Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 11
nan ya ke binta, har su ka shiga harabar couctry mall, ita a zuciyar Murja dadi ta ji za a je a barzo mata sivayya ne. Bata tashi ganewa ba sai da taga Larista ya yi parking a waskace ya fita a warce a gigice. Ita kuma Sakins da nutsuwarta ta yi parking ta fito da kasaitarta de isa zake takawa sabida ta san tarkon da ta dana, yau bom zai tshi, Tana jinsa yana binta yana "Look Sahina, Sakin da ke nake bakya ji ne?", Bata tsaya ba, da hanzari ya sha gabanta уд tsareta... Ta tsaya cak, ta kuna zare glass din idonta, ta kalle shi ido cikin ido ta ce, cikin sanyin murya "lafi Haske Maganin Duhur-3 MAITURARE ya ka kc bina kana min kiran farauta, tamkar na ci ban biya ba? mene ne kuma?" Ya yi ajiyar zuciya ya yi kasa da murya; "haba Sakina, idan da alkawari ruwa baya dafa kifi ba, na meye irin wannan gudun da ki ke min na me nc? Haba Sakina komin tsawon zamani ko don darajar 'ya'ya ba za ki ringa tsayawa ko gaisawa ne mu ringa yi ba?" Ta kalle shi sama da kasa, sai ta ja baya daga tutsiyan da ya yi mata, ta bi gefensa za ta wuce. Da ya gane manufarta, da zafin namansa ya warto Jakarta dole ta ja ta tsayà. Ta hadi rai, amma cikin nutsuwa ta ce, "wai me ne ne haka ne? Ya za ka biyo ni cikin Jama'a ka nemi zubar min da mutuncina, ba ni da alaka ni da kai, don haka don Allah ka yi hakuri ka kyale ni ka kama gabanka, ka bar ni nai sabgata da ta kawo ni." Ta warce Jakarta ta wuce ta haye saman. Ya yi juın yana kallonta har ta kulewa ganinsa kamar an-cije shi, sai kawai ya rufa mata baya. Hall din ya yi cikar dango da mata iri-iri, classclass, sai suka cika masa ido tunda bai hango namiji ko daya a ćikin su ba, sai makadan da su ka gaiyato can nesa da su, dole ya janye jiki don ya kasa gaпо inda ta shige, ba zai iya kuma tsayawa ya yi wannan kurullar ba. 'ta kuma tana kallonshi sai ta dan sunkuya suna magana da wata Maiama. Har ya fice tana kallonsa, ta yi tsaki. 85 Haske Maganin Duhn-3 MAITURARE lau Allah ya kai shi kofar Nassarawa gun Hajiya. A yanda ta ganshi ya shigo sai da zuciyarta ta dan sosu. Ta ce, "lafiya ko?" ya zauna dabas kan kujena ya sanya fuskarshi a tafin hannunsa tamkar me yin kuka, amma ba kukan yake ba, tsabar kidima ce. Har sai da Hajiya ta kuma tambayar shi dalilin wandan zugum din. Ya daga idonshi da ya yi ja, ya sauko gaba Hajiya ya ce, "Hajiya na sani ke mahaifiyata ce, na kuma san na tafa miki zuciya sosai lokacin matsalar zamana da Sakina. Kin yi duk kokarin da za ki yi ganin ba a kai. matsayin da ake kai ba yanzun. Komai nufin Allah ne kaddaraw. ce ta Ubangiji. Kin tunasar da ni alhairinta, ni da kaina na gano hakan, na nei Hajiya ki sanya baki ta janye dumin da ta dauka da ni, Haa ba ki amince ba. Karó biyu Hajiya gani gare ki ina neman goyan bayanki, na ani Sakina taki ce, za kuma ta iya miki alfamas ila ba Yowa za ta iya yiwa ba, don Allah nake son ki sa baki nayi, iya yi na Sakina ta kasa ba ni damar tsavawa ta fahimce ni, ina jin tsoron