a sume. Bana jin tun da nake a rayuwata na
taba karbar wannan marin. Rungume na ganni a cinyasa idanunsa
ya kada ya yi jajawur tamkar me cutar a polo hankalinsa a tashe
matuka, sai shafa min ruwa yake.
Amma dan tsananin masifa irin tawa da azababban kishin da
ya saukar min da wawan haukan na lokaci daya ina tashi ture shi
nayi na shiga kutuntuma masa sagi ina fadin sai dai ya sakeni aure
dani da shi ya kare tun da yasa hannu ya mare ni akan wata mace
mai kama da jaba. Na figi mayafina na yi waje, ina ta yi masa Allah
ya isa gamida gore-gore, sai gidan Abbana.
A gaskiya hankalin Abba yayi matukar tashi a inda aka yi sa'a
daya a lokacin hajiya Rabi ba ta nan ina zuwa na zube a tsakar gida
ina rabka kuka cikin sauri Abba na ya fito har vana tuntube ya
urrukeni yana ambatan Innalillahi wa Inna ilaihir aji'un. Humaira
waye ya mutu? Ko Auwalu ne ya rasu hatsari yayi ko ciwon farat
daya 'yan fashi ne suka kashe shi? dan Allah kiyi shiru ki gaya min
Humair ame ya faru ga Auwalun Hajiya lya ta shigo itama suka
hadu suna ta tambayata ni kuwa sai kuka nake da sheshshekar kuka
zuciya ta hanani magana zuwa can na nisa a hankali na bude bakina
amma magana ta da kar ta fito saka ye da tsananin bacin rai na ce.
Abba ni dai bana san Auwalu Auwalu ya cuceni ya gama dani
ya ha'ince ni yaci amanata na kara saka kuka me rikitarwa da gigita
mai tausayi. Abba na tsani Auwalu na tsane shi na tsane shi bana
san shi ashe Auwalu azzalumi ne basan Allah da Annabi suke yimin
ba daga shi har AlhajinA nan ne naga gaba daya jikin Hajiya Iya ya kama karkarwa,
ta kasa magana tsananin Sacin rai ya kama tsohuwar nan har ya
zama sanadiyyar yanke ji':i ta fadi Abba ya sakeni cikin sauri yayi
kan mahaifiyarsa ya shig ajijjiga ta yana fadin Hajiya dan Allah kiyi
hakuri Hajiya ana cikin haka Auwalu ya shigo nan dai ya taimaka
shi da Abba suka kinkimeta sai asibiti suka barni ni kadai a gidan
80
LUBABАН
sai koke-koke nake ina kuma tunanin halin da Hajiya lya take har
magariba shiru.
A nan ne hankalina ya kara tashi sai wajan karfe tara da rabi
naji tsayiwar motarsu, ni kuwa a wannan lokacin ko ruwa ban shaba
wuni guda nayi zuru-zuru na bala'in ramewa na fita daga cikin
hayyacina. Auwalu da Alhaji da kuma wasu mutanan dauke da
gawar Hajiya Iya Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un, kaga fa sanadi.
Ashe yanke jikin da tayi ta fadi jininta ne ya hau sosai har ya taba
mata kwakwalwa an yi kokarin a ceto ranta amma abin yaci tura da
misalin karfe takwas da rabi tace ga garin ku nan.
A lokacin da aka shigo da gawarta babu kowa a gidan sai ni,
dan haka Abba ya umarceni da in je in sanar da makota, na fita ina
kuka na shishshiga gida gida na sanar dasu, dana dawo ban tarar da
Yaya Auwalba ashe ya tafi ya fada a gidansu da gidan Alhaji Kabir
baban Mama kan kace meye wannan suma duk sun hallara gida har
ya cika kofar gida kuwa tuni babu masaka tsinke. Tun da nake ban
taba ganin Mama da Abbana suna magana ba sai a lokacin kuma
bata taba zuwa gidan shi ba amma a ranar su biyu na same su suna
gaisawa tana maza ta'aziyyay idelliiseni nsledne SUSA IUCEOLL
1616? nA kullum Mama a nan take wuni sai goma zuwa sha daya take
tafiya gidan ta ni kuwa Yaya Auwal sai kaya na ya kwaso min.
