Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
in riga ki isa gidan mugani. Ya fita yana yar dariya, yau saida muka hadu da amira a hanya ta makara ni kuma nayi rana a gurguje muka gaisa ta wuce a kofar lungunmu na tarar da tankamekiyar motar mmk ya kamani wato da gaske yake zai rigani. Daga bangaren yamma a inuwa yake zaune da wasu jakunkuna manya guda biyar inna kuma na can gefe idanunta jawur da alama kuka tayi. Wata irin faduwar gaba naji wadda ban taba jin irinta ba na karasa gabanta na dafa guiwoyinta nace inna lfy? Me kayi miki naga idanunki sunyi ja? Ta kara fidda kwalla tace dinkuna ne yayo mana kowa akwati guda sai kayan kwalliyarki shima akwati guda tsoro +fargaba ya dabaibayeni da kalamansa tare da cewar kada mu butulcewa rahmar Ubangiji domin shima bayin kansa bane. Taci gaba da kwarar hawaye nima kawai sai naj kukan ya subuce min musmmn da aisha ta fara bude min kayan ina kallo. DonAllah inna kiyi hkr kinga har kin sa itama ta fara abnka da ruwa-ruwa. Ya mike na barku lfy inna danAllah kuyi hkr saina kara zagayowa ya fice. Mun dade muna sharbe kafin mukai kayan daki su aisha har an fara gwadawa da takalma kala 5-5. Inna ta kalleni humaira naso kama yaron nan akan abnd nake zargi amma saina rasa hanyar da zanbi sbd hausawa sunce idan baka iya kama barawo ba shi saiya kamaka. Kuma shirun nawa yayi amfani domin daga nasihar tasa na gane cewar haduwar jinin kawai da kuma tausayinmu da Allah ya dora masa. Tsoro na daya saka kayan nan mu shiga jama'a anya baza'a zarge mu ba? Kafin nayi magana mukaji sallamar baba Alh Sheetu inna ta amsa ta fito da sauri daman da hijabi a kanta. Duk muka fito ya kalli inna me kike nufi da hanamu albashin humaira ko kuwa kina tunanin zaki cinyesu ne ranar aurenta kibarmu da siyan kayan daki kinci bulus? Ya girgiza kai zaki dinga bamu rabi duk wata kuna amfani da rabi wann shine babban adalcin da zamuyi miki idan kuma kin amince zaki aurar da ita ne toh! Inna ta sunkui da kai a'a yaya ai bansan haka tsarin yake ba tuni na aiko bari na dauko maka, ta shigo daki bata ko kalli inda muke ba yace maza dauko tunda kinaso ki koyawa yarki son abun dunia shiyasa kika dage abar miki yayanki don kiyi jari. Inna dai batace komai ba ta mika masa 10k ba kunya karba tare da tusawa yace sun cika dama an fada mana 20 ne nayi ta mmkin ina yaji? Ya mika mata yar leda daga aljihunsa ungo goron sanya auren mansura ne wato yarsa sati 2 masu zuwa. Inna ta shigo tare da wasance maganar makarantar su sumayya. Batayi min zancen ba nima na tsuke bakina sbd munga abnd yafi hk. Da dadaare yaxo na tsinci kaina da faduwar gaba na fita da kwanon fura ba tare da nace ya shigo ciki ba sbd banason hirar ta dade kamr kullum jikin nawan ina jinshi wani iri. Muka gaisa nace ga fura. Ya karba amma yau kadan ya sha na maida sauran gida na dawo. DanAllah ka rage zuwa min dadare kaini ziyarar ma gaba daya kadaina idan baka iya dainawa ba. Sbd baki damu dani ba? Ya fada cikin yanayin takura nace a'a. Da kinsan abnd ya kawoni yau wllh da baki fada ba amma bakomai. Tausayi naji ya bani har