Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 11
ce la yaya ai tuni ya fito dan sai da Khadija ta neme shit a sanar dashi kafin ta zo ta gaya min". "oh my God"ya fada yayin da ya kara da cewa, "kai amma Khadija ta karyamin bajet (any way) sai na karaso" Nan take a ajje wayar nima na ajje. Da na dawo dakina na kwanta, tunanin yadda zan yi in gamu da Yaya Auwal kadai nake yi kar ya dawo in fito yi masa sannu da zuwa Mama taji babu dadi karshe kuma in ki fitowa shima ya zaci wani abu ne ni dai haka na zauna naci gaba da tunanin angwan bunu tun da dai ai ba a shafa fatiha ba. To amma me? Na daukawa kaina alkawarin cewa ba zan nuna maitata a fili ba zan yi kokari in ga cewa na dan ja mutuncin kaina wato jan aji kamar yadda akasari 'yan mata yanzu suke fada sai dai bazanjashi har ya tale sosai daga karshe ya tsinke ba komai dan bi a sannu ne. Daga nan Mama ta leko tace dani ke Humaira zo kije gidan su Sayyada kice da ita dan Allab in tana da almun ta baki ki kawo min farat na yi nace wai ni Mama me ki ke yi da almunne, kike yawan nemansa?" "Idan matambayi" Jin haka yasa naja bakina na yis hiru ni dai na fita na nufi gidan aiken. Da na shiga gidanne muka ci karo da wata Amina, kawatace makarantarmu daya, amma har muka gama ban taba sanin tana zuwa gidan Sayyada ba na karasa cikin gidan na durkusa har kasa na gaida ita, murmushi tayi tace, "Malama Humaira manya an dai gama karatu sai aure ko?". Dariya na yi nace haba dai Yaya, (haka yaran gidan suke kiranta da Yayan,) ai ni yaya sai na yi digiri dina iye wacce makaranta za ki yi? Wallahi Yaya nafi son A.B.U Zariya sai dai ban san yadda za ayi ba ko za'a barni in tafi can karatu sai dai in har ba a barni ba to kuwa sai in je ni B.U.K ta sake yin murmushi tace lallaikam ko kuma ki tafi ABU gidan Auwalu ko Nasir ba, kinga kin shiga babbar makaranta kenan wato aure bautar Ubangiji. Dariya na saka nace haba dai aini ta gaskiyar zani tace ke kuji 'ya in banda abinki ai auren shine gaskiya nace da yauwa yaya daman Amina Isa, tana zuwa gidan nan ai 'yar makarantarmuce. 30 1 1 2 a 1 LUBABАН Tana zuwa mana jefi-jefi. Allah ne dai bai taba hada ku ba ashe makarantarku daya, kinga rashin sani ko yayin da ta tashi ta shiga dakin girki ta daukomin almun din na karba nace "an gode yauwa Yaya, Amina tace in ta kara zuwa za a rakota gidanmu". "То Humaira Allah ya kawota. Da shigata gida na ci karo da Yaya Auwal a tsakar gida yana nunawa Hajiya wata takarda. Wani irin kallo yaya Auwal ya watso min sannan ya biyoshi da tambayata shin daga ina nake? Amma abin mamaki ban iya masa magana ba, kawai sai na wuce cikin gida amma abin bai wani frigitashi ba dan ya san saboda Hajiya ne. Da shigata cikin gidan dakin Mama na wuce naje na ajje mata sakonta, sannan na wuce dakina kai tsaye gaban mudubi na tsaya idona kyar akanf uskata, hakika tana bukatar hoda, don haka sai kawai na dauko hodar na shafa a fuskata, sannan na shiga zizara kwalli a leben bakina, danni a zahiri ban cika sajambaki ba koma in ce bana sawa kwata-kwata. Da naga na kara fitowa fes da ni har da kara fesa turare a jikina dan karawa abin armashi. Gaba