ni. Kana so in kare ka da
shi?"
Waziri dai bai ce uffan ba, yana can yana fama da abin da ya
same shi. Aku ya faki idonsa ya yi masa gwalo, ya ce, "Ko ba ka
so ina gaya maka, ai mu abimmu muna yi don Allah ne. Sai ya
soma:
102
Raina Kama Ka Ga Gayya
Wata rana yautai yana kiwo a bayan gari sai tarko ya kama shi.
Ya yi ya yi ya kubuce, ya kasa. Yana nan yana kuci-kuci sai ga
wani tsohon kare ya zo. Da yautan nan ya gan shi sai ya ce masa,
"Don Allah, wannan kare, ka dubi zumunci, ka ji kaina, ka sake
ni, kai kuma Allah ya taimake ka."
Kare ya tsaya kamar ya ki, ko kuwa ya dan cinye shi ne ya
wuce. Ya ga dai kamar ko ya ci shi, ba zai san inda ya nufa ba. Sai
ya tafi kusa da shi, ya sa baki ya tattaune tarkon nan, yautai ya
kubuta. Da yautai ya ga an kubutad da shi sai ya yi wa kare
godiya, ya tambaye shi inda za shi. Ya ce za shi neman abinci ne.
Shi kuwa kafin ya zo nan a kama shi a tarko, ashe ya ga inda
wata 'yar akuya ta mutu, aka kai gindin wata itaciya aka yar.
Saboda haka ya ce wa kare ya zo ya kai shi, kafin dare ya yi
kuraye su cinye. Ya tashi, kare yana bin inuwarsa har suka isa
wurin. Kare ya tsaya, ya sa hakori ya barke cikin akuya, ya ci ya
ci, har ya koshi. Yautai ya ce masa, "Da ya ke ka koshi sai mu
tafi ka ga shekata, kullum in ka matsu da son abinci ka zo, ni
kuwa in tashi in kewaya gari, inda na ga wani abin da za ka iya ci
in zo in kira ka mu tafi."
Ya ce, "To, madalla! Mu tafi in gani."
Da suka fara tafiya suka kai kan titi, sai ya ce, "Wallahi naman
nan da na ci ya kusa ya kware ni, da za ka dan dakata mini in
kwanta nan in huta kadan, da na so."
Yautai ya ce, "Ai gaskiyarka. Kwanta ka huta, in kana son
barci ma yi, ni kuwa zan hau nan in tsaya in na ga yara zan gaya
maka ka tashi, don kada su buge ka."
Kare ya ce, "To, madalla!" Kwantawarsa ke da wuya sai barci
ya share shi. Can an jima kadan sai ga wani tafe da keken shanu,
yana dauke da buhunan gero. Da yautai ya hango shi sai ya ce
masa, "Kai mai keke, kai mai keke, yi kwana, don kada ka take
mini dan'uwa, ga shi nan yana barci.
Mai keke ya harare shi da fushi, ya ce, "Wane ne dan'uwanka
da ka ke tsai da ni dominsa?"
103
Ya nuna masa kare da ke barci, ya ce, "Ga shi nan." Mai keke
ya dubi kare, ya yi tsaki, ya ce, "Da ma don saboda kare ka tsai
da ni? Karen me? Kai ar, Allah wadanka!" Sai ya kora shanunsa
suka bi ta bisa karen. Bai ko shura ba, ya mutu, hanji waje.
Yautai ya tashi ya bi shi yana kuka, yana cewa, "Wayyo ni,
kaico kaina, ka kashe mini dan'uwa, bai ci ba bai sha ba. Na yi
maka magana ka lura, ka ki, don ka raina ni. To, yadda ka sa na
zubad da hawayena yau, kai kuma sai na sa ka zubad da naka. A
bar ma ta batun hawaye, yadda ka sa dan'uwana ya bar duniya
yau, kai ma kana barinta, in Allah ya so."
Mai keke ya yi dariya, ya ce, "Har kai nan dan tsuntsu, yadda
ka ke za ka ce ka iya sa ni kuka? Duban ni da kyau fa ka gani."
Yautai ya ce, "To, shi ke nan. Raina kama ka ga gayya!" Mai
keken nan kuwa a gaba ya ke zaune, buhunansa na baya. Da
yautai ya ga ya kora, sai ya yi gaba kamar ya wuce shi, sai ya
'dawo ya sauka bisa buhunan gero, mutumin nan bai sani ba. Ya
yi ta yi musu huda, gero na tsiyayewa, mutumin nan bai sani ba.