saida idona yayi kwalla nace kayi hkri danAllah. Idan banyi hkri dake ba humaira ya zanyi? Damuwata na kawo miki kamr kullum su fareda sun hada min tuggu mai martaba ya kirani wai sati mai zuwa sunan nan tafe za'ayi bikinmu da gimbiya kuma ana gama daurin aure zamu tafi gaba daya zuwa yola. Gaba daya hanjin cikina suka kada take suka bada wani irin kara mai kamar sautin hadari. Ya matso gabana Humaira mutuwa zanyi banason yin nesa dake rabuwarmu zata zame..... Kwallar da nake makalewa ta zuraro kuka bazai yi mana magani ba ki bamu mafita domin nasan kinajin yanda nakeji karancin shekarunki da kuruciya zasu barki ki fahimci wani abu dake bin jininki... Kiyi mgn kada nima kiga nawa kwallar. Allah ya sanya alhairi na fada kamr me koyon mgn, ameen tunda kin ambaci alhairi saidai inaso kimin alkawari zanje nayi shawara da mahaifiyata idan ta amince zanzo in rokeki wani abu zaki bani? Na kalleshi nawa ne? Kwarai kuwa mallakinki ne har abada Nayi murmushi cike da kuruciya ko ince wauta nace ba komai ko menene tun a yau ba sai watarana ba idan mahaifiyarka ta amince ka dawo ka amsa ko kuma tun a yanzu na baka ka tafi dashi idan taki amincewa saika dawon dashi. Yayi murmushin dake kara masa kyau yace what a confidence' kawo hannunki, nayi hamzarin mika masa sai naga ya zura min manyan zobuna na gwal baki bude na kalleshi sai yace na alkawarine saina sadda kai kasa. Gobe zamuje Kd sai jibi zan dawo me zan siyoi miki? Nace bakomai ya watsa hannaye kinyi daidai gobe kizo da wuri don mu kara bankwana 7am zamu wuce nace to. Maza shiga gida banda tsawon hira kada a makara. Bacci da wuri bashi ke sa tashi da wuri ba sbd uwar makarar da nayi yau har tafi ta kullum ko wanka bansamu yiba kwaskwarima kawai nayi inata uban saurin na isa amma ina! Ana kokarin rufe get har sun dau hanya sai kurarsu na gani wani irin zazzabi naji ya rufeni inajin saukar hawaye a idona. Sashen gimbiya yau aka kiramu zamu kammala mata kaya tare da wasu shirye shiryen biki na tsinci kaina cikin rashin jin dadi ni kadai nasan yanda nakeji a zuciyata to meke damuna? Yaushe mukai irin wannan shakuwar da har nakejin haka a raina? Meyasa nakejin haushin gimbiya a yau? Wasa sabon aji sabo kuma tirken wawa bansan cewa na shaku dashi saida dare har kuka nayi acikin mayafina tsoro da fargaba suka rufar min na fara zargin kaina kona kamu da SON SA ne? Bani da yawan magana haka bani da kazar kazar sosai amma duk da hk saida inna ta tambayeni ko banijin dadin jikina ne? Shiru kawai nayi mata duk wanda ya ganmu a yanzu sai yayi mmki sbd sauyin da muka samu musmmn fannin cima da sutura yan unguwa sai gulmarmu suke kowa da abnd yake cewa wasu ma cewa suke sata nakeyi a gidan sarki tuni ftar jikinmu ta fara sauyawa ga cima me kyau ga sabulai masu gyara jiki. Washe gari muka shirya zuwa sunan gidan kawu mande nan mukaga jin zafi da bakin ciki karara babu kuma wanda ya kula. A gida bayan mun dawo inna ke shaida min wai ana gulmar yanzu maza nakebi nayi murmushin takaici. Maimakon yayi 2days saida sukayi 4days sannan suka dawo lokacin gidan ya kacame da