Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
yake ji sabdoa abinda ya faru hakika da dai-dai da rana daya nasan Yaya Auwal zai min haka, da ban yadda dashi na sake dashi ba kaini a nan ma har dana sanin aurensa na yi na yi bakin cikin haihuwa dashi a lokacin dan tsananin kishi da haushinsa da nake ji inda ca aka yi ma 'ya'yan sun mace, kuma ya sakeni zan so hakan. 69 WANDA YACE NAMIJI UBA2 A gaskiya Yaya Fahad ina da tsananin kishi yadda baka zato maganganun da yawanci kawayena suka ringa gaya min sait a fara tasiri akaina, na tsani inji mace, tana da aure amma tana zagin namiji, wata ma har mijin da take aure. To amma a lokacin sai naji ba zagi ba in za'a tsine su ma, to nice kan gaba hakika kalmar nan da yawanci mu mata muke amfani da ita wato wanda yace namiji uba zai mutu maraya nan take tayi tasiri a kaina hakika sai yanzu na gane dalilin da yasa mata suke rike da ita tamkar kalmar kur'ani. A gaskiya duk matar da zata rike Namiji, tayi takama dashi ta riki banza, dan duk yadda kake zaune dashi zuciya daya, shi ba haka bane a zuciyarsa, komai yake kawo haka? oho. A zahiri na yadda da kalaman nan da suka yi tasiri a zuakatan mata da dama a cikin al'umarmu wato ta yadda suke amfani da ita wajen zagin maza san ransu, ba tare da kowanne irin tunani ba kalmomin kuwa sune da yawa, kasan ita hausa yawa ne da ita kowa da karin maganarsa da ya ga ya dace ya fada akan maza wasu suna cewa: WANDA YACE NAMIJI UBANE, MAZA BASU DA TABBAS, NAMIJI BA DAN GOYO BANE, MAZA RUMFAR KARA. Da dai sauransu. A askiya duk sai naji maganganun na sun dace dasu. Fahad ya kalle ta yace, "to shin zaki iya min bayaninsu daya bayan daya, wato dalilin da yasa ku mata kuke amfani da wadannan kalmomin don ku fc.fi abinda ranku ke so ga da namiji duk girmansa duk tsufansa, ko kuma duk yarintarshi? Hakika zan iya maka bayani dai-dai gwargwado ko kuma in ce dakai bisa abinda ni na sani ko kuma na fahimta. Abinda yasa mata suke amfani da wannan kalmar ta duk wanda yace namiji Uba ne zai mutu maraya shine. Duk abinda zaka yi da namji duk irin jin dadin da kuke yi dashi duk irin alkawarin da zai maka kai duk dai abinda zai maka sai kaga daga karshe yaje ya karo aure. Alhalin yabar mace ta sake sosai, har tan abawa makiya haushi ta sakar masa ragamarta da komai da komai, amma sai kaga daga karshe ya kwaso mata wacce bata isa bama ta hada kishi da ita ba ko yarinya kowacce ta girme ka koma wata nakashashiyar murmushi kawai yayi yace uhm ci gaba. 70 LUBABAН Amma kalmar nan ta maza basu da tabbas maza suna yawan amfani da ita ga wasu mazan sakamakwan tsabar rashin mutuncin da suke shirya musu, wato sai kaga namiji in zai aurcka, ya nuna maka babu yakai karya iri-iri kamar zai hadiyeka dan so kuma ya nuna maka shi mutumin kirki ne ya nuna maka cewa shi mai kula da gida ne da sauransu shi dai burinsa yaga cewa, ka aureshi amma da zarar kaje gidan sai kaga komai ya canza. Allah ya sama kayiw ata lafiyalau a gidan wasu kuma suna binka a hankalihar sai sun ga ka sami cki to fa sun san ka gama kafuwa sai su shiga shuka maka rashin mutunci iri-iri. Amma shi namijin da ake kiransa ba dan goyo bane, shine yayi dai-dai da kalmar da mata suke amfani da