kar in bata jikina sai da ta gama muka koma dakinta
muka zauna ta tambayeni mutanan gidan nace duk suna nan lafiya nan
dai muka zauna muna ta hira. 39
WANDA YACE NAMIJI UBA2
Da karfe hudu da kwata Abba ya dawo sai da na tabbata ya
kammala da komai sannan na shiga muka gaisa ya shiga tambayata
harkar makaranta, da yadda muka fuskanci jarabawa. Nan na nuna
masa alhamdu lillahi yace, to Allah ya bada sa'a nace ameen".
"Da kika dawo kin ji wani labari?" shiru nayi yayin da na
sunkuyar da kaina kasa yaci gaba da cewa. Humaira nasan dai kin ji
duk abinda ya faru a lokacin kin amakaranta. To abin da na ke so da ke
a nan shine ki tsaya ki sanar dani ainishin abinda yake zuciyarki.
Humair ain kika fuskanta zaki ga ina yawan yin wasa dake lokacilokaci to ba wai ina wasa dake bane dan raini ya shiga tsakani, a'a ina
yin wasa ne dake kawai dan ki ringa sakin jikinki aa guna ya zamto kina
fadamin duk abinda yake damunki.
Da farko da naso ace an barki kin dan yi ko da wata ukune, don ki
huta sosai, to amma Alhaji Safiyanu ya nunamin matukar damuwarsa
akan son a hanzarta yin auren hankalin kowa ya kwanta. Na tabbata an
sanar da ke lokacin da aka tsayar ina fatan dai kina ganin bant auye
miki hakkin ki ba. Humaira ni dai ta 6angarena na gama miki komai
lokaci nake jira. Amma in har akwai abin da kike bukata ki gaggauta
sanar dani.
Daga karshe, Humaira ina shawartarki da ki riki aurenki tamkar
ranki, ki so mijinki kamar yadda za ki so kanki. Ki rik mutuncinshi
kamar yadda zaki rike naki mutuncin. Ki mutunta danginsa tamkar
naki dangin. Ki tsare masa kanki sosai da sosai ki kiyaye masa
dukiyarsa ki boye masa sirrinsa, ki kasance mai tsafta da faranta masa
rai.
Don Allah Humaira ina rokonki da kada ki zama ballagaza, ki
mutun ta aurenki matuka da gaske ki kiyaye wajan magana da wanda
ba muharraminki ba. Ba wai ina nufin ki zama mai wulakanta jama'a
ba a'a akwai hanyoyin da musulunci ya yarda kayi magana da mutumin
daba muharramin ka ba wato musulunci ya yarda ka yi magana da
wanda ba muharraminka ba ta hanyar kasuwanci wato wanda siye ko
sayarwa ya shiga tsakaninka dashi.
Da kuma ta hanyar kare lafiya, wato ka duba ko a dubaka, walau
asibiti ko maganin gargajiya koyarwa, bawai sai na karatun Kur'ani ba
a'a harma na zamanin muddin za'a karu da shi, wato ya zamto kana
koyarwa ko ana koyar da kai sai kuma ta hanyar wa'azantarwa, wato
tambaya ga mai wa'azi ko kuma kai a tambayeka sai kuma taimako
wajen yaki wato ka taimaki wanda yaki ya galabaitar dashi ko kuma
40
LUBABАН
kai a taimakeka to muddin ba wannan mu'amalar bace ta hada ka da
mutum ba to duka sauran haramun ce.
Dan yanzu zamani ya riga ya juya, ko auren aka yi sai ana
taimakawa juna, to amma sai kiga wai yanzu har abota ake yi tsakanin
maza da mata, wai sai mace ta kalli wani katon balagaggen ta kirashi
abokinta, alhalin kuma ba muharraminta bane, waisu suna ganin ci
gaba ne. Dan Allah ni dai ki kiyaye ki tsare mutuncinki, dan hakika
kowa kika gani wayayye ne sai dai al'ada da fadar musulunci su danne
kuzarinsa.