wani sbu ajiya idona ya gano min wadansu abubuwa dor Allah Hajiya kiyi wani abu tun kafin na rasa wata daresta. Na sani Sakina tana da hakurin. juriya da kawaici, no kuma san matsayin da ts baki ba na wasa ba ne, zata iya komai sabida alfarmarki don Allah Hajiya ko don darajar yaran nan. Ina jiye Hscbo Mrarheuhug MAITURARE ن Haske Maganin Duhu-3 MAITURARE Gaba daya idon Barista ya rufe har ya manta tare da me fakinsa ne yake tafe, ya runtse ido yana bin mace ita kuma tana yakice shi, wanda duk wannan abun da ya faru tsaf a kan idon ita Murja din. Don haka lokacin da ya bita saman nan, ita kuma a lokacin zuciyarta ta kai kóloluwar kulewa, haba da takaici fa a gaban idonka? Don haka, ta saba Abdul a kafada ta warto Jakarta ta 6alle marfin motar, sabida tsabar takaici ko tsaya kulle shi ba ta yi ba, ta taka a hankali ta bar harabar gun. Idonta da zuciyarta sun makance sabida tsananin kishi, Wannan wace irin 'yar gwal ce ita da za a kasa runtse ido da ganinta a gabanta har sai an mata, kankanci? Kai rayuwar aure akwai wahala. Allah ya taimaketa babur din A daidaita ya tsaya, ta haye ciki sannan take gaya masa inda zata ya yi jim don ba nan ya nufa ba, amma ya karkace kai ya tsulo mata kudi, bata ko musa ba ta ce ya ajeta za ta biya. Ya manna a guje ya bar harabar gun. Barista Muttaka ya iso gurin motar shi, ganin motarshi can side din bude ya tunasar da shi tare fa da Madam ya ke, ya kuma san danbanzan kishinta, gabanshi ya fadi, amma kuma sai ya yi kamar abun bai dame shi ba, ya kulle motar ya zaga ya shiga gurin zamar shi, ya yi ma motar key wanda sauri ma bai barshi ya cire makullin ba. Yaja motar a guje tamkar zai tashi sama, la fiya 87 Haske Maganin Duhu-3 MAITURARE musu rayuwa ba a gaban uwa ba, in na tuna wannan - ina yin nadama sosai kan abunda ya faru. Hajiya ki gafarce ni don Allah ki taimake ni." Sai da ya kai aya, sannan ta nisa ta kallc shi tsayin wasu dakika ta gane yana cikin wani rikici babba. Sai ta ce, "Allah ya kyauta, ka je zan yi wani abu a kai." Ya yi godiya mai yawa ya taso ya fito. Sai da ya yi na'abba a mota ne ya fara tunanin ina kuma za shi? Gaba daya sai ya kwantar da kanshi kan sitiyarin ya gama rudewa. Ba Sakina, Murja na neman kubucewa. Baya son ya yi two zero kuskuren da ya yi a baya, ba ya fatan maimaita shi a gaba, don haka cikin rashin kuzari ya isa gidansu Murja, wanda ya sani nan ne dai inda ta nufa. Ya yi sallama a gaban falonsu Hannatu mai aikinsu ta-amsa, ta leko ta yi masa iso tunda ta san matsayinsa bai shiga ba, sai ya cake yana tambayarta ko Masantana na3?" Ta ce, "bata nan." "Murja fa ta zo nan?" Ta e "hata dzi iso ba, kila dai tana hanya Bar ce mata komai ba, sai ya juya ya fice. Zuwansa biyu ana cewa Mama bata nan kuma Murja bata zo ba. A karshe ys tambaya ko Maigidan na nan aka ce kwananshi biyu baya Kano.. Haka kawai zuciyarshi t ki yarda da cewar har karfe goma saura Mama bata gida ita kuma Murja bata zo nan ba, to ina zata? Ya buga wayoyin nasu duk is