yi kurum da shi bayan ya yi kasa da idonshi,
har ta gama amayo da abinda ta kulle nashi, ta kuma
tabbatar masa wannan aurenshi ne ba hannunta a
ciki. Sai kawai addu'a da zata yi, Allah yasa alhairi.
Daga nan bata kuma cewa komai ba. Ya yi godiya
ya tashi ya tafi. A ranshi da alwashin ba gudu babu
ja da baya.
Ta waya ya lalubo Murjanshi ta gama murje shi
da kalaman soyayyarta da take kashe masa jiki, ya
ringa jin no going back, Murja ita ce hasken
zuciyarshi da ke jagoranta duk wanihaske a
rayuwarshi.
A lokacin ya gabatar mata da maganar turo
magabata, tunda Hajiya ta amince, ita zancen ya yi
mata dadi ta yi wani sanyi da ita, ya ce "Ya na ji kin
yi shiru tawan?" Ta ce, "Na gama mutuwa nawan, na
kusan zaman amanarka, zan koma karkashin Inuwar
soyayyar nan taka, ka ba ni abinda nake ta buri a
kanka. Waiyo zan mutu kan sonka." Ya kyalkyale
da dariya ya ce,"Naki wasa ne, don nasan düik kuri
ne ina miki kamu daya duk za ki rikice ki ce kin fasa
ku din da ragwancin tsiya." Ta ce, "kai? Ka san
166
Haske Maganin...2 Maiturare
girman sonka kuwa? Ai sha kuruminka Jarumta
zan dinga'ma mai yawa." Ya ce, "to Allah ya sa."
To ire-iren wadannan kalaman su ke kara tunzira
shi wurin kara son dole sai ya yi wani abu da
gaggawa.
An bashi dama a gidan nasu da ya gabatar da
komai, don haka da kwarinshi ya isko gidan
Hauwa ya kuma samu mijinta, kallonshi kawai
ya yi, ya ce, "Ga shí kuma ni uzuri garan, Bauchi
za mų je kila in yi sati, sai dai ka tuntufi Yaya
babba su ne 'yan zaman gari."
Zancen bai masa dadi ba, amma baya so ya
sawa zuciyarshi damuwa, tunda ya ji ya gami, ba
gudu ba ja da baya. Ya sa ya kada kanshi ya yi
gaba.
Da ya same shi.da maganar, shi bai dau dumi
ba, ya ce "ba komai zan tuntufi sauran da su ka
dace." Nan dadi ya kama shi, ya karkace ya zaro
dubu dari.
A ranar da dare aka kai, uban ya ji dadi ya yi
godiya, ya ce ba ya son wani kai-komo ya sanya
rana wata uku su je, su ci gaba da shiri kawai,
11 don haka sai su ka ji dadi, sun rabu ana yaba
halin dattakon juna.
To fa aka ja tungar fara shirin biki. Barista na
Hajiya bai gaji ba, ya iso da tambayar ya za ai
maganar hado lefe ne? Ta ce, "Ya ko za ai
167
Haske Maganin...2
Maiturare
Muttaka? Ba kaga yanda akai ba, ai ko da kanka
zaka iya hadowa sai kawai ka kawo 'yan kaiwar
anan ai ba za su gagara ba."
Wani irin takaici ya kara kama shi, uwa uwa
ce, ya kuma san haka, da take me dalili ne, sai ya
yi kasa da kansa bai ce komai ba, ya yi sallama
da ita ya tafi. To da so da tausayi irin na uwa, sai
itama ta ji bata kyautawa gwaggwale shin da
take, to amma tana yin hakan ne don ya gane
babban kuskuren da ya yi, kada ya kuma gigin
sakewa.
