ce, "Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba? Ai ko wannan suna yana da ban mamaki. Haka sunayen-zuriyarku su ke?" Muzuru ya ce, "Mene ne abin mamaki ciki, ku da ku ke sa wa naku 'ya'yan Damburuntu fa?" Bera da ya ga kamar ya yi fushi, sai ya kyale. Da aka kwana biyu kuma, muzuru ya ce an sake haihuwa a gidansu, za shi wajen suna. Bera ya ce, "To, amma don Allah yau kada ka manta da ni, ka san ran nan ba ka rago mini kome ba." Muzuru ya ce, "Yawa aka yi a wurin, amma yau na yi kokari in samo maka ko da 'yar tsokar nama biyar." Ya fita, bai zame ba sai masallaci, ya shige, ya sami ajiyar ya ci ya koshi, ya komo waje ya kwanta. Da rana ta yi, ya tashi ya koma. Bera ya tambaye shi ya ce, "Ina tawa ragowar dina, ko kuma yau an yi yawa ne?" Muzuru ya yi biris da shi. Sai kuma ya bar wannan tambaya, ya ce, "Ina sunan da aka sa wa jaririn kuma yau?" Muzuru ya ce, "Yau-da-gobe-ba-ta-bar-kome-ba." Bera ya ce, "Yau-da-gobe-ba-ta-bar-kome-ba? Mts, wadannan irin sunaye naku ban taba jinsu cikin littattafammu ba." Muzuru bai sake ce masa ci kanka ba. Ran nan kuma ya ce an gayyace shi, ya tafi yà cinye sauran ajiyar da ta rage, ya dawo. Bera ya tambaye shi sunan yaro, ya ce, "Ta-faru-ta-kare." Don gudun zuciyar muzuru, bera bai ce kome ba, sai suka shiga sha'aninsu. Daga ran nan ba a sake kiran muzuru zuwa wajen suna ba, 'yan'uwansa suka rabu da haihuwa. A kwana a tashi dari ya tsananta, sai bera ya ce wa muzuru, 47 "Lokacin duba ajiya fa ya yi." Muzuru ya ce, "Tun kwanan baya na so in gaya maka na yi gudun kada ka ga karayata." Suka tashi suka nufi masallaci, muzuru na tafe na yi wa bera gwalo a kaikaice. Da suka isa, bera ya duba, bai ga ko burbudi ba. Ya yi shiru, ya dubi muzuru, ya ce, "To, haka ka yi mini? Na dai gane abin da ya faru. Ashe nan ka ke zuwa, kana cewa wai wani an gayyace ka gun suna. Ran da ka fara ci ka ce wai sunan yaro 'Wuyar-aiki-ba-a-fara-ba.' Da ka koma ka ce, 'Yau-dagobe-ba-ta-bar kome-ba.' Da ka zo na karshe ka cinye saura ka се wai sunan jariri..." Muzuru ya fusata, ya сe, "Ka rufe baki tun da girma! In na sake jin ka ce M, nan yanzu ina gama maka aiki." Dam beran nan na shiri ya ce, "Ta faru ta kare," muzuru ya kwabe shi. Saboda haka kafin ya yi shiru sai ga 'T', ta fita ta bakinsa. Ko da muzuru ya ji 'T', bai tsaya jiran wani abu ba, sai ya fada wa bera ya lakwame shi. Allah ya ba ka nasara, ka ji cutar shigege. Abin da zan kare ka da shi, in kai basarake ne, kome za ka yi nemi Sarakuna, malami ya nemi maluma, talaka ya nemi talakawa. Kowa ya ki bin abin nan da na fadi, in ya daka ta wadansu, shi ko ya rasa turmin daka tasa. Musa ya tashi ya shiga gida, ya ba da magani aka dafa masa, ya yini ran nan yana ta wanka da shi, yadda aku ya ce. Da rana ta fadi, aka yi salla. Musa ya kama wuridi, har can da asuba bayin Sarki suka yi barci. Sa'an nan ya yiwo shiri, ya taho wajen Aku, ya ce, "Zan tafi!" Aku ya ce, "Kai, ai ko wannan kintsawa da ka yi, ka fita fagen fama ba abin da za a so da kallo irinka! Ba shakka kowa ka gani nan duniya da irin dawainiyar da Allah ya aza masa. Malami ta neman ilmi, boka ta neman asiri, dan Sarki ta neman mulki. Duk ko fa, Allah ya ba ka nasara, wanda ya dami kansa a cikin wannan al'amarin da Allah ya dora masa don kyashin na. wadansu, ya ko sa kansa uku." Musa ya ce, "In ba rashin hankali ba, da