Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 11
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels WANDA YACE NAMIJI UBA NE NA Lubabah (Mrs Ado Dauda Bichi) WANDA YACE NAMIJI UBA2 WANDA YACE NAMIJI UBА 2 NA LUBABATU YA'U BABURA OMRS ADO DAUDA BICHD Z LUBABАН h MAW GODIYA GA: Sarki Allah da ya bani ikon wannan rubutu har na zo rubutu akan wannan littafi mai suna duk wanda yace Namiji Uba ne hakika mata da yawa sun raja'a akanw annan kalmar, manufata a nan shine mata su daina amfani da wannan karin maganar, dan kuwa hakikа jahilar kalmace nu nutsu mu fahimci marubuciyar. Ina kara mika godiya ga wadanda suke min jigilar da littafina har sai sun g aya fito wato Isah Mohd Tukur da kuma mai sayarwa Al'amin (Al'amin Bookshop). Godiya ta musamman kuma ga garzon maza Ado Dauda Bichi Allah ya kara mana so da yadda ya kuma kara mana 'ya'yanmu ameen. Abubakar Adamu (Baffa) Rukayya Adamu (Murfat) Rahama Adamu (Umaima) Zainab Adamu (Najla) 1 WANDA YACE NAMIJI UBA2 hima murmusawa ya yi cike da tsananin farin cikin, ganin S yanayin da na nuna, dan kuwa tabbas babu makawa ya gama gamsuwa da cewa na amince ko da yake tun farko mu muka yaudari kanmu amma ga yadda muke tafiyar da al'amuranmu, duk wanda ya ganmu, zai iya hakikancewa da cewa mu irin shakakkun masoya ne, wanda muka zamewa junanmu sassaken son da ka iyawa warkarwa dayanmu zuciya.st Shin wai dan Allah in tambayeki mana". Maganar yaya Auwalce ta doki dodon kunnena. Murmushi na yi gami da dan kada idanuwana kadan, hakan kawai ya gama gamsar dashi cewa tambayar sa nake jiran jebal so sb nivey snated sirlsd inno sSaboda me kike jin kunyata?" na yi mamakin wannan tambaya daga bakin yaya Auwal sai kace ba wayayye ba. Amma ai yana sane da cewa mace bata kunyar namiji, face sai da dalilai guda huduw ato soyayya, kauna, mutunci da kuma girmamawa wato darajja juna. "Son da hake miki Humaira ya wuce misali, kada ki dauka maganganun su Hajiya iyane suka haddasamin son ki a zuciyata. A'a ko daya, dan kuwa na dade ina tsananin son ki yadda ba kya zato, kusan in ce tun da na dora idona a kanki, na ji kibiyar son ki ta dirarmin zuciya. Shirun da nayi naki saurin sanar dake shi y abani damar kara fahimtar matsayina a gurinki. nse so, hakika yakan iya abkawa cikin kowanne yana yi, sannan ya an iya shiga, duk in da ya dace kada ki dauka ko aure bai halatta tsakanin mu ba dan kawai ina dan mijin babarki. Ni ba haka bane ke babu wani bangare da muka hadu, su Kadija ne dai suka haramta a gareni, tun da su Ubanmu daya da su ke kuwa uwarku daya dasu ya dago kai ya dubeni gami da sakarmin wani tsadadden murmushi yace, kin ga kin huta da futunan kannan miji ko? Kamar yadda akasarin mata suke yawan fada AECUcaiser eh ol Saboda haka daga yau nine sabulun so, ruwan kaunar da ya dace OWS in wanke miki zuciyarki ki yi tsai da ranki, mu shimfida soyayyar mu son rai, ta burge kowa ina fata kin fahimta. Na tabbata su kansu iyayenmu sun dade da fashim tarmu, kawai dai kyalemu suka yi ganin cewa ba mu yi magana ba, shi yasa suma suka yi watsi da mu, har sai mun gaji mun furta musu, da bakinmu. Humaira ina son ki so mai tsanani shi yasa ma na jingine kunyata waje daya naje na sanar da Abba komai dan kada amin sakiyar da babu ruwa. 2 LUBABAН Sanar da sudin da wuri hakika ba karamar dubara na yi ba. Humaira sanin kanki ne tsakanin miji da mata sai