yana manne da ita zance kadan
yace Amina kaza da kaza, in kuwa labarin wata ake bayarwa, yace
shima Aminarsa kaza da kaza. Amma suna dawowa gida ta
dauroma a kirji zai jefeta da jakar ya kama zaginta yana cewa
shegiya kin barni la jaka kamar wani yaronki, kuma in ta hana shi
jakar ma masifa ce duk wanda ta gayawa ba zai yadda ba ke ta ringa
zaman ukuba da mutumin nan tun tana hakuri har hakurin ya kare
suka fara dukan juna, tun da suka yi kokawa kuwa ta daina tsoransa.
Yana cikin zazzaginta kanwar babarta tayis allama a dai-dai
san da ya kai mata duka da kafa, da yake Alah ya kawo karshen
abin anan dai ta rikicewa kanwar babar ta tace sai an raba aure kai
Allah dai ya kyauta, ya sa mu gane gaskiya gaskiya ce. Amma fa
gaskiya auren yanzu ba wuya ya tumbuje. Ko da yake ke dai naki
labarin gaba daya kece baki da gaskiya dan kuwa rashin hakurin ki
ne yajawo komai. Amma da yake namiji shine karkatacciyar kuka
me dadin hawa har kike da bakin kiransu da duk wanda yace
Namiji Ubane zai mutu maraya ko da yake wasu mazan da laifinsu,
amma fa wasu basu da laifi lai fin mune mu mata da rashin
hakurinmu amma in aka zo zagin Namiji mun fi kowa zakalkalewa.
Yauwa Humaira dama ina san in tambaye ki wai ni ba za a dan
shafamin labarin in jiba?" "wane irin labari kuma? "a'a a dan
gutsuro min labarin abinda yake wakana tsakaninki da yayan nawa
LUBABАН
mana". Tayi dariya tace, kin ji ki ko? mene ne tsakanina da Yayan
na ki? kina tunanin wani abune?" "a'a bana tunanin komai, amma ai
in tayi tsami maji to sai ki bari in tayi tsamin kwaji sun jima suna
hira a junansu da lokacin sallah tayi suka yi har dare yayi su kansu
basu sanda re ya yi ba Hajiya ta sanar da su hakan.
Yauwa Humaira, sai yanzu kika tashi, lallai hakan ya nuna min
jiya baku kwanta da wuri ba kun zauna kuna shegiyar hira ta babu
gaira babu dalili". Cewar Hajiya, sanan taci gaba da cewa yi aniya
ki shirya kizo ki raka Shafa'atu, zan aiketa can gidan mu. Gurin
Babana abin ya daure wa Humaira kai, dan ita bata taba zatan
Hajiya na da ko da babban wa a raye ba balle mahaifi. Hajiya taci
gaba da cewa, "wallahi yajin daddawa ne na dan daka masa da
kuma dambun Nama, na ke son kuzo ku kai masa, kin san bakin
tsoho sai da abin kwadayi. Shafa'atu tayi dariya tace balle ace an
sami kwadayayyen tsoho Hajiya tace "Shakiya uwakice
kwadayayyiyar ba wani ba. nan dai suka sa dariya gaba dayansu
sannan suka shige dakinsu suka kara shiryawa, suka fito suka karbi
aiken suka tafi.
Yayin da suka fito ne suka ringa takawa dai-dai gaskiya ba
karamin jan hankalin jama'a suka ringa yi ba musamman mata sa
masu burin a gansu jere da tsala-tsalan 'yan mata. A gaskiya dole su
ringa tafiya da hankalinjama'a, irin wannan yanga haka musamman
ma Humaira da take takun ta sama-sama tamkar mai tafiya a iska.
To amma kallan nutsuwa zaka mata, ka tabbata abin ba yanga bace
halittar ce dai haka wata zabgegiyar mota ta ban mamaki,
zungureriya ta ringa kokarin gogarsu suna tafe tana kokarin
tsayawa dab da su. Hakika duk cikinsu babu wanda ya taba ganin
irinta, in kuwa z ąsu yi tunanin sun taßa ganinta to baiwuce su tuna
kisisina irin na Amerika ba hakika motar ta birgesu matuka. Yayin
da tazo dab dasu cikin hanzari aka budeta, wanda hakan ya haddasa
musu faduwar gaba. Dan kuwa dab da su motar ta tsaya. Tana
tsayawa wani mutum ya fito da sauri tamkar wanda aka jefoshi.
