Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
irin kallo da ya jefeni dashi nan da nan ya dirar min a kwaryar idona ya kwa ratsani har cikin uzciyata gaba da ta dauki dadadain bege. A san yaye na sanarwa da Alhajin cewar ta shiga wanka, sannan na fito na nufi nawa dakin Yaya ya shigo. "Dan Allah ki tashi mu tafi can kinga ke kadaice babu abokin hira nima haka, Hajiyama in ta fito gurin Alhaji za ta shiga ta taya shi hira, muma ba sai mu zo mu yi tamu hirar ba a sanyaye na mike don bana son Hajiya ta fito daga wanka ya zamto ta gammu tare. 10 LUBABАН Muna shiga dakin nasa ya rungumoni jikinshi yace, "na ma rasa irin godiyar da zan miki" cikin hanzari na kwace kaina nace "babu damuwa Yaya" "To abinda na ke so dake shine kimin alfarmar, ki tsaya muntuna in shiga wanka in fito". Na yi murmushi nace" yaya ke nan, to in koma ciki mana, in ka fito daga wankan ba sai in dawo ba. Ya kuran ido na dan lokaci yace hakane, amma kimin alkawarin, lallai zaki dawo nan da minti goma sha biyar, na kada masa kwayar idona nace in sha Allah. Mama ta kalleni, a daidai lokacin da take rike da farantin abincin Alhaji, tace "daga ina kuma kike? Kaina a sinkuye nace yayane, ya ce in kai masa cokali. A kalla tayi min kalon sakwan biyu sannan ta gyada kai tayi gaba ba tare da tace dani komai ba. Murmushi na ringa yi haka kawai ni kadai a dakina, ba komai nake murmusawa ba face in na tuno da irin kallon da yaya ya ke min zuwa can na tashi naje gurin kiran da yaya ya kemin. Ya nuna matukar farin cikin shi game da yadda na gyara masa dakin, ya kalleni yana kashe ido yace, "wallahi yau jina nake kamar wani ango mijin amarya. Haba ashe haka shiryayyun mata suke shagwaba nazajen su? Ni da yau kadai da aka min hakan, harna fada a rainada ma ans hafa fatiha, in nuna miki godiyata ta musamman, tunanin hakan kawai har ya sa na fara kiba. Na yi murmushin da har ya baiyana nace "yaya kenan mun jima muna hira cikin inganci da kula da bacin ran juna. Hakika na lura da yaya Auwal ba karamin so yake min ba. A a koma makaranta, cike da annushuwa da jin dadin haduwa da Ningarmar namiji a fagen soyayya. Na yi matukar maida hankalina a bangaren karatuna, wasiku zuwa sakonnin da nake samu daga gurin Yaya Auwal hakika, bazan iya iuna su ba. A duk lokacin kuwa da ya sami damar fitowa weekend daga makaranta, to fa sai ya zomin makaranta, in kuwa bai zo ba tabbatar wani babban dalili ne. Na kasance jininmu ya hadu sosai dani da wata Halima Yusif, saboda ra a yin mu da komai ma kusan ya zo daya, sai dai na kokari da 11. WANDA YACE NAMIJI UBA2 HARM ta fini, dan kuwa ita take zuwa na daya a ajinmu. To akwai lokacin da muna kwance a dakinmu'na kwana ni da ita a kwana daya muka zauna, kowa yana karanta littafi, kada ka dauka littafi na aikin makaranta, a'a, littafi ne irin na soyayya da marubuta suke fadakar da mata sosai don suf arka akanw asu abubuwa da ke faruwa a rayuwar al'umma, Halima ta muskuta gami da wurgi da littafi sannan tace a nemí na biyu wallahi na fi son in na fara akratun littafi ace na ji karshensa su marubutan nan sehgen son kudi, sai su yi ta kacal-cala labari don kawai su sami kudi. Na yi murmushi nace, "Allah