hidima duk yan aiki sun hadu ba maganr sauyi gaba 1 muke haduwa sai maghrib muke tafiya ba muna can anata soye- soyenaji ana rade radin ya iso da bataliyar abokansa harda yan'uwansa ina jin ana nemana na boye bayan katuwar tukunyar kaji nida amira muka fito zamu tafi na hangoshi tsaye sai wurga idanu yake nasan ni yake nema saina dan boye. Abayantakwana 4 nan ya kara kyau da girma muka wuce bai ganmu ba amira tace min zakije party? Nace Allah ya tsareni. Amira ta tabe baki nima bazan je ba nace mata meyasa? Tace ina gudn dizgi da wulakanci kinsan halin gimbiya musamman idan ta ga jama'a nayi murmushi kawai a kofar gidansu mukayi sallama ina shiga gida na tarar da inna a tsaye a tsakar gida ko sallama ta bata amsa ba tace ina kikaje? Zuwansa 4 nemanki ba kyanan yace duk an duba gidan sarki ba'a ganki ba? Yar dariya kawai nayi haba inna da kinsan girman gidan sarki da bakice haka ba muna can wani bangare suyar kaji kawai mukeyi. Na mika mata bakar leda me dauke da soyayyun kajin da aka bamu nace inna aiki fa mukeyi shi kuma yana can ga abokansa shiru kawai tayi ta fitar da naman daga ledar na dauki cinya ina ci aka fara kiran sallahr maghrib nayi saurin cinyewa na tashi na gabatar. Na hada goldenmon ina sha kenan naji ana sallama a tsakar gida Aisha ta leka naji tana cewa la yaya sannu da zuwa gabana ya fadi inna ta kalleni nayi saurin tashi sbd nasan ma'anar kallon koda ya ganni sai yayi baya kofar gida ya tsaya inda muka saba. Yace fushi kikeyi dani humaira? Nayi shiru kiyi hkri wllh gida na koma na kammala wasu abubuwan kuma mamana ta amince nazo na amshi alkawarinmu. Kafin nan ina son ki shirya zan aiko a daukeki ko inzo da kaina mu tafi gurin party ko bazaki halarta ba? Gsky ban zuwa, me yasa? Hakanan, wllh baiyuwuwa duk mai hnkli bai wani abu saida dalili. Yace shikenan dauko min tabarma nima ban zuwa na kalleshi da mmki yayi murmushi wllh idan ba zaki ba nima ban zuwa dama tilastani akayi. Na rasa yanda zanyi da rigmarsa kullum da wacce zai bullo nace muje ka tambayi inna, da mmkina inna tace a dawo lfy muka fito yace ki saka leshin nan ja da takalmi silver kinji? Na daga kai, zan tafi saina dawo anjima nace to. Ni kadai nake bidirina a daki inna tana tsakar gida ina kwalliyata harda ta saman gira na feshe turaruka na fito tsakar gida inna ta kalleni ido waje tana mmki wann kwalliya haka humaira anya baki wuce gona da iri ba? Na yi murmushi, nace. " Inna ban yi kyau ba? " " kin yi kyau, amma kmr tayi yawa".Na zumbure baki da fadin. " wlh inna haka ake yayi".Ta harareni, "Ina ruwan ki da yayi? kin ga wlh ki dunga tuna matsayin ki, kada ki janyowa kanki damuwa".Shiru kawai nayi. karfe 9 naji ana sallama, na kalli inna. " zamu tafi, Ina jin shine ya aiko".Ta ce a dawo lfy, Allah ya tsare".Na ce "Ameen". Har na Kai bakin kofa, tace."kada ki wuce 11 dk abinki"."INA". na ce tare da ficewa. Sbd tsinin tklm ga rashin sabo sai na dinga takawa a hnkl kada na fadi, ckn direbobin gidan sarki na gani da alama bai ganeni ba. Motoci 4 na tarar a jefe, ya bude min Wacce tafi ko Wacce kyau da girma, na