Da naji haka ne na daga kai ahankali nace to Abba, ya kuma
maganar aiki, uhm Humaira kenan, kina son yin aikine "a'a Abba na
dai tambaya ne kawai" "To Humaira, hakika zamani ya zo mana da
cewa in har mace bata aiki ma ba wani abin cinyewa bane. To amma
kinsan kuwa da ra'ayinsa ni a nawa ra'ayin in har mace tana da rufin
asirinta, gara tayi zamanta a gidanta ta sami ladan aure in kuwa aikin
ya zame mata dole, to kuwa babu aikin da ya dace da ita face aikin
jinya ko koyarwa shi yasa ma na kawo miki misali da cewa, musulunci
ya amince yin magana da wanda ba-muharamin kaba, ta hanyar koyo
ko koyarwa. Haka kuma ko ta hanyar duba lafiya, wato a duba ka ko
kumı kai ka duba. Ba wai kuma ina nufin sauran ayyukar haramun ne
ba a'a hakan dai ya fi mutunci.
Dan haka koda nan gaba zaki fahimtar da wata,t o kiyi mata
bayani sosai kartace kin jahilceta ko kuma ma ke a jahilceki, me ye
jahilci kuwa? Shi jahilci yana tasiri ne akan duk abinda baka sani ba ki
tuna da cewa ke kadaice 'ya a gareni, tabbas in har kika tsare
mutuncinki, to nawa kika tsare, dan kowanne da kukan gidansu yake yi
yana yin ki da maganarki su zasu nuna tarbiyarki ki zama mai tsoron
Allah a duk in da kike.
Don Allah Humaira kada ki zama mai munafunci a garemu da
kuma Ubangijinmu wato kada ki nunawa duniya ke tagarice, amma
zuciyarki ba haka bace, abin nufi kada ki zama kyandir, kina haska
jama'a amma ke kina kona kanki. Dan kuwa kamun mai ilimi da
kamun jahili ko agurin Ubangiji akwai banbanci haka ko gurin aikata
6arna me ilimiz ai iya nuna iliminsa da sanin abu, amma ya yaudari jahili ya aikata aikin asha dashi. Shi jahili shi yake nuna ßatancinsa a
fili shi kuwa mai ilimi 6oyewa yake,a mma in ya tashi ya yafi abinda jahilin zai aikata baki ji ana cewa sumu-sumu wutar kai-kai ba wanda
turawa ke fadin (green snak on ther green grasess) ba.
41
WANDA YACE NAMIJI UBA2
Dan haka dan Allah ki tsabtace zuciyarki kamar yadda kike
nunawa duniya ke tsabtacecciya ce Imaninki shine babbar tsaftarki a
musulunci rashinsa kuwa zai iya jawo miki kyamata ga dukkan al'uma ko ba dade ko bajima.
Dan Allah ki tsare kanki daga kyashi, dan hakika mai kyashi baya taba ci gaba kuma kis ani ba kyashin mutum sai ya isa kamar
yadda ba a zagin mutum sai ya isa kada ki zama mai zagin jama'a wato
gulma abin da akasari yanzu yake damun al'umarmu kenan cin naman
junanmu. Duk in da aka zauna babu abin yi sai gulma. Allah-Allah ake
aga mai rufin asiri asirinsa ya tonu a sami abinyi dan ita kaddara babu
in da bata fadawa ke dai ki tsaftace kanki a cikin irin wadannan
al'ummar in har kika kiyaye da haka to kuwa zaki sami ribar zaman
duniya Allah ya kareki, daga sharrin makiya da mahassada.
Duk abin nan kaina a sunkuye yake, duk jikina yayi san yi yayi
murmushi yace, to wais ai yaushe zaki zo kiyi mana kwanaki?" nace
insha Allahu zan zo yace ko da ya ke ma in bikin ya gabato ai dole ki
dawo gida, ko kuwa a gida daya zaku zauna kusha shagalin bikin?"
yana magana yana murmushi yayin da na sunkuyarda kaina ina
murmushi sama-sama na ke jin wata murya mai kama biyu suna
gaisawa da Hajiya Rabi.
Da farko na dauka Nasir ne, sai daga bisani na fuskanci muryar
Yaya Auwalce, muna cikin tattaunawa da Abba, shima ya shigo gami
da sallama sannan ya durkusa ya gaida Aban ya kuma sami guri ya
zauna. Abba ya hadamu baki daya yayi mana fada sosai da sosai, fadan
zaman aure da zaman duniyar kanta sannan Abba ya zauna damu yana
ta hira, sai kace jikokinsa ba 'ya'yansa ba. Bamu ankara ba sai ji muka
yi sallamar Hajiya Rabi ta kauraye dakin Abba yace lafiya?"
