kaina ya san darajata, kuma mun fahimci
junanmu, matsalarmu kadan ce, za mu iya
maganinta, ba sai duniya ta ji mu ba." Kallon da ya
yi mata ta fahimci jikinshi ya ba shi sosai. Amma da
ya ke dan duniya ne sai ya share, ya ce, "Тo
uwargida a taihaka min da ruwan sha ko?" Ta се,
A"ga shi kuma gidan duk ba yara sai dai ko ka karasa
da kanka kitchen din ka samo, tund aba bakon ka ba
ne." Bai fushi ba, ya tashi ya shiga kitchen din, yana
fitowa da kwalbar ruwan maigidan na shigowa. Ya
saki fara'a, ya ce "A'a Yaya barka da dawowa." Ya
131
Haske Maganin.... Maiturare
daga masa hannu "Yanwa barka kadai, ya shige
dakinsa bai kna fitowa ba." Hoka nan Auti Hauwa
tunda ta bi mijinta bata leko ba, abun ya ba shi
haushi ya daga murya, "To uwargida zan wuce."
Daga can ta-ce, "Allah ya tsarc hanya." Ya yi
sakoko, amma sai ya ce, "to fito ga sako ki aje ma
yara." Ta ce, "Sun gode, aje nan kan T.V. idan sun zo
sa dauka." Ya yi baktin Kelewa da gaske, kawai sai
ya juya bai aje uwar-Koniai ba ya fce.
Amma zuciya rshi cike da tunani maiyawa, ba
ya raba daya biyu sun fahimci abuu da ya fru, don
ya san mutanensa tamkar yunwar cikinsa, kuma ya
san ba su aje Sakina, kusa ba, wulakancin da su ke
ma sa ma dalili ne.
A faruwar al'amarin nan Hajiyaaai yake
shakka, don haka ya kasa outsowa ya yanke
shawarar bugar cikin. Maryam doa yu sen duk
bakinsu daya.
Ya doka wayarta ya fi sau gona, ba ta dauka ba,
sai can da taga, bai da alamar daina wa ta dauka, sai
ya kama fa da.
"Haba, wane irin aikis banza ne kiaa ji ana ta
kira ba ki daga ba?"
Ta сe,"Ba na kusa ne, shi-yasg, ya aka yi?"
"Au, ya aka yi ne ma za ki ce-min, saboda ni
sa'anki ne, ba ki iyu gaisuwa be kenan?"
"Au, yi hakuri ina yini?" Kawai sai ya Kara
Kulewa ya latse wayar. Itama ta tabe baki ta aje
Haske Maganin...2 Maiturare
wayar tana harararta. Bai san ita ta fi shi jin baushin
kansa ba.
Ya latse wayar ya zauna, ya yi shiru ranshi ya
ringa azalzala, amma can sai wayar salularshi ta fara
fidda kida mai dadin sauti, yana dagawa da yaga
sunan wanda ya yi appearing sai zuciyarshi ta yi
wani irin haske, ya kara mikewa sosai kan doguwar
kujerar ya kara wayar a kunnanshi, dayan hannun
kuma yana shafa.kanshi, kana kallon fuskarshi za ka
fahimci yana cikin mutukar nishadi mai yawa.
Ya ce, "Hellowww Murja." Ta ce,"Hellow.
