Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 11
bashi amsa. Me ki ka yi a kicin da zai dauke ki wannan lokacin Humaira? Kinsan kuwa yadda kika sa min damuwa? " koyan abinci". Na kara fada. Yayi ajiyar zuciya tare da waji murmushi mai fidda sauti. To idan za a tafi kicin ba a tafiya da waya ne? Haushi ya kama ni, wai shi ba ya magana kai tsaye sai ya hada da tambaya? Kin ji? Ya bukata. Na ce, na mantata ne kan kujera. Yayi yar dariya, yace Don Allah ni da a ringa makale wata ko'ina za ki shiga kada ki dora min hawan jini, Ko ba a sin kiran nawa ne? Aifa, na fada a zuci. Kinji ba kya son na kira ne? Nayi masa shiru. Yanzu me da me kika koya?? Allah ka raba wannan bawa da tamabay, na fada a zuci. Yayi kasa da murya Don Allah ki fada min irin abin d kika koaya. Ai suna da yawa. Nace da shi. Suna da yawa har guda nawa kika iya? Duka na iya, ai basu da wuya. To ji ma koya kin. Wai ina marar lafiya ka tsaya kana faman tsokana? Wallahi duk tunanina a zuci nayi wannan maganar, sai kawai na ji ya tuntsire da dariya. Ga shi nan kusa da ni, ko na bashi ne?? Nayi shiru, gabana yana faduwa. Hajiya Humaira Gimbiya, wannan kasaitar taki ke kara ruda ni wallahi, Toh ko milk and coconut balls din ne a koya mun. Wai ko Yarima yana dubiya ne? Nayi murmushi na ce. Hmmmm Yace meye humm? Gashi zamu yi tafiyar dare ballantana na taya ki hirar dare. Ba komai. Na fada da sauri. Ke a wurinki yake ba komai, ni kuwa akwai wani abu.... ga su nan sun fito za mu tafi, kar ki kashe wayarki fa. Na ce to. Sai na kira. Ya fada. Allah ya kiyaye hanya, Allah ya bashi lafiya. Cikin jindadi yace, Ameen. Ban jira ya kara magana ba na latse wayar. Na kalli wayar ko me ya sa yake yi min wannan surutun alhalin ba haka yake wa sauran mutane ba? Ban fama tunanin ba na ji karam! Ina dubawa na fa sako. Ina rokonki da ki ringa sakin jiki muna magana ko a wayar ne tunda a fili kin kasa. Ina cikin wani hali Humaira na rashin sukuni da kwanciyar hankali, ga matsalar ciwon maimartaba, ga ta Fareeda. Sannan ga ta jama'a, wurinki kadai nake jin zan samu kwanciyar hankali, ba komai zai haifar da hakan ba sai kin yi responding da duk wata magana da zan yi miki, don Allah ki saki jiki da ni ina rokonki. Murmushi kawai nayi. Ga tsayuwar kicin ' yan share sharen da na yi da magriba, don haka gajiya ta taso mini, ina gama wanka waje karfe tara na kwanta ban kara sannin abin da ake yi ba sai da na bude ido na fa karfe shidda da kwata na safe. Na hanzarta yin alwala na gabatar da sallah Sannan na koma kan gado na kwanta kafin na kara hutawa zuwa billowar rana. Da wuri kamar yadda tayi min alkawari ta zo, don tare da ita muka yi kalaci. Kamar yarda Yarima ya umurce ta cewa kwana biyar, to hakan akayi, amma fa na koya abubuwa domin sai dana cika littafina mai farka arba'in. Kwana biyu kenan ba mu yi waya da Yarima ba, kuma na kasa nemansa. Sai na dauko kamar zan kira sai kuma na fasa. Zaune nake ina gyaran kumbar hannuna naji motoci sun shigo, na mike tare da lekawa ta taga ba hango zungura zunguran motoci nan na sarauta masu kofofi hudu. Budewar farko na hango Yarima ya yi saurin fitowa daga nan na ga an kamo maimartaba sun nufi babbab gida dake bayan inda nake. Gabana ya fadi, na dafe kirji tare da koma kan kujera nayi laggwab. Har bayan isha'i ban ga Yarima ya shigo ba, nan jikina ya kara mutuwa. Haka