"Dama gani na yi magariba tayi amma babu alamar za ku fito ku
yi sallah. Dajin haka gaba dayanmu muka tashi, ni na nufi dakin Hajiya
Rabi su kuma suka nufi masallaci, yin sallah".
Da muka idar da sallah naci abinci, na tafi dakin Hajiya Iya muna
hira nace ai tun dazu na zo akace kin fita makota, wallahi muna dakin
Abba muna hira. Nan na zauna muka taba hira da ita ina jin lokacin da
su Abba suka dawo daga masallaci, nasan abinci za su ci shi yasa ma
ban riga na je ba. Sai da na tababtar da sun gama cin abinci tukunna na
yiwa Hajiya Iya sallama na je muka yi sallama da Abba da Hajiya Rabi
mun bar gidan da misalin karfe takwas an dare 8:00pm
42
LUBABАН
Da muna cikin tafiya ne Yaya Auwal ya ringa yabawa da irin
halayyar Abba yace, wallahi Humaira Abba babu ruwansa sai kace ba
mahaifinmu ba, ji yadda ya zauna yana hira damu babu abin da ya
dameshi. Ba kamar yadda wasu iyayen suke yiwa 'ya'yansu ba kiga da
yana tsoron Ubansa kamar Mala'ikan daukan rai, to tun farko an tashi
babu shakuwa, kullum daga muzurai sai harara, sam ba sakin fuska,
wai kada danka ya rainaka, to ai kuma shi yaran ya taso ba son iyayen
ko? To tun farko baka jashi a jiki ba, ka nuna masa ya kaunace ka ba
alhalin ko Manzo S.A.W. yana wasa da nasa 'ya'yan tunda har
sumbatarsu yake yi ya juyo ya kalleni, yace wallahi muma in har Allah
ya bamu 'ya'ya Humaira haka zan ringa yiwa 'ya'yana murmushi na yi
ba tare da nace komai ba.
Da muka karasa gida ne Yaya Auwal ya bani ledojin da yayomin
siyayya don kare da kaya daga kayan ciye-ciye zuwa kayan shafe-shafe
wanda bani bama hatta Mama tayi godiya Khadija tace, ke dai yaya kin
more wallahi za ki yi auren gida babu ruwanki, da wulakanci, kuma ba
za ki ci karo da matsalar kannan miji ba. To kannan nasa mun zama
daya ke uwarmu daya shi kuma Ubanmu daya Allah in banda malamin
islamiyyarmu yace ba haramun bane da sai in ga kama rbaida ce ba nan
dai muka zauna muna ta hira.
Da gari ya waye aka maida Khadija makaranta, tun da aka shiga
saura sati biyu bikinmu aka shiga shirye-shirye. Daga ni har Yaya
Auwal din babu wani mai matsala komai yana tafiya dai-dai kuma
hakika iyayenmu sun nuna mana so da kauna matuka.
B
yau laraba aka tashi da shirin kama amarya,w ato ni kenan. A
Tana fadar haka ta daga kai ta kalli Yaya Fahad yayin da tayi
murmushit ace yanzu zaka fara fahimtata.
A ranar Laraba aka kamani, wato aka sani a lalle a ranar alhamis
aka yi min kunshi ranar juma'a aka yi wuni ranar asabar aka daura
Aure da safe misalin karfe goma na safen, da yamma muka shirya
kayatacciyar walima ta alfarma yayin da kuma a ranar aka kaini gidan
Yaya Auwal a matsayin matarshi ta din-din-din kamar yadda yasha
fada a wancan lokacin. 43
WANDA YACE NAMIJI UBA2
A lokacin da jama'a suka watse, aka barni daga ni sai halina, sai
nayi tunanin in tashi in zagaya gidan don in ga yaddə aka kawata mana
shi, dan na ji jama'a da dama suna ta kwada gidan da irin tsarin da aka
yi masa, duk da cew anayi kuka sosai da za'a kawoni gidan, amma jin
babu kowa daga ni sai halina ya sani na yaye mayafin na shiga
zazzagaya gida hakika gidan ya tsaru yanda ya kamata gashi part-part
ina cikin zazzagayawa ne naji alamun an shigo gidan cikin sauri na nufi
dakin da akamin masauki na zauna, gami da kunshe kaina cikin mayafi
Yaya Auwal ne da abokansa suka shigo.