Hajiya Iya na da kwana biyu da rasuwa sannan Hajiya Rabi ta dawo
tun da aka yi wannan rasuwar babu wanda ya yi min magana
dangane da rigimat ani da Yaya Auwal, amma ban sani ba ko su
manyan suna tattaunawa a junansu. A ranar sadakar uku ne ma na
tarar da Mama da Abba a falonsa, suna maganganunsu, amma da
suka gannl sun yis hiru a ranar kuwa Hajiya Rabi kamar ta kashe
&kanta dan haushi. To ni dai na zargi akan maganata suke tattaunawa
amma babu wanda yayi min maganar in koma gida har sai ranar
sadakar bakwai da yamma naga 'yan uwa na kusa maza da mata sun
hadu falon bakin Abba su Alhaji Kabiru ne kawai zauné akan
kujeru amma sauran duk aa kasa suka zauna wato akan kafet. Abba
da Hajiya Rabi a gefe Mama da Alhaji a gefe sauran yan uwa na
itsakiya mai msgitis gitiz By Bzisylistan nea
sismiAn tura a kirani da na shigo naga Yaya Auwal makure a gefe
nguda ya sinkuyar da kai, duk ya rame kallo daya zaka mas akasan
08 81
WANDA YACE NAMIJI UBA2
ko wanka bai yi ba, nima a ramen nake a wannan lokacin kallan da
mukawa junanmu kadai zaka kalla ka tabbatarwa kanka lallai muna bala'in son juna kawai muna yaudarar kanmu ne, muna kuma wasa
da hankalin mutane na tabbatar da yawansu sun fuskanci hakan. Ni
ma dai na koma gefe guda na makure.
An bude taro da addu'a sannan aka kara yiwa Hajiya Iya
addu'a aka bawa Abbana dani hakurin rashinta. Alhaji Kabir yace
da Abbana ya yafe min kada ya dauka nice sanadin ran
mahaifiyarsa. Amma abinda yace a gurin yamin dadi, domin bai
nuna jahilci ba sai yace, "Haba dai Baba ai nasan kaddara, dama
Allah yayi lokacinta ya zo da zuwan Humaira cikin bacin rai da
rashin zuwanta ka'ida ne in lokaci yayi sai wa'adinta ya cika, dan
haka ni banma sa wannan a raina ba. Ni dai fatana su dai-dai ta
kansu dan ta koma dakin mijinta.
A nan aka nemi Yaya Auwal ya maida magana, ya maida
magana duk yadda aka yi, amma Yaya Auwal bai gaya musu irin
cin mutuncin da na masa ba shi da mahaifinsa kai hatta gore-goren
da na masa ma bai fada ba yarin ga magana yana kakkareni, ya
dauki laifin kacokan ya dora a kansa. Amma ni da aka tmabayeni
kiri-kiri na ringa hada masa karya da gaskiya, marin ma da yamin
ca nayi wayar video yasa ya zane ni. Nan aka shiga yi masa fada da
a karshe aka hadamu mu duka aka mana fada. Na fasan nice bani da
gaskiya, amma nayi kememe naki amincewa. Babu kunya babu
Isoron kowa babu kuma tsoron Allah na buda baki na murje idona
na furta bakar kalmar da ta tadawa kowa hankali. Dan kuwa ca nayi
niw allahi bazan koma gidan Yaya Auwal ba bana sanshi bana
kaunarsa ganin sama bana san yi da in zauna dashig ar ain zauna da
gawa.
A gaskiya ran Abba ba karamin 6açi yayi ba ya shiga zagina
yana fada yace dan naga ana nunan so, shi yasa nake wa mutane
iskanci ya kalli yaya Auwal cikin 6acin rai yace kai kuma Auwalu
in ka cika da ka saketa, kaje ka nemo yarinya ko 'yar gidan waye
zan aura maka ita, yarinyar banza yarinyar wofi da ina yabanki ashe
kema 'yar banzar kanki ce ya fizo wayar (cord wire) ya shiga
çalamin bulala ina ihu da kyar aka kwaceni, gaskiya ran Abba ya
Baci matuka. Amma don tsananin taurin kai irin nawa ban daina
82
LUBABАН
furta kalamun tsana ba ga Yaya Auwal kai har aka fara zatan ko ba
a hankalina nake wannan maganar ba.