Kallo daya za ka yi masa ka tabbatarwa kanka cew aba mamallakin
motar bane in ma da abinda ya dace a kirashi bai wuce a yi masa
lakabin da dan kanzagin mai motar ba.
91
WANDA YACE NAMIJI UBA2
"Yan mata ina za a ne haka? Ga shi kuma da sauranr ana a
gari, alhalin Allah bai yo ku dan rana ta dake ku ba, hakika babu
raban rana a jikinku. Banz a suka yi dashi yayin da suka yi gaba
yanabinsu. Haba 'yan mata ran gari, ya ana muku magana kuna kokarin wucewa abinku? Dan Allah ku karaso bakin motar ga me
san yi muku magana can. Daga kai su duka suka sakar masa wani
irin kallan banza, wato kallan iskar da ta kwaso shima bata ishesu
kallo ba, suka yi masa suka cigaba da tafiyarsu, su duka babu
wanda yace dashi ci kanka, bin su yaci gaba dayi yana musu magiya
wanda har ta kai su ga kulewa, hakika kallan fuskar mutumin za ka
yi ka tabatarwa da kanka, cewa abin ya bashi mamaki.
Ya dan tsaya yana kallansu dan shi tunda suke irin wannan
barka basu taba karo da yaran da suka yi musu wulakanci haka ba
wato sun dade suna jidar yan mata don holewa amma duk wacce
suka latsa sai ta bada kai bori ya hau kaf garin babu wanda bai san
shaharar kudi irin ta Alhaji Maude ba na unguwar Toka. Dan haka
duk wacce ya taya bata sanya wajen amincewa da binsu dan ta
dangwali arziki, san ranta dan kuwa yana da wani shahararren gidan
shakatawarsa da ke canw ata unguwa mai suna NIYU NAJERIYA
(NEW NIGERIA).
Ya kasance bashi da wani abin yi face neman mata, matanma
kananan yara. Sam baya lura da girmansa da kuma tsufansa, don shi
a tunaninshi neman kananan yaran shi zai haifar masa da kwarin
jikin shi ya ringa komawa yaro dan in yarinyama bata amince ba sai
yaje ya kashewa iyayenta kudi, har su bashi ita ya aura da zarar yaci
moriyar ganga sai ya yaga kauranta ya komawa wata. Dan kuwa
mutane ha rada masa wani suna suka yi wai bitamin (Vitamin)
wannan suna ya biyoshi ne tun daga jama'ar Sokoto. Dan da can
yake zuwa daukar mata, kafin abin ya shahara har ya shigo cikin
gari.
Yau dai ba da wanan nufin zait saida su Humaira dan bai ga
alamun za su amince da zancan ban za ba wannan karan nufinsa
yayi tayin aure dan it akanta ta fita da ban dan haka ta wuce irin
matan da sukewa lakabi da sunci burodi sun yaga leda ba. Dan ita
Humaira, ko anci burodin ledur ma adana take. Babu yadda dan kan
zagin nan bai yi ba amam suka ki kula shi abin haushinma ko ta tafa
92
LUBABАН
sa ma basu ce da shi ba. Har shi da kansa Alhajin ya gaji ya fito da
kansa, amma'basu kula shi ba gab dasu suka ji, tafiyar mota a
hankali waigawar nan da suka yi babu wanda bai yi murmushi ba
saboda murna da zukudı yayin da murmushin ya kara narkar da Alhaji a nan.
Yaya Fahad ne ya ke binsu cikin sanda shi kansa bai taba
zatan gamuwa da su ba lokacin da suka karasa gurinsa gaba daya ya wangale baki saboda dadin da ya ji ganin yadda suka wulakanta Alhaji amma shi har karkarwa yake yi dan su shiga motar wanda ya
tabba dan su huta da wani mai katan cikin nan ne Alhaji Maude.