Allah ina tsoron ka da Hajiya Rabi ta juyar masa da ra'ayinsa, yace zai bawa Nasir ke. To amma yanzu fa tun da naje na furta masa da kaina, ai kin ga ya fi daukar magana ta da mahimmanci ya dago kai ya yi murmushi yace ko ba haka ba ne? Soyayya ba za ta taba tafiya dai-dai ba in har ana dari-dari da juna, dan haka dan Allah ki saki jikinki, dani mu shimfidawa kanmu rayuwa mafi inganci, wacce za a yi sha'awarmu mu kuma bawa 'yan bayanmu darasi". "So yakan iya haddasa komai, hakika hakane yayin da na fada a zuciyata, to amma me ina jin kunyar yaya Auwal kuma hakika ban san yadda za mu yi mu yi aure ba, ko kuma in har muka yi auren ya zaman zai kasance? An ya kuwa in wani na aura ba zan fi sake wa in nuna masa tsantsar soyayya ba, akan wacce zan nunawa yaya Auwal? Can wata zuciyar tace dani wannan ba abin damuwa ba ne. Siiii... naji yaya Auwal ya yimin wata irin launinnan da akasari 'yan gayu suke kiran 'yan gayu 'yan uwansu. Firgigit na yi, na dawo daga duniyar tunani yace, "Ya naga kin yi shiru, ko kina tunania wani ne, da kika« riga kika fara tanadarwa kanki? Hakika Humaira ni dai zuciyata na matukar sonki yadda bakya zato. Dan Allah Humaira in da wani abu a zuciyar ki kada ki ji kunyata, ki sanar dani komai, sanin kanki ne, sai muna tare da cikakkiyar nutsuwa, muke da lokacin da zamu tsaya mus hiryawa kanmu rayuwa, shi kansa so sai ya samu zuciyar da bata da kunci yake samun damar sakin jikinsa har ya kaf abishiyar da zata girma ta watsa rassan da za su kasance tamkar igiyar kulla soyayya. A hankali ya zuro hannunsa ya dafa hannuna gami da sakin wani murmushi ya kuma lumshe ido yace ki yarda dani. Sinkuyar da kai nayi cike da matsananciyar kunya baya da wani wutar murmushi da nake saki ban iya cewa komai ba. Don ina ganin hakan ma kadai ya isa ya haska masa zuciya ya hanzarta gano komai mai zirga-zirgar kai abinci ta zo ta dure wanda muka nema a kawo mana, har yanzu hannunsa rike da nashi, yayin da shi kuma ya dauki cokalin.abincin yana nema ya bani a baki. A hankali gami da nutsuwa na sinkuyar da kaina, yayin da na dan kauda fuskata kadan ya dan matsen hannu na dago kai kadan muka hada ido yayin da ya shiga murmushi gami da lumshe ido, ya dan gyada kai alamun inci abincin. 3 C WANDA YACE NAMIJI UBА2 Sake kawar da kaina na yi, a nan ne ya dauko cokali cike da abincin ya umarceni da in buda bakina da kyar na daure na dan bude kadan cikin sigar yanga na karbI kadan na shiga taunawa a yangance, gami da karkatar da kai ta sigar yanga. A haka muka kammala cin abincin muka fito mary na ta bacci a mota. Sai wajen karfe uku da rabi na yamma muka karasa gida muna gefe muna ta hira irin ta ma'abota begen juna. Ta daga kai ta kalli Yaya Fahad a hankali, ta dan saki murmushi tace, "hakika soyayya Rahama ce. Shigarmu gida muna dariya ita ta tasar da Mary dag abacci yayin da take kwance a kafadar yaya Auwal dakin Mama muka nufa kai tsaye yayin da muka tarar da ita tana yin bacci. Dan haka sai yaya Auwal ya wuce dakinshi domin ya gabatar da sallah. Nima alwallar nayi domin in sauke farali. Nan na yi istingifari laifin da muka yi na kuma yiwa Allah godiya da hadakaina da dan uwan. A ama bata tashi ba sai wajan karfe hudu a lokacin ina cikin M yin sallah, don haka itama alwallar ta yo ta shiga salar, zuwa can muka idar da sallar gami da shafa addu'o'I, sanan take taml ayata da cewa tun