face fitar da hakkin
Allah, wato yin zakka yawaita sadaka, da kuma taimakon gajiyayyu ko
bayan raina Humaira, ki yawaita aiwatar da abubuwan da na zana miki.
Dan haka da zaki ringa yi ba ke bama koni dana haifeki sai albarkar ta
shafeni, kuma in sami rangwamen kwanciyar kabari. Tun da duk
wanda ya ji dadi ya shi miki albarka ya kuma ce Allah ya jikan
mahaifanki. Dan Alah ki zama ta gari a duk in da kike.
A gaskiya na ji dadi da naga Hajiya yau ta barni da mahaifina
munsha hira, amma da da zarar taga mun dan jima sai ta zo ta nannage
mana ta hana mu fadar abinda muke so. Da ta gama abincinci ta turo
min Mary ta zo ta kirani, inci abinci. Bayan mun gama cin abincin ne,
na wuce dakin hajiya Iya. Bayan mun gaisa, muka shiga yin hira, har
nake ce da ita yanzu dai sam Hajiya Rabi ta daina abinda take yi.
"A to Allah ya sa ta zarce da haka, ai dama duk laifin Baban naki
ne yanzu da ya nuna mata 6acin ranshi ai ta amince ko dan har sai da
ya sake ta bayan ya dawo da ita ne ya gargadeta, da cewar in har tana
san zama dashi to fa dole taso abinda ya ke so ashe dama duk yna lura
da ita kyaleta kawai ya ke yi to sai da ta kaishi karshe tukunna yaci
mata mutunci kuma yanzu dole tabi kowa ahankali dan tana tsoron
kada a karasa mata dayan.
Abba ya turo maryam ta kirani yace "ke baki ji ba Manu ya zo
daukarku", nace, "Allah ban ji ba Hajiya ce duk ta cikani da surutu"
yace, ja'ira Hajiyar ce take miki surutun. Daga nan ya janyo ledoji
manya-manya guda uku yace ga wanan ki rikewa Maryam ko?" na
karba ina godiya tun a nan nace a'a Maryam ta more bari in ga abinda
aka sayo mata. Ta farko na tarar da alawa, biskit da sauran kayan ciyeciye iri-iri kamar su cak da sauransu. Ta biyun kuwa sabulai ne da mai
da su jambaki kayan kyale-kyale dai dayar kuma riguna ne da siket har
kala hudu da kuma riga da wando guda uku, dogwayen riguna kuma
guda biyu. 20
LUBABАН
A gaskiya naji dadi sosai, dan hakika irin son da Abbana ya ke
yiwa Mama na ne ya shafe ni hakika Abba ba karamin so ya ke mata
ba. Hakika haka yake so babbar cutace, amma karamin hakuri yake
warkar dashi. Sanan ya fito da kudi dubu biyu ya bani yace in rike
mana. Na durkusa har kasa na karba Maryam ta dauki jaka daya ta rike
yayin da ni kuma an karbi jaka biyu na rike. Abba ya ruko hannun
Maryam sai da muka biya ta dakin Hajiya Rabi tukunna, a inda har fa
zaro dari biyu ta bawa Maryam, har da kullin gyada soyayyiya nan dai
muka yi mata godiya muka fita.
A hanyarmu ta fita zuwa waje ne Abba ya ke cewa dani.
"Humaira sai yaushe kuma? Na san tunda Auwal baya nan bazan ringa
ganinki ba yanzu na ce haba Abba, duk karshens ati zan ringa zuwa
gaisheka kafin mu koma makaranta". Ya kalli Maryam yace "Maryam
fa?" Tace "Nima zan dawo" yace "yaushe zaki dawo?" tace gobe gaba
daya muka sa dariya yace, banda gobe Maryam sake wata ranar tace,
"to jiya". Nan ma dariya rmuka yi yace to Allah ya kaimu. Allah kuma
yasa Maman naki ta barki na yi murmushi nace haba Abba mai zai
hana ta barta, yace kayya dai ai na lura har yanzu Maman taki haushina
ta ke ji.
