komai Yaya sirrin
mufa. Yace sirrinmu to waya ke ji? mu biyu ne fa. E ni dai don Allah
ka yi shiru cikin sauri na kammala da komai na shiga wanka cikakken
minti biyar na fito naje can yara kwalliyata ta gani ta fada saboda nasan
gidan mu zani amma duk da haka ban wani kure adaka ba.
"Zaiyana irin wannan kwalliya haka sai kace za mu yi zaman
gida". "To ai kai kaji Yaya Auwal in nayi kwalliyar ka furta in ma ban
yi ba ka furta ka dai san gidanmu zani ba gidan biki ba, to naji zo muyi
muci abinci ko ma tafi muna kammala cin abincin muka fice daga
gidan kai ka rantse irin fitar Ango da amaryan nan ne.
Zahiri ban ji ba dadi da muka je muka tarar Abba har ya fita, to
arnma babu komai tun da wuni na zo. Bayan mun gama gaisawa da
Hajiya Rabi ne take tambayata yara tace in Nur din ko basa nan
wallahi duk suna gurin mama, har Iftisan din kaddai in ce an yaye ta e
yau kwananta uku da yaye". "Shine ba a gaya mana ba, to Allah ya
rataya. Nace Ameen.
ta
Zan je gurin hajiya Iya in gaidata" To ai tana can akwance". "Bata
da alfiya ne?" ko ku sa tana dai hutawa ne na je na tarar da ita bayan
mun gaisa ne muka zauna muna ta hira. Ina yaran kuma? Iya
tambaya, wallahi duk suna gidan Alhaji, ke 'yar nan har da mai shan
nonon". "Iya ai na yayeta", "haba dai 'yar wata shidan Allah Hajiya Iya
ita taki shan nonon da kanta shi ne na yayeta, saboda in yi ciwon nonon
gaba daya in huta". To ai shi kenan Allah ya kyauta in dai baka mutu
ba to kuwa baka gaji da ganin abubuwa ba in banda zamani yaushe
yaro zai yaye kansa to Allah ya kyauta.
Zahirin gaskiya 'ya'yan yanzu kora da hali kukewa 'ya'yanku.
Nasa dariya nace kamar yaya Hajiya Iya "oho kuma”.
Zama nayi muna ta hira da ita nace wai ni ina Mary ne? tunda na
zo ban ganta ba" Ina jin sun fita da wannan dan dan sauda yawa tare
suke fita 'yar nan ai uwar nan taki ta dawo da halin nata irin na da shi
59
WANDA YACE NAMIJI UBA2
yasa aka ce ba'a yaban kuturu sai ya girma da yatsa shi kuwa mai hali
baya fasa halinsa".
"Zahirin gaskiya nima Hajiya Iya abinda na lura dashi kenan taje
dan kanta Allah dai ya zaba masa abinda ya fi alkhairi in Allah ya yaye
masa wahala sai kaga lokaci daya kamar an yi saka an yanke, Allah dai
ya kyauta shi dai Abba haka Allah ya shirya masa rayuwarsa "uhm ke
dai 'ya rnan bari, kullum dai addu'a nake masa Allah ya zaba masa
abinda ya fi alkhairi ameen.
Zuwa can da yamma likis sannan Abba ya dawo mun jima muna
hira, shima ya ringa nuna min rashin jin dadinsa na shiga harkar siyasa
nace to Abba ya za'ayi kasan duk abinda Allah yayi mutum zai yi sai
yayi sai dai mu taya shi addu'ar Allah ya zaba masa abinda ya fi
alkhairi.
Zaman da muka yi da Abbane muna hira yas ana fahimci, abinda
siyasa ryanzu ta ke ciki. Tabbas dole su nuna rashin jin dadinsu ni duk
ciki abinda na tsanama bai wuce yin harka da 'yan daba ba wai a yanzu
ya zama dole ace in har kana harkar siyasa to kuwa, sai ka ajiye ‘yan
daba saboda su ka reka daga ta addancin makiya to Allah ya kyauta.
Zu'va can Yaya Auwal ya zo shima mun jima mana hira dashi
daga kaishe muka yi sallama ya kawo kudi mai yawa ya bani yac e na
sayawa 'yar yaye alawa.