na kwanta ba don bacci ba, Can wajen karfe sha daya naji motsin mukulli ana bude kofa. Na runtse idona kamar mai bacci. Kamshin turarensa ya fara ziyarata kafin na ji ya shigo Na kara yin lami. Ya gama yan hidindimunsa duk cikin dakin ko wanka a nan yayi, sannnan naji yana kokarin hawa kan gadon inda nake. Na tamke idona. Ya hawo tare da yaye bargo dana lullube Shirun da na ji ya yi ya bani tabbacin kallona yake yi. Na tsargu saura kadan na bude idona sai kawai na yu saurin juyawa kamar cikin bacci ai sai naji ya janyo ni jikinsa tare da maida bargo ya rufe mu. Ai sai na fara kokarin zame jikina Ya kuwa rike ni tamau! Ya karkato bakinsa daidai kunnena yana magana a hankali. Ke ni ne ki kwanta ban yi niyyar tadaki ba. Amma sai da na zame jikina. Mene ne haka Humaira? Kina fa wahalar da ni da yawa Kin yi min rowar muryarki kwana da yawa Kuma yanzu sai ki hana ni jin dumin jikinki? Kin ji? Da ke fa nake magana? To me zance masa dan Allag? Ba ki magana? Ya tashi zaune. Wallahi ko ki matso konkuwa na hau kanki. Ba shiri na matsa. Yayi yar dariya. Matsoraciya duk kya gama Yan kauce kaucen naki ki dawo hanya......mun dawo me zan samu na sannu da zuwa? Ya rada min a kunne, na ji wani yarr!! Kamar na shakare shi duk na takura Wannan salon kuma ya dawo da shi? Lallai bone ta ci ni kuwa. Ba fa zan lamunci shirun nan ba wallahi. Humaira na gaji da wahalar nan Ko ba kiji ina magana ba? Ya jikin Baba?? Na fada kamar mai koyon magana. Da sauki yana nan gidan ma zai huta na wani lokaci Don haka kada ki sake ki nuna ina da alaka da ke. Gabana ya fadi ras! Lallai akwai babbar matsala. Yanzu me zan samu? Me fa! Duk tunanina a zuci na yi Sai da na ji yace Me fa ? Hmmmm. Yayi shiru sai na ga kamar ban kyauta ba Na daure na ce. Ka fadi me kake so sai in girka maka Bana burin abinci ya kwana Kuma ban san yau zaka dawo ba. Ni ba abinci nake so ba. Ban san lokacin dana ce To me kake so Ya dan kara kasa da murya kamar wani zai ji Ko dan kiss Ko motsi ban kara yi ba Kin ji? Zan samu? Humaira da ke nake Wallahi da Yarima zai gane da ya daina yi min wadannan tambayoyi nasa. Shi ne kika kyale ni? Kin ji? Na kara kulewa sai kace bakinsa aka yi kalmar kinji Don girman Allah ki taimaka mini Wallahi na kawo wa raina. Ya kusa bani ma dariya har da magiya. To tunda kin yi min bukulu juyo ki fuakance ni Ko hakan ma ba zan samu ba? Na dai yi masa shiru. Kinji? Wai don Allah kai ba ka san ina jin kunyarka ba?? Na fada kamar shirin yin kuka. Sai kawai naji ya kyalkyace da dariya. Ni ban sani ba. Ashe kunya ta ake ji? Wannan kunyar bata yi min adalci ba wallahi. Juyo na rage miki ita Don na lura ke ma ta takura ki Kin san Allah sai kin zaba Ko ki juyo ko kuma kiss. Sai me? Bakinsa naji ya hada da nawa Zan kwace yayi min wani riko. Na rasa inda zan sa raina don kunya. Ya dauki mintuna kusan talatin har jikina yayi lakwas. Yana zame bakinsa na yi saurin cusa kaina jikinsa kamar in bude kasa in shige abin da dama ya ke so kenan Ya kara gyara ni tare da rufe mu da bargo. Sama sama na fara jin nufashinsa alamar ya sami barci, amma da na motsa sai ya yi firgigi tare da matse ni. A haka har na hakura ni ma ban san kokacin da barawon ya sace ni ba. Ko da na farka ban ganshi ba, lokacin bakwai har ta wuce. Ban yi mamakin wannan muguwar makara fa na yi ba, na hanzarta gabatar da sallah ban tsaya gyaran