Amma na lura yan:u ta dan rage jin haushina. Har yanzu ta kasa
fuskantar wasu abubuwan in da ba a yi auren ba ya za a yi da rabanki
gashi har yanzu ban kara samun da ko daya ba, wama ya sani ko ke
kadaice 'yata a duniya. Tausayin Abba ya yi matukar kamani nan take
kwalla ta cikamin idona yayin da shima ya kauda kai gefe guda ban
sani ba ko shima kwalar ya yi oho.
A hankali muka karasa gurin mota, ya juya gurin maigadi ya
kwalawa Manu kira, yayin da ya taso cikin sauri, ya durkusa ya gaida
Abba Abba ya zaro dari biyar ya bashi yace ai gara ku hanzarta ku tafi
ko? Naga alama taku ta zo daya da mai gadi in ka zo gidan nan sam
baka son rabuwa dashi, ko dai 'yarsa yace zai aura maka, shine kake
masa fadanci? Muka sa dariya.
"A gaskiya ba yaban kaiba yaya Fahad wallahi Abąbna yana da
barkwanci, gashi sam ba shi da girman kai nan dai muka yi sallama
muka shiga mota muna daga masa hannu cikin farin ciki da
annushuwa. Nan ya tsaya sai da ya ga mun 6ace sannan ya koma cikin gida.
A lokacin da muka isa gida Mama kadai muka samu, dan su Khadija duk sun tafi Islamiyya. Har na bata labarin kawar da n ayi nan
21
WANDA YACE NAMIJI UBA2
na zauna ina bata labarin Kawar dana yi da kuma abin da ya wakana.
Daganan na shiga yi mata bayanin abin da ya faru tsakanin mu da abba
Maryam ta yi karab tace Mama duk kayana ne, Abba yace kar'in ba
kowa. A hankali Mama ta gama dudduba kayan tayi godiya sosai tun
da nake da Mama bata taba nuna farin cikint aba kamar na yau a duk
wata kyauta da Abbana zai mana.
A nan ne na kara nuna mata kudin da ya bamu tayi godiya, gami
da kallan Maryam tace, maryam yar gidan Abba Maryam ta yi dariya
tace "Hajiya kullum sai mun je yawo har ya kaini gurin nan. Ta juyo ta
kalleni tace yaya Humaira in da kuka taba zuwan nan ke da Yaya
Auwal har kuka ci abin ci yaya ma sunanshi? Ni na manta.
w A gaskiya yaro bashi da rufi kunya ta bala'in kamani, nama rasa
abinda zan ce da ita, Hajiya kuwa kallona kawai tayit a watsar banzan
da tayi dani shi ya sa ma na dan ji dadi dadi, duk da cewa hausaw ana
cewa shiruma magana ce. Hakika na yadda shiru magana ce to ni nafi
son a yi min shirun. Ci gaba ta yi da tambayata, ni kuw akallonta kawai
na ke zuwa can Mama ta yi murmushin da bai gama ratsa
makogwaronta ba, tace a'a ka ga su Maryam 'ya'yan Abba yauwa
Mama wai in ji Abba yace da yanzu ni 'yarsa ce?
Abin ba karamin mamaki ya bani ba to wai me yake damin
Abbana ne har yake irin wadannan surutan da akasari yake sa mama
fadar maganar da zata batan rai kar dai in ce har yanzu yana son
Mama". Amma shine har yake cewa waida zaki bashi ni da ya karba
ya hada da yaya Humaira mun zama mu biyu yauwa Mama wai Yaya
Humaira 'yarsa ce ba 'yar Alhaji ba?"
Amma abin mamaki sai naga mama ta yi shiru kallo daya zaka
mata kasan maganar Maryam ta ratsa ta. Ta dan yi murmushi ta shafi
kan Maryam tace, "Maryam kenan 'yarsa ce," "To Mama kuma keсе
babarta? Karab na yi nace, "E itace Babata Maryam 'yar jarida sai
shegen tambaya. "To kuma me yasa take zaune a nan gidan bata koma
can ba? to kuma waye 'yar gidan Hajiya Rabi? Kai maryam sarkint
ambaya 'yar gidan Hajiya Rabi ta tafi unguwa.
