gaya mata
yanda su ka yi, da kurmavia ta ke zaton hakan
bata samu ba. Ammata ce, "lah ya kyauta, Amin."
Ta dawo cikin daki, Musaddik ya tashi ta dauko shi,
tana fitowa da shi Amira Ranwarta ta karôe shi ita ta
shirya shi ta ba shi abinci, tana zaune tana kallonsu.
Da ya ke Asabar cc, gidan Alale su ka yi da kunu,
dama haka al'adar gidan take, ranar Asabar alala da
kunu ko koko, Lahadi kosai da kunu.
Ta jawo kwanon kunun, Kamshin kosan ya ratsa
kafofin hancinta, lokaci daya hankalinta ya daga
zuciyarta, abunka ga mai larura, ta faki idon Amma
ta matsar da su gefe, a hankali ta zame jiki ta ja filo
115
Haske Maganin...2 Makurare
sai ta kwanta. Ta rantee ido cikinta na ci gaba da
harbawa yunwa na damunta. A halin da ake ciki,
dankalin Hausa kawai ta ke kwadayin ci da yají,
atuna wa zain dagawa hankali ne da wwar tafйiyа
tunda ba shi a gidan? Dole ta rungumi kaddara,
cikintaya ci gaba da kartawą.
Idan becin sabani da kuna mutuwar auren naa,
da yanzun tana can tana shagwabarta, tana furta abin
da ta ke so da gaggawa ne za'a aemo a bata. Amma
yanzu ga shi ya yi mata cuta kashi biyu, bai bar
zuciyarta ta huta ta zauna lafiya ba, haka hea
Gangaren lafiyar ma ba tà samu ta huta ba, ina ranar
mata masu farin cikin.mutuwar.aure ne? Me ne su ke
tsinta a ciki? Zaman gidan miji shi ne cikakkiyr
sutturar mace, gani take da ita hamiji ce za ta yi
kokarin hakurin zama da 'ya'ya mmata, don rayuwa
kawai cikinsu ni'ima'te babba, kallon st ya sanys
farin ciki, taraiyarka da su ya sanyaya zuciya, su
kuma yi ma namiji tukuiçi da sanyin idaniya.
Tana wannan zancen zucin; Amma ta shigo ta cе,
"Wai har kin yi me ke nan?" Ta yatsuna fuska, "Ban
jin ci ne Amma, kila zuwa anjima." 'Ta mata wani
irin kallo cude da tausayi irin na uwa ta ce, "ko shayi
ki ka fi so ne, akwai ruwan zafi ai a flask."Ta
girgiza kai alamar "a'a." Ta ec, uh, ina fata ba sa
mutuwar auren za ki yi a ranki ba, in kö haka ki ke
niyya gara ki sauke, don dai in namiji ne kya muta
banza kan shi, kila randa ki ka mutu za a haifa mishi
sabuwar matarsa, kuma wannan ba zai hana shi
116
Haske Maganin...z Maiturare
amshe ta ya aure da dadin rai ba, gara ki yi wa kanki
fada ki mike ki fuskanci kalubalenki na rayuwa a
gaba, wa ma ya sani ko wata ce ta dauke mishi
hankali ya ga kin oika mishi filin wuri ya koro ki?"
Ta daga ido da sauri ta kalli Amma da wani yanayin
na mamaki. Ta yatsuna fuska ta ce, "in kina farkawa
gara ki farka." Kawai sai ta sa kai ta wuce abinta. Ta
bi inda ta yi da ido, zuciyarta da wani irin takaici
mai yawan gaske, ba ta taba jin ta tsani namiji
mummunan tsana ba, irin na yau, tsanar da take jin
har abada ba zata kankare daga zuciyarta ba, ta kuma
yi aji ta aje maza, daga yau ba sauran tausayi, ko
wani daga kafa. Rayuwar da zata gina a gaba, za ta
yi kokari ta zame mata jari ne, duk namijin da ya
fado, kokari za ta yi kawai ta wanke shi tas, te yi
masa wankin babban bargo, batun so kuma ta aje shi
gefe, ta gama yayinsa, tunda dai ta sani ba za'a barta
ta rayu haka kewai ba, amma ben cin haka da lawai
to ut zama i yan mazan jiyan nan, masu himmar
bautawa kasa kawenta bainawa Ubangiji, 'ya'yanta,
iyayenta da kuni Kasarta. To hakan ho mwuwe
ba ce..
