sun baci yaro tun yana karami ake
cudanya dashi cikin datti, abin nufi shine kaine kana shayar da yaron
ka ko yarinyarka, to amma me? Wai a yanzu an zubar da koyarwa na
matan Ma'aiki da Sahabbai suma kuma suna dora ginshikin rayuwarsu
a kan abinda Manzo (SAW) ya zo mana dashi, shi kuwa ma'aiki baya
aiwatar da komai face abinda Allah ya umarce shi da ya fada ko yayi.
A yanzu 'ya'yan yanzu in suka sadu da mazajensu basu damu da
su yi wanka ba ko daura alwalah sai kawai a dauki yaro a dan kara
masa nono. Alhalin kana cikin najasa. A da ne ake yin in kayi zuna ka
49
WANDA YACE NAMIJI UBА2
auri mace mazinaciya amma a yanzu zamani ya canza da mutuncinka
da komai sai ka bige da auren marar mutunci, kuma a yanzu ba ka yi
zunar bama, amma zamani yasa danka ya tashi da zuna ko a biyoka har gida a bata maka 'yarka a barka da kukan zucі. Abubuwan da suke faruwa a wannan zamanin abin ya zarce
misali. Ban taba zatan zan ga wannan zamanin ba a rayuwata to duk
mai yake faruwa sai mu duba baya shi kansa aurena yanzu yinsa kawai
ake yi ba bisa tarbiyar musulunci ba. Nasirryya da yahudiyya su suka
bi suka cinkushe zukatanmu ta hanyar kallace-kallacen banzan nan da
ake yi suna watso da manufofinsu a hankali, su narkar da dukiyar su
shirya abin su kawatashi ba don komai ba sai dan su siye zukatan
al'ummar musulmi burinsu su sauyawa mutane akida su cusa musu son
duniya su nukusar da addinin islama mu kuma musulmin mun aji muna
gani amma duk da haka ba zamu daukarwa kanmu mataki ba.
A yanzu masu kishin abin kalilan ne in ma kai kana da burin dora
yaronka akan tarbiyya ta gari to wuyarta ya fara fita shi kenan ya shiga
zo maka da wasu akidu na daban. To da zaka yi ba ka da dama karaba
'ya'yanka da 'yayan makota. Addu'ar ma sai ka dade kana yinta amma
kaga shiru saboda kai kanka ka kasa tsarkake zuciyar ka.
A yanzu ku 'ya'yan da kanku ku lura koda yake baku san
zamaninmu ba, amma labari ya isar muku ada in zaka kwanta bacci
bisimillah kafa ashirin da daya in ka tofa ta wadatar ku kwanta lafiya
ku tashi lafiya babu mugun da yazo maka to a yanzu fa kunga ga
addu'ar ga maganin kafin amma sai a tsallako gidanka a ci maka
mutunci a kwace dukiyarka a kuma bata maka iyali, ko 'ya'yan ka
kana ji kana gani to dan me ba zamu binçiki kanmu ba.
A nan sai mutum ya duba shi kan sa da kansa ya kuma binciki
kansa ya yankewa kansa hukunci abin nufi kaima ba do hanyar halak
ka tara dukiyar ba, son rai kawai kabi.
Abu na farko da za'a fara lura dashi shi ne kai da ka gina gidan ka
tara dukiya ta habaka. To ta wacce hanya ka tarata? Son duniya ya
hanaku neman halak in cinikayyar ka ke yi baka da abin son da ya
wuce jiba kowa yasan mu'amalar banki haramunce kuma riba ake ci
sannan kai kanka in kana da sana'ar baka da abin so da kauna face kabi
duk hanyoyin da zaka bi ka nakasa abokin kasuwancinka ko
makwafcinka koma dan uwanka kai dai burinka ka tara dukiya ace kai kadaine kafi kowa, ka fito kana fankama ana maka fadanci da maula.
50
LUBABАН
A nan ne ta dan yi tari irin nasu na manya t akuma gyara zamanta
yayin da ni da Khadija muka yi shiru kanmu a kasa muna saurararta
muna yin nazarin abinda take kokarin ganar damu.