maigida ya ya ka ke kana lafiya ne?" Ya yi dariyar
shalara, "lafiya lau tawan, duk yau ba ki ji ni ba ko,
awmma ai kinga sakona ko?" Ta ce, "wallahi dalilin
kiran kenan, ka san idan ban ji sarauniyar muryar
nan ba wani ganewa zan yi ba, amma dai za ka bullo
da dare ko?" Ya ce, "Ah sosai ma, to ina za ni rage
dare ban da nan in zo in kalli sanyi ido ni da nake
gwauro gida ba kowa, ko za ki daure ki zo min tayin
kwana ne, gidan ya yi min fili da yawa?" Tai wata
irin shu'umar dariya, zuciyarta tamkar aa sabunta
mata ita. Тазсе, "Мaigida da babbar harka irinka ai
kai ne ka so zaman kadaici, don me ka kori Madam
din, in ka san za ka takura?" Ya yi tsaki, "Shu'uma,
haka za ki ce min, tunda idonki ya shiga cikin nawa
kin kuma barin zuciyata zama lafiya ne da kowa? Ko
kin bar zuciyata ta kuma kallon wata mace da kima
ne? Gaba daya kin raba ni da kowa, kin tattara son
kowa kin Landame, ko cikin kadaici nake ban
133
Haske Maganin...2 Maiturare
damuwa don ina tare da, ke a tunanin zuciyata muna
zantawa da zuciynta ka: oyayyarki, shi ne za ki kira
min wata kusa na, Ailah da gaske kawai bakinta na
ke gani, na kasa hakurin dauke dona daga kanta,
gani nake komai ta yi don neman yardata, bakinski
nake gani. Wai anya ko Murja kin bar ni hakan?" Ta
yi wata irin dariya da sai da ya ji sautinta a jikinshi,
ta ce, "Maigida Allah ko na rantse ban maka komai
ba, so ne kawai don dai ba ka san yanda ni nake ji
din ba ne, shi yasa ka ke wannar "katon, na bar kowa
don kai, na hakura dakomai dor ia kasance da kai,
ban da zaman lafiya sai ina tere da kai a zuciyata ko
a fili, Allah man dinnan ka tafi da ni sosai."
Ranshi ya yi mishi dadi, Murja ta iya soyayya, ta
iya kashe shi dz kalmar so. Ya yi dan tsaki, "gara nai
wani abun Murja akan ki, tun kan son nan ya'ja mu
da yawa, don na gane wannan son mai rigima ne, ya
iso da babbar harka." Ta cc, "gaskiya ne ogana, ni
ma ina bayanka, karatun nan kawai ya gundure ni, ni
don dai an matsa ne dama can ni ba wani kwanta
nain ya yi ba, na fi son zaman aurena." Ya ce, "Haka
ne kam, zan ga Hajiya naga ta inda zan 6ullo mata,
kin san har yau ban fadi mata na rabu da Sakina ba,
na san Hajiya da Sakina ba sauki, ba su aje junansu
kusa ba."
Zancen bai mata dadi ba, don ita ba wannan ce
kawai damuwarta ba, kanta kawai ta sani, ga kuma
kishi da yake taba mata zuciya, don baka sai bata ce
komai ba, har ya gama wannan zsacen ya gama ya
184
Haske Maganin....2 Maiturare
komawa shafin soyayyarta gaba daya sai suka
shagalgale suka manta duniya da kowa sai jinsu suke
tamkar suna tashi sama kan tsuntsun soyayya.
Soyayya masu gari, Allah yasz ta dore ai ta ta ci
har a nade kasa. (Uhm imata da maza masn duniya)
Yau da gobe, a kwana a tashi, rayuwa mai
wucewa, Sakina a gidansu tana ta rayuwar maleji,
yau da lafiya gobe babu, yau zuciya da sukuni gobe
babu, duk da gwargwadon kula Amma na yi, Alhaji
idan ya dawo kasuwa ka'ida za'a shigo da kayan
kasuwa, ha Sakina daban ne 'yan kayan kwalam, da
na inganta jiki da lafiya kawo mat yake yi. Kuma
lokaci-lokaci yakan kirata ya zauna da ita su yi hira
ya kuma bata kudi wai ko zata ga wani abu tana so
ta saya, Sai takan yi dan murmushi soyayyar iyaye
soyayya ce mai dadi mai bau mamaki, babu wanda
ya kai iyaye daraja gun 'ya'ya. Amma wasu iyayen
ba su dau 'ya'yansu na su da daraja ba, bare su yi
musu kallon rahama.
Da da dukiya amana ce babba Allah ya ba mu.