ko? Ni kuwa ina ganin akasarin marubuta ba manufarsu ke nan ba, yin na daya dana biyun yana kara sawa makarantan su fuskanci inda suka sa gaba kins an abinda nake nufi? Wato in suka hada rikici, ko wani rikitaccen al'amari, hakan na haifar da mahawara zuwa ga musu a tsakanin makaranta, domin gano inda abin yake, to cikin muhawarar ne, marubuci kan karo da zagi ko. yabo kuma gurin zaginne ya ke haifar da samun wanda ya fahimța ya fahimtar da mai zagin. Domin akasarin makarantan yanzu sun fi son karatun litattafan soyayyar da zata tashi daga ta dan bahaushe ta koma turai, su dai su ji labarin rugume-rungumen nan, kawaj su ji dadi amma fa ba a damu da mai marubucin ke son ya koyar ba. evt ab ost Na taba karanta wani littafi ma da aka ringa za gin marubuciyar don ta nuna yadda yanzu abubuwa suka sauya wa ya nemi Kanwarsa, Uba kuma ya nemi 'yarsa da sauransu. Halima ta yi karab tace, kuma wallahi hakan yana faruwa. Danni a garin su babata ma naga wani mutum kuma alkali ne guda amma kuma ya yiwa jikarsa ciki. "Na shiga uku garin yaya?" na tambaye ta a rude, tace, 'wato dan sane, Babban ya yi kudi sosai har Allah ya sa ya koma Legas da zama, kusan 'yan mata a legas ba saurin samun muji suke yi ba, in ma ba'aci sa'a ba ki ga tarbiyar tasu ta sami miskila, saboda nan cikin Kabilu. To shine ya kwaso 'ya'yan har uku da suka isa aure ya kawo gidansu, wato gidan mahaifin nashi ya ce ya kawo su ne don su sami miji a cikin danginsa Hausawa kuma musulmai su yi aure, don tarbiyarsu ta gyaru, to fa'a nan ne aka yi gudun gara an tadda zago uban nasa ya yiwa babbar 'yar tasa ciki. To dan Allah in ba'a kawo irin wadannan matsalolin ana warwarewa ba ya za a yi kenan. "Ni ma kuwa na taßa jin wani labarin na fada çikin saurina muma fa haka aka yi kusan irin wanan a unguwarmu, mu kuma wani mutum ne da ya karanci jahilci har yayi masa yawa, yake tafiyar da rayuwar dabbobi a cikin auratayyarsa wato shi yawan aure gareshi, 12 LUBABАН amma uwar gidan ta na nan ba'a korarta, amma da zarar ya karo aure to Allah yasa tayi wata biyu zuwa uku ya sake ta ko da yake ba a tababtarwa da sakinsu ya ke yi ko kuwa guduwa suke yi wato Halima shi babu ruwansa da wannan girkin ki ne ko ba naki ba, shi dai zai kawo abinci in kunga dama, ku dafa tare, in kuma baku ga dama ba kowa tayi nata dan kuwa shi a kowane dare tare ya ke kwana da su wai dan masifa mace daya bata isar shi. Kai Allah ya rabamu da bala'i. "Amma wannan babu aure a tsakanin suma mace za ta iya neman saki, dan kowa ai yana bukatar sirri da kuma mutuntawa sannan ma ai kwata-kwata wannan rayuwar dabbobi ce. Na kasance cikin tagumi ina jimamamin irin wadannan matsaloli na rayuwa, wata 'yar ajin mu ta shigo. Na daga kai na kalleta gami da murmushi, tace "lafiya naga kina tagumi Humaira"?, tace, "wallahi wani labari ne na al'ajabi ya shiga dauremin kai. A hankali na bata labarin ita kanta tayi mamaki, tace ko da ya ke ba abin mamaki bane, mu ga wata nan a kusa da gidanmu ita take tura yaranta karuwanci dan kawai su ringa samo mata kudi saboda tsinancewa. Na yi murmushi nace, "ai wannan ba saban abu bane irin hakan ai ta dade tana fəruwa tayida riya tace har