Ya dube su yana dariya, yace Humaira kin cika tsoro, yayin da
ta zagaya can 6angaran tana kokarin bude gidan baya. Sauri ya yi
ya kulle bangaranta yayi yace mene ne haka ni direban kune? Tun
da ita ta shiga bayan ke ba sai ki shiga gaba ba". Bata masa musu ba
ita dai burin ta subar gurin sai da ya tada motar sane sannan
Humaira ta lura da shigar da yayi wato irin din kin nan yayi wanda
yawanci inyamurai suka fi yinsa da shadda kamfala ko atamfa, to
shima dai da atamfar yayi wata gajeren wando ne da riga dinkin T.
Sheet da aka masa. Hakika kayan sun burgesi tsarguwa yayi da irin
kallan da take yi masa yayin da ya waigo ya dubeta yayi murmushi
yace, ya dai Humaira?
Yayan naki ba da ma ne ko. Tun da har jikínsa ya bashi
kannansa na cikin tasku, ya zo ya cece ku daga gurın mai katan
cikin nan ko. Ni da na hangoshi ya fitoma na yi zatan hango ku yayi
ya fito zai hadiyeki, saboda yinwar rana kin san kuwa tun da nake a
garin nan ban taba ganinshi a tsaye ba. To mutum ne kullum yana
mota kamar sitiyari, murmushi kawai tayi bata bashi amsa ba
saboda ita bata manta cewa da Shafa'atu a motar ba yayin da shi
kuwa sam ya manta sai wani zakwadi yake mata.
Ya dubeta yayi murmushi yace to wai ma ni ina zaki ne? Na
dauke ki ba tare da na tambaye ki ba wai gowar nan da zai yi sai ya
hangi idan Shafa'atu kyar a akansu, ta mudubin motar na tsakiya,
nan take ya tuno tare suke, wanda da sam ya manta. Tace can gidan
su Hajiya zamu itace ta aikemu ya dan saki murmushi yana sosa
keya yace yanzu haka wani abu za'a kai masa ko? Ita daga ta dan
sami kudinta sai tayi ta kashewa wannan gawa taki ramin ko
93
WANDA YACE NAMIJI UBA2
dayake itama albarka take nema Humaira tayi murmushi tace, ashe dai ka gane Yaya.
Yaya Fahad shi ya kaisu suka shiga suka gabatar da sakon Hajiya, har Yaya Fahad din ya ringa tsokanar kakan nasu wai ga matanan ya yo musu sabuwa fil kakan nasu yayi dariya yace, Allah
yasa wannan nutsatstsiyace, wacce zaku zauna lafiya dan nan bana
san in ga ana irga maka aure, daga karshe har a ringa kiranka da sunan auri saki tun kana yaran ka karami yace in sha Allahu. Amma
sai da daddare zan dawo in baka labarin ta saura kuma ka tsuke
roman labarin daga karshe ka shiryo dafin yakata". Yace ato ina dai
nan in ajiranka.
Yayin da ya tsaida motarshi a kofar gidan nasu Shafa ce tayis
auri ta fice, dan ta san dole Yaya ya bukaci su dan zanta da gwanar tashi. Humaira na kokarin fita ya tsayar da ita yace "gaskiya zan shiga in yiwa Hajiya bayanin gara in tafi da ku yanzu ku karasa min
aikin saboda gobe ina da manyan baki daga Abuja saboda wani
abokina ne ya yomin waya yana min tsiyar, wai zan zo yaga wacce
ta hanani zama gurin aiki kuma su gani shin naci yakin, na kafa gwamnatin ko kuwa?
Yaya kenan in ji Humaira yayin da suka yi murmushi cikin
kasaita da nuna tsantsar kaunar au tambayata ma kike yi a gaskiya
ina bukatar ki nuna tsantsar son da kike yimin bana san ya zo ki
fara inda-inda kinga sai suyi min dariya tayi murmushit ace Allah
ya kawoshi lafiya.