Hattara iyaye, Allah ya taimake mu ya bamu ikon
sauke amanar da Allah ya bą mu, su kuma ya'ya
/Allah ya basu ikon bin iyayensu da kauna da tausayi,
amin.
Kin sani komai na Allah ne, sai ya amince ka yi
abu ka ke yinsa shi yasa a kodayaushe ake son
135
Haske Maganin...2 Maiturare
mutum ya nemi taimako gun Allah. Allah ka dafa
mana ba don halinmu ba, amin.
Kuma haka uan yayyanta' na bakin iyawareu,
gwargwado tana cikin mutsuwa da gatanta, sai dai
kodayaushe jinta take cikin kadaici, ta rasa wani
babban jigo, to heh (gare ta) aurc shi ne babban jin
dadi da kwanciyar hankalin mace, musamnan idan
Allah ya azurtata da mijí jarumi mai tsayuwe kan
iyalinsa, mai iya son mace, tamkar ita a lokacin de
take shanawarta.
Takan yi hawayc idan ta runise ido, ta kasa gane
dalilin da yasa nata mijin ya runtse ido, ya ringa
dandasa mata shegantaka, karshe ya sakcta ya ce wai
ta kara gaba ya saketa ta je ta auri Dangote a ci ci.,
Wannan maganar ba zata taba mantawa da ita ba.
Rayuwa kenan, mai juyawa kan salo guda biyu, zaki
da madaci. Aka.ce, duniya juyi-juyi, wai kwado ya
fito daga ruwa ya fada wuta.
Idan ta kadaice zuciyarta kan kasance oikin duhu,
dundum sai ta kan yawaita addu'ar Allah ya kawo
mata haske mai yawa.
A wani dare tana zaune tana kallon Zee Aflan,
yanayinta da nutsuwa sosai, sai dai 'yar kibar nan
tata kib-kib duk ta tafi sal cikuta da yanzun ya fitososai kowa na ganinsa. Ita kma Amma ita take
kallo kullum ta kalle ta tausaya mata take, don ta
gane abun da ya same ta ya girgiza ta ba da wasa ba.
Don dai kawai tana kokarin boyewa ae.
136
Haske Maganin...z Maiturare
Ta ce, "Sakina!" Ta juyo a dan firgice don
hankalinta ya tafi akan kallon sosai, ta ce "ni kuwa
ban ga kina shirin fara zuwa awon cikin nan ba, ga
lokaci yana ta dada ja ko shi wannan cikin, shi ba za
a masa awon ba." A sanyayc tai dan murmushi, "Zan
je ne Amma." Ta dan harare ta, "ko zaman jiran
Muttaka ki ke sai ya zo ya kai ki ne ko?" Wani
takaici ya kama ta, kawai sai ta yi kasa da kanta,
zuciyarta na dada azalzala, da tunanin a yanzun
yanda ta ke cikin duhun nan ko sharafa take bata
bukatar Muttaka kusa da ita, bare yanzun da take
numfashi mai kyau.
Abin da ya ke cikinta kuma tana son shi zata ci
gaba Ja rainon shi nata ne, laifin ubanshi daban, bai
shafe ahi ba. Sabanin wasu matan lokacin da namiji
ya kaita miki sai zefin zuciya yasa ki cire wata
soyayya da tausayi irin na uwa ki yakice yayanki
koda ba su kai lokacin da dole za ki yakice din ki
zubar da su ba. Wannan yana kawo rashin tausayi da
rashin shakuwa tsakaninki da danki. Komai na
duniya tan hakuri ne, duk abin da hakuri bai bayar
ba da gaske rashinsa ba zai taba badawa ba. Hakuri
maganin zaman duniya.