kin tunomin da labarin 'ya'yan dadi da 'ya'yın Momi amma ba zan baki labarin ba ki saurari wni littafi da yake shirin fitowa mai suna (BATAN BASIRA) saboda marubuciyar makociyar muce, to littafin ne na dan karanta kinga bai dace in baki labarin ba tun da tace dani amana muna cikin shirar wata yarinya ta shigo ta kalle nit ace (Senior) Humaira wai in ji Sa'adatu Bello tace ki je an zo miki ita masallaci zata wuce shi yasa ta aikoni. Na yi shiru kamar mai tunani nace ba ta ga ya miki sunan wanda yake sallamar dani ba, ko kuwa itama bata sani ba? wallahi sinior Humaira nima ban sani ba can na tuna mun yi da Yaya Auwal zai zo dan haka cikin sauri na gama shirina na fice cike da matsanancin doki. Na same shi jingine a jikin motarshi yana hangoni ya shiga murmushi ina isa gurin shi na durkusa na gaidashi kasa mikewa nayi tsaye saboda tsananin kunya. Babu abin da yake haifar min da matsananciyar kunya face irin kallon da ya ke min irin kallon da Yaya Auwal yake min kallo ne mai kunshe da manufofi daban-daban da kyar ya shawo kaina na mike tsaye muna hira mun jima muna hirarmu cikin jin dadi da kaunar juna ya ringa yayyafo min maganganun so da kauna, masu kwantarwa da ma'abocin kauna rai, mun kuma jima muns yarfowa junan mu murmushi mai gamsarwa. Hakika babu abinda ya fi 13 WANDA YACE NAMIJI UBA2 zama da masoyi dadi a duniya zuwa can da kyar mu ka yi sallama kasancewar Malamin da ya ke duty a ranar ya masa magana. Na ji haushin maganar da malamin ya masa to amma babu yadda za mu yi, dole haka muka hakura da juna ya kawo tsarabar da ya zo min da ita muka yi sallama ina mai bashi sakon gaisuwa ga mutan gida baki daya. Na dawo dakinmu cikin farin ciki, Halima ta tare ni da fara'arta tace babu tantama yayan zamani ne. Na harareta ina dariya, nace waye kuma yayan zamani? Tayi dariya tace "Yaya Auwal mana su ka yi dariya suka tafa nace ashe dai kin gane? Tace, wallahi sai wannan hausar ta zauna miki a baki in kuwa kika saba zai yi wuya ta fice daga bakinki muna cikin hirar Sa'adatu Bello ta shigo na yi mamakin ganin ta kasancewa rba wani shiri muke yi da ita ba sosai, to amma dai bamu nuna mata ba mun jima muna hira da ita sannan ta tafi. A washe gari bayan mun dawo daga dakin cin abinci muna zaune sai gata ta shigo, nan dai muka zauna muka dan taba hira, har muka fara sakin jiki da junanmu. Na ce lallai Sa'adatu ban taba zaton kina da surutu haka ba, ko da yake dama ance in baka zauna da mutun ba to fa ba zaka san ba ko shi waye. Ta bukaci in bata hotunana, ta gani na dauko na bata. N alura da ita, hankalinta ya fi tsayawa akan Yaya Auwal har raina ya dan so ya baci kasan kishinmu na mata. To Amma da ta nunamin shi tace "wannan shine ya zo miki jiya ko? Sai na dan saki raina, nace ina jin kallon yana da nasa ba da ta gano ko waye, ko kuma kama ta gani bata tantance ba. Nan ma mun jima muna hira sannan ta tafi tana fita Halima ta kalleni gami da murmushi tace naga alamar Sa'adatu nan nema take ta shisshige miki". Nace 'nima na lura da hakan. Na gama shirya mana komai a lokarmu muka zauna muna hira a ranar bamu da niyyar zuwa karbar abinci don a ranar bakin tuwo ake yi, wato tuwon dawa. Da