R
ranar litinin muka yi sallama da Yaya Auwal ya dauki Akayansa na sati daya ya nufi makaranta mun rabu cikin
tashin hankali da jimami amma kafin ya tafi sai da aka
dawo min da yara da kuma Khaidija da da farko mama bata yadda
ba tace ya duk za'a dauke mata 'yan matan a barta da mazan to
amma da kyar Alhaji ya shawo kanta ta amince ta dawo,
kasancewar ta gama karatunta sai islamiyya da take yi kawai, sai ya
zamto koda yaushe muna tare.
A lokacin da Yaya Auwal ya dawo weekend, sai itama
Khadijan ta tafi gida yin nata week end din, domin ta bamu fili
musha iska. Dan saban dan taya bera 6ari harda yaran ta tafi. Tun
da yammacin ranar də yaya ya dawo ya nemi ya hanani sakat, kai
ka rantse mun shekara bamu ga juna ba. Girkima kusan tare muka
shige shi dana gama ne na samu na gabatar da sallar insha'i daga
60
LUBABAАН
nan kuma na shiga wanka ai da na fito ko shafa mai ban barni nayi
ba barantana saka kaya baya ga body sprey dana fesa da farko naso
in ja masa aji to amma me da na fuskanci kwata-kwata ba ya cikin
hayyacinsa, sai kawai na sakar masa kan bori ya hau kada inje garin
jan ajin in kwasarwa kaina nauyi mai wuyar saukewa wato zunubi.
A zahiri nasan Yaya Auwal ya shiga damuwar da ba zata
musaltu ba yayin da ni kuma na wujijjiga a wannan daren, wanda
har sai da na dawo ina bawa Yayana hakuri, akan ya hakura haka
dan hausawa na cewa ciwo ne mai shiga lokaci daya sauki kuwa sai
a hankali dan na lura dashi wannan ciwon daya shigeshi ba mai jin
saukin wuri bane. Da kyar ya kyaleni na koma gefe ina huci yayin
da shi kuma ya zauna gefan gado yana mai da lumfashi dai-dai yana
mai shafa kai da hannu bibbiyu, kansa sinkuye a kasa tamkar mai
tunani zahirin gaskiya ba zan iya wanka ba a wannan lokacin dan
ina jima sai na shiga ruwan zafi, irin na masu jego, to amma ya
zame min dole in daura Alwallah tunkan in kwanta bacci kamar
yadda manzo (SAW) ya koyar damu.
A safiyar ranar sai na tsinci kaina da jin kunyar Yaya, sai kace
wata sabuwar Amarya saboda tun da muke, ba mu taba rabuwa ko
da kwana daya ba, a tsawan shekarun da muka yi to sai yanzu a
ranar yaya yace ai kuwa ya bar kwanan makaranta, Allah ya gyara.
A gaskiya ni kaina naji dadin hakan, dan kuwa hankalina ya fi kwanciya, gani da zargi na innanaha, ba kuwa komai bane ya kawo
haka sait sananin kishi, ni kaina nasan mijina ba mai yawace ya
wace bane, to amma sha'anin shaidan ako da yaushe in banda kitsekitse babu abinda nake yi.
A lokacin da zaßen siyasa ya gabato Alhaji ya tsaya a dan
majalisa aka shiga gaganiyar zabe akan dole dagani har Yaya
Auwal din muka dugunzuma harkar siyasa. Gwamnan da aka tsayar
na jam'iyar L.Y.B. ba karamin kauna ya nunawa Alhaji ba dan
haka muma aminci ya shiga tsakaninmu da mutan gidan. Wata
yarinya ko ince babba koda yake a yanzu girman ya hau kaina itac
ebabbar yar gidan Alhaji bature wato mai jiran kujerar Gwamna a
lokacin mai suna Sumaiyya ta nuna matukar kauna ga 'ya'yana
wanda hakan yasa daga ni har yaya Auwal din muka saki jiki sosai
da ita kasan ance maí da wawa gata da wayo. Tun da harta gama
61
WANDA YACE NAMIJI UBA2
digirinta na biyu yanzu ta shgia digiri na uku. Dan hakа
wayayyiyace sosai, sai dai akwai muni to amma wayewarta ita take
boye muninta kuma babu lefi dirarriyace.