shiga Ina addu'ar neman tsari kmr Klum idan na baro gida hk ya zame min tamkar sallah. Yana rufewa naji an janyo ni a tsorace na kalli gefena, sai kawai naga Yrm. Kunya ta kamani, na ce, " Ba ni na gyara".Ya sakeni na matsa nesa da shi Ina fadin. " Ban son haka, don Allah ka daina".Ya yi murmushi, sai ya matso na kara takurewa ya ce. " kin yi kyau kmr ruwa. Cire 'yan kunnen na baki sarka".Ya fada yana laluben aljihunsa. A ciro bakaken 'yan kunnena dk sun yi baki sbd tsufa. Ya miko min wata dankareriyar sarkar zinare da 'yan kunnen ta.Na make hnn, "kayi hkr bazan karba ba, sbd wdnn zobunan ma inna tayi mini fada sosai"."sanya aro na baki ba kyauta ba, zan karba idan mun dawo".Jin haka na Sanya. " Ina alkawarin mu?"Na yi murmushi, " ya na nan"."Zaki bani ynz? ""Idan kana ganin Ina da shi a nan din".yayi 'yar dry, " Ai ko Yaushe kina tare da shi".Na ce, " Bisimillah".Ya yi Kasa da murya, "kada ki manta kin fa mallakamin tun kafin ki san ko menene".Na yi shiru kawai. Ya kama hnnyna duka biyun. "Humaira Ina barar soyayyarki, don Allah". A firgice na kalle shi daidai lkcn mota ta tsaya. Harabar wurin dankam da jama'a duk hankalinsu kuma ya dawo ga motocin da suka tsaya lkc guda. Dogarawa suka rugo suna bude mini kofa, ta kowane bangare barori kuma na watsa filawoyi. Abokansa suka rufa mana baya, naja tunga da sauri na tsaya, suka yi gaba. Wuri na nema na tsaya kusa da wata mota zufa kawai ke tsatsagomini ta ko'ina. Na kasa fassara yanayin da nake ciki.A hnkl naji an dafa kafadata, kafin na dago naga an zagaye ni. Na kalli sauran abokansa, nayi Kasa da kaina. " she is pretty".Na ji wani ya fada. Na kusa da shi ya ce."Akwai class I see".A hnkl yace, "Humaira mu je ki bani kwarin gwiwa, wlh bana son partyn nan ". wani ya matso, "kada ki biyewa zcy Humaira, ki tallafawa mai kaunar ki kada ki jefa shi...""kan uban can". Na ji saukar uban zagi kmr daga sama, ckn karaji Gimbiya ce tsaye tana hura hanci gefenta kawaye da sauran barori na kewaye da ita. Na zaro ido Ina yin baya- baya ckn matsanancin tsoro da firgita. " Ni Zaka ciwa mutunci? Ni zaka kunya ta a gaban jama'a ka rasa Wacce zaka hada sonta da nawa sai BAIWATA? Dama duk zame-zamenka a nan ka sauke? Haba biri yayi kama da mutum, ban manta abubuwan da suka ringa faruwaba, sai dai ka haddasa mata fitina, bala'i da tashin hkl ita da iyayenta a garin KANO!" ji kake tas! tas!! mari na wanke fuskarta ko ta Ina. " shut up! Idiot! " Ya bita da wdnn kalmomin, "kin isa ki yi abinda Allah bai nufa ba ne? ko kina ganin za ki iya hana abinda Allah ya hukunta?" To bude kunuwanki kmr ydd na sha fada miki, ba ki daga ckn tsarin matan da nake muradin aure.Bacin hadin iyaye babu abinda zan yi da ke a AURAKA! snn ki sanya wa ranki cewar Zaki yi kishi da baiwar da kika raina a kirata da GIMBIYA kmr ydd kike takama da sunan".Ta fashe da kuka, abokansa suka janye ta suna bata baki, amma har lkcn bata bar fadin, " ita ka cusawa wnn bakin cikin, wnn zan bambance muku MULKI da TALAKA sai an batar da su a kasar nan! !" Yunkurin cafkota yake yi ana rike shi, sauran abokan suka