ma me zai sa wani ya kula da wani a cikin wannan? Ga shi kowa ya sani Allah ya halicci mutane, ya buda musu kofofi dabam daban wadanda za su bi su sami abinci." Aku ya ce, "Ai ka san halitta kowa da irin ra'ayin da Allah ya yi mata. Hala ba ka taba jin labarin wani jaki da sa ba ne?" Musa ya ce "A'a." Aku ya ce, "Haba, sai haka! Bari ka ji." 48 Labarin Wani Jaki Da Sa Wata rana an yi wani mutum wai shi Sale, wanda Allah ya yi wa arziki kwarai. Kullum dare mutumin nan sai ya yi ta addu'a, yana rokon Allah ya ba shi ilmin fahintar maganar dabbobi. Duk inda ya ji duriyar wani shaihun malami, sai ya aika masa da kudi, ya yi masa roko Allah ya biya masa wannan bukata. Ana nan, a kwana a tashi, Ubangiji maji kan bawa ya karbi rokonsa. Ran nan Sale na barci, ko da ya farka da asalatu sał ya ji wani zakaransa ya ce, "Kikiriki!" Sai wata kaza ta ce wa zakaran, "Kai, maigida kana da murya! Yanzu caran nan taka duk garin nan ba inda ba a ji ta ba." Zakaran ya kada fiffike, ya ce, "Don ma ina mura yanzu ba na iya yi da karfi. Da sa'ad da na ke lafiya ne, in na yi ai duk kasan nan a ji. Sale ya bingire da dariya, har ya rasa abin da ya ke ciki. Ya yi godiya ga Allah bisa ga amsa rokonsa da ya yi. Ya tashi ya yi alwala, ya yi salla, ya fita zaure wajen yaransa, aka yi ta tadin duniya, kowa na fad'in albarkacin bakinsa. Da rana ta yi zafi, sai Sale ya shiga gida, don ya kwanta kafin azahar. Da ya hau gado ya kwanta, sai ya ji ya kasa barci, ya dauko buzu ya fito gindin dabi a barga, ya kishingida. A cikin dabin nan kuwa da ya ke akwai sansa na noma da jakinsa na hawa, suna daure kusa da kusa. Yana nan kishingide, sai ya ji san nan ya ce wa jakin, "Kai dai ka ji dadi. Barorin gidan nan ko yaushe hankalinsu na wajenka. Dubi har wanka su ke yi maka, su ba ka abinci irin wanda ka ke so. Ni kuwa ga ni kullum sai a daura mini kaltibeta, a sa maketacin bawan nan ya tafi da ni gona, in yi ta aiki tun daga fitowar rana har ya zuwa faduwarta. Ba wannan ma ke ba ni haushi ba, sai dukana da ya ke yi in na dan tsaya in sarara. Don Allah dubi wuyana ka gani, duk ya kuje domin wahala. In mun dawo gida kuma ba wani abinci mai dadi ba za a ba ni in ci. Shin wanda ya ke haka don ya ga kyashin wadansu, ai bai kamata ba a ga wautarsa." Da jaki ya ji haka sai ya ce, "Af, ai wannan duk sakarcinka ya sa su ke raina ka haka. Tun da su ke zuwa daura maka kaltibeta, ka taba tunkuyin wani daga cikinsu? Ko ba ka tunkuye su ba ma, in kana tasam musu kamar za ka danne su, ka ga sun fara rage maka azaba. Ga shi Allah ya ba ka karfin da za ka neman ma kanka girma da shi, amma wautarka ta hana. Kuma ai ko ba ka fito musu ta haka ba, ka ce su kan kawo maka rubabbiyar dusa, to, in sun kawo kada ka ci, in ka sunsuna ka kau da kanka. Wallahi in ka bi wannan dabara tawa, ka ga al'amarin ya yi maka dadi har ka gode mini." Sa ya kama abin nan da jaki ya gaya masa, ya yi masa godiya bisa ga nasiharsa. Sale dai na kishingide, yana jinsu. Da gari ya waye sai bawan nan ya dauko kaltibeta ya daura wa sa, ya tafi da shi gona: Suka yi aiki, suka komo. Da dare, ko da bawan nan ya zo ya daure shi, sai ya ga ya tasam masa kamar zai halaka shi, ya ruga ya dawo, sa ya yi gunji, ya rasa yadda zai yi ya daure shi, sai ya rufe dabin, ya bar shi a sake. Ya'kawc dusa da kaikayi ya tura masa, yana cewa, "Yau san nan lafiya ya