To da wannan ne ta lallaba ta fara zuwa Anti
matal, nan asibitin Mariğayi Sani Madakin Gini take
karbar shawarwari na masana kadan-kadan take
takawa da yake ba su da nisa, sai ta ganganro, to
wannan fitar taga jama'a yana debe mata kewa da
rage tunani mai yawa a zuciyarta. Yaya Zainab tai
137
Haske Maganin...2 Maiturare
masifar sai ta bar asibitin ta ję ko Aminu Kano ne
Kememe ta kiya. Ta ce, "Duk daya ne Yaya, tunda
dai ba wata larura ba gare ni, suma suna dubawA
bakin iyawarsu, suna kuma bada magani ai kuma
koina ka ke Allah na nan." Ta ce, "un, Allah ya
kyauta duk kin bi kin sukurkuce, sai ka ce akanki
fareu, ko kuma shi Muttakan shi ne autan maza." Ta
ee, "Ai dole ne, ba karamin al'amari ba ne gare ni,
don dai ba ki dandani dacinsa ba ne da za ki fi
taussya min, doa ma ina gaban iyayena guda biyд,
ina kuma da cikakken gata ne? Da ya ki ke zaton zan
zama? Amma ai ba komai, rayuwa ce wata rana sai
labari, Allah ya kyauta gaba, ku kuma Allah ya baku
zaman lafiya da mazajenku, Amin."
Yays Zainab ta yi shiru shi yasa ta ke dads
taušaya mata kuma maganar da ta fada hakan ne.
(hattara mu mata, zaman gidan miji fa, shi ne gaba
da komai, in dai da damar sulhu, ya fi ma je mu yi ta
fadi-tashi, mu diss can da nan. Allah ya kyauta.
Hakuri maganin zaman söyayya in an yi aji dadi?
Lokaci-lokaci Maryam na zuwa ta dubata, takan
ruko mats dan käyen dadi ita da Musadik, kuma
wayarta knllum ce alkawari ne biyu ko sau uku,
kuma tana yawan turo matą recharge card har ta yi
mita, wai yá isa ita fa ba anfani take da su ba. Ta сe,
"haba Sakina ba ki da fans? Ko ko shi ke nan is the
end of your life?kokari za ki yi ki manta da komai."
Ta yi murmushi ta ce, "Na gode kwarai tawan." Su
kai dariya.
138
y
Haske Maganin...2 Maiturare
Hajiya ma bata dai cika zuwa ba, tana yawan
kiranta su gaisa, amma tana yawan yi mata aikc,
'ya'yan Anti Hauwa na kai mata, Anti Hauwan ma
bata barta ba, dá Karamcihta mai yawa.
A wani falo mai girma, da ya kawatu da manyan
kujeru na alfarma, da labulaye masu masifar kyau,
an aje komai a muhallinsa, falon tamkar na wani
baban basaraken ko kuma 'yan siyasar zamani.
A can gefe daya kan kujera mai zaman mutum biyu, wata maca ce, 'yar gajcra, ita ba fara ba, ita ba
baka ba, ta yi kwalliya da shadda ruwan hoda ta
karbi jikinta, gold ko tamkar ya yi magana, don
ko'ina ya dau harami, a yanayin fuskarta ba kyau irin
wancan shahararre, sai dai ba muni, abin da yake
dada haska ta yawan kwalliyarta, da yawan fara'arta,
ga hakwaran Makkanta guda biyu da suke dada nuna
uan ajinta na manyan hajiyoyi 'yan duniya tana da אע jiki mai kyau. Ba laifi matar ta hau sosai.
B
у
ar
bi
Π
ga
ba
Mata uku su kai wa falon shigar girma, sun sha
kyau tamkar su dige, kalar dai matan zamanin nan đa
duniya ke masu aiyiriri, don biyu daga cikinsu ma
mayafansu kan kafada su ke sai tima-timar
Jakkunan da suka sagalo. Tafiyar sannu-saan aki
yinta, maganar ma kasa-kasa, ana dariya Rasan lefc
(a'a mata fa masu duniya.) Hajiya Maryam ta saki
fara'arta ta al'ada, hakoranta su kai kyau a bakiuta
tana musu maraba.