Alhaji shi ya fara magana yace, kai ku tsaya kunga dai
yarinyar nan kusan ahannuna take tun tana yarinya, amma ban san
ta da taurin kai ba. A rabu da ita a shiga yi mata rokon Allah an ya
kuwa babu sa hannun makiya a ciki. A nan ne fa jikin kowa yayi
san yi ni kuma na sami makafa, a nan dai aka yanke hukuncin babu
maganar saki a barni kwana biyu za'amin addu'a da maganin karya
tambaya.
A kalla nafi wata guda ana min addu'o'I ni kuwa nasan kaina
nasan matukar bakin ciki ne da tsabar kishi suka gusar min da
hankalina suka kuma haddasa min tsana mai tsanani a zuciyata. A
duk lokacin da Yaya Auwal ya zo kuwa na shiga gaggay amasa
magana ke nan. Domin Hajiya Rabi in banda zuzzugani a kullum
babu abin da take yi saboda har ca tayi dani wai lallabani yake san
yi in koma domin ya rama wulakancin da na yi masa, saboda ta
lallabani na gaya mata gaskiya, sam na manta irin kiyayyar da take
yimin, ni a yanzu ba ni da babbar masoyiya irinta, saboda gani nake
ita take gayamin gaskiya. Can kuma ta karkashin kasa, tana t
ahadani da mahaifina kullum yana min fada yana fushi dani in nayi
kamar zan huce sai ta kara zugeni haka muke tayi da ita. Har sai da
tasa mahaifina yayi fushi dani.
Alhaji sau biyu yana zuwa yańa min fada yana kuma ban
hakuri, amma ni sai nake kallan shi a macuci,s aboda Hajiya Rabi
tace dani zai iya lallabani dan in koma kada uban Sumayya ya
tsorata yace bashi da rukwan aure a fasa aure, ai makamashi suke
san yi dani shi kansa Auwal din ba sona yake ba inda yana sona, ai
ba zai farki kara aure ba in banda haka in duba shi kansa Alhajin da
kuma Abbana su sun kara basu fishi kudi ba, da dadewar aure?
kuma tasa an yi istihara, ko na koma wahala zan sha dan ni zan
zama bora a gidan.
Akwai wani zuwa da yayi a lokacin wata na biyu a gidan na
gaggaya masa maganar da ta tada masa hankali sosai har ransa ya Baci, ya rubutamin saki daya. Ban taba yin nadama ba sai a wannan
daren na yi kuka kamar raina zai fita nayi da na sani mai tsanni na
fara gane irin zuganin da akeyi. Abinda yake bani mamaki a nan
83
WANDA YACE NAMIJI UBA2
shine ganin yadda mama ta rabu dani ko magana ta daina yi min
kuma rigimar mu da Auwal bata shafi nasu auren ba ko kadan.
A lokacin da nake zama idda ma yaya auwal ya dawo yana
bani hakuri, amma naki yadda, nace sai dai in zai fasa auren, shi
kuwa yace babu fushi. Ana saura kwana tara in gama iddata akа
sura masa aure. Gida ma keke da mata gwamna uban sumayya
yabasu suka tare naji aure nan so sai a raina ranar da aka kai amarya
kuwa ko ina gidan ne sai haka don kuwa kasa bacci nayi to kuma a
anne na dama me tsanani ta kamani, dan alokacin da ya dawo
ukika da na koma to amma bazan da yayi da nine yasa hudubar
hajiya rabi ta kara shiga raina. Na shiga zargi iri-iri.
Abinda yafi tadamin hankali bai fi ya fushi da Abba ya ke yi
min ba yayin da ita kuma Hajiya Rabi ta fara juyá min baya gashi
da kunya in koma gidan Alhaji da zama aduk lokacin da na tuno da
irin cin mutuncin dana yayiwa Yaya Auwal nakan zauna inyi kuka,
hadi da na cuceshi na cuci kaina dan duk da haka akwai wadan da
basa ganin lefina suke ganin lefin sa.