daddare sai ga Sa'adatu ta kara zuwa muna zaune muna cin abinci wato in do mi ce muka jikata da ruwan sanyi ya jiku, muka zuba miyar da yaya Auwal ya taho mana da ita muka fara ci. Na yi mata bisimilla, ta sa hannu muka ci sai da muka zauna muna hira zuwa can na ji tayi ajiyar zuciya gami da doka uban tagumi. Nace, "ke kuwa lafiya kike ajiyar zuciya? "Ta dan yi murmushit ace, "lafiya mana Humaira, amma dan Allah in har ba zaki damu ba dan Allah ina san in tambayekiw at amagana da fatan baki damu ba?" 14 LUBABАН Na yi 'yar dariya nace"in banda abin Sa'adatu me ye na bacin rai daga tambaya Halima tayit sagalt ace ko kuwa dai tambayar mai tsaurice nace "ato Allah yasa dai ba ta fi karfina ba don in kika yimin mai tsauri na hadaki da ban sani ba". Ta dan yi shiru ba ta ce komai ba Na yi murmushi nace, "uhm ina sauraron ki itama murmushin ta yi tace dama tambayar akan yayan ki ne nan da nan gabana ya yanke ya fadi, nace yayana lafiya?" Tace lafiya kalau, wato tun lokacin da naga dan uwan nan naki na dan far ajin wani abus ai da na zo naga hotonshi kuma sai na ji na kamu da sonshi so mait sanani, wal...."ke...ke tsaya dakata ina zuwa cikin za fin rai gamida tsananin kishi na dakatar da ita. Nace, wane irin zancen banza ne haka? Shi yasa dama kike wani mammanne mana. Halima ta karba tace, Sa'adatu kina da hankali kuwa? Ki zo gun matar mutum kice kina son mujinta cikin sauri ta zazzaro ido gami da dafe haba. Tace "dan Allah fa? Dan Allah kiyi hakuri Humaira ki rufa min asiri wallahi sam ban sani ba dan Allah ki yi hakuri, ai ko da da bakin shi yace yana sona ba zan yadda mu hada kishi da ke ba cikin sauri nace balle ma ba zai fada ba har abada ba ke bama ko wata ce, dan kuwa yaya Auwal tuni ya rufe bakinsa dan fadar kalmar soyayya kamar yadda ya rufe idon shi da kallon mata. Na kalleta na yi murmushi nace ba kima da hankali, ke ko yaya Auwal ya rasa mace kina tunanin zai soki, to kin yi kuskure dan kuwa ke ba irin tashi bace. "Ni dai dan Allah ku yi hakuri, kuma karku gayawa kowa. Na ce, "Jimin banza shasha, ke da ke a' magulmaciya kika daukemu?" "la wallahi ba haka nake nufi ba to mun ji fice ki bawa mutane guri. Ta daga kai a hankali ta kalli Yaya Fahad tace, wallahi tun daga lokacin na ji na tsaneta yaya ni macece mai tsananin kishi. Dan a lokacin in da za a bani izinin in kashe makiyyiyata to kuwa da Sa'adatu zan kashe. Na ji sam wata walwala tawa ta bace Halima taci gaba da bani hakuri na dubi Halima nace in ma banda iskanci Halima ta yaya za a yi ta tare ni da wannan maganar. Halima ta tuntsure da dariya, tace lallai Humaira kina da aiki. Duk ranar da yaya Auwal yace zai maki kishi ya haukacewa za ki yi. Na ce lallai kam ranar kuma ai dawanau salamu alaikum in kuwa ba nan ba na yada zango a gwauron dutse, gaba daya muka sa dariya muka tafa. 15 1 ta a y K ci WANDA YACE NAMIJI UBA2 Nace, "ko kina shakka ne? tace karyar banza wallahi wata rana da kanki ma zaki bukaci kishiyar ai ko ba mutuwa a'kwai cuta in kuwa babu cutar to kuwa akwai larura mai tasowa ke dai kawai Allah ya kyauta, amma wallahi ko alkawari yayi miki kada ki sake ki yarda wuyar ta dai ya aureki ki zama rabonshi", "kai