daya cakin ya kauraye da muryar Yaya Auwal yana fadin gashi ni na biyo ki har dakin ko an min magana in ji san yi, ko kuwa nayi wani laifin ban sani ba yanzu in nemi gafara murmushi kawai na yi masa yace "kin biyani tawan". Na yi sauri na rufe fuskata da tafukan hannuna yace in banda abin ki Humaira ai sai ki goge kwalliyar taki tun kafin in gama gani saboda kadan na dan gani ban san lokacin da dariya ta kubuce min ba". "Um sweety irin wannan make murya haka". Ya dan jamin kafa yace, "ba sannu da zuwa to ni zan koma daki in kwanta in huta in an jima dan Allah ki ko ina san yin magana da ke nace "To" Da fitar shi na mike na je gaban mudubi ina kallan kaina ina dariya, hakika na san na birge Yaya Auwal. To amma me? Ta yaya zan yi in wuce kai tsaye zuwa dakin shi alhalin Alhaji da Mama za su ganni ina cikin wannan tunanin ne naji Mama ta kwalamin kira, cikin saurina na fito tun kan in karasa durkusawar tace a'a tashi ki, jeki kan firjin ki dauko wata wasika dana danneta da farantin kofuna, ki dauka ki kaiwa Auwal kice wani abokinsa ne ya aiko masa ita yau kwana uku kenan. 31 WANDA YACE NAMIJI UBA2 Dajin haka na ji dadi sosai a raina dan na sami hanyar tafiya gurin yaya cikin ruwan sanyi, said ana dauko wesikar sannan nace da Maman bari in dauko mayafina lokacin dana shiga dakin nawa a gaskiya na dan jima kan inf ito dan Hajiya ma sai da ta kara yi min magana tukun na sannan na fito na shiga dakin Yaya na tarar da shi kwance a falonsa, akan doguwar kujera ko kayan jikins abai cire ba, hakanne ya tabbatar min da cewa lallai ba Karamin gajiya ya yi ba a hankali na yi masa sallama na shiga. Da shigata yace dani "a'a ke da na ce dake sai can an jima, to ya kuma kika zo yanzu, Alhajin ko kwalliya ban sake ba, kamar yadda kema kika yimin murmushi nayi nace Mama ce ta aikoni tace in kawo maka wannan wasikar, wani abokin kane ya kawo maka, wai yau kwana uku kenan. Duba wasikar ya fara yi sanan ya dago kai yana murmushi yace, Humaira kenan ba tun yauba na hanaki ambatar wai aiken manya ko maida maganar shugabanni, kalmar wai ta na nuna rashin amincewa akan abinda mutum yake fada. Dan haka ki kiyaye ko dan gaba. Daga nan ya shiga jofomin tambayoyi, na lura dashi yana son ya fahimci naji maganar ko kuwa, dan haka sai na shiga kakkaucewa komai ya tambaya in yi kamar ban sani ba. nant ake ya amince da ban san komai ba nan take ya shiga labartamin yadda komai ya faru yaci gaba da cewa saboda haka, ko jiya a waya da muna gaisawa da Alhaji yake ce dani nan da sati uku za'a daura mana aure in sha Allah". Ya dago ido a hankali ya kalleni domin ya lura da irin yanayin da na nuna murna ko rashinta. Da na lura dashi sai kawai na dan dake ban rig ana nuna murnata a fili ba ya ce ya dai ko ba a yi farin ciki da labarin nawa ba ne Humaira? Murmushi nayi nace, mai ka gani" yace "a'a na sani ko nasir ya yi mana farraku. Yana fada yana dariya dan naji yana cika bakin in dai shine sai ya kwace ki. Dariya nayi nace, haba dai ya kwaceni, haba yaya sai kace wani kudi. Nifa harma na manta dashi a rayuwa tun da sam ni bai daman ba kuma ai bai isa yayi abinda Allah bai yi ba ya shiga