haukace? Ko kuwa yana jin kishiruwa ne?" Ya tafi rijiya ya jawo ruwa, ya tura masa, sa ya ki ko dubansu. Da gari ya waye bawa ya dawo ya ga kwanan sa, sai ya tarad da shi kwance, ya mimmike kafafunsa, yana nishi, ya dubi kwandon dusa da na kaikayi, ya gan su yadda ya ajiye, sa bai ko taba ba. Ga ruwan kuma da ya kawo, ba abin da ya taba shi. Da ganin wannan bawan ya ce, "Haba, na san a yi haka, haukacewar da san nan ya yi jiya ba banza ba. Ashe yana da gaskiya, shi kadai ya san abin da ya ke ji. Yau dai bai kamata a je da shi gona ba." Ya ruga ya gaya wa Sale haka. 50 Da Sale ya ji, sai ya lura watau san'nan ya bi shawarar da jaki ya yi masa ne. Saboda haka ya ce wa bawan nan ya je ya kama jakin, ya tafi da shi gona. Ya ce ya daura masa kaltibeta, ya yi noma da shi maimakon sa, kada kuwa ya ji tausayinsa ko kadan. Bawan ya tafi ya kama jaki, ya kai shi gona, ya daura masa kaltibeta, ya yi ta aiki da shi, in ya dan dakata don rashin sabo, sai bawan ya aza masa kulki tim, jaki ya kara mai. Suka yi ta yin haka tun da sanyin safe har rana ta koma ga Ubangiji, sa'an nan bawan ya koro shi zuwa gida, ya kawo shajaran majaran. Sale na kofar gida zaune, ya ga sun dawo. Ya dubi jaki, ya ga lalle kamarsa ta sake. Ya tambayi bawan yadda suka yi da jaki, ya gaya masa duka. Sale ya'ce a ransa. "Bari in bi jakin in ji yau kuma me zai ce wa sa." "Daure jakin ke da wuya sai ya fadi yana nishi, ya dubi sa, ya ce, "Kai, yau in an kawo maka abinci, me ka kulla kuma za ka yi?" Sa ya ce, "A'a! Har da wata dabara ce da ta fi wannan da ka gaya mini? Ga shi yau duk ranan nan da aka yi sai kwance na ke cikin inuwa ina hura hanci. Ai ni wannan makwabtaka da kai ta yi mini amfani." Jaki ya harare shi, ya ce, "Kai sakarai, kana nan kwance ba ka san abin da a ke kullawa a yi maka ba. Yanzun nan da zan shigo na ji ubangijimmu na cewa bawan nan nasa, tun da ya ke ba ka iya cin abinci, balle ka yi wani aiki, gobe sai ya je ya kira Sarkin Fawa, ya zo a yanka ka a yi rarraba. Da kamar in kyale ka, sai na ga dai yadda ka yarda da ni haka, har ka ba ni shawara, bai kamata ba in ci amanarka. Don an ce kowa ya ci amanar wani, ko ba jima ko ba dade, ya ga sakayyar Allah. Abin da na ga ya fi yanzu, in sun kawo maka abinci ka sa hankalinka ka yi ta ci, sai ka koshi. Wallahi in ba haka ka yi ba, in gaya maka gaskiya, gobe war haka kai kuma sai labari. Wannan magana fa ta kama sa, nan take ya kama kiwo ba ji ba gani. Yana ta godiya bisa ga wannan nasiha da jaki ya sake yi masa. Sale ya kura wa sa ido, yana dariya da ya ga ya takarkare ba ya ko daga kai, in ya ci dusa ya juya ga kaikayi, sai cika bakinsa ya ke yi kamar mahaukaci. Sale ya yi ta mamaki, yana cewa a ransa, "Ashe duk abin nan da mu ke yi wa dabbobi sun sani, Allah dai ne bai ba su bakin da za su furta mana ba. Yadda Allah ya hore mana su haka, ba don karfimmu ba, ba abin da ya fi sai mu rika sawwake musu wahala matsananciya. Mu tuna duk abin da mu ke ji, su ma suna ji, mu lura da su yadda za mu lura da kammu, kada mu gode wa Allah da mugun aiki." 51 Ya tashi, ya kira bayinsa, ya hore su da rika lura da dabbobinsa da kyau, kada su sa su abin da za su wahala fiye da kima. Musa ya се, "А! Ashe har mutane na iya jin maganar dabbobi ko? Wannan abu da ban mamaki!"" Aku ya çe, "Ai ko ni na taba ba wani ubangijina maganin jin, sa'ad da ya auro