A gaskiya dole kaima masifu su yi ta barko maka shi kansa
kasuwanci an kasa tantancewa. A da mutum da ya karanta izawaka ya
wadatar masa yayi dukiya ya kuma sami rufin asiri. Amma a yanzu sai
kayi izawaka amma talaucinka na nan. Ita ayar Allah tana nan
yadda take, kuma da zaka tsarkake zuciyarka to da ta zame maka
garkuwa. To kai in kazo rokon. Tunaninka kawai, ka samu ka
muzgunawa talaka, kazo ka zauna zakayi addu'ar amma bakada tsarkin
zuciya. Ta yaya mala'ikun rahama za su zo kusa da kai, har su amsa
maka da amin ka ga dole kaima sai ka hada da iza kafa, manufa kaje
gurin da kafarka, sannan ka hada da iza baka wato ka kama maganganu
na karya da gaskiya kai dai ka sami kudin.da zaka kashe gararin
gabanka har abada ba zaka tsaya ka binciki kanka ba wallahi yanzu
zamani ya zo daya kamata dan adam ya yankewa kansa hukunci tunkan
gamuwarsa da Ubangijinsa.
A wannan zamanin ilimi ya wadata in ka 6ata ka sani in ma ka
gyara ka sani da ake cewa karshen duniya dan wuta yasan kansa, haka
dan alj.ınna ya sani, ai wannan zamanin ne mu a lokacinmu karyatawa
muka yi muke ganin babu yadda za ayi mutum yasan shi dan wuta ne
amma yaci gab ada rayuwa dai-dai kamar ta kowa. To amma a yanzu
zamani yazo dukw ata gaskiya abayyane take sai dai a taketa kunga na
farko ilini ya wadatu 'ya'yan yanzu ada sai ansa wahala ka bar gaban
iyayenka sannan ka sauke Alkur'ani mai girma mata kuwa sia a tare
arba'in ba'a sami cikakkun uku da suka sauke ba in kuwa akace danka
ya sauke ko kai ka sauke to fa babu abinda yafi wannan dadi a gurin ka
kuma girmawa ta shiga tsakaninka da jama'a kenan dan mu a
zamaninmu ma fadi muke ba mutumin banz abane yake sauke kur'ani.
Amma a wannanz amanin sai kaga yaro karami ay sauke ya iya
yasan baki radau musamman mata, sai a sauke kur'ani a makaranta,
amma in aka kasa a uku kashi biyu duk matane sai mutum ya sauke
kur'anin amma zuciyars aba akai take ba tana kan fadar yahudu da
nasara.
A yanzu 'ya'yan nan ku duba, ba shugaban banzane damu yanzu
anya ace kafiri ya mulki musulmi, tun da muke mun taba jin haka in ba
a wannan zamani ba. To ai ko lokacin da musulunci ya kafu yake-yake
aka ringa yi ana kafa daular musulunci, a yanzu kuwa yakin da duk
51
WANDA YACE NAMIJI UBA2
zaka ji an ayi sai kaga na son zuciya ne da san duniya na ji ana fadi
Malamai na nan suna ta addu'ar a sauke wannan shugaban na yanzu
Ubansengum yake ko uban shegu. To babban abu dai daga Malaman
har talakawan kasar mu gyara zukatanmu hakika in muka gyaru Allah
zai hadamu da shugaba na gari to amma yanzu manyan kasar sune
azzalumai basa san shugaba na gari, wanda zai kwatanta adalcin. To
amma babban abu shine mu gyara kanmu mu tsarkake zukatanmu
Allah zai gaggauta shiryar damu ya kuma hadamu da shugaba na gari.
A nan kuma ina san kara jan kunnenki ke Humaira, ko da gaba in
kin haihu kada ki gaggauta shayar da danki wannan nonon na farko,
wanda nasara suke yaudararku da ya fi lafiya ajikin yara. Dan Allah ki
matse su tas, ki wanke nononki kafin ki fara basu dan wannan nonon
shi yake sa 'ya'yan yanzu taurin kai.
A nan ne nayi dariya ance to amma Hajiya Iya har yanzu akwai
masu yin hakan, amma suna da 'ya'ya masu tsaurin kai, to su kuma ace
me? Ai kaji ki ko? Ku daman yaran yanzu ba dama a gaya muku
magana sai kun kawo wata hujjar kun kaf ako kun binciki mutum akai.
