Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 12
Biyar! Ko ba su da karfi fa akwai yawa. Sarkin Yawa kuwa ya fi Sarkin Karfi!" Biri ya ce, "Ai duk kanana ne, babban ma da tsawon kafa kadai ya fi ni. Kuma a nan duniya ai babu naman dajin da ya fi ki karfi, in ba zaki da giwa ba." Kura ta ce, "Kai, yi mini shiru! Namun dajin da suka fi ni karfi nan duniya wa ya san iyakarsu? Kai dai mu tafi mu gani, in da riba mu fafata, in kuwa babu mu yi ta kammu." Ko da bunsuru ya hango su sai ya ce wa matarsa, "Tura 'ya'yanki cikin kogo, in sun shige kuma su yi ta kuka baki daya." Da suka shige duk suka barke da kuka baki daya, Ba-a-a-a-a-aa-a! Bunsuru ya ce, "Kai, me ya sami yaran nan?" Akuya ta ce, "Wai sun ce duk cikin naman da ke gidan nan ba su cin naman kowa sai na kura kadai, wai ya fi dadi." Bunsuru уa се, "То, a ba su sauran na kuran nan da na kashe jiya mana su karasa." Akuya ta ce, "Na ba su, sun ce ba su cin naman da ya fara bashi, wai sai sabo su ke so." Bunsuru уa сe, "Tоo, su hakura kadan su bar motsi, don na ji biri ya ce wai kura yau tana tafe, za mu yi fada, in Allah ya kawo mana ita ai kin ga yau sa wadata in dai don nama ne, don na ji an ce ta yi mai kwarai." Kura ta dubi biri, ta ce, "Ka ji ko, gaskiyata ce da na ce lalle abin nan ya fi ni karfi, ka ji jiya ma sai da ya kashe wani kura. Na san lalle bunsuru ba ya iya daurewa ya yi mini haka ba, ko daji ma ba ya yarda ya fito ba, wanda kullum yana can boye cikin gari. Ni zan koma tun bai rigaya ya gan ni ba!" Biri ya ce, "Kada ki lura da zancensa, fankama kawai ya ke yi 80 miki da karairayi, na gan shi dan karamin abu ne, kuma da ganin tafiyarsa ka ga raggo. Da kura ta ji haka zuciyarta ta yi dan karfi, ta ce, "To, mu tafi." Ko da bunsuru ya hango ta, sai ya tura 'ya'yansa a cikin kogon kura, suka soma kuka gaba daya. Ya ce wa akuya, "Don Allah gaya musu su yi shiru, biri ya yi mini alwashin zai yi dabara ya kawo mini kura har nan gidana, in sun yi hayaniya yaya za ta yarda ta iso, balle mu samu mu kashe ta mu sami abin kalacin? Kun gani fa yau saboda ita ba mu yi tanajin kome ba, a gare ta muka dogara." Da kura ta ji haka sai ta kama biri, ta ce, "Ashe da munafunci aka kulla da kai, don ka sa a kashe ni a banza? To, Allah ya tona asirinka, dan banza!" Zai yi magana ta sa kafa ta taka shi, ta kashe. Ita kuwa ta yi baya da gudu tana zawo. Da bunsuru ya ga sun sami sa'a haka sai suka kwashe duk kayan da ke gidan suka kama hanya suka koma gari gidansu. Aku ya dubi Musa, ya ce, "To, mu tafi, kyaun dan halas duk abin da ya yi niyya ya cika. Abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa, in ka ji ai sai ka yi kurum." Musa ya ce, "Me ke faruwa ga mai saba alkawari? Don mutum ya yi niyyar abu, ya koma ya fasa, sai wani abu ya same shi?" Aku ya ce, "Babban mugun abu kuwa zai same shi." 81 Labarin Sarkin Busa Abin da ya sa na ce haka, a wani gari can ketaren Bahar Maliya a cikin kasar Jamus, tun shekaru da yawa da suka wuce, Allah ya saukar