dakin ba na fada kicin. Na soya dankali, sannan na dafa tsokar nama da albasa da kayan kamshi, sannan na jajjaga tattasai da dan tumatir tare da albasa duk na ajiye gefe, na dauko albasa ba yankata faken falen sannan na daka wannan dafaffiyar tsokar. Na zuba mai a tukunya na kawo yankakkar albasar nan na zuba cikin man ta dauka dahuwa sannan na zuba cijin man ta dauko dahuwa sannan na zuba jajjagena da dakakken nama na ci gaba da motsawa kafin na dauko baked beans shi ma na zuba ciki tare da kabeji dana yanka, sannan na zuba su maggi da sauran kayan kanshi. Wannan itace miyar cin dankali. Bayan na gama na soya kwai, sannan na hada kunun kuskus. Madara na zuba a tukunya kofi daya ta gari da ruwa rabin kofi suka tafaso sannan na zuba kuskus tare da kara dan ruwa na bar shi ya dahu lugub ba sanya maburki na burke ba juye a kwano na kawo flavour mai kamshin madara na zuba da madarar ruwa peak sai sukari. Na hada wadannan kaya na shirya wasu a tire na rufe da dan kyalle na rufe abinci, gyalena navdauka tare da fita wajen gidan Cikin sa'a sai ga wani zai wuce na kira shi muka gaisa yana min kallon rashin sani ban damu ba nace. Don Allah ka taimaka ka kai wa maimartaba kace daga gidan abokin Yarima. Yana ji na ambaci Yarima ya fara kyarma tare da karba cikin hanzari yayi gaba. Ni kuma na kima ciki don hada wa yArima nasa. Sannan na shiga gyaran gidan da yan share share cikin yan mintuna kamshin freshner da turaren wuta ya gauraye ko'ina. Na fada bandaki na yi wanka, abin mamaki ina fitowa na tarar an ajiye min wata doguwar riga mai dankaren kyau. Motsin kwanukan da na ji a falo ya ba ni tabbacin shi ne ya shigo. Nayi saurin shiryawa, amma kunya ta hana ni fita, yadda riga ta kame ni kam kamar daman an auna da jikina na kalli kaina na kara kallo. Kai duniya komai na son gyara. Ni kaina na yaba da kyan da nayi. Ganin lokaci zai kure har sha daya na niyyar yi yasa na daure nafito, saboda gabatar da abincin rana. Zaune yake yana faman latsa waya na dan karasa nesa da shi kaina kasa ban yarda mun hada idi ba nace Barka da sfiya, ya karfin jikin maimartaba? Gaisuwar tayi masa dadi a yadda na fahimta, yace. Alhamdulillahi da sauki wallahi, na je ma gida amso masa karin kumallo ne. Ina dawowa na tarar har ya gama cin wani abinci ta baiinsa mai dadin gaske, wai an kawao masa daga gidan abokina shi ne nakr neman wannan dan iskan in ji ko shi Abdul amma ba wanda na samu. Shiru na yi tare da mijewa na kwashe kayan, ga mamaki ya cinye komai. Ya kalle ni yana murmushi. Kr ni fa na lashe abincin, kin dai ci naki ki? Nayi yar dariya, Eh Dariya na baki? Ya fada cikin wata irin siga mai nuna matsanancin farin ciki. Ni dai na yi gaba abina in murmushi. Abin da na fara yi shine gyara kaza na wanke na jajjaga dan tarugu da albasa sannan na daka thyme da citta da tafarnuwa na hade wuri guda na kawi mai na zuba ciki, sannan na zuba maggi da gishiri na motse na shafe kazar nan da su ciki da waje, na saka gefe na dauko albasa davtumatir na yanka fyalen fyalen, na yanka kabeji kanana na ajiye gefe. Na dauki kazar na sa a oven tare da timing mintuna arba'in da biyar. Na wanke shinkafa da ma na dora ruwan zafi sun tafasa na zuba, sannan na barta ta dan dahu, sannan na sauke na wanke na tsane. Na yanka wani kabeji, karas, kokumba, koren wake da peas na tafasa hanta na yankata kanana da