A duk lokacin da take da lokaci to kuwa tana gidana tare da
'ya'yana. Tana bani girma na na cewa ni matar aure ce kamar yadda
nake bata girmanta a matsayint ana wacce ta girmeni sosai. Dan
kam in da tayi aure lokacin da 'yan da suke yi da sai ince ta haifeni.
Saboda ance wacce aka yi goyansu tare kwanan nan aka aurar da
'yarta ta fari. Ita kanta kannanta da yawa duk sun yi aure, harma
kannant amaza daga wansu sun yi aure.
A lokacin da harkoki suka yiwa Alhaji yawa sai ya rage bawa
Yaya Auwal kudi shi kuma yana jin kunyar tambayar Abba kudi
saboda a yanzu kusan ince Alhaji ya janyeshi, saboda yawan
aikensa da ya ke yi dan haka sai na shiga bashi kayan kwaldina
yana sayarwa yana biyawa kansa wasu bukatun na gida, da kuma na
makaranta. Hatta tangarayena sai da na sayar dasu na sayi irin
wanda ake yayi a lokacin 'yan kadan sauran kudin kuwa na
dankawa Yaya Auwal shima ya shiga hidimarsa da su. Badan
komai nayi haka ba sai dan nasan shima in har ya sami kudinsa
bashi da wani tunani sai ni da 'ya'yansa.
Akwai Munirat, wata makociyata da muka bala'in shakuwa da
ita, a gaskiya kaf makotana, ba bu wacce muke shiri da ita kamar ta
sai kuma wata da ake kira Saddika, to ita mutuncin namu samasama ne saboda tana da yawan surutu ita kanta bata boye sirrin
kanta ba balle na wani ni kuwa ina da wani hali na tsani in yadda da
mutum ya zo yaci amanata.
A gaskiya in na yadda da kai na yadda da kai kenan zuciya
daya, ba kuma na shayin in gaya maka duk abin da ke raina, sai dan
abin da ba'a rasa ba. Sai dai da zarar kaci amanata sau daya to kuwa
ni dakai har abada babu kuma abinda zaka taba min ka birgeni kai
ko zaka sadaukar da kanka saboda ni, zan kalli abin a munafinci ne
kawai saboda ako da yaushe kamin abu zan kawo wani zatan na
daban. Ta daga kai ta kalli yaya Fahad tayi murmushi tace ako da
yaushe ina sakin baki wajan sanar da kai halayyata ina gaya maka
ne Yaya dan ku fahimce ni saboda ku baku sanni ba.
62
LUBABAН
A yawanci lokuta in muka hadu da mata ana hira akan kokarin
nunamin cewa na muji ba abin yadda bane, amma ni na kan dauki
maganar a shirme da kuma tsabar jahilci. Duk matar da naji ta
ambaci wannan kalmar kuwa nakan ji raina ya masifar baci
matuka, w ato in naji mace tana fadin duk WANDA YACE NAMIJI
UBA NE ZAI MUTU MARAYA. A zahiri ni ban yadda da wannan
kalmar da mushimmaci ba, naga dai ni shekarata wajan nawa a
dakin miji amma babu wanda ma ya taba jin kanmu, kowa ya
banmu yake yi yayin da makiya suke jin haushi.
A lokacin gidana kusan zama yayi gidan kare maza. Saboda
duk wacce naji zata zagi namiji nakan hanzarta karewa. Akwai
wasu ma da suke cewa dani wai ni mace ce a fili amma a zuci
zuciyar maza ce dani, in raina ma ya so ya baci sai inga ai daman
duk wanda zai zam amai fadin gaskiya sai an nemi a bata shi
mutumin banzane za ka ga duk inda yayi ana son shi duniyar ce ta
zama haka duk abinda ka yi a zage yake.
A yawancin lokuta Sadika takan yawan bani shawara, wacce a
lokacin na dauketa gurguwar shawara. Dan takan min fada akan in
daina yawan sakin jiki da mijina zūciya daya, dan ta fahimci duk
abin da na samu kan in tuna dan cikina na tuna mijina, kuma hakika
hakane wai duk sanda ya sami kudin kansa aure zai yo. To amma ni
kallan mai zuga nake mata, dan kuwa yaya Auwal yasha ce dani
bashi babu aure har abada, kuma hakika na amince sam a lokacin
na manta da kalmar nan da hausaw akan cewa kana taka Allah na
tashi.