In ya ga kamar zai waiwayo sai ya boye tsakanin buhu. Zuwa can
gero ya tsiyaye, sai ya ji keke na gwaram gwaram, kamar ba kaya.
Ya tsai da shanu, ya sauka ya duba kaya, ya yi salati.
Yautai ya tashi, ya ce, "Kadan ke nan. Ai ban gaya maka ba,
raina kama ka ga gayya?" Ya tashi ya sauka bisa idon sa guda, ya
yi ta tsatsagewa, sa na tsalle-tsalle. Mai keke ya gan shi, ya dauki
wani gatari nasa zai kwantara masa, sai ya tashi, ya sami kan san.
Sa ya fadi nan take ya mimmike. Mai keke ya ce, "Wash!"
Yautai ya ce, "Tukuna. Ai na gaya maka, raina kama ka ga
gayya."
Mai keke ya ciji baki, ya sauka ya daura wa daya san keke, ya
hau ya kora, ya nufi gida. Yautai ya komo ya sauka bisa idon sa
dayan, ya fara tsattsaga, shi kuma ya yi ta tsalle-tsalle, yana
harbe-harbe. Mai keke ya dube shi, ya ce, "Lalataccen nan ya
dawo." Ya dauki gatari, ya tsaya tsai, wai ya dube shi daidai ya
sare sai ya tashi, ya sami kan san. Sai ya fadi, nan ya shure. Ya
sauka ya rasa abin da zai yi, sai ya saba gatarinsa, ya nufi gida
yana cizon yatsa.
Yautai ya ce, "Mu tafi gidan, ai na gaya maka, raina kama ka
ga gayya."
Da matarsa ta gan shi ya shigo yana zage-zage sai ta ce masa,
"Lafiya, babba da kai kana wannan irin mugun baki?"
•Ya ce, "Ina fa lafiya, wani dan tsuntsu duk ya sa na kashe
shanuna, wai don na taka wani kare a hanya?" Ya waiwaya sai ya
ga yautai bisa tukwanensu, ya ce. "Kin gan shi ma ya biyo ni,
lalatacce!" Matarsa ta ce. 'Kai ar, sululun wofi, yaya dan tsuntsu
104
kamar wannan, wanda bai fi a hadiye ba, zai ruďa ka haka?" Sai
ta fizge gatarin da fushi, ta wurgi yautai da shi. Yautai ya tashi, ta
sami tukwanensu, duk suka fashe.
Yautai ya koma cikin dankin matar ya sauka, ya ce, "Raina
kama ka ga gayya!"
Da matar ta waiwaya ta gan shi, sai ta sake daukar gatarin ta
wurge shi da shi, ta sami korenta, duk suka fashe. Kai, in gajarce
maka labari dai, suka yi ta yin haka har ta fasa kayan dakinta
duka.
Yautai ya dube su, ya ce, "Tukuna dai. Raina kama ka ga
gayya!"
Daga nan mijin ya tuna da wata dabara, ya matsa wurin
matarsa, ya rada mata ya ce, "Rufe taga maza, ni kuwa in rufe
kofa, mu rutsa shi, mu kama, mu yi masa irin kisan da mu ke so."
Suka zabura waje gaba daya, suka rurrufe. Suka koma ciki,
tarya nan tarya nan, har suka kama shi a hannu, Suka bude kofa
da taga, suka fa tsaya gardamar yadda za su kashe shi. Mijin ya
ce, "Hura wuta za ki yi ki jefa shi.""
Matar ta ce, "A'a, ba haka za mu yi ba. Fige shi za ka yi yanzu,
ni kuwa in nika tosshi in kwaba shi, in tsoma shi ciki. Ko kuwa ma
ba haka za mu yi ba, in mun fige shi in sa wuka in kwakule idandunansa yau, gobe in yanke kafa guda, jibi in yanke fiffike guda,
mu bi shi da yanka haka gaba gaba har ya mutu, dan lalatacce!"
Da yautai ya ji haka sai ya ce, "Ta Allah ba taku ba. Raina
kama ka ga gayya!"