Yau satinta biye a cikin dangınta kowa ya sani
auranta, ya mutu, masu takaici na yi, ma su gara da
akai haka ma ba za'a rasa ba. Daga dangin Barista ba
su ga ko sauro ba, a ranta tana mamaki don ganin
alakar ta mai kyau da danginsa.
Sai dai ba ta fiye zafafawa ba, tunda shi da ya aje
ta baya so, kowa ma ai dazun ne. Sai lokacin ta tuna
117
1
Haske Maganin...2 Maiturare
da wayoyinta tunda ta zo ta cire batiran ta watsa
akwati, duniyar ta yi mata zafi, to wa za ta nema
kuma?
Ta fiddo su, ta kuma sa aka cazo su, duk ta kunkunna.
Juma'a da yamma, Maryam a gaban Hajiya ta zo
mata wuni, suna hirar su ta yawan rai, Hajiya ta'kara
kashingida taice, "ni ko kin jiyo in su Sakina
kuwa? Kwana biyu bata Gullo ba, bata kuma kira a
waya ba mun gaisa, kuma nima na dan bubbuga sai
ban samu ba, shima Muttakan na kwana biyu ban ji
shi ba, duk da dai na san shima ya yi tafiya ne."
Maryam ta yi murmushi, alakar Hajiya da Sakina
mai kyau ce, har tana tunanin itama da Allah ya sa
uwar mijinta ta yi yawan rai, zata yi kokari su samu
fahimtar juna irin "haka, amma dai alakarta da
abokiyar zamianta mai kyau ce.
Та сe, "Hajiya an dan kwana biyu mun je
unguwa da Alhaji, sai na ce mu biya, ba mu same su
ba, kuma nima na nanneme ta a wayar ban san ime ya
samu ba, sai a ce a kashe ta ke, amna bari mu kira
Yaya mu ji, lafiya ai ita ke buya ko?" Ta buga ba
sa'a aka ce is not available at the moiment, try again
later. Ta yi tiki, kamar wasa, sai ta doka ta Sakina,
zuciyarta ta wani buga ta yi sanyi da ta fara ringing
bata sani ba, tana son Sakina, inda take jinta tamkar
ma ita ce 'yar uwar tata ba Muttaka ba.
118
Haske Maganin...z Maiturare
Sakina na ganin wacca ta ke kira, zuciyarta ta
ringa kidawa da sauri-da-sauri, tana ta kallonta har
kamar ba zata dauka ba, sanpan ta yi picking. Cikin
sanyin murya, ita kuma ta kana mita.
"Yo wayar ma sai an ma mutum yangar dauka,
ban da kukkulleta da ake yi, ko duk sarautar ce?"
Murmushi ta yi, amsa sai "Uhm" Kawai da ta cе.
Sun gaisa ta ke mata mitar ta dade bata ji ta ba, haka
kuma ta je gidanta ba ta same ta ba, wacce duniyar ta
shiga? Ta yi gatsine kamar tana ganinta saboda wani
takaici da ya taso mata, ta ce "Ina gida ai ko?" Mе
ake a gidan ko kawai ziyara?" Ta yi gajeran tsaki,
"Maryam kina nufin ba ki san ina gida ba all this
time? Ta ce "What? Wane irin gida kuma?" Shiru ta
yi ta má rasa me za ta ce mata, sai ita Maryam din ta
latse wayar. Ta kalli Hajiya, bari na je gidan Yaya
Muttaka, idan ba ta rike ni ba zan dawo, in kuma na
yi dare gida kawai zan wuce zan dai zo kila gobe."