Amma Yaya Fahad za ka ga ban faye maganar kawayena ko
abokan Yaya ba, to a gaskiya ina da kawaye sosai, kamar yadda
shima yake da abokai sosai, sai dai ina baka labarin rayuwata ne
kawai, in da aboki ko kawa suka yi tasiri a labarina ba mamaki kaji
na ambato su.
A gaskiya in har nace zan yawaita kawo hirarrakin abinda ya
faru a tsakanina da kawayena ko tsakanin Yaya Auwal da abokansa
to kuwa zamu dade ban gama baka labarin ba wanda har hakan zai
jawo kosawarka duk da cewa yanzun ma na isheka da surutu, to
amma na kusa gamawa.
63
WANDA YACE NAMIJI UBA2
A nanne yayi murmushi yace haba Humaira ta Yaya labarin ki
zai gudureni alhalin abinda nake so kenan kuma ni kaina ina ta
daukar darasi a ciki. Duk da haka yaya Fahad kasancewar shi dan
Adam ajizi ne, da ace ku da yawa nake bawa wannan labarin sai
wani yaji ya gaji da surutai na, shi dai burinsa yaji dalilin da na
gudo.
Amma da zan sanar dashi yaji dadin zancen ko kuma ya gama
jin dalilin, sai kuma ya shiga jin haushin ta yadda ban sanar dashi
tushen labarin ba wani kuwa jima zai yi duk shirme ne.
Akwai wani yammaci ina zaune a falon gidanmu sai ga Yaya
Auwal rai a bace, kallo daya na masa nasan ya shiga matsanancin
tashin hankali. Dan haka a dole na 6oye nawa farin cikin da nake
ciki dan kuwa kunshe nake da matsananciyar murna wato Abba ne
ya aikomin da cewa bana ya biya mana makka ni da Yaya to amma
ganin halin da yaya yake ciki sai na boye murnar tawa, dan ban san
abinda yaya Auwal din yake ciki ba.
A sanyaye na karasa gabanshi cikin sanyin murya, tamkar mai
nuna nadama ga wani aikin da tayi nayi masa sannu da zuwa
fuskarsa kadaran kadahan ya dan boye bacin ransa ya amsamin to
amma ni nasan boye bacin ransa yayi. Naje na kawo masa ruwa mai
sanyi da wani lemon tumatur da nayiw ato tomotoas juns, wanda
yasha kayan kamshi da file bo na bashi, bacin rai yaso ya hanashi
sha, to amma nan da nan na shiga yi masa kissa da shshsafa gami da
dubarun kissarmu irin ta mace ina bashi lemon a baki a haka har na
samu ya dansha da yawa.
A nan ne naga ya dan jin gina da jikin kujera, ya rufe idonsa
ya saki ajiyar zuciya a hankali. Ban matsanta da yawan tambayar sa
ba a lokacin sai kawai na shiga 6ablle masa maballin dake wuyansa
na sakar masa fankar falon na dan kauce na bashi guri.
A lokacin da na fito sai nan da nan na tura yara gidan Munirat,
ni kuma na shige dakina, na je gaban mudubi na kara gyara fuskata,
na shafa turaren da nasan yayana Auwal na san kamshinsa, na cire
kayan jikina na saka kananan kaya dan sauda yawa yaya Auwal yafi
nuna sanshi ga wannan shizar na kara feshe jikina da turare mafi
soyuwa a zuciyar Yayana sanan na biya ta dakin girki na kwashi
farantin kayan abincinshi na shiga falon.
64
LUBABАН
A lokacin dana shiga cikin hanzari da kidima ya dago kansa,
wanda babu tantama nasan kamshin turarenne ya dokeshi,
murmushi na sakar masa a hankali, gami da kada ido sama-sama
fuskata na kunshe da alamun taya shi jimamin abinda ke damunsa.
Cikin hanzari ya maidamin martanin murmushina yayin da cikin
doki ya tashi ya tare ni nan da nan zuciyata tayi sanyi, hakika nasan
nayi nasara wajan fatattakar 6acin ran da ya nemi ya mamaye masa zuciya.