Ko da suka ji haka duk sai suka fusata, matar ta zaro wani
takobin mai gidan da ke nan, ta çe, "Bari in sare shi."" Mijin ya ga
nawar ya bar matar ta sare shi, sai ya duka wai ya take shi, sai
matar kuwa idonta duk ya rufe don fushi, ta kai wa yautai sara
daidai da sa'ad da mijin ke dukawa ya take shi, sai ta sare kan
mijin. Ya fadi, ya mutu. Yautai ya tashi ya fita, ya ce, "Alhamdu
lillahi! Da ma hakin da ka raina shi ke tsone ma ido."
Ganin wannan al'amari ya sa matar ta haukace, ta dauki gatari
ta shiga jeji. Kowane tsuntsu ta gani sai ta kai masa jifa tana
cewa, "Raina kama ka ga gayya!"
Da aku ya gama ba da wannan labari sai ya tashi fir ya koma
fada.
Da Musa ya gan shi ya tambaye shi labarin da ya gaya wa
Waziri, aku ya ki gaya masa hakikanin abin da aka yi sai ya ce,
"Na gaya masa labarin Umaru Mu'alkamu ne da Shaihu dan
Fodiyo ya nuna masa karama."
Musa ya ce, "Wace karama ce Shaihu Mujaddadi ya nuna wa
Umaru Mu'alkamu, wadda ban tuna da ita ba? Alhali kuwa
105
labarun Shaihu da mu'ujizarsa sai mu gaya wa wani ba wani ya
gaya mana ba.
Aku ya ce, "Ranka ya dade, ai ka san sani wuyar al'amari gare
shi, kome abin mutum in ya san wani abu bai san wani ba."
Musa ya ce, "To, fada mini wannan labari in ji, ko na tuna da
shi."
106
Labarin Shaihu Mujaddadi Dan Hodiyo Da Umaru
Mu'alkamu
Wata rana, sa'ad da Shaihu dan Hodiyo na Sifawa, sahabbansa
suka taru ana tadi, daga nan sai wani daga cikin sahabban Shaihu
wanda a ke kira Umaru Mu'alkamu, ya dubi mutane, ya ce, "Kai,
ina ko son goro, ko akwai wani mai dan tsalli ya ba ni in ciza?"
Mutane suka ce duk ba mai saura.
Shaihu na kallonsu, ya yi kamar bai ji ba, sai can, har an saki
wannan magana, ya dubi Umaru Mu'alkamu, ya ce, "Tashi mu je
shan iska bayan gari."
Umaru Mu'alkamu ya ce, "To." Ya tashi, suka tafi, Shaihu na
gaba, yana biye. A lokacin nan ko la'asar ta yi sakaliya. Da
fitarsu kofar gari, sun dan taba tafiya kadan sai suka kai ga wani
dan rafi, suka sa kafa suka tsallake, sai suka isa wani daji, Umaru
Mu'alkamu ya duba, bai ga kome ba sai itatuwan goro ko'ina.
Shaihu ya dube shi, ya ce, "Ka ce kana kawar goro, to, ga su
nan, debi iyakar abin da ke isarka."
Umaru Mu'alkamu ya shiga diba yana mamaki, ashe akwai
dawan goro kusa da Sifawa ba a sani ba? Ya cika aljihunsa, ya се
wa Shaihu dan Hodiyo, "Ai wannan ya ishe ni, Allah ya gafarta
malam." Nan da nan suka tsallako dan rafin nan suka komo
gida.
Ana nan, bayan 'yan kwanaki kadan goron da Umaru
Mu'alkamu ya debo tare da Shaihu ya kare. Da ya ga dai dawan
goron nan ba nisa gare shi ba, sai ya tashi shi kadai ya kama
hanyar da suka bi da Shaihu, yana sauri ya je ya debo kafin hantsi
ya yi zafi. Ya yi ta tafiya, ya yi ta tafiya har rana ta take tsaka cur
bai ga ko alamar ya kusa da wurin ba. Sai ya yanke kauna, ya
juyo. Kafin kuma ya iso sai da la'asar ta yi sansanya. Da isowarsa
bai zame ba sai wajen Shaihu. Suka gaisa, ya dubi Shaihu, ya ce,
"Kai, yau na ga tasku!"
Shaihu ya ce, "Me ya same ka haka, har ka ke yaba wahalar da
ka sha?"