yi min zobe ganin Ina da niyar kwasa a guje. Tashin hnkln ya hana ni kuka, zcyta ta daskare kmr dutse, na kalli wnd ke bangaren damana ckn wani irin yanayi na ce. " ka taimakeni ka maidani wurin inna".Ya juyo da sauri jin muryata, hnn ya kama zamu bar wurin. wdnda suka janye Gimbiya suka tare mu da sauri. "Haba, Ina kuma zaka je kana ganin mun shawo kan Gimbiya? sauran 'yan korenta mun ja musu kunne su yi shiru da bakinsu".Ya kalle su, "Ba zan attending ba..." Suka rufar masa kowane da abinda yake fada, da kyar suka shawo kansa. wnd naji ya kira da suna sahabi ya karbi mukullin hnnsa zai mayar da ni gida, har mota ya Kai ni, snn ya saki hnn yana fadin "komai dare zan zo, kada ki yi bacci kin ji?" kmr na wawuro fuskar in cije don takaici, me kuma zai yi mini? wane bacci gare ni Ina ckn wnn tashin hnkln? A daidai Lungu ya tsaya na fita da sauri Ina jin yana cewa. " Mu kwana lfy ". Amma na yi kmr ban ji shi ba, zaman da na yi dabas ya sanya ta kalle ni da sauri, "Lfy? ""Da sauki inna ". Na fada ina rike kaina."Me ya faru? "Ta bukata a rude. Na zayyana mata komai. Ga Mamakina sai na ga ba ta wani razana ba, ta ce. " Ni dama na yi zargin haka tun farko, ganin cewar bai furta da bakinsa ba ya sanya na yi shiru, sbd maganar Hausawa idan baka iya kama barawo ba shi sai ya kama ka. Ba zan yi saurin cewa ba zai yiwu ba, sbd ba mu san hkncin Allah a kan lamarin ba, kada mu yi masa shishshi har mu saba masa. Amma da kmr wuya BAIWA ta auri DAN SARKI, kina karkashin mulkin gimbiyarsa". Na rike kaina da ke fizgawa tmkr zai bar wuyana tare da runtse ido, ba wai son shine ba ni yi ba, a'a ina hangar wa kaina tashin hnkln da ke gaba. Kmr inna ta karanci zcyta ta ce. " ynz kam dole runtse idanunmu, mu kuma toshe kunnuwanmu akan abinda zai biyo baya. A gaskiya zan roki yaron nan da ya janye bukatarsa abu ne mai whl ya rufa mana asiri, ya dubi maraicinmu". sai ynz kuka ya zo mini. Ta kalle ni. " ynz kika fara hawayenki su kare a banza, ko ki janyowa kanki wata matsala" "Ban katse ka ba, ina son ka gane abu guda. Yrnyr nan marainiyace, ka ga kuma ydd muke ba Wani boye-boye ynz, don hk son da ka ce kana yi mata to ka nema mata kwanciyar hnkl a rayuwarta. Gsky kayi hkr, wlh ba zan baka Humaira ba, sbd ka fi karfinta, ba km daya kukeba kai ni Ina shakkar son da kake yi mata da mamaki".Ga mamakin inna ta ga ya zube gwiwa bibiyu yana kwalla. " Haba inna, kada ki yi jayayya da ikon Allah mana, akwai wnd ya fi wani ga Allah ba ya ga mai tsoronSa? shin ya tsoron Allah ya ke? yin tawakkali da yrd akan dk abinda ya hukunta".Tausay insa ya far mata, sai kawai ta sunkuyar da kai. " Na amince, Allah ya yi mana jagora".sauran kwalln sk shatato masa."Nagode inna, Allah ya kara girma, ya kuma bani ikon rike Humaira bisa yrd da aminci". Yace ameen ya mike Zan koma sbd nabar gida kamr sansani yanzu abokaina basu sami runtsawa ba tace Allah yai mana jagora yace ameen. Har ya kai bakin kofa ya waigo donAllah Inna ku toshe kunnuwanku da duk maganganun da za'a zo muku dasu tace ISA ta fada tana mikewa shi kuma ya fice yana fadin zan