Amarsu ta ango naji gaba daya abokan nasa suna ambata, tamkar
wadanda suka shirya fadar hakan lokaci daya suka shigo suka
zazzauna, amma shi gogan naka sai ya zo ya zauna a kusa dani. Addu'a
aka fara gabatarwa sannan nasihu da jawabai suka biyo baya.
An jima ana barkwanci a tsakaninmu danni bance dasu komai ba,
kawayena kuwa tuni suka yi tafiyarsu, saboda dare ya yi sosai. "Auwal
manya duk ka kagu mu fice mu baka guri ko? Wani daga cikin
abokansa ya fada su duka suka sa dariya suka tafa, hakan shi ya
haddasa min faduwar gaba zuwa can suka yi sallama dani suka ajjemin
akwati guda da kuma kudi a kanta, wani daga cikinsu ya zare kudin
yace "ya za'a bata kudin siyan baki bayan taki tace la mu komai,
magaji shima a cikinsu yake, yayi karaf yace, a'a taci kudinta ai ni ina
lura da ita tana ziro kafa tana ta6o angwanta, baku lura da shiba ne sai
zabure-zabure yake kunga ai ba maganar da ta wuce wannan.
A nan ne yaya Auwal ya kwashe da dariya yace lallai Magaji ka
iya sharri. Don Allah ku muyi sallama haka dare fa yi yake yi. Nan ma
dariyar suka saka gaba daya, magaji yace ina fatan kun yadda da
maganata. Nan dai aka yis allama yaje ya rakasu har kofar gida ya
dawo.
Abin mamaki sai na tsinci kaina da jin kunyar Yaya Auwal, duk
nabi na takure guri daya hakika tun da muke da Yaya Auwal ban taba
jin kunyarsa irin ta yauba ya ta so a hankali ya zauna daf dani gami da
rike min hannu yana murmushi yace, "To Humaira yaufa addu'ar ta
gama ci saura tawa ina fatan kin fahimta. Ta tafasa bance masa ba,
yace ahaya baki ce komai ba yanzun nan muka gamu da Alhaji Kabir,
yana ta yimin tsiya wai nayi kane-kane na hana Malamina baccin dare
yana tamin rokon Allah akan in aureki, dan in kasheshi, to burina ya
cika, wai in rikeki sosai in nayi lakwakwakwa har gara taci igiyar to fa
44
LUBABАН
bazai bada maganin da za'a fesa mata ba,s ai dai shi ya kwashe igya
ya hada ta da igigoyin gidansa ya, kulle.
A gaskiya mun jima muna hira dashi yana ta bani shawarwa gaskiya Humaira ki godewa Allah duk dangi kowa sai ya banki yake yi babu mai kusheki, to Allah ya bamu sa'ar zama ameen.
A hankali yasa hannu ya zare mayafin dake kaina, yace waike si
kace wata bakuwa, amma tsayawa yayi cak cike da matsanancin
mamaki, ba komai ne ya daure masa kai ba face ganin hawayen da yayi
sharkaf a fuskata, yace, "ya salam Humaira me ke faruwa kuma ya jawoni jikinsa, yana lallashina, kamar wata karamar yarinya yace, haba
Humaira bai kamata ace hawaye na fita daga cikin wannan idanuwan
ba a dai-dai wannan lokacin da muke kunshe da farin ciki marar
musaltuwa ko da yake ban riga nayi tambaya ba shin hawayen na farin
ciki ne ko na bakin ciki?
A hankali ya kwanta akan cinyata, yana murmushi yace uhm
gayamin mana rufe fuskata nayi na kauda kaina gefe guda yasa
hannunsa ya rirrike hannuna, yana dariya yace, "Humaira na lura da ke
ma kunyata kike ji yayin da ya shiga wasa da gashina bayan ya cire,
dan kwalin da ke kaina ya shiga magana a hankali yace, Humaira,
amma fa kin san ina onki matuka, kamar yadda nasan kema kina sona
sanin kanki ne bana kaunar in ga hankalinki a tashe, to dan me kike son
tada min hankali, ya tashi zaune, yayin da ya kwato kansa ta gefen
kafadata ya shiga yimin magana sama-sama. Humaira ina sonki, ya
kamata ki saki jiki in nuna miki irin son da nake miki a yanzu ki tashi
ki yi wanka ko ki ragewa kanki wannan kayan ki zo muci abinci. Ga
kazanan da madara na sayo mana ga kuma wani farfesu nan da Hajiya Rabi t abayar tace a kawo mana".