Umaru Mu'alkamu ya ce, "Ai tashi na yi tun da safe, wai in
tafi dawan nan na goro da muka je da kai shan iska kwanan baya
107
na debo, in sake karowa. Na yi tafiya har Allah ya gajishe ni, ban
ga na kai ko dan rafin nan ba. Da na ga rana ta yi tsaka dai, sai na
rufa wa kaina asiri na dawo. Ka ga tun sa'an nan isowata ke nan,
ko ruwa ban biya gida na sha ba."
Shaihu dan Hodiyo ya dube shi, ya yi murmushi ya ce, "Da ka
san inda muka tafi fitarmu ran nan, da ba ka ce za ka bi ba. Ai
cikin dawan Gwanja na kai ka ka samo goron." Umaru
Mu'alkamu ya rike baki. Shaihu ya ce, "Ka ga dan rafin nan da
muka sa kafa muka tsallake kafin mu shiga dawan goron?"
Umaru Mu'alkamu ya ce, "Na gani."
Shaihu ya ce, "Wannan ai kogin Kwara ne ka ga ya tsulance
hakanan."
Umaru Mu'alkamu bai sami ta cewa ba, sai ya kada kai kawai,
ya ce, "Allah ya ba mu albarkacinku!"
Da Musa ya ji haka sai ya ce, "Af, wannan ai ina tsammani ma
shi na fara ji cikin mu'ujizozin Shaihu dan Hodiyo. In dai za ka
ba ni wani labari, na yarda ka ba ni, amma na Shaihu wannan
namu ne, sai mu ba wani, muddin dai an yi shi. Gama ko labarin
jihadin da ya yi, da biranen da ya gina, da wadanda ya ba tutoci,
duk a kaina su ke."
Aku ya gyara fiffike, ya ce, "Ai ni ma hakanan, Allah ya ba ka
nasara, ko da na ke tsuntsu sai dai in ba wani labarin Shaihu đan
Hodiyo, ba wani ya ba ni ba."
Da Musa ya ga aku ya tsunke da surutai yana yabon kansa, sai
ya ce, "Tsaya! Mene ne na yabon kai? Yabon kai jahilci. Ni ba
wani surutu na ja ka ba, balle ka cika mini kunne haka. Cikin
labarin mu'ujizozin Shaihu dan Hodiyo yanzu zan gaya maka
wanda ba ka sani ba, in kure ka. Ba na ma takalo labarin jihadi
ko labarin asalinsa balle ka ce na yi zurfi shi ya sa ka kasa. Shiga
kidaya,.sai na gaya maka uku wadanda ba ka sani ba, sa'an nan
in shiga in yi azahar, na ji an yi kira."
Aku ya ce, "To, ba sai ka fara ba mu ji? In dai lalle an yi shi, ai
sai na gani."
Musa ya ce, "Da fari ma ba ka san wannan ba. Wata rana,
sa'an nan Shaihu dan Hodiyo na yaro, suna zaune a Dagel da shi
da ubansa Hodiyo. Ran nan Hodiyo ya shiga ya yi alwala su yi
azahar, sai ya kira Shaihu ya ce, "Zo in aike ka Murnona--"
Aku ya yi farat ya karbe ya ce, "Wanda Shaihu ya tafi ya
dauko littafi har ya dawo uban bai gama alwala ba? Shaihu ya yi
alwala ya bi shi aka yi sallar da shi? Alhali kuwa daga Dagel zuwa
Murnona zango guda ne ga mai kaya?"
Musa ya ce, "Me ka ke faranniya haka don ka gane na fari? In
ka san wani ka san wani ne?""
108
Aku ya ce, "To, fadi mana mu ji, Allah ya ba ka nasara."
Musa ya ce, "Wata rana Sarkin Gobir Wuro Nafata ya aika a
kira Shaihu dan Hodiyo kamar abin girma-"
Aku ya karbe ya ce, "-ashe ko nan ya sa an gina rami mai
zurfi, ya kafa wukake da masu ciki, ya sa an rufe ramin da
tabarma, don in Shaihu ya zo ya ce ya zauna nan ya faďa ciki ko?
Shaihu kuwa ya zo ya zauna, bai fada ba. Sarkin Gobir ya daga
wata bindiga da ke gare shi nan boye zai harbi Shaihu, bindigar ta
fashe. Sarkin Gobir duk ya kokkone. In ko ba wannan mu'ujizar
ba, wata ka ke nufi ka fadi mu ji, Allah ya ba ka nasara."