A nan ne Mama ta tashi cak ta bar mana gurin. A gaskiya wannan
hutun ya min dadi sosai mun yi hutu cikin jin dadi da annushuwa muna
gama hutunmu muka koma makaranta da shirin karatu sosai.
Ana saura kwana shida mu fara jarrabawa ne yaya Auwal ya
rubutomin wasika. Da da farko da aka kawomin labarin ban dauka
22
LUBABАН
yaya Auwal bane, ni a zato na ma hajara Sale ce sai da aka kawomin
wasikar naga daga gurin yaya Auwal ta fito.
A hankali wata shakakkiyar dariya ta kubuce min sakamakon irin
kalaman da ya rubuta min a ciki a zahiri na kara tabbatarwa kaina lallai
Yaya Auwal ba karamin so yake min ba ban bata lokaci ba gudun kada
lokacin ya yi tsiya, na rubuta masa amsa da kalaman da nasan za su da
dada masa rai.
A gaskiya ba karamin maida hankali muka yi ba akan karatun mu
har muka kammala jarabawar mu cikin sa'a da fatan alkhairi ga
junanmu. A daren hutun muka shiga shirye-shirye da kade-kade a ranar
hutun kuma muka hada hadadden fatinmu na (Graduation) wato
murnar kammala karatunmu, karshen hadewa na hade dan kuwa wani
hadadden dinki ne da Mama ta aikomin na samu na yarfa don a zahiri
na sowa zuciyata cewa babu tantama yaya Auwal ne zai zo daukata.
Amma abin mamaki sai naga Manu direba yana ta bilinbituwar nema
na na ji rashin dadi sosai a raina.
A motane nake tambayar Manu cewar ina Yaya Auwal? Ya dan
yi murmushi yace Auwal ai tun jiya Alhaji ya aikeshi Legas amma ina
jin wajen jibi zaida wo". Nace "Allah ya dawo dashi lafiya yace
Ameen.
A kofar gida na fara karo da yara gaba daya suka dau murna
kamar sa goya ni. Mama kuwa tsayawa kawai tayi tana kallona cike da
mamaki." Kece kuwa Humaira?" yi Mama yayin da Hannunta yake
rike da habarta alamun matukar mamaki, to ni kuma sai hakan da
Mama tayi ya dauremin kai "irin wannan rama haka Humaira sai kace
ba kyaci bakya sha.
A nan ne nayi dariya nace "Mama kin san wannan karan mun
dade a makaranta ga kuma uwa uba karatu da muke ta faman yi".
"Amma duk da haka ramar tayi yawa, ga wani uban baki da kuka
yi. AN ya ma kuwa kina yin wanka na yi dariya nace" Mama wanka
kai Khadija tace" Yaya Humaira muma in za muyijarabawa sai mun yi
baki?" Na yi murmushi nace" ya danganta da yanayin karatunku da ita
kanta makarantar da kuma irin naki fargabar". Don Allaht ashi ki shiga
wanka.
A lokacin da na fito daga wanka har na shiga daki idan Mama na
kaina. Na shige daki na shirya nayi tsaf dani, ina fitowa ta kallenit ace
"Yauwa ko ke fa? Kinga yanzu har kin haskaka, dama nasan dai har da
rashin wanka yanzu ba gashi ba har kin haska na kalli Khadija nace
23
WANDA YACE NAMIJI UBA2
Khadija dan Allah je ki dakin girki ki daukomin abinci wallahi yinwa
na ke ji". "Uhm ai gara kiyi-kiyi, ki cicci abincin ko kya maida jikinki, wallahi na tsani rama a rayuwata.
A Mama wai ina maryam ne? ni tun da na zo ban ganta ba ko an
shiga gari? Mama tayi murmushi tace ai Maryam tun da ta ganewa
gidan Abban ki bata da gurin zuwa a yanzu sai can su tun wancan satin
aka musu hutu kuma tun kafin Auwal ya tafi Legas ya kaita, a takaice
yau kwananta biyar a can sai jibi idan Auwal din ya dawo zai je ya
dauko ta" "ke sai yaushe zaki can din "Gobe na ke son zuwa.