Hajiyan ta kalle ta a tsanake, "Sakinan dai lafiya dai
su ke ko?" Ta saki fara'a. "Kalau din su, sai dai kin
san mai larura irin tata sai dai maleji ko?" Та се,.
"haka ne, Allah ya raba su lafiya lau, bari na dan
duba musu wani abu, kya wuce musu da shi." Ta ce,
"To." Kamin Hajiya ta gama hade-hadenta, Maryam
ta gama kaguwa da ta bar gidan, hankalinta ya tafi
sosai, zuciyarta bugawa take yi da sauri da sauri.
Tana kokarin 6oyewa ne wa Hajiya wanda ta sani
dole gaba zata san ko menene.
19
Haske Maganin...2 Maiturare
Ta daidaits a cikin motar ca ta zo da ita ta
kishiyarta Carina 3, da gudu ta sa signal ba tai brach
a ko ina ba, sai goran dutse gidan su Sakina, ta yj
sallama dumuryar nutsuwarta, ta samu su Amma da
Ummi cuns tsakar gida suna shan iskar yamma tare
da yaranstu kasancewar ranar ba Makaranta, duk
suna gabansu. Ta tsuguna tana gaida su, sai
Musaddif tamkear ya sarita ya tako calau-calau ya zo
ya fada mata jiki yana dariya, ta yi masа
kyakkyawar runguma tana dariya. Su Amma ma su
kai dariya, Umma ta ce, "Ji be shi zai bata miki jiki
tamkar ya san ke tashi ce." Ta yi murmushi, tana
shafa masa kai. Aka dan nutsu. Ta kalle su kadan,
"Tana diki ne?" Amina ta ce, "Eh shiga tana çiki."
Ta mike dauke da Musaddik ta shiga falon, bata
nan, ta kutsa kai uwardakansu, tana kwance kawai,
tana karanta Jaridar Sandsy Trust, ta yi nisa wurin
karanta labarin ZzinabMaina mace yar
gwagwarmayar kwato hakkin mata, da wayar da
kansu. Suka kalii juna a tare, ta mike daga
kwancenta tama koka linke Jaridar. Maryam ta
tsaya tana kallonta, ta ce "ba ki jiu zafin garin nan,
irin baka ki ka kule cikin daki duk ga Jama'ar gidan
waje?" ta ce, "To ya za ai na riga na karbi rayuwar
yanda ta samu, nauyin zama nake yi waje cikinsu
kowa yż yi sallama idonshi cikin nawa, na ma riga
na saba zama ciki, ko falo su ke suna hayaniyarst
bana zuwa, Amma ma tai mita ta gaji."
120
ci
3
CIT
0B
Haske Maganin...2 Maiturare
Maryam da sanyin jiki ta karaso ta zauna gefenta, tana kokarin kara rungume Musaddik shi
kuma yana zamewa zai gudu ta dire shi ta rike
bannayen Sukina, ta ce, "Ke wai what do you want
tell me ne? (me ki ke son gaya min?) zaman meye ne
ki ke a gidan?" Ta yi murmushin takaici a takaice, ta
.cc, "Maryam kenan, kina son ce min wai ba ki san
Barista ya gaji da ni ba ya sake ni?" Ta bude baki
cikin tsananin kaduwa "Saki Sakina? Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un." Sai ta kifa kanta kan cinyar
Sakina kawai sai kuka, ita sai zuciyar tata ta karye. ДН cted Suka rungimi juna sai kuka, a haka Amma ta same
su. Ta kalle su ta ce, "lafiya kuma?" Maryam cikin
kuka ta ce, "Don Allah Amma ku yi hakuri, wallahi
dukanmu ba mu san abin da ya faru da Anti Sakina
ba, sai yanzun da mu kai waya ta ke gaya min tana
gida, saboda dukkan wayoyinta mun nema babu, na
N
dai je gidan sau daya ban same ta ba, na za ci dai
unguwa ne ta je ashe tana gida ne, ashe wannan
mumreunan a ne ya fu. Kai Yaya bai kyauta ba,
bai kuma kyauiawa kansa ba don ya yi wa kansa
babbar asare, Allah ya saka miki.