murmushi yana lumshe ido waishi an kushe wani a kanshi munjima muna hira dashi yace wannan yace wannan yace shin kin je gidan 32 LUBABАН Abba kuwa "a'a ban je ba da dai yau nake cewa zan je amma yanzu sai gobe," yace "tun da na zo ko? To mai zai hana in kaiki yau da daddare". "A'a Yaya ba gar amu bari sai gobe ba kaga sai ma in wuni a can yayi murmushi yace bari sahibar na dade a dakin yaya Auwal dag anan muka yis allama nace la'asar ta wuce kada kuma Mama ta meme ni "yace, "ke kuwa kina jin kunyar karta neme ki ace kina gurin angwan ko nayi murmushi nace, "ba haka bane kasan kunya itace mutum hakika ita 'ya mace da kunya aka santa kasan kunyar mace tafi t ana miji, in mace ta biyewa namiji to fa ita za ta sha kunya a gurin mutane: "Na yadda ba musu a nan daga nan muka yi sallama na tafi cikin gida. Da yamma misalin karfe shida da rabi gwaggo ta zo nan gidan a zatona da wata ta zo to amma jin cewar tana tambayar ina amarya yasa na tababtar da cewa lallait a sauko, ta kuma gane hanya taci gab ada cewa "Zuwa na yi gurin Auwalun yana zumudi ya taramu mu tambayo masa auren 'yar nan bamuyi kasa a guiwa ba muka tafi yayin da shi kuma yayi tafiya amma ace har ya dawo ba zai zo yayi mana godiya da huce gajiya ba. Ni ban san ya dawo ba sai da Sagiru yace ya gamu da Manu direba har manun yake sanar dashi wai Auwalun ne ya aikoshi siyan turare, shine nace to bari in zo har gida in yi masa tsiya. Dajin haka Mama tasa dariya, tace gwaggo ai kin san ba halinsa bane ba yau yau din nan ya dawo tun da ya zo ma bai fita ko ina ba. Amma ai nasan in dai har ya fita yaje ya gaisheki, haba aini sai Sagirin bai gayamin ba shi yasa, to yanzu yana ina yana dakinsa tunda ya dawo yake kwance ina jin gajiyace to a rabu dashi in ya tashi ance yazo ina nemansa zuwa can nima na fito na durkusa har kasa na gaida ita, yayin da ta shiga yimin tsiya ni dai nayi wucewata zuwa dakin girki. Da gari ya waye da wuri na tashi na gama shirye-shirye na da misalin karfe tara ne ina cikin shara na jiyo muryar yaya Auwal ya shigo zai gaida su Alhaji, ta dakina na hangoshi kowanka bai yi ba saboda kayan bacci ne ma ajikinshi, nant ake jikina ya yis an yi dan hakan ya nuna min tabbas ba da wuri ba zan tafi ba kenan na san ko na shirya ba zai bari mu tafi da manu ba nan dai hanzart ana gama sharata na shirya komai na kunna turaren wuta na shiga wanka ina 33 WANDA YACE NAMIJI UBA2 cikin wankanne naji Yaya Auwal ya leko dakina yace "Au har kin shiga wanka bance masa komai ba, saboda babu kyau yin magan a abandaki ya wucewarsa, shima ba tare da ya kara yimin magana ba. Da fitowata sai na gaggauta shiryawa na saka wata atamfata shudiya wacce ta bala'in karbata dinkin ambirela shaf ne (Umbreler sheaf) na fito ba tare da nasa sarka ko dankunne ba na nufi dakin Mama don in karbi Sarkar gwal dina don can nake kaita ajiya na saka na gama dai shirina na fito da nufin shiga dakina Khadija ta ce, "Yauwa Yaya wai ki zo in ji Alhaji yace zaki karbi kudi muje zango store ki yomin siyayyar tafiya makaranta, saboda shi bashi da lokaci wai sai Manu ya kaimu na kalleta ina hararta nace, "au wai nema. Da ganan