Musa ya ce, "A'a! Ashe dan tsuntsun nan a yi da shi. Ya dubi
aku, ya ce, "Ka san labarin Shaihu da madugu?"
Aku ya ce, "Shaihu da madugu? Wane labari ne kuwa na
Shaihu da madugu wanda ban sani ba? An ko yi shi? Allah ya ba
ka nasara, sai ka faďi mu ji."
Musa ya се:
109
Labarin Shaihu Dan Hodiyo Da Madugu
Wata rana wani madugu yana dawowa daga Gwanja, ya iso
Kwara ya shiga jirgi. Suna kan tafiya cikin jirgin nan, sai igiyoyin
Kwara suka murda, jirgin ya yi nan tangan tangan, ya birkice. Sai
madugun ya kama, "Shaihu dan Hodiyo, ka taimake mu! Shaihu
dan Hodiyo, ka yi agaji! Ni dai kam wallahi in na kubuta daga
wannan halaka, in na je Sakkwato sai na kai maka sadakar goro
kwarya goma:" Yana fadin haka sai ya ga wani ya zo ya kama
shi, ya fid da shi duk da kayansa. Ya duba ya ga kowane ne, sai ya
ga ba kowa.
To, a cikin wannan lokaci kuwa Shaihu Mujaddadi dan Hodiyo
yana Sakkwato, yana ba da karatu, kuma yana wa'azi ga jama'a.
Sai aka ga ya yi shiru. Can sai aka ga yana matsa hannun rigarsa,
ruwa na zuba tsurururu. Jama'ar da ke nan suka nemi bayanin
wannan al'amari daga gare shi.
Shaihu ya ce, "Wani bawan Allah ne ya nemi taimakommu a
Kwara da jirginsa ya kife. Allah ya nufa muka je muka taimake
shi."
Jama'a suka rike baki suna cewa, "Allah ya sa mu cikin ceton
Annabinsa, ya ko ba mu albarkacinku, Mujaddadai!"
Bayan an yi kusan wata biyu, ran nan sai ga madugun ya zo
Sakkwato, ya debi goro kwarya uku ya tafi wajen Shaihu ya kai
masa don ya cika alkawari, ya kuma nemi albarka. Bayan ya
gaishe shi, ya gaya masa abin da ya faru duka ga jirginsu sa'ad da
suna tsakiyar Kwara, da kuma yadda ya roke shi, ya zo ga
taimakonsa, ya ga kamar wani ya zo ya fid da shi, amma da ya
duba bai ga kowa ba. Shaihu dan Hodiyo ya tambaye shi wace
rana ce wannan hadarin ya auku, kuma nawa ga wane wata ne.
Madugu ya fadi ranar da watan, ya lissafa kuma ya fadi
kwanan watan sa'ad da wannan al'amari ya auku. Da almajiran
Shaihu su kuma suka lissafa, sai suka ga ya kama daidai da ranar
da Shaihu Mujaddadi ya yi shiru cikin wa'azi yana matsar hannun
rigarsa. Abin ya kara ba da mamaki.
Madugu ya fitad da goro ya mika wa Shaihu, ya ce, "Ga abin
110
da na yi alkawari zam ba ka in Allah ya nufa na kubuta."
Allah ya nufa na kubuta."
Shaihu dan Hodiyo ya yi godiya, ya karba ya ajiye, ya yi
murmushi ya dubi madugun, ya ce, "Ai ko ba ka cika alkawari
sosai ba. Kwarya goma ka ce, ga shi ka kawo uku."
Madugu ya rasa abin da zai ce don kunya, yatai gida ya ciko
kwarya bakwai ya kawo wa Shaihu, ya fadi ya yi godiya, Shaihu
ya karba, ya raba wa mutanen da ke nan sadaka.
Musa ya dubi aku, ya ce, "Ka ji labari daya da ba ka sani ba
cikin mu'ujizozin Shaihu Mujaddadi dan Hodiyo. Yanzu kana
daya. In dai ga labarun Shaihu ne, in na fara na iya gaya maka
goma ba ka sami wanda ka sani ba."
Aku ya tuma nan ya tuma can, ya karkata kai, ya ce"Allah
Sarki! Ai wannan labari na Shaihu ko na goye ya san shi, amma
ka ga duk da haka sai da ka yi babban kuskure cikinsa. Shi ya sa
ka ruda ni, na ji kamar ban sani ba."