notresponding, try again later. Haske Maganin D MAITURARE Ya dawo harabar gidan ya zauna cikin motarshi, ya kunna futulun motar lare da buds. kofofim hadi da kunna rediyo. Har shadaya saura yana gidannan Murja ta leko ta window su ta ce, da Mama har yanzun yana nan dan kwakwar bai tafi ba." Mama ta yi kwafa, rabu da shi ai mun sa kafar wando daya da shi ni ce zai ma kankanci, shi ke nan kullum matsala har yaushe a kai auren ne? Sabida ya ga na kyale shi yana zaune lafiya lau ko? To yanda ban yi boranci a gidanku ba, in Allah ya yarda kema ba za ki yi boranci a gidan naki auran ba, duk inda 'yanci yake za mu bi shi mu sayo shi da kudinmu. Sakar min labule na ki manta da shi, shanya yanzu ne ya fara sai ya ji i ji sannan zan saurara masa, da ni. ya ke zancen." Cika r sha daya ya hankure ya bar gidan cikin mutuwar jiki, bai yi fatan lamarin ya kasance a lhakan ba. Sakina ta yi walimarta lafiya lau ta wuce gida gab, gabatowar magrib ta kuma ja bakinta ta yi gum, bata gaya wa kowa ba. Amma ta yi ta tunanin abun a ranta ita kadai. Maimakon abun ya bata tausai, sai ya ke kona mata rai, in ta tuno irin takaicin da ta ringa cusa mata, tai alkawarin ba waiwaye Allah ya raya su Musadik amma dan su ba za ta koma in da ba za ta yi farin ciki ba. Sam. Barista ya yi sintiri ya kuma yi amsa daya се 级 Haske Maganin Duhu-3 MAITURAKE Mama ta fita, maigidan baya gari, Murja kuma ba su ganta ba. Ya gama amincewa kawai karya su ke masa,wahalarshi su ke. Gaba daya sai ya gama burkicewa damuwa wata kan wata. Karshe dai ya zo ya gayawa Hajiya yanda ake ciki, bai boye mata komai ba. Ta gyada kai, "Muttaka baka taba so na zauna lafiya lau, da cikar nutsuwa da kwanciyar hankali ko? Kowane dan uwanka yana zaune lafiya lau da Iyalinsa, yanzun ka gane irin rikicin da nake ta guje maka ko, na ke ta nusarka ka yi hakurin zama da Iyalinka lafiya kowa zaman hakuri ne da kawaioi sai rayuwa ta shige tamkar ba ai ba." Ya yi kasa da kai, "ki yi hakuri Hajiya, ba ni da sama da ke duk duniya kowa ya bar ni, na san komai lalacewata ke ba za ki bar ni ba, kivi hakuri ki yi min addu'a yawan rai ne ya kawo haka da ba kya rayc. da baki ganni ba, wanran na daga cikin kaddarori na da ba zan iya guje núsu ba." Ta jinjina kai ta ce, "To babban.madogara Ailah ba tsayawa za ka yi al'amuran duniya 'su ringa firgitaka ba, Jarumi za ka zama ta hanyar tsayawa da jajircewa da dogaro gaoan babban za Bango Alla sama maka mafita da Hoyan bayan rinjayedaHhtsuwa akan đuk al'amuranka. "Na gode Hod Hajiya, Hajiya, Allah ya Kara niki 'afiya va da'savin ral mai amfani Ta ce, "To anu a, ka 91 Haske Maganin Duhu-3 MAITURAR je kai ta wuridin Ya Jabbaru Ya Kahharu dubu đay da dari daya da sha daya (1111), bayan ker Annabi Salati ma'i'shi tare da Istigfari don netow gafara da karin kusanci gare shi." Sai ya ji tamkar an sauké masa wani babbaj nauyi a zuciyarsa ya samu nutsuwa sosa: ya y sallama da Hajiya ya taho gida tunda ta ce, zata kin 'yan uwansa kan maganar Murjz, ita kuma Sakina y