dawo anjima idan humaira ta tashi. Kwalla ta zubo min burinsa ya cika ya rabani da aikina, motsin inna naji ta sassauta murya ki tashi wann kwanciyar bata da wani amfani a gareki. Ba'aja da ikon Allah sbd har abada bazan mance alhairin yaron nan ba sanadiyarsa ina neman rasa cutar tun shekaru masu yawa nake fama da ita tun magungunan da alluran da yayi min bai kara tashi ba. Na fahimci Allah ya dasa masa kaunarki matsayinsa yafi gaban ya zubda kwalla akanki ko yaudara yazoyi zan iya mallaka masa ke sbd yaudarar tazo cikin tsafta sai gashi ya tsugunna a gabanki ni mahaifiyarki yana kuka yana rokon amincewata kina tunanin Allah bazai kamani ba da alhakinsa? Ko kuwa mun yaba kyautarsa kenan? Ta girgiza kai tunda fahimci kyautar da yake mana wllh zan jure duk wani wulakanci da cin mutunci kema sai kin jure sbd bayan wuya sai dadi. A matsayina na mahaifiyarki humaira yanda nasanki da rashin sun magana tashin hankali da sauransu ina jiye miki kishi da gimbiya. Sai a lokacin kuka kuka yazo min da karfi na dinga sharbe harda majina Ta girgiza kai yanzu kika fara kuka dama kin daina wahalar da hawayenki a banza sbd yanzu aka fara bamusan abnd gaba zata haifar ba. Mutane muka hango a tsakar gida ai bansan yanda akayi na ganni a kofar daki ba hanjin cikina suka kada waya nunawa gimbiya gidanmu? Na fita daga kofar dakin ganina ya kara mata bacin rai. Don ubanki ina kazamar uwarki? Yanda tayi zagin gabana ya kara faduwa anya zan iya dauke cin mutuncin iyaye? Yana iya dama inna tace saina jure. Motsin inna naji a bayana tana cewa ganinan... Ta nunata da yatsa ba asiri ba wllh ko tsafi kike da bakar jaba yarki bazata auru ba munafuka. Tsautsayi yasa inna ta matso tana bata hakuri ta kuwa kundumo mata wani mugun zagi ba tare data girmamata ba. Zan nuna miki cewar sarki da talaka akwai bambanci sai kun raina kanku a garin nan shegu MATSAFA! Maganr ta daki zuciata anya zan iya shanye wulakancin su? Magnr ta tunzuro hrt dina tsanarsa ta bijiro min don shine musababbin karar marurrukan dake sauka kuncin inna yasa ta tangal- tangal nayi saurin riketa gabana yana faduwa kada ciwonta ya tashi aiko nan da nan ta fara shessheka ina kokarin zuwa dauko mata magani naji gimbiya na cewa a dakemu. Kota ina duka mukeji maza da mata su Aisha sai kuka sukeyi ganin an hada mana jini daga ni har inna niba dukan ke damuna ba ciwon inna kada ya galabaitar da ita amma rashin imani da tausayi baisa sun kyalemu ba saida muka matukar galabaita tuni inna ta sume rai yana kokarin fita ganin haka suka fita daga gidan jini yana fita a hannuna da goshina Na rarrafa na dauko mata maganin su sumayya suna watsa mata ruwa ina shaka mata maganin. Cikin ikon Allah ta farfado amma hannunta yaki motsawa, ihun su Aisha ya tara jamaa lokacn su gimbiya sun tafi abinka ga safiya ba kowa ya fito ba mal bala ya kalli hannun yace kamr karaya? Inna ta rintse ido mike cikin radadi suka kamata hannun yayi baya sai kawai ta zube tare da yin wata kara nima na kurma ihu na tallabeta jamaar gurin suka rude wasu suka ruga kiran mai dori kafinsu dawo mukaga