Lokaci na dada ja, Barista bai yi komai ba
dangane da shirya lefe. A wani yammaci suna
yawo da ita Murjan, sai ya kalli kafarta ya cе,
"mu ga 'yar kafar nan taki, size nawa ne ki ke
sawa, idan na tashi hado kayą kada mutum ya yi
kuskure." Ta ce, "Au, da ba ka ma fara hadawa
ba?" "Wallahi bari kawai, ina da hidimomi ai da
ki ka ganni in wata sabgar ta rike ni ke ba kya сe
ni ba ne, ina ta kokarin ganin gun da za ki zauna
ya daidaita ne." Ta ce, "umk, to in haka zai baka..
matsala man, ka ba da ba sài Mama ta hado ma,
tunda tana hadawa mutane?"
Ya ji wani sanyi a ranshi, ya ce, "Haba?" Ta
ce, "Ah walzhi kuwa, ba ka san sana'arta ba сe?"
"Na dai, kina fadin tana saida kaya shi ke
nah, na huta, dama abun ya tsaya min a rai. Sai
168
Haske Maganin...2 Maiturare
ki gaya mata idan ta yarda sai kawai na tura kudi
ta hado din."
"Me zai ko hana, ta yarda ita da ke kwangilar hadawa wasu? Bare kuma surukinta."
Ta kashe masa ido, ya sa hannu ya lakuce
mata hanci ya ce.
"Kin gan ki da wani kallonki sai kin sa na
bugawa wani mota ko?"
Ta kuma yin kasa da kwayar idonta da wani
murmushi akan fuskar ta, ita dai tana son
Barista, gani take ba wani namiji da ya kama
kafar shi a dukkan komai. Soyayya manya. А
dade ana yi sai gaskiya.
A wannan daren taima Mamarta Maryam
maganar ta ce, "Ya kawo man sai a hada masa."
Ta kanainayeta ta ce, "Mama don Alian ki bude
ido ki zabo min komai classical, irin lefen da
za'a dade ana kwatancensa Mama." Mama
Maryam'ta yi đariya ta ce, "Ah to, ba sai abunda
ya bayar ba? Ko ko zan tilasia ya yi abunda bai
niyya ba ne?" Ta ce, "Ni dai Mama dou Allah
zan ma gaiyato miki shi, ku yi maganar." Ta ce,
"to sai ya zo din."
A waya ta gaya masa gobe ya iso zai ga
Mama za su daidaita kan maganar lefe." ya ce, to
zai shigo da dare."
169
Haske Maganin.... Maiturare
Har falon Maman ya isa, wanda shigarshi ta
biyu kenan, tun farko zuwan s1 da ya shiga ya
gaisheta sai kuma yau. A shi ya yaba ma
tsarin falon komai ya mishi a can-acan.
Bayan gaisuwa, Murja da kanta ta gabatar
masa kayan maraba da bako, se Mama ta koreta
ta ba su guri za su yi zancensu o da itz ne za ai.
Ta tashi ta shige ciki tana dariy. Tana shegumin
tsakanin ita da Maman ko wa 1bun jin lunyar?
(zamani kenan).
Sun yi magana ta fahimta ta ce "To kamar na
nawa za'a hadan?" Ya ce, "to amma .i ba zan
iya cewa ba tunda ba sani nayi ba, dai hada
wanda ya dace sai ai min bill na kawo" Tа се,
"Ba haka za ai ba, bári kaga a f da sle
kaga ni, sai ka san a wane ajin za kai magana."
Ya ce, "haka ne." Ta sa aka rito da lefen da ta
hada set biyu, daya dubu dari biyar da sittin
daya kuma na miliyan ne da 'yan canji ba ko yari
kaya ne kawal tsura, ya gani akai masa bayanin
kommai ya ce, to zan aiko da nawa kudin Mama
sai ki badą account number dir tāki, sai kawai na
turo da kúdin." Ta.ce, "Ba laifi." Aka rubuta aka
ba shi, ya yi sallarna da ita ya taћ.
Sha biym washegarin ranar da su kai
magana, bankinta na first bank su ka yo mata
170.