A lokacin da muka ajje kayan abincin ban yi aune ba sai ji nayi
Yaya Auwal ya rungumeni ya kuma kankameni sosai dan yadda ya
matse kirjina a nashi sai da naji alamun dukan kirjinshi ajikina mun
jima a tsayen yana rungume dani, gami da shashshafata yadda ransa
ke so, yayin da ni kuma ban kawo wani yinkurin saka masa cikas a
la'amarin saba saukar dumaman man hawayen da naji a jikina shi
ya hanzartamin daga kaina, Yaya Auwall ne ke faman zubar dashi
ya salam na ambata yayin dana dan zame daga jikinshi shi kuma ya
wuce jikin bango ya dake shi gami da kifa kai ahankali.
A nan ne na ruko hannunshi a hankali na zaunar dashi
adoguwar kujerar dake nan falon na zauna kusa dashi, sai da na
tabbatar jikina ya mannu da nashi sannan'na dubeshi a hankali nace
dashi. "Yaya ina fatan kana nan da sanin kaddara har yanzu ina
fatan kuma ka gamsu da hakan haba Yaya ka yi tunani fa komai
yayi zafi maganinsa Allah.
Allah shi kewa bawa maganin komai, kai kuwa Yaya maiz ai
tada maka zuciya haka ya nemi gusar da kai daga tunaninka ina
ganin ka fauwalawa Allah ya fi wannan dogon tunanin da ka iya
haddasa maka wani 6acin ran na daban shin wai mai ya tada maka
hankali haka. Alhaji ne kake ganin zai shiga tashin hankali, ko
kuwa? Ko kuma siyasar ce ta fita kanka wallahi yaya in har na
ganinka cikin bacin rai hakan ba karamin dugun zumanin tunanina
yake yi ba dan Allah koma meye ka fauwalawa Allah. Amma in har
da halin in sani, dan Allah ina san ka sanar dani in kuwa maganar
bata dace a gaya min ba, to dan Allah ka ware, ka kuma kwantar da
hankalinka ka fauwalawa Allah.
Ka yawaita ambatan innalillahi wa inna ilaihir raji'un ka kuma
yawaita istingifari, itace maganin yayewar kowane bala'i.
65
D
a
ki
in
Бa
ti
ka
y
WANDA YACE NAMIJI UBA2
Anan ma sakin ajiyar zuciya yayi sannan ya jawoni a hankali
ya dora bisa kirjinshi yana shaf akaina yace.
A gaskiya Humaira bazan iya boye miki ba ya kamata in sanar
dake ainishin abinda ke faruwa. Tun da wannan abu an dade ana
yinsa nayi kokarin in 6oye miki saboda halin da naga kina ciki,w
ato karamin cikin nan da kike dashi ina ga kamar tayar miki da
hankali a wannan lokacin ba karamin tashin hankali bane. Humaira
sanin kankine kin san ina sanki so ba na wasaba, ina kuma
kaunarki, kauna mai tsanani. Hakika, ina mai gudun bacin ranki a
ko da yaushe ko ba haka ba. A nan ne yayi shiru gamida girgiz
akai, ya kwantar da bayansa a jikin kujera yana girgiza kai cikin
takaici, wasu hawaye masu dumi suka zubo a kumatunsa.
A gaskiya na tausayawa Yaya Auwal, nasa hannu na goge
masa hawayen yayin da na isar da bakina anasa bakin muka shiga
tsotsa minti, na dan lokaci kalilan, nayi masa hakane dan in kara
kwantar masa da hankali. Nace yaya ina kara gaya maka da kabi a
hankali kada wani ciwon ya sarkake, shin Abba ne ya mutu ko
Alhaji ko kuwa Mama, kai koma waye ya mutu dan Allah ka
gayamin". "No Humaira babu maganar mutrwa a nan". "To zaben
da akayine aka fadi sakamakon basu ci ba ko kuwa? Ko kusa ba
haka bane Humaira ai fadar sakamakoma sai nan da kwana ukus
annan sun kara daddalewa.