ita, wato da suke cewa baka shaidar namiji, marassa kunyar ma har su kara da cewa ko da Ubanka ne, kada kayi shaidar shi zai iya nuna maka shi mutumin kirki ne ya shigo yana muzurai da sauransu. Amma in kaga yadda yake hudawa kadangarun bariki kunne yana saka musu dan kunnen gwal zaka sha mamaki. Amma kalmar maza RUMFAR KARA shi ne sai ka sami namiji ka sakar masa komai naka ta dauro ma ka sai da kadarorinka ka bashi dan a taimaki juna, amma lokacin da ya fara samu, sai ya yayeka ya barka kuen na kadaka. "Amma kin birgeni hakika kin san laifukan maza. To shin-su kuma mata meye nasu laifin? "haba su mata meye laifinsu, ka taba jin ance mace ba 'yar goyo bace, ko kuma mace bata da tabbas? Kaga kuwa ai mu mata namu da sauki, dukt siya dai ai mace a karkashin mijin ta take". Dariya ya saka yace, "amma lallai kin birgeni, bisa kalamanki, amma fa bazan iya yadda da hakan ba zan fi yadda da ke idan dai kika ce dani baki san halinku na mata ba, kin fi rike na mazan. To da ance dake ni zan gaya miki goma naku dukda cewa ke kwaya hudu kika fada. Kuma da za'ace za'a sami macen da bata da wadannan halaye to da hakika ta juya namiji son ranta, ba tare da taci karo da laifin ko daya ba daga cikin irin laifukan da kika zana na da namiji to amma yanzu karasa bani labarinki tukunna. A hankali ta daga kanta ta kalli Yaya Fahad sanan tace. 71 WANDA YACE NAMIJI UBA2 A lokacin da na cika sati daya a asibiti sai aka sallarne mu zuwa gida tun da muka koma na daukewa Yaya Auwal wuta saboda ni kadaice nasan abinda nake ji a zuciyata gashi ina da wani irin hali bana kaunar bayyanawa kowa sirrin aurena ina mai jin kunyar in fito in sanar da kawayena ko makotana, saboda sauda yawa, su suke kawomin labarin halayyar maza, amma ni sai in yi tsalle in се ni miji na daban ne a cikin maza. Amma sai gashi rana daya ya kunyatani ya tozartani waini Yaya Auwal zaiwa kishiya hakika maza basu da tabas. A hankali na ringa jin tsanar Yaya Auwal na shiga raina na tsane shi tsan amai tsanani wacce tafi ta da da na yi masa sam naji gidan yayi min zafi ina zaune a dakin kan gado na daga kaina sama ina tunanin irin hukuncin da ya dace in dauka sai ga Yaya Auwal ya shigo. Na daga kaina a hankali na kalleshi, yayin da na tattarashi na watsar sannan na saki tsaki wanda yayi dai-dai da faduwar gabana. Hakika na san matsayin matar da takewa mijinta tsaki dan ko a zuwan da Annabi yayi Isra'l da Mi'iraji da ya kai ziyara gidan wuta yayi karo da wasu mata da aka zazzago harshenta aka kuma nadeta dashi ana gana mata azaba da ya tambayi laifin da tayi sai aka ce tsaki ta yiwa mijinta kai dole mu mata mufi yawa a wuta sabosa sam kanmu yayi yawa. Ni dai nan take na sinkuyar da kaina kasa duk jikina yayi san yi matuka. Amma me lokacin da kishin ya kara turnukoni sai ma na manta da dukw ata azabar Ubangiji da nake tunani shi dai a sanyaye ya zauna kusa dani yace "dan Allah in tambaye ki mana? Banza myi dashi bance dashi komai ba. 