139
Haske Maganin...2 Maiturare
Suka zauna sosai, aka gaggaisa, Hajiya Kubra ta
cc, "Hajiya Maryam mun zo diban kaya, an cc mana
kin yo sabuwar dauka, na yi niyar na iyo miki waya
kafin mu zo, kinga mun zo biki wurin unguwar ku,
gidan Major- Salisu na ce da Hajiya Baraka kawai
mu karaso, bau so a bani labari, gara na bayar."
Hajiya Maryam ta ce, "Gaske kuwa, akwai kaya bari
a kawo dan lemu ku sha sai mu isa ku zabi wanda ku
ke so." Ta latsa intercom wata 'yar budurwar yarinya
ta iso da ladabinta ta ce, "ga ni Hajiya." A. yangance
ta ce, "A kawo ruwa da lemu masu sanyi." Ta amsa
ta fita, sai ga Budurwar yarinya ta iso, kyakkyawa da
ita, kana kallonta kana kalion Hajiya Maryam,
tamkar ta yi kaki ta aje. Ta iso tana wani karai-raya,
gaba daya hankalin uwar na kanta, tai wani dan
durkuso, ta gaida bakin Hajiya, Hajiya Kubra ta.се,
"Kai Hajja Maryam, yarinyar nan tamkar photocору
dinki akai, ta kuma girma sosai, wallahi ban fa dade
da ganinta ba, amma ji kamar ana janta." Ta yi
murmushin jin dadi.
"Girman 'ya mace kenan, ba shi da ko wuya ai,
gata nan yaazun level two ta ko a Jami'a, armma ta ki
kwantar da hankalinta ta samu koda degrce din ne,
kullum sai an yi fama da ita, tfi son kullum ta yi
kwance wuri daya ba ta ko jin nauyin jikinta, in ba ci
ba sai kallo."
Ta zumbura baki, ta ja Jakarta ta wuce fun tana
jin baushi an tuna. Suka bita da ido suna dariya.
140
Haske Maganin...2 Manurare
Hajiya Baraka ta ce, "Ni Hajjaju da naiwa dan gidana kamu, naga yarinyar ta min wallahi." Zancen
ya yi mata dadi, amma sai ta rausayar da kai, ta ce, "Wah! raba ni da Murjar nan 'yar rikici inda ta mutu akan son Baristan nan, na isa kawo mata zancen
wani? Ai a gidan nan in kana son zance ya yi tsawo
to ka tabo mäganar Lauyan nan. Ba ta ki a yanzun a
bude ide kawai a ganta gidan Lauyan ba. Hат
Babanta ya sallama. Ya ma yi na'am tunda ya ce ya
gano ba ya da aibu, mutumin kirki ne, kuma
iyayensa mutanen kirki ne, a part from that, ya fara
dagawa aljihunsa ya fara nauyi."
Suka kei banau suka tafa, Kubra ta ce, "kai
Maryam er yau kina nan dai ba sauki kudi tamkar
su kasheamma dada gaiyato su ki ke." Ta ce, "Ke
dai bari wallahi, ai kudi abokan tafiyar rayuwa, inda
mu kai uwar watsi da talauci kina ganin zan yarda na
kai 'yata ci rani gidansa ne? Ai inda nake juya daloli,
haka nan nake so itama da ta murmure in ringa tu ata
Dubai din nan da 'yar China, tunda mu kullum dada
girma mu ke, su kuma na kawo karfi, idan ta goge ai
neman wuri kawai zan yi na nade kafa, ita ta ringa
mana safara."
To kin ga ko yaushe za mu gaiyato mai
rangwamin gata, ya zo ya buwaye mu, gara kawai a
Karawa mai arfi-karfi."
Hajiya Baraka ta ce, "kina da gaskiya Hajja,
duniyar nan sai da masu gidan rana, rayuwar ba
tafiya take yi ba sai da su." Ta cc, "Ah to, gaskiya."
141
1
Haske Maganin.... Maiturare
Sun sha lemu, aka bude musu falon da aka
tanadar don haka, kaya ne tamkar banza iri-iri, suka
zauna, suka zaba, aka buga lissafi nan da nan masu
kyau su ka tashi.