wata karuwa da ta matsa mana lamba. Ta wannan hanya na raba su. Af! Kai, kada in tsai da kai da labarin, sai ka yi shiri ka fita kafin gari ya waye." Ya yi shirin fita sai aka yi asalatu. Ba dama ya leka ko waje, tun da ya ke kowa ya farka. Ya koma gida, tun safiyan nan har magariba yana ta tunanin dabarar da zai yi wa aku ya samu ya fita, ba da ya tsai da shi ba. Zuwa asubahin fari, da ya ji bayi sun yi baci, sai ya zo ga aku, ya ce, "Yau ba na son wani labari. Abin da na ke so sai ka gaya mini yadda kuka yi da ubangijin nan naka, da ka ba shi maganin jin maganar dabbobi, in tafi. Shí kaďai na ke so, ba kome ba." Aku ya ce, "Ka ko yi tambaya ga dan gida." Ya tsirgo, ya soma. 52 Yadda Muka Yi Da Ubangijina Ojo Kafin in zo wajen Balaraben nan da Sarki Abdurrahmani ya sayo ni a gunsa, da wajen wani Bayarbe na ke wai shi Ojo. A cikin garin nan da ya ke duk ba wanda ya kama ko kafarsa wajen arziki. Amma duk da haka abin ya ba ka mamaki in ka ji na се matarsa daya ce tal. Da yana da uku, sai ya auro wata hatsabibiyar karuwa, suka yi su huďu. Ko da karuwan nan ta shiga gidansa, sai ta tasam ma shiga bokaye da 'yam bori, don ta sami maganin da za ta kori sauran matan. Kwanci tashi, ta ko samu. Ojo kuwa da ma ba ya ganin kowa da gashi, ban da karuwan nan. Don tsananin son da ya ke mata shi ya sa ya aure ta. Da ta sami maganin da za ta yi ta raba Ojo da sauran matansa, sai ta ce, "Kome ya yi kyau. Amma ai fa an ce kau da bara ba ta ci sai an gama da gociya." Saboda haka fa ta soma kulla makirci, tana gama Ojo da matansa dai dai. Yau ta sa ya kori wannan, gobe ya kori waccán har ya zama gidan ba wata sai ita. Ga mijin kuma Allah ya ba ta a hannu. In kara ta gifta masa ba shi da ikon ketarewa, sai ka ce ba mai arżiki ba. Mulkin nata ya wuce bisa kan mijin, har yaran gida ba mai ikon tari in tana nan. Da wani, ya yi mata dan tashin kai, sai ta sa a kore shi. Kai, bari ta şu mutane, har ni ma da na ke dan tsuntsu shakkarta na ke yi. Ga mijin mutumin kirki, yana son yin wani abu, amma yana shakkar kada ta yi hushi ta ce za ta fita ta bar shi. Da na ga dai abin nan ya rude haka, sai na ce, "Abin nan ya kamata mu sa hannu." Na yi kwana uku ina shawarar hanyar da zan bullo wa wannan al'amari, yadda karuwan nan ba za ta ji ba, balle ta halaka ni, yadda kuma Ojo ba zai gane nufina sosai ba balle shi kuma ya tsane mi. Don ka san an ce, "So hana ganin laifi." Da na sami wata dabara, sai na kyale. Ran nan muna tare da Ojo, sai na ga yana sauraron wata 'yar tsuntsuwa da ke kuka nan bisa taga. Na dube shi na ce, "Da kana jin abin da 'yar tsuntsuwar nan, ke cewa, ashe da ban san abin da za ka yi ba don murna." Ojo ya ce, "Haba, yadda na ke da arziki haka, ya zama kuma 53 ina jin abin da dabbobi da tsauntsaye ke fadi, ai da ba haka ba." A raina sai na ce, "Wannan ya samu." Na dube shi, na ce, "Akwai maganin da a ke yi a ji, amma da sharadi guda mai wuya, shi ya sa ba shi da amfani sosai, ba don haka ba, ko ni ma da sai in ba ka. Ba wanda ya san wannan asiri ko cikin tsuntsaye, sai zuriyar gidammu kadai." Ojo ya ce, "Don Allah ka ba ni. Gaya mini sharadin kome wuyarsa na iya." Na yi dan musun karya, ya matsa ni. Sai na tafi, na samo maganin na ba shi, na ce ya sa a dandaka, a rika zuba masa ruwa cikin kunne kullum, da dare. Ya tambaye ni bayan kwana nawa za a bari. Na ce masa