yaushe muka dawo? Na sanar d3 ita. Na kuma gaya mata cewa mutan gidan na gaisheta.”Da Auwal din kuka dawo? E dashi muka dawo. Mama tace ke dai Allah ya hada jinin ku dashi, tun da kuka zo hutunnan shine ya ke ta faman zarya da ke. Lallai taku ta zo daya sai kije ki dauki abincin, ki kai masa kema ki zo ki dauki naki abincin kici, ni na yi zaton ma sai dare za ku dawo? Nace Mama ai jikin iyan da sauki, kuma Hajiyar bata nan shi yasa muka dawo da wuri. Mama amma fa mun koshi da abincin wallahi munci abincin a can. "E in ke kin koshi shi ki kai masa mana kika sani ko zai kara. Bashi bama ko wani aka ce ki kaiwa abinci kada ki kara cewa ya koshi, kika san cikinsa, ko kuma in yana son abincin fa kinga, ai sai kisa ya-ji koshin dole gar aki bari abawa mutum in ya koshi sai.ya fada da bakinsa kinga baki shigar masa hakki ba ko? Nace "to". LUBABАН Mikewa na yi cikin hanzari naje na dauki abincin Yayan na nufi dakinsa, na yi sallama a lokacin yana kokarin fita, dan kuwaya gama shiryawa tsaf murmushi yayi yayin da ya kóma ya zauna akan kujera gami da amsa sallamata, mai aka kawo mana?" ya fada yana murmushi. Nima murmushin na sakarmasa nace," Mamace tace in kawo maka abincin ka". "Mama? Amma na ke ganin kin fi kowa sanin zanci ko ba zan ci ba" "Nima abinda na sanar da Maman kenan tun farko, to amma sai ta nuna min gara dai in kawo maka tun da ban sani ba ko zaka Kara cin abincin", "Haba sai kace wani tanki kalli fa uban abincin da na loda kasancewar kina kusa dani, sam na shafa'a sai da na ji alamun cikina na gargadina da tabbas na kara saka loma daya shi kuwa zai turo sauran da naci su dawo. Nan take na fahimci nawa cikina lodin da na dade ban yi masa ba. Na daga ido na dan kalleshi gami da murmushi yayin da na dauki kwanan da abincin da nufin in tafi. Murmushi ya yi yace, "Humaira zan fita shin mai zan sa yo miki?" Tambayar ta bıni mamaki, sai kace irin miji da matar nan, amma idan da ya zubomin gami da murmushin da ya ke yi su suka tursasa mamakina ya koma kunya. Dan haka sunkuyar da kaina na yi cike da kunya ba tare da na iya cewa komai ba. Ya mikomin mukullin dakinsa yace "ga makullin fakina nan Ajiya, dan yanzu in har kina nan na daina yawo da mukullan daki durkusawa na yi har Kasa nan na karba. Murmushi ya yi wanda har hakoransa, suka baiyana, cike da jin dadin yadda na nuna girmamawa a tare dashi yace "Ni zan fita sai na dawo. Tun da kinkis anar min abinda kike so, to ni zan sayo miki duk abinda na ga ya dace dake yayin da yayi gaba abinsa, ba tare da ya jira yaji mai zance ba yayin da ni kuma na shige cikin gida bayan na rufo kofar. Mama na tarar a dakin girkin, na ajiye abincin, nace kinga Mama bai ciba kuwa dama na gaya miki ya koshi". Tace "to ai shike nan an dai fita hakkinshi". "Yauwa Mama akwai aiki ne?" tace "a'a in ce ko sana'ar za'a shiga kije ki kafa wannan shegen baccin naki, murmushi na yi nace, "a'a dama sharace ya ya Auwal yace in yi masa, amma ya fita "To tun da ya fice ya za'ayi ki yi 5 WANDA YACE NAMIJI UBA2 masa shara?" "ai ya barmin mukulin dakin". "E lallai taku tazo daya har mukullin dakinsa ya baki, mukullin da ba'a ba kowa tamkar mai ajiyar rai a dakin, ai sai ki yi aniya ki share masa kafin ya dawo". Ta fadi hakanne ba tare da ta dago kai ta kalleni ba. "Mama zan dau omo da izal gami da tsumman nan da kike goge ban dakin Baba". Har bandakin zaki