Dole dai sai kun nuna mu mutanan da bamu san komai ba to wadannan
kuma ai ya danganta da irin tarbiyarsu, in sun dauki a kida irin ta
bature da yake cewa, ko Ubanka ne yayi kayar kana da dama ka fito
kuru-kuru kace Baba karya ne, ai kinga dole tarbiyya ta gurbata.
Amma bari in bakiw ata addu'a ki ringa tofawa yaranki, in suna
kanana, kafa hudu a kunnan dama kafa uku a kunnan hagu. Insha
Aılah in kina karanta musu za su tashi da jin magana ai ita tarbiyyar ma
sai ka hada da addu'a don ka sami rabauta a ranar gobe kiyama. Tun da
ai akwai hisabi tsakaninmu da 'ya'yanmu, tunda suma amana ce aka
bamu. Kuma ita kanta haihuwar ai hikima ce ta Ubangiji in banda haka
ai da babu mai haihuwar wani, tunda zai iya. Da sai dai kawai a ringa
halittar mutum, da haka za'a tashi babu girmamawa, balle zaman
lafiya. Haihuwar da ake yi ai ita ta haifar da zaman lafiya.
A kAllah dole ka girmama iyayenka kuma zaka girmama na gaba
da kai, ka so dan uwanka, kaso danginka. A kuma yi zumunci.
A na cikin haka Yaya Auwal ya shigo yana ganin Hajiya Iya yace,
ai Hajiya Nur tayi fushi dan haka muke kiran jaririyar saboda me tayi
fushi to Hajiya iya ba gashi tunda tazo duniya ba kizo kin yi mata
sannu da zuwa ba". "To in banda abin Nur din ba sai ta duba yadda
garin yake ba ai jikin mai zuwa sannu da zuwan za'a duba gaba daya
muka sa dariya Khadija ta tashi ta fita ta bamu guri.
52
LUBABАН
A nan ma hirar muka zauna muna ta yi ta yi ta yi mana nasihu
hakika a yau daga ni har yaya Auwal mun karu da abubuwa da dama
sai da yamma likis direban Abbanmu Salale ya zo ya dauketa.
U
amana da Yaya Auwal ya kayatar kuma ya birge mutane sosa:, Z
saboda zama ne na gaskiya babu ha'inci muna son juna matuka,
kuma zaman mu ya tsonewa al'umma da dama ido Abba ya
jawo Yaya Auwal a jiki sosai da sosai don a yanzu haka shi yake kula
da yawancin harkokin sa na waje. Yayin da Abban nawa yake kula da
na nan Kasar.
Zamana ke nan a gaban mudubi domin fito wata daga wanka
kenan. Yaya Auwal yazo ta baya ná ya dafoni yace, Gimbiya zance ko
kuwa Beni bakya tsufa ki duba kiga yau kimanin shekarunmu biyar da
aure, amma ke kullum kamar amarya 'ya'yan nan biyu tamkar ba jikin
ki suka keto suka fito ba. Na yi dariya nace kai dai Yaya ako da yaushe
baka rabawa da tsokana. To gakinan bulbul kamar ba mai shayarwa ba
sai wani haske kike karawa kin san kuwa jiya ban iya yin bacci ba?
"Zauna zauna nawan ka gaya min abinda ya faru har yahana
gwarzon nawa bacci. Yace, kin san kuwa fakarain da nayi ba baccin
nake ba kawai na vi shiru ne sabdoa nasan in har na nuna damuwata to
kema ba zaki iya abccin ba, kuma bai kamata a wannan daren in hanaki
bacci ba. TO Amma ni abin da ma ya bani mamaki shine ta yadda na ji
shiru jiya ba'a binciki in da na jeba alhalin sai bayan sha dayan dare na
dawo.
"Zan yi tambayar sai na tuna da cewa amsar dai daya ce shi yasa
ma na fasa don ako da yaushe aka tambaye ka baka da wata amsa sai ta
kana kulla wata waya, in ta tashi zamu more, ita kuwa wannan wayar
har yau taki ta tashi muga irin wutar da zata tayar.