A'a ki bari sai wajen jibi koma gata kin ga sannan kin dan
warware nace toda g anan muka dan jima muna hira daga karshe nace
ni zan tafi in kwanta. Ina shiga dakin sai ga Khadija ta biyoni a baya.
“Amma dai kin san bacci zan yi ko? Shine za ki biyoni ki cikani
da surutu. A'a ni sako ne na kawo miki Yaya Auwal ne yace in baki
wannan wasikar in kin dawo tun dazuma mantawa na yi da tuni na baki
yauwa Yaya kin ga ko Alhaji ya tura su Baba mati, da Ankul (uncle)
Nasirun Baba Ambai da kuma Ankul sani, can gidan Abba wai su
tambayawa Yaya Auwal ke da da farko yayar Sani (yayar Alhaji ce ake
kiranta da hakan) tace wai gara bar ku kowa ya nemo a waje, amma sai
Alhaji yace a'a tun da kun yadda da juna i shikenan kuma aure ya
halatta a junanku kuma ai dama shi dama ya dade yana muku addu'ar
Allah ya hada kawunanku saboda shi ya yaba da hankalinki.
"Allah Yaya, Abba yana da kirki kin san kuwa ca yayi wai ya
yafewa Yaya Auwal komai hatta gidanda za ku zauna shi zai bayar
sadaki kawai yace a bayar, kuma ma naji suna maganar wai ko za'a
bashi aiki ko me?” Allah Abba yana da kirki don naji suna ta
yabanshi".
"Abba ke nan". Na fada yayin da na yi murmushi na dubi
Khadijan nace "To shin yaya Auwal din ya sani ko kuwa?" "La! Ya
sani mana har ya yi ta raban kudi yana cewa wai goron murna ne". Nan
ma murmushi nayi ban sake ce da ita komai ba, nace, "to bari in
karanta wasikar wai shin ina Habibu ne? ni tun da na dawo ban ganshi
ba" "La! Yaya baki sani ba? shima fa ya tafi can mina wajan Kawu
yace shima irin makarantar da Yaya yayi yake son yi, wai dan tafi
kokari. Da so yayi abiya masa ya tafi turai karatu shine Alhaji yace a'a
wai meye amfanin makarantun mu na kasar nan shi sam bashi da
ra'ayin tura 'yayansa makarantun kasar waje,s hi a nashi ganin rashin
kishin kaine,w anda su masu kudin suke ganin ci gaba ne.
24
LUBABАН
Amma ci gaban mai shiga rijiya in da masu kudin kasar nan da
shugabannin kasar nan z asu ringa barin 'ya'yayensu, yan karatu a
Kasarnan da za a fi tsayawa tsayin daka aga an gyara makarantun to
yadda karatu zait afi dai-dai a daina yawan yajin aikin da ake yi a kasar
nan".
"Amma nayi mamaki da ban san tafiyar saba. Shi ke nan jeki, ni
dama bacci nake son yi". Dariya tayi tace Yaya bacci ko karatun
wasika. Yaya nima fa nayis aurayi amma ba zan gaya maki shi ba dan
ko su hajiya basu sani ba na dai ce dashi ya bari sai na shiga aji biyar
tukunna dan har zuwan na hanashi, kinga in na shiga (form five) ai ko
yayi magana babu komai ko? Kuma ai Alhaji ba zai yi fada ba ko?"
A nan ne na karayin murmushi na ce şaura kwana na wa ku koma
makaranta". Tace saura kwana hudu mu koma in sha Allah" Nace to
jeki tana fita na shiga dogon tunani na yi mamakin yadda yayar Alhaji
ta dan fara rashin yadda da al'amarin, to amma me gaskiya Abba ya
burgeni dan gane da abinda yayi tunda ya nuna musu cewa mutunci ya
fi kudi. Hakan ma zai kara tabbatar musu da cewa bawai dan kudin su
ake son shi ba na ware wasikar na fara karantawa kamar haka:
Auwal ne
Amma na ji haushin dabani na dauko ki ba ina fatan kin is alafiya.