'Na dai riga nasan kina jina dan haka bana bukatar izininki, sai dai zan so ace kin bani amsa. Wai dan Allah me na yi miki kika tsaneni, tsana mai tsanani haka? A dai-dai lokacin da ni kuma Allah yake dada cusa min sonki a raina. Amma tabbas Yaya yama rainamin hankali dan me ba zai zabgamin mari ba, in san marina yayi da hannu in sosa. Da irin wannan dukan zuciyar da yayi mini". Ya ci gaba da cewa ek baki barni na sanar da ke gundarin abin ba, amma tashi daya duk kin bi kin dugun zuma tunanir ki, kin kuma hargitsa na kowa. Sanin kanki ne ina matukar sonki, don haka karin aurena ba yana nufin wargajewar soyayyar mu ba kin san Allah ni tausayin yarinyar ma 72 LUBABАН nake ji kawai tausaya mata nake, shi yasa zan amince da tayinta, domin in ceto rayuwarta dan bamu san hannun wanda namu 'ya'yan za su fada ba. A gaskiya kin ban mamami dan ni ina ganin kaf duniyar nan babu 'ya macen da nake ganin zan aurota in wulakantaki saboda ita. Barantana wannan da zan aura da bata kama Kafar kafarki ba haba dan Allah ki kwantar da hankalinki ina fatan kin gane. A gaskiya Humaira matakin da kika dauka sam bai dace ba asalima babu adalci a cikinsa. Humaira sanin kanki ne in har akwai abinda na tsana a rayuwata bai wuce bacin ranki ba. To danme ke ba zaki guji duk wani abu daka iya haddasamin 6acin nawa ran ba. A gaskiya abinda kike yi bashi da amfani sam-sam kuma babu wata hanya da zai amfanemu baki daya. Sanin kanki auren nan bani nasa kaina ba sani aka yi yarinyar nan ita ta fara aikowa tana sona, kuma ni ban ma san hakan zata kasan ce ba" E ai dama ku maza har abada bakwa neman mace ku aura sai dai in ita yarinyar ta zabeku. Ato ni dai ina sanar dake ne ban kuma damu da ki yarda ko kada ki yarda ba. A lokacin da ta aikoma ba ki ji haushin da najiba saboda ni kwata-kwata yarinyar bata layina bama ta cikin tsarin irin matan da nake lissafawa zan iya zama dasu, koda ban same ki ba. Baran tana wannan kyauta da Allah ya yi min na mace daya da daya kamarki yayin da ya dago kai ya kalleni ni kuma na akwar da kaina gefe guda. Wallahi ba wai cika baki ba, kema dai ai kin santa sam bata da wani diri ko fasali irin na mata da ya kamata ace wani da namiji ya ganta yace zaia ura, wannan ai dole ma ta rasa mashin-shini. Ga uban shekaru falka. To da in auri wannan a budurwa ba gara in auri bazawara ba in san bazawarar na aùra ba. Ana cikin haka kwatsam sai Allah ya hada mahaifina da mahaifinta, sanadi kuwa itace siyasa yayin da ni sam na ma manta da ita a rayuwata. Lokacin da Alhaji ya aikeni gun mahaifinta kallo daya ta yi min ta gane ni yayin da ni sai da tayi min bayani ma sannan na gane ta. Saboda shekara daya fa kenan, amma tsufanta ya fito sosai, ga uban muni da ta kara. Tunda ga lokacin sai tabi ta zakemin. Daga karshe ina ta sanar da mahaifinta, shi kuma ya yiwa 73 WANDA YACE NAMIJI UBA2 mahaifina magana shi ne fa ban san yadda suka kulla maganar su ba kawai sai ji nayi ance wai an yi min mata. Amma za ki sha mamaki in nace miki duk da cewa har sun sa rana amma Abban ki da Mamam basu san maganar nan ba saboda ya rasa hanyar da zai bi ya sanar dasu, w allahi Humair ani nace ba zan yi aure yanzu ba to amma sun matsamin. Daga karshema uban yarinyakiran ayayi ya ringa rokona akan dan Allah in rufa masa asirikada in bashi kunya dan har ya gama sanar da jama'a shi kuma Alhajina har ya kama min gidan haya inda zamu zauna. A gaskiya ni kaina ban san yadda zan yi ba amma ni a ganina