B
yau dai Hajiya ta gaji da kumbiya-kumbiyarki, tace in Akiraki ki sanar da ita labārin ki naso ni in gaya mata amma
tace ita daga bakinki take san jin labarin. Shafa ce ta shigo
ike da fara'arta tana gayawa Humaira, taci gaba da cewa haba ai ta yi ma ban taba zatan zata barki har iya wadannan watannin ba, ba
are da taji labarin ki ba, to amma kije yau zan yi zaman kadaita na dan lokaci kafin ki dawo, koda yake sai in duba wani saban littafi da ya fito kwananan wai shi kishin Bal-Bal. Humaira tayi dariya
tace kishin me? Lallai za a yi bala'i. Bari dai in je in dawo mun yi ΟΔ
LUBABАН
da Yaya Fahad zai zo yanzu dan Allah ko ya zo kice ina can Hajiya
ta ritsa ni.
A lokacin da take dab da fita daga dakin ne sai ga Fahad ya
leko yace, "Ke Humaira ina zuwa zani in gaida Hajiya Inna fito ina
jiran ki a waje". Yayin da ya tsareta da iro. Ta sakar masa
murmushin tace, "yaya kenan yanzun nan nake bada sallahu a gun
Shafa wallahi Hajiya ce take kirana, kuma labarina take san in bata,
yayi murmushi yace, dan Allah fa ki kiyaye, kada aje a saki baki da
yawa ko danma, ke Shafa tashi ki fita yayin da ya tsare Shafa da ido
Shafa'atu ta tashi ta fice, a ranta tace kai Yaya kenan yana ji da
Humairar nan sai kace soyayyar saurayi da budurwa.
"Amma fa dan Allah Humaira ka da ki tona min asiri a gurin
Hajiya abin nufi a nan shine, dan Allah kada ki bata labarin irin
soyayyar da kuka yi ke da Auwal dan abin zai iya tsaya mata a rai,
kuma kin ga ko Aure muka yi ta gama sanin irin soyayyar da muke
yi duk da cewar tamu da zamu shimfida ta take ta yayanki ya dan
murmusa sannan yace, kin san Allah Humaira ki yadda dani
soyayyar da nake burin koyar dake za ki sha mamaki, don kuwa in
har kika kasance cani ko mata dari nace zan aura ba zaki iya guje
min ba. Baran tana ma kece daya da daya. Ko da yake, bani ke da
rayuwata ba, ban kuma san abinda zai faru ba nan gaba, kada wani
tsautsayin ya gitta ki gujeni, kice na karya alkawari.
Amma fa ke kanki kin san da wuya likita ya ajje mata biyu a
gida ya riko hannunta yayin da ya kura mata ido ya miko kai da
nufin ya sumbaci kumatunta, ko mai ya tuna oho.. B adai ya wuce
rashin kyan hakan a sharadin musulunci sai ya dakata ya lumshe ido
yace, I love you Humsy na lallai shin sai yaushe zan kaiki gurin
gyaran gashin ko kin fasa ne? Tayi murmushi tace,"gobe ba sai mu
je ba. Amma yanzu ka barni in je gurin hajiyar ka da taga shiru ya
kashe mata ido yace kada ki damu nasan tuni Shafa ta sanar da ita
muna tare nasan in kika je, sai magariba kin ga ni kuma ba daman
zuwa sai gobe saboda dokar da Malam ya kafa mana.
A gaskiya yaya ina jin kunyar Hajiya ka barni in tafi kaga
ta.... Yayin da ta sinkuyar da kanta tana murmushi sakamakon
kallan da ya watsomata yana mai kashe mata ido yana murmushi,
wanda hakan yaso ya damalmala mata lissafinta. Ba dan komai ba
95
WANDA YACE NAMIJI UBA2
sai dan sanin sirrin abin da tayi ta dan kauda kai gefe guda tace, "ni
zan wuce sai goben ko. Binta yayi da kallo har ta fice, bai iya ce da
ita komai ba shi kadai yasan tunanin da ya ke yi.
A lokacin da ta shiga dakin Hajiyar sai ta tarar da Shafa, tana
ta bata labarin soyayyar su da Fahad duk kun ya ta rufe ta, ta
durkusa tace Hajiya gani kasancewar Hajiya ta fuskanci kunyarta
take ji sai tayi murmushit ace, ki gyara zaman ki mana yau labarinki
zaki bani, ko da yake wannan Sarkin şurutun har ta fara na kwabeta
dan na fi son in ji maganar daga bakin ki, uhm ke Shafa tashi kije
kiyi abinda na saki ba tare da tace komai ba ta tashi ta fice. Tana
fita Hajiya ta umarci Humaira ta fara tace kada ki boye ni da komai
kin ji ko kin san abinda naji daga gareki, shi zan tunkari Malam
dashi, saboda haka ki yi min gamsassan bayani ta yadda zan yadda
da ke fiye da yadda na amince da ke ada.