A ranar da na gama idda ta ne naje banki na karbo duk
sarkokina da nake kaiwa ajiya naje akawun dina da abba ya bude
min tun ina karama na kwaso kudi dubu dari biyu da hamsin babu
wanda ya san na karbo dare na yi gab da asuba na baro garin nayo
nan.
A
aya Fahad ya nisa gami da gyara zama yace, to aini banji Y
dalilin da yasa za'ace duk wanda yace Namiji uba ne ba
saboda abinda kika masa ya fi wanda yayi miki, kuma
dama abinda na ke san gaya miki na daga halayarku ku mata kenan.
A duk lokacin da Namiji ya dan bata muku tofa duniya sai ta sani,
amma ku sai ku shekara dubu kuna 6ata musu kuma hakika kishi na
gusar muku da hankalinku har ya tafi da imanin ku. Hakika abinda
kika yiwa Yayan nan nak: Auwal in da wani kika yiwa sai ya kusa
kasheki, ku mata kuna da babbar matsala wato manta alkhari sai ku
shekara goma namiji na dadada muku, amma rana daya in ya bata
muku sai a manta da kyautawar baya ku kirashi da "Da namiji ba
84
LUBABАН
dan goyo bane, ko kuce bashi da tabas ko kuwa kuce duk wanda ya kirashi Uba. A gaskiya ina ganin wannan ba dabara bace. An san akwai mazand abasa kyautawa amma wasu ai suna kyautawar.
Ya kamata duk ku hadasu ku batasu? Ke kanki kiyi tunani,
abinda ki ka yi masa ya dace ga gori a cikin mace kamar me?".
a
Yaya Fahad ni kaina nayi nadama mai tsanani daga baya. Shi
yasa bana kaunar, a tunomin abinda ya faru a baya. Amma
gaskiya abinda na ýiwa Yaya Auwal ban kyauta ba kuma inna tuno
da hakan, shi yake sani kuka. Hakika da zan iya kira ga mata, to
kuwa da na tara su na basu shawarwari, masu dama bai dace ace mu
mata muna wa maza wannan lakanin ba. Ni ina ganin jahilar kalma
ce da ya dace ayi watsi da ita. Dan kuwa dai-dai take da kalmar nan
da ake karin magana da ita, wato Dodo daya ake wa tsafi. Me mako
yanzu mu sauya muce Allah daya muke bautawa.
Yaya Fahad wannan kalma tayi tasiri matuka a zaukatan mata
wanda kwata-kwata bai da ce ba kuma wallahi maza suna matukar
hakuri damu hakurin da suke da mu ya fi wanda muke yi da su mu
mata mun fiye son kanmu da yawa.
Yau mu da muke karkashin kafar wani, kuma shi yake
aurenmu, amma mu dai burin mu su bimu, kuma wallahi duk gidan
da aka ce mace ce take mulki sai kaga gurbacewar al'adar gidan da
kuma rashin tarbiyya saboda mu mata duk tunaninmu maza sun
fimu. Nasan a yau in zan tara mata in gaya musu haka wata ma sai
ta tsinemin tace na bada mata saboda ba'a san gaskiya. Amma
wallahi ma fi yawan rabuwar aure laifin mata ne babban abu rashin
hakuri da tunani.
Yawanci hakan kuwa baya tashis ai an yi maganar aure. Sam
bama tunanin yau muma fa muna da kanne, kuma muna da 'ya'ya
mata in muka ce kowanne namiji ya auri mace daya to akwai
lokacin da mazan za su kare, 'ya'yanmu da kannanmu dajikokinmu
za su rasa mujin aure. Alal hakika mu mata ta 6angaran kishi mun
fiye san kanmu mu mu hana ayi mana amma in kanwarmu ce take
san wani to fa sai in da karfinmu ya kare saboda tsananin san kai.
Yau da ace mu mata zamu ringa taimakawa, ana auro wasu
wallahi da yau ba'ace muna yin kwantai ba kuma da mata basu
85
WANDA YACE NAMIJI UBA2
ringa zawarcin mazan wasu ba. To amma ina shaidan da jahilci sun yi katutu a zukatanmu.