ta dago kai ta kalli Yaya Fahad tayi murmushi tace, kaji ko wai nima an yimin fada yayi murmushi yace ni dai aci gaba Allah, Allah nake in ji abinda aka yi miki, da yayi miki ciwo har kike amfani da wannan jahilar kalmar, wato in da kike fadin duk wanda yace namiji ubane, wai cewar ku zai mutu maraya murmushi tayi masa tace, ai nazo gangara, in banda na maka alkawarin bazan boye maka komai ba, to da hakika ban jaka da nisa ba don kr.wa wasu surutanma bai dace in tsaya ina yi maka su ba ina fata ka fahimta gyara kai kawai yayi ba tare da yayi mata magana ba. Daga nan taci gaba da cewa, "wallahi Yaya garama da zai bani kudin nafi siyan abinda raina yake so, cewar Khadija. Na yi murmushi nace da ita, "da can ba'a sayo miki abin da ran naki yake so?' a'a ba haka bane, amma ai gara dai mutum ya je da kansa. Lokacin dana shiga dakin Alhajin baya falon yana cikin dakinsa. Amma da nayi sallama ya amsa min yace in jirashi. Nan na sami guri na durkusa rungume da bandir din kudi 'yan naira ashirin ashirin a hannuńshi. Daga nan shima ya zauna a kujera daya yace dani in ce harkin shirya? Tun da kin shirya to kije kice da Auwalu ya yi sauri ya kaiku, ku dawo in Allah ya so sai kice dashi yabar sakon, in Manun ya dawo ma fita tare dashi. Amma fa ku yi sauri ku dawo yayin da ya mikomin kudi dubu goma yace, in sayo mata duk abinda ya dace a sai mata. 34 LUBABАН Durkusawa na kara yi na sa hannu biyu na karbi kudin. Don Allah kuyo siyayyar hankali kada ki biye mata duk ku kwaso shirme, dan naga tana ta faman murna, wato ita zata yi abinda ranta ke so. Nace dashi "To". Ina fitowa dakin mama na wuce, na sami Khadija ana ta daukan shiri, na kalleta nayi murmushi, dan kuwa nasan da kyar ne in har Yaya Auwal zai yadda mutafi tare. Na nunawa Mama kudin da Alhaji ya bayar tayi godiya sannan na sanar da ita cewa Alhajin yace in je ins anar da Yaya Auwal ya kaini. Dan yana san fita da Manu in ya dawo cikin sauri Khadija ta juyo yayin da ta bata rai tana bubbuga kafa, irin na shagwaba66un nan tana fadin, "ni dai wallahi ina ma ki roki Alhaji ya yarda mu tafi da Manu, in ba haka ba ni nasan Yaya Auwal ba zai tafi da ni >a". nace to kije ki sanar da Alhaji mana, ki ce kina san zuwa kin ga 'n ya sanar da Yaya Auwal da kansa to zai yarda amma nasan in ba baka ba ba zai yarda ba. Da sauri Khadija ta fita t anufi dakin Alhajin sai gashi ta dawo cikin fushi, rai a mugun 6ace 'ace Mama, ca yayi in zauna su tafi ba sai na bisu ba, tun da ni za'a sayowa kayan yaya Auwal ya shigo cikins hiri wanda har na zaci ko Alhaji ne yayi masa maganar tafiyar ya kalli Khadija yace, "ke kuma kumbure-kumburen me kike yi haka. Daga nan ya juyo ya kalleni yana murmushi yace, "har kin shirya ko? To kijirani Alhaji ne ya aikeni, in na dawo sai mu tafi, nace dama yace in gaya maka kada kaje gurin aiken shi za shi da kansa idan Manu ya dawo, sai su tafi tare, amma kuma yace ka kaini Zango zan yowa Khadija sayyar makaranta. "Dama shi yasa naga. Khadijan tana ta kumbure-kumbure bakyasan komawa makarantar ne? Mama tace, "a'a ba dan haka bane, wato ka sani ko so take aje da ita, shine Alhajin ya hana ya juya ya kalleta yace, da dake ake zuwa ko kuwa? Ke in banda abinki ke dai ba akawo miki kaya ba. Daga nan ya mike, yace bari in je in maidawa da Alhaji takardun nashi ke kuma Humaira in kin shirya kije ki sameni a daki, yayin da ya fakaici idon Mama ya dagan gira gamida kashen ido ya ficewarsa abinsa. 