bataliyar abokansa tun daga waje suka gidan dankam da mutane suka karaso a kidime basu jira komai ba suka dauki inna sukai asibiti da ita tuni ya tasa keyar su Aisha dama ni tun shigowata ya rike hannuna ya cika da tambayoyi. Bani iya masa fitsara dana gwada masa yau, kafinmu isa zazzabi ya rufeni ruf. Ni asibitin ma tsoro ya bani sbd kyaunsa nan da nan aka shiga da ita tiyata ni kuma aka bani daki da gado allura 2 akayi min sai magunguna da nasha shiys dressn din da akayi min banji zafi ba ita kuwa inna gurin kare dukan ne suka karyata kai Allah ya isa! Bacci ya daukeni wasan kusan 3 na farka gadon da ke kallon naga inna kwance itama tana ta sharar bacci. Su Aisha da abokansa suna zaune shi kuma yana tsaye ya jingina da bango ya harde hannuwa. Gaba 1 suka taso zuwa gaban gadon nayi saurin rufe idona sbd wani abu danaji yana harbin zuciata. A hnkl naji ana mgn kusa da fuskata kiyi hkri ki tashi kiyi sallah tym yana wucewa komai yayi zafi mgninsa Allah! Da sauri na bude ido jin muryar sadauki ya kada min kai ya kalli yarima ya maido kallonsa gareni muna tausaya muku anci zarafinku kuma zamuyi saurin daukar mataki wannan cin mutnci yayi yawa they have crossed their limit! Ga maganarsa ga kuma sannun da sahabi yake min narasa wanne zan saurara yarima kuwa har tym din ya kasa cewa komai da alamu ni yake kallo amma na kasa bude idona na ganshi Bayan nayi sallah suka fitineni saina ci abnc saida na cusa kadan. Sahabi ya kalli sadauki yace muje ko? Yace su Aisha muje waje muyi kallon haraba...... Turo kofar da akayi ne yasa maganr ta makale saura kadan na kwasa da gudu wata shamkiyar mata ce ta shiGo da dogarawa 4 a bayanta kallo 1 zaka mata kagane fuskarce bambancin tana mace yana namiji. Sadauki da sahabi suka zube a kasa suna barka da yamma Mama. Nayi saurin sunkui da kaina inajinta amsa kasa-kasa a tym din ya taho daga tsayuuwar da yake sai kawai ya fada jikinta baice komai ba ita kuma tasa hannu tana dan bugun bayansa alamar rarrashi, ta janyo hannunsa zuwa bakin gadona ga mmkina saita zauna kusa dani shi kuma ya zauna muka sata a tsakiya. Nayi saurin sauka kasa na zauna kusa da kafafunta. Sai naga dogarawan sun fice da alama umarni ta basu. tace dawo ki zauna nan ta nuna inda na tashi na girgiza kai kawai ina mmkn zuwanta a wnn tym din. Tayi shiru kamr yanda dakin ya dauki shiru cikin dabara sahabi ya fiddasu sumayya sanna ya dawo ayi komai a gabansa. Ta gyara murya toni yanzu mezanyi mk Hameed? Kamr yana jiran tambayar ne ya kalleta ido jajur cikin damuwa yace Mama duk duniar nan baya ga Allah banida wani gata saike ki dubi girman Allah zucita tana cikin tsananini ki rabani da wann auren na gimbiya bani kaunarta da duk wanda ya shafeta... Ta katseshi Bazan iyayi maka wann alkawarin ba sbd mai martaba ya bar wasicci ko bayan ransa idan baka auri farida ba bai yafe ba. Ya sassauta murya mama yarinyr nan bata da hnkl ki dubi inna... Sun karyata sannan dubi raunukan da sukaji mata ita da humaira shin Sarauta hauka ce mama? Ni nace inason yarnyr nan wllh har yanzu ban sami wata amsa dg gareta akan