A hankali Humaira ta fara bata labarinta duk da cewar kanta a
kasa yake, amma jikin ta ya bata tabbas labarin ya tsima Hajiyar
saboda yadda taji yanayin numfashinta na sauka koda yake a yanzu
zuciyar Humaira ta dake, sam babuw ani alamun kuka a tare da ita
har ta gama bata labarin. Sai da ta kawo karshen labarinta ne sannan
ta daga kai ta kalli Hajiya a sanyaye, dab da lokacin da ladanin
masallacin na kusa dasu ya bude murya dan kwarara kiran sallar
magariba wanda hakan yayi dai-dai da shigowar Shafa'atu dan ta
sanar da su an fara kiran sallah ita a zatan ta basu san an fara ba.
A hankali kuma a sanyaye Hajiya ta dago kai ta kalli Humaira
tace, sai ki tashi ku je kuyis Allah sannan ki dawo. Dan hakika da
nasan haka labarin ki yake, da ban barki kin yi wannan dogon zama
har na tsawan wata biyar ba. Saboda hakika laifin bai kai na kibar
gidan kuba, cikin gatanki ki taho ki barsu cikin zulumi. Na tabata,
dai da kyar ne in za su yi tunanin zaki fada cikin wani halin na bata,
wato cikin halin sabon Ubangijin ki sakamakon irin tarbiyar da
suka yi miki kema kuma kika tashi dai ta ko da yake, mu mata rauni
ne damu. Gashi kishiya ma tasa farat daya kin sake halayanki kin
sauya ra'ayi balle ace kin gabar gaban iyayenki kin kuma bar
garinku. To Allah dai ya kyauta da ji dai zama kika yi har shaidanun mazuga suka zugeki. 96
LUBABАН
A gaskiya lura da jama'a nutane sunc shaidanu ko dan gaba
su da za su zo su na zugaki, su za su koma gefe suna miki dariya.
Don sai shaidanin mutum du inda zaman lafiya yake burinsa ya ga
ya zuge masu zaman don a 6ata su sami abin fadı 'yar nan hakuri
da rashinshi banbancinsa kalilan ne in da kin yi hakuri ma wannan
auren babu in da za shi. Domin dole cikin zaman aurataya Allah
yana jarabar bawansa ta kowanne hali.
A iya jarabtar bawa ta cusa masa san 'yar da bata isa yayi
zaman aure da ita ba wanda za ki ga al'umma da dama suna surutun
basu dace ba. To amma an yi haka ne dan a jarrabesu baki daya daga shi har matar.
A iya jarabtar bawa da aure wacce sam ba kashin arzikinsa
bace, amma hakan ma jarabtace, kiga mutum da rufina sirin da
komai amma da zarar ya shiga neman aurenta, shi kenan an shig
ahalin kaka na ka yi kenan ko ja jarabci bawa da haihuwar da
makaho, ko gurgu ko wata nakasa, Allah kuma ya jarabceka da son
dan fiye da masu lafiyar in ka dangana ka rikesu amana kamar
sauran 'ya'yanka kaga sakamakon in kuma kana korafi da kai karar
Ubangiji ta hanyar mita nın ma kaga sakamako kuma Allah yana jarabtar bawansa da auren macen da bata ta gari ba. To amma
babban abu a nan shine yawaita ambatan istingifari da kalmatul Shahada, da innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
A gaskiya auren mijinki, wata katuwar ishara ce gareki da kin
daure da kinga sakamakon gaggaw ake da kanki kika ce, ke kin
kasance mai bawa mutane shawarwari, kuma ke mai goyon baan
maza ce, baki yadda da duk wasu kalaman 6atanci da ake
danganawa da suba, ammå gashi a yanzu tashi daya. Allah da ya
tashi jarabtarki, sai ya zamanto kin kasa jurewa. TO kinga hakan ya
nuna dama dan baki da ita ne kike yawan surutan nan ko? Yayin da
ta daga ido ta kalleta gami da murmushi, dab da lokacin da taji an
shiga masallaci a nan ne ta yi salati tace 'yayan nan maza kuyi
aniya ku dauro alwallah nima bari in mike kun ji an shiga masallaci.-
A wannan ranar dai a dakin Hajiya suka zauna suna t ahira.