Haske Maganin...2 Maiturare
alert na shaidar kudi sun shigo daga account kaza. Tasha mamaki, miliyan biyu ya turo mata.
Eho, daga uwar har 'yar tsalle su kai, suna
murna. Barista ya yi magana da babbar murya.
Nan da nan aka tashi tafiya, ta hada wasu 'yan
kudinta sai tafiya, aiki ya samu mata.
Gwargwado ta tsaya ta fito da 'yarta kaya ne
gasu nan har da na banza, itama sai da ta ci
jikinta, don so take tai komai na garari, bikin 'yar
fari? Ba dai gold a kayan amma kuma an zuba
fashion har da na banza, duk yawancin kayan da
zata saka da kalar fashion din. Haka nan ta iso
Kano a wata safiya ta Juma'a.
Lokacin da Murja taga kayan, wai duk nata
ne tamkar tai iskoki don murna.
Har falon aka kuma ķiranshi ya gani. Bai san
Value na kaya ba, amma kana ganin kalan kayan
kasan sun ci kudinsu, ya ce, "Sun yi Mama,
Allah ya saka da alhairi." Ta ce, "Yauwa amin,
an dai kara wasu kudin, kasan mata da tsatsuba."
Ya ce, "to kamar nawa kenan?" Tai dariyar nan
tata ta ce, "Ah ba komai, ai duka yiwa kaine, sai
dai lan sanys gold ba, in ka samu dama kana iya
zuwa da kanka sabon gari ko bakin asibiti ka
zabi wacca tai maka ka saya junda ana sawa, an
dai sa fashions ai ka gansu."
171
Haske Maganin...2 Maiturare
Ya ce, "Ba damuwa za ai insha Allahu." Yan
aikin gidan ne su''ka.jide masa kayan tas aka
dure su a boot din imotar shi. Bai tsaya ko'ina ba
sai gidan yayarshi Maimuna, ta ce, waiyo
Muttaka lefen nan ya yi min, Allah ya sanya
'ya'yanmu a wannan danshin." Ya dadа
Gararrajewa akan kujera dadin an yaba masa
kayan Sweet heart Ya ce, "To amin Yaya." Та
ce,"Kai amma ba zzan yarda da kanka ka hado ba
komai latestne fa, kuma na zaman yayin gari."
Bai tunanin komai ba, jin an sude da yabo,
ganin da yanda ake gwasale shi kan auren kawas
sai ca ya yi "Ai uwar Murjar ce la hado-min, a.
fitar da ta yi warman satin yau din nan ta dawo
kin san 'yar kasiwa ce." Ta dago kai da sauri,
"uwar Murjar kima ita ta shige gaba ta hado
lefe?" Kallon da ta yi masa sai da ya ji a jikinsa.
Sai yá rage zumuıdi ya -ce, "To ya za ai gani nayi
sana'arta ce, kuma ni na nema, dana tuntubi
Hajiya da maganar da ta ce kawai na hado da.
aina sai na kawo nan sai akai, to kin dai san ba co
an iya sanin komai na mata ba, kada naje na
wafsa da ta tuntubeta sai ta ce na kawo ba
comai ta shirya fita don hakan." Ta ce, "Umk ta
kyauta kuma nawa? Ganin yanda reaction dinta
ya yi, sai yasa ya rage kudin ya ce miliyan guda
na bada." Ta ce, "kai amma dai sn yi da yawa,
172
4
Haske Maganin.... Maiturare
3
d yake su sun san komai kai duk da hakan dai
su fi karfin wannan kudin." Ya ce, "Eh ai itarma
ta fada, da na tambaye ta ciko ca ta yi yiwa kai
ne." Haka ne ni 'yar ina ce ne? Zan ee turyanturyan, kwatance tsaf ta ce "kasan da yake ba а
je irin sa-ranar nan ta al'ada ba, duk ba a waye da
komai ba."