abnd tayi musu shin meyasa zucoyata bazata buga ba? Kina ganin wanda yayi wann aika-aikan bazai iya kisan kai ba? Kafiya gareka Hameed ina jiye maka fushin mahaifinka kana sane da cewa bazai amince maka ka auri wacce ba jinin sarauta ba gaba na ya buga da karfi taci gaba da cewa... Zuwan nan kadai ya fahimtar dani wani abu wllh na yaba da kunya nutsuwa da kuma hnkl kana da tabbacin kai sarki yabar wasiccin ka gajeshi idan ka tsaya akan wann ra'ayin lallai sarauta zata bar hannunka har abada. Wani abu naji ya tsikareni jikina yayi sanyi lakwas. Mama ya kira sunanta cikin wani ayanayi ta amsa ta kalleshi cikin jimami, duk dunia ba wanda yasan damuwata halina da kuma al*amurana kamar ke sbd ko tari nayi ko a bayan idonki saina sanar dake dn hk nakeso kibani mafita ayau wllh mamana zuciyata tana min zafi. Ina kallon sadauki ya matso kusa dashi ya dafa kafadarsa daidai tym din inna ta farka na mike zuwa gareta amma saiya rigani. A hnkli mama ta iso inna ta kallemu sai tayi smiling. Sannu ya karfin jikin ne? Mama Ta fada tana kallon hannu daya karye, da sauki ta fada tana kokarin tashi muka kamata har maman ta zauna saman gadon ganin hk yasa na koma na zauna yana ta koakrin mu hada ido amma naki. Mama ta dafa hannunta sannu inna, murmushi kawai tayi. Ganin hk ta fara magana donAllah kuyi hkri an zalinceku an shiga hhakinku amma danAllah kuyi hkri. Inna tayi shiru ta kauda kai, bazan gaji da baku hkri ba wllh inajinku har cikin raina domin duk abnd Hameed zai so ina son shi kamr yanda nake kin abinda bayaso. Nayi farin cikin ganin Hameed ya sami wacce tayi masa kuma ya furta yana kaunarta da bakinsa. Abnd na dade ina mafarkin gani yau gashi Allah ya tabbtr min dashi sbd kowa yana tunanin ko bashi da lfy ne baligi kamr sa ace baisan SO ba kullum sai yace bai sami wacce tayi masa ba don har dariya mukeyi masa tare da yan'uwansa idan yana suffanta yanayinta. A gsky na gasganta halayen Humaira dan zuwan nan da nayi nasan Hameed nice mahaifyarsa nasan kuma wayeshi wllh bazan taba jayayya da kaunar da yake mata ba nasan na gsky ne daga Allah. Kamr yanda nayi farin ciki ta wani fannin kuma ina bakin ciki sbd lokacin daya tsinci kansa cikin kaunar wacce yake mafarkin samu a lokacin ne mahaifinsa yasha alwashi akansa. Nasan halin mahaifinsa da tsatstsauran raayinsa akan duk abnd ya zartar mutum ne me zafin gaske me kishin sarautarsa baya kaunar talaka ya shigo masarautarsa da sunan haduwar jini duk kaunar da yake wa dansa zai iya yafeshi akan wann. Bani ba har inna saida ta razana da wann maganar a hnkli na zame na sulale kasa jikina ya dauki zafi sosai. Taci gaba da cewa shiyasa ayau abun ya daga min hnkl sosai jin kalaman da yake fada min a waya nasan zai aikata abnd yake fada. Ta kalli inna kaunar da yakewa Humaira ya zarta tunani amma ina da wata shawara guda, mu duka mu dage wajen fadawa Allah yanda ya hada wannan soyayya da yardarsa zai warware komi cikin sauki idan abun zaiyuwu yafimu sanin tsarin yanda zaiyi haka idan bazai yiwu ba. Ta dafa kafadar inna danAllah muyi hkri wata rana sai

Chapter 5 of 11