haba Allah ya kiyaye da bakina in bukaci kishiya, sai kace wace ta kur6I giyar wake, ke ni uwata ma ban ganta da kishiya ba balle ni. "Na ji, amma ai namiji bashi da tabbas maman ma ai ba ki ga ta tsufa ba, ba a yi mata ba komai ki kaga bai faru ba to lokacin shi ne bai zo ba. Na yi dariya nace haba sai kace uban Lariya Musa kin san fa lokacin da aka cire ta daga makaranta za'a mata aure da da daurin auren babanta za'a hada, to amma sai aka daura auren aka daga bikin uban sai zuwa satin sama kuma kin san Allah itama babanta bai taba yi mata kishi ya ba? uhm to Allah dai ya kare iyayanmu muma kuma Allah ya kare mu. 'Na kalle ta nace, ku dai tuni an yi tace, Uhm ke dai bari, ina hutun nan wanda ana yin hutu a washegari na kai miki ziyara kuma da aka dawo ban dawo ba ina can jahar Jigawa a gidan Kawuna wallahi gidan ramu ne babu dadin zama, kullum Mamanmu suna čikin fada ita da sa kishiyarta su duka kowa babu hakuri. Yayin da shi kuma mahaifinmu Ti sam yaki daukar wani mataki, akan fadan nasu. Da dadawa ne ma naji a' Babanmu yana cewa zai kare aure tun da sun ki dai na fadan amma kuma har yanzu shiru kake ji, komai ya s aoho kin san abinda ya shafi iyaye ba lallai ba ne mu sani. ya ail ga ya taf cik nin tsal kur gud dan da s sanı shig Ana Na yi murmushi nace "ni da Baban nawa m azai kara auren da naso, wallahi Allah ya hadashi da mace masifaffiya". Tace, "aiya dai wallahi gara karya kara, dan kuwa in har ya kara yin auren masifa се zata karu, tun da dai ba a san wacce za'a auro ba kuma kin ga in Allah bai kawo karshen abin ba sai ki ga ya shiga wata damuwa da tafi ta yanzu haka dai muka zauna muna ta ttauna matsalolin aure. A B wannan hutun bamu da lokacin kanmu sai na karatu saboda yawan gwaji da ake mana saboda lokacin yin jarabawa sai kara matsowa ya ke yi. A ranar da aka yi hutu Manu direba ne ya zo 16 LUBABАН daukata. Na je na tarar da su Kadija duk an dauko su. Bayan an gama murna da ganin juna aka zauna ana ta hira. A washe gari muka ta wuni gidan Abbana, har su Khadija. A can muka wuni muna hira har da Abban nawa. Da muka tash tahowa ne Maryam tace, ita a can zata zauna wanda nan muka bugaw Mama muka yi mata bayani dan ta Alhaji mai sauki ne na tababta ba zai damu ba. Da farko ta nuna sam bata amince ba. Amma daga baya ko mai ta tuno oho sai kuma tace a barta ta kwanan. Amma kwananta biyu kawai Mama tace, dani da manu muje m daukota. A lokacin da muka je dauko tan sai muka tarar Abba ya fita da ita. Dan haka sai Manu yace shi zai tafi, da yamma ya zo ya dauke mu. Da na yi niyyar tafiya can kewayen Hajiya Iya, amma sai Hajiya Rabi tace in zauna mana in taya ta hira. Tuni na lura da irin shishshigin da take yi min a yanzu da farko an yi zatan don in saki jiki da ita ta zugeni in yadda da kaninta amma sai wata zuciyar ta shiga kokwantan an ya kuwa Abba bai dau mata ki ba a kanta. Hakika haka ne, dan kuwa nan zuciya ta tafi tsayawa dan haka tabbas ba karamin babban mataki Abban ya dauka ba. Amma me muna zaune muna hira da ita zuciyata ta dan saki kadan dan har yar.zu ban ga dalilin da zan saki jiki da ita ba sosai. Kaninta Nasir ya shigo. Sallamarsa kawai na ji na bala'in hada