yarinyar babu wani daga kai da zata yi miki, kinga dai bata fiki gata ba kuma duk gatanda za'a nuna mata ba'a nuna mata wanda a ka nuna miki ba to mai zai dame ki yarinyar nan bata fiki kyauba, bata fiki komai ba, to me ne zai dame ki a kanta. A yanda Yaya Auwal ya nunamin a takaice dai auren dole za a yi masa kai sam wannan tsarin nasa ba abin yadda bane. A dai-dai lokacin da na tuna da irin shawarwarin da yawancin kawayena suke gaya min. Demin sun sha gaya min cewa, duk lokacin da namiji ya shiga neman aure, ya shiga tsatstsara matarshi kenan da karya da gaskiya. Hakika hakan abin yake a raina nace to ni da yazo yake nuna min cewa matsa masa aka yi akan ya aureta, ni waya san abinda yaje yace. A zah.ri babu mamaki ma zuwa yayi yace da yarinyar ni ladan noma aka bashi ni, ko nima din yace mata hadin iyaye ne. Hakika namiji ga abin yadda bane kuma ma har yaushe za'a ce za a yiwa namiji auren dole. Yadda yanzu zamanin nan ya juya macen ma ta daina yadda da auren dole balle namiji. Tabbas na yadda da cewa tsarin ne irin na da namiji, kamata yayi kawai in shareshi dan hausawa ma sunce duk wanda yaje ya zagi wani a gabanka, to kuwa kaima zai je ya zage ka. Amma abin lura a nan shine, ta yaya za'a yi yace Alhaji shi zai tursasa masa akan wai ni a yimin kishiya hakika wannan da sake. Ai 'yaya ne dashi yaya Auwal din dan me ba zai matsa masa akan ya mallaki gidan kanshi ba. A'a sai dai ya nuna masa hanyar kara aure asalima shi kansa yayan ko sana'ar kirki bashi da ita motar ma gata ga kamarta, muna zaman rufin asirinmu amma ya tashi ya 74 S 1 2 D LUBABАН nemo aure, yace tilasta masa aka yi, wannan ma ai zance ne. To ma wai shin wacece ita yarinyar da zai aura, in ma dai yana sa rai da siyasar Alhajin ce wato in yana nufin siyarsar da Alhaji ne yake yi yake tunanin zai sami wani abu har yake tunanin aure, to Alhajin yn fadi in ga ta tsiya. A nan ne ya katseni da tunanina yace, wallahi Humaira da kin san yarinyar da baki tada hankalinki a kanta ba. Ni fa ba wani santa nake sosai ba wallahi ko an yi auren ma sakinta zan yi. A nan ne na dago kai na kalleshi hakika lallai Yaya Auwal ma ya raina min hankali kwata-kwata ya rainan wayona. "Ba ta wata bace illah SUMAYYA YAR GIDAN ALHAJI BATURE. Ai da yasan abinda zai faru hakika da bai sanar dani ba. Masifa, Bala'i, zaza'i su kawai naji suna fita daga bakina, mai makon in ambaci Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, kamar yadda musulunci ya koyar damu hakika na amince tsananin kishi yana iya fitar da mutum daga cikin hayyacinshi. Auwalu na ambata cikin bacin rai da dacin rai, hakika kayi kadan wallahi sai dai ka za6I daya tsakanin ni da kuma ita karasa wacce zaka auro min a matsay'n kishi ya sai wannan gogaggiyar da idonta ya gama budewa. Asalima ta fini ilimi kai kanka iliminku daya haba wallahi da sake, an bawa mai kaza kai, daga kai har ita kun girmeni, wato don kusani a tsakiya kuyi ta cuta ta kama rasa wacce zaka auro min saiw annan mummunar matar marar mutunci tsohuwar guzuma, wacce mutane da dama suke zarginta da yawaceyawacen banzan ta to wallahi ba zata taba sabuwa ba bindiga a ruwa. A gaskiya sai dai ka za6I daya tsakanin Humaira da Sumayya. Sinkuyar da