Yaya hakika nasan mu mata muna da kishi don Sayyadina
Aishatu lokacin da aka ce za'ayi mata kishiya tana cikin tukin tuwo
dan tsananin rudewa ta dauki yashit a tuda a zatanta gari ne, to
amma da ta daure mene ne dole muji kishi ya kamamu. To amma in namiji zai kwatanta adalci ai komai mai sauki ne, azzalumin Namiji
shine abinji sai dai yawanci fa ku maza ku kuke haddasa komai a
gida janku gashi duk yawanci namiji me mata biyu magulmaci ne
yaje nan yace wannan yaje nan yace wannan yaje ya kushe wannan
yaje ya kushe wannan irin haka kuwa bashi da amfani, kuma hakika
shi ke kawo kallan banza a tsakani kowacce tana ganin tafi wata".
"Yauwa me yasa kina sane da haka amma kika tada
hankalinki, har kika yadda kuka rabu da mijinki?" "Babban dalilin
da yasa na ki zama a gidan mijina shine, kishiyar da zai mince sam
bata kwantamin a rai ba kaga na daya gata kwantaice, gashi kowa
yasan ubanta ba dan mutunci ba ne bin matan banza a cikinsa
kamar dar kare. Alhali Allah ma yace ka aura daga gidan mutunci,
kuma Anrabi ma yace in za ku auro ku auro daga ababan sanku.
Ya za a yi shi kuma a bashi mace ya aura, kuma duk matar da
kaga iyayen ta na magiyar a aureta tabbata suma sun gaji da ita. Ga
shegen taurin kant siya ga munafunci ga kuma miskilanci ita kanta
kamar zararriya. Bakikirin da ita fiska kamar ta mugun dawa babu
fara'a babu komai yadda take bakikirin a fuska hakama zuciyarta
take. Gashi sam bata da kirki ko kadan. Amma Annabi ma mai yace
ka auri mace dan kyanta da dukiyarta da danginta da kuma addinin
ta, amma mafi alkhairi ka aura dan addininta. To ita addinin ma da
sauki gashi uwa ubama sikilace, sai yawan laulayin tsiya. Ni
wallahi sam bata kwanta min ba kwata-kwata, wallahi Yaya Fahad
ba zancen wasa ba don tsananin tsufa hatta rankwafa, to ina dalili a
taru a tsofar da ni.
Yaya Fahad yasa dariya yace "na dai lura a takaice kishi ne ya
haddasa miki komai "To, ta iya yiwuwa kai kace haka, tunda baka
taba ganinta ba". "Amma duk da haka ina ganin dai kishi ne ya
rabaki da mijinki,ba wai laifi yayi miki ba". "A gaskiya kusan ince hakanne, amma fa Yaya Fahad Auwal fa alkawari ya yi min kan 86
LUBABАН
cewa ba zai taba yimin kishi ya ba, amma ya zo ya karya alkawarin
ina ganin tunda yaya Auwal ya yi min kishiya, to kuwa zai iya
sakina. Ni kuwa da ta kaimu ga lokacin da zai sakeni a wulakance
gara in san nayi dan wallahi an gaya min cewa kishi ne da 'yan gidan su Sumayya ga shegen asirin tsiya ka kuwa san uwartama
babarbariya ce? A'a ban sani ba sai yanzu da kika gaya min.
Ya kamata mu bar wannan maganar ni dai na gama fahimtar
dalilin da yasa mata kuke kiranmu mu maza ba uba bane. To amma
a gaskiya in bera da sata to kuwa daddawa da warinta. Humaira ya
kamata mu rufe wannan maganar mu gangaro tamu. Ni dai ina
ganin wani dirkeken rabon ne ya kawo ki nan Humaira tunda kika
dira a garin nan na kuma ganki naji nan duniya babu wacce na ke so
kamarki. To amma labarin ki ya dan rikitani, danni sam ba haka na
zata ba. To amma duk da haka na fahimci wani abu daga labarin ki,
ke mace ce mai tsananin kishi, wato irin matsanancin kishin nan da
yake rufewa irin ku da dama ido har ku manta abinda ya dace a
rayuwarku, ku zamto masu tsananin zato, ga duk wanda kuke zaune
dashi. To amma na gama gamsuwa da irin ladabinki da kuma
biyayyarki da kuma iya nuıa kwazonki ta bangaren nuna tsantsar
soyayya ga wanda kike so. Kuma kin zama me iya nuna kiyayya ga
abinda bakya so wannan shi ya nuna min cewa ke kaifi daya ce baki
kuma da ha'inci balle yaudara wannan shi ya kara inganta mins an
ki a raina.