rai. Yayi gyaran murya gami da langaße kai yace, "Humaira manya, sai kace, wacce aka aikowa da Mala'ikan daukan rai. Sam ban tanka masa ba har ya sami guri ya zauna, ya gaida Hajiyar sannan ya kalleni yana murmushi yace Malam Humaira babu gaisuwa kuma?" to ina wuni" Cikin daurewar fuska nace, "lafiya". A nan ne Hajiya Rabi ta daga kai t akalleni yayin da taci gaba da tambayar Nasir" ya mutanan gida?" yace, suna nan lafiya, hirar muka kara yi tana gurin baifi ta minti hudu ba ta tashi ta fice ta barmu mu kadai. A raina nace, "lallai kuna da fama tana nufin zan zauna da wannan kurjajjan mutumin ne. Cikin kasaita ya zaro karan sigari ya dasa a bakinsa yayin da ya karo ashana a yangance yana shirin Kyastawa. Amma ni tashi nayi da nufin in bar gurin duk da cewar warin taba baya hanani sukuni. Ina fita ya shiga kwalomin kira, amma banza na yi dashi na nufi gidan makotanmu, dan kuwa ba zan iya zama daga ni sai shi ba a dakin to in ce masa me? 17 WANDA YACE NAMIJI UBA2 A zahiri na yi matukar farin ciki dangane da irin karbar da suka yi min duk da cewar zuwana bai fi daya, zuwa biyu ba kai tsaye falon Hajiya Nafi aka yi dani daya daga cikin matan gidan munz auna muna ta gaisawa da mutan gidan, wata Budurwa fara jajir da ita ta fito daga can cikin dakin hajiya Nafin irin matan nan ne da fari ya yi musu yawa muka gaisa da ita, haka kawai naji ta kwantamin a rai, Hajiya Nafi ta fice zuwa dakin girki ta barmu da ita muna ta hira. "Amma ba a unguwar nan kike ba ko?" Ta tambayeni, na yi murmushi nace, da ita "a nan na ke mana. Ga gidan mahaifina nan nan makotanku, saida i ince da ke ba'a gidan na ke a zaune ba. Shin ya sunan ki ne? murmushi tayi tace ita sunanta Hajara Sale, amma ita ba 'yar unguwar bace, zuwa dai tayi kanwar Hajiya Nafi ce ita na sake tambayar da cewar, à wacce makaranta take? Murmushi tayi tace E to kafin shekar abiyu da suka wuce in kika tambayen wacce makaranta na yi na iya ce da ke 'yar gaya. Amma a yanzu haka matace a gidan wani. Abin ya yi matukar bani mamaki dan kuwa ban taba zatan hakan ba danni kallon ba ta fi sa'a ta ba nake mata jin tace ita matar aure ce, sai jikina ya yi san yi dan a zatona ba zata yi kawance da ni ba. Tacig aba da ce dani maigidana na tane ya tafi Saudiyya sł.i yasa ta zo ta za ına a gidan har sai ya dawo, kasancewar kanin maigidan take aure. Ama ita a Saban titi suke da zama taimin kwatancen gidan ta har na gane. Na yi mamaki da na ji tace dani tana fata zumuncin mu zai dore, abin yaban mamaki nan take nace da ita in sha Allah. "Amma ke ba 'yar gidan Hajiya Rabi bace ba ko?' Na dan yi murmushi nace" saboda me kika ce haka?" murmushin itama ta kara yi tace, "a'a dan naji anc e bata taba haihuwa ba" "Hakika ni ba 'yar ta bace uwata tuni ta fita daga gidan na bata amsa daga nan na mata kwatancen gidan gami da sanar da ita cewar a wannan uwata nake, itama tace in sha Allah zata kawomin ziyara. Nan dai muka zauna muna ta hira. Hajiya nafi ta shigo tana dariya, tace sai kace kun san juna daga gamuwa yau daya amma kun kama hira kamar kun shekara da fara ganin juna. Muna dariyar muka yi gami da kalon juna nace Hajiya ai gamuwar jini ne muna cikin hira