Ta dade tana juyayi da takaicin kai namiji dai
mace ba bakia konai take a gurinsa ba, idan har ya
so ci mata mutunci, ko ita wacece, komi girmanta
komai yarinta, komi heduwarta, rufe ido kawai yake
ya ci mutunci, bai duba shakuwar zaman tare ko da
soyayyar ta gushe." Amma ta ce, "To sai hakuri
zaman ne kila ya kare." Ta ce,"Amma, amma mu ma
121
Haske Mujann 2
Maiturare
kun mana laif yn kamata ace vun tmtube mu da
maganar nan, bare da ka ka j: mu shiru, wallahi ba
mu san korai a kai ba, yanzun 1na ina zaune ne gaban
Hajiya ta ke tambayata su na ce mata ban ji komaí
ba daga gare su ba, saboda ban samu dama ba.
Yanda mu ke da Sakina ta zama tamu ba, ba
zama ba ne na munafunci ai ko mu ba mu zo ba, na
sani Hajiya dole zata zo; tsohuwar ta damu da
Sakina sosai, tamkar ita ce ta haife ta ba wai Yaya ta
haifa ba, sabida itama bata aje ta kusa ba, matsayin
uwa ne sosai ta bata. Ina juyaya yanda zata ji
maganar nan marar dadı."
Amma ta ce, "haka ne, mun sani bisa al'ada zai yi
wuya saki ya auku a ce wurin sati uku, namiji ya
kasa gayawa iyayensa, musamman shi da yake da
jarumar uwa irin Hajiya, dole mu yi kurum tunda dai
mu aka batawa maganar gaskiya; kuma dai da gaske
mun yi mamakin rashin ganin kowan daga wurinku,
har tsayin wannan lokacin musamman da yake ita
din ga halin da také ciki. Babanta ma shi ya hana
tuni aje a kwashe kayan, ya ce sai ta haihu tukun."
Maryam ta ringa girgiza kai. Ta mike a hanzarce, ta
rusuna ta ce, "to Amma an bata muku ku yi hakuri
da gaske." Ta juya ta kaili Sakina, ta dauke kai ta
dafata, "Kiyi hakuri don Allah na tafi."
Bata jira komai za su ce ta juya da hanzari ta
wuce gida. Aniyarta ta wuce gidan Hajiya kawai ta
gaya mat abunda ya ke faruwa, to amma sai
zuciyarta kwabela da ta daga kafa har zuwa gobe
122
y
V
Haske Mag.onin...2 Maiturare
da safe, don ta san Hajiya ba da wasa ba, mace ce
jaruma, amma wani lokacin tana da sa abu cikin
ranta. Ga dare wannan na iya hanata barci, ga jikin
girma komai na iya faruwa. Haka nan ta kada kai
cikin takaici ta isa gida!
Mijinta shi ne ta gayawa abun da ya faru ta rasa
da wa zata tauna maganar da take ci mata tuwo a
kwarya, shima dai ya jinjina. Ya ce, "Allah ya
kyauta." Ta kalle shi wani iri, gaskiya ku maza ba ku
da adalci." Ya yi dan murmushi "ya za ki yi
Jama'u?" Ta ce, "dole na yi, abun ya gigita tunanina,
iyakar sani na yaya mutumin kirki ne, na rasa me
yake taba masa kwakwalwa irin haka yake abu ba ya
ko lissafi." Ya ce, "To ai ba ki sani ba, shi sha'anin
aure wani abu ne cukurkudadde, da sanin hakikanin
gaskiyar abunda yake Sata zaman aure sai su
ma'auratan, be ki san ainahin dalilan da suka sa shi
yin sukin ba,,mai dakin ai shi ya san inda yake masa
yoye," Ta ce, "ba wani nan, Alhaji rashin kirkin
mazan ne рotsa, ba wani inda yake masa
yoyo, Allah na riga na fahimci matarshi gwargwado
mace ce, metuniyar kirki, kana gani dai da diyar
manya ce, gata da kyzu daidai nata ga iliminta, ba ta
da kazanta, ba ta da vweni mugun halin da za a ce an
yi kuka da is, gwargwado mu danginsa ta bamu
babban matsayin da duk surukar kirki za ta iya ba wa
kowa, shima yayan sonsa take gwargwado tana kula
da shi, shi ko Yaya me yasa ya yi mata irin hakan?