kai yayi ya rasa abinda zai ce dani zuwa can ya dago kai ahankali yace, Humaira idan ki kenan kike kirana da Auwalu kai tsąye, to amma f aki tuna da cewa aljanata tana karkashin kafar mahaifana, to ta yaya za'ayi ki fadi haka amma fa kin san dai aure Kaddara ne ko?. Alal hakika nasan da haka, to amma ni ban dauki aure a Kaddara ba, dan me zaka ga yarinya kaji kana sonta ka zurfafa sonta a zuciyarka har Allah ya biya maka bukatarka sannan ka ce wai Kaddara ce. Ni abin da na daukesu a kaddara shine danka ya fada 75 WANDA YACE NAMIJI UBA2 wuta ko mota ta kaďe shi. Gidanka ya kama da wuta ko ruwa ya cinye shi ka haifi gurgu ko makaho ko kuwa kuturu ko gurgu, fa dawa rijiya da sauransu, it akanta asara duka aikin kaddara take shi ya sa ma Allah yace ka yadda da kaddar amai kyau da marar kyau. Amma a gaskiya ba zai yiwu ka sa aurenka a ciki ba, in banda haka ai da musulunci bai yadda da kayi istihara akan aure ba, dan kaga kyanshi ko rashin kyansa. Ni gaskiya na kása kaddara a abu biyu ni a iya fahimtata kaddara ta Ubangiji da ake cewa a yadda da kaddara itace, ka yadda da abinda Allah ya kadarta wato Allah yayi duniya ya kuma yi lashira ya kuma yi sama yayi kasa ya kuma yi halittocinsa iri-iri wadanda suka dace da zaman gurin. A sama ya halicci Malaʼiku. A kasa ya halicci bil adama, ya kuma hada da dabbobi da tsintsaye, tsutsotsi da kwari, yayida bbar gida da dabbar dawa yayi na ruwa yayi kan kasa. Da akwai halittun da za su rayu akan kasa akwai kuma haittun da za su zauna aruwa, kai da duk wani abu da Allah ya halitta. Haka kuma akwai wuta akwai aljanna. Ga kuma littafan da ya sauka rda maganganun da yayi to ana so duk mutum mumini ya yadda da wannan haka kuma shi yayi aljan. Akwai kuma Kaddara t amutum da dan Adam zai raya a ransa, ya kuma karfafa san abin, Allah kuma ya bashi ikon yi sanin kankane Yaya Auwal Bature shi ya yi jirgi na kasa ko na sama ko kuma jirgin ruwa. Haka su suka kirkiri mota ko kake, da Babur ya kuma yi hanyar mota don ta ji dadin murza tayunta. To amma Allah shi ya basu ikon yi ka duba kaddara irin ta mutum da yayi talabijin, aka yi bidiyo ga kuma talfon ga wutar lantarki, amma duk kaddara ce ta mutum Allah dai shi ya basu ikon yi. A lokuta da dama jama'a na jahiltar kansu sai su aikata abu suce kaddara ce wasu ma sai su sakankance ga ibadarsu, su ce in Allah ya kaddara su 'yan uwatane za su shiga wuta in kuma Allah yayi su 'yan Aljanna ne za su shiga a gaskiya wannan duk kuskure ne babba. Allah da ya halicci wuta da Aljanna ai kuma sai ya bawa mutum za6I bai kuma bamu a cukurkude ba, wato bai samu a duhu ba komai sai yayi mana shi dalla-dalla, fadan dillih wato ya sanar dakai hanyoyin da zaka bi dan shiga Aljanna ya kuma sanar damu hanyoyin da zamu bi don shiga wuta. 76 LUBABAН A sanan kuma dangane ga tsara rayuwarmu, wata tana ga Ubangiji, wata kuma tana garemu.A yau mutum yana tasa Allah na tashi akwai mutumin da zai tashi da kafafuwa daga karshe ya gurgunce ko ya tashi da idonsa daga karshe ya makance, wannan duk kaddara ce. Amma fa mutum ba zai je ya zabawa kansa matar banza ba, yace kaddara in haka ne ai Allah ya hore mu da mu auri mace ta gari, domin 'ya'ya yanmu su dace da uwa tagari. Akwai