35 WANDA YACE NAMIJI UBA2 Daga nan nima na tashi na nufi dakina, don in dauko mayafına da jakata don in zuba kudin a ciki ina kallan Yaya Auwal ya fito daga dakin Alhajin ya nufi dakinsa, sai da ya dan jima da shiga dakin nasa sannan na bishi a baya. Sallama daya nayi na danna kaina dakin ba tare dan ajira an amsa ba, kasancewar nasan a shirye yake. Da farko sai na tsinci kaina ina mai ja da baya sakamakon abinda kunnena ya jiye mini wato rungume yake da waya a kunanshi yana fada yana cewa, "waike wacce irin makwawaciya ce? Nace dake ki kyal eni ki kyaleni, amma duk kin bi kin nace min in da ana yi dake, to yanzu an daina Allah ya hada ni da 'yar dana ke so itama take sona kuma nasha gargadinki da kada ki kara yomin waya amma a banza. To wallahi kici gaba, amma zan dauki babban mataki a kanki. Dajin haka sai nayi saurin juyawa, tuntuben da naji ne ya hanzarta sakin wayar ba tare da ya maidata a dai-dai ba yace, subahanallahi Humaira lafiya? Amma ni ina kokarin fiçew anake yace hony dan Allah ki tsaya mene ne na fushi da matsayinki la komai wawan tsaki muka ji gami da zagi cikin harshen turarci gagarab aka ajje wayar kasancewar tana nan bai maida ita ba a daidai. Dajin haka gabana yayi mummunan faduwa yace, "Ina kuma zaki mu da tafiya take gaban mu dan Allah ki jirani in sako babbar rigata mu tafi. Amma me kawai sai na tsinci kaina ina mai tare da tsananin kunci a cikin zuciyata. Hakika raina ba karamin baci ya yi ba. To me ye wannan kishi ne ko me? Saboda a wancan lokacin ban san kishi ba, tun da ban taba hada son abu daya da wani ba duk abinda naso zaka ga ni kadai nake son abina. To amma sai gashi ana kokarin shigo min san abinda nafi so a rayuwata tabbas wannan shine kishin da akasari naji mutane na yawan dorashi a kanmu mu mata. Dan haka sai na tsinci kaina da ina shan kunu sam bana Kaunar yi masa fara'a duk da cewar nasan koma wacece bata da matsayi a gurinshi amma fa gaskiya na kishinta dan kuwa namiji bashi da tabbas. Da muka fito muka shiga mota, muka tafi sai ya shiga surutansa, da ko sauraransa bana yi ya jüyo yana murmushi yace hakika da an 36 LUBABАН dankan igiyarki a hannuna da nayi maganin wannan fushin da ake yi in banda abinki ta yaya mutum zai cada kwaliya kuma yazo ya buge da fushi to amma ni duk da haka kalloma bai isheni ba, ban ankaraba kawai sai naga mutum ya gangara bakin titi yana kokrin tsayar da motar sai da ya tsayar da motar sannan yace dani. "Dama Humaira nasan da wani abu da kike 6oyemin, dan wannan karan tun da kika dawo baki tsaya mun yi maganganun kirki ba ko kuwa tsabar kishi ne irin naku na mata ina ganin ni a ganina sai in an damu da mutum ake kishi dashi, ke kanki kinsan yarinyar nan bata gabana. To kuma meye na kishi da ita. Da farko naso in yi banza dashi amma sai na kauda kai gefe guda nace kai ka zaci hakan