A nan ne na daga kaina cikin sauri nace Hajiya Rabi fa kace, kai
yanzu har hankalinka ya kwanta da abinda zata yi mana ka tuna da
kalamun mana, ana cikin tsaka da bikinfa ta nuna kyashinta da
hassadarta a fili. Ganin cewa duk abin da Abba zai min baya wani
nemanta sai dai ya aikawa Mama. Saboda lura da take-taken ta dayayi
harfa gulmar take yi tana cewa wai an ga biki amma bataga zaman
auren ba, ko da yake duk abinda ya faru ga bawa mukaddari ne, to amma fa ita kanta kaddarar addu'a tana sauyata akwai kuma abinda dan adam yake jawowa kansa yace, ai Allah ne ya dora masa kaga yanzu tunda furucinta ya dawo kunnanmu ko zamu ci a tsarge zamuci
to kaga duk abinda ya faru akanmu mu muka jawowa kanmu don haka
45
WANDA YACE NAMIJI UBA2
dan Allahı yaya karkaci. Danni ban yadda da ita ba kalli fa kalaman da
Kaninta Nasir yayi a kanmu. Tun da Allah ya fisu to muma fa sai mu
tashi ya ci gaba da karemu.
A nan ne ya ke ce dani kin san ni kuwa da har Allah-Alah nake
muzo muci. Ai shi kenan gobe in Allah ya kaimu an ba almajiri "a'a ba
za a yi haka ba na fada saboda kasan ba'a san abinda yake ciki ba ba
gara ka ba karen ka batun da namane yace to shikenan. Amma na riga
na rufe kofa sai dai da safe in Allah ya kaimu.
A nan ne ya shiga taimakamin wajen rabani da kayayyakin dake
jikina, sai da ya shiga ya kwancen zane nane sai nayis auri na rike
saboda kunya yace "a'a Humaira meye haka kuma ai gar aki cire kayan
ki saka rigar bacci ko najima sai kamshi kike bama sai kinyi wanka ba,
nine dai nake bukatar yin wanka saboda za fi duk nayi gumi. Daga nan
ya mike ya shiga bandaki cikakkiyar minti biyar ce ta ishe shi wanka
daga shi sai gajeren wando ya fito duk a lokacin ina takure guri guda.
A nan ne ya umarceni da in sakko muci abinci, kai tsaye nace
dashi na koshi "ai kuwa baki isaba dan kuwa dole kici abincin nan
murmushi yace in ba so kike ki galabaitar da muba, ki haddasa mana
haihuwar guzuma 'ya kwance uwa kwance. Wata matsananciyar kunya
ta kamani dan kuwa na fuskanci in da yasa gaba, gabi. na ya ringa
faduwa, to amma ire-iren nasihun da aka ringa yimin lokacin bikin su
suka ringa fado min a rai.
a
A hankali na sako na zauna daf da shi, amma fa duk da haka kaina
kasa yake. A hankali muke cin kazar, gami da sassanyan nonon
sahanu ahankali yana dan jana da wasa har cikina ya dauka yadda ya
kamata. Da kaina na ce dashi na koshi, yace yayi kyau sai da shima ya
gama ci sannan ya shiga hilatata da hira gami da 'yan wasanni jan
hankali wanda ya taimaka wajen gusar mani da hankali tun ina jin
kunyar har ta fara guduwa da kanta.
a A hankali ta dago kanta ta kalli Yaya Fahad tace amin afuwa
nan bazan iya zaiyane maka yadda muka raya wannan daren ba
murmushi yayi yace dalili. Tace duk da cewa na maka alkawarin bazan
6oye maka komai ba, to amma abu biyu ne za su sa in ki gaya maka.