Musa ya сe, "To, ka fara ba? Kai dai wani ba ya yin abin kirki
in ba kai ba. Wannan labari na ji shi ya fi sau kam, amma duk
ban taba jin inda suka saba ba."
Aku ya ce, "Saurara, Allah ya ba ka nasara, abin da na gaya
maka duk na labarin Shaihu dan Hodiyo sai ka yarda, Madugu da
ka ce ba madugu ba ne, farke ne. Ai ka ji batan da ka yi."
Musa ya ce, "Wasalam! Ka ji ka ba? To, me ya raba dambe da
fada?"
Aku ya yi dariya, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, zage-zage."
Sai Musa ya yi dariya, ya yi tsaki, ya ce, "Kai dai ba ka gajiya
da surkulle. Ko mutum ya tashi yin hushi da kai sai ka ba shi
dariya. Allah ya kai mu dare, kai ka gaya mini naka wanda ba
mutum duka ya sani ba. In na bi taka yanzu, har lokaci ya wuce
ban yi salla ba.""
Aku ya kada fiffike, ya ce, "Allah ya kai mu. Amma ina da
fatawa. Don Allah, Shugabana, shi sai mutum ya sa da me da me
a jikinsa za a san lalle ya yi ado, ba abin kushewa?"
Musa ya ce, "Kai fa na san ka, wadansu tambayoyinka duk na
ba'a ne. Kai ba ka kan gani da kanka ba? Ai ko tsuntsu ya san ba
abin da ke kambama mutum irin ya sa wando mai zina, da jabba,
da riga aska takwas a bisanta, kana ya sami-."
Aku ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ai ma ado ya kare. Kada in
tsai da kai, sai da dare."
Musa ya ce, "Allah ya kai mu da alheri."
Da dare ya yi, barci ya share Musa, sai can da asuba ya farka,
ya tashi, ya shiga damaru, ya dauko mashi ya zo wajen aku, ya cе,
"Madalla, ai kowa ya yi karyar dare gari ya waye! Ka ce labarin
111.
Shaihu da na bayar jiya ko na goye ya san shi. To, ina son in ji
naka wanda ba a sani ba."
Aku ya kada fiffike, ya dukad da kai, ya ce, "Allah ya ba ka
nasara, yanzu ko ka ji."
112
Labarin Shaihu Dan Hodiyo da Wani Malami
Wata rana wani malami daga gabas da ya ji labarin Shaihu sai ya
yiwo wa Sakkwato tsinke, ya zo ya ga abin da a ke fadi da
idanunsa, domin an ce gani ya kau da ji. Da ya kusa da Sakkwato
ya yi shiri irin na alhazai, ya shiga kokuwa, ya tafi wajen Shaihu
Mujaddadi, ya ce, "Ina da fatawa, ya Shugabana."
Shaihu dan Hodiyo ya amsa, "Allah ya sanasshe mu!"
Mutumin nan ya ce, "Ya Shugabana,. da me a ke miya a nan
kasarku?"
Shaihu ya ce, "Da kuka, da gishiri, da tosshi, da daddawa."
Mutumin nan ya се, "То, ashe sun sha bamban da na
kasarmu." Ya yi ban kwana da Shaihu, ya fita. Shaihu ya ci gaba
da sha'anin da ya ke ciki na jihadi. Aka ci kasashe, aka ba
wadansu tutoci, sai can bayan shekara biyu har an manta da
wannan mutum da ya yi tambaya, sai mutumin nan ya dawo, ya
sami irin kayan Hausawa, ya yi shiri yadda ba mai ganewa shi ya
zo bara waccan. Ya tafi wajen Shaihu ya gaishe shi, ya ce, "Da
me kuma?""
Da ya ke Shaihu dan Hodiyo al'amarin nasa ya yi nisa, ya tuna
tambayar bara. Ya dubi mutumin nan, ya ce, "Idan da wadata a
kan sa nama."
Ko da bakon nan ya ji haka, sai ya fadi ya nemi Shaihu dan
Hodiyo gafara, ya sallame shi ya koma garinsu.
"Tsakaninka da Allah, Allah ya ba ka nasara, ka taba jin
wannan irin labari na Shaihu Mujaddadi in ba yau ba?"