amma ni ba haka bane a gurina. "To mene ne? ya tambaya yana murmushi ko kuma dai wani ya zugemin ke ne? kauda kai nayi gefe guda sannan nace dashi uhm-uhm. "Dama kin iya fushi haka? To wai me ke faruwa ne Humaira? To wallahi in har baki sanar dani ba babu in da zan daga daga nan da na tabbatar da cewa in har ban sanar dashi gaskiya ba to fa ba zai tafin ba sai na kauda kaig efe guda, na shiga magan acikin shagwaba na ce wacece wacce na ji ku kuna waya tare? Ya tuntsire da dariya yacе, munanan dai ni nace kishi ne ke kince ba haka ba. To wata makwawaciyace, wacce ta taya aka ki sayar mata ko da yake da farko ni na taya, ta watsar da yina saboda ta samu wani yana zugeta. To sai da ta murza taga gyadar babu alamar mai shine ta dawo gareni a daidai lokacin da ni kuma na sami wacce ta fita. To ke in banda abinki meye na fushi, tunda Allah ya kashe ya baki. Dan baki jiba yadda kika rudani aini Humaira da bacin ranki gara amin bulala dari. Ban san lokacin da dariya ta kubuce min ba, saboda yadda ya langwabe kai sai kace wani yaro yace, au dariya ma na baki ke nan? Nace yaya ke nan ka ga kuwa yadda ka yi sai kace irin sokwayan yaran nan to ni Humaira in dai zan ga farin cikin ki ba sai in koma tamkar wawan sarki ba karewar sokwanci. Dama ku mata ai abinda kuke so kenan ayi tayi muku shagwaba kuna murja zarenku son ranku". Daga nan ya haura motar kan titi, yayin da ya juyo yana kallona yace, Humaira amma fa naji dadi da kika nuna kishina afili. Haka nan ya kara tabbatar min da cewa son gaskiya kike min na tababta da Nasir ne ba za ki kula ba. 37 WANDA YACE NAMIJI UBА2 Dariya na sa nace koda kuwa na sarne shi da mata dubu ne ba damuna abin zai yi ba hakika furucina ba karamin burgeshi ya yi ba, har wani shan kanshi yake yi, wai shi an zabeshi an zagi wani a kanshi. Da irin wadannan hirarrakin muka Karasa Zango Store, na dube shi ina murmushi nace in shiga, in fito kana nan shima murmushin yayi yace ina ganin gara mu shiga mu biyu, dan kuwa bibbiyun ya fi daidai, muka shiga ina zaba yana karba yana sawa a kwando har na gama mata siyayyarta, na kashe kudi dubu tara da dari biyu yayin da duk abin da na dauka ina tare da biro da takarda ina rubutawa, da kudinsu duk da cewa nasan suma za su bugo kudin ajikin 'yar takardar da suke yo printing. Daga nan yaya yace, nima in zabi abinda nake bukata, amma saboda kunya na kasa yace in je muzuba kayan yana zuwa yayin da ya mikomin mukullin motar muka fita ni da dan dakwan Zango, na bude masa but din motar ya gama zuzzuba komai, na kawo naira hamsin na bashi mai makwan in koma ciki, sai na yi mazana a motar zuwa can Yaya ya fito rike da ledoji a hannunsa, har guda biyu cikin sauri na fito na tare shi dan in karbi kayan amma sai ya hana ni, wai har da cewar shi ya isa, ai aikin uwar gida ne a can ma an bukaci ya bayar a kawo masa mota yaki yace, aikin uwar gida ne nayi murmushi na rabu da shi gidan baya ya bude ya saka kayan, sannan ya za ga yo ya zauna a mazauninsa sannan yaja motar muka tafi. Da muka isa gida mun tarar da har a wannan lokacin Alhaji bai fito ba naje na nunna masa kayan na kuma bashi canjin, yayi