musu da wani babbar bala'i. Aka saukar musu da beraye ko'ina cikin garin. Berayen nan suka yi ta karuwa, har mutane suka rasa abin da su ke ciki, duk inda mutum-ya duba garin ba ya ganin kome sai beraye. Ko wajen barci mutum in ya zo sai ya tarad da kamar ashirin tuku-tuku suna kwance. In hula ka ajiye, ko riga, kafin da safe sai ka tarar aljihun cike da beraye. In takaice maka labari, yawansu ba su kidayuwa. In da za ka kidaya su, ka kidaya kudajen da ke garin, sai ka ga sun fi yawan kudajen nan kamar sau dari. Gari dai ba wajen sa kafa, duk beraye ne. Abinci kuwa mutum ko ya fi Aula dabara, ba yadda zai yi ya ajiye shi. Kome za a dafa sai a yi daidai da yadda za a iya cinyewa, don ko cikin akwati ka sa abinci ka kulle, sa san yadda za su yi wa akwatin nan huda, su shiga su cinye. Duk wani abu da ka sani ana yi da fata sun cinye. Ba ka ganin mai takalmi, ko matashin kai, ko gafaka, ko buzu a garin. In ko sun kai ga abin da ba su ci, sai su yi masa hudoji, su bata shi. Ta ishe ka ma ko jariri suka tarar yana barci, sai su tasam masa da cizo za su cinye. Sai in ya yi kuka iyayen su kwace shi. In dare ya yi kuma su kan hana mutane barci da kuka da gujeguje. In sun ga jikin mutum waje, sai su kama da cizo, wai za su cinye shi. To, kada ka zargi mutanen garin, ka ga kamar sakarci ya hana su kashe su. Bala'i sai sa'ad da Mai abu ya sawwake abinsa. Da sun ga kare sai su tasam masa, su nuna masa Sarkin Yawa ya fi Sarkin Karfi. Don kyanwa kuwa, wannan karamar alhaki, ba su kula da ita ba. Abin mamaki, mutane kuma in sun tasam ma kashe su, sai ka ga kamar kara su su ke yi. Don a sa tarko kuwa, ko a sa dafi cikin abinci a ajiye, duk wannan ba ya rudinsu. Da sun gani sai su kewaye, kamar gaya musu a ke yi. Duk mutanen gari suka rasa yadda za su yi, sai suka tasam ma mai garin, suna cewa shi ne ke da gashin tsiya, don tun da aka 82 halicci duniya ba su taba jin irin wannan ba, sai cikin wannan zamani da ya ke sarauta. Suka ce ko dai ya san yadda zai yi da berayen nan, ko kuwa su fitad da shi, su kore shi daga kasar. Sarkin ya rasa inda zai sa kansa. Mutanen gari kuwa sai kara matsa masa lamba su ke yi. Ran nan yana zaune zugum, wadannan dattijai su zö su zazzage shi su wuce, wadannan su zo su zunzungure shí su wuce. Sai ga wani dan tsoho bako ya zo, ya duka ya gai da Sarki. Sarki ya dube shi, ya gan shi wani iri, sai ya ce, "Malam, daga ina? Wace sana'a ka ke yi?" Tsoho ya ce, "Ga ni dai. Inda na fito da nisa, amma sana'ata busa, har mutane na kirana Sarkin Busa." Sarki ya ce, "To, sai ka je ka sauka, in kana iya sauka nan, mu ba ta busa mu ke yi ba yanzu, ta kawunammu mu ke yi da wannan bala'i." Sarkin Busa ya ce, "Ai ni ma ba busar banza na ke yi ba, wani asiri Allah ya ba ni wanda in na yi busa duk ko wane abu mai rai ya biyo ni. Da kwadi, da macizai, da beraye, da dukan naman ruwa da na tudu, da tsuntsaye, har da masu tafiya da kafa biyu, duk wanda ya ji na yi busa, ba sauran zama, sai ya yi ta bi na. Don wadannan 