Idonta ya taru da kwallah, zamani ya canza, shi yasa
123
Haske Magantn.... Maiturgre
lyaye suka dage neniawa 'ya'yansu ilimi da zą su
dogara da kansu, don rage ma zuciyoyinsu radadi da
na fargabar rayuwa."
Alhaji ba ka ga a yanda nå ganta ba, ta wani
dashe ta yi fari da rama sai hancinta da ya dada
fitowa, ga kuma nauyin ciki, ban da Yaya ko don
wannan nauyin ba zai tausaya ba? Ta ban tausayi
inda take 'yan kazar-kazar da harka duk tai laushi
tana abu da rashin kuzari a wani darare, Gaskiya
mutuwar aure bala'i ne." Ya ce, "haka aeAllah ya
ba ni ikon rike ku da adalci da gaskiya." Na ce,
A'min.
Ranar Maryam da mugun takaici ta kwana,
maigidan ma bai samu yanda yake so ba, sai bai
matsa ba, shima ya tayata jajantawa. Da safe bayan
ogan ya fice, bata tsaya ko cin abinci ba sai gidan
Hajiya. Tana lazimi ita daya don Hafsat ta je
Makaranta Don bayan barin Maryam Hafsat 'yar
gidan Anti Hauwa ce ta komo gurinta.
Ta kalle ta kadan, haka nan sai ta ji gabanta ya
fadi. A zuci ta ringa ambatar Innalillahi! Da ya ke
mai tawakkali ce. Bayan ta shafa fatiha ta kalle ta
sosai suka gaisa. Ta ce, "Da safe haka lafiya dai ko?"
Ta dan marairaice, "lafiyata lau Hajiya. Jiya kuma
sai ba ki ga na dawo ba ko?" Ta çe, "Ai kin raba min
magara ne, da ban ganki ba na san kin wuce gida ne,
suna lef ya ko?" Ta cc, "Eh to, lafiya ta jiki suna da
ita, itara ba lau ba, don zuciyarsu cikin rauni take,
Hajiya Yaya Muttaka bai ji maganarku ba, ashe
124
Haske Maganin...z
Haske Maganin....
Maiturare
Maiturare
sakin Sakina ya yi, yanzun wurin sati uku kenan tana
gidanşu." Da nutsuwarta take gyada kai, sai can ta yi
haukala tare da tasbihi, abin da ta ce, shi ne Allah ya
kyauta.
Sun bata shiru, ta ci "Hajiya kuna da abinci ban
ko iya tsayawa na karya ba, da tarin takaici na
kwana." Ta cc, "Sai dai. ruwan shayi da guntun
burodi, ban sani ba ko zai ishe ki, idan kuma ba kya
so sai ki shiga kitchen din kiga ko za ki iya yin wata
dabarar." Ta yi gajcran tsaki, barshi kawai bari naje
gun Anti Hauwa, kila, na samu wani abun ko in sa a
karbo min waina da miya." Gyada mata kai kawai ta
yi, ita kuma ta mike ta fice.
aAnti Hauwa na kwance bayan ta gama 'yan
kintse-kintsen gida, tana hutawarta tunda full house
wife ce, tana karanta sabon littafin,Maiturare 'kwai
tara tsinana.' Ta daga kai tana amsa sallamar
Maryam, ta tashi zaune ta harare ta, "Ai ciki nake da
ke, an ce mi9n jiya kin zo, ina ta zuba ido inga inda
za ki shigo, sai shiu ta gaya min." Ta tabe baki, ta
isa kujera ta zatuna bayan ta aje mayafinta da Jaka.