murmushi yace ke kuma baki 'siyowa kanki komai ba? Nan take ya zaro kudi dubu biyu yace, gashi sai ki kara ko. Nan na karba nayi godiya,s annan na kara fitowa da kayan na kaiwa Mama, na kuma nuna mata kudin da Abba ya bani, wato na tashi da dubu biyu da dari bikwai da hamsin. Na ba mama nace ta ajjemin. Daga nan tace dani kin kuwa sanar da Alhajin maganar zuwanki gidan Abban? Na ce la ban gaya masa ba ai ni nayi zatan kin sanar dashi nan dai na tashi na koma na fada masa, yace to sai kiyi sauri ki sanar da Auwalun ya kaiki yanzu tunkan ya fice, dan na aiki Manun ya samo mana man fetur kin ganni nima har yanzu ban fita ba. Nace "to" A hankali yayin dana fito naje na sanar da Mama yadda muka yi tace to ai sai ki yi aniya kije ya kaikin. Da na fito na yiwa Hajiya sallama na nufi dakin yayan yayan da muka gamu da Khadija a hanya nace "ke kuma daga ina? Ga kayan can 38 LUBABАН na sayo miki! Mu kuma zamu gidan Abba sai mun dawo muna cikin tafiya Yaya Auwal ya jawo hannuna yace Humaira mene ne wannan a hannunki haba Humaira da wayon ki da hankalin ki kike nema ki maida kanki wawiya mene wannan kuma? Da farko ban fahimci me yake nufi ba to amma sai daga baya na gano akan abin da yake nufi. Na yi kokarin in kwace hannuna amma sai ya rike shi yace, "bazan saki ba har sai kin sanar dani manufar tara farce, wai me yasa 'ya'yanmu na hausawa kuke da irin wannan wautar ne me ye amfanin tara farce, ga tsaftar dan Adam. Humaira sanin kan ki fa bashi da kyau gashi kuma ni a ganina kazantace ta inna na ha. Dan babu abin burgewa ga tara farce, da farko dai kai kanka da ka tara ya hana ka sakat, ga shi ka yiwa datti gurin kwana, dan kuwa babu abin da karkashin farce ke tarawa baya ga dauda. Da ni mane bazan taba sha'awar tara farce ba, ko dayake wasu mazan ma suna tarawa, to amma mu har abada abinda yake bani haushi ga jama'armu shine ko yo mi da nasara. Allah ya yoka a matsayin mutum mai hankali ka ringa kwatanta kanka da daba. Ni dai in har kin aso mu shirya ki daina sha'awar irin wadannan shirman da kabilu suke yi, dan babu abin burgewa a nan dan Allah da mun je gica ki yanke shi, dan ina kyautata zatan Mama ma bata kula ba dan hakif.a da ta yi miki magana ki dai yanke shi in ma kin tara ne saboda kwalliyar biki to fa ki sani shi wannan angwan tsoransa yake ji, dan kada a karkarce shi. Dariya na saki a hankali yayin da na kautar da kaina gefe guda, cike da 'yar munafukar kunyata, dan a lokacin gani nake nafi kowa san lokacin ya iso. Dan babu abinda ya fi yiwa mace ta gari dadi a rai face ta ganta a dakin mijinta. Da muka karasa kofar gidan Abbanne Yaya Auwal yace, "In kin shiga kya gaidasu dan nasan yanzu Abba ya fita zan je wani guri in dawo ki gaida Hajiya Iya da kyau". Nace "To" ya yi murmushi yayin da ya kalleni yace, "sai da yamma ko na daga masa hannu gami da ce masa sai ya dawo yaja mota ya tafi, ni kuma na shiga cikin gidan. Dana shiga na tarar da Hajiya Rabi a wajen Hajiya iya tana mata shara, yayin da ta ce Hajiya Iyan ta fita makota, abin ya dauremin kai lallai Hajiya Rabi ta sauko na so in karba in karasa sharar, amma ta hanani tace, wai

Chapter 4 of 11