Tana ta yi musu fadan zaman rayuwa. Taci gaba da cewa Humaira
ko da yake na lura da cewa kin yi nadama sosai da sosai dangane da
97
WANDA YACE NAMIJI UBA2
abinda ya faru, to amma dai a kiyayi gaba hakuri shine babban turken daura zaman lafiya. Musamman ga rayuwar aure ai tabakin naki ne da kike cewa, mu mata butulci ne damu, hakika hakan ne, ko da yake akwai mazan da basu da mutunci, ko kadan, amma wasu kaddarace take gifta musu amma sai muyi mursisi, mu man ta alkhiarin baya, mus higa furta kalaman rashin mutunci a garesu. Alhalin mu namu laifin ma yafi yawa. Amma da yake su masu tunani babu abinda suke kiranmu dashi illa dai da z aka ji Namiji
yana kiran mace karamar kwakwalwace da ita wannan kuwa kasan
in ce hakane saboda mu mata mun cika rauni.
A yanzu zaka 6atawa mace ka wulakantata, ita da iyayenta. In
aka gamu da marar mutuncima ya hada daga ita har iyayenta ya
zaga. Amma da an jima in ya kyautata mata sai kaga ta manta
wancen batancin na baya kuma mu mata in aka fiye sakar mana
mun fi kowa iya shege da mu aka bawa ikon saki to bana jin akwai
macen da zata iya zaman wata guda da namiji. A yau ya bata mata
yauz ata sake shi gobe ta auro wani. Dan haka dan Allah 'ya'yan
nan ku rinka hakuri, shine ribar zaman lafiya mu kanmu iyayen
naku ai suna bata mana, amma wake jin labari, abinda mazan dama
suke yi na yanzu ba sa yi saboda yanzu mazan yanzu sun san dadin
aure fiye da nada ku tuna fa da cewa mutanan da fa daga mazan har
matan babu mai ikon, ya za6I macen aure, ko ita ta za bi mijin aure.
Amma Al'ah ya canza mana zamani, ilimi ya yawait ahar kowa
yasan kansa da matsayinsa. Amma sai matasan yanzu kuke neman
kaucewa, har kuke Ikirarin kwatarwa kanku 'yanci. To ke da kike
karkashin wani, shi zai fita ya nemo ya baki, ina kike da wani
'yanci, baya da bautar Allahda kyautatawa aurenki wato bin miji
sau da kafa meye kishiya da zata bi ta dame ki a rayuwa in kinga
mutum na hauka to shi kansa bai yadda da kansa ba.
A gaskiya ku yiwa kanku fada, ko nan gaba ita rayuwa ba haka
take ba yau ko zane gareki in kika canja sai kin yi dokinsa, wanki
daya biyu shi kenan kin gama dokin sai su koma layin sauran. Dan
Allah ku ringa hakuri a ringa tausasa zuciya. Ta dade tana musu
fada har lokacin bacci ya yi suka tafi suka kwanta.
A washegari tun da suka yi sallar asuba suka koma bacci. Har
sai da Malam ya shigo kewayen Hajiyar sannan tasa aka ta so su
98
LUBABАН
dan su gaidashi. To a nan ne ya kamasu da fada yace me ye amfanin
komawa bacci bayan sallar asuba. Ai an fi son in mutum ya tashi
kada ya koma bacci har sai rana ta fito sosai,w ato kamar bayan
gama haka saboda a wannan lokacin Allah yake saukar da arzikinsa
don Allah 'ya'yan nan ku rage bacci. Ku yawaita addu'a dan
inganta rayuwar ku ku kuma yawaita ibada don inganta lahirarku.
Daga nan suka tashi suka koma dakinsu.