barta da ita. Bayan kwana biyar da haduwar Barista da Sakina, da hantsi ranar Talata, zamaain ya Makaranta su na hutu, don haka suma Malamai Da hutawarsu cikin Iyalan su. Sakina na gida tare da yaranta tana karatu da Musadik tana kokari koyarshi A.B.C.D. Wayarta ta dau kara, abun mamakinta Hajiyan Barista ce. Ta ji wani nauyi de ta manta yaushe rabon da ta kirata ta gaisa da itama har ta manta, ita dai tana ganin darajar tsohuwar mutunce kuma ta nuna mata kauna da halarci mai yawa, shi yasa itama take sonta da girmamata. Ta amsa wayarta cikin ladabi da sanyin murya ta ce, "Sakina kuma kwana biyu sai mu ka daina jin ko muryarki ko mun miki laifi ne?" Ta yi kasa da kanta tamkar tana ganinta ta ce, "ko. daya Hajiya laifin me? Ku yi hakuri don Allah." Ta ce, "Ba komi, ai kina ma kamantawa, ya su Musadik din?" "Lafiyarsu lau Hajiya." "To yaushe za ki kawo min Haske Maganin Duhu-3 MAITURARB su ne na kara ganin su, kin san rai bako ne, nama sha zazzabi har kamar ina tunanin tafiya ce kinga da sauran shan ruwan ashe a gaba." Ta ji wani iri da tausayi mai yawa, ta ce, "OЬ sannu Hajiya ba mu sani ba, Allah ya kara lafiya, sha Allahu zan shigo da su anjima da yamma mu duba ki." Ta ce, "To na gode Sakina Allah ya yi miki albarka." To da wannan Sakina bata koma ta kan abunda takc ba, sai ta tashi tsalam ta nemo Yusuf kaninta ta ba sbi kudi ya je mata abbatuwa ya sawo mata hanta me kyan da yawa da su alaiyaho da kayan miya. Ta yi matu shiryayyiyar miyar alaiyaho, da lemuka na kwalba masu Karin lafiya da jini. Ta shürya yaranta da shiga dan dagwas cikin irin kayan da Babansu ya kawo musu, itama ta saka daya daga cikin after dress din da ya kawo mata bayan ta yi kwalliyarta ta ciki da material mai kyau. Bata boye ba ta gaya ma su Amma inda zata, su ka ce a gaida tsohuwar suma ganin kimarta su ke yi, ta debi yaranta a motarta sai kofar. Nassarawa gidan Hajiya. Ita daya suka samu tai murna da ganinsu, suna zaume suna hira kadan-kadan na ciwonta da kuma wasu Jama'u da ita Sakinan ta san su a dangi, kadan- kadan sai Hajiya ta sako zancen da shi ne ta janyo ta ta isar mata. Haske Maganin Duhu-3 MAITURAKE Sakina ta yi kasa da kanta sosai, wani irin abu ya sauko mata. Hajiya ta ci gaba. "Na san an bata mikí Sakina da yawa, kuma duk wanda ki ka ji an ce ya yi hakuri an san an cuce shi ne, Sakira ba wai ina nufin tilasta miki yin abun da ba ki y niyya ba пе, н'я alfarma ce nake nema, na sani kina ban girma da jin maganata tamkar ni ce na haife ki, nima kuma na sani ina jin dadin hakan, wannan ya sa nake jin zan iya neman alfarmar koma, wacce iri ce ba tare shakku ba ki amsa min ita. Ki dubi girman Allah da darajata da ta yaranki, ki yi hakuri ki, komaws Muttaka don ci gaba da rayuwarku, ki dauka abin da ya faru kaddara ce gare ki babba. Na sani ina magana ne da yawuna, amma koma na san shi din wanda nake yi abun domin sa ya fini bukatarki gare shi, kuma ni kadai na san halin da ya ke ciki yanzu kan ki, don haka nake jan hankalinki da