"Haka ne." Ta ce, "kada ka kuma gayawa
kowa ita ta hada kasan fahimta fuska ce, mu
kuma mata da daukar dumi komai akai sai an yi
tsegumi da wanda ya isa da wanda bai isa ba."
Ya ji dadi ya ce, na gode yaya, sai ki shirya
mu je gidan Hajiyan a zuwan ke ee ki ka hado
kayan." Ta ce "Ba komai, sai mu je din."
An kaima Hajiy& kaya ana ta daddaga mata,
ana ta mata bayani, ta ce "bassu haka Maimuna,
Allah ya sanya alhairi, yasa da mu za ai." Ta се,
"to amin Hajiya,"
Nan aka bar kaya sauran dangi nata zuwa
gani, Anti Hauwa tana kallo fadi take, "Ah lallai
Barista da gaske yake, yanzu ne yake cewa wani
abu." Wata Kakarsa tana gurin ta ce, "ke dai
Hauwa ko dai kishi ne?" Ta ce, "Da shi dinma
baba Uwani. Don ni ko hankici ban gani ba na
fadar kishiya bare inga akwatu, dole ko na yi
kishi." Ta ce, "yo na nawa kuma, kin dai 6oye
kawai dai fada ne ba kya yi." To haka ne baba
173
:
STOYNTIьМ ...impoM Stat
ρ 290 zmu 2η λαγο Ο q3! PIKsu qI K
sasi is a 22 BY Mahest ratin airs it frua
ist swix in stto of at vadmiss an eb THE B
- 55 Es in 30 Bi ny in on adati "a
a sd ster El riseed" so at teet acnatak setin
sb avaw a gd lub ed abs 3 1-82 1
Esasag nus ks Kags CC 9 DO. LHIKS
பா 97 sari srinist Es Bed st gli swo
iv as ice indo ismod is a mாய
p KOWS!
".ed sai ind shas ab sai By sigaw sh inugoes
uda il ise yay sbog nec ibsb ij sY
onsi sit or os (avuss neviish sbig at in
air le am at kons Ba ce IS KSANE
siear easbbEb a1 SUs EyA AYH stisi nA
anaisM silen vaasd".insved sism at a E
SO ET IS sub ennisdis syas By dalia
"svijsH nims ot"
Ewus Bien igasb πε2 s isd sis asν iellsi dA" ,axst ibat olist snas swosH taA .insg
inew swso syny sley lay sb stersal
isb s niug sast szisksK ssW ".uds
emnib ide " 33 &T "Son inaid isb ok swusH
an sd insg ad isilnsd oк in nod jaswu spa
iy an od slob aiswis sgri. ossd syirieit isbst
eyod isb nik smuk swan aa py" 55 aT "idz
sded on'sXed oT "iγ sγd 26 3α sbst isb iswn
13
Has:ke Maganin...2 Maiturare
dont care ne, babu ruwansu suna taya shi giggiwa. Shi dai Ibrahim sannu-sannu yake bin
al'amari, baya ko bashi sha'awa a ganinshi akwai
zalunci da son kai a gurin Barista, to oho dai.
An shiga satin biki, amarya dubu dari biyu da
hamsin ya sauke mata kudin nata shagalin, ban
da nasa reception da ya shirya a Samir Palace,
maza da mata kowa ya zo ya ci banza. A satin
aka tara Jama'a aka kai kaya, dangin anuarya baki
har kunne. A dangin ba wasu gaiya da aka debu,
jerin su Anti Hauwa da yayyansa, sai kanwar
babausa kawai su suka kai. An ko ciko su da
harkar arziki, fadi suke lallai Barista ya debo
babbar harka, dole ya ringa komai isa-isa.
Anti Hauwa ta dawo gida abunta, jikinta da
zuciyarta da mutukar sanyi, shi kenan namiji
kenan idan yana yi. da kai babu ya kai, yana
gama yayinka shi kenan kashi ma ya fika daraja,
ta Sakina ta kare, ta Murja ake yi.