Humaira nasan z aki ci karo da zazzakan labarida ga bakin mutane. To
ina gargadinki da kada ki saurari kow akijira nawa labarin abin nufi ki
jirani in zo, in na dawo zan kawat amiki shi har kiji, tafi zuma dadi in
yarane suka kawo miki labarin ki kwabesu in kuwa manya ne ki tashi
ki gudu sai ki fake da cewa kunya kike ji dan Allah kada ki saurari
kowa ni na ke son in karbi goron albishir din dan haka nace da Kadija
da zarar kin dawo ta baki (take my first kiss).
A hankali na lumshe ido ina murmushi nace kai Yaya Auwal baka
da dama na rungume takardar ina lumshe ido nace to Yaya ka makarа
in ma riga himan masallaci ne to Khadija ta zama, amma in har ya
dawo zan yi kokarin nuna masa tamkar ban san abinda ke faruwa ba
ina cikin wannan tunani ne bacci mai nauyi ya sureni. Bani na farka ba,
sai gab da magariba na yi mamakin da Mama bata tashe ni ba duk da
cewa tan ayawan gargadınmu akan baccin bayan sallar la'asar saboda
bisa sunna ta ma'aiki an fi son yin baccin rana tsakanin sha daya na
25
WANDA YACE NAMIJI UBА2
rana zuwa sallar azzahar, ba'a son baccin bayan sallar la'asar ne saboda
a lokacin ake saukar da cutuka, har zuwa bayans alar magariba. Shi
yasa ake son ko jin jiri ne da zarar almuru ta yi, wato gab da sallar
magariba ake son a dauke shi a goya shi to amma sai gashi har
magariban tayi ba'a tasheni ba to ashe Alhaji ne yace a barni dan yasan
baccin gajiya na ke yi ina tashi naje na gabatar da sallar la'asar da
kuma ta magariba.
A lokacin da na fito rike da carbahata, sai na sami guri na zauna
nima ina ta jan carbahata, kafin a kira sallar insha'i. Ana kiran sallar
kuwa Alhaji ya mike yayi mana jam'I muna idarwa aka zauna ana dan
taba hira bayan doguwar addu'ar da aka gabatar. Gamida yin yasin
kafa bakwai muna masu addu'ar Allah ya bamu shugaban kasa na gari.
To amma me sam na kasa sakewa a lokacin da aka koma falon Alhaji,
sabon 'yan gidane da dddare akan hadu a falon Alhaji a dan taba hira,
in ma ya shigo da tsire ko balangu, ko gashin kaza a nan ake zama ake
ci zuwa karfe taran dare sai kuma kowa ya koma daki ya kwanta.
A ranar ni dai kasa zama na yis aboda kun ya dan haka sai na
tashi na koma dakin Hajiya na yi zama na zuwa can naji shirun ya yi
yawa na mike na koma namu dakin na yara na yi kwanciyata. Duk da
cewa ni ba kasa fai nake kwana a dakin yaran ba nafi kwana ni kai dai
dakin Mama. Amma yau dakin yara na nufa can sama-sama na ke jin
muryar Maryam tana cewa "Mama tun da tayi bacci kawai mu cinye".
Mama tace "a'a a bar mata kayanta da safe ta ci. Haka ake yi kici
rabanki ki ci na wani, abinda a ko da yaushe nake muku fada akai ke
nan.
A washegari tun da asuba mama ta tasheni na je nayi alwala muka
yi jam'in sallar asuba, bayan mun idar ne muka gabatar da addu'o'i,
sannan na koma na yi kwanciya, kasancewar ha a lokacin akwai sauran
bacci a kaina sai wajan karfe goma na safe sannan na tashi daga baссі,
ban fito ba har sai da na yi wankana na shirya tsaf, tukunna na fito daga
dakin. Na tarar da su Mama a tsakar gida. Naje na durkusa na gaida
Mama, nace "bari in je in gaida Alhaji”. Ta kalleni tace, "ko? Da yake
shi Alhajin zama zai yi ya jiraki ba ni tun bakwai yabar gidan nan yau.