Zan so ace ka sanar dani abnda ya haddasa maka rashin baccin a
daren jiya. Wallahi ke dai bari Alhaji ne yana zaman zamansa mutane
suka zugeshi akan ya shiga harkar siyasa yanzu don Allah Humaira,
mai Alhaji yake nema, wanda da bai samu ba. haka kawai muna zaman
zaman mu cikin jin dadi da kwanciyar hankali zai taki shiga siyasa.
Alhalin yasan yadda siyasar ta dawo yanzu in banda zalinci da murdiya
babu abinda ake yi kuma in bai yi wasa ba haka za su kallameshi, su
53
WANDA YACE NAMIJI UBA2
kwace masa dukiyarsa ya zo bai ci ba su gudu su barshi tun da ita
siyasar nan bai tabá yin taba kuma ba harka yake da masu yi ba. To me
kike tunani in har aka ce yau ya shiga harkar nan ya zuba kudinsa, akan
siyan jaki mai kaho yana tura ribar a bankin asara.
Zahirin gaskiya ni abin nan bai kwanta min a rai ba kwata-kwata.
Naje na sami Alhajin nayi masa magana, ba ki ga irin fadan da yayi
min ba har cawa yayi wai ko bakin ciki nake, mai makwan in yi masa
addu'a zan zo masa da irin wadannan maganganu? Kin jífa wai yau
saboda abin duniya har Alhaji yana tunanin akwai abinda zan masa
bakin ciki akai a matsayina na dansa, dan ma na cikinsa. Yayin d aya
nemi ya tashi nace.
"Zauna, zauna to in banda abinka yaya Auwal meye na tashin
hankali a nan, kaima yaya ai dakai, hanyar da kabi ne wajen bada
shawarar bai kamata ba tun da kasan hankalinsa yayi gaba sosai to
kamata yayi kabi abin a hankali. Hakika duk abinda kake so yana da
wiyar banbaruwa lokaci daya. To amma abinda ya kamata sai ka bishi
ahankali, in Allah yayi ba zai yi ba, sai kaga abin ya ruguje in kuma
Allah ya yi zai yi to fa dole ya yi sai dai ka hadashida addu'ar Allah
yasa haka shine mafi alklairi.
Zai yi shugabanci niai tsafta, in dai har yaci ni na tababta da
wannan to mai ake gudu ga shugabanci ba dai rashin adalci ba? Amma
ai sanin kanka ne wajan adalci Alhaji bashi da rauni a nan in ka duba
tun daga shugabanci gidanshi. Dan su kanśu Shugabannin ko a lahira ta
shugabanci gida za'a fara tambayarsu don haka dan Alah ka daina
yawan sa abu a ranka bana son in ga kana ta da hankalinka, ka gane
ko? Gaskiya tashin hankalinka ba karamin rikitani yake ba saboda ni
ban saba ganin irin wannan ba.
"Zayyana sunan wani allo da ake yiwa masu sauka shin wannan
kwalliya da kika yarfo sai akce mais hirin fita yauwa ni dan Allah in
tambayeki wai me yasa a gida sai ki cada kwalliya, ki kuma kure akwati, alhalin babu in da zaki asalima dakin girki zaki shiga. Amma in
muka zo fita unguwa sai kiyi kwalliyar sama-sama ki dauko wata uwar bakar riga ki yaba, koma ki nade kanki tsaf cikin laffaya. Har gara ma in tare zamu fita kikan dan yi kwalliyar kadan?
Zan so ace kasan dalilin hakan ba sai na baka amsa ba. To amma
bari in yi, maka halin namu na 'yan Afrika dan Afrikanma nan Najeriya wato tambaya kan tambaya shin in zàn fita na cada kwalliya
54
LUBABАН
wa zan birge? Sanin kanka ne ko a shari'ance an fi san macc tayiwa
mijin ta kwalliya ba wai sai zata fit aba, to cada kwalliya ba.
"Zauna nan kan cinyata wallahi kamshin turaran nan naki ya
isheni. Ni da a tunanina gara ki ringa kure akwatin dan kar mutane su
dauka baki da kaya ka jika ko? Kaima sai kace mace to su fauka mana,
dan mutane nake saka kaya, to in baka sani ba ka sani a dane na yi
wannan saboda a lokacin ni Hajjace, kayan Hajja kuwa sai da tsafta, da
kade kura a kan kari, dan masu tayawa, su taya da kwarin gwiwa. To
yanzu fa? Kai ka dai na ajje a gaban dan haka kai kadai nake da
muradin cadawa kwalliya burina ka kyasa.