wanke masa? Lallai da kun taimaka danni ban san ba ko shi yake wankewa? Dan kuwa ban taba jin yace a wanke masa ba. Ni dai dariya na sa yayin da na je na kwashi kayan aiki har da tsintsiya na nufi dakin, dan in yi aikin. Mamace ta biyo ni da kallo, da alamun mamaki take yi, ko kuma tunanin wani abu. Ni dai wucewata nayi, ba tare da na waigaba, kada yin hakan ya haifar mata da wani tunanin. Har tayi saurin gano bakin zaren. Maganin kashe kwari na fara dauka na feshe bandakin dashi, dan nasan ba za'a rasa kananan kwari ba. Don gaskiya da gaskiyar Mama bandakin yayi datti da yawa sanan anjanyo kofar ban dakin na rufe don maganin ya sami damar aiwatar da aikinsa ba tare da iska ta dame shi ba. Sannan na shiga cikin dakinshi na gyare masa shi tas, kai maza Allah ya basu, sam basu damu da gyara mahallinsu ba ko da yake akan samiw asu masu zama su gyara dakinsu. To amma banda yaya Auwal dan kuwa za kasha mamaki in har kaga irin dattin dana fito dashi. Murmushi na yi yayin da na tsinci wata takarda a karkashin filonsa, yar siririya da ita ya rubuta ina son ki ki matuka Humaira! Na yi dariya sosai nace yaya bashi da dama sai kace wani karamin yaro ko ina nabi a dakin na goge hatta yana sai da na rabata da bangon dakin nan take dakin ya dauki sheki wani katan kwali da na ganshi irin kwalin frige din nan babu komai a ciki dan haka sai na sashi a bayan kyaure na zuba kayan wankinsa a ciki. Maganin da na fesa ba karamin aiki ya yi ba, wato ina gama gyaran cikin dakin ban daki na nufa, in da na tarar da kwari birjik a kasa, sai da nasa tsintsiya na share kwarin tas sannan na hau wankin bandakin duk wani datti dake manne da tayal (mables) din dake jikin bangon sai da na fitar dashi da taimakon Omo da kuma vi. Nan take bandakin ya dauki sheki da haske tare da fitar da wata ni'imtacciyar iska mai dadi da bata hadi da wani wari ko doyi ba 6 LUBABAН nasa tsimma na goge bandakin tas, kai baka ce an taba zuba masa ruwa a wannan lokacin ba. Minti talatin na dauka cif ina tsabtace bandakin kasan cewar ina da kazar kazar sannan kuma na dawo falo don shi bashi da dauda sosai ya kan dan kokarta ya dan gyara saboda kar da ya yi bakin kunya musamman ma ni. To amma tani ta kare tunda na gane dawan garin, duk wata boyayyar dauda ni na kawar da ita. Minti goma sha biyar ce ta taimaka min wajan kawar da duk wani datti da yake makale a falon, nan da nan kayan alatun da ke falon suka dauki sheki, kama daga kan na'urorin dakin zuwa kayanda suke danganci katako, shi kansa bangon falon saida na rabashi da yanar da zagaye shi. Ina gamawa naje dakin mama na dauko turaren wuta na kunnawa dakin, nan take ya gauraye da kamshi mai sanyaya zuciya na ja kofar daki na rufe, na nufi cikin gida. Mama ta kalleni tace, "wannan wacce irin sharace haka, kin shige dakin kin yi lif ko kuwa sana'ar baccin aka kama ba aikin ba. Na yi murmushi nace haba dai wallahi Mama aiki na yi sosai dakin yayanne dattin nashi yz yi yawa". "Ai fa gashi na jiya kamshin turaren wutana, ke haka kika bakakashi da yawa duk ya cike gidan. Dariya kawai nasa na nufi dakina. Mama ta gama duk abinda ta ke yi, muka zauna muna taba 'yar hira, muna ciki hira Alhaji ya dawo na hanzarta durkusawa na yi masa sannu da zuwa gami da gaidashi ya dubi mama yace yanzu da ke da Humaira ce kuke ta hira haka. Har da dariya sai ka ce ba yar fari ba. Tashi na yi