Musa ya ce, "Gaskiya dai, ban taba ji ba. Shin don Allah ko
kai ka kaga shi yanzu?"
Aku ya kada kai, ya ce, "Haba, Allah ya ba ka nasara, wallahi
ba yanzu na kera ta ba, ni ma haka na ji shi. Ko mutum na hauka,
irin karairayin nan da a ke wa tatsuniyoyi a yi wa tarihi kamar na
Shaihu Mujaddi dan Hodiyo? Haba, ai wargi wuri ya ke yi."
Musa ya ce, "To, ko da ya ke haka, kana tsammani wannan ya
fi wanda na gaya maka jiya ban mamaki?"
Aku ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ai ba gardama na ke ja da
113
kai ba. Wadannan al'amura ne na waliyyai, idan aka yi zurfi ciki,
sai a tasam ma yin sabo. Ba mu da wata ta cewa, sai Allah ya ba
mu albarkacinsu, amin, amin, amin!"
Musa ya ce, "Gaskiya ne, Allah dai ya kiyashe mu azabobin
Jumma'ar da ba ta da Asabar, domin alfarmar Shugaban
talikai!" Ya juya zai tafi.
Aku ya ce, "Af, Allah ya ba ka nasara, kana ya sami me?"
Musa ya waiwayo, ya ce, "Kana ya sami me fa?"
Aku ya cе, "Tambaya na ke. Kana ya sami me?"
Musa ya ce, "Me ka ke nufi da 'Kana ya sami ne?' Wa ka ke
maganarsa? Wane abu zai samu? In kana tambayar wani abu ne
ka faďi mu ji. Kai ba abin da ke dibarka sai samartaka. To, ni na
aske."
Aku ya duka, ya ce, "Allah ya huci zuciyarka, yallabai. Sauran
tambayar da na yi maka jiya, da na so in gani in ka iya iyad da
jawabin da ka fara ba ni, don ka ce tarihin da na bayar yanzu na
Shaihu Mujaddadi ba shi da bam
mamaki kamar wanda ka bayar
jiya."
Musa ya ce, "Wane tambaya
ka yi mini jiya?"
Aku ya bushe da dariya, ya ce,
"Jiya-jiya har ka manta, ranka
ya dade? Na tambaye ka shin sai
mutum ya sa me da me a jikinsa
za a san lalle ya yi ado, ba kushewa. To, ina ga wannan da aka yi
da shekara biyu?"
Musa ya dubi aku ya ce, "Hо
dan nema! Kai dai ba ka barin
ko ta kwana, duk inda mutum ya fito maka kana make kana
kallonsa." Ya duba haka sai ya ga gari ya waye, ya harari aku, ya
ce, "In don mugunta ka ke mini wannan abu, ba kome, Allah ya
isa." Ya shige gida.
Azahar na yi sai ga Sarki Abdurrahman ya aiko da dan bushara
an ci nasara, gobe kuwa tun da safe ga shi nan tafe. Musa ya
tambaya. "Ina Mahmudu? Ya warke? Dan busharan nan ya cе,
"Ai da ma ba abin da ya same shi, gobe ka gan shi." Kafin Musa
ya sami damar tambayarsa sai ya hau ya koma, don an ce kada ya
zauna. Duk gari ya rude da gude-gude, ana ta murna, Waziri ko
sai ka ce an yi masa mutuwa.
Magariba na yi sai ya kira wadansu samari hudu daga cikin
yaransa, ya gaya musu abin da a ke ciki duka, ya yi alkawari in
114
sun yi kokarin da suka kashe Musa daren nan na yau, ko da su
murde wuyansa ne, shi ko ya ba su fam ashirin ashirin.
Bayin nan suka ce, "Don wannan har wani aiki ne?" Suka
shiga neman kayan ado irin na mata suna sawa.
Aku kuwa da ya ke ya san haka zai faru, magariba na yi sai ya
ce wa Musa, "Yallabai, yau bai kamata a yi barci ba, sai mu
koma babban zaure, mu gamu da bayin nan a yi ta hira."
Musa ya ce, "Ai ko hakanan ne," Aka kai kujera, Musa ya tafi
ya kame bisa, bayi suka kewaye shi.
Jimawa kadan aku ya biyo, ya duba ya ga bayin nan ba mai
wani
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 12