"Amma Humaira da musun tsiya kike kin min musun lallai wai
kina yin wanka, to gashi kwana daya kawai amma har kin haska. Na yi
murmushi nace, "Allah Mama ba haka bane kwabin nanne dai dana
saba yi wato zuma da garin alkama, wanda nake shafawa fuskata, kafin
in kwanta shi ne nayi na kuma shafa". "Amma shine har kika has ka
26
LUBABАН
haka. Hajiya ai bayan na wanke na yi alwallar sallar asuba sai da na
kuma shafaw ana kwanta, sai yanzu ne da na tashi tukunna na yi
wanka".
"A ina kika gani? Ko kuma in ce miki waya koya miki mama a
littafinnan na gani wato sirrin zuma murmushi Mama tayi tace ai kuwa
kin gano sirrin da yawa". "Kuma wallahi mama ko zuma da zaitun aka
hada sai ayiwa mai kuraje amfani dashi,w ato in irin kurajen nan suka
fesowa yar asai a shafa musu su kwana dashi, gari na wayewaa wanke
musu da ruwan dumi to kuwa da ikon Allah za'a ga saukinsu in sha
Allah ai nasan wannan Humaira, gashinan mai magani a gonar yaro
yana fadar ire-irensu a tashar talabijin ta C.T.V. ako wacce lahadi, ai
gaskiya mutunin an ba karamin kokari yake yi ba Allah dai ya saka
masa da alkhairinsa" "Amin.
Au Humaira kinga na manta in gaya miki kawarnan taki da kika
yi wacce kike bani labarinta ta zo a lokacin kuna makaranta, an yiwa su
Khadija hutu to ta zaci har ku shine tazo" "wacce ke nan Mama?" A"a
kawar nan taki da kika bani labarinta, wace kika ce anan makotan
gidan Babanki kuka gamu da ita. Har ma ta kawo miki Bagaruwa da
dabino, har ma da zam-zam, da kuma carbi da mayafi. Amma babu
abinda zaki samu a ciki sai mayafin, don dul: muncinye hatta carbin
Alhaji ne ya daukeshi, da yake yana da kyau dan kuwa irin na
daddannawar nan ne". La Mama wane irin mayafi ne? kai amma na
gode Allah ya saka da alkairi, in sha Allahu nima zan je.
"Abincinki yana dakin girki kije ki dauko Khadija ta fito tana
mika Mama tace kema kina baccin ko? Wai don Allah ya kuke yi a
makarantunku in kun koma?" Khadija tayi murmushi tace, "Mama ai in
an koma makarantar sai a nemi baccin a rasa.
27
WANDA YACE NAMIJI UBA2
A
a daddare ne muna zaune a falon Alhaji muna hira, ta kure Dnake gefe guda sam na kasa sakewa a dakin, saboda gulma
da kinibibin da na doraw akaina saboda kunyar Alhaji na
ke ji yanzu. Alhaji ya dubeni yana murmushi yace, "Humaira 'yan makaranta, har an gama makaranta ko?" na sunkuyar da kaina kasa cike da kunya nace, "E" Ya sake yin murmushi yace, shike nan dai
wai-wai shiru ko?" Mama tayida riya tace, ato da aka sami
makarantar aka hana kowa sakat to gashi dai har an gama an huta.
"Daman ai wuyarta a fara kwance tashi ai ba wuya a gurin Allah. To Humaira an dai gama karatu lafiya, shin cigaba da
karatun za ki yi ko kuwa aiki za ki yi?" Cewar Alhaji sunkuyar da
kai na yi ina murmushi Alhaji ya kalli Mam ayace, "wai mai yasa
yarinya rnan take jin kunya tane?" "oho mata wani sabon sanaben
ne, ta tsiro da shi a yanzu" "ko dai maganar yaron nan ne Auwal?
To kinga ki kwantar da hankalinki ki sakir anki, ni da ke da Auwal
da su Khadija duk daya ne a gurina kada ki daukeni a matsayin
suruki, ki rikeni uba kamar da kada ki zafafawa kanki, don in kika
tsiri kunyata tun yanzu ke zaki wahala kin ga dan tsiren da nake siyo wa mu hadu asa hannu gaba daya aci sai ya zama haramiyarki
Gaba daya yara sukasa dariya.