'yan berayen da suka dame ku, in ka iya ba ni abin da na ce, yanzu sai in raba ku da su." Sarkin ya ce, "Don Allah ka taimake mu! Kome ka ke so nan duniya na ba ka. Tambayi, mu ji." Sarkin Busa ya ce, "Ka ba ni sule dari, in na raba ku da su?" Sarkin ya dube shi, ya ce, "Yau ga abin mamaki, mene ne sule dari kuma! Sule dubu goma ma, in kana so sai in ba ka. Kai dai mu rabu da wannan bala'i." Sarkin Busa ya ce, To, madalla." Ya sa wata irin mabusa bakinsa, ya yi ta-busa, yana yawo cikin gari rariya rariya. Sai berayen nan suka yi ta fitowa ko ta ina, suna binsa tururururu, wadansu manya, wadansu kanana, wadansu tultul, wadansu kyamas-kyamas. Ga wadansu ja wur, wadansu fari fat, abin har da shudda da rawaya. Ka ga wadansu ruku-ruku da ciki wadansu kuwa ga 'ya'ya kanana ke biye da su. Sai tsalle-tsalle su ke yi, suna 'yan kuka tsui tsui, kamar suna fara'a da wata bushara. Da ya kwashe duk, sai ya nufi kogi yana busa, suna biye, mutane na kallo na murna. Da isarsa bakin kogi sai ya fada cikin ruwa yana busa, beraye kuma ba su san sa'ad da suka bi shi ba, duk suka mutu cikin ruwa, sai daya kadai ya tsere. Mutane suka yi ta yi wa juna barka. A tsaya ma a fadi farin cikin da mutanen garin nan su ke yi da rabuwa. da wannan bala'i, ya zama kauyanci. 83 Da Sarki ya hangi Sarkin Busa na dawowa, sai ya ce wa mutane kowa ya koma gidansa, su kwaba kasa su lillike ramummukan da berayen nan süka giggina. Da Sarkin Busa ya iso, Sarki ya yi masa godiya kwarai. Sarkin Busa ya ce, "To, madalla, sai ka cika alkawarinka ko? Allah ya ba ka nasara." Sarki ya bata fuska, ya ce a ransa, "To; yanzu in na ba shi sule dai dai har dari, to, ni yaushe zan tara kudi in ina haka? Beraye dai ne ganin idon kowa sun mace, ba su ko komowa. In ma ba zarinsa ba dan tsoho da shi tukuf haka, me zai yi da sule dari?" Ya dubi Sarkin Busa, ya ce, "Ai da wasa na ke yi maka da na ce zan ba ka sule dari. Ashe kai ba ka san wasa ba? Ga dai sule sha biyar sun ishe ka. Me za ka yi da kudi da yawa ga shi ka tsufa?". Sarkin Busa ya harari Sarki, ya ce, "Zancen banza. Kai din ba ka tsufa ba da ka ke alkawari ba ka cikawa? Yi maza ka ba ni in kana ba ni, in ci gaba. Ba a kanku na fara ba!" Sarki ya ce, "In ba rashin hankalinka ba, yanzu yanzu da isowarka har ka yi aikin sule dari? Ko sha biyar din da na ce ai don dad'in girmana ne. In an bi kididdiga ne, ni ke uku da sisi ba ka ci ba. Dubi fa tun da safe har la'asar mutum ke aiki a ba shi sisi, balle kai yanzu yanzu!". Sarkin Busa ya ce, "In fa ba ka ba ni abin da ka yi alkawari ba, yanzu na sake mabusa, ka ga kuma abin da zai faru." Sarki ya yi fushi, ya ce, "Sake mana! Mu-ze a ci da burga, sai ka ce ba mutanen birni ba? Wanda ya mutu ban da Allah wa ke iya rayad da shi?" &4 Sarkin Busa ya ce, "Ko ni ban ce ina iyawa ba, amma ka ga abin da zai faru." Sai ya dauko wata mabusa ya fara busa, ya shiga gari titi titi yana busawa. Sai yaran gari duk mai iya tafiya, tun daga mai shekara uku har goma, suka yi ta