hakuri da Juriya da yafiya kan laifukan baya. Na fi farin ciki da ke a rayuwarshi fiye da kowacce irin inace zai kawo cikin gidansa don tuni na ganc ke gare shi futila ce mai haske duk wani duhun shi. Duk yanda na kai da nusarshi da be gane ba, sai da yaga uwar bari yanzun, in kinga halin da ya shiga akan ki za ki yi mamaki, don haka ki manta da komi ki rungumi kaddarar da ta faru ki komawa aurenki tunda da sauran damar zaman." Tunda take magana kanta a Kasa yake, kuma 94 Haske Maganin Duhu-3 MAITURARE hawaye ne ya ke diga daga idonta ta kuma kasa controliing dinsu (dakatar da su) ana wannan gabат tamkar da masaniya ko hadin bakin Hajiya sai ga Barista daga sama tsidik. Yasha mamaki da ya ganta ita da yaran gaban Hajiya, duk da motar da ya gani kofar gidan ta dan tabi ransa, amma sai yake ganin kai anya tata ce ashe kon ita din ce. Sai ya nemi kujera ya zauna ya yi ma Sakinan zuru da ido, har Hajiya tai maganarta ta kare ta tashi a hankali take takawa sabida girma ta fice ta bar shi shi da ita. Mashkurah uwar kankanba sai ta bita dakin da ta ga ta shiga, shi kuma Musadik tun da yaga Babansa sai ya manne masa. Barista yana ganin shigar Hajiya sai ya mike daga zaman da ya yi kan kujerar nan ya dawo kasa kusa da ita ya zauná. Duk wasu kalamai da dan Adam zai yi amfani da su da iyakar fahimtarsa ya bada hakuri Barista ya yi don jan hankali da ban hakuri ga Sakina. Amma tun da ta sadda kannan bata lago ba, kuka take yi sosai, wanda, har shima ya raunana masa zuciya ya ji kwallah sun taru a idonsa. Sabida tausayinta ya san shima ya bata mata de yawa ba laifin tsaye bare na zaune kawai sabida soyaryar wata. Kawai sai ta mike tsaye ya yi saurin mikewa Maganin Dиви-3 MAITURARE jikinar na rawa tamkar ya rungameta ca ya ke yi, "ins m ki ne Sakina?" Ta kalle shi a sanyaye, "Zan kauut nva ne a bandaki." Sai ya kauce ya bata wuri, tn flop tpknr gida ta dau butnr ta shige, sannan ya koma ya zauna akan kujerar ya yi zuru Musadik na miski tambayar fwafwaf bai kwe ba. Sakiaa tai kama ruwan ta dauraye fuskarta, sai ta leko tsakar gidan taga la kowa, ta dauke aumfashinta sadaf-sadaf ta fice da sauri waje a guje tu Rarasa motarta ta teshe ta da sauri ta bar unguwar dame Jakarta da wayoyinta suna mota, mukulinta ne kawai a hanaunta. Ba de wass take gudu ba, sai da tai nisa maimakon tai gida sai ta dauke kan motar tni caa shagari kwatas gidan kawarte, abokiyar aikints Malams Amins Mu'azu can ne ta je ta zauna her sai Xusan Karf tara sannan ta baro gidan da tare da ta paya mata abundayake damunta ba. TAMAT BI HAMDULLAH Ya Allai, Allab ka farawa Annabi Daraja, jikan iyuyenmn da wadenda su ka gabace mu daga cikin Jama'ar Musulmi.. Hauwa diyar Abubakar. Matar Yusuf Uwar ir Addul. AKARA ÖITY BOOKSHOI 07028826909 Daaa Marubucivar: KHAIRIYYA 1-2 BIYAYYA 1-2 BABBAR MACE... 1-2-3 JARABIN RAYUWA 1-2 KWAI TARA..1 Masu Fitowa: KWAI TARA...2 Tsarin Bango: ANKA - GRAPHICS FAGGE 07030319787 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11