Ya kamata ace nima kin bani goyon baya dari bisa dari, ki
kuma bani ishashshen dama dan in nuna miki tsantsar soyayya.
Hadin kanki kuwa shi zai taimaka mana wajen shimfida soyayya
wacce tafi wacce kuka shimfida da yayan naki Auwal. Zan tabbatar
miki da cewa ni malamintane na gaske. A gaskiya Humaira na
raina wayon yayan nan naki Auwal, da har ya biyewa zuciyars
akika kubuce masa ko da yake kuma fa mata sharrinku yawa gare
shi, a yau zaku ďaukaka da namiji ya saki jiki matuka har ya ringa
ji, tamkar ya fi sarki sarauta amma ranar da kuka birkice duk
nutsuwar mutum sai kun haukata shi. Har kuja a rada masa sarkin
mahaukata dan kuwa, ku sharrinku yawa ne dashi.
Ya kamata shima anada masa wannan mukamin, karkicena
ciwa uban 'ya'yanki fuska. To amma fa gaskiya samun irinku a
87
WANDA YACE NAMIJI UBA2
cikin mata sai an tona, irin ku ne ake kiranku bani bakwa tsufa, sai
dai kuyi girgiza ku sake sabon tofo. Saboda haka dan Allah zan
oke ki in har ki ka zo sanar da su Hajiya labarin ki ki kasance kin
boye wasu abubuwa na daga sirrin aure, dan in kika sanar da ita
umkarkin tona mana asirin mune, nan gaba in mun yi auren a ringa
raninmu fanko ko ya kika ce? Yayin da ya zura min ido dan yaga
in actin din da zata nuna. Yaci gaba da murmushi ya taso yazo
gabanta ya durkusa yace, ina so mu riki junanmu tamkar bamu taba
in aure ba ina fata zaki amince dani murmushi tayi gami da lumshe
do ta bude a gance, alamun ta amince.
Yayin da ta fito daga dakine taci karo da Shafa'atu Shafa'atu
ace da ita, yauwa daman kiranki zan yi yanzu kinga bamu gama
ikinmu ba gashi har Hajiya ta aiko tana kiranmu, saboda taga
yamma ta yi. Tace ko bamu gama ba mu koma gida gobe mazo mu
farasa.
Yaya Fahad ya fito shima daga dakin hannayansa gaba daya a
cikin aljihunsa, yana ta murmushi tamkar wanda aka aikowa da
sakon zuwa maka ya kalli Sahafa'atu yace ke Shafa kin gama aikin?
Tayi murmushi, amma can kasan zuciyarta takaici ne ya rufeta tace,
s'a ban gama ba Yaya ai aikin yana da yawa fa ya kalli Humaira
yana murmushi, yace, 'Humaira ya dai? Zaki iya ko kuwa, abar
nikin sai gobe koma kamata yayi in sami yara almajirai su share
gami da wanke gidan ko'ina da ko ina". Shafa'atu tace, dama Yaya
yanzu Hajiya ta aiko Sagiru ya kiramu, tace ko bamu gama ba mu
tafi yamma tayi gobe ma zo mu karasa. Ya kalle su yana murmushi
cikin kasaita yace Yayi kyau sai ku zo in mika ku gidan ko? Dan
nima fita zan yi yanzu. Sun yi tafiyar kurame sai dai jefi-jefi
Isakanin Humaira da Yaya Fahad suna kallan junansu ta mudubi su
kuma watsawa junansu murmushin jan hankali. Safa'atu dake gefe
guda duk tana lura da abinda suk eyi, amma tun da basu nuna
damuwarsu akan ta fahimci halin da suke ciki ba itam asai t abasar
da su kawai, tayi tamkar bata fahimci komai ba. Sai da ya sauke su
sannan yace to Humaira sai goben ko?" "To" tace, yayin da suka
shige gida suka biya sukr. gaida Hajiya sannan suka wuce dakinsu.
Yayin da suka shiga daki sai suka kafa hirar duniya abinsu.