Zuro hannu ya yi ya danki wiyana ta baya sannan ya sakeni ya
jawoni jikinsa, muka kama dariya yace, Humaira komai naki yana
birgeni wallahi ina son ki shi yasa bana taba tunanin zan kara miki
wata ba.
Zo mu koma falo Humaira akwai wata shawara da nake san mu yi
da ke sai da muka koma muka zauna daf da daf a doguwar kujera yace
dani Humaira ina son muyi wata shawara ne, wato a gaskiya ina son in
nemi aikin gwamnati dan in ringa karbar albashi,w allahi Humaira har
kunyar abinda Abba yake min ake yi gaskiya gara in nemi aikin
gwamnati in Allah ya so sai in ci gaba da gudanarwa da Abba aikinsa
ba tare da yana biyana ba ko da yake dama abinda yake bani ya wuce
abinda ya dace a bani a aikina nasan bani kawai yake yi.
Zaman Humaira kullum canjawa yake yi in yau mune gobe ba mu
bane kada in sakankance zuciyat ata mace ba kuma zai yiwu ba ace har
girmana haka za'ayi tayi min ba, in kika lura hatta Alhaji ya fara rage
yimin wasu abubuwa saboda shima kullum nauyi hawa kansa yake yi
to bai dace ace a ko da yaushe muna karkashin iyaye ba kada dadin
yayi mana yawa ke ya kika gani ke?
"Zan so ace ka.... Ko da yake ka kawo shawara mai kyau saboda
ita rayuwa ba a dogaro da mutum shi kamfani mai zaman kansa
matsalarsa guda daya ce duk sanda ya karye to fa ma'aikatansa sun
karye, amma shi aikin gwamnati baya taba karyewa. To amma duk da
haka ni shawarata anan itace, ka fara kaiwa manyan shawara duk
abinda suka ce, dashi ya dace ka yi amfani ko ba haka ba e to kema
kince wani abu na je in kaiwa manya shawara amma da Abba zan fara
nace, wannan kuma kun fi kusa.
Zahirin gaskiya muna ji da junanmu yadda ya kamata, dayanmu
baya aiwatar da komai sai da shawarar wanin mu.
55
WANDA YACE NAMIJI UBA2
Zaman da jama'a suka ga muna yi na lafiya kuma babu wanda ya
taba jin kanmu yana kokarin boye sirrinmu, kamar yadda nima nake
6oye mana sirrinmu in da akwai babu mai sani, haka in babu babu mai
sani saboda duk bukatar da ka tunkaro dayanmu da ita zamu hada kai
mu biyawa mutum bukatarshi, dan kawai kada a gane saboda wani
lokacin yakan tashi bashi da shi, saboda yana da kawaici wajen yawan
tambayar kudi ko makamancin shi wani lokacin ma Alhaji ko Abba har
tambayar yaya Auwal suke yi cewa ko yana wata sana'ar a 6oye basu
sani ba.
Zahirin gaskiya Yaya Auwal yana da kokari sosai da sosai saboda
duk wanda ya ga shigar da nake yis ai ya rantse wani hamshakin mai
kudi nake aure. Dan haka na tsayawa mata da yawa a ransu mutane da
dama addu'arsu daya Allah yasa amin kishiya su ga yadda zan yi wani
lokacin in muna zaune muna hira da Yaya Auwal nakan bashi labari
ina ce dashi Yaya na rasa abinda na tsarewa mutane sai su yi ta yimin
addu'ar Allah yasa amin kishiya su ga yadda zan yi sau da yawa sai
yasa dariya yace, ai mutane ibilaisai ne duk in da aka ga zaman lafiya
burinsu daya shine a wargaza kawai.