ne nake ce da ita nima na kusa kammala karatuna in mun koma wannan hutun ba zamu dawo ba sai mun gama jarabawa. Itama taci gaba da cewa dani, cikin satin mijinta zai dawo in sha Allah, saboda haka da zarar ya dawo zan ganta. Nan dai muka yiwa juna alkawarin kaiwa juna ziyara a kai-akai. 18 LUBABАН "Abba yace ki zo mun dawo". Maryam ce tá shigo da gudu tana sanar dani sakon nace, kai Maryam, baki da hankali ne? ta yaya zaki shigo mana daki a guje ko sallama babu wallahi yaya nayi sallama kece dai baki ji ba. Abba ne yace in zo in kiraki daga nan muka yis allama da Hajarar, na kuma je na yiwa su Hajiya Nafin sallama na rike hannun Mary muka tafi, muna zuwa kofar gidan ta fizge hannunta ta shige gidan a guje daga ita sai irin farar T shet din nan da gajeren wando ka yan sun yiwa mary kyau matuka. A kishingide na tarar da Abba, don ina shiga gidanf alons ana zarce. Na durkusa na gaidashi, na kuma ce Mama tace, a gaisheka murmushi yayi yace, ko kuma Humaira tana gaisheni ba. Nima sunkuyar da kai na yi dan kuwa karyar na shirya. To amma ai irin wacce ake so na yi, wato gyara zumunci mun jima muna hira zuwa can ya yi gyaran murya yace, "Humaira yaya yayan naki Auwal?" Sunkuyar da kai kawai na yi nayi murmushi yaci gaba da cewa, Humaira, Allah ya sani bani da burin in tursasaki akan abinda bakyaso, saboda kema kina da hakki a kaina kamar yadda nake da hakki a kanki sai dai kuma ina da damar da zan sanar dake ra'ayina, in kinga da hali kibi, in kuma ke bai miki ba to. A gaskiya Huniaira in da a son raina ne nafi sha'awar in ga kin auri Auwal,s aboda shi Auwal yaro ne mai hankali gashi kuma dan mutunci, kuma ina ganin Auwal ba zai taba cin amanar ki ba, balle yayi sha'awar cin mutuncin ki kowa yana yabawa da hankalinsa kuma dagani yana tsananin sonki, gashi kuma sam bashi da fitina, dan Hausawa na cewa alamar mai karfi tana ga mai kiba ko da yake hausawa na fadin ba a ya ban kuturu sai ya girma da yatsa, to amma fani tun daga yanzu na yabe shi. A zahiri na so in sanar dashi sirrin dukiyata tun da wuri to amma nahaifiyata tace kada in kuskura in yi saurin yin haka tun yanzun in ari har sai an yi auren in an yi auren ma sai kin haihu in ba a ga wani an ji a zamanku ba saboda akasari samarin yanzu sha'awa tafi yawa a 'amarin auratayya, shi yasa za ka ga wuyarta mace ta haihu tana ahuwa za'a fara shiga babi na daban ko da yake tuni nake sanar da ke akan komai zan fada miki maimaici ne. A nan ne na daga kaina na kalleshi na dan lokaci, hakika ba -a, amin so mahaifina yake yi min ba, na bude baki a hankali nace, to -bba ya jima yana shimin albarka, wanda hakan ba karamin dadi ya yi 19 WANDA YACE NAMIJI UBA2 min ba. Daga karshe yamin addu'ar Allah ya bani 'ya'yan da za su yimin biyayya a raina nace ameen. A nan ne Abba yaf ara sanar dani kadan daga cikin irin dukiyar da yake da ita, abin ya ban mamakida naji yace, in sha Allah zan tattara dukkan bayani a rubuce in baki komai a hannunki, ina fata dukiya ba zata canza miki ra'ayi ba. Dan kuwa ko rabi ban sanar da ke ba. Har'abada kada ki dauka Allahn da ya bayar ba zai iya kwacew aba tsimi ko dabar aba su za su habaka dukiya ba,

Chapter 2 of 11