na nufi daki na cike da matsananciyar kunya. Hakika da Alhajin ya lura ma a wannan lokacin da ya ga ne sabuwar tsurfar da na tsira ayanzu dan haka sai na shige dakina na yi zama zuwa can na dauko wani littafi da na siyo shi ban karan taba mai suna INUWAR BAGA RUWA. Na kara karanta sunan littafin nace, a raina lallai kam haka yake, wato ga dadi ga kaya. Karshen labarin na fara budowa, domin in ga in da ya tsaya a labarin. Mamaki ya kamani da naji tace ya kenan amma za ta nemi Lubabah ta warware mata, to amma naga na bugawa Lubaba waya rannan ita tace in nemi littafin in karanta, da na tambayeta ya 7 WANDA YACE NAMIJI UBA2 labarin littafin yake kai tsaye tace dani ai itama bata karanta ba. Na yi shiru ina tunanin ashe Anty Lubabah rufa ta tayi da maganar, dan karta gayamin yadda labarin yake? Ai shikenan dama Hausawa na cewa ana zaton wuta a makera sai a sameta a masaka sam abin babu kama kara karan to gurin nayi, a nutse sai kuma na gano hikima irin ta BILKISU YUSIF ALI wato dai tana so ta taya Anty Lubabah murnar haihuwar da tayi, ta sabuwar 'yarta mai suna Zainab mutanan da suke yiwa Lubabah cin cirodo a gida da na gaya musu abinda BILKISU marubuciyar Inuwar Bagaruwa take nufi. Dan tace dani suna zuwa suna bata shawar da ya dace ta sanar da BILKISUN. Nan take na jiyo da labarin na fara karantawa tun farkonsa. Zuwa can na fara jina ba dai-dai ba. Mikewa na yi na nufi bandaki na duba kaina yayin da na lura da halin da nake ciki, nan da nan na yi shirin wanka, sai da na gama kwalle kaina tsab sannan na fito na shirya, wata atamfata na saka, mai shegen kyau dinki ya dan sakeni kadan hakika.kayan suna yimin kyau sosai,s annan na zauna na tsiri tsifar kai. demin ta lura da bani da Mama ta leko tanamin magana, niyyar fitowa balle in yi sallah ta sameni ina tsifar kai tace, 'Humaira yanzu kan kike tsefewa? Har yaushe aka yi miki kitson? ku dai yaran yanzu shi yasa sam kanku, baya gaba baya baya, yau an yi kitso gobe an tsefe jibi, kuma ba za a kara yi ba sai in ya fara kadewa sannan a kara yi, Allah dai ya kyauta. To ki taso ki yi sallah, kowa yana kokarin sallah ke kina nan kina fama da kai sinkuyar da kai nayi ba tare da na bata amsa ba, kallo daya tayi min ta gane inda na dosa. Nan take ta saki tsaki tace. "Mu dai mutanan da abinda muka sani shine, muddin mutum yana haila baya tsefe kansa, saboda muddin mutum ya shiga wannan halin duk abin jikinshi najasa ne shi yasa ba a son tsefe kai ba kuma ga yankan farce, saboda ance a ranar tashin alkiyama komai naka zai dawo jikinka kin g aduk abinda kika yanke a lokacin kina cikin najasa to zai tashi, babu tsarki a jikinki, kinga gashinki ko farcenki zai tashi dabbare-dababre ke nan. Saboda haka ki kula". Yayin da ta juya tayi tafiyarta. Murmushi na yi na fada a hankali Mama ke nan ko a ina ta jiyo irinw anan wa'azin to yanzu in jinin biki ne fa ya mutum zai 8 LUBABАН yi? Barya masu yin zuba kamar kanya har sukai wajan kwana sittin shi ke nan babu su babu kitso babu yankan farce? To ni dai cikin ikon Allah ban taba ji ba an fada to, amma ba lallai bane in sani tun da yaushe na zo duniyar kuma shi ilimi ai kogine, shi yasa bincike yake da dadi, amma nima zan kara tambaya dan ya zamto ko zan fadawa wani ya zamana ina da kwakwkwarar hujjah kenan kasancewar na gama tsifar sai na ga ya zama dole in taje kan tunda ba zan barshi kamar kan