Rayuwa kenan!
An daura aure lafiya lau ranar Lahadi a ranar
ne aka kare shagalin bikin za'a kawo amarya
gidan hasken ranta. To a ranar ne dole 'yan
uwansa da abokan arziki suka cika gidan Hajiya
wunin biki ya tashi, amma da hannunta bata
175
Haske Maganin... Maiturare
baiwa kowa cinga ba. Kuma nan nc za'a fara
kawo amarya kafin a kaita gidan mijínta.
An iso da amarya sha biyu saura yawancin
dangin ango sun wuce sai na kusan da dole dama
kwana za su yi, aka kaiwa Hajiya ita aka danka
amanarta a gurinta. Taima Annabi Salati, ta ce,
"To an gode muku su kuma Allah ya basu zama
lafiya." Abinda tai ta maimaitawa 'kenan.
Nan aka gama haska Video din da akai
comeboy da shi, a tare da wakar da aka shirya
musu ta aure tna tashi kadan-kadan, don ma da
hayaniya gidan ıxmkar ya tsage.
Nan dai aka tattarata sat gidan miji fagen
fama. Nima sai na bisu da addu'ar fatan alhairi
(to ko ya ya).
To a ranar Asabar din da kai dinner din
Barista, Uinmi Yusuf, kawar kanwar Sakina ta
zo gidansu Sakinan gun Bilkisu, dauke da irin
Jakar nan da ake rabawa gen biki wacca akan
manna hoton ango da amarya. Jakar ta dauku
wadanda su kai aikin Computer sun dauke su da
kyau, shi yasa hoton yakc plashing idon duk
wanda ya gani, sai an tanka, couples din sun yi
kyau a hoton, duk da hadawa a kai, amma dai
sun yi bala'in kyau.
Wa iu ke zato? Barista ne da amaryarshi
Murjanatu. Lokacin da take yin sallama, Sakina
176
Haske Maganin...a Maiturare
ta na gama alwala ita ce a tsakar gida ita ke amsa
mata, lokaci daya Jakar tai plashing dinta, ba
wai don ta gane ko waye ba, da ta yi masa kallo
na biyu sai gabanta ya yi watz irin faduwa,
Barjsta Muttaka hooks Murjanatu Sidi? Eye!.
Ji ta yi duniya na juya mata tamkar tana yawo
kan gajimarc, da hanzari da bata san ta yi ba ta
isa gun Ummi Yusuf, ta karbi Jakar tana kara
gani sosai. Ummi Yusuf ba tare da ta san komai
ake ciki ba. Та cс, "Oh ni 'ya su, wanzan Jaka
tunda na amsheta kowa ya dora idonshi anta sai
ya tanka, ni har Jakar to fara ban haushi, shi yasá
wasu suka ce basa ra'ayi don tallan kai ne, waní
namijin yana gani sukuf za ka sbige masa rai ina
dadin wannan sabgar."Bayani take gaba daya ita
hankaliuta ya dauku kan karema Murja kallo ta
gano abin da take da chi da ya ja ra'ayin Barista
har ya yi nata korar kare irin haka ba laifin tsaye
ba na zmne. Lallai da gaske namiji ba abin yarda
ba ne, avun da kawai za kai kokarin rayuwa d.
shi da zuciyar zaman zaman tare amma ba vai
sadaukar da kai da soyayya ba.
Da gasken dai mace ce ta dauke masa hankali
daga kanta. Don haka ba wai fahimtar Ummi
take, ba, bare ta gane batunta. Ta saki ajiyar
zuciya, Ummi tana.. murmushi, "Anti ke meye
naki ra'ayin don naga kowa ya gani sai ya tanka."
177.