Anan ne Humaira ta bawa Sahafa'atu labarinta, dai-dai da abinda ya
88
LUBABАН
dace ta sanar da ita. Hakika duk da bata ji duka ba, amma hakika
labarin ya tsimata. Sun kuma jima suna tattauna irinw annan
abubuwa. Shafa'atu tace, w allahi Humaira saboda irin haka har
tsoron auren nake ji yanzu fa akwai wasu kawayena su su biyu da
muka shaku dasu sosai da sosai. Aka ringa gulmata akan ni naki in
yi Aure alhalin ina da manema da yawa. Tun abin namin ciwo har
ya dawo bama ya damuna. To kin san wani abu wallahi su duka
suna gida duk an sako su ni na rasa dalilin da yasa aure yake yawan
mutuwa kome yake jawo haka yanzu oho".
"Yanzu kam yawaita sakin aure sai karuwa take. To amma in
muka duba abins ai muka ga kashi saba'in zuwa dari rashin hakuri
ne yake tsinke igiyar aure kashia shirin cikin dari kuwa dama can
bisa yaudara aka shirya abin ke kin yaudare shi, kin 6oye masa
shekarunki, da wani labarin naki da ya dace ya sani, shi kuma ta
daure ya miki karyar shime kudi ne, to kinga dole a duk lokacin da
gaskiya ta bayyana ki ga yadda tayi wuya".
"Yauwa kin san kuwa haka ta taba faruwa akan wani dan
uwanmu dan wa da dan kane muke da shi,w ato ya shiga neman
auren wata yarinya a lokacin ma da kudinsa da komai, cikin ikon
Allah da Allah ya yi ba abokiyar arzikinsa bace sai karayar arziki ta
sameshi yayin da sun gama shirya rayuwarsu tunda ga waje. Aifa da
aka yi biki aka yi komai, sai tazo gidan ba taga alamun yin wata
rayuwa ba, sai ta rena shi ta shiga yi masa iskanci iri-iri, har ya
ringa zargin ko dai bata da hankali ne, ke daga karshe sai da ta
kaisu ga rabuwa suna rabuwa ko wata biyu ba'a rufe ba Allah ya
jefo masa wata kwangila, nan da nan ya maida kudin sa har ma ya fi
da. Da yake bata da kunya sai ta zo tana rokonsa akan ya dawo da
ita.
"Ya Salam" Humaira ta ambata. "Amma lallai ba ma ta da
kunya kai Allah dai ya kyauta a gaskiya dogon burima yana kashe
aure matuka, saboda hangen yau wacce mijinta ya kaita maka ya sai
mata mota, ku kuwa kunanan kudin atamfar Nicam ma sai ya yi
taro. A'a baki damuda cewa ita waccen din wane irin zama take yi
da mijinta, wata ma ba zaman lafiya suke ba shi kansa mijin ba dan
Allah yake mata ba, yana yi ne don mutane su gani suce yana mata
ke kuma aduk ranar da gumi ta gumi kika kai kara ba lalle bane
89
a
WANDA YACE NAMIJI UBA2
yadda dake. Amma ke kuna zaman lafiya kuma ma ai ance ka auri
mai zuciya ba mai dukiya ba ai da yawa mata ba sa gane hakan
"Yauwa harkin tuno min da wani labari da wata kawata ta bani
wato ita kuma mijin yarta ne Allah ya hada ta da mayaudari mai iya
kissa kamar mace ban taba sanin namiji ya iya kissa ba sai a kanta
mu dai da ta bamu labarin mun yi dariya har mun gaji wato kin
gane ko? Ita yayar tata mutum ce mai surutu kin san duk mai surutm
da faran-faran bai iya munafunci ba. To ita kuma saurayin nata
shiru-shiru ne dashi, bayan an yi bikin kowa na mata murnar samun
miji na gari, ana cewa in futuna ta tashi to daga gareta ne. Shafa'atu
ta sa dariya sannan taci gaba da cewa wato in suna gida su kađai
abu kadan zata masa ya kamata ya doka san ransa, ke masifa da
bala'I kamar me duk kuma wanda ta gayawa ba lalle bane ya yarda.
Ya kasance duk sanda za su fita unguwa shine dan rukon jaka,
in kuwa cikin mutane ma suka shiga