Ta ce, "bari Anti, na iso da yammaci ba shiri na fice
daga unguwar, bakin ciki kuma ya hana min
dawowa." Ta shiga nutsuwarta. "lafiya dai ko?" "Вa
lafiya Anti, Yaya Muttaka ya ja mana abun fadi, ya
yi karanta, bayan anmishi harkar girma ya saki
Sakina, ashe kusan sati uku da suka wuce." Ta raka
salati da rudani, ta ce, "oh ni Kulu na banu, matsalar
sai da ta kai nan?"
125
Haske Maganin..2 Maiturare
"Wallahi Anti Hauwa ba mu sani ba, sai jiya da
Allah ya taimake mu ya sada mu a waya, shi ne fa na /
fita na bar unguwar na je gidan su."
Ta rike haßa, tana jajantawa. Ta ce, "To Allah ya
shiryc shi, ya ganar da shi, ya yi halin 'yan duniya ya
aikata ba daidia ba ya kuma ja baki ya yi kurum, kai
da namiji sai a hankali. To Allah ya kyauta, ba a fisati ba mu kaį waya da shi, dan duniyar ko a mura
bai nuna min da damuwa ba ina ta tambayarsu ya ce
suna nan kalau din su." Ta ce, "Hmn, bari ni abun.
tambayar me yake damun kanshi da rayuwar
gidanshi ne? Ba ya tuna kowa hakurin yake yi?" Тa
ce, "Ki dai bari kawai Allah ya kyauta."i
A nan ta ci abinci har ta yi dan barci, don jiya
barcin nata fifty-fifty ne. Anti Hauwa ko waya tai
ma mijinta ta gaya masa. Nan da nan zancen ya zaga
kofar Nassarawa, kowa nata nita da fadar
albarkacin bakinsa, gwargwado an yabi Sakina da
kyakkyawar shaida. Wannan kenan.
Rayuwa duk abun.da ka yi ka yi kokarin yinshi
da tsarkin zuciya da kyakkyawar manufa. Allah na
jare da kai, na
Tare suka je gun hajiya wai su ji ta bakinta, tunda
ba ta ce komai ba, dole auren igiya daya aka cire
akwai yiwuwar ai kokarin daidaitawa, ya fi ai shiru
azuba ido, Sakina rashinta duhu ne a cikin
zuriy arsu. Baiyanarta haske ne babba..
126
Haske Maganin.... Maiturare
Tana shan ruwan shayi suka isketa sun gaisa da
Hauwa ta ce, "kinga abun mamakin da Muttaka ya
yi ko?" Ta ce "wallabi ko Hajiya, kuma sai ya yi
kurum don kada kowa ya yi masa magana kan abun,
bare a samu a daidaita su." Ta ce, "hmn." Ya yi da
mu ne ai, ina so ne ke da mijinki da sauran yaran
kada wanda ko a fuska ya nuna masa ya ji abun da
ya faru, a barshi da abunda ya yi, Sakina idan tana
da rabon dawowa cikinmu Allah ya saka mata ya
daidiata su, idan kuma bakin zaman ne kenan Allah
ya musanya mata miji da wanda ya fi nata, Allah ya
raya zuriyarta da albarkar rayuwa mai yawan gaske."
Suka amsa da amin. Amma ita Anti Hauwa da ba
haka ta so ba, kamar da inda aka taru aka daidaita su,
wannan ma ai akwai dama, gara kawai manya su
shiga. Ama tunda Hajiya ta ce hakan ta san akwai
hikimomi casu yawa a ciki, Allah ya kyauta, amin.