Haske Maganin...2 Maiturare
Wani busasshen murmushi ta yi da ya tsaya
iyakar lab6anta, ta tsare ta da ido ta ce, "ke ina ki
ka san su?" Ta yi murmushi, "Kawata ce Anti
Sakina, taré mu ke B.U.K da ita, son gayen nan
take kamar ta mutu, shima ba laifi yana taya.
mata so, don waní lokutan yakan zo tafiya da ita
daga school, idan muna iare yakan dan gan mu.
da 'yan canji, wai ma sha lemu, yana da alheri
sosai, ya kuma aje masu kyau. Dama. Murja 'yan
karya na sani ba zata auri miji mai sauki ba, mai
zafi zata kawo.
Ya yi kuma babbar harka, don bikin nan ba
laifi kudi sun ce wani abu." Ta gyada kai, nuna
gamsuwa, a daidai lokacin Bilkisun ta shigo
itama ta zuro kai tana kallon abinda ake sharhi a
kai.
Itama gabanta ne ya fadi, ta yi saurin hada
ido da Sakina, sai ita ta yi saurin dauke kai, ta
saki Jakar ta yi saurin tada sallah, don ma kar a
ci gaba da kirar.
Bilkisu ta saki Jakar a sanyaye ta kalli Ummi.
Тa сe, "Mеe ye ki ka kalle ni da ido? Ke ba tai
miki ba ne?" Ta tabe baki, "Ummi mijin Anti
Sakina ne fa." Ummi ta bi tsayin garun dakin da
sulu ta zauna dabasa Kasa. Ta ce, "Don Manzon
Allah? Kai, gaskiya na kwafsa wai! Don Allah
ku yi hakuri, ban sani ba. " Ta ce, "To me ki ka
178
{
SADINSION
RI Sudiy as into ses is amaa seel st
s sai by stil is sise un Sdential
Bresi ue trolled gass sex menis agat Logidz
ovewed snез
Wegi san sainst us at unded azet
ued yod ne and ida awirt sisd s ide is Ad
s trast in unitany sy lawad in dedud ab ijay ay
skap nsuek naY inasgdaz iriswcil in sysiug
.swumsh stsw sb
30 dest st
oyswad ede aT "Cawok ikyits siad sloga"
susi inwel IN I BWEysaT "ismokB cc
25 18 sinids mad sol
ise sd is sid a l sg b
sisa so st SISIN EVER Slst 30 mA
ide aboda"00 1oz owio sb nud s is ilakned
ss dub nswnduds nnnna s ise" Yol um at isa is
veb sbug sh i si sli sb udst i stniki id лг
"uvid salub site in is sbs
A"shusy sy deliA am"ce si ccsp s stusK
sewed or mand musaSY MEISY N HOST
200 KID 221 e0 quiris 25 20KS DE SEL
is side STIS 'ES basy sish a mus
τS
SEWIDE shiswaven iss ism iubut igat
Ishad esami sb staintsdas sving67 sti
ebud as obi sisli of sws'sdz oyek n sgn
180
Haske Maganin...2 Maiturare
da fadan da Amma ta yi, kasa motsi ta yi, bare ta
tallashe su, sai Umma ce ta ji kukan ya isa ta
shigo. Taga Sakinan zaune tana kallon su itama
tana hawayс.
Tasa hannu ta dau Mashkura tana jijjigawa,
har tai shiru ta bata ruwa, shi kuma dan boy har
ya gaji da kukan sai kawai ya yi shiru ya tashi a
guje ya yi ficewarshi sabgarshi. Yaro kenan baya
da wata damuwa.
Umma ta manna mata Mashkurah ta ce,
"ungota bata, lafiyarki kuwa?" Ta share hawaye
ta ce, "Ba komai." Tsayawa ta yi kawai tana
kallonta, har ta fara bata abincinta. Sai ta fice
daga dakin tunda bata ce mata komai ba. Sai
Amma ce take gaya mata tana fada. Ta ce, sai a
hankali ai a buri da ciwò sosai ta ce, "Saboda shi
ai sai ta mutu ko? "Sai a sannu abubuwan duk za
su bi jikinta, ki rabu da ita ta ji da guda daya,
kada ki yi mata duka biyu."