in lokacin bari ya yi, ba sai an gaya masa ba, zai ji abin da ya ke so ya samu. Yana doki zai shiga gida ya bayar a dandaka, sai na се masa, "Ai ba ka ji sharadin ba." Ya dakata. Na ce, "Sharaď'insa shi ne duk wanda Allah ya yi wa wannan baiwa kada ya bi shawarar mata, kome mace ta gaya masa, ko 'yar wane ne, ko da abin da ta fadi gaskiya ne. Ran da kuwa ya kuskura ya bi shawarar mata ko sau daya, ran nan fa shi kuma sai labari. Wannan, ma in an faďi ba a kwana, ni na kara shi." Da ya ji haka sai ya harare ni, ya ce, "Da ma don dan wannan sharadi ne ka ke cewa ba na iyawa? Me ka mai da ni ne?" Na ce, "Iyakarsa ke nan. Da ma batun mutuwan nan kadai na ke tsoro gare ka." Sai ya yi tsaki ya shiga gida ya dandaka maganin da hannunsa, ya kwaba, ya zuba ruwa cikin wata 'yar kwalaba. Kullum da dare sai karuwan nan ta zuba masa cikin kunne sa'ad da zai kwanta barci. In ta tambaye shi dalilin da ya sa ana yi masa haka, sai ya ce mata kunnensa ke ciwo, aka ba shi magani. A kwana a tashi, ran nan da ya farka barci, sai ya ji wani dan bera yã ce wa gudan, "Shin Damburuntu, me ya sa kyanwoyi ke cimmu ne? Su ba su da wani abinci sai mu? Da haka a ke zaman duniya, wanda ya fi wani karfi ya cinye shi, ai da yanzu ba kowa!" Damburuntu ya ce, "Haba, raina mu dai suka yi. Babban munafikin kuwa mai gidan nan. Shi ba Sarki ba, ba Waziri ba, har da ajiye kyanwoyi uku! Don Allah dubi yadda ya kwanta ya bude ciki, sai ka ce taiki!" Ojo murna ta cika shi, ya yi kamar zai yi dariya, sai ya kanne, don kada ya yi su gudu. Yana nan shiru, sai ya ji wancan na fari ya ce, "Damburuntu, kewaya can, ni in kewaya nan, mu ciji kunnuwansa, ko nan ma mu more.'" Da jin haka sai Ojo ya yi wuf ya tashi. Beraye suka watse. Ya bushe da dariya, yana godiya ga samun wann an babbar baiwa. 54 Yana nan kwance, ya kasa barci don murna, har aka yi kiran asalatu. Ya tashi matarsa ta kawo masa ruwan alwalla, ta ajiye ta tafi. Ya fito ya fara alwalla. Ya kusa gamawa, sai ga wani burtu nasa da ya ke kiwo ya nufi wajen wata kaza, ya ce "Ni dai, kaji, kuna ba ni mamaki wajen butulcin nan naku da cin amana." Kaza ta ce, "Me ka gani ne, ka ke tsinammu haka?" Burtu ya ce, "Dubi alherin da mutane ke yi muku. Da rana su ba ku hatsi da ruwa, ku sha a huce. Da dare su sa ku cikin daki su rufe, su yi ta saurare don kada muzuru ko maciji ko wani naman jeji ya je ya cuce ku. In kun haihu' su sa 'ya'yanku daki, su yi ta ba su abinci har su yi girma, don kada su fito tun suna kanana, shirwa ko shaho su raba ku da su. Hasali ma dai, zaune ku ke kawai, ba abin da kuka rasa. Amma kuwa ran da suka ce za su kama daya daga cikinku, duk ku gama gari da kuka, ku tashi ku fada bisa wannan shigifa, ku yi tsalle bisa wannan zaure. To, wannan ba butulci ba ne, mene ne? Hala irin godiyarku ke nan?" Kaza ta yi masa wata irin duba haka yakine, ta ce, "To, kai da ya ke ba butulu ba ne, gaya mini ta inda ka fi mu godiya ga mutane."" Burtu ya ce, "Ni a dawa Allah ya halicce ni, ba kamarki ba, amma duk da haka in mutane suka kama ni suka kawo gida, sai in dangana, ko da ya ke ban saba ba, in yi ta yi musu duk abubuwan da su ke so suna dariya. In sun kira ni, sai in taho. In na ga ubangidana sai in bi shi, in rika hawan buzunsa ina wasa. In ya jefa wani abu in bi in rida, don ya yi dariya. To, wannan ba rashin butulci ba ne,

Chapter 5 of 12