mahaukaciya ba. Murmushi ta saki ta dago kanta a hankali ta kalli yaya Fahad tace, "Ai ba za'ace na kuskure maganar uwata ba ko?" yayi murmushi yace, "hakane". Amma fakisan wani abu? Nima fa ban taba jin wannan maganar ba, don haka nima zan ta ya ki tambayar duk wanda yasan hakan dan Allah ya gayamin in sanar dake, kin san shi ilimi kogi ne ko ba haka ba kinga sai in tambayo miki hadisin ko ayar da ta zo da hakan ko? Saboda komai yana bukatar hujjah. Mama na tafiya sallah ni kuma na fito a lokacin da na kammala da komai na nufi dakin girki gurin mai aiki na daıki abin cin Yayr. Auwal na kai masa na shirya masa akan tebirin cin abincinshi, hatta robar wanke hannu na kai masa ina komawa daki ban yi cikakken minti biyar ba bacci ya daukeni. Mamaki ya kamani jin ana yimin tafiyar tsutsa a kafata, dan kuwa su Khadija basa nan balle in zaci sune. Yaya Auwal ne.tsaye a kaina yana min murmushi, yace a'a kaga 'yar hutu kai mata kun ajin dadinku mu maza muna rama muna nema ku kuwa kuna daga daki, kuma shan A.C. rayuwa kawai ni bani mukulan nawa, nabar kaya a kofar daki. Murmushi na yi gami da kada idanuwa nace yaya ke nan sannu da zuwa abin da yasa yaya ya bani dariya shine ganin cewa yace wai suna rana suna nemowa, ko me yake yi oho? Na dauko mukullin na dan rissina na bashi, ya karba yana murmushi yayin da ya kawomin duka da mukullin aka yace, "Na yi zatan zaki zo ki budemin. Nace, "a'a yaya gaskiya bazan iya ba, in fa muka fita tare Hajiya ta ganmu?" "shine me, kuma? Ke wallahi kin cika tsoro dan wanan ba kunya bace to in kin sami dama ki leko ina san ganinki". 9 WANDA YACE NAMIJI UBA2 Murmushi na bishi dashi ba tare da na amsa ba, amma me? Kо minti goma bai yi ba da tafiya saig ashi ya dawo cikin sauri, ya shigo dakina fuskarsa cike da wani kawataccen alnuri, ya dan tareni da ido yana murmushi gami da kashemin ido yace, "Humaira shin ke kika gyara dakina ko kuwa tambayar ta ban mamaki wa yaya yake ganin zai share in ba ni ba. Na dan kawar da kai gefe guda nace nice cikin sakan daya ya duro gabana, ya durkusa har da dafan cinyoyina ya saki kawataccen murmushi, wanda shi kansa ya tabbatarwa kansa ya kawatar dani sannan yace (thank you my love) na gode kwaraida gaske. Murmushi kawai na yi gami da lumshe ido dan jin dadın kalmar da ya ambaceni da ita "Dan Allah ki taso mu koma dakina, gaskiya yau kinsha aiki kinga ba dan saboda wasu dalilai ba ai yau da kinsha tausa irin wannan aiki haka. Gaskiya naji dadi sosai, gaskiya irin kamshi da iskar dake dakin suna ratsani cikin nutsuwa kyanta ace mutum kusa yake da masoyinsa dan Allah ki taso", yayin da ya rike hannuna yana kokarin tayar dani. "Mama fa! kasanfa gaskiya ina jin kun arta", tun kan ya bani amsa muka ji sallamar Alhaji, sauri nayi ra fito dan in yi masa sannu da zuwa na je na durkusa har kasa kamar yadda na saba na masa sannu da zuwa na karbi jakar hannunsa Brife case na kai masa falonsa. A dai-dai lokacin da ya shigo yana tambayata ina Hajiya. Na ce ina jin tana can ciki gurin 'yan aiki, bari in kirawota." A zatona yaya Auwal zai shigo amma abin mamaki sai naji shiru na shiga cikin gidan banga Hajiyar ba,s ai da na shiga dakinta sannan na tarar da ita ta shiga bandaki tana wanka. Mama ki ya kamani da naga yaya Auwal yana dakin zaune bisa kafet a lokacin dana dawo dan in sanar da shi cewar tana wanka wani

Chapter 1 of 11