Abu na farko shine ina mai matukar jin kunyarka kuma sannan
sirrin mune, bai kama ta dan bama tare ba, in kasance mai tona mana
sirrinmu, alhalin ako da yaushe Allah yana horarmu da mu kasance
masu boye sirrinmu musamman mu mata mu kasance masu boye sirrin
mu matuka. 46
LUBABАН
A hankali ya lumshe idonsa yana murmushi cikin jin dadi hakika
Allah ya hada shi da irin matar da ya ke so.
A washegari na tashi cikin mutuwar jiki da kasalar da take
barazanar haifar min da ciwan jikin daka iya hanani ko da dora ruwan
shayi ne. Dan haka shi da kansa ya shirya mana abinda zamu gabatar
wa da cikinmu kuma a wannan ranar wuni nayi ina baki kawaye da
'yan uwa.
A gaskiya kowa yana sha'awar yadda muke tafiyar da
soyayyarmu ni da yaya Auwal yi nayi bari na barin nan gami da
tsantsar biyayyar aure, rashin kiwa wajen gamsar dashi a shimfida kula
da dukkan wani motsinsa, tattali da tsantsar tsabta, walau ta tufafi ko ta
jiki kin rabuwa da kamshi ako da yaushe su suka taru suka taimaka min
har na ringa juya mijina son raina ta yadda nima duk motsin da nayi
yasan manufata, in na kawo dauki ne kan kiftawa da bisimilla ya kawo
masa daukin haka muka ciga ba da shimfida rayuwarmu muna masu
tattalin junanmu kamar kwai.
A zahiri muke nuna wa junanmu tsantsar kauna bawai a badini ba
mun shimfida so tsantsa a gidanmu, mun kuma shuka gonar soyayya
dan haka babu irin soyayyar da bamu nomaba. A hankali ta dago kai ta
alli Yaya Fahad, wanda ya kura mata ido, yana faman murmushi,
nakika labarin yana kawatar dashi.
A gaskiya muna san junanmu, ba kuma mu cuci junanmu wajan
nunawa juna kauna ba. Bana mantawa akwai wata rana muna zaune da
Yaya Auwal a falon gidanmu yayin da yake zaune a doguwar kujera, ni
kuma ina zaune daga kasa a gabanshi. Al'adatace matuka a duk lokacin
da muke tare, to fa ina nan ina masa tausa, ko ja masa kafa, domin in
inganta irin hirar da muke yi ya lumshe ido ahankali yace. Humaira a
gaskiya wutar sonki kullum sai kara ruruwa take a zuciyata. Hakika ina
sonki matuka wanda har na yankewa kaina alkawarin babu ni babu
karin aure.
Allah bai haramtamin kusantar wata matar ba, muddin in
matatace, to amma ni na haramtawa kaina. Humaira ko aure na Kara
bana tunanin zan iya kwatanta adalci a tsakaninku kinga kuwa ba ma
shi da amfanin in kara din ya jawoni jikinshi yana shafani, yayin da
muka shiga tsotsar minti, mun jima cikin wannan halin hakika, muna
nunawa juna so da kauna wanda a duk lokacin da na tuno irin gata da
shagwabanin da yaya Auwal yayi amma daga karshe ya min haka gaskiya hankalina yana matukar tashi.
47
WANDA YACE NAMIJI UBА2
Amma kamar yadda yawancin ma'aikata suka ware ranar Lahadi
saboda hutu na musamman ga junansu to fa mu da wuya ka zo a
wannan ranar ka same mu saboda mu mun ware wannan ranar rana ce
ta sada zumunci, sai mun gama zaga dangin da ya dace muna gaida su
daga karshe ya ajjeni a gidansu ko kuma gidanmu. To kuma a ranar sai
dare zamu dawo. Dan yawanci a duk inda muka sauka kusan tare muke
wuni. Ba ma ace gidan Abba muka sauka ai fa muna tare dashi a dakin
Hajiya Iya muna ta hira muna dariya. Dan kuwa tun bayan bikinmu
Hajiya Rabi ta rage yi mana fara'a. To kuma wannan ita ya shafa ciwan
ido kuwa ai sai hakuri. Dan kuwa ni da Yaya sai dai muce maki gani
ya kauda idan shi.
Amma fa hakan ya haddasa mana makiya da masu yi mana
kyashi. Ganin cewa a kallah mun shafe shekaru da dama amma babu
wanda ya taba jin kanmu dashi. sai da na shekara biyu sannan na sami
ciki koda yake ban cika biyun ba.