fitowa suna binsa da gudu, suna tafa hannu suna rawa. Wani yaro mai dan dama daga cikin 'ya'yan Sarki ya rika ba da waka, saura na amsawa baki daya. In ya fadi ta farko, su kuma su fadi ta biyu, suna cewa: Ku zo ga daula wa zai ki, Alo alo, mu ci daďi! Kowa ya bari ta gota shi, Alo alo, mu ci daďi! Tuwo, nama, sai mun koshi, Alo alo, mu ci daďi! Nono da zuma ba mai zari, Alo alo, mu ci daďi! Siliki ran Salla ba datti, Alo alo, mu ci daďi! Zagi, mari, mun huta shi, Alo alo, mu ci daďi! Aikin wahala duk ba ma yi, Alo alo, mu ci daďi! Alo alo, mu ci daďi! Alo alo, mu ci daďi! Mutane ba su san abin da suka yi da Sarki ba, suna tsammani wasa Sarkin Busa ke yi da 'ya'yansu, sai suka tsaya suna daáriya, su ga ikon Allah. Amma da suka ga ya nufi kogi duk sai ransu ya baci, suna tsammani zai fada ne. Da Sarkin Busa ya fita bayan gari, sai ya tasam ma wani tsauni nan kusa da gari. Sarki da mutanensa na tsaye na kallonsu. Sarki ya ce a ransa, "Na san dai yaran nan ba su iya hawa wannan tsauni, na ga yadda zai yi da su." Ko da Sarkin Busa ya isa gindin tsaunin, sai mutane suka ga tsauni ya bude. Sarkin Busa ya kutsa ciki, duk yaran nan suka duru bayansa. Da suka shige duka, saura daya da aka bari can baya yana d'ingishi, sai tsauni ya rufe. Mutane suka yi ta kuka saboda batan 'ya'yansu. A cikin yaran nan akwai 'ya'yan Sarki su hudu, su ko ke nan gare shi, duk suka bace. 85 Inda Allah ya kyauta wa Sarki da ya ke mutane ba su san rashin tsaida maganarsa ta sa wannan abu ya faru gare su ba. Da sun sani nan take su ke halaka shi duk da zuriyarsa. To, ga shi kuma duk nasa sun bace, balle a ce wani makirci aka kulla da shi. Da uban yaron nan mai dingishi ya ga abin da ya faru, sai ya ruga ya jawo dansa, yana murna. Aka tambayi yaro me ya sa su ke bin mutumin nan? Yaro ya ce, "Ai mun ji yana cewa mu biyo shi, duk abin dadi na duniya ya ba mu. Ya ce akwai tabkin zuma, da nono, mu yi ta sha. Ga nama soyayye da dafaffe, wai inda zai nuna mana shinkafa ba a maganarta. Ni yanzu, duk bakin ciki na ke yi da aka bar ni baya. Yanzu suna can suna cin dadinsu, ni ina nan." Beran nan guda kuwa da ya haye, sai ya tafi ya iske wadansu beraye can, ba irin wadannan na bala'i ba. Ya rika ba su labari, yana cewa, "Ba ku sani ba, na yi daron cin dadi. A can ketaren rafi wani mai busa ya tara mu zai nuna mana inda daddawa ta ke banza, ga nama, ga mai, ga abinci iri iri, ba mai hana ka ci. Ya ce wajen nan da zai nuna mana ba a taba sanin akwai wani abu wai shi kare ba balle kyanwa, karamar alhaki. Zan isa, saura kadan, sai na ji na fada cikin ruwa. Yanzu 'yan'uwana na can sun yi kiba ni rashin sa'a ya sa ni na tabe!" Saura suka yi ta cewa, "Allah ya sa wata rana mai busan nan ya zo nan kasar, ya tafi da mu mu ma!" Sarki ya baza mutane cikin duniya, ko a sami labarin ya bulla wani wuri da 'ya'yansu. Aka yi nema, ko labari. Suka gaji suka dangana. Manyan gari suka ce, "Kai, ba ku sani ba fa, Sarkin nan ke da duk wannan gashin tsiya. Tun da aka halicci