yar albasa. Na zuba mai a tukunya kadan yana yin zafi na juye vegetables dina da hanta sannan na zuba zuwa kadan na kawo shinkafar na zuba tare da motsawa, ruwan suka hau kanta kadan yadda zan ida dafata na rufe. Ina cikin gyara kayan miya Yarima ya shigo ya sha uban ado da irin kayansu na sarauta nan da nan jikina ya dauki rawa na kasa ci gaba da yankawa. Ya matso tare da shishige min. Me kike dafawa haka gida ya rikice da kamshi?? Zaka fara ko? Na fada a zuci, amma a fili na ce Abinci. Zan sami kamar na mutum hudu zuwa biyar? Insha Allah. Na bashi amsa. Ya rungume ni very good my princess. Zamu zo around 2:30 mu ci , kaya na nan su za ki canja kinji? Nace To. Duk na kagara ya tafi. Ya kai hancinsa a wuyana. Inason wannan turaren very sexy. Na dai yi shiru saboda na riga na yi mutuwar tsaye, ko me ye sexy kuma? Na tambayi kaina. Gobe dani za ayi girkin nan gaskiya, yau ma don am busy shi ya sa. Ya sake ni, sai mun zo cin abincin. Yana fita na saki wata ajiyar zuciya jikina gaba daya ya bige da kamshi turarensa. Da hanzari na kara gyara wasu kajin uku tunda wankewa ce kawai, akwai a firij na yi musu hadin ta farkon na kunna dayan oven din nasa su a ciki. Daidai shinkafar ta dahu na kwashe a katuwar kula kafin na gama na san ina zan zuzzuba. Muna da lemuka kala kala don haka ban wahalar da kaina wajen hada wani juice ba gani har biyu da mintuna biyar. Na sami babban kwando na zuba abinci na shirya wa maimaryaba komai na ajiye gefe, sannan na je na shirya wa su Yarima nasu a fako a kan table abin mamaki naji ana buga kofa. Na san ba Yarima ba ne sabida yana da makulli, na hanzarta isa sai na ga wani dogari da kwanonina, na bude ya durkusa. Maimartaba ya ce a yi godiya sosai. Na ce yauwa tsaya ka tafi da wannan. Na hanzarta na dauko lemuka kansa na sanya masa kusan kala takwas. Na kwashi nawa na yi daki na tarar ya ajiye min wata danyar shaddda galila ta sha aiki sosai, na yo alwala na saka, sannan na fara gabatar da sallah. Ina kabbarawa na ji motsin shigowarsu, wani dadi ya baibaye ni. Ya leko Au sallah kike yi? Ya fice. Koda na gama naci gaba da cin abincina a tsanake tunda su ma na ji suna cin nasu ne. Na gama nayi lamo ina jin hirarsu sai faman santi suke yi, sunabyi wa Yarima sharri. Wai da man don ya kwashi girki yasa ya haukace kaina. Na yafa gyalena na leka muka gaisa, za su fara tsokanata nayi saurim komawa ciki. Muryar wani na ji yana cewa, shege ina ka samo wannan shuwa arab din? Dole Gimbiya ta haulace bala'in nan alkur'an yarinyar tsoro ta bani......amma da ita zaka tafi jibi ko? Dadi ya ziyarce ni, ashe tafiya zai yi jibi? Ni dama gobe ko yau ne. Baka jin maganar Yarimaan saboda kasaita da jan girma wannan mutumin akwai isa. Yaushe ne ta ke haihuwa Gimbiyar? Ciki gare ta ashe? Na fada a bayyanr. Suka dai gama hirarsu ina ji suna amarya mun gode amma na yi shiru. Tunanina da shi aka fita sai kawai na ga mutum ya shigo alkyabba a hannu. Ya miko min. Ungo ki kai min daki. Na mike na isa tare da mika hannu sai kawai naji mutum ya rungume ni. Haba irin wannan delicious ai sai da tukwicin hug. Wallahi kwakwalwarki na ja, na san ko ita malamar taki da ta koya miki girkin yanzu ba zata hada kanta da ke ba. God bless u my princesss. Ya sake ni, zan je na amso wa maimartaba abinci, Umma har ta kai ga yi min waya. Nace to kawai. Har ya juya ya dawo Zo