abinda yake bashi da amfani a kanka, ka kuma zafafa san shi a zuciyarka, har ka hada da rokon Allah in Allah ya soka da rahamarsa yayi ta kawo maka wasu hanyoyin dan ka farga kasan babu alkhairi a tare da kai to amma in ka zurfafa rokonsa da son abin sai ya biya maka bukatarka kaga duk halin da ka shiga ba za kace shi ya dora maka ba. Haka kuma akwai abinda yake alkhairi a gare ka ana nuna maka kana gudu, saboda kai kana hangen wani abu na daban, sai abin ya wuce kace dama Allah bai kaddara zan samu ba, alhalin ya baka kai ka gujeshi, hakika addu'a tana canja kaddara, marar kyaut a koma mai kyau kuma tana canja mai kyau zuwa marar kyau. Amma Yaya Auwal abin lura anan shine don me mutum baya hawa tsakiyar titunan mota ya shiga tafiya ta tsakiyarsu, yace in Allah ya kaddara za'a kaďeshi za'a kađe shi, in kuwa Allah bai yi za'a kade shi ba ba za'a kade shi ba? sannan kuma me yasa mutum ba zai hau bene hawa uku ba ya ga in ya biyo ta matattakala zai bata lokaci kawai bari ya diro in Allah yayi zai karye zai karye in kuma ba zai karye ba ba zai karye ba? To dan me yasa mutane ba su yin haka a'a sai mutum ya tafi ya nemo aure da kafarsa sannan ya roki Allah ya biya masa bukatarshi sannan a kirawo kalmar da kaddara? A gaskiya a sake tunani. Amma gaskiya kin bani mamaki Humaira kada fa zafin kishi yasa ki kauce hanya kina sane da cewa komai yana da sila, ita kuwa silar nan Allah ne yake kaddara ta shifa aure ha6o ne, mudun lokaci yayi sai an yi da mutuwa da haihuwa da kuma aure basa wuce lokacinsu kin manta sai kiga mutum tun daga Landan ya zo Afrika yayi aure ya koma saboda dama can Allah ya kaddara matar sace. A gaskiya ni duk bayanin ki na yadda da wasu amma wasu ban yadda da su ba in banda haka ya mutanan da suke yi su da daukan matan 77 WANDA YACE NAMIJI UBA2 ake a basu ba tare da sun je sun nema ba to in banda kaddar aya za'ayi haka Humaira ki tsaya ki nutsu, bana san imaninki ya wuce saboda kishi. A hankali ta daga kai ta kalli Yaya Fahad tace, yaya in gaskiya yar Allah ce ni kai na nasan aure kaddara ce. To amma kishi shi ya sani wannan zubar kamar kanya to amma duk da haka yana da kyau a duba batuna. To amma bazan gayawa mata haka ba saboda yawancinmu bamu da nutsuwa, da cikakken tunani, dan haka sai ya bawa mata da dama wata kofa ta shuka rashin mutunci suce, ai Humaira tace Aure ba kaddara bace, a'a Humaira ma ta sani takewa tayi saboda na taba cin karo da wacce ta taba gaya min haka. То amma a lokacin ban yadda ba sai yanzu. Dakishin ya taso min har nima nake adar da hakan. A hankali ya kalleta yayi murmushi yace, Gaskiya fa da yawan ku mata kuna sane da abu kuke takewa saboda kishi. Yanzu ki duba misalin zuwa maka ai dai tana daya daga cikin shika-shikan musulunci to amma ki duba ki gani sai kiga me kudin yana ta daukar niyya har ya biya amma wani abu ya zo ya hana shi zuwa kuma kiga wanda bashi da ko kwabo yaje wanna.n duk ba kaddara bane ato ku dai mata ku iya bakin ku kada za fin kishi ya kwashe imaninku "uhm ci gaba wallahi na matsu in ji dalilin da yasa kika gudo zuwa nan wannan ma ba kaddara bace ba to Allah ya yi zan aure ki ne shi yasa ina fatan kin yadda da maganar Hausawan nan da suke cewa