Ranta a 6ace ta ce, "umk, Allah ya kyauta." A
ranta tana tunanin yaran yanzun basa ko kawaici
tamkar su ne suka san darajar so. Sai aikin son
amma ba dabarar yanda za'a sarrafa shi, a ci
moriyarsa.
Ta yi kudiri mai zafi, rayuwarta sabuwa za ta yi facing ba ragaiya tsakaninta da maza kamar
yanda su ke 'yan sha'awa to itama ido zatą bude
180
1
Hasloo Marganinna Maturare
ta bi layin nata 'yan kwadayi kawai a ci kudi,
soyayyn K oho,
A satlyar washe gri, ta karkade takardun
Makarantas a, da. niyyar neıhan matallafin
rayuwa. Ko ta rage radadin zuciya. Da farko
muji taiwa magana ya ce, ba komai ta yo
photostart zai kai mata Nepa yana da hanya. Ta
ce ita dai ta li sha'awar teaching, don ya fi
saukin ai'amari ga sabgar mata Ya ce, "ke dai
kawai ki yi ta addu'an dacewa, wanda ki ke
tunani ba lallai ne ya zama shi ne mafi alhairi
gare ki ba."f
Ta ce, "haka ne, Allah dai ya ba mu sa'a,
Amin." Da kanta ta iyo photostart din takardun,
ta kuma je Teachers board ta sayo form ta yi
applying aka gaya mata ana ko gab da daukar
Ma'aikata a cikin board din, don haka tai addu'a.
Wannan ya sanyaya mata rai, Yaya Muji yana
tunanin suna da kafa bangaren Nefar nan, shi ne
ya fi saka buri akai. Da kanshi ya kai takardun an
kuma ba shi tabbacin insha Allah kwana kusa za
su yi replacement, don akwai da yawan Jama'a
da suka bar aiki a lokacin.
Don haka sai ta dawo ta dukufa da addo'a,
wannan ya sanyaya mata zuciya, tana da buri a
geba mai yawa, wanhan ne ya sata fara dan
ziyarar Jama'arta.
181
Haske Maganin...2 Makurare
Ranar talata, ta sa aka fito da motarta daga
gareji akai mata service aka bata abinci, aka dai
tabbatar da lafiyarta, har Muji ma ya hau ya dana
sannan ya dawo mata da makullan.
Ta shirya tsaf, da'yan yaran a sun dan gyara,
sun yi kyau. Ta ratayo Mashkura a kafada za su
fita.
Tana sallama da su Amma ta ce, yau zan je na
gaida Hajiyan su Musadik, Amma ta tabe bakil
ta ce, Za dai ki je jin gulmar auran da ubansu ya
yi ne kawai." Ta yi wani irin sak da ita, ta kasa
cewa komai, don har ga Allah i ta ba wannan се
manufarta ba, don ma zatan.
Sai ta ce, "kai Amma, ni wallahi ba wannan
ne a gabana ba, duk tunanina ita din yanzun ta
zama wani bangare na rayuwata da dole mu
kasance cikin tuntubar juna da zumunci idan na
duba kyakkyawar alakar da ke tsakaninmu,
amma tunda kin ce haka na hakura na fasa."
Umma ta ce, "kinga yi tafiyarki inda ki kai
niyya, in ma gulmar ki ka je ji ai ba ki yi laifi ba,
don gulınar taki ce kuma mai dalili ce, yi
tafiyarki, kada shaidan ya rinjaye ki, ki fasa abin
da ki ka yi nufi na alherin." Amma ta yi dariyad
ta ce, "Allah to ya baku hakuri, da naga kina
rawar kan a fito miki da mota, shi ba za ki maida
182
8
Haske Maganin...2 Maiturare
masa abarsa ba, tunda kin je kin kwakwale naki
kayan?"