Zamana dake Humaira ai ya fiye min zama da matan duniyar nan
ke ni bani ma da ra'ayin kara aure a rayuwata burina ni daman shine
mace daya ta isheni a rayuwa, kin san Allah bana san hada matan nan
azo ana ta haihuwa, wannan uwarsa daban,w anan haka. Ni ina
sha'awar inga 'yan gida daya uwarsu daya ubansu daya. A duk lokacin
da ya fada min nakan ji dadi sosai matuka in kuma kara sakin jiki
dashi sosai da sosai.
Zaman da muka yi dashi zama ne na lura da dangana, gami da
hakuri da kuma kawaici, gami da taimakon juna, wallahi Yaya Fahad
ko nawa na samu bana kyasyin in bawa mutumin nan ganinc ewa
shima in ya samu ya kan yi min abinda ya dace. Lokacin da yakai
shawarar ya nemi aikin gwamnati sam hana shi aka yi dan su suna
ganin 6ata lokaci ne sai dai ya sami tasu shawarar ta ya koma karatu.
Dan haka nan da nan ya nemi adimition cikin ikon Allah ya samu.
Zaune nake a falo yara duk suna bacci a lokacin wajan karfe biyu
da rabi na rana, sai ga Habib da Khadija sun zo cikin doki da murna na
tare su. Nan muka gama gaisawa na gabatar musu da abin ci da kuma
na sha. Na tambaye su mıtan gidą kamar yadda suka tambayeni yarana
na sanar da su suna bacci suma sanar dani suka yi cewa suna nan lafiya
nace, ina Maryam, Khadija tasa dariya tace, "ai yau satin Maryam daya
56
LUBABАН
a gidan Abba rannan ne da muka je gaidashi shine ya rike ta a can da
har Mama tace aje a karbota Alhaji ya hana kamar wasa nake ce da
Alhaji wallahi Alhaji Abba yana san Maryam har ca yayi da zaka bashi
ita da ya dauka, ya sata a makaranta har muna cewa zamu sanar dakai
amma sai yac emu yis hiri wai ko mun fada Maman mu ba zata yadda
ba.
Zaunar dani yayi a falonsa Yaya Humaira yace in zauna ya buga
masa waya ya tabbatar daga bakinsa yana buga masa wayar suka gama
magana, a washegari kuwa aka hada kayanta aka kai mata can. A
takaice dai maryam ta koma gurin Abba da zam ana dindin din. Da
farko mama taso ta tada hankalinta sosai dan da har ca tayi zata bar
gidan to amma yanzu an dai-dai ta. Dan Allah Yaya Auwal bai gaya
miki ba? ai kuwa shi ne ma ya ringa bawa Mama hakuri.
Zamana na gyara nace, lallai ma yaya Auwal wallahis am bai
gaya min ba, amma ina jin baya so ya gayamin ne dan kada hankalina
ya tashi, amma ai gobe ma in Allah ya kaimu zamu gidan Abban dan
mun yi kwana biyu ba muje ba ranar da muka je can muna cewa zamu
biya ruwa ya hana, Habibu yace wai ke Yaya Humaira me ya sa har
yanzu ba zaki daina cewa Yaya Auwal Yaya ba?
"Zai yi kyau kasanar dani dalilin tamba.yar". "Gani na yi yanzu
mijinki ne". Da ya zama mijina kuma sai na girmeshi ko? To ai duk da
yana mijina Habibu ai ya girmeni ko? Kaga kuwa dole in kirawoshi
yaya kaima in kayi aure ba sai kasa matarka ta kirawo ka da yaya ba?"
Na fada ina dariya yayin damu duka mukaci gaba da yin dariyar a daidai lokacin da Yaya Auwal ya shigo sallama yayi kawais annan ya
kalleni yayi murmushi yace lallai Humaira duniya tayi muku dadi irin
wannan dariya haka?
Zama yayi mukaci gaba da hira dashi ya dubi habibu yace kai ka
kuwa sanar da ita cewa jiya Alhaji ya tabbata dan siyasa. Dan har an
bugo fastoci (Posters) shiru yayi saboda yawan surutun da ake yi masa.
Nayi murmushi nace to yaya Allah yasa hakan shine mafi alkhairi daga
cikin abinda Allah ya 6oye. Nan dai muka zauna muna ta hira, har
yamma likis, Khadija ce ma ta dora mana abincin rana a ranar misalin
Karfe shida da kusan kwata ne Manu yazo ya daukesu ya maidasu gida.