"Dariyar ta isa haka in ji Mama, to in ma banda abinku meye
abin dariya? Khadija tace "Allah Alhaji da ni nayi zatan ma
Humaira 'yar kace". "Yata ce mana wa yac e dake ba 'ya ta bace?"
Sai tayi dariya kawai nan dai suka zauna suna hira ni kuwa ina daga
gefe guda na takura sakamakon takunkumin da na sawa kaina, kirikiri ina san yin magana, to amma abinda Alhaji yace ma ya kara
haddasa min kunya. Domin ina ganin kamar in na ware zaice dama
can gulmace ba kunyar ba.
Da naji zaman shirun ya isheni sai na tashi nace da su sai da
safe. Alhaji yace, "za a tafi a kwantane?" nace, "E, muka yi sallama
da sauran na tafi, ina zuwa dakin na dauki irin zumar nan da na
kwabata a jiya na shafe fuskata fes, wannan na yi kwanciyata cike
da tunanin kwarzon nawa ina kuma yiwa Allah godiya da ya hadani
da suriki na gari. 28
LUBABАН
Da sassafe na tashi kasancewar tun asuba na bada farali dan haka babu tunanin sallah a kaina sai da naci abinci na kammala da komai, sannan na shiga dan sunne-sunne, wato ina san in yiwa Hajiya tambayar ko yaya Auwal ya bar mukullin dakinsa, zuwa can dai na gama nuku-nuku na na tambayeta ko ya bar mukullin?.
"Da kike neman mukullin dakinsa ajiya ki yi masa ko kuwa? Ko kuwa ya aiko yace ki share masa? Wato kin ji an ce yau zai dawo shine kike ta rawar kai, da kafa ko? Wallahi ina ji ye miki
shishshigewa da namiji to wallahi bari in gaya miki namiji bashi da
tabbas in ma banda raini irin naki, koma ca aka yi miki ga mukullin
dakin nasa ai kyaji kunyar karba ballantana har ki kalli kwayar
idona ki tambayeni mukullin dakinsa. To in ke ya bawa ajiya ba sai
kije ki dauka a inda kika ajiye ba. To wallahi ki kiyaye ni da rashin
kunyar nan taku ta 'yayan zamani bana san futunar tsiya kaina a
sunkuye jikina yayi san yi babu abinda ya fadomin a rai face littafin
nan na kaddara ta riga fata nan take na gane abinda Mama take son
ta fahimtar danit abbas namiji bashi da tabbas.
Duk kunya ta mamayeni, take na bawa Mama hakuri tace", ato
ki dai bi a hankali kada ilimin ki ya zama na banza":
Da yamma na kwada wankana, tare da yarfa kwalliyata dai-dai
misali doguwar riga na saka mai hadaddiyar hular nan. To amma
me? Sai na tsinci kaina da kasa fita ko da tsakar gida ne, don ban
san da yadda Hajiya zata dauki kwalliyar tawa ba ina cikin tunani
hadija ta shigo tace, Yaya Humaira yanzu yaya Auwal ya bugo
waya dakin mama yace a tura masa Mani ya dauko shi shine ya
tambayeni ko kina nan shine nace e kina, nan shida ya zaci ko kina
gidan Abba. To dai a takaice yace kije, ki dauki wayar". "Shine da
ke baki gayamin sakon ba shine kika barni ina jin wannan bayanin naki, shin Mama tana dakin ko kuwa?""A'a bata dakin tana dakin
Alhajit ana share masa.
"Da fatan ka dawo lafiya?" Dariya yayi yace abin da za ki fara fada kenan, in banda abinki, ai tun da nace a kirawoki ya kamata ki
fahimci hakan ya kuke? ina fata kuna lafiya kin ga ba wani tsayawa
za mu yi wani dogon labari ba dan ban san ba ko yangar amarcin ne
aka fara tun daga yanzu? Oho dan kuwa dük kin cinye rabin lokacinki a waya tun kafin ki iso.
29
WANDA YACE NAMIJI UBA2
Dan Allah ki rako Manu Direba daukata saboda ina son in
nunawa wani abokina ke kafin ya wuce Malumfashi yanzu fadan da
mama ta yi min shi ya fara fado min a rai. Na yi sauri na