Ita da kanta ta yi musu rakiya har wejan gate inda
suka tafi, ta dawo ciki.
Mai karatu sai na ji kamar nan gidan ne Baristan
Sakina ya ke kwankwasawa ya ke neman iznin shiga
ciki. To Allah ya raba shi da da na sanin ya shiga
haske ya koma duhu, beyan kowa fata ya ke idan da
cikin duhu ya ke ya dawe haske.Mu na dai ji muna
gani, muna kuma sauraro.
Barista ya yi juyi ya kuma juyi, da gaske kaďaíci
ya dame shi, zaman shirun ya dame shi ba abokin
rayuwa, kadaicin da yake ciki ba na wasa ba ne.
Gaba daya zuciyarshi ta tafi akan samun sanyin
zuciyarshi. Sakina ta fado masa ya dan ji tausayinta
da baby Musaddik ga baby cikinta ko a yaya su ke?
Oho! Zuciyarshi ta yi dim. Wani abu na aõa ta,
kawai sai ya samu kansa da lalubo lambarta yana
bugawa. Da kyakkyawan network bugu daya aka
sada su.
Tana barcinta na tofan gira, wayar daidai kanta ta
fara ringing ta dan farka a firgice, sai da nutsuwa ta
shigeta sannan ta dau wayar. Abun da mamaki,
Barısıa Muttaka a waya? Wani irin mugun takaici ya
42
Haske Maganin...2 Maiturare
kana ta, ta sa hannu ta tatsc wayar. Wayar da ba ta kums kunnata ca, sai bayan sati guda.
Ya yi tsaki da ya fahimci abun da ya faru, ranshi bai so ba, ya ce, "Oho dai." Ya muskuta gefe ya
lalubo lambar hasken ranshi, ya same ta sun ci Çredit sosai don sun yi soyayyarsu mai yawa.
A wannan ranar ne ya samu kwarin guiwar
tuntubar Hajiya da maganar auranshi, da kuma
maganar rabuwarshi da Sakina.
Ya yi wankanshi, ya dauki boyel mai hasken
sararin samaniya, 'yar shara sun amshe shi, sai bai sa
bula ba, sai ya taje sumarshi, ta yi luf-luf da
takalmanshi slifas mai yatsa daya na fata. Kamshin
turarenshi na manyan na taşhi.
Ya dai fito sosai, ya yi fresh ya gyara motarshi,
ya fice ya yi ma Hajiya siyayya mai yawa, wacca ta
danganci kayan abinci da na marmari, kuma da
yawan da dole sai ta bada, don dame shi haka yake
ya iya babbarharka.
Tana-gyaran dakinia ne ake ta shigowa da kaya.
Ba ta raba daya biyu ba, ta san Muttaka ne. Shima
ya shigo da sallamarshi da fara'arshi sosai. Ta fito ta
amsa kadaran-kadshan, su ka gaisa sai kuma can
hira kadaa-kadan. Tsakanin da da mahaifi sai Allah,
musamman da ya ke yans kokarin kyautata mata.
Sun se nutsuws sai can ya yi kasa da kansa,
muryarshi can Kasan makogwaran ya ce, "Hajiya ku
gafarce ni, ban dai san yands za ku dauki maganar
ba, wannan yasa nake ta nuku-nuku da ita tsahon
143
Haske Maganin...2 Maiturare
lokaći, amma don Allah ku yi hakuri, abin da na
dauka a rayuwa komai nufin Allah ne, komai na
faruwa bisa Kaddarawarsa. Na rabu da Sakina wurin
watanni uku da suka wuce." Ya da saci kallon
Hajiya yaga wane reaction zata yi, sai ya ganta cikin
nutsuwarta, tamkar ba wata muhimmiyar magana ya
fada ba.