matar mutum kabarinsa. A lokacin dana gama soki burutsuna, murmushi yayi yace to su kuma matan da suke gani suce suna son namiji wasu har su hada da asiri dan su auri mutumfa, shi kuma me zaki ce a kai nace ai wannan sai dai in Allah yayi dama can matarshi ce in banda haka in zata shekara tana sirinta, asirinta ba zai taba sawa a aureta ba, kuma ki duba ki gani hatta sakin aure lokaci ne sai kiga wasu suna wani irin zama kashe kansune kawai ba sa yi, amma suna tare, saboda Allah bai kaddara rabuwa ba wasu kuwa suna cikin zaman jin dadi kamar sa hadiye juna sai sabanin da bai kai ya kawo ba ya haddasa dalilin saki saboda Allah ya kaddara lokacin za'a rabu. Sakima kenan da Allah ya kirashi da halak, amma halak din da baya so. 78 LUBABАН A gaskiya Humaira kiyi tunani kuma da kike cewa wai sai dai in zabi daya ko ke ko ita to wannan kuma ya rage naki ke ya dace ki yanke hukunci, tun da ni nawa iyayen sun riga sun gabatar min da tasu dokar babu kuma yadda zan yi in tsallaketa. Don duk abuna ba zan iya sauya su ba mace fa? A nan ne fa na dugunzuma rain aya masifar baci, na dawo tamkar mahaukaciya na ringa zage-zage, nace aini gar ain rabu da kai daman can ba zaman Allah da Annabi kuke yi da muba daga kai har Alhajin, wallahi sai Allah ya sakamin macuta kawai sai da kabi ka kalallame mahaifina ya saki jiki da kai shine daga karshe zaka ci amanata ai nasan in ma auren za ka yi to kuwa da kudin ubana za ka yi shi shi Alhajin da kake takama dashi me gareshi, siyasa ta tatukeshi gashi kuma bai ci ba. Ba dole ya lallaßa ya jona maka 'yar gwamna ba, ko ya ringa samun kwangila. Aini wallahi ba'a burge niba in banda haka da a zabo maka yarinya danya sharaf mana ba wai tsohuwar da tayi kwanti aba har ma ta rankwafa saboda tsufa alhamdu lillahi ai dai bata fini da komai ba in dan kudin siyasa ce ai aikin banza ne gasu haram daidaine masu aikata gaskiya shi kuwa wannan gwamnan babu abindı zai yi in ba cuta ba daga shi har jama'arsu. Dan ba za su taba yin abinda Gwamna Shekarau zai yi ba gwamna mai adalci da sanin ya kamata kafa hujjojinsa akan islama kai gaba daya jam'iyyarma babu na banza har suka sauka kowa yabansu yake yi babu mai zaginsu amma me uban Sumayya zai yi tun yanzu shi Azzalumi ne yana ruguza zaman aure na dadaddun masoya balle ace ya hau mulki. A nan ne ya kwashe da dariya hakika da da farko na lura dashi ransa ya dugunzuma matuka kuma hakika hankalinsa ya masifar tashi, sakamakon gore-goren da na yi masa to amma ina fadar wannan kalmar ya tabbatar ba'a cikin hayyacina nake ba, wanda har ya sakida riya. To amma da ya ji naci gaba da yi masa bakaken maganganu na fitar hankali,s ai shima bacin rai ya fitar dashi daga cikin hayyacinsa. A lokacin ne fa na kalli tsabar idan Yaya nace dashi daman nasan Alhaji shi yayiwa Mama asiri don karta zauna a gidan 79 WANDA YACE NAMIJI UBA2 Abbana ya ga gara ya aureta ya kuma rungumeni hannu biyu don ku samu ku hau dukiyarsa ta Allah ba taku ba azzalumai. A nan ne fa ransa ya baci matuka ban ankara ba sai ji nayi ya saka rmin wani wawan marin da ya nemi tafiya da raina to mai ya rage ma don a kalla marin ya tafi da lumtashina na dan lokaci a kalla minti talatin na yi

Chapter 8 of 11