duniya kun taba ko jin inda irin wadannan al'amura suka faru?"" Saura suka ce, "A'a, lalle in ba tasam masa muka yi ba, har mu kuma zai sa a halaka mu." Sai suka taru suka tafi gidan, suka kunna masa wuta. Mai gari ya fito da gudu, suka bi shi da jifa, suka kore shi garin, ya fita tsirara. Iyalinsa kuwa suka fid da su, kowace ta nufi gidansu. Suka kwashe dukiyar da ya tara, da akwatunan kudi da ya jibge. Suka kona gidan, don kada sabon Sarkin da za su yi ya kwashi ciwon wancan na tsiya. Ka ji abin da ke aukuwa ga mai yin alkawari ba ya cikawa. Musa ya duba ya ga wuri ya yi haske, ashe har rana ta fito ba su sani ba. Sai ya ce wa aku, "Na ji abin da ke aukuwa ga mai alkawari ba ya cikawa. To, me 86 ke faruwa ga irinku masu hana a cika alkawari? Bai tsaya garin jiran amsa ba, sai ya shiga gida a fusace. Da azahar ta yi Waziri ya kira tsohuwan nán ya yi mata kwando goma na zagi, don har yanzu ta kasa dabarar da za ta yi tfito da Musa. Tsohuwan nan ta ce, "Kullum ina kokari, wani dan aku gare shi mai tsai da shi da labaru ko yaushe har gari ya waye." Waziri ya tashi ya mangare ta, ya ce, "Tun da ba ki da wata dabarar da za ki wayace dan tsuntsu, tafi, yau na sa wani." Sai ya kira bawansa Barakai, wannan da ya aika wajen Sarkin Sinari kwanan baya, ya gaya masa abin da ya ke so, da kuma yadda aku ke hana Musa zuwa da labaru. Barakai ya yi shiri irin na mata, ya tafi gidan Sarki, ya tarad da Musa inda tsohuwan nan ta yi masa kwatanci. Ya yi masa maganar Mahmudu na can rai ga Allah, ya ce wai Mahmudu ya сe a gaya masa, tun da ba ya kaurfar zuwa su gana, shi ma ko lahira kada Allah ya gama su. Musa ya fashe da kúka, ya ce, "Kullum ina so in tafi, dan akun-nan ke tsaishe ni da labari. Ga ko Sarki ya ce in na yi wani abu ba da na shawarce shi ba, bai yarda mini ba duniya da lahira." Barakai ya ce, "Don dai wannan dan tsuntsu, yau ka tafi. Nan zan kwana, da mun ji bayin nan sun yi barci mu je tare ka sallami akun, in hana shi ya tsai da kai." Musa ya ce, "Da kin kyauta.". (Don yana tsammani mace ce.) Suka zauna nan, har barci ya share bayin da ke zaure. Suka tashi suka nufi wajen aku. Ko da aku ya hango su tafe su biyu, sai ya gane Barakai namiji ne, ba mace ba ce. Saboda haka, kafin su iso su yi masa wata magana, ya riga su ya ce, "Don Allah, yallabai, yau ka tafi. Ni ba na iya ba ka wani labari. Duk inda ka ke son zuwa, ka tafi." Barakai ya dubi aku, ya ce, "Ko ba ka ce ba, da ma yau ba mu son wani labari naka." Aku ya langabe kai kurum, sai tausayi ya kama Musa, ya ce masa, "Me ya same ka yau?" Aku ya ce, "Tunani na ke yi." Da ya ke Musa ba ya son ya yi wa akun nan abin da zai motsa masa rai, sai ya tambaye shi tunanin da ya ke yi. Aku ya ce, "Ina tunanin abin da ya faru ga wani masassaki ne, wanda ya yi kokari ya tara fiye da abin da Allah ya ba shi." Musa ya ce, "Wannan masassaki ýa ja wa kansa halaka." Aku ya ce, "Da. ma ka ji abin da ya same shi, ai da ka san lalaçewar ba ta da iyaka." Bai tsaya a ko ce ya