ki yi min rakiya. Ya fizgo ni muna zuwa bakin kofa ya mamayeni ya kai bakinsa ga nawa, sannan ya saki ji tare da yi min gwalo, sai kawai abin ya bani dariya sosai. Shi ma da dariyar ya bar gidan, na gaya shiga wani farin ciki mara misaltuwa, Yarima Hameed kenan. Karfe shidda na marece naji ana kwankwasa kofa, na hanzarta tare da tambayar waye? Yace kwanoni ne aka kawo na abinci. Na hanzarta budewa da man da hijabi a jikina. Kamar jiya ya risina. Maimartaba yace, ayi masa godiya mai tarin yawa, Allah ya albarkace ku ya azurtaku, ya rufa muku asiru duniya da lahira. Nayi murmushi cike da jin dadin wadannan addu'oin nace. Amin ya rabbi. Na karbi kayan ina shirin juyawa gida, sai ga Yarima kamar daga sama. Gabana ya fadi jikina yayi sanyi, ya kalli dan sakon da tuni ya zube kasa yana. Allah ya taimaki Yarima! Ya daure fuska, ya ya dai? Na maido wa matar abokinka kwanoni ne, kuma maimartaba na dada godiya, Allah ya bar aminci. Tashi ka tafi. Ya fada a hanzarce. Ni kuma nayi ciki da sauri. Ya biyo ni har kicin. Dama Humaira ke ce ke aikawa da abincin da maimartaba ke faman yabawa? Ke ce matar abokina da yake faman fada wa duk wanda ya ziyarce shi? Waye ya baki wannan shawarar? "ba kya tsoron hakan xai iya janyo a yi saurin fahimtar tsakaninmu 2nda kin nemi wannan kusancin har an san da ke? Kin ji?". Ba tare da na kalle shi ba, na ce. "ka yi haquri". Ya matso kusa dani "ba laifi na ce kin yi ba, shin kina ganin ba wata matsala ko ba kiyi 2nani ba kafin ki yanke hukunci?" a qagare na ce da shi "ba wata matsala in sha Allah". "kin tabbata?" "eh". Na fada ina shirin gifta shi na fita. Ya janyo ni jikinsa. "Allah ya yi miki albarka humaira". Bai qara fita ba, ya ce muje na taya shi harhada kayansa, sai wajen 9 muka gama, saboda mun yi sallar magariba da isha'i sannan tambayoyi da yawan maganarsa suka ringa bata mana lokaci. "wai humaira don Allah sai yaushe xaki saki jikinki da nawa?" murmushi kawai na yi "kin san shawarar da na ke yi yanxu?". Na ce "a'a". Ya ce "so nake yi idan na dawo na san yadda xan maida ki makaranta, ko ba ki so?". Na fadada murmushin kusan xuwa 'yar dariya "wallahi ina so saboda ma 2ranci". Ya kalle ni sosai "2ranci kuma?". "eh wallahi, ina son iya 2ranci sosai". Ya qyalqyale da dariya "to ko london xan kai ki qasar 2rawan?". Cikin 'yar dariya na ce "da ko ka kyauta". Wasa- wasa hira ta barke tsakaninmu, nan da nan ya fahimci lallai ina son ilimi 2nda ga shi ina hira da shi cikin sakin jiki, abin da ba taba ba. Da yake hirar ta yi min dadi ban damu da yadda muka kwanta gado 1 ba, muna ci gaba da hirar har sai da na lura da irin shige min da ya yi tare da yadda salon maganarsa ke... sauyawa nan da nan tsoro da kunya suka kama ni, amma ina lokacin da na farga na makaro, 2ni yarima ya kasa sarrafa kansa, yana faman salo... Ya rasa ta inda xai billo min nayi shiru, ni kaina na san kukan ba wai na ciwo ba ne, tsabar kunya ce ya sa na kasa tsaida shi, saboda ina 2nanin ta inda xan tashi, ga shi a dakin ya kasa ya tsare. "don Allah humaira ki yi haquri". Kalmar da yake ta nanatawa kenan 2n tashinsa. Ganin ba wani sauyi sai kawai ya dauke ni cak xuwa bandaki ya hada min ruwan dumi da komai sannan ya fito. Na sami damar dago kaina daga qasa ina raba idanu kamar wacce ta yi qarya. Na ma ba kaina dariya na samu na yi wanka amma fitowar ta gagareni. Sai