Gaba dnya sia ta cire mayafin jikinta, ta
kwantar da Mashkurah ta ce, Amma yi hakurí na
fasa zuwan wallahi, amma maganar mota, tawa
ce ba aro ya ba ni ba, kyauta ce, tunda ko haka
ne ba zan taba maida masa ita ba ko da ita ce
karshen motar da zai hau a rayuwa. Musulunci
ma ai bai ce ka mai da ihsanin da miji ya yı
maka ba a halin zaman jin dadi ba. In na maida
ma zan iya maida sadakina kenan."
Sabida kuluwa da ta yi fitar da ba ta yi ba
kenan a ranar.
Ta yi ta kunai, amma ko ko kallo ba ta isheta
ba, sabgoginta kawai ta shiga.
Washe gari da ta huce, gidan Yayarta Zainab
ta wuni, sukai hirarsu ta zumunci mai dadi. A
nan suma suka rakashe da 'yan gulmammaki don
itarna ta jiyo labarin maganar auran.
Ta ce, "ni na taba zuwa gidan matar wata
rana sarin kaya da ta kawo wasu Pakistan, na bi
Rukaiya Ado da yake itama 'yar kurda-kurda се,
ita ta kai ni, kai Barista dai to. Allah dai shi
kadai ya san karatun bebe, amma ya zura jiki da
yawa. Idon iyayen matar na bude su ke, duk da
dai ba zan ce ga wata illa ta su ba, amma
kwankwarru ne.
183
Haske Maganin...2 Maiturare
Irin wadanan yaran kusan su 'ya'yan da ba a
sa su, ba a hana su, sai abin da su ke so, shi
Iyaye ke so. Da wuya ya dede matsala ace ya
kaita gidansu ai mata duban tsaf, her a yanke
hukunci mai ma'ana." Sakina ta ce, "ohon masa
shi ta shafa, ni ai nai masa nisan da ba zai iya
kamo ni ba abadan."
Yaya Zainab ta ce, 6acin rai dai inda ki ka
mato akan son Baristan nan, yana gama dawowa
hayyacinsa, yana ta50 ki amincewa za kiyi." Тa
yi kwafa "Anti, na sani yawancin al'amuran
duniya Ubangiji shi yasan makararsu da
mafararsu, amma a inda na cire rai daga Barista,
cirewa ta har abada nake nufi, wallahi yaran da
nake kulafucin rayuwa da su, Allah na dangana.
Su ne zaman gidan Barista ya zamewa dole, ni
da na samu 'yanci? Ba zan waiwaya baya ba,
Allah ya raya su da albarka mai yawa, wuya bata
kisa, sai idan har kwana ya Kare. Ni a yanzun ba
na ko dar da ya zo ya karbi kayansa. Nima zan fi
sakewa na yi zawarci mai dalili."
Yaya Zainab ta dai yi murmushi ne kawai
don ta san dokin zuciya ta hau. Rayuwa kenan,
kowane mutum da salon'yanda ake jarraba shi a
rayuwa.
184
a
Haske Magunin...2 Maiturare
Sai da Magariba sannan ta wuce gida, wannan fitar da ta yi ta sha iska, ta rage mata radadin da zuciyarta ta kwana yi a jiya. Ta dukufa da addu'ar samun nasarar dagewar aiki, ba'a dade ba, kuwa aka kira su Interview a
Teachers board. Bata da kowa sai Allah sai abinda ta karanta don haka da wannan ta yi kyakkyawan dogaro.
Ba laifi. da nasara ta samu damar amsa
yawancin tambayoyin da akai mata, har tana ganin ta gama samun aiki ta gama. To sai dai
halin Najeriya a yawancin lokuta ba wai
cancantar ake dubawa ba, an fi duba doguwar
kafar da ka ke da ita, wannan ya sanya
tabarbarewar yawancin al'amura a Najeriya,