fadi ba, sai ya fara: 87 Kowa Ya Yi Kokarin Ya Sami Fiye Da Abin Da Allah Ya Nufe Shi Da Shi, Ya Ja Wa Kansa Lalacewa Domin wai akwai wani masassaki a Katako, yana da 'yarsa mai shekara biyar da haihuwa, sunanta Halima. Ko da ya ke an sanyaro a kan son tambayar kome ya ji ko ya gani, duk da haka son tambaye-tambayen Halima sun wuce kima. Wata rana da safe uban na zaune na sassakar wata kujera, sai Halima ta shigo, ta ce masa, "Baba, inna ta ga mussa ta ce mata kyanwa, ashe ba ta san sunanta ba, ko ta sani ke nan?" Kafin uban ya bayyana mata da mussa da kyanwa duk daya ne, sai ta sake masa wata tambaya, ta ce, "Baba, kawu ya ce wai akwai giwa na yawo nan sama, ita ce ke yin fitsari da damina muna cewa ruwan sama, gaskiya ne?" Uban ya fashe da dariya, zai bayyana mata ba gaskiya ba ne, sai ta ce, "Baba, wai kai ma inna ce ta haife ka?" Uban ya ga za ta hana shi aiki da surutu, sai ya ce mata, "Fita waje can, ki yi wasa da yara, sai in na kare ki dawo." Sai ta tashi ta ruga. Tana fita, sai ta ji yara na bin wani wada, suna cewa, "Malam Dogo, Malam Dogo! Halima kuwa ko wane karambani ya ja ta, da ganinsa sai ta tsaya daga kofar zaurensu, ta ce, "Malam Dogo, Malam Dogo, ka zo, baba na kira." Malam Dogo da ya ji haka sai ya nufo zauren. Halima ko ta ruga zaure wajen ubanta, ta rungume shi tana kuka. Tsammaninta wani dan sanho da wadan ke rataye a bayansa duk ba kome ciki sai 'yan yara kamarta. Malam Dogo ya zo, ya durkusa gaban masassaki, ya ce, "Ga ni, 'yar matan nan tawa ta ce kana kirana."" Masassaki ya kawo sadakar abinci da goro da kwabo, ya ba shi, ya ce, "Tun da Halima ta kira ka, ai lalle in sallame ka." Malam Dogo ya yi godiya, ya bude sanho ya fitad da wata 'yar nakiya da aka ba shi sadaka, ya mika mata, ta ki karba, don ita ce gamuwarsu ta fari. Daga ran nan kullum kuma in zai wuce sai yar biyo ta zauren -gidan, in ya ga Halima a waje ya ba ta dan wani abin da ya samo sadaka. Tun tana gudu, yau da gobe har ta saba da shi, ta rika tsayawa tana karba. Da ya gan ta dai sai ya zauna, ta hau bisa kafarsa suna wasa. In ta fara irin 'yan tambayoyin nan nata na yara, sai shi kuma ya rika ba ta amsa irin yadda ya kamata. In ta tambaye shi, "Me ke cikin sanhonka?" Sai ya amsa mata, "Tuwo da nama da sukar." In ta ce, "Ina innarka?" Sai ya nuna ungulu ko shirwa, ya ce, "Ga ta nan tana tashi." Sai su bushe da dariya. Duk sa'ad da yarinyan nan ta ga ungulu ko shirwa sai ta ce, "A! Ga innar Malam Dogo." Ta dubi uwarta, ta ce, "Inna, ke ba ki iya tashi kamar innar Malam Dogo?" Uwar ba ta ko kulawa da ita in ta fara tambayarta. Suna nan haka, ashe wadan nan wani mai sihiri ne, ba a sani ba. Ran nan sai ya zo wurin masassaki dauke da 'yan kayansa duka, ya ce, "Na yi niyya yau zan koma kasarmu. Amma in Halima ta tambaye ka inda na ke, ka ce ni ma na yi fiffike na tashi kamar innata, don kada ta yi kuka. Kullum ku ce mata zan dawo gobe." Masassaki ya yi bakin ciki, don 'yarsa ta rasa abokin wasa. Ya shiga gida ya dauko