Nan Yaya ya zauna yana bani labarin zai fa fara zuwa karatu a 22nd
March in Allah ya kaimu nace Allah ya bada sa'a.
"Za fa muje gidan Abba gobe, dan haka ki tashi da wuri ki shirya
ba wai sai kin bata mana lokaci ba" nace "to wai shin sai yaushe zaka
57
WANDA YACE NAMIJI UBA2
fara zuwa makaranta?" Ranar litinin dinnan insha Allahu, sai dai ina tunanin yadda zan ringa tafiya makaranta ina barinku dagaweekend saі weekend. A to ba sai ka fara yin bodin din ba". "To kin sani ne wallahi in har nace day zan yi to kuwa karatun nawa zai zamanto gashi ga yadda yake saboda muddin muna tare ina kuma kallon idanunnan naki to kuwa babu abinda zan iya aiwatarwa, alhalin kina kusa dani. Amma kinga inna yi bodin din na fiyin karatu" "ai shike nan Allah ya za ba
mana abinda ya fi alkhairi", "ya kuma bani sa'ar karatu ba
Zaman da muka yi muna ta hira a nan na fuskanci sam-sam Yaya
Auwal bashi da ra'ayin 'yan matan jami'a. Dan a cewar sa duk yawancinsu, sun dade basu yi aure ba, kuma gashi sun waye matuka,
idan su kuma ya bude sosai, ya dai ringa kwsilemin 'yan makarantar ta yadda hankalina ya masifar kwantawa saboda nasan Yaya Auwal kaifi daya ne, bashi da abokin washi.
Zan kuwa tambayeka na manta wai shin Alhaji a wacce jam'iyyar
ya tsaya. Ya yi murmushi yace jam'iyyar da kowa ke sone kin san
yanzu kan kowa ya waye an shiga wani irin hali, da an kasa gane a
wane kaulin muke shin milkin mallaka ake yi, ko kuwa milkin sojoji
ko milkin siyasa. To abin ne dai gashi mutane ma sun zabl shugaba
mai adalci, amma an yi milkin mallaka an juye abin. An/kuma kasa
aiwatar da komai shi yasa suka hadu suka kafa wata jam'iyya mai
tambarin yayyafi wato a yayyafawa abin ruwan san yi zaki ga rumfar
kwano ruwa na zuba su ka sawa sunan jam'iyyar L.Y.B wato LOKACIN YAYEWAR BARAGURBI hakika wannan sunan
jam'iyyar yayi kuma sai yayi dai-dai da kalmomin sunan wata marubuciya sai dai bazan gaya maka ita ba tun da kai ma makaranci ne, ka gano da kanka. Haka muka zauna muna ta hira har muka gaji muka kwanta cikin nishadi dokin juna bamu muka sami bacci ba sai wajan karfe uku na dare lokacin da muka sami sararawa juna. "Zan tafi, kina ji dai aka yo waya ana nemana kuma kamata yayi
ace karfe tar ana safe na bar gidan nan jifa Yaya Auwal ai dai na hada
kadai
mana abincin safe ko?" To mai kika tsaya yi, yara dai basa nan ke ee kuma shirin nakima kawai sai kin 6ata lokaci?" Murmushi kawai nayi nace haba Yaya ka tuna irin wujijjiganin da kayi a daren jiya, ba dole in tashi a gajiye ba".
kamata,
Zahirin gaskiya lokacin da ta fadi haka kunyar Yaya Fahad ta to amma ta masa alkawari ba zata 6oye masa komai ba duk da
58
LUBABAН
cewa ta 6oyc abubuwa da dama saboda bai kamata ta fayyace masa
sirrin auren taba.
"Zo, zo nan ki maimaita abinda kika fada cewar Yaya Aulwa, a
jiyan nina wujijjiga ki ko ke kika wujijjigani, kin sanfa har wani saban
salo kika tsiro min dashi, wanda kika gama rikitani, kika fitar dani daga
cikin yayyacina, dana tambayeki sai kikace.... Aah! Na kwalla kara
yayin da nayo kansa na rufe bakinshi dan Allah karka fada, wallahi in
ka fada zaka rikita komai dan kunya zata kamani