Anma dai Yaya koma mene ne bai kamata ka tsaya kana
jamin raiba kaga nima in ada wani labari mai dadi, da nake san
sanar da kai, to amma na fasa. A nan ne ya dago kansa idonsa cike
da hawaye, yana murmushin karfin hali yace, Humaira ki sanar dani ROL
naki labarin insha Allah zan sanar dake nawa cikin gaggawa". "Alkawari yace ya dauka
"Abba ne ya aikomin cewa ya biya mana kudin maka ni da kai, kaga insha Allah bana damu za'a sauke farali. Ga mamakina sai
naga ya saki wani murmushi mai hade da hawaye baki daya. Ya
jawoni ya kara matse kaina sosai a kirjinshi, sannan yace dani. "Amma wallahi na ji dadi matuka, Allahya saka da alkhairi Humaira gobe zan turo Manu ya kaiki ki yiwa Abba godiya, dan nì bazan iya zuwa ba saboda ina jin kunyarsa matuka". "Kasan kuwa dama kwanan nan da najeni sai da yayimin wannan tambayar yake
66
LUBABAН
cewa wai kwana biyu baya ganinka, ko laifi yayi har yake cowa dan
ka daina zuwakayi masa aiki ai ko gaisawa kajo ayi tunda shi kansa
ya san abubuwa sun maka yawa.
Amma Yaya ai dai yanzu an gama zaben ya kamata ace ka
samu kaje kun gaisa, maganar jin kunyarsa ma ai bata taso ba yace
muje mu fadi sunan da ya dace ma abawa masu yin takardar gida
dan yana son ya dankamin wannan gidan ya dago kai a hankali ya
kalleni yace, Humaira duk wannan bata taso ba zan sanar dake wata
magana amma ina san kimin alkawarin ba zaki tada hankalinki ba
ki tsaya ki nutsu kiji abinda zan sanar dake Har yanzu kaina kwace
yake bisa kirjinsa yayin da ya shiga shashshafani, ya fara magana
kamar haka:
Alhaji yasha kirana kan wata magana a watannin baya da suka
wuce yana sanar dani wata magana, da naki amincewa wanda har
ya nuna 6acin ransa sosai da kyar Mama ta shawo kansa ya hakura,
har ya fara yimin magana. Amma ita kanta bata san abinda yake
hadamu ba. Amma sauda yaw ain taji musu ya kauraye tsakaninmu
takan shigowa tasa santamu, amma cikin ikon Allah bata taba
tambayata Jalilin hakan ba ban dai sani ba ko tana tamtayar Alhajin.
A gaskiya na fahimci Alhaji kunyar Mama yake ji na kuma san
ba zai iya tunkarar ta da wanan maganar ba, balle uwa uba ya
tunkari Abba da ita.
Alhaji ya yi min abinda babu yadda zan yi tunda mahaifina ne.
To amma daga karshe na fuskanci shi kansa dole aka sashi, bawai
yin kansa bane kuma uwa uba siyasa na neman sauya masa akida
kwata-kwata kuma wallahi Humaira jikina yana bani cewa da kyar
ne in zaici kuma wallahi in dai har ya fadi to sai dai muce Allah ya
kyauta.
A gaskiya an dade ana ruwa kasa na shanyewa kuma gero ya
dade da fitowa, to ya kamata a fitar masa da kai yau. A hankali na
shiga shafa kirjinshi, na kura masa ido na dan lokaci, na ce "Yaya
ka sanar dani ainishin abinda ke faruwa ni ina ganin wannan
zagayeyeniyar kawai 6ata lokaci ne ka gayamin yayin da na kura
masa ido kallo ido cikin ido nace" uhm ina sauraranka me ke
faruwa ne. 67
WANDA YACE NAMIJI UBA2
A gaskiya nayi mamakin yadda na ga nan take wani gumi ya
keto masa, kan kace meye wannan jikinsa ya fara jikewa da ruwan
gumin. A hankali ya buda baki yace Humaira AURE ZAN YI.
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un me kuma kunnuwana suke jiye min
ayau hakika da Yaya cakamin wuka ya yi na mutu da nafi so da
wannan bakin labari da bani da abinda zan kwatantashi da shi.