Sun dade suea tattaunawa, sannan ta umarci
Maryam d ta koma gida, itama Hauwa sai ta yi
salläma su ka wue g
Washe gari da kanta ta fito bata nemi kowa ba, ta
samu a daidaita sehu aka kaita har kofar gidan su
Sakina. Amma bata nan ta je asibiti sai dawowa ta yi
ta ganta, sun gaisa da mutunci, sun jajantawa juna da
kyau tare da basu bakuri, ta ce, ba komai ba mu
kullaci kowa ba, Allak shi yake shirya dukan
abubuwan da su ke faruwa a duniya, Idan da sauran
rabo a gaba sai kiga an daidaita a gaba an koma." Ta
ce, "haka ne, na gode muku, ni bani da abin saka
127
Haske Maganin...2 Maiturare
maku, ko da wannan na san Muttaka ya yi babban
rashi, in da duniya ta rinca6e da rikici, mutane na
rayuwa ba Allah a gabansu -duniyar kawai su ke
tsikara da tsinke, Allah ya kyauta, amin.
Hajiya ta yi taima Sakina nasiha kan ta yi hakuri
ta manta da komai ta fuskanci Kalubalen da ke
gabanta a rayuwa, kada ta bari wannan ya takurata a
rayuwa, komai da yake faruwa ai da sanin Allah." Ta
bude Jakarta ta mika mata dubu biyar Sakina ta rike
baki ta ce, "Kai Hajiya, wallahi ki bar su, ba ni da
bukatar kudi tunda komai nan'yi min su ke yi." Ta
ce, "Karbi kar ki min musu Allah shi ne'ya isa ya
miki dukan komai, nima da na bakin ai ba ina nufin
kiyi komai da su ba ne, ai su kudi rana gare su,
sanyin zuciya ne, zaman gida bayan ka barshi gaban
iyaye wata rayuwe ce babba mai wahala, wace a in
ba samun tsayayyun iyaye akai ba, su kuma
zawarawan masu kwatanta tsoran Allah ba, sai kiga
daga nan rayuwa ta gurbace a shiga yawo kwararokwararo, lungu-lungu. Rayuwa ta shiga garari."
Ta mika hannu ta karba, ta dibi dubu biyu, ta ce,
"Hajiya ki bar wadannan sm isa." Kallonta ta yi
kawai ta fara kokarin mikewa zata yo sallah, itama
ta rigatace taje ta zuba mata ruwa a buta, ta yi
sallah nan ci abinci har magriba ta kai a gidan ta
ce tana sór penia Alhajinsu ne.
Ya ji dadun ganinta, shima ya ce ya yi mamakin
rashin ganin kowa daga nasa, wannan yasa shima bai
nemi kowa br Ta ce, ne ku yi hakuri ni yanzun
128
e
Haske Maganin...2 Maiturare
ba biko na zo masa ba, ka sani yaran nan na zamani
danyan kai gare su, tunda mun yi sulhu abu kamar
ya gyaru sai kuma bai garu ba, kila dai akwai abun
da ya dauke masa hankali, wanda hakan yake jin ko
mu ma ba mu isa ya gaya mana ba, don kar mu yi
masa dole, to zan kawo ido ne na zuba, Allah dai ya
ba mu rai da lafiya, amin."
Allah shi ya san gobe, ita kuma Allah ya raba su
lafiya."
Alhaji ya'ce, "Amin, na gode." Su kai sallama ya
saka Muji ya maidata gida, don hankalin 'yan jikoki
ya tashi ba a san inda ta yi ba, ga shi har Magriba ta
wuce dare ya shigo.