na jiyo motsinsa can bayan daki, ai ko na yi hanxarin fitowa. Ga mamakina ya gyara dakin tsaf! Ya sauya xanin gado sai qamshi ke tashi. Ta taga na hango shi yana shanya xanin gadon da ya kware, wato wankewa ya yi. Ina cikin saka kaya ya shigo, ai ko na yi cikin wardrope din sai kawai na ji yana dariya. "xan je gurin maimartaba, ki hada abincin da ni don sai xuwa jibi xan wuce, na fasa tafia yau". Gabana ya fadi, ni kam na so ya tafi yau din kamar yadda ya tsara. Kamar kullum na hada abinci kala-kala, na shirya masa nasa na aika wa maimartaba sauran. Na sallame shi sallah kenan na ji shigowarsa da baqi. Har suka gama ban fita ba, shi ma bai shigo ba, da suka tashi kuma suka fita tare. Ina xaune falo ya dawo da qa2war leda. "sorry humaira, kadaici ya dame ki ko?". Ya qaraso inda nake. "wallahi 2n fitarmu ina kasuwa don samo miki abin kore kadaici". Yana maganar yana bude ledar tare da fiddo littatafan hausa da fina-finan hausa sabbi, masu kyau. Dadi ya kama ni, da ma in taba kara2n hausa ko a gida, musamman littattafan jamila ibrahim kankia, naja'atu haruna 'najnoor nasimat', da kuma na xainab dahiru wauwo 'xeedee'. Ya miqo min littattafan kusan guda 20, a sama wani sabon littafin mu2niyar ne, wato xeedee wai shi 'INA XA MU JE?' daga jin sunan littafin nasan dole ya yi dadi. Na yi murmushi "na gode qwarai". "ga kuma hausa films xo in koya miki hada kayan kallon yadda xa ki ringa sauyawa daga DVD xuwa satelite wataqila ba xa ki iya gane connection din ba duk da a hade suke ko da remote sai ki sauya". Nace "to". Tare da matsawa cikin doki da murna, saboda gaskiya xaman kadaici ya ishe ni kam. "abin ma ba wuya". Na fada ina yar dariya. Ya yi murmushi. Gare ki mai saurin fahimta ba...... Akwai sairan abinci? Wallahi yunwa nake ji. Eh na dafa wancan babu na ga ba ku rage komai ba. Yauwa bari na watsa ruwa, hada min kafin na fito Na shirya masa hadadden farfesun 'yan ciki da fried taliya, sai kemon kuskus mai madara da kwakwa a ciki. Ya kwashi girkin nan da kyau, da ma kadan na yi daidai ni da shi, ya cinye nasa duka. Na yi yar dariya tare da kallon empty kwanonin da farantin, sai ya kyalkyace da dariya. Me kike son cewa? Na kwashe kawai na wuce kicin. Ya ci gaba da cewa. Ko fiddo maganarki yarinya, so kike kice ina da ci ko? Kin manta garinku kenan lokacin da kike ba ji abinci halan? Daren ranar mun yi hira da kallon wani fim na Hausa mai ban dariya na dan Ibro. Washegari kuwa tunda ya fita da safe sai yamma ya dawo, sai ga shi da uwar tsaraba kayan daddawa, kuka,kubewa sauran tarkace wai in ji Inna. Na yi ta murna, tamkar Inna ce gabana. Goma na safen washegari ya bar gari da alkawarin bai wuce sati daya ko biyu. Nanji dadin tafiyarsa saboda na sami damar sakewa in yi karatun littattafan da ya sawo mini da fina finai. Maimartaba ya bada kayan itatuwa kwando kwando aka kawo tare da dumbin godiyar dawainiyar da ake da shi. Kullum idan Yarima bai kirani sau hudu biyar ba, ya kira ni sau uku karanci. Kamar daga sama ranar wata asabar, sai ga mahaifiyarsa da wasu barorinta guda biyu. Na ji dadin zuwanta sosai, saboda itace wadda ta fara kawo m8n ziyara daga bangarensa. Na zubo mata abonci dankayan makulashe, abin mamaki ta ci komai tana yi tana mini nasihar na rike mijina, kuma na dage da addu'a. Da za ta tafi na zubo mata dambun naman kaji cikin wata katuwar