Sun San bata shiru, ya dan finga muskutawa,
yana neman ta ce wani abu, ta yi shíru tamkar bata ji
ba. Ya dan kalle ta, "Hajiya -kun yi shiru?" Tа се,
"Haka ne, Allah ya ba wa Sakina mijin da ya san
darajarta da kimarta, namijin da zata samu
soyayyarshi de kwanciyar hankalinta mai yawa. Kai
kuma Allah ya sanya haske a zuciyarka."
Wani irin nauyi ya ji, tamkar abun nan dannar ya
danne shi, da kyar ne Allah ya taimake shi ya iya
daga ido da harshe zai kawo uzuri, kan abun da ya
faru. Tai saurin daga masa harmu ta ce, "Yi hakuri
ba komai kar ka damu, matsala kafin ta yi zafi ake
magance ta, tunda ta baci'hakuri kawai za a yi, ta
Sakina ta wuce saura kuma wacca ka shirya kawowa
madadinta."
An zo gabar da zai yi farin ciki ya tunkareta da
niaganar, amma ya sani, magangaa ta yi masa mas
harshen damo, don haká bai kuma céwa komai ba
ya tashi a sanyaye ya wuce. Ta fada gidan Anti
Hauwa, tana tsakar gida tana gyaran kayan miya, ya
yi sallama ta daga ido ta amsa masa. Tana jajen
kwana biyu, va ce, "Ah wane zai dunga rawar jikin
144
ل
o
anitoketaba
Haske Maganin...2 Maiturare
zuwa gurin ki tunda bakwa maraba da bako? Та се,
"Ko haka aka ce maka? Wa ya gaya min ni na gani
da idona." Ta ce, "To kila dai idou ne." Ya yi dan
gajeran murmushi, ya ja kujera fara ya zauna can
kadan da ita. Suka gaisa ya ce "Tsakani da Allah
Anti Hauwa na tambaye ki, kin ji abun ia ya faru da
gi?" Ta kame fuska wanne daga ciki? Ya ce, "Hmn,
kin san mun rabu da Sakinakuwa wata uku da suka
wuce?" Ta ce, "Um kai baba dai, har wata uku ba
labari?" Ya ce, "Ban raba daya ko biyu kun san
komai kun dai yi kurum ne kawai saboda ni ban
tunkarc ku da maganar ba, ni kuma fadan Hajiya ne
nake jin tsoro don na san bata aje Sakina kusa ba.
Don ni kuma abun da na dauka aure da mutuwa
ai lokaci ne pu ? Da ya karc ba sauran zama
sai tafiya." Та се,"Нaka ne mana, ai ka yi min
daidai, yaushe zaka juri zama da mai warin baki,
uwa na Jaba da shegen ci sai ka ce rumbu, irin
wanuan matan ai matsala ne, yanzun dai Allah ya
taimakeka sai ka auro 'yar Kasar Faris, ka san kuma
su Turawa ba su fiye sakin ciki wurin nadar gara ba,
dan abinçin, da su ke ci, tamkar na Jariri- sobon
haihuwa, kaga sai bubun shinkafarka ya fi shekara
kuna tsakura abunku, hankalinka kwance."
Ya yi dariya sosai, ya cc, "Antina ke nan,
wanman zambon da habaici rin haka ni na kasa gane
mé dame Sakina ta yi har na bari ta ture gwamnatina
gurinki? Duk kup ki dan gida kun riki bako." Та
ce, "Ganinka kenan, Sakina ta wuce duk inda ka ke
a
145
Haske Maganin...2 Majturare
L
zato a gurinmu, ba baki nai ma ba, Sakinan nan ita
ce hasken rayuwarks, hasken da gushewarsa, duhu
ne zai maye gurbinsa. Duhu kuma masifa ne, Allah
ya yi mana tsari da shi amin. Ka rasa babban bango.