A lokacin da suka koma ne Humaira ta duba agogon hannunta
taga sha daya da rabi har da 'yn mintina dan haka sai ta hanzarta
shiga wanka don kada Fahad ya zo ya tarar bata shirya ba, don yace
za su biya gidan wani abokinsa kafin su je gurin gyaran gashin.
Tana cikin sa kayanta kuwa taji sallamarsu ka'ida ne in ya shigo
gidans ai ya leka sun gaisa kafin ya wuce dakin Hajiya ko kuma
kawai ya buga kofar dakin yayig ab a abinsa yauma kamar kullum
buga kofar dakin yayi sannan yayi tafiyarsa zuwa dakin Hajiya a
wannan lokacin Shafa'atu ta shiga wanka dan Humaira tace ta
shirya don ta raka su.
A lokacin da Shafa'atu tana kallan Humaira ba komai bane ya
kamar da ita sai dan ganin irin kwalliyar da ta varfa, tunda suke da
ita tsawon wata biyar, ta ganta tana yafa kwalliya iri-iri na burgewa
da kayatarwa to amma yau komai da banne. Dan kuwa bata taba
ganintama cikin shigarba haka kuma bama ta taßa ganin kayan ba.
Tun da take a rayuwarta. Da ganinsu kasan tsadaddu ne.
A hankali tayi ajiyar zuciya tace kai Humaira, gaskiya bazan
raka ki ba. Murmushi tayi tace dalili? Tace, "Haka kawai irin
wannan shiga rhaka ai nasan dole ki tafi da imanin Yaya na, babu
abinda zai mai shamaki wajan nuna maitarshi afili". Tayi dariya
tace lallai ma Shafa rnan, dan Allah kiyi sauri ki shirya gashi nan fa.
Dan yan zun nan ya wuce gun Hajiya. Bai ma lekoba bugawa kawai
yayi ya wuce. Tayi dariya tace koda na ji fa ni nasan in da ya leko
to kuwa babu mai fitar dashi, sai dai ni in fita in sanarwa Malam A
hanzarta Daurin Aure tunkan al'amura su Gurbata. Dan babu da
namijin da zai ganki kusa dashi a wannan shigar ya tsaya a hadiyar
yau can cadi sai kace....
A yangance Humaira ta saki 'yar kayatacciyar dariyar tace.
Amma lallai Shafa baki da dama Shafa ta kwashe da dariya tana
99
WANDA YACE NAMIJI UBA2
tufawa tace kaddai ace haka mutuniyar ta kewa Yayan nawa. Irinw
annan make murya kamar kuna tare. Tafiyarsa t ajiyo da gudu ta
shige cikin bandaki yayin da Humaira taci gaba da tace kanka.
A hankali ya shigo gamo da sallama, cak ya tsaya a kofar
dakin yayin da ya zubawa Humaira ido ko kibtawa ba ya yi, Ya
rasulillahi ya fara fada, sannan ya karasa in da take, fuskarsa cike
da nishadi gaba daya idan shi ya rufe, yama manta yayi tunanin ko
Shafa'atu na dakin ya kara cewa ya salam mutum ko aljan
mayaudariyar dariya mai fita da sautin sarewa ta kubucewa
Humaira, wacce ke zaune bisa kujra. Tace Yaya inajin dai aljanarce
ya karasa kusa da ita ya durkusa a gabanta, cikin isa da kasaita
gami da jan ra'ayi yana wani kashe ido, ya buga tagumi gami da
zuba mata ido. A hankali ya lumshe idon yace I love you my sweet
hart.
A gaskiya yau din nan kin rudani da yawa tun da nake a
rayuwata ban taba ganin matar da ganinta ya sa na fita daga
hayyacina har na shiga sake-saken baku gaira babu dalili ba sai
akanki. Ya kama hannunta ya rike, ya shiga wasa dashi, ta yi
murmushi gami da lums'he ido, da yin magana cikin rada-rada,
wanda ko kana kusa dasu ba lalle bane ka ji saboda maketa. Amma
tayiwa mai sauraron dau a kunne tace Shafa na nan cikins auri ya
mike tsaye a daidai lokacin da Shafar ta fito. Don zaman bandakin
ya isheta. Ita da tayi zatan fita waje za su yi yace da ita