samira, sannan na kunso mata snack na ba daya daga cikin barorin na ce ta rike mata. Ta dinga yi min addu'a sannan ta tafi. Kwanan Yarima goma da tafiya ya yo mini waya ga shi nan zai hau jirgi yau zai dawo. Nan da nan na fara shirye shiryen tarbarsa. Ga mamakina har kusan karfe biyun dare ban yi bacci ba ina sauraron zuwansa, amma shiru! Na kira wayarsa sau wajen uku a kashe, hankalina yayi matukar tashi. Baccin da ban sami yinsa ba kenan har garin Allah ya waye. Da safen ma har kusan karfe sha biyu ba wani labari. Haka na ci gaba da aiki kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Ina cikin harhada kayan abincin maimartaba na jiyo alamun budewar kofa, da hanzari na fito. Ya shigo a hargitse kamar ba shi ba, gabana ya fadi, kada dai ace maimartaba ya rasu? Ya kamo hannuna idanunsa jawur, muka zauna bisa kujera. Humaira tare muka zo da Zarina, kuma yau maimartaba zai koma fada. Na saki ajiyar zuciya a hankali. To mene ne abin damuwar a nan? Na fada a zuci. Ya karkace kai kamar mai shirin yin kuka, ya ci gaba da cewa. A dalilin kyautatawarki da abin da kike aika masa tun zuwansa yanzu haka ya ce zai zo a yi miki godiya, kuma har da Zarina yanzu haka... Na dafe kirji tare da zaro ido ina shirin yin magana muka jiyo bugun kofa. Da sauri ya mike tare da lekawa, ya dawo da gudu. Wallahi su ne! Take na ce Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma laa sahlan illa maa ja'aktahu salan, wa'anta tij'alik hazna iza'shi'ta sahlan. Na je na bude ina kara karanta adduo'in neman sauki a kan duk wani tsanani a zuciyata. Su Umma ne a gaba kafin wasu dattawan mata gudu biyu, sannan shi maimartaba wasu manyan mutane hudu na bin bayansa. Sannan dogarawa, a bakin kofa dogarawan suka tsaya. Rakube nake jikin oofa, ban da kyarma babu abin da nake yi kaina kas. Kutumar uba! Aka biga wannan zagi da karfi, a firgicr na dago kaina. Ganin Gimbiya na yi kusa da ni da alama ita ce karshe wajen shigowa. Munafuka! Algunguma!! Kowa yayi cirko cirko tare da kura mata ido, amma ban da Umma da ta sami kujera ta yi zamanta. Da ma ke ce matar abokin Yarima yar iska? Makircin da kuka hada ke nan ke da uwarki? To wallahi ba ku isa ba, ina Yarima? Na rantse da Allah yau sai ya sake ki..... Ke wai lafiyarki kalau kuwa Zarina? Duk wannan cin zarafin da kike wa yar mutane na mene ne? Shin ko kin san dalillin zuwanmu wurinta kuwa? Cikin dattawan matan nan daya ta katse ta da fadin haka. Ta hankado keyata na yi taga taga zan fadi, kawai na ga mutum ya tare ni na fada jikinsa. Da sauri na kalle shi sai kawai muka ga maimartaba ya zauna a duke. Ganina jikin Yarima ya kara harzuka Gimbiya, ta fara zubda ruwan rashin mutunci ba tare da ta yi la'akari da wadanda ke wurin ba, tana fada wa dattawan kobji wace ce, saboda suna da masaniya kan maimartaba ya haramta aurena da Yarima ko bayan ransa. Sau biyu tana kawo harin za ta dake ni yana tarewa, ni kuwa banda kuka babu abin da nake yi, saboda tashin hankali. Ni ba na Gimbiyar ya fi damuna ba, irin hukuncin da maimartaba zai yanke a kaina kawai na ke ji. Wuri ya harmutse, fada tsakanin Yarima da Gimbiya su kuma dattawan wasu na goyon bayan Gimbiya su kuma dattawan wasu na goyon bayan Gimbiya, wasu na nuna cewa ba ta kyauta ba ta yi rashin kunya sosai, tunda ta aibanta Yarima gaban iyayensa. Duk wannan hargitsin su

Chapter 9 of 11