Gidan Anti Hauwa ta shiga, ta ce Hajiya ana ta
jajanki." Ta ce, "wallahi ina gidan u Sakina,
mutanen kirki can na wuni na kuma tsaya har naga
Babanta na ba shi hakuri, dattijon kirki mai fahimtar
yanda rayuwa take, bai zafafa ba, ya bar komai a
hannun Alah ne ya ce ba zai dai saurin kwashe
kayanta ba, sai har te haihu." Anti Hauwa ta yi
jagule tana jimami. 1
Bayan kwana uku da bazuwar labari a wani
yammaci, ya shigo agowar su cikin lafiyayyar Ieep
dinshi sabuwa da ya sake, sai daukar įdo taks, ya
fito cikin shadar shi, ta sha starch turarenshi sai tashi
yake yi, fotar shi ta dada kwantawa ya yi fresh
alamar yana hutawarshi. Bisa al'adar cikin gari idan
yamma ta yi akan ga yawanci maza sun yi majalisa
suna hirar zumunci, don yawanci an taso daga aiki
12
Haske Maganin...2 Maturare
ko kuma an taso kasuwa, sai akai sa'a ranar ma butu
ne aka bayar na rasuwar gwarzo dan kishin kasa
Dokta Muhammad Abubakar Rimi, wanda Allah ya
yi wa rasuwa ran Lahadi sakamakon bugun zuciyar
da ya same shi lokaci daya da ya hadu da Mala'ikin
duniya 'Yan fashi. Allah ya jikan sa da rahamarsa
mayawaiciya, Kanawa mun yi rashi da Nigeria in
general.
Jin shi ya ke yi'wani sama-sama, duniya ta yi
mishi dadi, ya ringa gaisawa da jama'ar unguwa har
ya iso gidan Hajiya. Ya same ta ta yi-bakuwa suna
tsakar gida suna shan iska. Ya baza riga bayan ya
nemo kujera ya gaishe su, suka amsa, bakuwar ta
ringa tambayar ya iyalin? Marar gaskiya ko a ruwa
jibi yake yi, yanda yake amsawa da magana, amma
Hajiya sai ta dake, da dai bata san komai ba, ya
kawo ihsani ya yi ma Hajiya da bakuwarta, bakuwar
ke godiya, Hajiya kanzil ba ta ce ba, shi da kansa sai
da ya tsargu, amma haka nan ya mike ya yi sallama
da su.
Ya fita zuciyarshi na wasi-wasi ya leka gidan
Hauwa, tun a tsakar gida yake cewa, "Kulun
Majadin ina ki ke ne, har ya iso falo. Tana zaune
tana kallo tana kuma jinsa. Ya cake ya harare ta,
"Au, ku fa uata tsiyata da ku kenan, da kun ci kun
koshi, sai ķ fara ma mutene hartin iska kuna hura
hanbi ravr ta tagbi hake kina jina ina. ta
shargake ni cai?". Ta kalle shi a dage don da gaske
haushmsa trkoui, tana kirha tausayinsa don da wuya
Haske Maganin...2 Maiturare
y& cike gurbin da ya rasa na matar kirki saliha, inda
matan zamanin nan kansu kwance yake ba noti.
Ta ce, "Eh guri na samu ne, ka sani ni dai ba inda
za ku yi da ni na zama takalmin kaza, mutu ka raba,
garkami wandon karfe, ko an kashe maciji, ba a cire
kai ba an yi ta banza, don ba inda za ni." Háka nan
sai ya ji maganar ta tabi zuciyarsa da yake mai
gyambo ne. Amma sai ya yi dariya ya ce, "dama mu
tnun isa ne, ina za mu kai uwar tuwo ne?" Ta tabe
haki, "Ah wai ko da kuna niyya tunda, idonku ya iya
gane-gane na kyalkyal banza ko?" Sai ya yi
murmushi, rigima ki ke ji kawai uwar tuwo, kuna
lafiya dai ko?" Ta ce, "ai ka ga ni da idonka, tunda
ba a kwance ka ganni ba," Ya ce, "A'a, kan ki guda
uwar tuwo, wadannan maganganun da ki ke saki fa,
tamkar da biyu ko an miki laifi ne, ni na zo zán taka
san barawo Yayana ya yi laifi?"
Ta ce, "gwargwado Yayanka ai mutumin kirki
ne, ya san