wata tsumman riga, ya ba Halima ya ce ta kawo wa Malam Dogo a zaure. Yarinya ta jawo riga da gudu, ta kawo masa. Ta fada jikinsa tana murna. Malam Dogo ya dube ta, duk idonsa suka cika da hawaye domin sabo. Ya zauna nan har magariba. Da suka yi salla, ya ci abinci, sai ya kira masassaki, suka fita bayan gari, suka yi tafiyar kamar loko guda cikin daji, sai suka kai ga wani dutse. Da suka isa, wada ya dubi masassaki, ya ce, "Ka san an ce soyayya gamon jini ce, ko ba haka ba?" Masassaki ya ce, "Hakanan ne." Wada ya ce, "To, tun da na zo garin nan, ban ga wanda jinina ya hadu da shi kamar 'yarka ba, Halima. Tun da tana tsorona, har ka ga yanzu ba wanda ta ke so da gani irina. Kome ta ci ta rage mini. Kai kuma kana yi mini alheri iyakar gwargwado. Saboda haka ni kuma zan saka maka. Ko da ya ke kana ganina haka a wulakance, don in jarrabi mutane shi ya sa na wulakanta kaina. Nan kasar duk kafin ka sami wanda ya ke al'amari da aljanu kamata, ka dade." Ya tsuguna ya tara 'yan hakukkuwa, ya debi ganyayen kan dutse, ya yi turare. Masassaki ya rike baki ya ga al'ajibi. Da hayaki ya tashi, sai Malam Dogo ya dubi dutse, ya ce, "Fayau, bude dutsen kudi!" Nan da nan sai dutse ya bude. Da budewarsa sai Malam Dogo ya dauki wata 'yar fitila nan rataye cikin dutsen, ya kunna. Másassaki ya duba cikin kogon dutsen nan, ba abin da ke ciki sai 89 karfe ja wur cikin wata katuwar randa. Ya bude baki yana mamaki. Malam Dogo ya ce, "Na ba ka abin da ke cikin dutsen nan duka, amma da sharadi guda. Duk sa'ad da ka zo, kada ka debi abin da ya fi fam guda kowane zuwa. Na san fam guda dai ya ishe ka kashewa yini guda. Daga nan har ka mutu ba ka ganin kudin nan na raguwa. Ka lura in Halima ta isa aure ka yi mata kaya masu kyau, ga dai gudummuwata nan na bayar." Masassaki ya fadi yana godiya, yana rokon Malam Dogo gafara in ya yi masa wani laifi da. Suka gafarta wa juna. Malam Dogo ya ce, "Ko da rana ka zo sai ka diba, in dai ba ka gudun kada mutane su gan ka. In ko da dare za ka zo, in ka fita, ka yi turare da ganyen nan, ka tabbata ba wani abin firgita da zai dame ka. In ko ka zo, ka ga abin da na yi ba wani abu ba ne mai wuya. Sai ka debi ganyen nan na bisa dutse, ka yi turare da shi a gindin dutsen, ka ce, 'Fayau, bude dutsen kudfi.' In ka shigo, ga fitila ka kunna, in da dare ka zo. In da rana ne ko, ba ruwanka da ita. Ka kuma amince, ba kayan aljannu ne ka ke sata ba, balle ma ka ce za ka ji tsoro. Kai dai ban da dibar abin da ya fi fam guda kullum." Ya dubi masassaki ya ce, "Fara daga yau." Masassaki ya duka ya kidaya fam guda, suka fito. Malam Dogo ya ce, "Garam, kulle dutsen kudi!" Dutse ya koma ya rufe. Malam Dogo ya dubi masassaki ya ce, "To, sai mu yi ban kwana, ni zan wuce." Suka yi sallama. Malam Dogo ya wuce, masassaki ya komo gida yana tsalle-tsalle don murna. Ya kwashe duk labari ya gaya wa matar, amma bai gaya mata abin da za a се da dutsen ya bude ba. Suka yi ta murna. Gari na wayewa, ko da magariba ta yi

Chapter 8 of 12