Akwai wani zuwa da muka yi gidan Abba a lokacin muna zaune a
dakin hajiya Iya ciki ne wata uku manne a marata, babu mai cewa ina
da ciki. Hajiya Iya ta kalleni tace ke dai har yanzu shiru to shegen fitina
irin tasu ko an sami cikin basu za su kafar da abinsu ba kullum-suna
manne da juna kasancewar ta tsufa ba kunyar bace ta isheta ba, Inna
biye mata kuwa to sai azo ana aika-aika dan haka sai na yi sauri nace
haba dai Hajiya Iya Allah ne dai bai bayar ba, tace tun da kika ce Allah
yar nan ai kin kare magana.
A lokacin da cikina ya shiga wata na shida sai na fahimci an fara
dagoni don haka sai na rage yawan fita kasancewar Khadija ta gama
makaranta to takan zo ta taimakamin da aiyuka a gidan shi kuwa Yaya
Auwal.shagwabata har ta fara isarshi, to amma babu yadda zai yi dani
dole yake biyemin.
An nuna kulawa ta musamman a akaina musamman da na shiga
wata na tara da lokacin haihuwa ta zo mace Allah ya bani. Na ga so da
kauna da kuma kulawa ta musamman dani da yata a gurin yaya
Auwal. Da ranar suna ta zo yarinyar ta karbi sunan Fatima sunan
mahaifiyarsa kenan da farko mutane sun yi surutu dan da yawa mutane
sun yi zatan Safiya za a sa mata wato sunan mahaifiyata, to amma abin
da mutane da dama basu fahimta ba shine kowane da da sunansa.
Hajiya lya bata sami damar zuwa ganin jaririya ba sai bayan suna da
kwana uku saboda yadda jikin nata yake'yawan matsa mata.
48
LUBABAН
A lokacin da tazo babu kowa a gidan daga ni sai Khadija
kasancewar ranar aikice yaya Auwal yana gurin aikinsa mun jima
muna gaisawa. Ta kalli jaririyar tace an kwayi mata aski?" Nace haba
dai asiki Khadija tace Hajiya ai yanzu an daina yayin aski. Haka kawai
mutum ya askewa dansa kai gashi ya tashi fitowa da sidin ludayi kuma
ma gashi baic ika tsawo ba da yawa.
A hankali ta saki dan tari tace ai 'yayan yanzu kun yadda sunnar
ma'aiki kuma kuna sane tun da fadar Ubangiji bata sauyawa wallahi
sam bashid akyau kuma kun sani ba ba ku sani ba kuma abanza da ku
aske da kada ku aske alkawarin Allah ne sai kan ya kade tas tun da
haka kawai kan zai yi ta kadewa gudun sudin ludayin da ake yi kuwa
sai ya sude tas shi yasa sam 'yayan yanzu basu da gashi irin na
mutanan da to sam ba'a biyayya da fadar Ubangiji. Ba ga shinan bama
nasara sun bata ku duk abin da yake da kyau sun hana ku ayanzu.
A hankali cikin dubara suke dulmiyar da ku suke gurbata muku tarbiyarku da dabi'unku. A yanzu fa turawa sun hanaku matse nonon
nan na farko wato wanda ake matsewa kafin a bawa mutum yasha
alhalin kuma shi yake haifarwa da yara taurin kai shi nonon da likitoci
suke ce da ku ya fi lafiya ajikin yara to babu abinda yake hnifarwa face
taurir kai sai kiga ya'yan yanzu shegen taurin kai karıar 'ya'yan
nasara.
Amma in an gaya muku bakwa yadda sai ku ringa cewa ai
abubuwan da ne to wallahi harkar da, da kuka watsar da ita ta ke
taimakawa wajen watsar da tarbiyar 'ya'yanku mu gashi nan har a
yanzu yaro duk girman sa muddin iyayansa na raye ba'a daukan kansu
manya komai sai sun tuntube mu, mu magabatansu ku kuwa fa yaro tun
yana karamis ai abinda ya ga damar yiz ai yi to meye amfanin hakant
abbas da kuna bin hanyoyin da muka bi muka raini namu 'ya'yan, da
kuma hanyar da muka bi dasu wajen tarbiyantar da su da ba haka ba.
A yanzu 'ya'yan yanzu