Amma ban iya cewa dashi komai ba sai kawai na tsame jikina
tsam daga jikinshi na mike tsaye da nufin barin falon saboda ni ban
ma san abinda zance da shi ba. TO amma me ga mamakina sai na
tsinci kaina idona ya rufe gaba daya ban fasa tafiyar ba ina kokarin
in fice daga falon ba tare da tabbacin ina zan dosa ba rangaji naji
ina yi wanda babu tantama jiri ne ke daukata. Ban ankaraba sai naji
nayi waniw awan karo da bango gagaram nant ake na dauke wuta
wanda ban farkaba sai a asibiti, shima ina kyautata zatan kulawace
ta musamman da na samu gami da taimaka wani azababban ciwon
ciki da ya shiga murda min, tamkar wacce ake shirin kwashewa
kayan cikin.
A lokacin dana farkama ban fara furta komai ba sai cikina.
Hakika cikina ya mikar dar.i daga dogon suman da nayi kankace
wannan Yaya Auwal yayi dirar mikiya a gabana, carab ya café
hannuna,w anda yayi dai-dai da fitar wani azababban ruwa mai
bala'in dumi daga jikina amma babu shakka ba fitsari bane, dan
kuwa babu wani yinkurin yinshi da nayi karan da naji Yaya Auwal
ya saka shi ya tabbatar min da cewa babu lafiya.
A nan ne naga wata Nos ta shigo aguje, tace yeeh! Kasancewar
Arniyace babu bakin salati, ko da yake musimin ma kara rya fara yi
kafin salatin ya biyo baya wanda a gaskiya musulunci bai horar
damu haka ba musulunci ya koyar damu cewa ya kamata duk wani
bawa mumini mai Imani ya kasance ya rike wata kalma ta alkhairi a
asararsa abin nufi ya zamana ya rike yawan fadar Innalillahi, ko
ayatul kursiyyu, ko dai wata addu'ar a duk lokacin da yaci karo da
abinda bashi da kyau ko mai kyau saboda ance in har ka rike abu ya
zama sarar ka koda salati ne to a duk lokacin da Mala'ikan daukar
rai ya zo maka abinda ka saba fada zaka ambata ko da tashinka aka
yi daga kabari. 68
LUBABAН
Amma in har ka saba da ashar, ko ihu to kuwa da shiz aka
tashi yayin da aka tashe ka a kabari, ko kuma Mala'ikun daukan rai
ya zo maka hakika saurin rabka ihu ko kwa ashar, a lokacin
gamuwa da abin tsoro ko kuma na alkhairi bashi da amfani saboda
bawa bai san tayaya Mala'ika zai zo masa ba. Abin nufi a nan bai
san da wacce irin siffa zai zo masa ba.
A lokacin da ta yi ihun, itama waje tayi sai gata tazo da likita
wanda sai a lokacin na fuskanci ainishin abinda ya faru gareni,
sakamakon ambatar blood din da na ji yayi, hakan kuma ya tabbatar
min da cewa, nayi barin cikina dan kimanin wata uku, idan ma da
kari baifi 'yan kwanaki ba.
A gaskiya ni kaina, nayi bakin cikin abkuwar hakan. Hakika
tsananin faduwar gaban da nayi ne a lokacin da Yaya Auwal ya
sanar dani labarin aurensa shi ya haddasa min 6arin cikina, da nake
tattalinsa a lokacin duk da cewa na dan same shi da wuri, to amma
ina san abuna sosai, kamar cikin fari. To amma babu abinda zan yi a
kai, tun da haka Allah ya kaddaromin.
A gaskiya na sha wahala sosai a lokacin kwanana uku a
asibitin, yayin da 'yan dubiya suka ringa zuwa Sumayya tazo
dubani ita da Kannanta a lokcin dauke da kaya niki-niki, wanda a
lokacin nayi matukar farin ciki da zuwan nata har suka tafi yaya.
Auwal bai zo ba.
A lokacin da ya zone na shiga yi masa bayanin zuwan su
Sumayyar, na kuma nuna masa kayan da suka kawo min. Halin ko
in kula daya nuna, sai ya nemi dasa min wani zargi na daban to
meye dalilin haka. Amma ban tambaya ba bai kuma furt awani
kalami dangane da maganar zuwan ta ba.
A nan dai muka zauna muna 'yar magana dukda cewa mun
kasa sakin jiki da juna saboda ni ina jin haushin irin halin dayake
shirin sani shi kuwa ban gamsu da abinda yake nuna min ba shin
fushin barin dana yi masa yake yi ko kuwa kunyata