Za mu zuba ido kuma muga wacca za ka kawo,
muga irin naka idön zaбен," Yа се, "Kamar kin san
da zancen da na zo kenan, na san Hajiya ba sauki,
shi yasa na kasa tunkararta da maganar duk da ta
kashe ni da mamaki, fadan nan da nake zato ba ta yi
min ba, sai dai maganganun azanci da ta baibaye ni"
da su, don haka yanzun ke zan wakilta." Ta yi sauri
ta mike ta süngumi bokitin kayan miyarta. Ta cе,
"kada ma ka fara, ni Hajiya ta ja kunne na da kyau,
kuma gwargwado na fahimci manufarta, don haka ba
na wannan layin, kuma tsakaniua da Sakina akwai
kyakkyawar ma'amala, don haka a zan shiga layin
'yan neman auranka ha, ąkwaı irina da yawa, ba damuwa muna daga gefe za mu yi addu'a ko?" Ya hade rai, "Gaskiya duk wanda ya yi min haka bại
adalci ba, a kaina aka fara sakin aure helfe ace nai
laifin da ba za'a iya gafarta min ba? Ita-an san abun
da tai min ne da na kasa hakuri? Ko ko don ni ban
da baki ne, ban kuma iya ba da cin hanci ba, shi yasa.
za'a nemi juya min baya." Ta ce, "Gaskiya kam, ai
karfar wakilcin aurenta ba, amma ai kai zaka iya wakiltar kanka a daura aure ya dauru sumul. Ka yi hakuri ka taba ganin in da fike ya zama kaya? Ni ce dai ba na layin 'yan neman auren matarka."
Ya zuba mata wani banzan kallo sai ta yi sauri ta
146
Haske Maganin...2 Maiturare
shige kitchen ta kama sabgarta tana ji yana ta masifa
ba ta ko kulawa ba, ya gaji da mita ya taso ya leko kitchen din to, "Uwas huwu na tafi idan kin huce zan
dawo sai nmu ci gana da maganar." Ta ce, "Kan ka
dai ake ji, na gama magana." Haka ya kada kai ya yi
waje zuciyarshi da rashin kuzari. Ba ya son komawa
gida, don haka ya juya kan motarshi zuwa gidan
abokinshi Pbrahim
Ya same shi ya na gida, yana tare da Madam
dinshi suna tare, su fadi gabanshi su tashi da
soyayyarsu mai shiga rai, hakan sai ya taba mishi
zuciya. Su ka gaisa dai da Ummi.
"Barista ya gidan da yaran, bata dai sauka ba ko,
ji nake cikin tamkar a jikina yake."
Ibrahim ya saci kallonshi don shima yana adawa
da abun da ys yi din don har kwana biyu sun dan yi
'yar tsama da shi, daga baya ne dai suka daidiata,
kuma shi don haushin abun bai ko gayawa Ummin
ba, shima ya saci kallon Ibrahim din da mamakin
rashe bai gaya mata ba? Lallai masu mata bukulun na
da yawa, kawai. sai ya dan hade rai, ya amsa a
gajarce.
"Lafiya lau." Ya rabo Ibrahim din yana mishi
wata hirar. Sal ita Ummin ta hada yaran suka fuce
daga falon.
Ibrahim ya samu dama ya juyo ya galla masa
harara ya ce da shi.
"Na dade ina, mamakin mugua hati da rashin
tausayi irin naka Matiaka, kan bau da mugun hali,
147
Haske Maganin...2 Maiturare
wane irin girman laifi ne Sakina take maka da ba
zaka kasa hakuri ka taussya mata ba, tana cikin
larura ka rabu da ita, lokacin da ta fi bukatar so da
kulawarka don tana cikin halin meciva da rayuwa,
kawai ka rufe ido ka cuce ta, kai ko me ya same ka."
Ya daga masa hannu.
"Kaga Malam zumunci na zo mu sada da kai, ba
wai fitina ba, abinda ya faru ni kadai ta shafa." Ya
mike yana hads takardun da suke gabansa. Ya
rungume su a kirjinsa. Ya masa kallon kankanci ya
ce, "Haka ne, kai ta shafa, wata rana za kai kuka da
idonka ne, Allah ya ba mu alhairi." Kawai sai ya
shige dakin matarsa
Wani irin azababban takaici